Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zanyi amfani da salo akaina kuma ina tabbatar muku bashi da tsawo domin dai bai kai sauran labarai da ya gabata ba '". Lokaci yayi da Yazid zai bamu labarin AlJANNIN SAJIDA labari ne cikin labari ina fatan zamu chigaba da tafiya cikin kulawar ku let's go Narnah ƙanwar soja ✍️ 🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗 Book two BY NARNAH KANWAR SOJA 💫ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION 💫 SADAUKARWA Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕 Zahrah Royal Star Yawan sharhin ku yawan typing banyi alkawarin posting kullum ba , mujeee zuwa tafiya ta fara tafiya show me some love guy's 🩷 بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على محمد وسلم 26 / 27 Rayuwa tana da ɗanɗano kala-kala wani lokacin kana cikin dariya amma zuciyar ka na kuka, wani lokaci kuma kana cikin shiru ne, amma ranka yana tafasa da ruɗani. Suna na Ishaq ne matashi ne mai matsakaici tsayi da kyau nagarta baƙar fata gari ne A ranar Lahadin nan ne wata ƙawarmu a makaranta, Sajida budurwa ce mai jini a jika a ƙalla tana da shekaru goma sha takwas fara ce fatt kyakkyawar yarinya kowa ya santa da suna baby Sajida ta gayyace mu zuwa bikin zagayowar ranar haihuwar ta ban yi wata-wata ba, na shirya cikin shigar ƙananan kaya wanda suka ƙara min kyau da nagarta ina cikin farin ciki da zuwan wanan ranar domin zamu haɗu da abokan makarantar mu na ɗauki mota na fara ɗauko abokaina guda biyu: Ameer da Abdul “Lafiya lau,” na faɗi a zuciyata lokacin da muka ƙaraso bakin gidan Sajida mun zo da ɗan jinkiri, domin wani abu ya ɗan tsaida mu a hanya amma da alama ba mu makara da yawa ba, domin kowa yana nan, kuma taron yana da ɗimauta. tsoffin fuska da sabbi, 'yan makaranta da 'yan unguwa, iyaye da ɗangi komai yana nan kamar ɗaurin aure idanun mutane sun zuba inda za a yanka cake, amma ban gane me ake jira ba har sai da Sajida ta nufe mu da gudu. “Lalle da babban baƙo!” ta faɗi hakan tana saki murmushi murmushin da na ji tamkar wata ƙaƙƙarfar ƙugiya ce ta ja zuciyata na tsaya cak ina kallonta, sai kuma na ji kaina na mayar da mata daidai murmushin da bata taɓa gani daga gareni ba. Sajida kyakkyawar yarinya ce don kowa ƙon wanda ya rasa Allah ya zuba mata hasken idano tamkar farin wata tsayawar fari ga cikakken tsarin halittar jiki tabbas idan tayi murmushi ko maƙiyanta sai ya tsaya kallon halittar fuskanta “Ina son mu yanka tare cake, kai ne babban baƙo kuma aboki na na musamman ,” ta faɗi hakan a cikin kasalalliyar murya da bata da karyatawa na waiwaya, idona ya haɗa daAbban ta wanda ya girgiza kai alamar amincewa haka nan Umma ta murmushi kawai take yi Abdul da Ameer kuwa sai dariya suke min. Ban san ya akayi ba, sai dai na tsinci kaina da hannu ɗaya na rike wuƙa, ɗaya kuma hannunta muna tare yankan cake shewar jama’a ta kaure, liƙi ya fara kwaranya kamar ruwan sama. Wani abu ya faɗa zuciyata: dhin wani abu ke faruwa a zahiri ne, ko kuwa mafarki ne kawai nake? domin a lokacin, hankali na ya riga ya fita daga jikina. ** Bayan an ci an sha, lokacin da dare ya fara ruruwa ne na ce wa Sajida muna shirin tafiya. amma ita kuma tace, “A'a, sai munje gida ku huta.” na ce: “gidanmu zamu huta mana.” Sai Abdul yayi dariya yace: “kai Bilal, idan kaga gida irin nasu, baza ka ce a tafiya ba.” Gidan ya fito kamar aljanna haske ke fita daga ko ina, kwalliyar da ba a saba gani ba. muka shiga muka zama kamar 'yan ƙauye, duk inda ido ya sauka sai jin kaɗa da ban mamaki. aka kawo mana abinci irin na manya, drinks iri-iri — wato lallai ba wargi ba ne wannan gidan. Bayan mun sha mun koshi, na faɗa wa Sajida cewa muna son tafiya. Tace “to,” sannan ta kira Abbanta domin mu yi sallama. Abban Sajida ya ce, “dama ina son muyi magana da kai, amma yanzu dare yayi. sai ka zo wata rana.” Yace: “kin basu kyautar da nace?” tace: “Na saka mai gadi ya saka musu a boot.” muka ce “nagode” muka fito. Muna fita, Sajida ta rako mu har mota, tace: “Kyautar na ciki, kowa ɗaya.” muna tafiya sai Abdul yace: “Wallahi dole a duba kyautar nan.” Ya buɗe boot — muka ga jaka cike da gwalagwalai da kuɗi dollars ne da wasu kuɗaɗe da ban taɓa gani ba. Zuciyata tayi wani irin nishi, wata damuwa ta fara girgiza ruhina meyasa yasa irin wannan kyauta? me nake nufi a gare su? a haka muka bar maganar a tsakanin mu da alkawarin gobe zamu kuma gidan su Sajida mu mayar musu da dukiyar su nan na ajiye Ameer da Abdul a gidan su . ** Ina kan hanyata gida lokacin da motata ta tsaya chak wurin duhu ne, babu kowa na fito na duba fetur akwai nayi ƙoƙarin tada motar taki tashi kamar wasa. Ina cikin ƙoƙari na kira wani daga abokaina kawai na juya, na hango Sajida a cikin mota. tana min murmushi , da sauri na rintsa ido na domin wanan gizo gizo da take min ya fita a kan ido na , sai dai ganin abun nakiye da gaske itace na rufe mota da sauri na fita zan gudu — na juyo, na same ta a gabana tana nan, murmushi kawai takeyi. wani murmushi ne mai saka zuciya rawa... Ina juya motar, kawai na ganta a mirror tana tsaye a bayan mota sai na ji numfashina ya tsaya... duhu ya mamaye komai. Umma na tana gefena, Ameer da Abdul suna nan zuciya ta kamar an watsa mata ruwan sanyi. “me ya faru dani?” na tambaya da rauni. Abdul yace: “hatsari kayi. wasu suka kira mu a daren jiya amma fa, abin mamaki — kai kaɗai muka tarar a wurin...” Umma na tace: “Sajida ta kira tace a maka ya jiki...” *to, me Sajida ke nufi? Wacece ita a zahiri? kuma me wannan kyauta ke nufi? " Bamuga mutanan da suka kira wayar ba sannan kuma number ɗin da aka kirani da ita private number ce ballantana mu kira muyi musu godiya, umm kuma Sajida tace ayi maka jiki kafin su zo ita da iyayenta ,wallahi , yarinyar hankalinta ya tashi jin halin da kake ciki, sai kuka take yi." Fadar sunan Sajida da Ameer yayi ya sanya na tuna da abin da ya faru da ni a wannan dare. Na faɗawa Ameer dan Allah ya kira Sajida ya faɗamata cewa na sami sauki, kar ta zo. Cikin rashin fahimta, Ameer, Umma sukace, "Haba Bilal, meyasa zakace haka, bayan kuma kana kwance a asibiti? Aikam yakamata tazo domin kasani cewa hankalinta bazai ta6a kwanciya ba muddun batasan halin da kake ciki ba." Nace, "Umma, nifa wallahi, indai sai Sajida tazo asibitin nan ne to a kira likita ya sallameni, gara nayi jinyata a gida." Umma tace, "to, wai maye matsalar ne?" nace, "Babu komai." Nan Ameer ya kira number Sajida, amma abin mamaki, wayanta a kashe, wanda tunda nake da ita ban ta6a ganin wayarta babu chaji ba. maye mai zaisa wayanta a kashe? a zuciyata nace, "Lallai akwai abinda yake shirin faruwa." Na juya na kwanta, ina tunanin shin yanzu idan Sajida tazo nan da wanne irin siffa zatazo kuma da wanne kudiri zatazo? Drip ɗin da aka sanyamin ya ƙare, hakan ya sanya Ameer ya kira doctor domin ya sakamin wani , likita tana shigowa tayi sallama, muryan Sajida naji hakan ya sanya na juyo da sauri kawai nayi arba da Sajida cikin kayan likitoci. Idanuwana suka zaro, zuciyata ta buga da ƙarfi duk da ciwon da yake jikina, na zabura na nufi kofa a guje. Ameer da Umma suka kamoni suna lafiya!!! lafiya!!! lafiya!!! nikam inata buɗe baki amma nakasa magana inata nuna Sajida da hannu. Umma tace, "Likita ce fah, nikam Sajida kawai nake gani." Tanata matsowa kusa da ni, hakan ya sanya na suma. Abinda ya tayarwa Umma hankali matuka, ta fashe da kuka tana cewa, "Ɗana Sameer , Allah baka lafiya, Allah yasa ba ta6in hankali ka samu ba." Bayan na suma ne sannan Sajida da iyayenta suka zo asibitin sun gaisa da Umma, sannan ta faɗamusu cewa anyimin alluran barci ne saboda na sami hutu sai zuwa dare zan farka. Sajida ta bukaci cewa ita iyayenta subarta a asibitin har sai na farko taga halin da nake ciki, sannan zata tafi idan ta kama ko kwana zatayi ban farko daga dogon sumar da nayi ba sai 12:45 am. Ai kam ina farkawa, nayi tozali da fuskan Sajida, tanata kallona, fuskarta cike da hawa. Inayin arba da ita na ƙwalla wani ihu mai razanarwa, hakan ya sanya Umma ta farka a tsorace, itama kanta Sajidar tayi zunbur kamar zata ruga. Umma tace, "meya sameka?" Abin mamaki a wannan karon bakina ya buɗe, ina iyayin magana amma sai nayiwa Umma karyar cewa, "Mafarki nayi, wasu mutane suna bina zasu kasheni." Umma tace, "ai mafarki ba gaskiya bane, yanzu kayi addu'a ka koma ka kwanta." Washegari, Sajida taje gida ta kawomana breakfast mai rai da lafiya, mukaci nikam, itace ma take bani a baki. Haka ta dinga dawainiya da ni har kwana 12 tukunna aka sallame ni, muka koma gida. A daren ranar da muka koma gida misalin 1:00 am, hadari ya taso sosai, anata walkiya da tsawa mai ƙarfin gaske. kawai sai aka ɗauke NEPA, sai naji kofar ɗakina tana buɗewa tamkar wani ne zai shigo cikin ɗakin. a tsorace nace, "waye? shiru shiru?" Na laluba wayana domin haskawa, nagani ina ɗauko wayar na kunna fitila, sai naga Sajida a gefen gado kusa da ni. 6angaren hagu na juya 6angaren dama, nasake ganinta, na ƙwalla uban ihu, nayi tsalle na sauka daga gadon, na nufu kofar ɗakin da nufin na fita na ruga wurin Umma. Kofar ɗakin ta kulle, sai ji nayi wata murya tare da amsa kuwwa, tana cewa, "haba masoyi, ni kake gudu, nice fah, Sajida, Sajida, Sajida." Kawai naga ta zama kusan kashi goma ko ina a bangon ɗakin, itace wata tana kiran sunana, wata tana kiran nice Sajida, wata kuma tana cewa, "Ka rabi da Sajida domin kuwa matar sarkin mu ce, hhhh hhhh hhhh." Jinayi kaina yana juyawa, naga ƙofa ta buɗe, a guje na nufin kofar da nufin nabar ɗakin, kawai sai naga wata mace da fararen kaya, babu kai a jikinta kuma ita bata sama bata ƙasa take na faɗi ƙasa a sume. Iskan da ke kadawa ne gami da sanyi suka sanya na farka daga sumar da nayi a hankali na buɗe idanuwana domin zuciyata cike take da fargabar zan sake ganin wannan hallita. Abin mamaki a wannan karon banga komai ba, da ƙyar na samu na mike a hakanma ina dafa bango domin a wannan lokacin jikina babu ƙarfi haka na koma cikin ɗakina na fasa zuwa ɗakin Umma na domin bana son hankalinta ya tashi idan tasan halin da nake ciki. na dauki wayana ina duba time sai naga ashe har 2:00, nayi addu'a na tofa ko ina sannan na kwanta zuciyata cike fargaba. Bansan lokacin da barci ya sace niba, jinayi ana tashina Ishaq ka tashi kayi sallah yau kam wanne irin barci ne kakeyi haka? a hankali na buɗe idanuwa na "Umma" nagani tace yau kam wanne irin barci kakeyi har rana ya fito bakayi sallar asubahi ba. "Umma" idan kayi sallar sai ka fito ga breakfast na haɗamaka" , ta juya ta fita haka na tashi nayi sallah sannan nayi brush sannan na fito mukayi breakfast sannan nayi mata sallama na wuce kasuwa. Bayan na shiga mota na fara tafiya jinayi wayana tana ringing, ina dubawa kiran SAJIDA nagani take jikina ya fara karkarwa tamkar wanda ya fito cikin ruwan kankara, wuri na samu nayi packing sannan na fara tunanin shin na daga wayar ko a'a. Haka dai nayi ta maza zuciyata tana dukan uku-uku na daga wayar, muryar mahaifin sajida naji yacemin" yaya jikin naka" ? na amsa da " jiki kam yayi kyau tunda yanzu gashi har na fita kasuwa. " Alhamdullah tunda yanzu kaga ka sami lafiya yau idan ka tashi daga kasuwar sai kazo gida mu tattauna maganar mu, ji nayi gabana ya faɗi zuciyata ta buga da ƙarfi kaina yamin nauyi domin naji ya ambaci zuwa gidansa, nayi shiru daga chan sai nace to Abba in sha Allah zan zo, amma yanzu da safe yakamata na zo saboda bana son yamma yamin ballantana kuma dare. Ya amsa da shikenan sai ka zo, nikuwa haka na juya motana na nufin gidan su sajida jim kadan na isa, ina shiga na tarar an hadamin abinci iri-iri tamkar za'a tarbi wani babban basarake ko shugaban ƙasa. Abba yamin izini da na zauna sannan yamin nuni da na fara cin abinci tukunna sai muyi magana, nayi breakfast kafin na fito na faɗawa "Abba ni yanzu a koshe nake, "haka dai Abba ya matsamin dole naci kadan daga cikin abincin. Bayan na kammala sannan Abba ya tara iyallan yayi gyaran murya " nasan bakasan dalilin da yasanya nake nemanka ba"? , nace eh Abba gaskiya bansani ba sannan kuma zuciyata cike take da son jin abinda zaka fada." " Ishaq na zauna nayi nazari gami da tunani ganin irin shakuwa da Aminanan taka da tausayin juna da yake tsakanin ka da Sajida. wanda yanzu har kun zama tamkar yaya da kanwa, to ne da Umma SAJIDA mun yanke wani hukunci. Wanda zan fadamaka a yanzu amma kamin alkawarin cewa zaka kar6i abinda muka zo muku da shi domin kasan bazan cutar da ku ba". Maganganun Abba sun sakani cikin rudani gami da wani dogon tunanin daban, shin maye Abba ya yanke a kanmu? Yanzu idan namar alkawari kuma ya faɗi abinda bazan iya cikawa ba fa. Haka na faɗawa Abba cewa nayimaka alkawari domin bazan iya musu da maganarka ba 'Abba" domin kana bani kulawa tamkar uba agareni duk abinda uba zayyiwa Ɗansa kanamin bazan iya butulci agareka ba." Abba yayi murmushi sannan yace Allah yamaka albarka, dama ba wani abu bane face ina son ka auri Sajida mikewa nayi zunbur tamkar wanda aka sanyawa shocking da lantarki muka hada ido da SAJIDA ta sakarmin wani tattausan murmushi sannan ta sunkui da kanta . Abba yayi murmushi " zauna mana ai dama nasan dole zakaji mamaki gami da farin ciki marar musaltuwa amma kuma ba abin mamaki bane, duba da duk abinda sajida take so to muma muna son shi. Yanzu ina son ka turo iyayenka domin muyi magana gemu da gemu bana son auren ya wuce 2 weeks," nikam tuni na fada cikin dogon tunani gami da damuwa wacce ta gagara 6oyuwa a fuskata. Ganin damuwar da take kan fuskata 'Abba" yacemin kar ka damu domin duk dawainiyar auren ni zan dauka bana son ka kashe ko naira ɗaya, Allah sarki shi a tunaninsa wannan ne damuwa ta. Nikam tunanin maganar aljanun nan ce ta faɗo a zuciyata da tunanin abinda zai faru da ni muddin akayi wannan auren, ni babban abinda yafi dawuna shin maye tsakanin "SAJIDA" da sarkin aljanu shin, aljanna ce ko bil'adama? Tabbas kyawun ta ya kai yaja hankalin duk wani ɗa namiji sannan kwalliya tsafta gami da iya ado, ni kaina ina jin kaunarta a cikin zuciyata amma tsoron abinda zaije ya dowo shine a cikin raina. " Ni zan wuce domin ina son na tafi kasuwa kar na makara " na faɗa masu mukayi sallama sannan na fito abin mamaki wannan karon batamin rakiya ba bayan na fito na wuce kasuwa. Ban iya aikata komai ba a kasuwar sai tunanin na saka wancan na warware wancan hakadai har lokacin tashi yayi sannan na rufe shago na wuce gida. Ina shiga gida Umma na tarar a falo tana karatu nikam sai na zauna na jirata har ta kammala sannan na faɗamata cewa ina son muyi magana, wacce magana ce wannan ɗana Umma tace ai da ka bari idan ka watsa ruwa sannan ka ci abinci ka huta sai muyi maganar. " Aa idan da hali muyi maganar yanzu to shikenan ina saurarenka." Na kwashe duk yadda mukayi da iyayen Sajida na faɗamata ALHAMDULILLAH "ummm" tace abinda na dade ina mafarki abinda na dade ina jira abinda na dade ina yiwa tanadi yau kam gashi Allah ya kawomu. 'Umma" tace yakai ɗana guda ɗaya tilo kasani cewa na Dade ina jiran wannan naga kayi aure domin ka zama cikakken mutum sannan naga jikana, lallai kam yau ranar farin ciki ce a garemu dan haka gobe tun safe zan tafi gidan kawunka Alh 'labaran"suje a tsayar da magana. Nikam yaƙe ne yake bayyana a fuskana domin bana son Umma ta fahimci akwai wani wanda yake damuna, yanzu ka shiga ciki ka watsa ruwa sannan kazo mu ci abinci. Bayan mun ci abinci mun kammala sannan mukayi fira da ita sosai tace " kasan fa ranar bikin nan naka duk da tsufana dole nayi rawa na chashe" Duk da ina cikin damuwa bansan lokacin da dariya ta kamani ba gami da jin kunya, nace ummana gaskiya ina alfahari da ke kuma lallai ko bayan nayi aure bazan iya barinka ba dole gida ɗaya zamu zauna. " Nan dai mukayi fira sosai har dare yayi sannan 'umma" ta wuce ɗakinta ta barni a falour nikam sai na dauka wayana ina buɗe data sakon sajida ne ya shigo wayana Kamar haka: Angaishi da autan samarin duniya ina fatan ka isa gida lafiya? gaskiya nayi sa'ar kasancewata zan zama mata a gareka burin da yadade a cikin zuciyata yau gashi Allah zai cikamin shi. Duk da baka ta6a furtamin kalmar so ba amma sai dai naga hakan a cikin idanuwanka sannan naji hakan a cikin bugawar zuciyarka, Kamar yadda nima na gagara fadar hakan a gareka yau kam zan fada. Ni 'sajida" Ina son ka ina kaunarka sonka ya riga yayi nisa a cikin zuciyata ta yadda bazan iya rageshi ba ballantana har na iya cireshi, dan Allah ina son ka zama garkuwa a gareni kazama uban 'ya'yana ka kasance tare da dani a kowanne irin yanayi, da wannan nake maka sallama masoyina bissalam ka kulamin da kanka. Babu zato ba tsammani kwatsam sai naga wani sako ya shigo wayana Kamar haka: yakai bil'adama shin ashe bakaji jankunnan mu a gareka ba ashe taurin kai ne da kai. Tabbas Auren SAJIDA a gareka tamkar tamkar ka sayi tikitin yin bankwana da farin ciki zaka kulla alaƙa da bala'i da masifu a rayuwarka, domin kuwa tun daga ranar da aka haifi Sajida" ta zama mata a gareni kuma nayi alkawarin babu wani bil'adama komai hatsabibanci shi da ya isa ya aureta take wayar tawa ta fara ci da wuta a tsorace nayi wurgi da ita ta window ɗin da yake a falon. Lekawa nayi window ɗin ina hangen wayar a haka har ta ƙone kurmus sannan naga wannan tokar ta tana rikidawa ta zama wata siririya tamkar igiya sannan tana mikewa a hankali take naga ta zama wani siririn aljani mai siffar ban tsoro. Wannan aljani yana da munin siffa kwarai da gaske idanuwansa jajaye ne tamkar garwashin wuta sanan ya wangame bakinsa yamin wata mahaukaciyar dariya yana dariya bakin nasa yana kara girma, sannan ya tsuke bakinsa ya murtuke fuska idan kaga fuskarsa saboda tsabar muni sai zuciyar mutum ta tashi har yayi amai sannan ya nunani da hannunsa wanda yake da wasu yatsu zaro zaro wanda duk iyakar kallon kurillar mutum bai isa ya irga adadin yawan yatsun wannan aljani ba. Kunbunansa kuwa suna da tsayi sannan ga tsini tamkar karamar takobi, sannan wannan aljani ya gyara tsayuwa ya rike kugu yana kallona, nikam addu'a kawai kawai nakeyi a cikin zuciyata wani lokacin ma bansan maye nake karantawa ba saboda tasanin tsoro abinda yabani mamaki shine yin arba da wannan aljani amma zuciyata ta dake har haka. Kwatsam sai gani nayi wannan aljani yayi wata girgiza sannan naga yanata chanja halitta daga Ƙarshe sai naga yazama guguwa wannan guguwa tayi sama tun ina kallonta har ta 6ace 6at jim kadan sai ganin nayi wayata ta faɗo a dai-dai wurin da wannan aljani ya tsaya, na kalli wayar nan sosai naga tabbas wayata tace wacce ta kama da wuta kuma abin mamaki babu abinda yasami wayar, tsoro ya hanani fita ballantana na iya daukar wayar. STORY BY Iliyasu Falalu Lawal WRITTEN BY NARNAH ƘANWAR SOJA https://chat.whatsapp.com/Bd1Zu1cwIO81A7rrATd4Cu 🌗🌙BAYAN WATA🌙🌗 Book two BY NARNAH KANWAR SOJA 💫ROYAL STAR WRITTER'S ASSOCIATION 💫 SADAUKARWA Wanan littafin sadaukarwa ne a gunke gaba-daya ta bisa jajjircewa da bajinta a duniyar mu na marubuta Allah ya taimaka ya kara basira da hazaƙa gaba gaba sister 💕 Zahrah Royal Star Yawan sharhin ku yawan typing banyi alkawarin posting kullum ba , mujeee zuwa tafiya ta fara tafiya show me some love guy's 🩷 بسم الله الرحمن الرحيم اللهم صل على محمد وسلم Page 28 / 29 18**5**2025 " Yakai masoyina abun alfahari na kuma uban 'ya'yana lallai yanzu haka ina cikin fargaba da tashin hankali wanda bazan iya musaltawa ba domin kuwa a yanzu haka nayi wani mummunan mafarki wanda hankalina ya tashi matuka duk da nasan cewa mafarki ba gaskiya bane amma hankalina ya gagara kwanciya zuciyata ta kasa samun sukuni dai-dai da second ɗaya. Wannan dalilin ne yasa na kiraka a cikin wannan daren namaka kira babu adadi amma bakayi picking call nawa ba Hakan ne ya saka zuciyata ta sake karaya matuka bacci ya kaurace a idaniyata hankali ya gushe daga kwakwalwata nayi kokarin bare zuwa safiya ya gaggara Dan Allah idan kaga wannan sakon nawa kamin reply domin tabbatar da lafiyarka, kasani cewa bazan iya barci ba idanuwana zasu kasance suna kan screen wayana har sai naga sakonka." Babban abinda yabani mamaki dukkan abinda ya faru tsakanina da wannan aljani shine ta fadamin cewa tagani a mafarkinta sannan ta faɗamin cewa lallai idan bataga kirana ba ko sakona to gari yana wayewa zatazo har gidan mu da safe. WASHEGARI Ina gama karanta sakon kenan Horn ɗin mota naji a bakim gate a zuciyata nake fada kar dai yarinyar nan da gaske zuwa tayi. Lallai kam nasan ƙaramin abu ne a wurinta haka na fita nazo ina buɗe gate ba kowa na gani ba sai "sajida" tana ganina tayi wani lallusan murmushi nikam na mayar mata da yaƙe domin ni yanzu tsoronta nakeji matuka haka na buɗe gate sannan ta shigo ta gyara parking. Na kai hannu zan buɗe mata marfin mota amma sai tace haba ba girmanka bane ai nice zanyi hakan a gareka, nace haba kekuwa ina girma ga mijin hajiya mijin gimbiya ai idan ina tare da ke to bana da wani girma face girmanki. Dan haka idan munyi aure ni zan zama driver a gareki, kukun ki, ɗan aiken ki, a taƙaice dai ni zan zama hadiminki. Tayi murmushi tace kaikam kace zolaya ba kowa a gidan ne Sajida" ta fada naga kai ɗaya nagani kuma naji babu wani motsi a gidan eh nace domin "umma" ta fita kuma dama kin san mu biyu ne a gidan. " Alhamdullah" Sajida ta fada yanzu sai mu shiga ciki muyi magana domin magana tana bukatan jin haka yasa zuciyata ta buga da ƙarfi idanuwana suka zaro naji tamkar andauki guduma an bugamin a kirjina, domin gani nake tamkar idan dai har muka shiga gidan nan da Sajida to lallai komai zai iya faruwa da ni. Murya na tana rawa nace haba kekuwa kinga cikin gidan babu kowa bai kamata ace mu shiga mu kebe daga ni sai ke kinga mu ba mata da miji ba kuma Annabi {SAW} yace matukar mace da namiji zasu kebe ba muharraman juna to lallai shaidan zai kasan ce na ukun su kuma kinga mutane da zargi bana son wasu kananan maganun su dinga yawo a kanmu. 'Sajida" tayi murmushi sannan tamin wani irin kallo cikin alamun mamaki tace ashe baka yarda da tarbiyyar da iyayen mu suka bayar a kanmu ba ashe kana tunanin zamu iya cin amanar junan mu? cikin sanyin murya nace haba sajida ba haka nake nufi sam kafin nagama rufe tayi charaf tace to indai hakane mu shiga ciki muyi magana. Tana gama fadan hakan ta kunna kai ta nufi cikin gidan tana

Chapter 8 of 18