Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
murmushi ko waiwaye batayi, nikam cikin Alamun sanyin jiki da fargaba nabita a baya. "Sajida" tana shiga ta nemi wuri ta zauna sannan nima na shigo nace to bari na kawomiki kayan breakfast tukunna, tace a'a nayi breakfast a gida tukunna na fito nace duk da haka to bari na ɗan kawomiki ko ruwa ne kinsan bakonka Annabinka "Sajida" tace au ashe kallon baƙuwa kakemin? Nayi murmushi sannan na wanyance nace ba haka nake nufi haba ai ni da ke mun zama abu ɗaya kawai dai naga kin sha tafiya ne shiyasaka kuma ma kinga idan baki ci komai ba ai ba zanji daɗi ace kinzo har gidan mu baki ci komai baki sha komai ba. "Sajida" tace ni yanzu ba wannan ne damuwana ba nazo domin duban lafiyarka domin jiya nayi wani mummunan mafarki a kanka wai ma tukunna ina kasaka wayanka?. Tun a lokacin da na farka daga wannan mummunan mafarki ban sake runtsawa ba hankalina bai kwanta har sai yanzu da nake tare da kai shin baka kirana ba da kuma saqonnina "sajida" tace. Nikam sai na wayance na faɗamata cewa lallai banga sakonta ba kuma banga kiranta da yake jiya nasha aiki a kasuwa na dawo gida da gajiya barci ne mai nauyi ya saceni yanzu haka kinga wayan can a chaji bari na dauka na duba sakon naki, a'a barshi kawai ba bukata" ta fada ka zauna kawai sai na fadamaka abinda yafaru da kai a cikin mafarkin ko nace ya faru da mu. Sajida ta kwashe dukkan abinda ya faru tsakanina da wannan aljani ta faɗamin tabbas babu abinda ya rage wanda yafaru tsakanin da wannan aljani wanda sajida bata fada ba, nayi mamaki matuka sannan tace shin da gaske a daren jiya hakan ya faru agareka kokuwa dai kawai mafarki ne take tambayana. Naja dogon numfashi sannan na kalli fuskanta naga lallai tana cikin damuwa kuma idan na faɗamata cewa wannan mafarkin gaskiya ne zata shiga tashin hankali yarinya ce wacce bata son damuwa ko tashin hankali kokadan kawai sai na wayance nayi murmushi nace haba Kekuwa masoyiyata tabbas wannan mafarkin naki ba gaskiya bane ai babu wata halitta da ta isa ta rabani da ke walau ko dabba ke har aljan fadan hakan ke da wuya naji wani abu tamkar guduma ya daki kirjina faɗowa nayi daga kan kujerar da nake nayi taga-taga Sajida ta tallabeni tana fadin lafiya maye ya sameka? A tsorace nace babu komai da ƙyar na koma na zauna kan kujera ina numfashi sama-sama a wannan lokacin jinake tamkar zuciyata zata fito daga kirjina tsabar zafin wannan duka da kuma fargaba da razana wanda suka addabi zuciyata, hakanan nake ƙarfin hali saboda ina tare da ita bana son ta fahimci halin da nake ciki sannan na fadamata cewa yakamata ta tafi gida tunda ta tabbatar ina lafiya kuma mafarki ne ba gaskiya ba sannan nima ina son zan fita kasuwa babu wata kasuwa da zanje kawai dai na kosa ta tafi saboda wallahi a wannan lokacin tsorace nake gani nake tamkar kasancewa da ita zai iya zama barazana ga rayuwata da kuma lafiyata. "Sajida" tace bana son rabuwa da kai ko na second ɗaya amma yazama dole babu komai idan da rai da rabo ai saura kiris ka zama nawa mallakina, ni yanzu zan wuce idan na isa gida zan kiraka. Mukayi sallama da "sajida" ta wuce. Na dauka wayana na kira Abdul lallai yazo gida akwai matsala ina cikin damuwa da tashin hankali, ganinan zuwa "Abdul" ya fada da Ƙyar na tashi na shiga ɗakina sannan na kwanta ina numfashi sama-sama ina jiran zuwan Abin mamaki sai barci ya saceni. Kiran sunana naji anayi tamkar daga sama buɗe idona ke da naga abinda yabani mamaki kuma ya tayarmin da hankali matuka Abdul nagani a tsaye fuskarsa cike da mamaki da takaici yana tambayana " shin maye ya kawo Sajida ɗakin ka? ". Ina dubawa naga lallai"Sajida" ce a gefena tana barci abinta fuskarta cikin da annushuwa nayi zumbur na mike na sauka daga gadon ina goge idanuwana a tunanina mafarki nake sannan na fahimci cewa lallai ba mafarki bane gaskiya ne. Zuciyata ta cika da sake-sake da tambayoyi wanda bana da amsar su sannan da tunanin tayaya zan fahimtar da Abdul abinda yake tunani ba haka yake ba, ina cikin wannan tunanin ne ta farka cewa take " haba masoyi gaskiya ya munajin daɗin mu zaka tashi ka barni kakuwa san yadda naji daɗinka gaskiya kaidin na mussamman ne ashe haka kake da kwarewa gaskiya idan mukayi aure zanji daɗi sosai, a tsorace na kalli cikin idanuwanta naga tamkar wacce ta sha cocaine hakan yasanya na tabbatar da cewa lallai ba "Sajida" sannan ta dago kanta ta kalli Abdul au Abdul ne mara da babban baƙo "sajida" shikam tsaki yayi sannan ya juya cikin fushi ya fita yana fadin lallai Ishaq kabani mamaki wallahi ban ta6a tsammanin haka daga gareka ba Ashe kai fasiki ne mazinaci wallahi yau da ace wani ne ya fadamin cewa ka aikata hakan wallahi sai inda ƙarfina ya ƙare domin na yarda da kai fiye da yadda na yarda da kaina. Amma abin takaici da idona naga wannan mummunan alaƙar kuma abin takaici da yarinyar da zaka aura wacce iyayenta suka yarda da kai kaji kunya Ishaq dan haka daga yau babu ni babu kai kaga tafita. Ya juya yafita daga falon nikam inata binsa ina "Abdul Abdul" dan Allah ka tsaya ka saurareni ko juyowa bayyi ba nabishi har gate kawai ya tarbi abin hawa ya tafi idanuwansa cike da ƙwalla, ya tafi ya barni cikin dimuwa tashin hankali da rashin sanin abinda yakamata nayi. Na duka tsakar gida inata kuka gami da tunanin abinda yakamata nayi, ina cikin wannan halin ne dariya naji mai kama da sauka aradu a tsorace na dago fuskata ba kowa nagani ba sai "sajida" itace take mummunan dariya mai cike da sanya fargaba da tashin hankali sannan tayi wata girgiza take naga ta zama wannan aljanin da yazomin a daren jiya. Ya fara da cewa " yakai bil'adama mai taurin kai da rashin kunya lallai bakasan sharrin mu ba kasani cewa zan sakaka cikin tashin hankali dimuwa da bala'i wanda baka tsammata ba, nasani cewa yanzu zuciyarka tana cike da tunanin yadda zaka shawo kan "Abdul" lallai bazaka iya ba domin nayi nasar rabaku har abada, kuma wannan ba komai bane daga sharrina zan rabaka da dukkan farin cikinka wanda zaka gwammace mutuwa da rayuwa Zan jefa rayuwarka cikin masifa bala'i da jalala lallai tashin kiyamar rayuwarka zai zo tare da hisabinka batare da ka mutu ba. Sannan ya sake kyalkyalewa da wannan mahaukaciyar dariya ya 6ace. Da Ƙyar da rafe da bin bango na koma cikin falo sannan na faɗi ƙasa a falon ina shiga ɗakina amma abin ya faskara take na fita hayyacina sai dai farkawa nayi naganni a gadon asibiti kokadan banyi mamakin ganina a wannan hali ba domin kuwa abinda ya faru dani kamata yayi kawai na farka a kabarina ina ganin sai nafi samun kwanciyar hankali da nutsuwa. Ummana ce kawai a tare da ni banga "Ameer" ba ko sauran dangina shi daman "Abdul" nasan ba lallai yazo ba ita kuwa ummana kuka kawai takeyi, ganin hakan ya sanya nayi tunanin shin kodai "Abdul" ya tonamin asiri ne lallai idan 'Abdul" yamin haka yaci amanata. Cikin sanyin murya gami da tsora nace "umma" kukan maye kikeyi firgigi "umma" ta dago kai jin muryata tace ALHAMDULILLAH ashe zaka tashi ai har mun cire rai da rayuwarka yau satinka 4 baka ko motsi ballantana muyi tunanin tashinka. Likita ya tabbatarmin cewa lallai saidai tsanin rabo tashinka domin rayuwarka tana cikin tashin hankali kadan ya rage zuciyanka ta buga saboda abubuwa sunyi yawa a cikinta ya bukaci sanin maye yake damunka nikuma ban sani ba. To amma ya fadamin cewa lallai idan Allah yasanya ka tashi yakamata musan damuwar ka sannan a kiyaye dukkan abinda zai 6atamaka rai, ni da uncle ɗinka mun zauna mun yanke wani hukunci wanda muke da tabbacin tabbas zai faranta ranka fiye da yadda ake tsammani zai kore duk wata damuwa da take damunka, amma yanzu idan mukaje gida zakaji koma maye. Cikin ƙarfin hali nace to amma ya naga babu kowa a tare da ni sai ke kadai kodai wani abu ya faru ne?, "Mama" tace a'a babu komai ai "Ameer" yanzu yabar nan uncle ɗinka ma ɗazu da safe yazo ita kuwa "sajida" nan take wuni yanzu ma taje karbomin wani Sako ne, amma abinda yabani mamaki ace duk wannan dadewa da kayi a kwance yaron nan "Abdul" baizo ba shin kodai kayi masa wani abu ne?. Nayi charaf nace a'a Umma wallahi babu abinda nayi masa ta yuwu ayyuka ne suka mishi yawa kokuma dai wani uzurin, murmushi tace har kayi wannan kwanankin kana asibiti rai hannun Allah baizo ba sannan kace wani uzuri ai ince ko bangon duniya yake a abotar da take tsakanin ku wacce ta rikide ta zama 'yan uwantaka yabar duk abinda yake yazo, kawai dai akwai abinda yake faruwa tsakanin ku wanda kake 6oyemin yanzu dai mu bar wannan maganar ga abinci kaci nasan kana jin yunwa. Umma tabani abinci da hannunta naci abincin sosai har na ƙoshi sannan muka cigaba da fira da ita har dare ya fara, kwatsam muryan "sajida" naji tayi sallama abinda yabani mamaki kenan tana shigowa ta tarar dani a farke " ALHAMDULILLAH naji ta fada ashe ka farka ashe rabon zan sake ganinka ashe da rabon zanyi rayuwar aure dake Ashe kafin ta faɗi abinda zata fada "Umma" tayimata nuni da tayi shiru. Nikam jin wannan kalaman nata suka sakani mamaki da tunani da kuma tunanin maye zata fada Umma ta katseta. Nace "SAJIDA" tace na'am " shin maye yasakaki zuwa asibiti yanzu ashe bakiga dare yayi ba yakamata ace kin bari sai da safe ai, tunda kinga ke mace ce bai dace ace kinayin yawo haka ba, Sajida " tayi dariya tace ai yanzu zan tafi gidan dama nazo ne kawowa 'umma" sako sai kuma nayi dace na tarar da abin farin ciki. " Ni yanzu zan wuce amma in sha Allah gobe da safe zan dawo, nace to sai da safe domin kuwa a wannan lokacin na matsu ta tafi gani nake tamkar wani abu zai sake faruwa da ni mukayi sallama ta tafi." Bayan kwana 2 likata ya sallameni sannan yace nayi kokarin cire damuwa a raina sannan duk abinda zai 6atamin a kiyeyeshi, muka koma gida kullum "Umma" burinta farin cikina duk abinda zai sakani farin ciki shi "umma" takeyi rannan sai na tambayeta akan ta faɗamin maganar da suka yanke ita da uncle tace nabari sai gobe da safe uncle dina zaizo zanji koma maye, nikam na kosa gari yawaye domin jin wannan abin farin ciki. Washe gari da sassafe sai ga uncle "labaran" yazo gidan mu a nan yayi breakfast bayan mun kammala sannan yace Ishaq a matsayin mu na iyayenka masu kaunarka masu son ganin farin cikinka tabbas wannan abin da yake damun zuciyanka wanda bamu san dalilin wannan damuwa taka ba, kai kuma ka gagara fadamana gashi abin har yana neman rabaka da rayuwarka, to ka sani cewa mu bazamu matsamaka dole sai ka fadamana ba amma dai mun zauna munyi nazari akan abinda zai kawo mafita da farin ciki na har Abada a rayuwarka. Ishaq idan baka manta ba kafin ka kwanta wannan rashin lafiyar aban "Sajida" ya baka auren 'yarsa wacce har naje mukayi magana akan auren ku nace hakane "uncle". To kasani cewa munyi nazari munyi hasashe ni da mahaifiyarka da kuma Abban ita "sajida" ɗin mun tabbatar da cewa aureka da ita shine kawai zai sanya farin ciki a rayuwarka da kwanciyar hankali wannan dalilin ya sanya lokacin kana kwance a asibiti aka daura aurenka da "sajida" a lokacin da mahaifin nata yasanya tun kana da lafiya ba'a chanja lokaci ba. A taƙaice dai yanzu sajida matarka ce dama mun bari idan Allah yabaka yabaka lafiya sai ayi biki sannan ku tare sannan mahaifinta yace zakaje a nuna maka gidajensa ka za6i wanda yayi maka domin ku tare kai da amaryarka. Innalillahi!!! innalillahi!!! innalillahi!! Na fada har sau uku domin kuwa na fita cikin hayyacina a wannan lokacin sannan na dora hannuna akai ina fadin " shikenan kun kasheni wallahi nasani yau bazan kwana ba saidai cikin kabarina nasan bazasu barni ba, suwaye fadamana "ISHAQ " lafiya kake kuwa kodai ka sami ta6in hankali ne?" STORY BY Iliyasu Falalu Lawal WRITTEN BY NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️ https://chat.whatsapp.com/Bd1Zu1cwIO81A7rrATd4Cu 🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗 Book two BY NARNAH KANWAR SOJA 💫ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION 💫 SADAUKARWA Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕 Zahrah Royal Star Page 30 "Tabbas lafiya na kalau amma abinda kuka yanke kuke tunanin shine zai sakani farin ciki to lallai kunyi kuskure, lallai hakan da kukayi tamkar kun nisantani da farin ciki ne tamkar kun salwantar da rayuwta ne lallai ina da tabbacin cewa Ƙarshen rayuwata yazo. Cikin damuwa da rashin fahimta "Umma" ta kamani ta zaunar dani nikam a wannan lokacin jikina rawa kawai tamkar wanda aka sanya cikin kankara sanna tace Ishaq " bamu fahimci duk wannan sambatun da kakeyi yakamata kayimana bayani abinda yake faruwa. Na kwashe labarin duk abinda yake faruwa na faɗamusu hatta rabuwar mu fa "Abdul" Umma" ta tsorata sosai da jin wannan labarin kuma jikinta yayi sanyi matuka hatta shi uncle "labaran" " tace lallai yakamata a nemi mafita domin ni bazan bari rayuwar ɗana guda ɗaya tilo ta salwanta ba, lallai ko raba auren idan takama dole ayi. Uncle "labaran" yace dole a nemi mafita amma lallai babu maganar raba aure akwai wani malami wanda yake garin maiduguri lallai ya kware wurin fitar da aljanu komai taurin kan wannan aljani dole ne zai fita ya barku kuyi rayuwa da matarka. Bayan kwana biyu mukaje gidajen Abban Sajida aka kewaye da mu ni da ita gidaje ne sun wuce 150 har sai da muka gaji da yawa sannan dai muka za6i wani guda ɗaya daga ciki, sannan aka kirawo wannan malamin yayi addu'o'i da rukiya a wannan gida bayan kwana biyar akayi shagalin biki muka tare ni da amaryata. Aikam a wannan dare naga bala'i da masifu wanda ko a littafi ban ta6a jin irinsu ba a wannan dare na gwammace da banzo duniya ba. Farkawa nayi naga Umma , Sajida uncle"labaran" "Ameer" umman "sajida" da Abbanta da kuma wannan malamin da yayimana saukan Alqur'ani da addu'o'in kafin mu tare a gidan malamin ya fara da cewa yakamata kayimana bayani abinda yake faruwa da kai domin musan ta wacce hanya zamu iya taimakonka ga dukkan alamu wadannan aljanu so sukeyi sai suna halakaka. Nace tabbas hakane Malam bacin tsarewa ta ubangiji da tuni sunyi gunduwa gunduwa da sassan jikana na kwashe duk labarin abinda ya faru dani na faɗamusu "umma" ta fashe da kuka sannan ta kankameni tana fadin wallahi nidai kawai a raba auren nan bazan bari a kashemin ɗana guda ɗaya tilo ba shi kadai Allah yabani. Malam ya bawa Umma hakuri sannan yayi mata alkawarin lallai a yau kuma a nan dole ne zanyi maganin wannan aljani komai taurin kansa yanzu ina bukatan a kawomin wuta take aka kawo wannan wuta malam ya ciro wani garin magani ya zuba a cikin wannan wuta sannan ya umarci Sajida da ta dawo kusa da wannan wuta domin ta shaki yakin wannan magani. Amma duk da haka a banza domin wannan wannan aljani bai bayyana ba shi kanshi malam yayi matuqar mamaki yace lallai wannan aljani hatsabibancinsa yayi yawa tunda nake ban ta6a yin wannan hayaki ba ba tare da aljani yayi magana ba amma idan yasan wata baisan wata ba, take malam ya ciro wata 'yar karamar kwalba tamkar kwalbar turare sannan yacewa Sajida ta shaka. Shakawarta ke da wuya take sai ji mukayi muryar ta ta chanja idanuwanta suka kada sukayi jajur tamkar garshin wuta, sannan ya fada cewa malam ka kirani naki zuwa amma shine sai ka kirani da tsiya to kasani cewa komaye zakayi bazan fita jikin "sajida" ba domin ita ɗin matata ce. Ina ka ta6a ganin anyi aure mutum da aljan Malam ya fada lallai kai cikakken azzalumi ne kuma yau zan kawo karshen zaluncinka ko da tsiya ko da arziki dole ne yau ka rabi da wannan baiwar Allah zan konaka da ayoyin ubangiji ko kaki ko ka so yau zaka bar jikinta dan haka ina mai shawartaka gara katafi ta lalama. Aljani ya bushe da dariya wacce ta sanya duka falon nan sai da ya girgiza tamkar za'ayi girgizan ƙasa sannan yace abinda baku sani ba dukkan ku hatta mahaifin Sajida da mahaifiyarta tun kafin ku haifeta kakanta kanta ma'ana babanka kai babanta ya dauramin aure da ita. Abinda ya matukar bamu mamaki kenan sannan Malam yace yakai wannan azzalumin aljani wannan abin da ka fada bazai ta6a kasancewa ba. Aljani yafara bada labari kamar haka:- a shekarun baya kakan wannan yarinyar Alhaji "wada" ya kasance bashi da komai shi talaka ne talakan tilik tsabar talauci ya sanya kowa yana gudunsa hakan ya sanya ya rasa matar aure babu wanda yake son hada jini da shi, wannan al'amari yana matukar damun "wada" sosai hakane ya saka ya shiga kungiyar shan jini cikin kwanaki kalilan ya sami manyan kudade ya tara gidaje na alfarma da motoci tun a wancan zamanin yayi aure amma bayan yayi aure da zarar ya sami haihuwa sai wannan kungiyar ta sha jini bukaci ya basu yaron gashi shikuma yana son yara sosai. Abin yana matukar damun sa hakan ya sanya yayi tunanin bujirewa wannan kungiya tunda yanzu ya sami kudi gara ya gudu ya chanja gari idan yaso a can zai raini duk yaran da aka haifa masa ya zauna cikin farin ciki, wannan kungiya suna sane da duk abinda yake ƙullawa hakan yasan sukayi masa kashedin cewa lallai idan ya bijirewa umarnin su zasu haukatashi sannan su kasheshi. Abin ya matukar tayar mashi da hankali kullum baya bacci yadda yaga dare haka yake ganin rana yana cikin wannan halin ne nazo na taimaki rayuwarsa da yarjejeniyar cewa lallai idan ya sake samun haihuwar 'ya mace to idan ta girma zai bani aurenta saboda ina son auren macen bil'adama. Alhaji Wada ya amince sannan na cigaba da kareshi daga wancan matsafan ina kare masa dukiyarsa sai da ya zama a lokacin duk yankin babu mai tarin dukiya wacce tayi rabin ta Alh "wada" ana hakane matar Alh "wada" ta sami juna biyu amma abin takaici sai ta haifi ɗan Namiji ba kowa bane face kai. Nayi bakin ciki matuka bisa ga rashin cikar burina amma sai mahaifinka Alh "wada" ya bani hakuri sannan yace yamin alkawarin ko cewa muddin idan ka girma kayi aure idan ka haifi 'ya mace to yabani aurenta ko yana raye ko baya raye shidai burinsa na cigaba kare dukiyarsa da kuma kai kanka, a bisa wannan alkawarin nake har yanzu da nake baku wannan labarin kasan mu aljanu bama karya alkawari kamar ku bil'adama. Munyi matukar mamaki da jin wannan labarin na wannan aljani mun shiga cikin alhini matuka kuma tabbas abinda ya fada zai iya kasancewa gaskiya saboda kudin mahaifin Sajida tabbas ko shi bai san adadin su ba, Mallam yace " to munji duk abinda ka fada amma yanzu ina son ka fita jikin wannan yarinya saboda kana cutar da ita babu aure tsakanin mutum da aljan kuma ita batasan abinda yake tsaninka da kakanta ba. Wannan aljani yace bafa zan fita komaye zakuyi kuyi Malam yace tunda haka kace zaka gani yanzu kuwa na malam yasake shakawa Sajida wannan turare tayi wata kururuwa sannan tayi zunbur ta nufi kofa a guje nan "Ameer" da abbanta suka riketa da Ƙyar sannan malam ya cigaba da addu'a da karanta ayoyin Alkur'ani sannan ya ciro wasu kalolin turaren sunkai biyar yasanya aka danne ta ya shaka mata halin da naga "Sajida" a ciki sai da nayi ƙwalla. Wani nishi takeyi tamkar gurnanin zaki sanna aljanin yace dan Allah kuyi hakuri zan fita amma komai daren dadewa sai na dawo jikinta, malam yace au haka kace ashe baka dandara ba kenan nan ya cigaba da karatu yana shaka mata wannan turari. Ba shiri wannan aljani yace wallahi zan fita daga yau babu ni babu ita haihata haita har gaban abada bazan sake dawowa ba wata irin atshawa "Sajida" take sai ta dawo hayyacinta tana kallon mu cikin mamaki, jikinta babu karfi yayi lugub lugub har sai da doctor ya sakamata drip 2 sannan karfin jikinta ya fara dawowa. Mukayiwa Malam yace godiya sannan Abban "sajida " ya ɗauko kudin masu ya baiwa malam sannan yamar alkawarin kujerar maka shi da dukkan iyalansa, ni da Sajida muka fara rayuwar farin ciki domin a wannan lokacin mukasan mu ma'aurata ne bayan shekara ɗaya Allah ya azurtamu da samun karuwa ɗa namiji. ALHAMDULILLAH nan shine karshen labarin Sajida da Ishaq BACK TO STORY BAYAN WATA Yazid bai gama rufe baki ba sukaje ƙarar bindiga ba taƙaitawa da sauri John ya Shure Ihsan Maryam da Ado suka ƙankanme hannu a yayin da Yazid ya fara Lega musu hanyar waje da gudu suka nufi ta baya suka fara gudu ba kama hannun yaro Gaban su yana bugawa da ƙarfi kamar ana buga ganga, zuciyoyin su sun kasa kamewa da tsoro da fargaba. Ado na ja gaba da sauri yana nunawa da hannu: "ga wata mashiga! wannan hanya ce ta tsallaka zuwa Jordan! mu yi gaggawa!" John da har yanzu ke ɗauke da Ihsan a kafaɗarsa, ya danne raunin sa yana bin Ado da sauri. Maryam kuwa na kokarin bin su da ƙarfin hali, hawaye yana kwaranya a fuskarta. Amma Yazid... Yazid ya tsaya baya kadan yana duban motocin da suka sake dawowa da wasu sojoji masu bindiga. "ku cigaba!" Yazid ya ɗaga musu hannu da karfi, yana fadin: "ku cigaba da gudu! kar ku tsaya! nima zan biyo baya!" ya waiga yana kallon su cikin duniyar tausayawa Suka ci gaba da gudu da ƙyar, zuciyoyinsu na kuka. Amma kafin Yazid ya juyo... Gudu-gudu — ƙarar bindiga! "TA! TA! TA!" A gaban idon su, Yazid ya faɗi a kasa yana kwance sai jini dake zuba a saman ƙirjin sa ya juyo da idon sa yana ganin hanyar da ƴan uwan sa suke , a hankali yaki motsa bakin sa idon sa tsaye chakk akan hanyar su Maryam ta ɗaga hannunta tana kiran sunansa da karfi: "Yaziiid! Yazid ka tashi! Yaziiid!!" John da Ado suka rike ta da karfi, suna toshe mata baki John ya girgiza kanta da hawaye a idonsa, yana cewa: ba za mu iya dawo da shi ba... Maryam, don Allah... don Allah ki ci gaba da gudu..." Hawaye kamar ruwan sama suka zuba daga idon Maryam, zuciyarta na shan wani raɗaɗi mai tsanani sun tsallaka shingen bodar Jordan cikin kuka da wahala. Sun tsira — amma sun rasa ɗaya daga cikin su! lokacin da suka hau ƙaramin tsauni, suka waiga baya, suna ganin hayakin harbe-harbe da ƙarar bindigu da hayaniya. Rayuwa ba ta tsaya jiran kowa ba. suka ci gaba da tafiya cikin Jordan — da hawaye, da rauni, da zuciyoyin da suka karye. kowa ya san... ba za su taɓa mantawa da Yazid ba har abada. Bayan sun shafe kwanaki biyu suna tafiya a cikin garuruwan Jordan, cikin wahala da ƙuncin zuciya, suka kusa tsallaka bodar zuwa ƙasar mai tsarki Saudi Arabia. gaban su, rana na saukar zafi kamar wuta. ƙasa ta bushe, iska na fuskantar su da ɗan ƙura kowa na tafiya kamar wanda aka shake da ƙunci da raɗaɗi John ne ya tsaya, ya ajiye Ihsan ƙasa a hankali ya shafa gumi daga fuskarsa da hannunsa mai rauni. Maryam ta durƙusa a gefe, tana hawaye da ƙyar tana kallon shafin ƙasa kamar tana gani a cikin sa Ado kuwa ya tsaya gefe ɗaya yana kallon sararin sama mai shuɗi, kamar yana neman Yazid a cikin taurari , ya sauke numfashi mai nauyi yace da raɗaɗin zuciya: "Yazid... Ka tafi ka bar mu mun zo tare, amma ba za mu ƙare tare ba ..." Maryam ta fashe da kuka da karfi, ta ɗauki yashi ta yayyafa a kanta tana fadin: " da ace zaka jure, Yazid da ace zan iya dawo da kai!..."John ya dafa kafadarta da ƙyar yana cewa: "Allah ya jikan sa, ya gafarta masa, ya sanya

Chapter 9 of 18