Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya Ähmäd roba ne yana daidai da 'kugun kowa kaci gaba dayin shagwa'barka lokacin kane dama ka samu tunda kai ba'a fiya takura maka kamar niba" ta karasa maganar tana wucewa bedroom ta aje littafin ta shiga toilet tayi brush ta fito tana dawowa parlor ta wuce dinning zamanta keda wuya taji sallamar Ahmad ya shigo ji tayi abincin ya 'kwareta da sauri ta dau'ki ruwa tasha Khairat na can gefe nesa dasu Mami Sultan kuwa tuni ya daidai kansa ya nutsu sosai a hankali yasa hannu yana kokarin kar'bar spoon d'in dake ri'ke a hannun Mami dan kada Ahmad ya gani kallonsa Mami tai tana cewa. "Ya haka Sultan ka bari na karasa baka man"? Kaiya girgiza yana kallon Ahmad yace "a'a Mami zan qarasa da kaina" ya fad'a yana kar'ba da sauri ya mi'ke bai karasa ci a gurin ba ya koma can saman dinning ya zauna kamar gaske ya ri'ka she'ka loma da ana bashi yana shagwa'ba kamar baby zatai dariya haka ta zuba masa ido tana kallon sa zuwa wani lokaci ta kallo parlor ganin hankalin Ahmad baya kansu zance kawai suke da Mami yasa tai qasa da murya tana cewa. "A'a autan Mami yau kuma yada cin abinci da kanka wato ganin boss Ahmad yasa ka nutsu ko? Wallahi naso lokacin da muka shigo sannan shima ya shigo ya sameka kana shagwa'ba humm ya fasa bakin shagwa'bar sannan yau ka wuni har dare kana kar'bar service" d'agowa Sultan yayi yana kallon ta kamar bazai magana ba ya mayar da hankalinsa kan cin abincin saida ya gama ya dau'ki tissue ya goge bakinsa ya aje sannan yace "ai bazan yarda nayi abinda zai dakeni ba domin niba jaki bane kalli man Ina da hanyar kare kaina yana shiga na nutsu na tattara ya nawa yanawa na baro gurinsa hanyar lafiya a bita da shekara ban zauna bama balle yace nayi kuskuren wani abu kuma da salona kuka d'auka daga yau bazai sake kamaku da laifin wani abu ba balle ya hukunta ku" murmushi Baby tai tana girgiza kai tace "humm Sultan da alama ka manta waye ya Ahmad duk abinda muke yana hankalce damu wallahi ra'ayin kula kane baiyi ba da yaso zakaji yayi magana tun lokacin daya shigo ai ya ganka ana baka abinci a baki kuma yaga shagwa'bar da kake yi mata amma da baiyi niyyar yace maka komai ba kana gani ko inda kake bai kalla ba kawai kai dai kace kana da sa'a mukam bamu da bakin magana saidai muce alhamdulillah" qara qasa da murya Sultan yayi yana cewa "Aunty Baby na fad'a miki mafita ta yadda bazaki sake shiga tarkon Yaya Ahmad ba"? Kaita girgiza tana kallon sa tace. "kaima ba tsira kayi daga tarkon nasa ba kayita kanka kafin kayita wani". "Allah Aunty Baby da gaske nake". "Da gaske kake me"?. "Shawara zan baki akan hakan". "A'a bana bu'katar shawara saidai basir indai akan ya Ahmad ne duk ta inda ka 6ullo zaka sameshi yana kofar shima a tsaye yana jiranka da akwai inda zai 6ullo maka dan haka kaima kaji da kanka baka da wata shawara da zaka bayar anan". "Amma Aunty baby ai baki bari kinji me zance miki ba"?. "Nifa basai kace komai ba Sultan na fahimta ka 'kyale ni dan Allah karka d'aga min hankali na kasa cin abinci kai ka gama ci" mi'kewa yayi yana cewa "shikenan tunda bakya son ji na fad'awa Aunty Khairat" Baby na kokarin 'kara zuba abinci a place tace "yauwa saidai itan zaku daidaita amma dai banda ni kome zanyi ya Ahmad bazai fasa d'irka taba" ta karasa maganar tana d'agowa ta kallo inda yake magana suke sosai da Mami cikin sakewa kaita jinjina tana fara cin abincinta tana kallon Sultan yadda ya zauna a kusa da Khairat ya kifa kansa qasa yana fad'a mata abubuwa ita kuma tana d'aga kai tana murmushi wani lokaci kuma tad'an zaro ido ta rufe baki cije lips Baby tai a ranta tace ''tabd'ijan da ace ya Ahmad zai ganku a haka humm yanzu jikinku zaiyi d'umi" ta'be baki tai tana mayar da hankalinta kan cin abincinta har Ahmad suka gama zance da Mami ya tashi yayi waje yana fita Sultan ya dau'ki mp zai kunna Mami tace. "Wallahi Sultan ka kiyayi kanka ka guji had'uwarka da Ahmad akan wannan mp idan ba duka kake nema ba maybe yanzu ka ganshi ya dawo saboda akwai shi da wasan baya domin irinku marasa jin magana balle yaga duk ku ukun kuna part d'in". Zama Sultan yayi yana kokarin kunnawa yace "ai Mami nasan bazai dawo ba ya fita kenan". "Au haka kace saboda ya fad'a maka dazai fita cewa bazai dawo ba"? To ai shikenan nidai kasan ba tankawa zanyi ba idan ma ya kamaka kaine jikin ka zaiyi tsami". "Ai Mami inada kafar gudu bazan zauna ya riske niba ni ba irin Aunty Baby bane dazan tsaya ina gani ya ri'ke ni ko zomo bazai fad'a min zilliya ba yasin saidai muyita zaga masarautar nan da gudu har ya gaji ya barni". Kai Mami ta jinjina tana sakin murmushin zancen nasa tace "lallai kam amma shikenan ba matsala bansan shirinka ba nidai na fad'a maka kar tsautsayi ne yake janka a kowanne lokaci zaka iya ganinsa ya dawo kuma ba ruwana nidai na fad'a maka gara kaji dakyau kar kace baka sani ba ko kayi tunanin zan bashi hakuri ya 'kyale ka ina kallo zaiyi maka shegen duka" tana rufe baki Sultan ya d'ago zaiyi magana sai ganin Ahmad yai ya bud'o kofa kamar a mafarki yana cewa "Mami nabar key d'in motana anan"?. Humm tabd'ijan aguje Sultan ya tashi kamar iska na cirashi sama tsabar sauri wuff ya fad'a bedroom Ahmad da baidan me yakewa gudun ba yace "shi kuma wannan fa"? Murmushi Mami tai ganin tun ba'a je ko'ina ba gashi ana shirin kama shi tace "humm Sultan nefa ai ya zama saidai addu'a" kawai haka tace saboda taga alamar kamar Ahmad d'in baiga mp dake aje a gurin ba. "Baby kira min Sultan" Ahmad ya fad'a yana qarasa shigowa parlon to Baby tace tana mi'kewa da sauri ta shiga part d'in Mami amma babu alamar Sultan kira ta fara kwalla masa ya'ki amsawa saida tace ya Ahmad ne yace yaje aiko sai gashi ya fito daga toilet yana cewa ''yana Ina"? Juyawa baby tai tana cewa "yana parlor man nidai na fad'a maka idan kaga dama kazo ko ka'ki zuwa ba ruwana tsakanin kune Kai dashi" jin abinda tace gashi tana shirin fita yasa da sauri yabi bayanta Ahmad yana tsaye a gurin da yake Sultan ya fito yana ra6ewa duk xatonsa ko Ahmad yaga mp a zahiri kuwa babu abinda ya gani kawai dai yaga ya tashi da gudu ne tambayar da zaiyi masa kenan, karasowa yayi yana cewa. "Gani Yaya kayi hakuri dan Allah" a tsume Ahmad yace "gudun me kake wato saboda kaga ban dad'e da fita ba na dawo kamar wanda kaga dodo shine harda d'ame kafa kana cin uban gudu ko"? Da sauri Sultan ya girgiza kai yana cewa "dan Allah kayi ha'kuri Yaya ba ganinka ne yasa na gudu ba gudawa nake" Sultan na rufe baki Mami ta fara dariya tana kallon yadda yake d'an ri'ke ciki kamar gudawar gaske yake tace. "Tofa Sultan wannan 'karyar har Ina kai d'in ne kake gudawa ban sani ba amma yanzu dawowar Ahmad ta kamaka ko"? Da sauri ya girgiza kai yana cewa "A'a Mami dama tun jiya da dare na fara wannan abun da kika ban naci ne". "Au 'karya zaka koya wanne abun na baka jiya wanda ya saka gudawa daga safe zuwa dare"?. "Wannan abun fa" Sultan ya fad'a yana sake ri'ke ciki yace "kinji yanzu ma cikina yana 'kugi ga ciwo wayyo Allah na" ya karasa maganar yana dur'kusawa ya fara murd'e-murd'e kamar gaske. "Uhmm" kawai shine abinda Mami tace dan tasan ya fad'a ne kawai neman hanyar tsira yake domin idan ya bari Ahmad ya fahimci dan shi ya gudu tofa saiya sakashi gudawar dole anan gun ko Kuma yace suje toilet d'in ya gani idan gaskiya ne ko kallonsa Ahmad bai sake yiba daya dau'ki key d'in zai fita yace "kaje gurin Abdul-Hamid ka kar'bi magani" da sauri Sultan yace "to". "Ba fad'in to ba idan na dawo yace bakaje ka kar'ba ba wallahi ni dakai ne a gidan nan sai naci ubanka tunda kuna son sake da lafiyarku musamman Baby" yana fad'in haka ya fice 'kak'karfar ajiyar zuciya Sultan ya sauke yana kallon Mami wacce itama ta zuba masa ido da murmushi akan fuskarta zatai magana Sultan yace "ya zanyi Mami" kaita girgiza tana cewa "a'a bansan yadda zakai ba ni babu ruwana sai kaje ka kar'bo kafin yaje inda zaije kasan ya dawo ko baka so saiya saka a gaba kasha alhali ba jinyar kake ba gara ka wuce ka kar'bo sai kazo ka ajiye". "To Mami bari na kar'bo" ya fad'a yana fita ganin Sultan ya fita Baby data mi'ke daga dinning bayan ta karasa cin abincin data zuba parlor ta dawo kusa da Mami tana zama tace "hummm yau dai bari mu d'ana zaman parlon kafin ya Ähmäd yayi yabar mana gu gaskiya wallahi Yaya Ahmad yana da matsala ba dama yabar mutum ya sha'ki iska mai kyau haba jama'a nifa na matsu naga ya koma yaushe nezai ya tafi Mami"? Kai Mami ta girgiza tana cewa "taya zan sani saidai na tambayar miki shi" zaro ido Baby tai tana kallon Sultan daya dawo ri'ke da magani dariya ta saki ba shiri tana kallon sa tace "masu gudawa sai azo asha magani ko ta sauka tunda wanda yasa ka kamu d'in ya tafi" zama Sultan yai yana sauke numfashi yace "barni Aunty Baby ai banyi tunanin zan tsira ba na d'auka zai gane 'karya nake". "Humm ai ramin 'karyar 'kurarre ne maybe daya dawo nan zai fara shigowa ya duba jikinka saidai ka ri'ka kula da kaji dawowarsa ka shige bedroom ka kwanta". "Ai Kuma idan na kwanta zan jawa kaina allura". Kallonsa Mami tai tana cewa "eh ai kaima ita kake nema tunda kai "karyar jinya kayi fatan idan ya dawo kar yasa a d'aura maka ruwa ma" Mami na rufe baki Baby da Khairat suka fara dariya ganin yadda Sultan yayi da fuska Khairat tace "humm yau wani ya fad'a tarko Allah ya fitarka lafiya boss yana nan dawowa gare ka" tashi Sultan yayi yana nufar hanyar bedroom ganin zasu d'aga masa hankali yace "wannan maganganun naku ma kad'ai she'ke ni zasuyi idan naci gaba da zama anan gara na baku gu" ya fad'a yana wucewa cikin tsokana Khairat dake kallon Mami tace. "Please Mami ki tambayawa Baby Yaya Ahmad yaushe zai tafi" Khairat na rufe baki Baby ta dafe 'kirji tana zaro ido waje tace "na shiga uku Aunty Khairat karki yala min masifa so kike yau yayi farfesu na kenan"? Dariya Khairat tai tana cewa "a'a ko d'aya ba son sani kike ba shiyasa na tuna mata ta tambaya miki ko"?. "A'a wallahi ni bance ba kawai abar maganar tashi ma muje 6angaren Sultana Addah mu ganota" ta fad'a tana mi'kewa tace "please Aunty Khairat taso mu tafi Mami dan Allah karki fad'awa Yaya Ahmad komai" kai Mami ta d'aga mata daidai Khairat ta mi'ke suka fita. ✍️Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë. Banda kamarka ya rasulullah a duniya Banda kamar ka ya rasulullah lahira. Ga Mai kyauta da aljannah irin rabon kud'i Ga Mai kure Mai bu'kata yayan imam Ali Ga Mai bayar da kyautar rai zo a hankali Zaka fahimci ba kama Tai duniya da lahira. Gashi da kyan siffa da haiba najidul awatiki in kaga sayyidil wara bakai ba ba'kin ciki ya najamul hudah Annabi dauke shamaki lamunce mu ganka ya mai salsabil da khausara. TYPING 📲+234 81 60 9 8 3 0 83 Chat with me Yusrah Musa Abubakar. 👑 ROYALTY 👑 Dedicated to my daughter Fatima Zarah Elham little Zarahn Aunty. ANNURI WRITER'S ASSOCIATION 💫 Home of hospitality and harmony gidan kar'bar mutane hannu biyu da zaman lafiya ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta. STORY YUSRAH CE WRITTEN YUSRAH CE EDITING YUSRAH CE Idan mutane suna nuna naka kula kaima ka nuna musu.. MRS ÄL'ÄMËËÑ ÄHMÄD ÇË 🌹. 4~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Khaifinah. @YUSRAHMS CE Page 07 & 08 Ayrah tana kwance a bedroom d'inta Abidah ta shigo da ruwa a Kofi a hannunta yaye bargon data lullu'be jikinta tai tana watsa mata ruwan tace "tashi 'yar matsiyata tun d'azu muna jiran kizo ki had'a mana breakfast ashe ke barci ma kike wato gaki isasshiya 'yar gidan isiyaku ko"? Ayrah data tashi a firgice tana sharce ruwan data watsa mata a fuskarta ga sanyi muryarta na rawa tace. "Kiyi hakuri bansan gari ya waye ba wallahi tunda nayi sallah na koma barci" wani irin ba'kin kallo Abidah tai mata tana cewa "oh baki san gari ya waye ba? To ai yanzu kin sani zaki tashi kije ki had'a mana ko saina d'auke ki da mari"? A zabure Ayrah ta mi'ke tana saukowa daga kan gadon ganin Abidan ta d'aga hannu tace "dan Allah kiyi hakuri" a tsawace Abidah tace "zaki wuce ko saina fasa miki baki" ta karasa maganar tana hankad'ota gaba suka yo waje suna fitowa parlor Hajiya Khubura dake zaune ganinsu yasa ta sakarwa Ayrah harara daidai sun karaso Ayrah ta dur'kusa tana cewa. "Ina kwana"?. "Ubanki keda kwanan 'yar gwana na nemi gaisuwarki ne ko shisshigin da kika saba zaki min hamsha'kiya daga barci kika tasheta Abidah ko kuma a zaune kawai take raini ne ya hana tazo tayi mana breakfast d'in"?. "A'a a kwance na sameta sai gwarci da munshari take kamar rago Wai Kuma na tasheta harda wani batasan gari ya waye ba". "Au batasan gari ya waye ba meyasa data fad'i haka baki buge mata baki ba ko ki sharara mata mari yadda zata wartsake da wuri ta dawo cikin hayyacinta"?. "Humm kinsan ma wani rainin hankali Umma tana tashi sai cewa tai wai wani uwarta barci ta koma bayan datai sallah kamar batasan da aiki a gabanta ba". Jawota Hajiya Khubura tai tana tula mata duka a baya tace "Iya barci kika koma ba mutuwa kikai ba naso duniyar kika bari zaki wuce ki had'a mana ko saina tashi a kanki kika zuro min wadannan mayun idanuwan naki masu kala dana mujiya" cikin takaici da 'kunan rai Ayrah ta mi'ke da'kyar take d'aga kafarta tsabar rashin dad'in da take ji a jikinta ta wuce kitchen harta bud'e kofa zata shiga ta tuna bata tambaye su me za'a dafa musu ba dawowa tai tana tsayawa daga nesa dasu ganin yadda duk suke binta da wani irin kallon rashin mutunci tasan ta karaso gurin su sai taci shegen duka muryarta a hankali tattare da damuwa tace. "Me zan had'a muku"?. A masife Nadiya ta mi'ke tana cewa "uwarki da ubanki zaki had'a mana 'yar bagidajiya kullum sai ana fad'a miki yadda zaki aiki idan kinga dama ki kawo mana d'anyan abinci ko kuma ga hanya nan ki wuce ki koma kiyi barcinki ina daidai dake a gidan nan badai gadararki Aiman ba? To wallahi koshi bai isa yai min na 'kyale shiba balle ke banza a banza da'ki'kiya ma irinki" shiru Ayrah tai kamar zata fashe da kukan ba'kin ciki ganin yadda suka saka ta a tsaka me wuya zata iya dafa abinda basa so shiyasa ta tambaye su domin mafi yawancin lokuta suna yi mata haka saita dafa musu suce bashi suke soba suyita bata wahala tana kai komo daga kitchen zuwa dinning karshe idan batai sa'a ba bayan zagi harda duka suke had'a mata.................. Aje wayar hannunta Nadiya tai tana mi'kewa tayo wajenta ganin ta tsaya bata juya ta tafi ba cikin tsawa tace "kee ubanki kike kallo? Zaki wuce kiyi abinda aka saka ki ko saina kashe ki a gun nan" ta karasa maganar tana yowa kanta da gudu Ayrah ta koma kitchen tsaki Hajiya Khubura tai tana cewa "ni wallahi na kasa gane wannan yarinya sam ace kwa'kwalwarta bata ja kullum dan masifa sai ana maimaita mata magana kamar batasan me zatai ba". "Ai Umma idan baki gane ba nasan manufarta so take tayita ja mana lokaci har wannan mara mutuncin Yayan nata Aiman ya shigo ya samu tana yi mana aiki shine dalili saboda tasan kema ba darajaki yake ba balle mu daya tsane mu kamar gidan ubansa ne bayan shima d'an karo ne gara mu munada uwa a gidan zamu taka bazarmu muyi tun'kaho shifa gidan 'kanin ubansa ne kawai bayan haka baida wani hurumi a gidan sai nuna gadara"? Abidah ta fad'a tana hararar kofar da Ayran tabi. Tsaki Hajiya Khubura tai tana cewa "gadararsa ta banza dad'in abun ma tunda ba gado ne dashi ba tanan nake godewa Allah da ace wannan mara kunyar yaron d'an gidan Alhaji ne toda na kad'e wallahi ni kaina bazai barni na huta ba zama saiya gagare ni a gidan nan balle ku saidai ku koma gidanmu to inda Allah ya rufa asiri shima a raka6e yake yana cin arziki shine dad'in abun". "Humm ya kwantar da hankalinsa zai gane kurensa a gaba sharrin da zamu shirya masa saiya gwammaci dama ya mutu kafin zuwan wannan ranar ni nasan abinda zan shirya masa kawai kuyi shiru ba tun yauba na fahimci so yake yasa sai munbar gidan nan 'karfi da yaji d'an Daddy ya share shine shiyasa yanxu ita kuma take sake hura tata wutar da zatai mana sharri kinga idan ya shigo ya tarar tana aiki ai zaiyi magana hakan yasa ta'ki wucewa tai abinda muka sakata jiran shigowar sa take ni kuma saina gwada masa aikin sharri domin sai nayi sanadin barinsa gidan nan". Duk wannan zancen da suke Nadiya tana tsaye tun lokacin data mi'ke zata bi Ayrah bata zauna ba sai yanzu ta koma ta zauna tana cewa "ai kuma tayi a banza wallahi indai ina gidan nan sai tayi aiki ba Aiman ba ko ubansa ne yazo bai isa ya hana ba idan kika ga na daina sata wahala a gidan nan d'ayan biyu ne ya faru kodai nayi aure ko kuma Umma aurenta ya mutu" tana rufe baki Hajiya Khubura ta zaro ido waje tana cewa "ke baki da hankali kike min fata aure na ya mutu kuma? Dan ubanki daina fad'a karki fad'a a bakin mala'iku yana dawowa kisa ya sakeni mu fito rana" dariya Abidah tai tana cewa "ai Nadiya muda gidan nan mutu ka raba takalmin kaza wallahi bamai fitar damu haka Umma babu inda zataje tana nan sai tayi masa takaba wa zai bar irin wannan dukiyar kina gani fa daga iya wannan yarinyar baida wani d'an to me kike zato idan akace ya mutu dukiya ta zama tamu domin wallahi ko sisi baza mu bata ba sannan saita bar gidan kota shiga duniya ko tasan inda dare yayi mata". Kai Hajiya Khubura ta jinjina tana cewa "yauwa 'yar albarka har kinsa naji dad'i domin hakan da kika fad'a har kinsa na shiga wani yanayi kawai haskoni nake dukiyar nan ta zama tawa humm akwai wada'ka dan saina mayar mana da rayuwar mu irin ta turawa yau muna wancan 'kasar gobe muna wancan 'kasar mu zaga duniya mu bud'a idanu ba zama kuma babu wanda ya isa ya tuhume mu duk wanda yayi yunkurin tarata da maganar gadon Ayrah wannan dama sunansa gawa". "Tabbas Umma kin fad'i gaskiya domin babu wanda zai taka mana burki duk wanda yayi yunkurin hakan kuwa zai had'u da bala'in da yafi karfin sa sai mun mayar da rayuwarsa abar tausayi''. Humm Allah sarki duk abinda suke Ayrah tana jinsu saboda ta d'auko plask d'in shayi data dafa zata kawo musu taji abinda suke fad'a jikinta na rawa ta juya zuwa kitchen tana kuka a ranta tana tunanin ya zatai wa zata tara da wannan maganar duk da watsar da ita da mahaifinta yayi a hakan tana son abinta batasan wani abu ya sameshi taji su suna wadannan maganganun innalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah ya fidda mahaifin ta daga wannan tarkon da suke shirya masa Allah ya toni asirin su fasa fita takai musu tea d'in tayi kawai ta juya zuwa kitchen d'in tana kuka tsabar yadda jikinta ke rawa da abinda taji suna fad'a da'kyar ta iya karasa had'a musu abubuwan breakfast d'in sannan ta d'auko ta kawo musu fuska ba walwala tai musu serving zata tafi Abidah ta dakatar da ita ta hanyar fisgota baya tana cewa. "Ke tsaya min anan gidan ubanki zaki tafi dama mun sallame kine"? Ran Ayrah a 6ace ta d'ago tana kallon Abidah wacce ta koma tana huci ta zauna babu wanda ya kalli inda take suna ta zancen su har suka gama suka mi'ke duk sunyi banza da ita kamar sun manta da tsaiwarta a gurin parlor suka koma Hajiya Khubura dake waya bayan ta sauke ta kalli Ayrah dake tsaye kamar an dasata tana cewa. "Ita kuma wannan tsaiwar uban me take ne acan nifa bana son ganinta a parlon nan domin ba irin gurin zamanta bane ke Abidah me zatai miki kika tsayar da ita" d'agowa Abidah tai a wula'kance tace "oh nina manta da ita ma dama takalmi zata goge min zan fita anguwa" ta karasa maganar tana kallon Ayrah tace "ke zo nan ki goge min kafin na tashi tunda naga yau da wani sabon raini kika tashi kuma zanyi maganinki" ko tari Ayrah batai ba balle ta nuna taji haushin maganar da Abidan ta fad'a ba sai qarasowar datai tana shirin dur'kusawa a tsawace Abidah tace. "Da ubanki zaki goge min baki d'auko towel ba" ta fad'a tana kai mata duka da sauri Ayrah ta matsa baya dukan bai sameta ba daidai Aiman ya shigo baiga dukan da Abidah ta kai mata ba amma yaga sanda Ayran ta matsa baya fuska ba rahma ya karaso yana kallon Ayrah data sau'ke sansanyan numfashi cikin jin dad'in ganinsa har tana d'an sakin fuskata dan karya fahimci wani abu muryarta a daidai tace. "Yaya ina kwana"?. Bai amsa ba sai tambaya daya jefo mata "me kike yi anan"? D'an sauke kai tai tana cewa "babu komai". "Babu komai kike tsaye a gabansu matsawar ne naga kinyi"?. Nan ma kaita girgiza tana cewa "babu komai" ganin bazata bashi amsa ba kuma yasan wani abu suke mata amma ya share yana jinjina kai yace "ok muje" wucewa gaba tai yana bin bayanta suka shiga part d'inta da harara duk su ukun suka rakashi Hajiya Khubura data ja tsaki tace "anya wannan yaron kalau kuwa kullum yazo ya 'kule a bedroom d'inta yayi shiru kamar ya mutu ba iskanci suke yiba karfa nan da 'yan kwanaki muga ciki a jikinta dan ban yarda da wannan yawan shige da ficen nasa ba tabbas akwai wani abu a 'kasa". Ta'be baki Nadiya tai tana mi'kewa zata bar gurin tace "aiko Umma da gani babu tambaya kina ganin yadda yake mata abubuwa bayan ba uwa d'aya uba d'aya suke ba kinsan bazaiyi mata a banza ba wallahi akwai morar da yake mata kuma abinda kika fad'a saiya zama gaskiya nikan nayi anguwa" tana fad'in haka ta dau'ki handbag d'inta tai waje kai Hajiya Khubura ta jinjina tana cewa "to haka ne kenan na canka daidai iskanci yake yi da ita tabd'i aiko wallahi ba'a gidan nan ba bari Alhaji ya dawo xan fad'a masa ya dakatar da Aiman ya daina shiga d'akin ta idan yaki wata rana yana gaf daya bud'e ido yaga 'yarsa da cikin shege a cikin gidansa" dariya Abidah tai tana girgiza kai tace "a'a Umma ki kyale shi kawai karki fad'a masa dan Allah ki bari ta haihu idan cikin ya tabbata muci ragon suna musha minti". ''A gidan ubanwa zaku sha mintin kuci ragon? hummm nifa bawai cikin shegen da zatai ne damuwata ba a'a tsorona kar ace 'yar gidan mijina ce labari ya karad'e ko'ina samari su'ki zuwa neman auren ku gara idan ma cikin zaiyi mata ya bari na aurar daku ko kuma ku fara samun wanda zasu aure ku bayan an gama komai saitai cikin nasan dai duk tsiya ita da mahaifinta ne zasu shiga cikin tozarci bani ba ke wannan maganar ma tasa dole naje gurin Hajiya Basirah naji yaya meke tafiya" tana rufe baki Abidah tace "indai haka ne Umma muje na rakaki ayi komai a gabana domin duk burin da

Chapter 5 of 22