Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da Ahmed da yanayin sa ya d'an yi murmushi yana girgiza kai cikin tsokana yace. "Ahmad please ara min wayar ka zanyi amfani da ita yanzu tawa banyi mata chaji ba tun jiya". Da sauri Ahmed ya d'ago ya kalle shi dan yasan bom yake son had'a masa kafin ya kalli Abban su da shima ya d'ago yana kallon shi yace. "Yayanka ba magana yake maka ba ka bashi waya kayi shiru kamar sabon kurma". Rasa abin cewa Ahmed yai sai ido kadai daya zubawa prince Hamid wanda ya kauda kansa yana dariya kasa-kasa. "Hummm bros Hamid is so funny............. Jin Abba yace "Ahmed". "Na'am Abba". "Meke damun ka ne"?. "Babu komai Abba". "Babu komai kayi shiru ana maka magana"? Hamid meke damun sa"?. Gyara zama Hamid yai jin anzo daidai wajen da yake so azo yana kallon Ahmed dake masa magana da ido yai kamar bai ganshi ba. Yace "Abba banace ba amma inaga shida Baby ne". Zaro ido Ahmed yai yana kallon Hamid daya sakar masa hararar gargad'i sannan yaci gaba. "Abba akwai abinda ke damun Ahmed saidai bansan maye ba amma shi Ahmad d'in ya sani ya'ki fad'a". Wani kallo Abba yaiwa Ahmed yana cewa "AHMED what your problem"? Kasa cewa komai Ahmed yai sai bin kowa da kallo da yake har ya dawo kan Abban. Mamaki ne ya kama Abba amma sai yace "shikenan ka samu nutsuwa daga baya zan tambaye ka saika tanadar min cikakkiyar amsa yanzu inada gurin da zanje ina Zuhra da Ummul-khairi suke ko a part Ashraf suka kwana naji banji motsinsu ba"?. Kai prince Hamid ya d'aga "eh Abba suna can". "Ok shikenan Ahmad kai kuma zan dawo gareka" yana fad'in haka ya mi'ke momy ta rufa masa baya zuwa rakiya ina motocin dukkan masarautar suke. Ganin saura su biyu yasa Ahmad ya hade rai yana cewa. "Meyasa zakai min haka gashi yanzu ka jefa ni cikin risky". Ta'be masa baki prince Hamid yai yana cewa "Ba wani risky dana saka ka meyasa kaima ka kasa yiwa Abban bayani saboda ka daki 'yar lelen shi da ya sani da kaima ka samu rabon ka". 'kara hade rai Ahmed ya kuma yi "oh wanne irin rabo kenan zan samu"?.. "Kafi d'an dako sanin tasha saidai ya fika d'aukar kaya Allah yasa babyn su had'u da Abba koda a gurin Sultan Ameer ne aikaga asirin ka ya tonu abinda kake 6oyewa Abban zai gani ko bata fad'a Ahmad saina fad'a ko baka so kai mugu ne na ajin 'karshe". Mi'kewa Ahmad yai zai fita yace "ai baka sani ba Abdul-hamid Aliyudeen Sharfaddeen isa nai muguntar ma iyawa ce idan wani ya isa shima yayi" yana fad'in haka ya fita a parlon d'aga murya prince Hamid yai yadda Ahmad d'in zai jiyoshi yana cewa. "Zakaga mugunta iyawa ce wallhi so kake nasa a hanaka yarinyar nan in nuna maka qarshen mugu haba mutum sai zalunci da zafin rai kamar wani wuta kodan dama haka ka tashi tun kana yaro 'ya'yan bayi ma sunci duka hali ne a jikin rai tunda haka kake bazaka ta'ba canzuwa ba" shima prince Hamid d'in mi'kewa yai da lap Cort a hannunsa ya fita a parlon. Mami tana zaune Sultan yana kusa da ita kuma dama shagwa'ba yake mata ganin Ahmad ya shigo yasa yai sauri shiga hankalin sa yana daidaita kansa yace. "Good morning yaya"?. Zama Ahmad yai yana kallon sa batare daya amsa ba yace "uban me kakewa shagwa'ba"?. 'Dan zaro ido Sultan yai yana soshe soshe yace "uhmm uhmm". "Uhmmm me bana son shashanci so kake yanzun nan jikinka yai tsami Mami miyake nema bai tafi school ba sai lokaci ya fita". Murmushi Mami tai tana cewa "waifa jiya ne ya tafi da tart makaranta yaji dad'in sa shine yace yauma saiya tafi dashi nace masa ba kamar indomie ne ko meat pie da za'ayi a rana daya baya amma ya d'age sai shagwa'ba yake zubawa harda shura qafa kodan yaga ya girma baida qani ne oho masa" Mami ta qarasa maganar tana shafa gashin kan Sultan wanda yai wuqi-wuqi yana d'an satar kallon Ahmad daya had'e rai yana cewa. "Oh har yanzu bakai hankalin da za'a fad'a maka magana kaji ba tunda bazai yuwu a yau ba why not ka ha'kura zuwa gobe ko wani abu zai haifar ma idan baka ciba"?. Shiru Sultan yai ya kasa cewa komai sai addu'a da yake Allah yasa kar hakan dayai ya zama laifi "get lost" yaji muryar Ahmad aiko da sauri ya mi'ke kamar zai kifa yai hanyar fita dakatar dashi Mami tai. "Sultan dawo ka manta plantain mosa d'in naka ko ka fasa tafiya dashi"? Eh kawai Sultan yace sama sama bai tsaya ba hai yake ya fice saboda tsoron karma ya tsaya ya jawa kansa laifi tunda Ahmad yazo. "Kaii dawo ka d'auka". Cak ya tsaya waje daya cikin firgice ya juyo yana kallon Ahmad muryarsa ya kasa fita balle ya iya furta kalmar ya fasa tafiya dashi...................... "Me kake kallo ne dawo ka d'auka nace kada ka bari in tashi a kanka". Jin abinda Ahmad yace yasa da sauri Sultan ya dawo yana ra'be ra'be ya matso a hankali yana kallon Ahmad dan abun na kusa dashi gani yake idan yazo d'auka zai rikeshi da 'yar sand'a ya yasa hannu ya d'auka da gudu kuwa ya juya faaaaaaaa🏃🤣 ya fice daga part d'in wanda yasa dole Mami tai dariya ai dama Ahmad d'in ne daidai dasu tunda prince Hamid bamai zafi bane Shadat ne d'an uwan Ahmad kuma baya nan sai ranar daya dawo shima haka yake da zafin rai.............................. Hankalin Ahmad ya mayar kan Mami yana cewa "barka da safiya Mami fatan kin tashi lafiya"?. Har lokacin fuskar Mami da fara'a tace "lafiya qalau na tashi Ahmad ya kake ya gajiyar zama wuri daya dan nasan yanzu a takure kuke ku sojoji kun saba rai da rai kuna tsinka jinin jiki idan kunzo hutu kuma ba wani abu zakuyi ba duk sai kuji ku a takure". Murmushi Ahmad yai yana kallon ta yace "ai Mami duk wanda ya saba da aikin ko zaman awa biyu yai batare da yayi wani abu dazai motsa jikinsa ba duk sai yaji babu dad'i shiyasa na dau qaramin hutu da wuri zan koma". "To Allah ya taimaka Ahmad Allah ya fitar daku aikin nan lafiya". "Amin Mami ina baby da khairat ko ba anan suka kwana ba"?. "Kaita d'aga "eh anan suka kwana domin da asuba na buga musu qofa su tashi suyi sallah kuma ko sun tashin Allahu a'alam inaga barci suka koma". "Ok" Kawai yace yana mi'kewa yai hanyar bedroom d'in a qanqame yaji qofar sun saqace ta taciki bugawa yai da qarfi batare dayai magana ba jin shiru babu ko motsi yasa ya qara bugawa still baiyi magana ba juyi Khairat tai tana jan tsaki ta sake sabon kwanciya daidai an qara bugu mai qarfi fiya dana baya a hasale ta tashi zaune tana cewa. "Sultan dallacan meye haka idan baka bar bakin kofar nan ba saina fasa maka baki idan ka bari na fito banza kawai". Jin abinda tace yasa Ahmad ya jinjina kai yana cewa "Ok fito ki fasa min bakin, zaki bud'e ko saina 6alle murfin kofar na shigo naci ubanku ashe dama barci kuke baku tafi school ba yau sai jikinku ya fad'a muku". Zaro ido waje khairat tai cike da tsoro domin yanzun kam ta fahimci waye d'ora hannu tayi aka tana cewa "nashiga uku dama ya Ahmad ne jin ya sake bugawa yana daka tsawa yasa a firgice tace "baby baby tashi yau za'ai farfesun mu yau mun kad'e har ganyen mu" ta qarasa maganar tana girgiza Baby wacce ke barcin ta hankali kwance batasan meyake faruwa ba jijjiga ta tayi da qarfi tana cewa. "Baby ki tashi dan Allah masifa cefa ta tunkaro mu wacce bamu da maganinta sai Allah ba lallai muga gobe ba". Bud'e ido Baby tai cikin muryar barci tace "Aunty Khairat lafiya kike tashi na"?. "Inafa lafiya Baby ya Ahmad ne yake buga mana kofa yanzu na d'auka Sultan ne nace zan fasa masa baki yace na fito na fasa masa yana jirana". Jin abinda Khairat tace yasa Baby tai cilli da bargon data lullu'ba gefe tana tashi zaune a rud'e zatai magana suka ji qarar 6alle kofa kafin su farga sai gani sukai murfin ya fad'o ciki, cikin 6acin rai Ahmad ya shigo zabura sukai a gigice musamman Baby da bata warke daga dukan dayai mata jiya ba tsayawa yai a bakin kofa yana kallonsu su gama iskancin rud'ewar yana daidai dasu ganin sun rikice sosai yasa ya buga musu tsawa....... "Uban me ya hanaku zuwa school yau, raini ko"?. Da sauri khairat ta girgiza kai tana cewa "wallahi ya Ahmad a'a ni bani da lecture da safe sai karfe uku zan tafi". Maida da kallonsa kan baby yayi wacce ta gama haukacewa domin ita bata da hujjar kin zuwa yace "ke kuma fa uban me kika tsaya yi baki tafi ba". Kuka kawai baby ta saki na tsantsan tsoro jikinta sai rawa yake ta kasa magana cikin tsawa yace "uban me ya hanaki zuwa school yau baby"?. Yana rufe baki ta d'ora hannu aka a gigice tace "yaya wallahi bana jin dad'i ne da zazza'bi na kwana". Wani kallo ya mata tare da jinjina kai yace "ku biyo ni" juyawa yai yana fita a rud'e suka mi'ke suna bin bayansa Mami dake zaune Ahmad yazo zai fita yana cewa "ki huta lafiya Mami". "Ok Ahmad nagode sai anjima" ta karasa maganar tana binsu khairat da kallo Wanda babu me cikekken nutsuwa a cikinsu hum tasan za'ai haka dama tunda naji qarar 6alle kofa tasan basu suka tashi suka bud'e masa kofa ba karyawa yai ya shiga aiko yau sun shiga uku. Yana tafe suna binsa a baya har part d'insa yana shiga ya wuce bedroom ya barsu a falo kowa hankalinta a tashe sun dad'e bai fito ba harsun d'auka ma koya manta dasu ne can suka sake jin qarar bud'e kofa ya fito yana gyara allura zaro ido baby tai a firgice tana fad'in innalillahi badai ita zaiwa allura ba............. "Ke zomin nan" taji muryarsa a susuce ta fara zubar da hawaye kuma ta kasa d'aga qafarta balle taje. "Baby kada ki bari na tashi a kanki"?. Jiki na 6ari ta fara takows zuwa inda yake kafin ta sake ja ta tsaya tana kuka tace "dan girman Allah ya Ahmad kayi ha'kuri" tana rufe baki ya mi'ke yana tasowa inda take aguje ta juya zata fice ya dam'kota yana matseta a jikinsa da yadda ko motsi batai masa sannan ya juyata yayi mata allurar humm tsabar tsananin kuka daya ci qarfinta har shid'ewa take wulli yayi da sirinjin yana zama akan kujera ya d'ora kafa d'aya kan d'aya yana kallon ta yace. "Can you be quiet or not"?. "Idan baki rufa min baki ba na tashi sai jikinki ya fashe tsabar duka". Jin abinda yace yasa dole da sauri ta had'iye kukanta tana na zuci kallon Kharat wacce ke qame guri d'aya yayi yana cewa "ba baki da lecture ba? Sai qarfe uku kince, saiki wuni zuwa Nan da qarfe ukun kina karbar hukunci kinga gaba ranar da baki da lecture bakiyi barci ba saiki dau littafi kiyi karatu fara frog jump" yana rufe baki da sauri khairat ta ri'ke kunne ta fara zaga falon wani kallo yaiwa baby yana cewa "ke me kike jira, ko allurar batai miki ba zazza'bin bai sauka ba" jin abinda yake fad'a yasa baby da sauri ta girgiza masa. "Ok fara up and down". Innalillahi up and down kuma nashiga uku yaya kashe ni yake son yi............ "Tunanin uban me kikeyi". Baby batai aune ba taji saukar duka a bayanta a hargitse ta fara abinda yace mata yana zaune yana kallon su kowa kuka take tsabar wuya gashi babu damar d'an tsayawa su huta daga wannan su koma wannan iya gala'baita sunyi saida ya tabbatar yadda jikinsu zai fad'a musu sannan yace su tsaya haka tsayawa sukai da'kyar suke iya jawo numfashinsu kai ya jinjina yana cewa. "Get to the point gobe ma ku kwanta kuyi barcin safen Ina daidai daku get of my sight" yana rufe baki har gware suke waje gudun fita kowa jan qafa take musamman baby da bata da lafiya har juwa ke dibanta suna shiga parlon Momy kuwa ta yanke jiki ta fad'i qasa bata ko motsi subahanallahi da sauri khairat ta dur'kusa tana jijjiga ta daidai Momy ta fito tace. "Innalillahi khairat meya samu babyn kuma yakai ta fad'i"?. A rikice Khairat tace "Momy baby bata da lafiya da zazza'bi ta kwana dan Allah ki kira ya Hamid yazo ya dubata". "Hamid ya tafi hospital bari naje Ahmad ya kirashi waya na network d'inta ya sauka " Momy ta fad'a tana ficewa mi'kewa Khairat tai ta nufi frigde zata d'auko ruwa ta shafawa babyn amma me itama tana mi'kewa juwa ta debeta ta fad'i a gurin, tare da Ahmad Momy suka shigo ganin itama Khairat d'in ta fad'i yasa hankali tashe Momy tace. "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un meye yake damunsu ne kodai sunci wani abu me guba ne"?. Shiru Ahmad yai ya zuba musu ido yayin ta Momy ta shiga kai komo a parlon hankalinta inyayi dubu ya tashi har Hamid ya shigo Shima dai babu nutsuwa a tare dashi ganin ba iya baby bace harda Khairat yasa mamki ya rufe shi yana kallon Momy yace. "Meya faru dasu haka suka fad'i a lokaci guda". Kai Momy ta girgiza tana cewa "ban sani ba Hamid bansan meke damunsu ba kawai ka dubasu" Momy ta karasa maganar daidai wasu bayi masu ayyuka a part d'in sun shigo ta umarcesu dasu shiga bedroom d'in Khairat su ciro katifar dake kan bed d'in su kawo mata ita parlor, amsawa sukai kamar ta basu umarni suka d'auko suna kawowa Hamid ne ya taimakawa Momy ta dorasu akan katifar sannan tana tsaye tace ya dubasu, hum yayi mamaki baby zazza'bi take kuma a gwajin dayai Mata ya sauka to amma Khairat fa baiga komai ba saidai gaskiya dika su biyun suna bu'katar a qara musu ruwa, kallon Ahmad yai wanda ya had'e rai kafin ya jinjina kai yana d'aurawa kowaccensu drip a hannunta da zaiyiwa Momy wata magana amma sakamakon da Ahmad a gurin kuma zasu iya yin hayaniya yasa kawai ya share daya kammala abinda dazai musu ya koma hospital yace idan ya dawo zaiyi magana da Momyn, Ahmad ma bai zauna ba ya fita sai iya Momy ce a gurin su ta d'auko bargo tana rufesu domin sunyi barci. 'Dorayi^^^^ ____Tafe wata budurwa take ita kad'ai ko ganin inda take jefa qafarta batayi saboda irin damuwa da tunanin datai zurfi a cikinsa ga kuma hawaye yana zuba na ba'kin ciki da takaicin rayuwar gidansu da halayyar yan gidan musanman matar ubanta da kuma shi kansa mahaifin nata wani lokacin har tunani take anya shine ya haifeta ba tsintar ta yayi ba uba na qwarai bazai ri'ka cutar da yarsa irin haka ace ba kula ba walwala ba nuna qauna magana ta fatar baka wacce zatasa taji dad'i bazai Mata ba ya'ki mayar da hankali akan iliminta amma yake biyawa su Abidah da Nadiya bashine ya haifesu ba ita da take 'yar hatta kud'in da zata hau napep baya bata kullum a qafa take zuwa makaranta amma su Abidah kwanan nan ya sauya musu mota ta zuwa school........ kuka ne me qarfi taji yana tunkaro ta cikin dauriya ta danne taci gaba da tafiya ga masifar gajiya datai ga yunwa kuma ta tabbata saita koma zata d'ora musu girki ta gama ta dauko ta kawo musu dining tai serving kowa kamar wata bewar su suyi kaca-kaca da dinning din ita zata gyara ta tattare kwanuka ta wanke ga su sata wanki suna zaginta da injin wanki a gidan amma tsabar sun karanci mugunta ruwan da zatai musu wankin ma sai sun zuba Mata qanqara d'uma d'uma a ciki yadda hannunta zai sanqare haka zasu tulo Mata kaya ta wuni a tsakiyar rana tana wankewa su bushe ta goge ta kaiwa kowa cikin wardrobe dinta abin nan yana mugun ba'kanta Mata rai rashin uwa maraici yaja Mata haka da ace mahaifiyar ta tana nan bazata tozarta haka ba share hawaye tai har ta kusa ta tuna littafinta ta mantoshi akan kujera cikin class da sauri ta juya zuwa FCE d'in batare data tuna cewa hakan zai zama Mata laifi bane a gurin Hajiya Khuburah gashi kuma data koma bata ganshi ba sannan babu students ko d'aya balle ta tambaye su ha'kura tai cikin damuwa ta sake d'auko hanya ta dawo gida tana bud'e gate d'in gidan saida gabanta ya fad'i ganin motar Daddynta ya akai yau ya dawo da wuri bayan kullum sai magriba yake dawowa gida yau kuma tun la'asar shiga tayi jiki a sanyaye ta bud'e kofar falo da sallama shiru kamar ba mutane babu wanda ya amsa Mata sai tu'kuicin baka'ken harara data samu kaita sunkuyar zata wuce cikin tsawa hanya Khuburah tace. "Zo nan dan uwarki". Jin abinda hajiya Khuburah tace yasa ta dakata tare da juyowa ta dawo har gabanta ta dur'kusa tana cewa. "gani Mama''. Wani irin kallo tayi mata cike da tsana tana cewa "a gidan ubanwa kika tsaya sai yanzu kika dawo ana jiranki kizo ki d'ora girki tsabar ba'kin hali shine kika tsaya a wani wuri baki zo akan lokaci ba bayan kinsan Nadiya tana da ulcer bata juri zama da yunwa ba amma kika kama kika zauna a hanya ko, a gidan ubanki kika tsaya"? ta karasa maganar tana kai mata mari, hawaye ne masu zafi suka shiga zubowa Ayrah wato ita da yake bata da wanda zai tambaye ta taci ko bataci ba uwa balle ta samu kulawa a yau banda biscuit da drinks data sha a gurin qawarta Zarah bataci komai ba domin datayi musu kayan breakfast hajiya Khuburah cewa tai ta 6ace mata da gani haka ta tafi school amma ga wacce kawai dan batazo ta d'ora girki da wuri ba har ake zaginta............... Ba zato taji sun rufeta da duka kamar zasu kashe ta sai tattaka ta suke hajiya Khubura tana zaune a hakimce ta d'ora qafa d'aya kan d'aya sai kad'a kai take tana cewa "kuci uban daya kawota duniya sawa tace ku fasa Mata baki". A fusace Nadiya dake faman d'irkarta ita da Abidah tace "anya mum wannan da ba dabba za'ai yi bata akai mutum kwata kwata ace yarinya ta zama me dod'add'iya qwaqwalwa duk abinda aka fad'a Mata bazai shiga kunnen taba saikace jaka"?. Ta'be baki hajiya khubura tai tana cewa "da alama dai jakar ce domin bata sahun mutane a gurina dan naga qwaqwalwar jakuna gareta dukan da kuka lakad'a Mata bai shigeta ba shiyasa ta tsaya kuka kuci gaba da nad'ar 'yar isa sawa tace ku fasa mata baki" hajiya Khubura ta karasa maganar tana hankad'a Ayrah baya tare dasa qafa taka Mata ciki, qara Ayrah tai cike da azaba a take wani wahalallan amai ya fara fito Mata har ta hanci, da sauri hajiya Khubura ta matsa gefe tana sa hannu ta kare hanci da baki wai karta d'auki cuta tace. "Kan uba mu zakiwa qazanta a parlor gurin zama da hutun mu aiko saikin shanye sa😳". Kuka Ayrah keye sosai cikin damuwa hannuwanta a bud'e alamar neman yafiyarsu muryarta na rawa tace "dan girman Allah Mama kiyi hakuri zan gyara gurin". Cikin tsawa hajiya Khubura tace "karki kuskura ki sake kirana mama domin ni ban haifi 'ya asararriya irinki ba kije can qabari ki nemi uwarki Allah ya sauwa'ke na miki kallon 'ya hayyy tabdijan amma baki ma da hankali Wallahi daga yau na sake jin wannan tsinannan bakin naki ya kirani da Mama saina kusan kashe ki a gidan nan kuma kiyi abinda nasaki ki shanye wannan aman" ta fad'a tana kifata a gaban wuri tace. "Abidah ni ta raina min wayo kuzo kusata ta shanye wannan qazantan data zubar mana". Tasowa sukai Nadiya ce akan gaba tana zuwa ta d'auke ta mari zatai magana itama taji saukar wani irin firgitaccen mari me tafiya da ji da gani ya sauka a fuska kafin ta wani yunkuri sabo wanda yafi na farko ya sake sauka a daya 'barin a gigice Nadiya ta fasa qara wata ba'kar juwa ta debeta tayi baya timm ta fadi kasan carpet tana fashewa da kuka wanda kafin su farga cikin zafin nama Abidah ma ta samu nata rabon itakam da yake tafi Nadiya raki ihu tai ta zundumawa tana burgima a kan carpet d'in kamar ana yankar jikinta. Yana tsaye a kansu ransa a mugun'bace idonsa yayi ja kallon yadda jikin Ayrah ke rawa yayi takaici na sake rufeshi kamar ya cire belt din jikinsa ya musu shegen duka yake ji sai kuma ya fasa dukawa yayi yana d'ago Ayrah batare da yace mata komai ba sai mahaifiyarta da yake tunawa irin ri'kon datai masa kamar d'an data haifa idan ya zuba ido akaci gaba da cutar da yarinyar nan bazai ta'ba yafewa kansa ba............... Katse masa tunani hajiya Khubura tai sakamakon wata ba'kar d'anyar ashar data danna tana cewa "Aiman ka fita idona a cikin gidan nan ina ruwanka da lamarin mu na rantse da Allah bazan yarda bari Alhaji ya fito ya mana iyaka domin wallahi saidai ka koma gidan ku ko kuma ni ya sakeni na bar masa gidansa bazanci gaba da zama kana nuna min rashin tarbiyya irin wacce Fatima ta koya maka ba kasan laifin da tai min kawai zaka dau hukunci a hannunka wato kaiga isashshe d'an isassu me qanwa ko''?.. (Fatima mahaifiyar Ayrah ce ta rasu shekaru uku da suka wuce itace ta reni Aiman shi d'an qanin Daddyn Ayrah ne tun daga yaye ya'ki gidansu yake zaune a gurin Fatima komai nasa kuma tamkar uwa haka ta daukeshi sannan ta raineeshi a matsayin nata). Wani irin razanannan kallo me firgitarwa Aiman yayi mata wanda yasa cikin shakka ta soma matsawa baya baya tana cewa "wallhi bari kaji tunda juninka fitsara zan gwada maka Nima ba kanwar lasa bace zanje gidan naku zan hadaka da wadanda suka isa dakai suyi min maganinka Ina daidai dakai d'an marar kunya kawai". Nunata Aiman yayi da yatsa a fusace yace "karki sake zagina kin gane"?. Itama a fusace tace ''na zaga ubanka ya buge uwarka tsinanne la'ananne ni zakaiwa rashin da'a? To bari kaji ko Zainab uwar data haifeka bata isa fad'i in fad'a Dani ba balle wani banza kai data haif............. Bata karasa ba ya wanketa da mari ihu ta zunduma daidai Daddy ya fito baiga sanda yai Marin ba ihunta kawai yaji gasu Abidah da Nadiya har lokacin suma suna kukan zafin da fuskokinsu ke musu da sauri ya karaso yana kallon Aiman yace. "Subahanallahi me yake faruwa Aiman ya naga haka kukan me suke"?. Tun kafin Aiman yai magana hajiya Khubura dake ri'ke da kunci cike da takaici tace "au Alhaji shi zaka tambaya bayan wulakanci da cin mutumcin dayai min marina fa yayi". "Mari dai"?. Daddy ya tambaya cikin mamaki yana kallon ta da alamar rashin yarda akan abinda ta fad'a, haushi ne ya rufe hajiya Khubura a fusace tace "eh mari yanzun nan ya mareni akan nayi masa magana ya mari Abidah da Nadiya". Kallon Aiman Daddy yayi yana cewa "meyasa ka maresu Aiman me sukai maka"?. "Daddy Ayrah suka saka a gaba suna dukanta kamar zasu hallaka ta harda amai kalli inda tai kuma tsabar rashin imani wai saita shanye, wacce irin rayuwa ce wannan suzo suna qarqashin inuwar mahaifin ta suna cutar da ita komai itace take musu hakan bai ishesu ba sai suna dukanta to wallahi bazan yi lamani ba" ya karasa maganar yana hararar su Nadiya dake gefe suna jan ajiyar zuciya. Shiru Daddy yai ya tsume yana kallon Ayrah jin a kanta ne komai ya faru kuma Aiman harda marar masa mata nunata yayi da yatsa yana cewa "wato ke kin zama shed'aniya ko? Kullum sai an samu sa6ani a gidan nan a kanki kin hana zaman lafiya to bari kiji idan har baki gyara ba sai na dauki mummunan mataki a kanki zan bayar dake". Daddy na rufe baki Aiman yace "Daddy ba laifin Ayrah ga babbar me lefi nan Hajiya Khubura itace ta gur6ata zaman gidan nan ba kowa ba da a lokacin da Umma tana raye ai ba haka muke zaune ba bamusan rayuwar 'kunci ba sai sanadin shigowarsu cikin rayuwarmu dan haka Ayrah tana gidan insha Allahu babu inda wadannan agololin zasu sa taje". Mi'kewa Hajiya Khubura tai tana cewa "idan Kaine ka haifeta saika hana ya sadakar da ita me gida yace bazata zauna masa a gida ba kaga ko kai dan karere baka isa ka hana ba

Chapter 2 of 22