kallon ƙauyen su da ke raguwa a bayanta kamar mafarkin da ya ɓace. hannunta na cikin haɗaɗɗiyar rigarta, amma zuciyarta na cikin tsohon zanin ƙauyenta.
Motoci suka fice daga Gembò, suka fasa hanyoyi masu kura, suka dosa garin Yola inda jirgi zai tashi zuwa Abuja. Halima na zaune cikin mota, amma kamar a mafarki ta kasa kallon sabbin gine-gine da suka wuce su, kamar ba su da ma'ana gareta.
A lokacin da suka isa filin jirgi, an ce mata "Halimatu! Ki sauka ",ta sauka cikin rigima, tana kallon ƙasa kamar tana tsoron ƙasa ce zata buɗe ta haɗiye ta ba ta san me ake nufi da “ticket” ba ba ta san yadda ake biya ba yanzu ne Halima ke fara jin bambancin rayuwa, ta kasa cire takalmanta a wajen sakan na’ura, sai da ma'aikaciyar ta fara dariya ta ce:
“Yarinya! ba salla za ki ba wannan tsafta ne da dokar jirgi.”
taji kunyarta sosai Idonta ya cika da ƙyama da tozarta a zuciyarta:
“kai! ashe akwai duniya kamar haka?”
Bayan an kaita cikin jirgin, aka ɗaure mata seat belt, ta riƙe kujerar kamar wacce ke cikin ruwa mai zurfi. Da jirgi ya tashi, ta saki ƙara mai firgitarwa:
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Wayyo Moddibbo…! na mutu!”
Alhaji Saminu ya rike hannunta da dariya “babu komai Halimatu, jirgi ne ke tashi kawai.”
Kamar sabuwar tsuntsuwa aka ɗauke daga ciyawa, aka ajiye cikin gini mai fanfo. As zuciyarta, birni kamar wata. Amma tambaya ɗaya ke ci mata rai: Shin wannan sabon garin da take ciki zai taimake ta ta samu sabuwar rayuwa, ko zai ɓata mata tunanin da take tsaye da shi tun ƙuruciya?
Tunda suka hau cikin jirgin sama, Halima ta kasa zaman lafiya idanunta na zagaye cikin hadadden komai wanda ba ta taɓa mafarkin wanzuwarsa ba , tana kallon tagar gefe, tana ganin sararin samaniya da ƙasa na raguwa kamar yadda aka rage wa tunaninta hankali. amma wani abu ya sake ɗaukar mata hankali...
A kujerar bayan nata, wani saurayi ne zaune, ya murtuƙe fuska, idonsa kamar na damisa mai zurfin tunani , fuskar sa doguwa ce, fara tas kamar bulo, ƙuncinsa yana da ɗan launin ja, bakinsa siriri ne amma mai ɗan ƙasaita gashin kansa an rage shi tsaf yana sheƙi, sai karan agogon zinare a hannunsa na hagu ya ƙara ɗaukar hankali.
Shima yana kallon Halima, ba da sha’awa ba, amma da mamaki da tausayi kadan kamar yana cewa da kansa, “Ina aka samo irin wannan ‘yar ƙauye mai tarin kamala?”
suna cikin tashi ne Halima ta saki ihun da ya gigita kowa
“Wayyo Allah naaa! waye ya ce jirgi zai ɗaga?! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”
Mutane sun juya suna kallonta, mata suka dinga dariya a nutse, wasu kuma suka tausaya amma shi saurayin da ke baya—ya kalli fuskarta da jajayen idanu, yana juyar da kansa a hankali cikin murmushin gefen baki, kamar wanda ya saba da irin haka a rayuwar zuciyarsa , sun sauka a filin jirgin Abuja, wanda ya bude musu sabon shafi a rayuwa.
Alhaji Saminu ya nufi Maitama da su, inda katafaren gidansa ke cike da girma da kima. gidan na da kofa babba mai lanƙwasa kamar ƙofar masallaci a Makka. farfajiya ce a waje, da lambu mai yalwa, sai tsuntsaye ke ta raira waka kamar sun san sabon baƙuwa ta iso.
Yayin da Halima ta kalli ƙofar katafaren gidan, zuciyarta na wani irin doki da tsoro da fargaba, wani sashe na ruhinta na faɗin "kin fito daga ƙauye, amma an jefa ki cikin birnin masu hannu da shuni..." da zuciya ɗaya ta shiga, sanye da kayan aure na gargajiya: mayafin fulawa, zobba a yatsu, da dankwali mai yatsin zinariya.
A cikin gida, motoci sun sha jerin gado, masu gadin gidan biyu a ƙofar shigowa suna miƙa gaisuwa da ban girma. Gidan kuwa – katafaren alfarma ne wanda ba a taɓa mafarkin Halima zata taka kafarta ciki ba. Babban falon yana da manyan tagogi masu labulen fata na turkiyya, cike da fitilu na chandelier masu hasken zinariya, cikin falon ne Hajiyah Nafisa ta karɓe ta da murya mai cike da mamaki:
Matar Alhaji Saminu, Hajiyah Nafisa, ta fito sanye da kayan alfarma gashinta a jikin mayafi yana sheƙi kamar rigar sarauta ta kalli Halima da murmushi na ɗan lokacin, amma idanunta na cike da alamun tambaya:
“Itace wannan yarinyar?”
Halima ta kasa magana ganin palon gida kadai ya isheta tiles ne na zinariya da hoda mai sheƙi, fanfo a bango da tebur na gilashi. tana takawa kamar ana binsa da ƙasa. Zuciyarta na cewa:
“To wallahi... haka birni yake ko dai na mutu ne an kawo ne gidan aljanna ?” kwalliyar da aka yi mata da kayan Fulani na auren ƙauye—maye da zobe da mayafi na fulawa—ya sa ta ƙara haske , amma a fuska akwai shakku, akwai salo na “ba sani ba sabo.” sai dai akwai mutunci a tafiyarta, wanda ba’a koya shi a birni.
“Nafisa itta ce amaryata na biya sadakinta tun can ƙauye kamar yadda na gaya miki. Allah yasa alkhairi.”
Hajiyah Nafisa ta tabe baki cikin murmushi mai nauyin fahimta daga kallon ta ɗaya ka gane ko da tana ƙoƙarin karɓarta, zuciyarta ba ta cikin hakan gaba ɗaya.
Sai da aka kai ta ɗakinta da aka tanadar mata cikin gida ɗaki mai faɗi sosai, bangon sa mai launin cream da zinariya an shimfiɗa masa carpet mai laushi, akwai gado babba da labule mai juyawa kamar na sarauta taga biyu na dakin suna kallon lambun cikin gida, inda tsuntsaye ke ta shawagi, cike da kyan gani. dakin na da fanka da AC, amma Halima bata san amfani da komai ba. Sai kallon su take kamar kayan sihiri.
Ta zauna a gefen gado daidai lokacin wata mai aiki – Hasiya – ta shigo da murmushi a fuskarta. Hasiya daga Sokoto ce, mai ƙanƙantar jiki da zubin kawaici atake suka fara haɗuwa Hasiya ta ce da ita:
“Wallahi Aunty Halima kin yi kyau, da gaske ne ke daga ƙauye?”
“Eh... daga Gembo,” ta ce da dariya mai daɗin ji. “kin taɓa jin sunan kauyen?”
“A'a, amma yanzu na ji ki. sai dai ki gyara nan Abuja fa ne Idan baki yi wayo ba, sai a cuce ki.”
Nan suka fara zama ƙawayen gaske. Halima ta fara ɗan sabawa cikin gidan, musamman da yaran Alhaji Saminu goma da ke gidan. akwai Muneerah da Ruqayyah – ‘yan mata manya masu haɗe da kwalliya da rashin kunya, masu jin turanci da yi wa Halima kallon kamar uwar kauye suna kiran ta “that girl from bush” a bayan ta.
Sannan akwai Aminu Junior da Zaid, samari matasa da suka fi ɗaukar lokaci a wajen gidan basu damu da sabuwar mace, sun fi shagaltuwa da motocinsu da rayuwar club da Instagram.
Yara uku ƙanana—Sulaiman, Abbas, da Fadilasun fi sabawa da Halima suna zuwa ɗakinta suna wasa da ita ta dinga yi musu wasan shanu da dabbobi da kida da rawa irin na ƙauye, suna dariya kamar an saka musu annashuwa a zuciya tana ɓoye wannan zumunci da su domin kada uwayensu su ji.
Matar biyu kuwa, Hajiyah Mariyah da Hajiyah Sabeerah, su ne abokan huldar Nafisa amma Hajiyah Mariyah ce shaidaniya, mai haƙurin fitina da halin mugunta tana kallon Halima da kyankyami, tana cewa:
“Wato wannan ƙaramar ‘yar Fulani ce ta zo mana da daddare? Allah ya sa ba za ta ja mana Alhaji ba.”
Tun daga rana ta fara tsara yadda zata nunawa Halima cewa gidan ba da sauki ba ne. tana tura mata ayyuka kamar ba matar aure ba: “ki share wancan, ki gyara kicin, ki tafi can ki goge banɗaki.”
Halima kuwa, da jin kunyar Fulani da biyayya, sai ta dinga yi tana mika hannu da zuciya, ba tare da kuka ko korafi ba inda Hasiya ta fi shiga tsakiya, tana mata nasiha da rarrashi:
“Ki yi haƙuri Halima, nan ne birni idan kika nuna rashin juriya, sai su hana ki kwanciyar hankali amma Allah yana tare da mai gaskiya.”
A haka Hajiyah Nafisa ta dinga kallon yadda Halima ke yi wa yara wasa, tana girki da kyau, tana wanke-wanke da murmushi da farko tana kyamar ta, amma wata rana ta shigo dakin Halima sai ta ganta tana dinki wa Fadila riga da hannu wani abu ya motsa a zuciyarta. Ta ce da kanta:
“Wannan yarinyar... ba ta da mugunta kuma girmanta yana shigowa hankali.”
Halima kuwa har yanzu bata san haka ba. zuciyarta na yawo ne da tambayoyi: “shin wannan rayuwar ita ce rabona? ina mahaifina da mahaifiyata? W
wannan Alhaji Saminu fa, me yasa yake sona?
wani dalili ne yasa ya kawo ne gidan sa ya ajiye tsawon lokaci bai dawo garine ba?
Ohhhhhhhh ga Halima ga Abuja
a sannu a hankali zamu shiga labarin Halima
continued ƙanwar soja in Sha Allah
✍️
https://chat.whatsapp.com/BsQ0CkOCA83FgwnQ177z9y
🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗
AFTER THE MOON🌕
BY
NARNAH KANWAR SOJA
MARUBUCIYAR
MIJIN MAGE
FARASHIN SO
BIYAYYA GA UWA
DUHU CIKIN HASKE
RUHI BIYU
HANYAR RUWA
MAI CIKI CE
MADOBIN IDO
AHLIN LASHKAR
PRINCESSS RAHILAT
RAYUWAR UMMAH
BAYAN WATA
💫ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION 💫
SADAUKARWA
Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕
Zahrah Royal Star
Wannan page na sadaukar dashi ga mutum biyu Sister Juwairiyya M Lawan tare da Najeeb Allah ya bar zumunci enjoy the page guys
19 / 20
Wata bakwai kenan cif da zuwan Halima gidan Alhaji Saminu wata uku na rayuwa da ke cike da shiru, da sanyi, da kewa, da dogon kallo zuwa fitilun falon cikin dar wata bakwai bata taɓa ganin fuskar mijinta ba sai sau biyu kacal sau na farko da ya kawo ta gida, na biyu kuwa yana wucewa da mota, ya tsaya da taga yana kallon ta ba tare da ya sauka ba.
Tunda lokacin, Halima ta fara tantama: “shin ni matar aure ce ko kuwa ba haka bane? ko kuma na fi zama ‘yar aikin gidan alfarma da ba ta san ko wane ne mijinta ba?”
Gidan kuwa kamar gida ne na almara: bangarori fiye da shida, kowane ɗaki kamar wani gida daban. Halima ko bandakin da aka ce na nata ne ma sai da Hasiya ta koya mata hanyarsa da yadda za ta kunna ruwa daga famfon lantarki ta ƙi fita daga dakin nata sai idan da gangan, yaran gidan sun zama mafita ga zuciyarta Sulaiman da Fadila na mata wasa, suna biye mata da dariya da kida da rawar kauye ita kuma tana jin daɗin hakan, tana samun nishadi duk da zuciyarta na ci gaba da yin rauni da damuwa.
a wannan daren, kamar kullum, ta zauna a dakin nata cikin sanyi mai daɗi daga AC da fitilar tagwayen da ke ba dakin ƙamshi ta jingina da kujera, tana kallon hoton kwane-kwane da aka ɗora a bango hoton tsaunuka da furen da bata taɓa gani da ido ba, hawaye ya fara gangaro mata ta shafa su da gefen zane, tana kiran zuciyarta da sunan gida: “Kauna, Kaka, Baraka... ina kuke? ko na fice a nan in dawo Gembo da ƙafa ne? ko gidan da kuke tsirfa hatsi yanzu, ko na fi wannan?”
Daga nan, bacci ya ɗauketa cikin sanyin dare mai ɓoye zuciya cikin mafarki, Halima ta tsinci kanta a kusa da wani tafki mai ruwan shudi gabar tafkin akwai ciyayi masu launin zinariya, tsuntsaye na waka, iska na busa kamar karamar waka, ta tsaya cikin tufafin fararen zinariya, kanta a rufe da mayafin rawaya , can gefe kuwa, wani saurayi na kallon ta tsayuwarsa mai ƙayatarwa ce: dogo, baƙi, yana sanye da farin riga da wando. amma fuskar sa dukk ta ɓoye a inuwa kamar fuskarsa na ɓoye da nufin ya dawo wata rana.
“Halima...” muryarsa mai sanyi, mai kaɗa, tana ratsawa har cikin jijiyoyinta.“kai wa kake ne?” ta tambaya da muryar yarinya. “kayi kama da wani na kusa da zuciyata...”
“Ni ne mai zuciyar da ta kira ki cikin bacci... da zuciyar da zata so ki fiye da yadda kike so kanki.” ya miƙa mata hannu, amma kafin ta kamo ta farka tashi da sauri, numfashinta ya kadu, zuciyarta na bugu tana kallo sama kamar zata gan shi a cikin silin.
“waye wannan? me yasa mafarkin nan ya shige ni haka? Kuma me yasa fuskar sa ta ɓoye kamar akwai abu da ba a shirya bani ba?” karo na farko tun da ta zo birni, Halima ta fara jin wani abu daban – kamar mafarkin soyayya da sabuwar rayuwa na faɗa mata, "akwai wani sirri da ke tafe... kuma akwai wanda zai sauya maki rayuwa, ko da ba yanzu ba."
Kullum cikin dare, Halima na ƙoƙarin rubuta abubuwan da ke faruwa da ita a cikin wani ƙaramar littafi da ta ɓoye cikin almara ,tana rubuta mafarkinta, ƙiyayyar Hajiya Mariya, da muradinta na ganin wata rana zata fita daga gidan nan cikin daraja.
“Ina mafarkin wata rana zan fita daga nan ba da hawaye ba, sai da murmushi kuma duk wanda ya raina ni, zai ga matsayi na kuma wanda ya tsare zuciyarsa a gareni, zai gane cewa ba wai 'yar kauye bace, sai dai baiwar Allah da daraja ta ɓoye.”
******************"""""
Abdullahi Khalil Usman wanda da dama ke kira Mr. Abdullahi, shine shugaban babban kamfanin gado na mahaifinsa wanda aka sani da Usman Holdings International, wanda hedikwatarsa ke cikin Abuja, amma reshe-reshen sa sun watsu a duk fadin Najeriya da kasashen waje duk da wannan girman arziki, Abdullahi mutum ne mai natsuwa, mai son zaman shiru, kuma yana da ɗabi’ar kin yarda da auren dole.
“Ni bana son aure yanzu. Ina jiran yarinyar da zuciyata zata karɓa ba tare da tilas ba,” inji shi kullum idan mahaifiyarsa Hajiya Binta ta taso masa da lamarin aure.
Tun yana ɗan shekara ashirin da shida, Abdullahi ke yin wani irin mafarki na wata budurwa mai kamun kai, mai kyan hali, cike da nutsuwa , kullum fuskar yarinyar bata bayyana gaba ɗaya, sai murmushin ta da kuma yadda take tafiya cikin kwanciyar hankali kamar ba ta san duniya ba.
Yanzu yana da shekara talatin da ɗaya, amma har yanzu bai manta wannan mafarkin ba har ya kasa yarda da kowacce mace – saboda zuciyarsa tana jiran wannan mafarkiyar da bata bayyana ba.
Ranar da ya hau jirgin daga Yola zuwa Abuja, yana tsaye yana shan iska da kallon mutane, sai idonsa ya sauka akan wata yarinya da ke tafiya da Alhaji Saminu – cikin riga da zani, fuskar ta cike da tsantsar kauyanci da kamun kai. Fuskar yarinyar kamar dai fuskar yarinyar mafarkinsa ce! amma sai ya girgiza kansa:
“A’a, ba zata iya zama ita ba… ai ita kauyaniya ce ko turanci ma bata iya ba.” ya fad’a a ransa, yana danne mamakin zuciyarsa amma tun daga lokacin, idonsa na bibiyar Halima, duk da cewa bai san sunanta ba, kuma bai ce da ita uffan ba. Sai dai a zuciyarsa… ya kamu da wata ƙayatarwa mai cike da ban mamaki.
Yanzu da suka sauka Abuja, Abdullahi ya koma rayuwarsa, amma zuciyarsa bata daina tunanin Halima ba duk wata yarinya da ya gani, sai ya kwatanta ta da ita, amma babu mai dacewa shi kuwa Alhaji Saminu, yana cikin shirye-shiryen cin gajiyar auren Halima – yana kula da ita da nisa, amma bata san yaushe zai dawo ba Halima kuwa, tana fama da azabar rayuwa a gidan kishiyoyi, tana ta mafarkin sauyi da ƙauna, amma bata san cewar zuciyar wani saurayi mai daraja tana neman nata ba
Abuja cibiyar kasuwanci da masarauta ta zamani wannan karon, babban taro ne da ya haɗa manyan kamfanoni, 'yan kasuwa, da shugabannin kasashen duniya Alhaji Saminu, wanda ya kafa taron kasuwanci, yana cikin wani kwararren d'akin taro a babban otel na Abuja, wanda ke dauke da kyan gani da yanayi mai cike da alfarma duk duniya na kallon wannan taro da alamar samun ci gaba ga kasuwancin Najeriya manya da ƙananan kamfanoni sun hada kai domin samun nasara da bunkasa tattalin arzikin kasar.
A cikin wannan dakin, Abdullahi ya tsaya cikin cikakken kwalliya jikin sa yana ɗauke da rigar alfarma mai kyau, wanda ta haɗa da jallabiyah mai launin zinariya da farar rawani fuskar sa tana cike da kyan gani da kwarjini. Duk wanda ya kalli shi zai fahimci cewa yana ɗan kasuwa ne mai daraja, wanda ke dakin taro ba domin wasa ba a cikin zuciyar sa akwai fata na samun nasara mai girma, amma akwai wata yarinya da ta mamaye zuciyar sa – Halima.
Abdullahi, wanda iyayensa ke son shi ya auri wata mai matsayi daga cikin iyalai masu arziki, yana neman neman soyayya ta gaskiya. bai taɓa ganin wannan soyayya ba a cikin kowanne daga cikin yarinyoyin da iyayensa suka so masa amma a cikin zuciyar sa yana ɗokin haduwa da Halima, wanda ya ga a cikin mafarkinsa a jirgin sama lokacin da suka haɗu tabbas yanzu zuciyarsa yafi karkata ga cewa ya haɗu da mafarkin sa a rashin lura irin tasa .
A yayin da aka gudanar da taron, Halima tana cikin wani dakin hotel ɗin da Alhaji Saminu ya shirya mata wannan d'akin yana ɗauke da kayan alfarma da kyakkyawar kwalliya – gado mai kyau da tsayayyen fata na zinariya. Halima ta zauna cikin dakin, tana kallon kayan da aka tanadar mata, amma zuciyar ta cike take da tunani wataƙila, wani abu ya faru da ta rasa kwarin gwiwarta, ko kuwa har yanzu tana jin cewa wannan ba shi ne rayuwar da ta yi mafarki da ita ba.
Alhaji Saminu ba ya kula da wannan sha'awar da ta ke nunawa a saboda haka, yana son ta zama abokiyar rayuwarsa, amma yana ɗaukar ta a matsayin daya daga cikin matan da zai kula da ita daga ɓangaren kyakkyawar tarbiyya da kuma halayen aure.
A cikin taron kasuwancin, Abdullahi na cikin dakin taro, yana kallon yadda ake gudanar da al'amuran. A zuciyar sa, yana jin cewa ba zai taɓa samun zaman lafiya ba sai ya sadu da Halima. ya tuna da fuskarta a cikin jirgin sama, da yadda zuciyarsa ta shiga cikin hayaniya saboda soyayyar da ta shige masa cikin zuciya ,yana ganin ta a cikin wannan dakin, amma ba zai iya neman ta yanzu ba. wannan tsari na al’amura yana nuna masa cewa soyayya ba ta da sauki, kuma yana bukatar lokaci don samun damar yin matakin da ya dace.
Tsawon kwanaki biyu ana wanan gagarumin meeting nin inda ake shirye shirye rufe taron a kwana na ukku Alhaji saminu dalilin ɗauko Halima daga gida bayan kumawae sa gida cikin gaggawar kirar taron da suke gabatar wa yanzu cikin bazata ya iso gidan ganin halin da Halimar ke ciki ne ya bashi mamaki kwarai da gaske wannan dalilin yasa ya ɗauko ta a tare dashi ....
RANAR TARON ƘARSHE
Ɗakin taron babban hotel ɗin na Abuja ya cika da hasken chandelier mai sheƙi kamar taurari fata-fatan zinariya da tabarmar da ta shimfiɗu kasan tiles ɗin falo suna haskakawa da salo irin na manyan duniya.
An shimfiɗa dogon babban tebur na gilashi, aka jera kujeru masu launin royal blue da zinariya agefen teburin akwai lambun furanni masu ƙamshi, da sauran kayan kyauta na kamfanoni.
mutane masu siriri da sirarrun suits sun cika gurin: 'yan kasuwa, manyan ‘yan banki, masu hannun jari, da CEOs daga kamfanoni daban-daban.
Abdullahi, sanye da suit mai launin baki da farin riga da blue tie, ya zauna a tsakiyar babban kujerarsa girman sa da kamewar sa ya ja hankalin kowa — da kallo daya zaka san ba na yau aka haife shi ba fuskar sa ba dariya, ba kuma fushi tsaka-tsakin kamewa da matsayi
Hausawa sukace yaro da kuɗi abokin tafiyar manya
Har lokacin da Alhaji Saminu ya shigo cikin taron, aka mika masa gaisuwa irin ta manyan masu kuɗi ya zauna da kamun kai, yana ta gyaran hula da hancinsa lokaci-lokaci, alamar rashin jin daɗin zama saboda tunanin a maryar sa , lolz
A takaice an yi taron a cike da muhimman magana: aka rattaba hannu akan sabon kwangilar gine-gine da haɗin gwiwa bayan an gama taron, mutane suka shiga gefe suna ta yin hotuna, musabaha da exchange card.
A gefe kuma, Halima wacce aka bar a dakin hotel na VIP floor, tana kwance tana ƙoƙarin danne kukan kewar gida da tsoron birni.
tana sanye da kayan gida masu kyau amma ƙauyanci ke bayyana sosai a fuskarta Fuskarta bata da kwalliya, sai ruwan hawayen da ta share, tana kallon window tana ganin duhun dare yana sauka kan manyan titunan Abuja.
bayan taron, Alhaji Saminu cikin gaggawa ya amsa kira daga gida an kira shi da sauri, wani ɗan matsala ce ta dangi da gaggawa ya fice daga hotel ɗin... amma sai ya manta da Halima a cikin ɗakin hotel ɗin!
Halima tana jiran shigowar sa, tana jin tsoron shiru da tunanin abubuwa daban daban
Halima ta jawo ƙofar ɗakin a hankali, tana hango hanyoyi masu haske da furen bango. tana sanye da doguwar riga mai launin shudi mai launin ruwan sama, wanda ke fita da kyau akan fara fatarta, tana tafe da ɗan ƙaramar gyale mai launin milk da ya ɗaura mata fuskarta kamar an kare ‘yar Sarki.
Tsoron da ya mamaye ta ya hana ta saka takalma — tana tafiya a siraran ƙafarta, tana kallon dukkan gefuna da tausasan idonta.
tana jin kowane sauti kamar wani abu zai fito daga cikin duhun corridors ɗin hotel ɗin.
ta isa ga wani ɓangare na babban hotel ɗin gaban lift — lokacin da abinda ta gani ya firgita ta.
Da gudu ta nufi cikin tsoro tana neman mafaka — gaban ta a bude — tayi karo da mutum mai tsayi, sanye da baƙin suit mai sheƙi, riga fara ta ciki, wanda ba kowa bane illa Abdullahi.
Shi kuma yana tsaye yana danna wayarsa, iska mai sanyin ƙanshi na air conditioner yana kadawa a gashinsa mai santsi.zuciyarsa tana bugawa da sauri kamar ana gaggauta dokin sarauta, Halima cikin firgici ta fado jikin Abdullahi — hannuwanta suka kama rigarsa, tana fitar da ƙaramar ajiyar zuciya, idanun su suka haɗu ,wani zafi mai daɗi ya ratsa tsakanin su, wani sirrin shiru mai nauyi ya cika sararin tsakanin su.
wayar sa ta tsaya hannu, zuciyarsa ta kasa ci gaba da bugawa daidai Idonta ya cika da tsoro, nashi kuma da wani irin salo na jin "na gan ki amma ban gane ki ba".
A hankali Abdullahi ya daidaita kansa, yana ƙoƙarin saukewa Halima daga jikinsa.
Ya sauke ta a hankali kamar kar ya tsoratata, sai ya ɗauke numfashi ya runtse ido tsakanin su shiru ne mai nauyi, kamar ana iya jin karar fitar numfashin juna.
Abdullahi ya tsaya wuri guda, idanuwansa suna zurfafa cikin kyawawan idon Halima waɗanda ke cike da tsoro da rashin tabbas cikin kin sauti mai kaɗan amma cike da girma da tsari, anji muryar Receptionist “Please, Hajiya Halima...! Reception is calling you, Hajiya Halima!”
Muryar ya sake maimaitawa daga speaker din da ke jikin bango, kamar an daga karar.
Halima ta ji sunanta a sarari, kamar daga sama, kamar ruwa an zuba mata ,wani sabon firgici ne ya sake ratsa ta kamar numfashin ta zai tsaya a firgice, ta sake matse jikinta da ƙarfi a cikin ƙirjin Abdullahi, tana neman mafaka daga kowa da komai ,Abdullahi kuwa ya saki wayarsa ta faɗi ƙasa ya kasa motsi.
Numfashin sa ya tsaya cak
gaba ɗaya jikinsa ya birkice kamar karamin yaro da aka tsorata masa da aljani.
A hankali yana jin kamshin furen Halima — kamshin shinkafar ɗanye da ƙamshin turaren wuta idonsa ya lumshe, zuciyarsa na harbawa da irin bugun da bai taɓa ji ba a rayuwarsa.
ya buɗe idonsa, ya kura mata ido, yana kallo cikin fuskarta mai tsantsar kyau da rashin fenti fatar ta laushi tamkar auduga, launin idonta kamar kalar ruwa mai tsafta
Bakin Halima ya motsa kaɗan, tamkar zata ce wani abu, amma ta kasa.
Abdullahi ya bi bakin nata da kallon da ya kashe masa nutsuwa — laɓɓanta sun yi ja kamar sabuwar ɗan itacen ɗinya, santsi da kauri irin na 'yar asali.
Abdullahi ya shige duhu da hasken idonta.
wani abu mai daɗi da tsoro na haɗuwa ya cika shi abu da bai taɓa jin sa ba tun daga haihuwarsa " tabbas ittace mafarki na ".
Abdullahi ya kasa inda zai sa kansa.
Zuciyarsa tmkar an kunna ganguna.
wani yanki na zuciyarsa na ba shi shawarar ta hanyar hankali: "ka sauke ta, ka da ka zalunce ta!"
Amma wani sashe kuma, na tunani mai zurfi da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 18