Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hajiya Lubabatu, dan harga Allah tana jin kewar mijin nata, tana matuƙar tausayinsa, ba yadda suka iya haka suka baro shi cikin sanyin jiki.
















BAYAN SHEKARA BIYAR


Abubuwa da yawa sun faru, ciki harda auren Khaseem da ILHAM, kuma aure yayi riba dan Yaransu uku, twince ne a farko mata kyawawa ana ƙiransu da Miemi da Miema sai Amal da Aiman, suna cikin farin ciki sosai, Ilham ta zama hamshaƙiyar mace mai ji da kanta, ilmi da sanin rayuwa, mijinta sosai yake sonta, yana kuma bata kulawa, Hajiya Lubabatu ta rumgumi Ilham ta maida ita kamar ita ta haifeta, tana sonta sosai, hakan yasa Ilham take mata biyayya kamar Mahaifiyarta, dan duk wani abu da uwa takewa Ƴarta to Hajiya Luba tayiwa ILHAM, ga dangin mijinta da suke sonta sosai dan tana kyautata musu, FAISAL ma ya maida ta kamar Ƙanwarsa ta jini .






















Ilham tin bayan aurensu da Khaseem ya maida ita makaranta, alhamdulillah kasancewa ILHAM ɗin tanada kaifin ƙwaƙwalwa nan take ta maida hankali, zuwa yanzu tayi degree a ɓangaren Busness Administration, kuma alhamdulillah tana kasuwanci sosai, Kayan kitchen, kayan sawa tin daga kan Shadda, Les, Atamfa, Materials, Takalma, Sarƙoƙi, Yarirrika, Akwatunan kayan lefe, ku harda kayan furnitures, babu abinda bata saidawa, kuma kaya ne na waje bana gida Nigeria ba, tayi shura sosai babu wanda baisan Campanyn Alkhairat Resources Nig Ltd ba, ta zama hamshaƙiya, ga taimako da takewa marasa ƙarfi, har gidauniyar tallafawa mata tayi, duk wata kuwa sai ankai kayan abinci gidan marayu da gajiyayyu,








Haka Khaseem da FAISAL sun zama manyan Lowyers wanda ƙasa take ji take alfahari dasu, sun bawa Billoyoyi baya ta hanyar halak, FAISAL yaje Ƙauyen Bichi ya mayarwa ahalin da mahaifinsa ya cuta kadarorinsu, dan harda ƙari saida yayi musu, kuma ya nemi su yafewa mahaifinsa, wasu da yawa sun yafe masa amma masu riƙo da zafin rai daƙyar suka saduda saida Dagacin garin ya ƙira su ya nuna musu muhimmancin yafiya a addinin muslimci, sannan aka samu suka yafe, haka ya baro garin Bichi yana mai jin farin ciki, dan so yake mahaifinsa ya dawo sakayau.














Yau ne ALHAJI BELLO RABE ya cika shekara biyar cif-cif a Kurkuku, kuma yau ne zai fito, Hajiya Lubabatu, FAISAL, Khaseem, duk suna harabar wajen da ake tsayawa domin jiran wanda aka sallama, suna tsaye duk idanuwansu yana kan ƙofar fitowa, can suka ga wani Gandiroba ya buɗe ƙaramar ƙofar baƙin ƙarfen da duk ƙarfin mai ƙarfi bai isa ya fasata ba saboda ƙwarinta, gata gajeriya dole sai mutum ya sunkuya sannan zai fito, Ƙafarsa ya sanyo waje sannan ya ziro kansa ya fito tare da ɗaga kansa sama alamun godiya ga Allah, hannunsa ɗauke da Carbi ya haɗa ƙasumba yayi baƙi ya rame, da badan sanin da FAISAL da Hajiya Lubabatu sukai masa ba to babu yadda za'ai su gane shi.










Hajiya Lubabatu kuwa tuni hawaye ya jiƙa fuskarta, bai kula dasu ba saida ya fara waige-waige cikin sa'a ya hangesu fuskarsu cike da farin ciki da kuma tausayinsa, shima ƙwallar ce ta tarar masa sai dai ya hanata zuba, ƙarasowa sukai Faisal kuwa da sassarfa ya tawo ya faɗa jikin Dad ɗin tare da sakin kuka, bayansa Dad yake bugawa alamun lallashi, ya kasa magana, Hajiya Luba ma gefe ta raɓa ta rumgumo shi, hakan yasa ya hade su ya rumgume hawayen da yake ɓoyewa suka gangaro, sosai Khaseem ya ji tausayinsu ya kama sh, shima saida ya goge tasa ƙwallar,












"Barka da fitowa Dad", cewar Khaseem daya matso wajen, da murmushi ya gyaɗa masa kai, dan kunyarsa sosai yaji yana ji, hakan yasa ba shiri ya ɗauke idonsa dan wata muguwar kunya ce ta baibaye shi, tir yake da rayuwarsa ta baya yana jin dama a tariyo masa ya gyara kuskurensa, gaba ɗaya ji yayi walwalarsa ta kau, danasani ya maye gurbin farin cikinsa, Hajiya Lubabatu ta nazarce shi haka FAISAL, barin wajen sukai suka nufi motocinsu, direct katafaren gidan da FAISAL ya dandatsa musu suka nufa, dan dama basu jima da dawowa nan ɗin ba.
















Gida ne mai kyau da ƙawa, gida ne wanda daka ganshi kasan masu gininsa sun san me suke, sannan suna da ilmin abin, dan gida ne kamar an ɗakko daga turai an kawo shi, part biyu ne dana su Dad da na FAISAL wanda idan yayi aure anan zai zauna da Iyalansa, sosai Dad yayita kallon gidan kamar ɗan ƙauye.






kamar yadda gidan FAISAL yake haka na Khaseen yake dan gini iri ɗaya akai musu.






Suna shiga Mom takai Dad ɗakinsa wanda ya wadatu da kayan alatu, ruwa ta haɗa masa masu sinadaran ƙamshi, ta taimaka masa yayi shaving ɗin duk wani gashi na jikinsa, dana fuskarsa, sannan ta taya shi yayi wanka, nan take ya fito fes dashi, sai dai ramar da yayi, kaya ta taya shi ya sanya, tama lura dashi duk yayi sanyi, muryarsa ta tsinkaya yana faɗin "ki yafe min Luba, na kyare ki na baƙanta miki, na cutar dake, dan Allah ki yafe min sannan ki ƙara nemar min yafiyar Yarinyar nan, wallahi kunya da danasani ne yake ɗawainiya dani, wani iri nake ji", ya faɗa cikin ɗacin rai.






"Alhajina, wallahi na yafe maka dama ban riƙeka ba na yafe maka tin randa aka yanke maka huƙunci, kuma nayi farin ciki matuƙa da ganin Allah ya amshi roƙona mijina ya dawo mutum na gari, wallahi wannan kaɗai ya ishe ni, sannan Dota ta yafe maka dan da ita mukai maka girke-girken tarba dan mijinta ya kawo ta da kansa dan ta taya ni aiki", rumgumeta yayi yana ajiyar zuciya.












Bayan sun gama cin abinci, Khaseem kuwa tafiya yayi, su Twince da Amal da Aiman suka shigo suna ƙiran Granny wato Hajiya Luba, "Granny zanci tuwo", cewar wata Kyakkyawar Yarinya, tana cuno baki, Amal kenan, shi kuwa Aiman cewa yayi "ni dai kunun Gyaɗar nan zaki bani nasha", su Miema kuwa zama sukai suna cire takalmansu ko uffan basu ce ba dan da alama aun gaji, basu kula da Dad dake zaune ba, Dad kuwa ƙura musu ido yayi, dan sosai yaji Yaran sun shiga ransa, dan dama ya taɓa ganin hotunansu a wajen FAISAL, yana ƙaunarsu har ransa, katse tunaninsa yayi jin Amal da Aiman sun matso inda yake suna cewa "Laaaa Grandfa oyoyo, dama Momma ta ce mana ka kusa dawowa daga tafiyar da kayi, ashe yau zaka dawo bamu sani ba?", suka faɗa suna faɗawa jikinsa, wata ajiyar zuciya ya sauke ya ƙara rumgumesu, "ƙwarai na dawo Yarana bazan kuma barin ku ba", cikin murna suka ce "yawwa Granfa kaga sai mu dena kallon hotanka tinda gaka", da murmushi ya ce "ƙwarai kuwa tinda gana cikin hoton ya zo da kansa ba", dariya suka sanya har su Miema da suka taso cikin farin cikin ganin Kakan nasu da suka daɗe suna ganinsa a hoto, rumgumo Dad sukai ta baya "am happy to see u my Granfa, we missed u so much, kullum Momma da Granny suna ce mana ka kusa dawowa sai yau ka dawo, sai dai muyita ganin hotanka, pls karka kuma tafiya ka barmu", suka faɗa cikin shagwaɓa, ƙwalla Dad yaji ta tawo yayi saurin maidata, sannan ya girgizawa Hisham kai alamun bazai kuma barinsu ba, haka ranar ya lalace wajen wasa da jikokin nasa, fatansa ya ga na FAISAL haka.












Ƙaunar da Faisal yake nunawa Yaran Abokin nasa ne yasa kusan duk weekend anan gidan suke yinsa, sun saba sosai da Hajiya Luba dan ILHAM ta nuna musu itan Kakarsu ce, haka Khaseem dan yana jin daɗin yadda suke nunawa Yaran nasa ƙauna ta haƙiƙa, gashi Khaseem yayi-yayi da FAISAL ɗin yayi aure amma yaƙi, ya rasa abinda abokin nasa yake jira, ga shi dai babu abinda ya nema ya rasa kuɗi kyau da nasaba, ya dai ƙyale shi yaga iya gudin ruwansa, Hajiya Luba har ta gaji da yi masa zancen aure.












Wannan dalilinne yasa su twince suka shaƙu da Hajiya Luba, kamar yadda suke son Umman Ilham haka suke son Hajiya Luba, Dad kuwa a hoto suka sanshi, hakan yasa da suka tambayi waye, ILHAM ta basu labarin kakansu ne, kuma yayi tafiya ne ya kusa dawowa su dinga masa addu'a, hakan yasa suka dage yi masa addu'a tare da tambayarsa koda yaushe, hakan yayiwa FAISAL daɗi, ganin yadda ILHAM ta cusawa Yaranta soyayyar mahaifinsa duk kuwa da abinda yayi mata, hakan yasa ta ƙara ƙima da daraja a idonsa,












Bayan dawowar Daddy da sati har gidan ILHAM tazo tayiwa Dad ɗin sannu da zuwa, har kuka yayi yana neman yafiyarta, kuma ta ƙara jaddada masa ta yafe masa.














Lokacin da ALHAJI BELLO yaji FAISAL yaje har Bichi ya gyara ɓarakar da ya tafka, har kuka yayi yana godiya ga Allah daya albarkace shi da FAISAL a matsayin Ɗa, har Bichin FAISAL ya kaishi ya ƙara neman yafiyarsu, kuma alhamdulillah yafiya ta samu saura ta Ubangiji.


















Mama tayi aure inda ta aure Abokin Alhaji BELLO RABE, ya ganta ne lokacin da ake shari'ar ILHAM, daƙyar ta amince saida ta tabbatar ba halinsu ɗaya da Alhaji Bello Raben ba, sannan ta yarda, mai kuɗi ne sosai, matarsace ta rasu tabar yara biyar duk manya, kuma suna girmamata sosai, Mama da Hajiya Luba sun zama ƙawaye na ƙut da ƙut, har gida Alhaji Sale da Mama suka zo sukaiwa Dad jaje tare da murnar dawowarsa, sosai yaji kunyar Mama kuma yayita bata haƙuri, da neman yafiya, kuma ta yafe masa.














ILHAM ta saki jikinta fa Dad tana zuwa ta gaida shi, tana kuma girmamashi a matsayinsa na mahaifin wanda ta mayar kamar Yayanta.






"FAISAL ina neman Alfarma a gare ka, akwai wata Ƙaramar Yarinya da aka kai Kurkuku bata fi shekara goma sha biyar ba, wai tayi kisan kai, kuma da ganin yarinyar nan bata aikata abinda ake tuhumarta dashi ba, dan kana gani kasan sharri ne, wallahi abin tausayi, bakaga yadda ake cin zarafinta ba, dan Allah ina so ka tsaya mata dan idan bata samu adalci ba, zata ƙare rayuwarta a kurkuku tana ƙaramar Yarinya",










Sosai FAISAL ya ji tausayin Yarinyar, kuma yayiwa Mahaifinsa alƙawarin zai je dan ganawa da Yarinyar, kuma yayi mamaki da yaji kurkukun maza aka kaita bana mata ba, kuma a matsayinta na mai ƙananun shekaru, dole akwai wata sarƙaƙiyar.










Alhamdulillah, yau muka kawo ƙarshen Book ɗinmu na haɗaka wato *HANYAR RUWA*






Ina fatan Ubangiji ya ya abinda muka rubuta ya zama izina ga masu aikata wannan lamari a duniya gaba ɗaya, wato cin zarafin Ɗan adam da yin rufda ciki akam abinda ba naka ba, cin zarafin Ƴaƴa mata ta hanyar fyaɗe ba tausayi babu jinƙai, da kuma tsanar talaka wanda bashi ya tsarawa kamsa kasancewa talakanba, ya kamata masu hali irin wannan su gyara saboda dama sau ɗaya take zuwarwa mutum, wallahi ya mutu bai tuba ba to ya kuka da kansa dan Allah bazai barshi ba.












Abinda mukai dai-dai Allah ya bamu lada abinda mukai ba dai-dai ba Allah ya yafe mana.
















Sabon Littafin ƘANWAR SOJA wanda zata fara nan bada jimawa ba, wato *BANIDA HUJJA*

Wato Yarinya ce Ƴar kimanin shekara sha biyar zuwa sha shida aka kawo gidan yari da laifin kisan kai, kai da ganin yarinyar kasan bata san koda kisan kiyashi ba balle mutum duk da ance mutum mugun icce ne, sai dai na wannan Yarinyar akwai lauje cikin naɗi, akwai lamari mai ban mamaki da zallar chakwakiya a ciki, dan a ƙa'ida ma shekarunta bai kai a kaita kurkuku ba, amma sai gata an kawo ta, hatta gandirobobi, birsinoni mamakin hakan suke kuma ba komai ne abin mamakin ba shine magarƙamar maza aka kawo ta ba ta mata ba, wannan duk yana cikin littafin *BANIDA HUJJA* na ƘANWAR SOJA, karku bari a baku labari, labarin yazo da sabon salo cakwakiya, firgici da rikita-rikita, tausayi da dai sauransu, ku bibiyi wannan book mai tarin abin mamaki.










By Rumyn Royal
















*Alƙalamin mu Ƴancinmu✍️*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment