Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
za ta fara ba su a sansani, zai kasance labari cikin labari, wanda zai haɗa ƙauna, yaƙi, al’amuran fada da sirrin da ta ɓoye har yau. ) PRINCESS RAHILA EPISODE ONE 2000 Years Back Sunanta Rahila – kyakykyawa ce tamkar hasken wata, bakar fata mai sheƙi, jikinta dirin coca-cola shape gashinta ya sha bamban da na kowa a masarautar Buga African, kuma idanunta sun yi farin haske har cikin duhu. murmushinta na bayyana haƙora masu tsabta da kyau halittarta ta ban mamaki ce, fiye da na kowace mace a wannan ƙarni. Rahila ita ce tilon 'yar da King Numan ke da ita bayan shekara da shekaru ba tare da samun ƙarin 'ya'ya ba, sai ya tara soyayya da dukiyarsa gaba ɗaya ya miƙa mata. Baiwar da bai ba kowa ba, ya ba Princess Rahila – wacce ake kira da wannan suna cikin girmamawa. Masarautar Buga African ta kasu gida biyar: 1. Yankin Burum 2. Yankin Dusrum 3. Yankin Tursum 4. Yankin Kurum 5. Babban yanki – Buga African, karkashin King Numan. Tunda mahaifiyarta ta rasu tana da shekara biyar, Rahila ta tashi tare da mahaifinta duk wata buƙatarta ana cikawa, kuma soyayya ce ke ratsa tsakaninsu tana da shekaru goma sha biyar amma ta riga ta kware wajen amfani da makamai kamar takobi, kwari da baka, guggar zana da salon yaki – duk sabili da Slave Kodo, babban gwarzon bawa kuma mai ba King Numan kariya. Fadar King Numan cike take da dukiyar duniya da bayi duk da cewa bai ƙara aure ba bayan rasuwar matar sa, yana amfani da wannan damar wajen tilasta wa matan bayi duk matar bawa da ta rasa mijinta, ko baiwar da take kyakkyawa, za ta faɗa hannun sa. Rahila ta kai shekaru ashirin kyaunta ta kai kololuwa duk sarakuna da attajirai sun so mallake ta amma ta ƙi. a cewarta, ba za ta bar fadar mahaifinta ba kuma ba za ta zauna ƙarƙashin kowane namiji ba. Wannan ra’ayi nata yasa wasu sarakuna suka rasa idanuwansu saboda kallonta da soyayya. Ta yi imani cewa mahaifinta zai rayu har abada ta ɗauka rayuwarta zata kasance cikakkiya har abada a haka ne ta fara koyon mugunta, ta nuna ƙarfin hali da alfahari. Ta san ta fi kowa kyau da ƙarfi. Ta ƙi yarda wani namiji ya kwanta da ita. Tana ganin ƙarfinta da na mahaifinta da na mayaƙa – musamman Slave Kodo – zai iya kareta har abada amma sai wani abin mamaki ya faru… Lokacin da ta dawo daga kogin da ta saba wanka, tana kwance a gadonta, bayi biyu na tausa ƙafarta, wasu na shiryata, sai wani bawa ya shigo cikin gaggawa tayi mamakin ganin shi ya shigo ɗakin ta ba tare da izini ba. Cikin fushi ta watsa masa mari har sai da ya firgita. Yana kokarin cewa “The king sees…” amma ta katse shi da bacin rai, “So what? He's my father, I can go to him anytime I want!” Da ƙyar ya fice, amma cikin mintuna sai ga King Numan da kansa ya shigo ɗakin wani abu ya dame shi, hakan yasa Rahila ta shiga fargaba – abu da ba ta taɓa ji ba. Bai taɓa shigowa ɗakin ta ba da kansa. "My baby, we must leave Buga African immediately!" ya faɗa cikin damuwa. "What? Leave our kingdom? What is happening?” Rahila ta tambaya, cikin tsoro da rashin yarda. "Zuma people (Dursum) have invaded our palace! We've been betrayed. Even our soldiers have been sold out!" in ji King Numan. "NO, Father!" ta ce cikin jin kai. “nu shugabanni ne! Dole mu yaƙi mu mallaki su mu mayar da su bayi!” Ta ɗauko takobinta mai haske, wanda ta keɓe, tana shirin yaƙi. Amma fa, yaƙin da ya zo ba kamar sauran bane. Cikin hanzari, Slave Kodo ya shigo. “Your majesty! Prince Tarhim na Dursum ya shiga tsakiyar fadar da mayaƙansa!” King Numan ya kama hannun Princess Rahila. "My jewel, please, follow Kodo. He will take you to safety." “No! I won’t run like a coward!” Ta ce cikin kuka da bacin rai. Amma King Numan yasan lokaci ya kure kuma burinsa shine ya ceci tilon 'yarsa King Numan ya dube ta da ido mai cike da ƙauna da alhini. Hannunsa yana rawa yana riƙe hannun 'yarsa Rahila, kamar yana ƙoƙarin ƙara ji da ƙarfi a jikinsa da ya fara rauni. "My jewel... I know my time has come," ya furta cikin rauni. "But I will not let them take you. You must live, even if I die." Princess Rahila ta dafa ƙirjinsa da duka hannayenta biyu, idonta na cike da hawaye masu ƙyalli, tana girgiza kai. "No Baba, don’t say that! You will live! we will fight together!" Amma Sarki Numan ya girgiza kansa cikin sanyi."I’ve seen this in my dream... Kodo knows what to do. He’s been waiting for this day." Yayi kallon ƙarshe ga Slave Kodo, wanda yanzu ya yi shiri da kayan yaƙi, gashi yana kama da jarumin da ba a taɓa ganin irinsa ba. "Kodo," in ji Sarki Numan cikin murya mai ƙarfi, "take her... and make sure she survives. That’s an order." Kodo ya durƙusa, ya ce da kwarjini:By the gods of Buga Afirican, I will protect her with my life." Princess Rahila ta sake fashewa da kuka. Tana janye hannunta daga na mahaifinta tana cewa:"Baba... don’t let them take our land..." Sarki Numan ya matsa kusa da ita, ya sa hannu a bayanta ya rungume ta na ƙarshe. Ya furta a kunne ta da ƙasa sosai: "You are the land now. You are Buga Afirican. Go... before it’s too late." Sai ga wata ƙara ta fashe daga wajen fadar. Wuta ta fara tashi daga ɓangarorin fada, ƙamshin hayaki da jini na ratsa iska. Wakilan Zuma da Prince Tarhim sun karya ƙofa, sun shigo da mayaƙa cikin izza da azama. Slave Kodo ya ɗauki Rahila kamar jaririya, ya fice ta wata ɓoyayyar ƙofa dake bayan gadonta—ƙofar da aka gina shekaru dari da suka gabata domin irin wannan lokaci. Sarki Numan ya tsaya da kafarsa, ya zare takobinsa mai daraja, wanda aka gada tun zamanin kakanninsa Ya fuskanci mayaƙan Zuma da ƙarfi, yana ba da na ƙarshe na jinin sarauta domin kare masarautarsa. An bar fadar cikin hayaki. An bar sarki cikin yaƙi. an fita da Rahila cikin duhu. Wannan rana ce ta zame wa Buga Afirican tarihi Ranar da wata sarauniya mai ƙarfi ta rasa gida, ta rasa uba, amma ta samu sabuwar rayuwa—rayuwar da zata yi nasara ko ta mutu tana ƙoƙari...... Continued by narnah ƙanwar soja ✍️ https://chat.whatsapp.com/DoFR3n8lLtI1RB5Zd2z2IT 🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗 AFTER THE MOON BY NARNAH KANWAR SOJA ( Sayeddan Addah ) 💫Royal Star Association,💫 SADAUKARWA Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕 Zahrah Royal Star Page 5 & 6 Yawan sharhin ku yawan typing banyi alkawarin posting kullum ba , mujeee zuwa tafiya ta fara tafiya show me some love guy's 🩷 بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على محمد وسلم Haka abin ya faru da Sarki Numan haba ɗaya mutanensa sun gaji da mulkinsa, wasu daga cikin mayaƙansa sun juya masa baya, suka sayar da kansu ga mutanen Dursum, wanda suka sayi rabin mayaƙan domin samun nasara a kansa. "Kado, ka kula da ‘yata. Ita kaɗai ce abin da na mallaka," inji Sarki Numan, ya faɗa wannan karo fiye da goma. "Eh, mai martaba, zan kareta da raina," Kado ya sake amsawa cikin nutsuwa. " Baba ka bar ni na tafi tare da kai!" Princess Rahila ta faɗa cikin kuka, tana faɗawa jikin mahaifinta. Ba ta son wani abu ya same shi ita fa ba komai ba ce idan ba tare da mahaifinta ba. “Je Kaɗo , tafi yanzu da ‘yar gadona. Ka kiyaye ta kamar zinariya.” Sarki Numan ya faɗa da murya mai ƙarfi, irin ta jarumai, sannan ya juyawa wajen baya yana barin gurin. Princess Rahila ta sake gudowa ta rungume mahaifinta daga baya da jin ɗumin hawayenta a bayansa, zuciyarsa ta raunana sai dai ya ƙi juyawa saboda kar ta hango hawaye a idanunsa — alamar rauni ga jarumi kamar shi. Duk da haka, yana son Rahila ta ci gaba da tunawa da shi a matsayin jarumin sarki, gwarzon da yaƙi bai faye shi ba, ba mai zubar da hawaye saboda galaba ba. Bayan wani lokaci, Rahila ta saki mahaifinta, sannan ya tafi ba tare da ya waiwayo ba. Baba Baba Ka kalleni ko sau ɗaya,” Rahila ta faɗa tana fāɗowa kan gwiwowinta, amma Sarki Numan bai waiwaya ba yana ƙoƙarin ɓoye hawayensa.“My princess, dole mu tafi yanzu,” Kado ya faɗa yana ƙoƙarin tashi da ita, amma ta ture shi.“Kar ka kuskura ka saka kazamin yatsunka a kaina!” ta faɗa cikin ƙiyayya. (Duk da girman haɗari, girman kai na sarauta ya mamaye ta.) Kado bai ce uffan ba. ya saba da halayenta, tun da shi ya horar da ita duk da haka, shi kansa bai tsira ba suka fice ta wata sirriyar hanya da ba kowa ke san da ita ba, sai dai shi da Sarki Numan. Yayinda Sarki Numan ya dawo fadar sa, sai ya tarar da rabin masarautar an lalata ta. Mayaƙan Dursum sun riga sun mamaye wajen. Sarki Numan ya shiga ɗakin sirrin da ke ajiyar makamai, ya sa tufafin yaƙi, ya ɗauki manyan takubba guda biyu zuciyarsa cike da fushin jarumi, ya kuduri niyyar mutuwa a matsayin gwarzon sarki maimakon guduwa kamar gwanin fargaba. A lokacin yaƙi... Yaƙin ya riga ya barke, sara suka hannu da ƙafa. Sarki Numan ya fafata kamar zaki, yana yanke mayaƙa tamkar bishiyoyi lokacin da ya hango Prince Dursum, tun da farko ya ɗauka Prince Tarhim ne, sai dai da ya kalli fuskar, ya gane cewa uban ne — Sarki Mujus. Da haka ya soki kansa ƙasa, alamar ƙarshen nasarar da yaƙin zai iya kawo masa. Sarki Numan ya ci gaba da gwabzawa har sai da zuciyarsa ta fara kasa dukan da kyau. Bugun zuciya ya rikice, zuciyarsa ta mutu da ganin 'yarsa cikin halin ƙaskanci ya sulale ya fāɗi ƙasa, ya zubar da makamai, hawaye na zuba daga idanunsa. “Ba zai yiwu ba! wannan ba gaskiya ba ce!” ya ƙwala ihu cikin azaba. “… ku bar ta ku kyaleta, ku bar ta haka kawai,” Sarki Numan ya roƙa yayin da aka jawo Princess Rahila cikin sarka, tana kuka. Jikinsa ya kasa tsayawa, ya durƙusa, yana kallon Prince Tarhim yana ja da sarkar Rahila, har ta durƙusa ƙasa yana kai ta gaban mahaifinta, yayin da wasu zaratan mayaƙa suka kewaye su yanda yake ganin ‘yarsa tamkar bayi, ya girgiza zuciyarsa sosai. Princess Rahila ba komai ce a wannan lokaci ba face bawa, jikinta da datti da ƙura, gashinta ya bazu. “Ga ‘yarka, Sarki Numan babu sauran princess, yanzu bayi ce a ƙarƙashin masarautar Zuma,” inji Prince Tarhim, ɗan Sarki Mujus — jarumin da ya kashe dabbobi da suka kai hari garinsu, Zuma shekaru 27 ya fafata yaƙe-yaƙe masu yawa. Dogo ne, baƙi fari, da kyakkyawar fuska. Fuskarsa da sunansa suna tayar da hankali, musamman ga mata.“Wannan ba zai faru ba!” Sarki Numan ya ƙara faɗa. “, ku bar mahaifina shi ne Sarki na Buga Afirka,” Rahila ta faɗa cikin kuka. Sarki Mujus ya fusata, ya jawo gashin kanta. Rahila ta yi ihu cikin ciwo da azaba. “Great king kike kira? kin san abin da mahaifinki ya aikata wa mutanen masarautata?” inji Mujus. Sarki Numan ya ce, “Kaɗo ne ya yi alkawarin kare ki.” “Baba Kaɗo ne ya ci amanar mu,” Rahila ta faɗa cikin murya mai cike da raɗaɗi. Mahaifinta ya firgita. “Kado? Amintaccena?” “Eh, Baba ya ƙaddamar da komai.” Kado ya bayyana yana faɗi, “Na tuna kuka na iyayena da ‘yar’uwata lokacin da suka mutu a hannunka. kayi musu hukunci da wuta saboda haraji na jure, na koya darasin rayuwa har na zama bawan da kake amincewa da shi amma yau sai na ɗauki fansa ta, in ga yadda ‘yarka ke zama bayi, kamar yadda ka mayar da ‘yan’uwanmu bayi.”Sarki Numan ya ƙara fashewa da kuka, “Kado, me nayi maka har ka yi haka?” “Zan bar ka da rai, Sarki Numan amma zan tabbatar ka gani da idonka lokacin da ‘yarka ta fuskanci cin mutunci kamar yadda wasu suka fuskanta.” “Don Ubangiji… a kyale ta ku daina wannan,” Sarki Numan ya ce yana ihu, yana ƙoƙarin miƙewa a lokacin ya sharɓi wuka daga hannun wani mayaƙi. ...ya sharɓi wuka daga hannun wani mayaƙi, ya sharɓa a cikinsa da ƙarfi, jini ya fara malala daga bakinsa, yana kallon ‘yarsa da ƙyalli na ƙarshe a idanunsa. “Rahila…” ya furta cikin muryar da ta dushe. “Babaaaa” ta ƙwala ihu da karfi, tana ƙoƙarin tashi daga kan guiwowinta, amma ankai mata dukan da ta sume nan take. Kafin idon Sarki Numan ya faɗi ƙasa shikake, ya rasa numfashi daga nan, aka ɗaukaka tutar Zuma a saman fadar Buga Afirka aka kama bayi da mata da yara, aka raba su. Masarautar Buga Afirka ta faɗi ƙasa, ta koma cikin tarihin da ake karantawa da ba’a taɓa tsammani ba. "Father please don't dîe. Please don't... don't, I beg you! Somebody please help me. Please save my father." Princess Rahila tana roƙon mayaƙansu "Save your... breath.. my jewel, take...take...care of yourself. I love you my baby rahila ke tuna ke sarauniya ce juye duk abinda kekeso da zaran kin samu dama " King Numan aya faɗa wanan shine sautin sa na ƙarshe , "Father please, please stay with me please don't leave me." p rincess Rahila ta faɗa cikin ƙunar zuciya tana daman jan tokobin daga cikin sa sai da tasha wuya kasancewar hannunta da Chain "Father please don't leave me. "Father no...you can't do this to me, you can't leave me here all alone!" Princess Rahila ta f ad'a da ƙarfi wanda gabaɗaya ta razana gun da ihun ta ta ɗaga tokobin sama tana kallon yanda jinin mahaifin ta yaki wanzu akai , ta saita dai dai cikin ta da wuƙar , "let me go you ....Let me go right now, ka bani tokobi na zan kashe kaina na huta Princess Rahila ta faɗa tana ihu lokacin da Prince Tarhim ya ƙwace makamin hannun ta , "Tarhim ka barta ta mutu duk da haka uban ta baya nan da zaiga kalan hukunci da zan mata let her kill her safe and go , Shashasan ya kashe kansa already don haka ita ma barta ta kashi kankara kowa ya huta useless girl I do not care anymore" ."Father, do you think it will be okay for us da zamuga tana kashe kanta " ya tambaya ciki da sonjin amsa daga mahaifin nasa" ƙwarai da gaske wannan shine tabbatar da cewa mun gama samun nasara a wannan yaƙin.... "Keep quiet, shut up you son of bitch , don't talk to my father like that!" Prince Tarhim ya faɗa yana tunkuɗe ta daga kusa dashi Wanan yayi dai dai da zartar War tokobin king Mujse saitin kanta sanadin bangaja da ta sama tayi ƙasa tokobin ta kwace wa kanta cikin haushe da takaice rashin samun ta raised up his sword again after yayi rashi nasara daga farko da zumar filli kanta charraf Prince Tarhim ya kama hanun sa kafin tokobi sa yakai head of princess Rahila " father u don't have to do this akaiw hanyoyi da dama da zamuyi amfani akanta "What is wrong with you son? shin kaman ta yanda Uban ta ya kashe ɗan uwan ka ?" king Mujse ya faɗa cikin kaɗuwa da mararrin jiki . The king Mujse Taki yaji komai ya zama sabo burin sa kawai kashe ta ko zai rufe wanan chapter daya jima yana mafarkin samun nasara akan sa. Prince Bella firstboy na king Mujse wanda ya bashi matsayi prince yana da mata Princess Afrah wanda suki zauna lafiya sun haifi yarinya ɗaya Aflim tana da wata biyar Prince Bella ya haɗu da mummunar ƙaddarar sa da ta janyo baƙin cikin da tsananin ɗaukar fansa na king Mujse.. King Mujse ya aika Prince Bella zuwa meeting to wanda za'ayi a birnin Kursum inda manya manyan sarakai zasu haɗu su tattauna to solve a issues affecting their kingdom prince Bella Jauro got dressed and said goodbye to his family. inda suka rabo d kyar ta hanyar kukan baby Aflim king Mujse ya amsheta da rarrashin ta yana cewa shi bazai samu zuwa ba duk da cewa yaron sa yana. tareda da sabon baby babu but ya hallarchi taron kasancewar shine next of the king . Shin a hakane zaka jagoranci kujerar mulki idan bana nan ? zaka ajiye duty saboda akan kukan baby ?! a lokacin da ya hangi tsantsan tausayi baby Aflim da mutuwar jikin Prince Bella , "Her mother is here and your mother is here too. We are all here to take care of her so please, you must leave at once son." King Mujse ya maimaita maganar cikin ƙwarin guiwa da yaki bawa Prince Bella ,They didn't know that it was the last hug and last goodbye. Duk sarakuna sun kammala haɗuwa a inda Aki jiran king Numan wanda ya ƙaraso da dukkan tawagarsa cikin isa da mulki da kaddara dukkan su suka miƙi tsaye wasunsu har ɓoya bayan wasunsu suki , kasancewar sa Jarumin jarumai da babo mai ƙarfin ikon sa a wannan nahiyar , Duk abinda yake faruwa Prince Billa ya chigaba da zama ba tareda ko kallon sa yayi ba In one-time ba zato ba tsammani ya zaro tokobin sa ya sara kansa taki y rabi gida biyu sai jini da ya wantsala umarni ya bawa Slave's nasa da susa kansa cikin akushi su ƙona ganganr jikin sa da wuta a idon duniya su " ku ɗauki tokan ganganr jikin sa kukai ga uban sa ku sanar masa dukkan abinda yafaru ya sanarwa ɗaya daga cikin dakarun da suka sa prince Bella rakiya inda yayi arrest na sauran suka zama Slave's nasa . A lokacin da King Mujse yaji wanan Labarin sosai ya razana inda queen Afra ta. kamu da heart Attack a wanan time Prince Tarhim ya chigaba dajan ragamar shugabancin Dursum After sometime soon king Mujse ya warke yafara plan tareda mutanen sa plan to their revenge hakan ya faru sukayi nasara ganin ga king Numan kwance a cikin jini a masaurautar sa king Mujse yana shirrin Kashi Princess Rahila prince Tarhim ya dakatar dashi ..... BACK TO STORY "Father, wanan shegiyar yarinyar can't dîe just like that. I have a better plan for her ." Prince Tarhim ciki da tsananin fushi da fusata King Mujse baxai iya jira ba yaji wanan plan nin ba King Numan already dead but still bazai iya yafe mishi akan kashe ɗan sa ba dole sai ya kashe ta zai samu sallama He would do anything to complete his revenge mîssion "Father, you will be helping her if you kîll her now. a rashin sani uban ta ya tsira daga punishment za muka shirya masa taya zamu barta itama jikinta ya tafe a banza Rahila dole ta biya bashin da ubanta yaci akanmu mu barta har sai ta roqe mutuwa da kanta da muguwar azabar dazamu ɗanɗana mata let's kill her slowly Kanta ta ɗaga sama tana kallon sa da idannunta da suki wanzuwar da jini a kowani tsako daki da jijjiya a. ƙwayar idon "son of bithch kill me now you have only one change kar kabari wanan damar ta wucce ka Tarhim because jaine mutum na farko da zan fara kashewa idan ka barni a raye da Rayuwa ta "I shall kîll you all one by one. gabaɗaya ku sai kun ɗanɗane zumar kaɗai na mutuwar ku a tafkin hannuna i sweer with my beloved father ." "I, the princess of Buga Afirican promise you all today. sai na kawo ƙarshen ƙasar Dursum ta durgusa a kan guiwarta sai na sa kun tsani kanku ta faɗa with her fire eye's bata damu da zaratan mazajen da suki kewaye da ita ba burinta kawai suyi zuciya su kashe ta ko zata huta da wanan bak'ar rana da ko. mafarki batayi tunanin kasancewar sa ba .. "Son, did you hear that? jinin Numan yana kewaye da ita she is devil too kill her rayuwarta tamkar na uban ta ne" , dogon tsaki yaja Prince Tarhim ya kasa fahimtar meyasa ta kasance very hot stubborn duk da cewa tana ganin tana daga da mutuwa even in the face of dànger. "Father, I know how to handle people like her." "One day, you will beg for my mercy." Prince Tarhim ya faɗa yana matso da hannun sa akan fuskar ta matsar da fuskar ta tayi da tofa masayawun da ya haɗa jini in his face dariya ya kicce dashi yawa hannu ya gogge yana dungule hannu yakai mata wani mugun nashi da saida ya fasa mata kefin bakin ta King Mujes daya amince da yaron sa ya yanke hukuncin ya barta ta kasance matsayin baiwar su ,it felt like a dream to Rahila batasan da cewa watarana wanda yaki chan sama duk matsayin da mulkin sa ko ƙaddara sa da dukiyarsa watarana zai faɗo ƙasa warwas ba kaman ƙitfawar ido King Mujse later cût off king's Numan head from his body. ya ƙona ganganr jikin sanan ya umurce dukan bayin sa suyi wasan harbil harbil da kansa a sansanin masarautar buga Afirican the most powerful king of Buga Afirican bazai iya aikata komai ba kasancewar yau da kansa ki wasa a sansanin masarautar da idon dubanne mutane da bai ɗauki su a bakin komai ba yaki wulakanta su sa kiran su baye marasa amfani sai gashi shine yau a wannan matakin All that happened front of Princess rahila wacce taki kuka ta tana rogon sa da yadaina azabtar da kan mahaifin ta sai dai kash hakan ƙarawa king Mujse ƙarfin guiwa yakiye da azama Har abada zaki yafi ƙarfin ayi wasa a gaban shi har akai masa raini ko suka sai dai idan ya kasance mattace har yaro zai iya matsowa don yayi wasa dashi hakan ta kasance kansa ya zama abin nunawa da dariya ga muradun buga Afirican . Cikin Chain a maƙale da wuya ta da hannun ta da ƙafarta Prince Tarhim yana kan dokin sa yana janta cikin ƙunchi suka kama hanyar Dursum ana ball da kan mahaifin ta wanan abin yafi mata muni akan yanda mutanen buga Afirican suki kallon ta a wulaƙanchi even when she asked water sai dai tasha ruwan hawaye ta wanda suki zuba layi layi tsananin tsana da ɓaci rai da mugunta daban daban taki saƙawa prince Tarhim tabbas indai ta ƙungiya shine mutum na farko da zata kai lahira kasancewar bata da wani babban maƙiyi sama dashi ...... Princess Rahila batayi tsammanin isowar Dursum zai kasance sillar tsayawar hawayen ta sakamakon ganin cincirindon al'ummar garin sun fito kansu da ƙwarƙwartansu suna watsa mata duwatsu wasu kuma tumatur da takalma lallai ta sami tarbar na musamman haushi mulkin ubanta da nata taki amsar hukuncin daga gari su Numfashi ta ne ya tsaya chakk lokacin da aka harba wani talkami ya sauka akan fuskar ta tunawa da cewa idan ace yau yana raye babo wanda ya isa ya ɗaga mata ɗan yatsa a gaban ta Taki ta yanke jiki sunammaya inda yayi dai dai da isowar su wani bakin ɗaki su dark and hurt prince Tarhim ya tsuma ta da umarnin kawo ruwan mai ɗumi aka watsa mata taki ta dawo daga suma ta cikin. azaba ta ƙwala ƙara tunda taki for the first time taga irrin wannan duhu duk da cewa takan iya azabtar dawasu a irrin sa batayi tunanin kasancewar haka a garita ba . NARNAH ƘANWAR SOJA 🖋️💞💝💝 https://chat.whatsapp.com/DoFR3n8lLtI1RB5Zd2z2IT 🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗 AFTER THE MOON BY NARNAH KANWAR SOJA ( Sayeddan Addah ) 💫Royal Star Association,💫 SADAUKARWA Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕 Zahrah Royal Star Page 7 @ 8 Yawan sharhin ku yawan typing banyi alkawarin posting kullum ba , mujeee zuwa tafiya ta fara tafiya show me some love

Chapter 2 of 18