magana akan abinda tai min".
Kai Momy ta girgiza tana sakin murmushin da bata shirya ba domin wannan wasan 'kwai'kwayon da Maryam ta shirya batai nasara ba ko Ahmad baya duniya qarewarta kenan ta tabbata Baby bazata ce bata tsoronsa ba ko tace babu wanda ya isa ya hukunta ta balle tasan yana cikin gidan hum ta fahimci ba zaman lafiya ya kawo Maryam gidan ba babu wata ziyara da tazo musu kawai tazo d'aga musu hankali ne dole zata dakatar da ita dan bazai yuwu ta ri'ka shiryo 'karya tana zuwa tana karanta musu ba dan ta zama gizo.................................
Katse mata tunani Maryam tai ta hanyar cewa "kuma abun ba'kin cikin ma harda Khairat itace me taya ta tana zugata ta wulakanta ni wai nazo musu gida zanyi kwad'ayi ina gidan ubana da bazan zauna ba ko baza'a iya ri'ke ba shiyasa ta tattaro na dawo musu nazo ina addabarsu to suna daidai dani idan ban had'a tsunmokara na nabar gidan nan ba wata rana sai sun yimin dukan dazan kasa tash..................
Bata karasa ba Momy tace "kinga Maryam kiyi shiru haka ya isa dan Allah bana son sake jin komai indai su Khairat ne kiyi hakuri zanyi magana dasu tashi ki tafi ki kwanta Allah ya tashe mu lafiya" shiru Maryam tai zuciyarta babu dad'i wanda tazo tana yin maganar danya tanka harta gama ko kallon inda take baiyi ba balle tasa ran zaice wani abu zazzafan huci ta fitar tana mi'kewa kamar zata rufe Momy da duka akan tafiya ta kwanta d'in da tace tayi da'kyar ta mi'ke tana turo baki tace "saida safe" ko jiran amsar da Momyn zata bata batai ba fuuuu ta wuce tana bud'e kofa ta shiga tana rufowa da qarfi kai Momy ta jinjina tana bin kofar da kallo zatai magana Ahmad da yaja tsaki yace.
"Momy zaman me take banga amfanin zuwanta ba tunda tazo gidan nan take had'a fitina da damuwa a tsakanin yaran nan suna zaune lafiya haka kawai ta baro gidansu taxo ta d'aga musu hankali to wallahi bata isa ba ki fad'a mata sa'ko daga ni ta had'a kayanta ta koma gidansu idan ta'ki zataga sakamakon taurin kai zan nuna mata niba sa'an wasan ta bane tsabar ta rainawa mutane hankali Babyn ce zata iya fad'ar duk wadannan stupid d'in maganganun data lissafa ai daga nan zaki fahimci zama tai ta shirya kayanta nasan halin 'kannai na nasan abinda zasu iya da wanda bazasu iya ba dan haka ki fad'a mata tayi taka tsantsan karta kuskura na sake jin bakinta ya shirya wasu banzayen kalamai sannan ta jigina su tace Wai Khairat da Baby ne suka fad'a idan ta sake ranar zata ga 6acin raina dan zan nuna mata tayi kuskure".
Sauke ajiyar zuciya Momy tai tana cewa "gaskiya ne Ahmad dukkan zancen nan da Maryam ta fad'a babu 'kamshin gaskiya a ciki kawai dai na biye mata ne kartaga kamar ina goyon bayan su wulakanta tane nikuma duk d'aya suke a gurina bana bambanta su itace take kokarin saita fahimci a wanne irin muhalli na ajeta".
"Ok abinda take son sani kenan? Ta samu zan sanar da ita Allah yasa na sake jin ta maimaita hauka irin wanda tai yanzu na rantse da Allah ranar saita kwana da tsattsaman jiki babu ruwana da girmanta indai tai abinda ba daidai ba saina hukunta ta kamar yadda nake hukunta su Khairat" yana fad'in haka ya mi'ke yana shirin fita yace "goodnight Mom ki huta lafiya"? "Ok Ahmad Allah ya kaimu saida safe" yana fita Momy ta mi'ke taje ta saka lock a kofar kafin ta dawo ta wuce part d'inta Maryam dake la6e tana jin komai hawayen ba'kin ciki ne ya zubo mata ba maganar da Ahmad yayi ne ta 6ata mata rai ba a'a ganin datai har lokacin bata fara samun lambar yabo wacce xata samu shiga a gurinsa ba shine ya sakata kuka ashe dama duk wankan da take d'auka da kwalliyar da take yi baya gani a banza takeyi ko kallo bata ishesa ba balle ta fara kokarin jawo hankalin sa sakin kofar tai tana kuka taje ta d'au wayarta a daren karfe sha d'aya tayi amma bata lura da wani lokaci ba saboda tashin hankalin da yake gabanta Mama take kira burinta kawai ta d'aga suyi magana Kota samu salama.
Mama tana kwance a bedroom Abban su Maryam shi kuma yana gaban laptop yana rage aiki yaji wayarta na ringtone da mamaki ya kalli Mama da ke sharar barci kamar ya tashi ya duba waye me kira a wannan daren sai kuma ya fasa ya mayar da hankalinsa kan aikinsa jin an sake kira yasa yai tsaki yana tashi yaje har inda take kwance ya tasheta cikin magagi Mama ta bud'e ido tana cewa "Alhaji lafiya kake tashi na" batare daya bata amsa ba ya juya yana komawa inda yake da mamaki ta tashi zaune tana kallonsa zatai kira na uku ya shigo zaro ido waje tai cike da fargabar waye yake kiranta a wannan daren kodai akan haka Abba yai fushi da sauri ta dau'ki wayar tana kallon number Maryam jikinta na 6ari ta kasa d'agawa har kiran ya katse kallonta sosai Abba yai yana cewa "Waye yake kiran wayarki a wannan daren"? Kai Mama ta girgiza cike da tsoro muryarta nadan rawa tace "Maryam ce" jin abinda tace yasa baida niyyar d'agowa amma saida ya daina abinda yake yi ya kalleta kamar bazai tanka ba sai kuma.
"Maryam dai me zatai miki a wannan daren nifa irin haka ne bana so hankalina bai kwana da yarona yaje wani guri har yayi kwanaki ba kawai dai na barta ne saboda naga gurin yayarki zataje amma badan haka ba wallahi babu inda ta isa taje a wannan yanayin da ake ciki tana mace bana so ta ri'ka nisa da gida" shiru Mama tai tana rarraba ido ta kasa magana sai numfashi da take saukewa kamar wacce tai gudu ganin duk tabi tayi tsuru-tsuru yasa yad'an girgiza kai yana mayar da hankalinsa kan aikinsa bai sake ce mata komai ba Mama da jikinta ya gama sanyi so take tayi masa bayanin abinda zaiji ya gamsu kuma ta kasa sannan tabi bayan kiran Maryam d'in nan ta kasa kusan rabin awa tana zaune ta kasa kiranta domin batasan me zatace mata ba saboda Abban kar yaji abinda suke shiryawa ya hana ita kuwa tasa a ranta cewa koda ace aurenta zai mutu indai burinta na Maryam ta auri Ahmad zai cika bata da matsala zama bazawara ba damuwarta bace tunda ba'a kanta farau ba kafinta an saki wasu bayanta ma za'a sake wasu tunda tasan idan Maryam d'in ta aureshi akwai jin dad'i gani take hatta gidan da zata zauna Ähmäd ne zai gina mata.....................
Sabon kiran da Maryam tai mata neya dawo da ita daga duniyar tunanin data fad'a da sauri ta mi'ke tana dirowa daga kan gadon ba arziki ta nufi kofa ta bud'e ta fice Abba daya bita da kallo ya jinjina kai kawai yaci gaba da uzirinsa ita kuwa Mama part d'inta ta shige har bedroom ta shiga toilet tai qasa da murya tana d'aga kiran tace.
"Hello maryam kina jina? Ina jinki meya faru kike kirana a daren nan kinsa Alhaji zai zarge ni"? Mama na rufe baki Maryam ta fashe mata da kuka tana cewa "Mama gaskiya bazan iya ba wallahi na gaji kaina bazai d'auka ba tun daga yanxu na fara kwasar ba'kin ciki a gunsa taya kuma zan shawo kansa wallahi nikam bazan iya wannan masifar ba da kinji irin maganganun daya fad'a min d'azu Wai saiyai min dukan hallaka sabida wata shegiyar cousin d'insa ta zageni nakai qararta gurin Momy yayi min tas yace qarya nake yi nikam na gaji Mama gida zan taho bazan iya ba ha'kurina yaje karshe".
Jin abinda take cewa yasa cikin kad'uwa Mama tace ''ban gane bazaki iya ba kenan ha'kura zakiyi dashi ki dawo gida ki zauna tare damu kome naji kina wata magana wacce bata gamshe niba"?.
"Eh Mama gida zan taho domin zamana anan bashi da wani amfani kawai 6ata lokaci nazanyi Ahmad bazai ta'ba kallona ba balle ya soni da kinji abinda yake cewa d'azun wallahi kema abun saiyai miki ciwo a ranki baza kiso na sake koda sakan d'aya ne a gidan nan ba dan haka nikam gobe tun asubar fari zaki ganni bazan qara zuwa gidan nan ba na ha'kura da Ähmäd" ta karasa maganar tana sake rushewa da kukan ba'kin ciki.
Hankali tashe Mama tai saurin girgiza kai kamar Maryam d'in tana ganinta tace "a'a kul na haneki karki kuskura kiyi wannan gangacin karna ga kafarki kin dawo gidan nan saidai idan Ahmad shima yabar gari kin gane ki qara ha'kuri yaushe ma kikaje gidan da zaki fara 'korafi ai dole saikin dad'e dama koda ma ace zai saurareki".
"Wallahi mama nikam na gaji bazan iya ba haka kawai zan zauna yana yimin kallon banza shegiyar cousin d'insa tana zagina da fad'a min ba'ka'ken maganganu na cewa gidansu naje na sameta ba itace tazo ta sameni ba abun ba'kin cikin harda Khairat a ciki" takaicin maganar da Maryam ke fad'a ya gama rufe Mama ji take inama zataga Maryam a yanzu da take mata wannan sakaryar maganar da saitayi mata dukan tsiya meyasa bazata kamasu tai musu duka ba tana zaune suna zaginta idan Maryam d'in bazata iya dasu ba ita zataje har gidan taci ubansu a gaban Momyn tunda tana sane ta bari suke mata abinda suka ga dama.........
Kukan da Maryam take harda shid'ewa yasa Mama ta sake harzu'kowa a masife tace "ke dan uwarki ki rufa min baki shashashar banza kawai kenan tunda kikaje uwar me kika tsaya kallo baki abinda ya kaiki ba sai yanzu zaki kirani da daren nan ki dameni da kuka dan kisa na kasa komawa barci na kwana ina tunani"?.
"Nayi iya yina Mama na ko'karta kamar nayi hauka amma Ahmad ko mutum bai mayar dani ba kamar package ka cire abinda yake ciki ko wani abu mara amfani haka ya mayar dani ko saurarata bayayi gashi ya kusa tafiya inaga bazai sake kwana biyu ko uku ba gaba zai koma" dafe 'kirji Mama tai tana cewa "ya kusa tafiya kuma na shiga uku Maryam zaki d'ora min masifa da bala'i me kike son cewa ya kusa komawa bakiyi 'ko'kari kinyi wani abu dazai amfane muba"?.
"Nayi wallahi nayi Mama kawai Ahmad ya fita dabam ne a cikin maza yana da wuyar sha'ani baya yin abinda bai dameshi ba baya shiga safgar daba tasa ba bayayin abinda yasan bame amfani bane a gunsa da ace Abdul-Hamid ne matsayinsa da duk haka bai faru ba wallahi ko kaffara bazanyi ba da ace shid'in ne da yanzu an wuce gurin na tareshi na fad'a masa abinda ke raina kuma nasan zai amince min amma shifa na tabbata idan yasan ina sonsa maybe karshen ala'ka ta dashi kenan kona jawo ya koroni daga gidan".
"Ya koroki saboda kinje gidansu humm aiko wallahi bai isa ba zanyi magana da Auntyn nizan kirata na fad'a mata dalilin zuwanki da zamanki a gidan inyaso ita saita fad'a masa na tabbata indai yaji haka shikenan ai ko baya sonki yasan kina sonsa sannan batu ya biyo ta gurin mahaifiyar sa idan tace masa ya aureki dolensa ya amince ko baya so shiyasa nake fad'a miki ki qara ha'kuri nasara tana gaba idan gari ya waye ki saki ranki karki nuna wani abu ma ya faru ki nuna musu bariki har ita wancan yarinyar da kike magana akai ki sharesu kawai kiyi abinda ya kaiki ki manta dasu kinji"? Kai Maryam ta d'aga tana goge fuskarta tace "ok shikenan Mama na fahimta zanyu yadda kikace" "yauwa Maryam har kinsa naji dad'i ki tsaya ki nutsu kiyi abinda ya kaiki ni bari na koma kar Alhaji yaga na fito na dad'e" "ok Mama saida safe"? "Tom mu kwana lafiya" ta fad'a tana cire wayar a kunnenta tare da tsayawa tana jinjina kai ta ciji yatsa tana cewa "tabd'ijan amma lallai Maryam tsabar d'anyan kai kice zaki dawo gida batare data kin jawo hankalin Ahmad kanki ba humm wallahi bazan amince hakan ta faru ba zan kira Auntyn nida kaina na fad'a mata dalilin zuwanki gurinta sai naji me zatace zata goyi bayan abinda nace ko bayan d'anta zata bi indai ta nuna abinda yace shine take kai hum'um heyyy dan'kari akwai hayaniya a gaba da tashin hankali indai akace yaron nan ya'ki na'am da auren Maryam harna hasko ya'ki da guguwar da zata faru matukar bata umarci Ahmad ya aureki ba Maryam bari dai Allah ya kaimu goben ayi wacce za'ai'' ta karasa maganar tana fitowa daga toilet ta goge gumin datai kafin ta fita ta koma part d'in Abba ta d'auka zai sake mata magana akan kiran da Maryam d'in tai mata sai kuma taga bai tanka mata ba shiyasa tana kwanciya tai saurin komawa barci saboda karma abun ya ciyo zuciyarsa ya sake mata tambaya akan haka.
•°•°•°+°•°•°•
Sanin da khaleel yayi yanzu Aiman baya 'kasar kome zaiyiwa Ayrah babu me d'aukar mataki a kansa yasa gabadaya yabi ya matsa mata iskancin yau daban na gobe dabam yakai da hatta muryarsa idan Ayrah taji gabanta ya ri'ka fad'uwa kenan tun ranar daya nuna mata cewa ga abinda yake so ta amince masa ta bashi kanta zaiyi mata komai ta'ki shikenan tun daga sannan ta sake tsanarsa take jin mugun tsoron sa batasan kad'aituwarsu guri d'aya koda yana tare dasu Hajiya Khubura ne balle kuma ace gata gashi iyasu biyu ji take kamar numfashinta zaibar jikinta tsabar firgici da take tsintar kanta a ciki kullum bata samun isasshen barci saboda shi wani lokacin kamar aljani har batasan ta inda yake shigowa bedroom d'inta ba kawai saidai ta ganshi.
Yauma kamar koda yaushe haka ya shigo mata d'aki cikin dare saiji tayi ana ta'ba mata jiki a firgice ta farka tana tashi zaune zatai ihu ya d'ora yatsarsa saman bakinsa yana cewa "shittt kiyi shiru ba wani abu bane ba wani abu zanyi miki ba kin gane nine fa Khaleel nazo taya ki kwana ne kawai big girl ba wani abu ba" ya fad'a yana shirin zama a gefen gadon zaro ido waje Ayrah tai zuciyarta na bugawa da 'karfi muryata na rawa ta matsa baya da sauri saboda saura kad'an ya zauna akan cinyarta kuma yana sane yai hakan a susuce hawaye yana zuba mata tace.
"Dan Allah ka fita min a d'aki niba 'yar iska bace kamar yadda ka d'auke ni bana son ganinka khaleel wai me kakeyi haka ne? nayi maka kama da irin 'yan iskan matan banza da zakace kazo taya ni kwana ni bana bu'kata ka fice min a d'aki domin ban kasance 'yar iska kamar yadda ka d'auke niba" tana rufe baki ya saki dariyar nuni da cewa abinda ta fad'a nishad'i kawai ya saka shi yana kallonta yace "oh me kike nufi waye d'an iskan kenan nine"? Shiru tai a razane tana kallon yadda yake binta da wani mayen kallo ganin bata bashi amsa ba ya mi'ke daga zaunen da yake yana nufar kofar bedroom d'in ya sanya mata lock kafin ya juyo yana cewa "nan da gari ya waye babu wanda zaisan tare muka kwana da asuba zan fita na koma bedroom d'ina kinji zan baki duk abinda kike so kud'i gida mota ko yawon sha'katawa kike bu'kata da kaina zan kaiki duk 'kasar da kikace kina son zuwa komai fa da kike so babu ce kawai bazan baki ba itama da ana ganinta wallahi zan baki saboda ta ko'ina kin cika mace kalli 'kirjinki a cike sai she'ki suke cikin kyakkyawar rigar barcin ki kalli fararen cinyoyinki dubi dogon wuyanki kalli le6an bakinki masu taushi da kamshi wayyo Allah Baby kin had'u fa musamman yanzu dana tsaya ina kare miki kallo babu manyan Kaya masu rufe surarki wash Baby kin tada hankalina wallahi kalleki komai a wadace dubi hips d'inki oh my God please Baby taho guna I love you" ya fad'a yana bud'e mata hannuwan sa alamar tazo gareshi qara matsawa baya Ayrah tai tana 'kan'kame jikinta tare da sakin kukan damuwa da ba'kin ciki musamman yadda taji yana lissafa tsarin halittar jikinta ji tayi kamar ta dau'ki wu'ka ta da6a masa ya mutu kota huta ganin dayai ba daina kukan zatai ba yasa ya baro bakin kofar da yake yana tahowa gurinta dur'kusawa tai tana sake fashewa da wani mayataccen kukan tace.
"Dan girman Allah khaleel karka ta'ba ni ka barni dan Allah" ko sauraron ta baiyi ba balle yace tana masa magiya bare ya ha'kura sai kanta da yazo yana saka hannu ya ri'ko nata hannnun zai mi'karta tsaye taga yana shirin ta'ba breast d'inta da qarfi da make hannunsa zata fasa 'kara ya hanata ta hanyar toshe mata baki da tafin hannunsa du'kawa yai yana d'aukarta zai nufa kan bed da ita ganin idan tai sake fa gayan nan zai cika burinsa a kanta na ganin ya lalata mata rayuwa aiko yana direta tai saurin hankad'a shi tana mi'kewa da gudu ta nufi kofar fita bin bayanta yai yana zuwa ya sake dam'karta ihu ta zunduma masa da iya 'karfin ta wanda a d'ari Khaleel ya bud'e kofa ya fita da gudu yana fita Ayrah ta karasa kofar da gudu taje ta rufe jikinta na rawa da'kyar ta iya baro gurin ta dawo tana bud'e wardrobe ta dauko Kaya kawai tasa a jikinta ta ha'kura da kayan barci hakan zaifi mata alkhairi data bari ya lalata mata rayuwa a banza koda ta koma ta kwanta bata iya barci ba sai daga baya da yake barci 6arawo ne da'kyar ya d'auke ta batare data sani ba.
Khaleel kuwa tunda ya koma bedroom d'insa kasa nutsuwa yayi ko zama bai iya yiba balle shi ya samu damar komawa barcin sai zaga cikin filin bedroom d'in yake yana goye da hannu a baya babu abinda zuciyarsa take hasko masa sai surar Ayrah tsabar jaraba da yasa a ransa har wani sid'ar baki yake kamar me shan minti can kuma ya dam'ke joystick d'insa daya mike tsaye da qarfi yana runtse ido tare da cije lips yace.
"Ohhh Baby zaki kisa a gidan nan indai baki amince min ba na rantse bazan barki ba sai nasha kalar d'and'anon za'kin da kike dashi daga ganinki zaki ni'ima dad'in ki wane zuma a baki dole nema ki amince min ko bakya so" ya karasa maganar yana bud'e ido ya kalli yadda har lokacin joystick d'in nasa yake mi'ke huci me zafi ya fitar yana cewa.
"Bazan iya barci ba bazan iya ha'kura dake ba Baby dole na koma zanyi amfani da abinda dole ki amince min batare da kin sani ba komai zai faru nayi alkawari yau bazan rabu dake ba saina cimma burina a kanki" ya karasa maganar yana bud'e drawer ya d'auko wata kwalba ya kalla tare da jingina harda sakin murmushin mugunta kafin ya bud'e bedroom ya fita yana komawa part d'inta amma kofar a rufe ruf babu yadda zaiyi ya iya shiga d'an kwankwasa mata yai a hankali saboda dare d'aukar magana yace.
"Baby please open the door" jin shiru ba'a amsa masa ba ya zagaya ya koma ta window yana zura hannunsa ya d'age labule ya ganta kwance a lullu'be ta koma barci dafe kai yayi yana sake kallonta ga 'koshi ga kwanan yunwa inama yadda tai barcin nan ace da kofar dazai shiga ko kuma d'azu ne yana zuwa shi kad'ai yasan inda zai fara ta'bawa ganin bashi da yadda zaiyi saidai kallo daga nesa yasa yaja tsaki yana barin windon ya koma bedroom haka yayita yawo yana son ya ragewa kansa zafi amma a banza har kiran sallar asuba a kunnensa tunani ne yazo masa yasan yanxu maybe ta tashi amma kuma yana tsoron kar Daddy ya fito ya ganshi bari yayi sai yaji an shiga masallaci zai lalla6a yaje kafin a fito yayi abinda zaiyi haka ya sharad'a a ransa amma yasan duk tsiya dole yaje masallaci shima idan baije ba Daddy yana dawowa zai tambayi meyasa bai ganshi ba tuna hakan yasa ya ha'kura kawai yai wanka sakamakon ya 6ata jikinsa ya tadawa kansa sha'awa a banza.
Ayrah kam da abun ta farka da daren abin bai dameta ba kamar sanda gari ya waye haka tayita kuka a bedroom ita kad'ai idonta ya zama jawur fuskarta ma haka ganin d'akinta yayi haske sosai yasa ta fahimci gari ya waye yadda zataje ta d'ora musu breakfast mi'kewa tai tana shiga toilet ta wanke fuskarta ta fito tad'au hijab tai parlor babu kowa dan haka wucewa tai ta shiga kitchen ta fara aiki sauri take ma saboda batasan haka rana ta fitoba saida ta fito yanxu ta gani gashi zataje school dole ta takaita abinda zatai musu saboda karta makara a gaggauce ta kawo musu dinning ganin babu wanda ya fito yasa ta koma part d'inta ta shirya ta dau'ki hijab da handbag d'inta ta fito gabanta ne ya fad'i lokacin da suka had'a ido da Daddy daidai sun fito shida Hajiya Khubura jiki a sanyaye ta karasa tana dur'kusawa har qasa tace.
"Daddy ina kwana"? Da'kyar ta iya karasawa muryarta na rawa shima kuma maimakon ya amsa mata sai tambaya daya jefo mata "ihun uban me kikewa mutane jiya da dare"? Jin tambayar dayai mata yasa a razane ta d'ago ba shiri tana kallon sa zuciyarta na harbawa da mugun 'karfi a tsawace yace "kallona nace kiyi ko amsa nake jira ki bani ubanme ya sakaki ihu da dare ki fad'a min tun kafin ki fusata ni na yanke miki hukuncin da baza kiji dad'insa ba" ya fad'a kamar zai kai mata duka yana zaro ido rai 6ace kuka Ayrah ta fashe dashi cikin tashin hankali ta d'ora hannunta aka tana cewa.
"Dan girman Allah Daddy kayi hakuri idan na 6ata maka rai ka yafe min bada sona nayi ihu dan na tasheku daga barci ba".
"Ok bada sonki bane to dason wa kikai ihun? Iye fad'a min dason wa kikai ihun nace ki fad'a ko saina mareki tukuna"? Ganin da Ayrah tai yana shirin kai mata marin da gaske yasa da sauri ta matsa baya tana girgiza kai zafafan hawaye suna zuba a idonta ta kasa magana ganin khaleel ya fito yasa a rud'e batasan lokacin data nuna shiba wanda a d'ari Hajiya Khubura ta zaro ido tana cewa.
"Kan bala'i lallai yarinyar nan wato sharri kike shirin 'kulla masa me kike nufi naga kin d'aga wannan mitsiyacin yatsan naki kina nuna shi nufinki shine ya saka ki ihun ko mafarkinsa kikai"? Kai Ayrah ta girgizawa tace "wallahi ba sharri zanyi masa ba kuma ba mafarki nayi ba a zahiri na ganshi da dare ya shiga d'akina wai saina bashi kain.........................
Cikin azama Hajiya Khubura ta gwa6e mata baki saboda karta 'karasa jin abinda take fad'a a masife tace "dan uwarki Khaled d'in ne zai shiga d'akin ki ubanme zaiyo miki wato saboda kin kawowa mutane 'kwarto gida kuma kinga asirinki yana Shirin tonuwa shine kike neman la'kawa khaleel 'karyar shine to wallahi bari kiji idan ma haushinsa kike ji nan gani nan bari babu yadda zaki dashi zama a gidan nan yanzu ya fara koda ace wannan mara kunyar Aiman d'in ne ya dawo bashi da bakin magana balle ke banza wacce ba'a mayar da ita mutum a gidan nan ba Kinga bangon nan ya fiki kujerar nan ta fiki takalimin 'kafatar me gadin gidan nan ma yafiki daraja a gurina wallahi kuma ki saurari gargad'i na a kanki duk ranar da tsautsayi yasa kika sake d'aukowa mutane 'kwarto cikin gida sannan kikece wai khaleel ne humm na rantse da Allah wallahi tallahi saina 'karya ki a gidan nan kuma na 6alla banza babu wani abu da wani ya isa yai min".
Allah sarki tsabar kukan da yaci 'karfin Ayrah har wata iriyar shid'ewa take numfashinta yana d'aukewa Daddy da ransa ya gama 6aci da maganar kwarton da yaji Hajiya Khubura tana ambata yace "harda kwarto kike kawo min gida Ayrah kwarto fa? Kneeldown Ayrah tai tana cewa "wallahi Daddy ka yarda dani ban kawo kowa gidan nan ba ni kad'ai nake kwana" tana rufe baki Hajiya Khubura tace "sannu sarkin musu 'karya akai miki kenan baki kawo kwarton ba tsana tasa mukai miki haka ko"? Kasa magana ayrah tai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 22