Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zakiyi kinsan iyayensa ashe iyayen kud'i ne siyansu yayi suka zo akai auren idan kin tsaya kinyi tunani laifin kine Kuma na tabbata kika bisu Lagos da nufin d'aukar fansa bazaki ta'ba dawowa nan ba sai sun tsafe ki batar dake zasuyi nidai ba ruwana dama na fad'a miki haka batun yanzu ba dan kin 'ki jine amma yanzu Kam kin fahimta ai da kika ga uwar bari". Shiru Hajiya Khubura tai damuwa goma da ashirin wanda take yi danya karfafa Mata gwiwa yace ba ruwansa to taya zata d'auki fansa saidai kawai ta kyalesu Allah ya saka mata Allah ya isa tsakanin ta dasu bazata ta'ba yafe musu ba tana gani Daddy da khaleel suka tafi ita kuma ta koma cikin asibiti. Barinsu gidan ba karamin barazana bane ga Ayrah saboda khaleel ya samu lokacin dazai ri'ka fad'a mata zancen banza da duk abinda yaga dama saidai bai samu cikar burinsa ba duk yadda yaso ta bashi kanta ta'ki ko kad'an bata bashi fuska shiyasa ya samu Daddy akan yana so a saka lokacin bikinsu hakan zaifi masa alkairi idan ta dawo hannunsa amma a hakan nan yana ganinta yana jin sha'awar ta gashi taki amince masa zai iya shiga mawuyacin hali shiyasa ya nemawa kansa mafita tun wuri kafin yaiwa kansa illa Daddy ya tabbatar masa suna kammala school zai d'aura musu aure ko kad'an Ayrah bata sani ba Daddy ba kulata yake ba balle ta sani khaleel kuma ganin yanzu tana da waya yasa bai tareta da maganar tana graduate za'ai musu aure ba saboda tsoron gudun karta fad'awa Aiman ya kira Daddy ya hana a bashi. ***Fara wanka da maganin da Maryam tai humm yadda ta fara cikin nasara haka samari suka ri'ka yimata layi kullum idan ta fita mutun uku hud'u biyar shida sai sun biyota gida lamarin yai mugun damun Mama ganin yadda ake mata layi wanda akai hakan danshi bai ma dawo ba data sani ba'a fara ba saida ya dawo yanzu batasan yadda zatai ba tana ganin saidai su koma gidan me maganin ko akwai wata 'yar dabara da zatai wadannan samarin su daina biyota. Mama tana zaune ita kad'ai a parlor tana tunani har batasan Amaan ya shigo ba duk maganar da yake saida ya ta'bota sannan ta sauke ajiyar zuciya tana kallon sa cikin basarwa dan kar yayi tunanin wani abu tace "Amaan lafiya kuwa naga kamar da akwai abinda zaka fad'a min ko wani abune ya faru"? Kaiya jinjina shima a nasa 6angaren yana sauke numfashi kafin ya d'ago ya kalli Mama data zuba masa ido yace "am Mama dama wata magana zan fad'a miki d'azu Ashraf d'an gidan abokin Abba yace min ranar yazo gidan nan gaisar dake yaga Maryam a lokacin ta shigo yana sonta dan Allah a fad'a miki idan babu kowa nidai nace masa babu duk lokacin daya samu lokaci zaizo" yana rufe baki Mama ta zabura har tana 'kwaruwa wajen cewa. "Yana sonta kuma shi Ashraf d'in ne yace ka fad'a min haka"?. "Eh hakan yace a fad'a muku idan kin amince zai shigo su gaisa Maryam d'in duk yadda sukai shikenan domin bada yaudara yake sonta ba aurenta zaiyi". Kai Mama ta jinjina tana cewa "kuturun ubancan tabd'ijan amma wallahi yaro bashi da hankali uban me Maryam zatai dashi harda wani bada sa'ko a fad'a min? Ya fad'a a banza dan ko Maryam ta rasa masoyi bazata aureshi ba garama karya kuskura naga 'yan 'kafafunsa a gidan nan idan kuwa tsautsayi yasa yazo min gidan nan saina wulakanta shi dan ubansa shid'in banza uwar meya tara a duniya dazai nemi auren mace irin Maryam shashashan banza" ta karasa maganar da 'karfi har kumfan baki take da mamaki Amaan ya zuba mata ido kamar me nazari tambayar dake ransa wanne dalilin ne yasa Mama take fad'a da zage zage dan kawai ya fad'a mata Ashraf nason maryam bayan abun farin ciki ne yayi zaton zaiga ta amshi abun da armashi sai Kuma yaga ta ta'kile shi numfashi ya fitar yana sake d'agowa ya kalleta ganin shita zubawa ido itama yasa yace. "Haba Mama da girman ki kike cewa haka irin wannan maganar ba taki bace Ashraf fa nake nufi d'an gidan abokin abbanmu Abba Ibrahim ko baki gane bane"? Wani irin kallo tai masa tana cewa "ai tunda kace Ashraf na sani basai ka fad'a min kayan takaici ba uwarsa zatai dashi zaice yana sonta ita ba sa'ar auren irinsa bace karya kuskura yazo min gidan nan idan kuwa yazo ubansa zaici". "Kenan yayi laifi Mama dan kawai ya fad'i abinda yake ransa cewa yayifa yana sonta kawai to mene abun laifi anan"?. "Ni a gurina yayi laifi kuma ya fad'i iska ya sota a banza wallahi dan bai isa na bashi auren Maryam ba kome zaiyi ita ba sa'ar aurensa bace tafi karfin irinsa ita saiya canza tasha anan dai bai samu kar6uwa ba". "Ban gane ba Mama taya Maryam tafi karfin aurensa bayan itama mutum ce kamar sa babu wanda yafi wani sai wanda yafi tsoron Allah dukiya basune rayuwa ko jin dad'i ba naga kuma kamar ita kike hange"? Harararsa Mama tai tana cewa "eh Maryam mutum ce bance maka aljana ba amma tafi karfin aurensa ka gane ina nufin bazan bashi aurenta ba kuma kayi min shiru daga haka kar tsautsayi yasa naji ka furta wannan kalmar a gurin alhaji kasan idan magana taje gurin sa kozan mutu sai Maryam ta aureshi kabar zancen iya nan muyi tono mu binne komai a manta da zancen domin hakan bamai yuwuwa bane". "Meyasa zanbar zancen Mama bayan abun alkhairi ne yake bibiyarku amma kuna korewa meyasa hakan"?. "Meyasa zaka bar zancen kake tambaye ta Amaan? saboda ubanka zaka bar zancen ka gane kar nasake jin kayi maganar nan ina gargad'in ka idan tsautsayi yasa ka furta har Alhaji yaji wallahi saina tsine maka gara tun wuri ka kama bakinka" zaro ido waje Amaan yai da mamaki sosai akan fuskarsa yace "Mama meyai zafi tsakaninki da Ashraf haka dan kawai yace yana son Maryam sonta fa yace yana yi kuma dai naga ba wani aibu ne dashi ba kaso masoyinka fa idan ka'ki shi zakaso ma'kiyin ka". Rai 6ace Mama tace "tashi ka bani gu Amaan duk uban da zakiyi Maryam bazata aureshi ba saika ha'kura sannan idan mugun fata ma kake mata itakam bazata auri ma'kiyin taba saidai ta auri masoyinta" mi'kewa Amaan yayi batare daya sake furta koda kalmar aba yabar parlon da harara Mama ta rakashi tana cewa "jimin sokon banza uban me Maryam zatai dashi ga Ahmad jinin sarauta irin 'kasaita zataje tayi zaman aure a gidan sarauta inda mulki da daula suka samu masauki wanda ya fake a inuwarsu maya huta balle Maryam me kankat da zata auri Ahmad gaskiya Amaan yau na yarda baka da hankali anace maka ga gabas kana ga yamma ana ga ruwa kana ga wuta shashashan banza kawai bari zaka dawo ka sameni saina gargad'inka dole saina sake kashe maka warning akan wannan maganar nasan ba hankali ne dakai ba zaka iya idan Alhajin ya dawo ka fad'a masa saidai naji kuna maganar" ta fad'a tana tashi da sauri ta le'ka harabar gida ko yana nan tai saurin fad'a masa kar taje ya tafi office d'in Abbansu yaje ya fesa mai labarin ya jefata a uku ganin babu motarsa harya fita yasa ta dawo ta zauna ita kad'ai sai fad'a take tana zage zage karshe da taga bazata iya ha'kuri ba ta kira Maryam a waya tace tazo yanxu zasuyi magana an samu akasi da akwai matsala gagaruma wacce ta sakosu gaba zaiyi wuya idan zasu iya tsalle wannan damuwar hanya d'aya zatabi dakatar da Amaan shine matakin farko da zata d'auka kafin ta kira Ashraf har gida tai masa tas ta nuna masa 6acin ranta bata goyon bayan Maryam ta aureshi ba matar irinsa bace ya cire idanunsa a kanta. Mama tana zaune Maryam ta shigo ganin yanayinta yasa ko zama batai ba tace "Mama lafiya naga ranki a 6ace haka"? Tsaki Mama taja ta kad'a kai ta ri'ko hannun Maryam ta zaunar da ita a kusa da inda take zaune tana cewa "inafa lafiya Maryam yanzu naji wani abu daya daga min hankali Wai wani shige Ashraf d'an gidan Alhaji Ibrahim ne yake sonki ko a gidan uwarsa ya ganki oho masa to wallahi bari kiji ko tsautsayi zaisa yaxo karkije inda yake idan Kuma kinje kiyi masa mugun wulakancin da takaici zai hana yasake dawowa inda kike ki fad'a masa ba'ka'ken maganganu marasa dad'in ji ta yadda idan ya tafi bazai sake marmarin waiwayar kiba har abada" jin abinda Mama tace yasa ta yamutsa fuskca tana cewa. "Wanne Ashraf kuma a ina ya ganni nidai a tunani na ba had'uwa muke ba balle yace nifa ko fuskarsa yanzu na gani bazan ganeshi ba saboda dad'ewa da mukai bamu had'u ba amma har yace wani yana sona a Ina ya ganni". Cikin takaici Mama tace "koma menene nibai dameni ba sauri zamuyi mu dakatar dashi kafin alhaji yasani kinsan daya sani sai anyi abun nan Niko bana so me laifi ace Humairah yake so bake ba dan kan uwarsa wallahi bazaki aureshi ba idan bazai auri Humairah ba ya ha'kura" ta'be baki Maryam tai tana girgiza kai tace. "Wallahi bai isa ba Humairah ma bazata aureshi ba tunda tana da saurayi me zatai dashi balle ni ina kallon Ahmad kyakkyawan gaske jarumtaccen soja me karfi da kwarjini me zanyi da Ashraf wanda baisan fita filin daga ba baiyi training jikinsa ya murd'e ba kullum yana banki sai kace d'an ministan kud'i nidai bazan auri banker ba garama ya sani ba kud'i nake nema ba sarauta nake so Naga idan zan wuce ana du'ka min ana yabona da yimin kirari ga bayi masu yimin hidima ina tafe ana take min baya wannan shine burina mezanyi da kud'i 'ya'yan banki ina dasu kuma sun wadatar ni tunda nima ba zaman banza nakeyi ba inada sana'a ta balle yace zai rud'e nida kud'i". Murmushi Mama tai harda dagewa tana jinjina kai tace "Yauwa fa karkije gurinsa idan yazo nasan maybe tunda har ya tari Amaan da maganar ki ganshi yazo tunda ba hankali ne dashi ba ya saka mu shiga uku musamman idan akasi yasa Alhaji yana gida ya ganshi yazo d'in kuma yaji ke yake so tabd'ijan heeyyy dan'kari Allah ma ya kiyaye wannan masifa ta samemu domin masife babba ma kuwa da zarar akace yazo shikenan mun kad'e" Cizon yatsa Maryam tai tana cewa "aiko zan nuna masa rashin hankali indai tsantsan hauka ne ya tara ya samu saina tafasa masa jiki da ruwan zafi wallahi saina 'koneshi Allah ya kawoshi ina jiransa zaije yadda ake hauka ganin idonsa". Kai Mama ta jinjina harda cije lips irin muguntar nan ta saki murmushi tana cewa kaji 'yar gari na tabbata kina yi masa haka azaba zatasa bazai sake marmarin zuwa gidan nan koda ziyara bane balle ya furta yana sonki hakan kawai zaki masa idan yazo ki tafasa ruwa me shegen zafi ki lalla6a ki watsawa shege a fuska idan fuskar ta 'kone yai tabo ya samu wacce zata aureshi a cikin nakasassu ko makauniya ko kuturwa amma dai bake ba kekam sai gidan da ake tambari da kakaki inda algaita take tashi wato gidan sarauta" mi'kewa Maryam tai tana cewa "tabbas Mama kin fad'i gaskiya kiran da kikai min kenan zan koma school maybe ma anshiga mana lecture ina nan". "Eh kiran kenan dama abinda zan fad'a miki ne dan kar yayi mana shigar sauri baki sani ba amma tunda kin sani yanzun shikenan naji d'an dama-dama hankalin nawa bai kwanta ba tukuna dai" sunkuyawa Maryam tai tana d'aukar handbag d'inta batare data sake magana ba ta fita Mama kuma ta dau'ki wayarta ta kira Momy taji mene labari akan Ahmad yaya a ina suka tsaya shin yana Shirin dawowa kwana kusa ne su d'au shiri suma ko a'a domin gaskiya itafa ta matsu taga Maryam taje gidan nan matsayin matar Ahmad so take taji tambari da algaitu suna tashi shiyasa bata so abun ya dau'ki dogon lokaci ba'ai ba kar wani akasi ya shigo ciki a fasa". UHMM ALGAITA KUWA ZATA TASHI ZAMU ZO MUSHA BUSA RANAR AUREN NAN MAMA🤣. Nice zanyo gudunmawar ruwan da za'a yayyafawa Maryam idan ta suma🙊 kufa FANS me zaku kawo mata kodan idan kukayi Mata sannu ma ya wadatar😂.............✍️YUSRAH MUSA ABUBAKAR CE. Mrs Äl'ämëëñ Ähmäd çë mai tambarin yma dutse Jigawa state. See you tomorrow morning be with me at always my lover's tnks for ur supports we will meet again ina sonku masoya godiya sosai sosai godiya da jinjina gareku thanks you so much I really appreciate it Yusrah ce. 17~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Shakirnah. Bismilllahir Rahmanur Rahim 📿 @YUSRAHMS CE. Page 33 & 34. Bayan sati d'aya Amaan yana gurin aikinsa Ashraf yaje ya sameshi domin su karasa maganar da suka fara yayi sa'a kuwa a lokacin baya aiki yana free zama yayi suna gaisawa cikin sakin fuska ya kalleshi yana cewa "ya ake ciki ne banker ko kud'i ka kawo min yau nima naje na huta da shan shurba"? Dariya Ashraf yai yana cewa "eh abinda yafi kud'i na kawo maka maganar mu nazo mu karasa akan Maryam yaya kukai da ita ko baka fad'a mata ba"?. "No na fad'awa Mama kaje ne"? Kaiya girgiza yana cewa "banje ba ai baka bani amannar naje d'in ba sannan bansan ka fad'a matan ba idan ka amince ko ayau zan iya zuwa muyi maganar da ita". "Ok karka damu Ashraf duk lokacin da kake free kaje ku gaisa ka fad'a mata komai saboda zatafi fahimtarka akan nina sameta na fad'a mata tunda bansan me yake ranka ba shiyasa gara kaje zuwa dakai yafi sa'ko ko"?. Kai Ashraf ya jinjina yana cewa "Eh tabbas gaskiya ne haka ne amma kasan inada matsala na rasa meke damuna haka kawai ina jin tsoron tarar mace nace mata ina sonta ne sai naji wani irin kwarjininta ya kamani" murmushi Amaan yai yana cewa "tab aiko zaka Sha wahala a gurin mace da zarar ta gane kana jin tsoronta shikenan ta samu kofar da zata ri'ka juyaka kamar waina ka daina fad'a ma kar sujika kawai yanxu idan ka shirya koda yaushe ne kaje ku gaisa" kaiya jinjina yana mi'ka masa hannu suka sake gaisawa yana cewa "ok nagode sosai Amaan insha Allahu zanyi kokari naga naje mun had'u zan tafi ka gaida min Mama kafin na samu na 6ulla"?. "Ok insha Allahu zata ji". Shiru Amaan yai bayan tafiyar Ashraf yasan da akwai ya'ki yau indai ya koma gida ya fad'awa Mama shiyasa a take ya yankewa kansa shawara kawai gara yayi shiru idan Ashraf d'in yaje shikenan ai dai sunsan ba shine ya kawo Shiba balle Mama tai fushi dashi yarda yayi da shawarar abinda zuciyarsa ta yanke masa domin hakan ne mafita tunda ya lura Mama ko kad'an batai na'am da maganar Ashraf yana son Maryam ba ya rasa meye dalili amma yasa a ransa zai bincika ya gani. Watan Nadiya guda cur a asibiti sannan aka bata sallama ta dawo gida badan ta warke ba Hajiya Khubura ce to gaji da zaman can din ganin abu ya'ki ci ya'ki cinyewa ana magani kamar ba'a yi 'kafa kullum a kumbure ba sau'ki kuma iya kokarinsu likitocin sunyi sun rasa inda matsalar take a hakan tana iya tad'an dafe wani sanda da suka bata tana tafiya dashi amma ita kad'ai dai bazata iya ba saidai idan ri'keta za'ai kullum tana zaune guri d'aya tunda tafiya wahala take mata ba ranar da zata fito ta fad'i batai kuka ta tsinewa mahaifiyar Sabit ba dashi kansa Sabit d'in daya yaudareta saboda yana so ya aureta ya'ki ya fad'a mata asalin mahaifiyar sa Ashe duk matar da take zarya ba uwarsa bace uwar kud'i ce siyanta yayi yanzu tana kallo babu yadda ta iya da Ayrah saidai ta zuba ido idan Abidah tana yi mata masifa da zagi amma banda ita domin ba wannan ne a gabanta ba damuwarta ta warke kawai shine a ranta. Yauma tana zaune a parlor ita kad'ai babu kowa sai iya khaleel shi kuwa ba'a cikin parlon yake ba yana can gefe kan dinning ya saka bluetooth a kunne sai kad'a kai yake kamar 'kadangare yana murza yatsunsa alamar kid'an yana shigarsa fitowa Ayrah tai a shirye zata tafi school da littafi a hannunta sauri take ma dan taso makara ganinta yasa Nadiya cewa "ke d'auko min ruwa a fridge d'in bedroom d'in mu ki kawo min yanzu karki 6ata min lokaci" kallonta Ayrah tai kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta aje book din nata tana shiga part d'in ta d'auko mata ta dawo mi'ka mata tai bata kar'ba ba sai wata harara data sakar mata tana cewa. "Oh bazaki aje ba dole saina kar'ba 'yar isa"? Ajewa Ayrah tai tana shirin d'aukar littafinta cikin tsawa Nadiya tace "ke jaka ki mi'ko min cup mana da uban me zansha ruwan kika aje min zaki tafi wato yanxu rainin ki kika tattare ya dawo kaina saboda kinga ba iya tashi zanyi cikin sauri ba balle na kamaki ko"? Wani irin kallon Ayrah ta aiko mata fuska a d'aure tace "saiki nemi jakar ta mi'ko miki kofi kisha ruwa amma badai niba domin ni mutum ce idan baki sani ba ki sani Ayrah Abdul-Kharim nake da kike maganar dan naga kina zaune guri d'aya ne nake miki haka ina ruwana da zamanki dama nina zaunar dake balle ki huce a kaina tashi kiyi yawonki man waye ya hanaki ina tunanin nan a gidan mijin mahaifiyar ki kike ba'a gidan yari ba balle kice baki da 'yanci sai yadda akai dake ai daman kwad'ayi mabud'in wahala tunda kika bi son zuciya kina tare da nadama Dana sani yanzu kika fara gani sai a gaba ma domin hakkina bazai ta'ba barinku kuji dad'i ba kuma zaki gani" tana fadin haka tai gaba takaici da ba'kin ciki ne suka rufe Nadiya ji take inama ace tana da damar tashi lafiyarta kalau yau babu abinda zai hana ta karyawa Ayrah 'kafa ta fasa mata baki cikin 'karaji tace. "Ke dan kan uwarki dawo min nan idan ki isa"? Batare da Ayrah ta juyo mata tace "na isa harna wuce inda kike tunani amma baki da matsayin da kika isa na dawo miki idan kin matsu dani ki taso kizo ki sameni ina daidai dake" sabon ba'kin ciki ne ya sake kama Nadiya ganin yadda Ayran take tsaye tana jiran taje inda take d'in kuma ta juya mata baya ba ita take kallo ba kamar zatai hauka tace. "Wallahi tallahi bashi kikaci kin d'aukowa kanki masifa da bala'i kin d'ebo ya'ki Allah ya bani lafiya na warke zama saiya gagare ki tsabar dukan fitar hankali dazan nad'a miki a gidan nan ni dake ne" baki Ayrah ta ta'be tana cewa "karyar banza kenan na saba jin irin haka a bakin ki sau tari kuma babu wata tsiyar da kike yi sai kuri dama Abidah ce take ganin damata Kuma itama tunda na goge mata baki a jikin bango take shakkata kodan ke baki sani ba amma yanzu kin sani saura ke yadda na fitar da jini a bakinta kema wadannan ru6a66un hakoran naki sai sun fitar dashi ki jira dawowa ta" Nadiya tana kallon Ayrah ta fita ranta in yayi dubu ya 6aci tana zaune Ayrah ke fad'a mata haka yarinyar da suke cin ubanta take tsoron su amma yau itace take fad'a mata maganganu masu razanarwa da nuna alamar ta fara d'aukar fansa................... Jin 'karar bud'e kofa yasa ta mayar da hankalinta gurin ganin Hajiya Khubura ta fito cikin shiri alamar anguwa zata fita ta kalleta idonta yana kawo hawaye cikin takaici tace "wallahi Umma indai na warke saina kashe Ayrah a gidan nan saita ga ukuba da bala'i zatasan wace ni" dakatawa a kanta Hajiya Khubura tai tana kallon 'kafar tata cike da fargaba tace "metai miki ko 'kafar taki ta taka"? Kaita girgiza tana cewa "ba gara ta taka min 'kafa ba akan irin munanan kalaman data fad'a min wai yaushe kukai sake yarinyar nan ta Raina mutune har take cewa ta gurjewa Abidah baki saura ni". "Au haka tace"?. "Haka tace min harda wani wai minbi kwad'ayi da son zuciyar na auri wanda iyayensa basa kaunata sunci ubana na dawo gida kema ba 'kyale ki take ba yanzu baki da wata martaba da Zaki saka ta abu tayi balle ni banza wacce kashin me gadi ma yafini daraja a gidan nan yanzu" zaro ido Hajiya Khubura tai tana cewa "Wai du Ayran ce me fad'in wannan maganar"?. "Itace man yanxun nan ta fita zata tafi school kinga ruwa nan akan nace ta d'auko min kofi nasha bakiji irin zagin cin mutumcin data ri'ka min ba wai ai tasan babu abinda na isa nayi mata ina zaune a daskare guri d'aya kamar bishiya Allah yasa karna warke Allah yasa 'kafar ta ru6e haka tace min" Nadiya ta karasa maganar tana sakin kukan 'karya cizon yatsa Hajiya Khubura tai tana jinjina kai tace. "Aidai addu'a tai Allah yasa karki warke ko? Humm yau kuwa zan gwada mata rashin imani bari ta dawo wallahi saina saka Abidah tai mata dukan mutuwa ta 6alla mata tata 'kafar itama ta zauna guri d'ayan sannan mu hanata abinci yunwa ta kashe mitsiyaciya bari naje anguwa na dawo wannan case d'in har gaban Alhaji sai yaje yaja mata kunne karta kuskura ta sake miki fatan kafarki ta ru6e idan kuwa bai kulaba zaiga hauka ganin idonsa wallahi sai mun kasheta a gidan nan" ta karasa maganar tana huci saboda yadda ranta yake turiri ta kalli Nadiya wacce ta zubawa kafar ta ido tace "bari na dawo Nadiya ki kula sannan karki damu da abinda ta fad'a indai tsautsayi ya dawo da ita gidan nan da kaina zan jawo miki ita har kusa dake na zauneta kiyi mata tsinannan dukan da zata kasa tashi bari Allah ya dawo dani lafiya itama ta dawo" ta fad'a tana wucewa ta fita duk abinda suke cewa khaleel yana zaune yana sauraron su baice musu 'kala ba har Hajiya Khubura ta fita saida ya gama abinda yake zai mi'ke ya kalli Nadiya yana cewa. "Ke dan ubanki idan Umma ta dawo ki fad'a mata sa'ko na idan tsautsayi yasa ta kawo miki Ayrah kuka daketa na rantse da Allah wannan shegiyar 'kafar taki saina mayar Miki da ciwonta d'anye saina take ta da takalmi na mutsustsu ke ta yadda bazata sake moruwa ba saidai a yanke dama ba 'karyar da kikawa Ayran kenan ba alhali bata fad'a humn zan wakilce ta naci ubanki keda Abidan Allah yasa ku daketa na gani" yana fad'in haka shima ya fita daga gidan aka barta ita kad'ai domin Abidah ma tana school gashi Hajiya Khuburan ma ta fice kuka kawai Nadiya ta kamayi saboda ba'kin cikin hanata taci uban Ayrah da yayi tasan tunda yace haka indai tsautsayi yasa ta daketa ba karamin aikinsa bane ya take mata kafar ya dawo mata da d'anyen aiki tasan ba hankali ya cika ba ga6o ne indai ya fad'i magana ka yarda gaskiya ya fad'a maka bai cika ya fad'i 'karya dan barazana ba................... ***Tunda Ashraf sukai magana da Amaan akan zaizo gurin Maryam bai ta'ba zuwa ba saboda tsoron a yadda zata kar'beshi tunda yasan halinta 'yar rainin hankali ce yana so ya gwada zuwan ya kasa abun na matukar damunsa karshe dole ya samu abokinsa ya fad'a masa matsalar sa shine ya 'karfafa masa gwiwa ya bashi shawarwarin ta yadda zaije mata da yadda zai fara ya tsike ya nuna jarumta kar yayi wani abu da zata gane yana jin shakkar tararta da maganar soyayya yarda yayi da shawarar ya kuma saka a zuciyarsa zaije ya gwada sa'arsa fatansa ta amince masa indai yaga ta amince saboda gudun matsala abun bazai dau'ki dogon lokaci ba za'ai bikinsu kawai hakan shine mafita dayin maganar tasu yakai kusan kwana goma baije inda take ba duk da yace zaije sai daga baya har Mama da Maryam sun manta da wani Ashraf yace zaizo yana sonta kamar a mafarki rana tsaka sai gashi yayi musu dirar mikiya ba sanarwa ba zaton zuwansa ganinsa yasa ran Mama 6aci da'kyar ta amshi gaisuwarsa saboda wani irin damuwa da fargaba daya lullu'be ta domin yau Abban su Maryam

Chapter 20 of 22