Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa "Ummah saifa kun kwantar da hankalinku kun ba shari'a had'in kai duk abinda kuka sani kuyi k'unk'urin sanar da court kar wani abu ya baku tsoro ta hakane zaki kwato ma d'iyarki y'ancinta", sosai ya k'ara nusar da ita.








A wajan Faisal kuwa yana shiga gida ya tadda Dad d'in sai masifa yake ma Hjy Lubabatu inda yake shiga bata nan yake fita ba sai hawaye take na bak'in cikin mijin nata Faisal na shigo ya nufi wajan mahaifiyarsa zuciyarsa na tafartasa Alhaji BELLOH cikin masifa ya ce "yauwa ai dama kai nake jira harni zaka rink'a jayayya dani a cikin court harni zaka tsaya kana tuhuma a bainar nasi ni Faisal?", Ya idasa maganar yana nuna kansa a hargitse Faisal zanyi magana rantsa a jagule da sauri Hjy Lubabatu ta girgiza mai kai cike da masifa Alhaji BELLOH ya k'ara cewa "barshi bana ya zage ni ai ke kika bashi k'ofar raina Mahaifinsa wallahi wallahi akan wannan shari'ar Faisal zan iya tsine ma" wata irin masifaffiyar bugawa zuciya ce ta sami Hjy Lubabatu dafe k'irji tayi ta ce "Alhaji tsinuwa fa kace", ta idasa maganar hawaye na bin k'uncinta Faisal kuwa baiji wani abu ba dan shi akan gaskiyarshi yake ko Allah ya ce koda iyayanka sun tsine ma indai wajan gaskiya ne da bin umarnin Allah kwata-kwata Allah bazai amshi wannan tsinuwar ba bare shi da yake ubane ba uwaba.




Cike da k'unar zuciya ya ce "kware kuwa yadda kika ji kai kuma wallahi karna fito na taddaka kai cikin gida na tunda ka zab'i wasu banzaye a kaina kuma mu zuba muda ku muga wa zaiyi nasara karna fito karna fito na sameka a cikin gida na kaji na mai-maita maka inba haka ba wallahi billahil azim zanma abunda baka tab'a tsammani ba zan cire sani na wai kai d'ana ne na shinfid'a ma rashin mutumcin da sai ka zubar da hawaye". Yana idasa maganar ya haura sama yabar su sake da baki........✍️














*ZAHRA ROYAL STAR CE*🌟✍️










Comment and share Fisabilillahi🥰🙏⚖️💧HANYAR RUWA⚖️


💦The way of water💦






Together
By


ƘANWAR SOJA


RUMYN ROYAL


ZAHRA ROYAL.




A heart toching story💔say No Rape❌








In the name of Allah, the beneficent the merciful.








After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).










🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*










PAGE 3️⃣4️⃣➡️3️⃣5️⃣


HAJIYA LUBABATU kuwa tsoro da firgici da tashin hankali ne ya ziyarce ta, mamakin mijin nata take tana ƙarawa, FAISAL kuwa ido yabi Mahaifin nasa da shi dan dama yasan za'a zo wannan wajen, cikin ƙunar zuciya Hajiya Lubabatu ta ce "nima bazan zauna ba FAISAL tare zamu bar masa gidan, banga amfanin zama da mutum irin wannan ba, dole na barshi bazan tsaya ina kallo kabar gidan nan ba, ƙafa ta ƙafarka", kallonta yake tare da haɗiyar abinda ya tokare masa wuya ya ce "Mom kiyi haƙuri ki zauna bazan so akaina kibar gidan nan ba, zan tafi kuma kinsan ina tare dake ba zanyi nisa dake ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki, addu'a zaki taya Dad da shi na tabbata wataran zai gane ba akan gaskiya yake ba, kuma duk abinda yake faruwa zan dinga sanar dake", ya faɗa cikin lallashi da son kwantar mata da hankali, cikin rawar murya ta ce "to ka gaya min inda zaka je ko hankalina zai kwanta", ta faɗa da sanyin murya, tausayi ta bashi ya ce "Mom ina tare da Khaseem", abinda ya faɗa kenan ya nufi side ɗinsa, bai jima ba ya fito ɗauke da troly a hannunsa,










gaban Mom ya tsaya ya sumbaci goshinta tare da kwantar mata hankali da idonsa kana yabi hanyar fita, cikin murya dashashshiya ta ƙira sunansa, juyowa yayi ya kalle ta dan shima idonsa ya kawo ruwa, "ka ci abinci FAISAL karka dinga zama da yunwa, zan masa magana in sha Allah zaka dawo gida", kai kawai ya gyaɗa mata kana ya ja jakarsa ya fice.












Khaseem ne ya maida su Umma gidansa, sai kwantar musu da hankali yake, Umma dai jinsa kawai take dan jikinta gaba ɗaya yayi sanyi ƙalau, ILHAM kuwa banda ajiyar zuciya babu abinda take jerawa, hawayen idanunta ma sun ƙafe sai kukan zuci take, suna isa wanka sukai suka yi sallar azahar kana ya gabatar musu da takeaway ɗin da ya siya musu, ILHAM kasa ci tayi dan ko kaɗan Abinci yanzu ba shiga yake ba a gare ta, sai Umma ta tsawatar mata tukunna take ci.




















Fitowar Khaseem kenan daga wanka bayan ya shirya wayarsa tahau ƙara, isa wajen da take yayi ya ɗauka ganin FAISAL ne yasa ya ɗaga yasa ta a handsfree "kana ina?", cewar FAISAL, jin muryarsa da Khaseem yayi yaji shi sai a slow hakan yasa ya ce "what going on?", ya tambaya ba tare da ya bashi amsar sa ba, numfashi ya sauke ya ce "Dad ya kore ni a gidansa, yanzu haka ina Raihan Hotel", hankalin Khaseem ya tashi ainun, cikin wani irin yanayi ya ce "FAISAL ta bakin Umma anya ba zamu haƙura da wannan shari'arba, ka duba fa ka fara samun matsala da Dad, anya ba zamu canza shawara ba?", ya faɗa fuskarsa da alamun tsoro, murmushin takaici FAISAL yayi ya ce "no going back Abokina, kasan bana iya haƙuri da abinda na fara, dan haka ka cire duk wannan musa abinda yake gaban mu da muhimmanci, yanzu dai ya Umma da ILHAM?", cikin yanayi na ba yadda ya iya ya amsa masa da "suna lafiya, sai dai gaba ɗayansu jikkunansu is so cool", cikin ƙarfin gwiwa FAISAL ya ce "encouranging them please", ya faɗa, sun tattauna magana kana suka datse ƙiran.
















Cikin ɓacin rai Hajiya Lubabatu ta nufi sama zuwa ɗakin Alhaji Bello, tana shiga ko sallamar da ta saba batai ba ta ce "yanzu abinda kayi ya dace kenan BELLO!, Ɗanka na cikinka ka kora saboda son zuciyarka, wallahi ina danasanin saninka da nayi a rayuwa, da ana komawa baya dana gyara kuskuren da nayi na aurenka, ka cika mugu azzalumi BELLO bansan halayyarka ba saida na aureka, ashe kai ƙungurmin macuci ne azzalumi murakkabi kuma mazinaci, wallahi idan baka tubarwa Allah ka nemi waɗanda ka cuta su yafe maka ba wallahi kai ɗinnan abincin wuta ne kai, kuma....", bata kai ga ƙarasa maganarta ba taji saukar wani bahagon mari a fuskarta, bata gama jure zafinsa ba ya ƙara mata wani gigitacce wanda yayi sanadin faɗuwarta ƙasa, dukanta ya shiga ji kamar ya samu jaka, saida ya tabbatar ta daku kana ya nuna ta ya ce "har kinyi zarrar da zaki zo gabana kina jifa na da maganganu irin wannan har kina ambatar sunana kai tsaye, to bari kiji wallahi koda wasa kika ƙara zuwa gabana kina gayan magana ba tare da kin tauna ba saina kusa kashe ki, kuma tabbas ni macuci ne kuma mazinaci kamar yadda kika sani, sai dai zama dani dole tinda har muka aje ɗa a tsakanin mu, kinga kuwa zama da mazinaci dole", yana kammala faɗa ya rushe da dariya ya fice ya barta hancinta da bakinta duk jini, banda kukan takaici babu abinda take.




















Rana bata ƙarya aka ce sai dai uwar ɗiya taji kunya, yaune Alƙali ya bada damar dawowa Kotu domin cigaba da gabatar da shari'a, kowa ya halatta kamar wancen lokacin, sai dai yawan mutanen na yau na daban ne, dan Kotu ta cika tayi maƙil babu masaƙa tsinke.✍️
















*By Rumaisa Aliyu Inuwa(Rumyn Royal Star🌟)*⚖️💧HANYAR RUWA⚖️


💦The way of water💦






Together
By


ƘANWAR SOJA


RUMYN ROYAL


ZAHRA ROYAL.




A heart toching story💔say No Rape❌








In the name of Allah, the beneficent the merciful.








After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).










🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*

















3️⃣6️⃣. ➡️. 3️⃣7️⃣.


Rana bata ƙarya aka ce sai dai uwar ɗiya taji kunya, yaune Alƙali ya bada damar dawowa Kotu domin cigaba da gabatar da shari'a, kowa ya halatta kamar wancen lokacin, sai dai yawan mutanen na yau na daban ne, dan Kotu ta cika tayi maƙil babu masaƙa tsinke.✍️














Mi'kewa Barrister Khazeem yayi ya gabatar da kansa sai dai abun mammaki har yanzu Barrister FAISAL bai iso ba , , court ce ta bada dama ga Barrister YUSUF domin ya gabatar da hujjar kare Alhaji BELLOH RABE wanda ake tuhuma da yewa yarinyar dake aiki a gidan sa fyad'i ,da kuma barazanar kisan kai,, . nan kmtake aka kira wane bawan Allah mai suna Iro cikin hikima Barrister YUSUF ya Fara jiro masa tambayoyi bayan yayi rantsuwa cewa zai fad'a gaskiyar al'amari akan abinda ya gani..








"Shin zaka iya sanar wa court abinda kasani da kuma waye kai a gidan Alhaji BELLOH, "? cewar Barrister YUSUF, zufa ne ya gogge yafara magana cikin karkarwa " da farko suna na Iro ina zaune a gidan Alhaji ne da mata ta da yarinya macce d'aya tsawon shekaru ashirin ina masa aikin driver , kuma ban ta'ba ganin cin mutuncin ko tsanguma daga Alhaji BELLOH ba ,a koyaushe yana taimaka wa idan an Hamza m ,babban abu ma akaiw masu aiki dewa a gidan sa maza da mata amman hakan bai ta'ba faruwa ba kawai daman sharri ne da hasada irrin na wasu talakawan, " ,




" Shin Iro 'karfe nawa Alhaji BELLOH ya dawo a ranar Laraba da ake tuhuma sa da aikata fyad'i " kamar yadda mu ka saba dawo wa dashi yalla'bai 'karfe shidda ",








"ya mai girma mai Shari'a wanan shine babban shaida ta bansaniba ko lawyer masu 'kara suna da ja ,"? murmurshi ta 'ka'kalo na dole ganin Barrister FAISAL Bai samu hallara ba har yanzu da ido Khazeem ya ganta take ta mi'ki tayi tattaki har gaban Iro da tunda ta ganta gaban sa ke fad'owa "








"MY lord suna na Barrister Suhaima daga 'bangarin kari hakkin mata ina da wasu tambayan da xansa driver ALHAJI BELLOH wanda ake tuhuma da ya aikata fyad'i.?"





Izzine aka ba ta " Mallam Iro kace kana da yarinya 'ya macce ko " ey ya amsa da gumin dake addabar sa ga buguwar zuciya sa dake nuni ta rigar sa , "shin baka tsoro hakan ya iya faruwa da taka d'iyar kasancewar Mace mace ce a ko ina ," Barrister YUSUF ne ya mi'ki "ya mai girma mai Shari'a wacce ta ke kare masu 'kara tana kai farmaki zance a gun shaidata ,"








murmurshi ta sake nasa ta chigaba da tambayan ta har ta gama ,chan sai ga shaidar sa na gaba wato Isa wanda yake aiki da Alhaji BELLOH RABE a office shina tambaya sa akaye time da Alhaji ya bar office a wanan ranar sai dai duk amsar d'aya ce ma'ana dai "karfe shidda basu sauya amsar su ba , Al'kali ne yayi rubutu ya d'ago har yanzu Barrister FAISAL BELLOH RABE bai bayyana a gaban court ba duk da cewa yayi alƙawarin wasu shaidan sa , mai jar ragamar case nasa.














Barrister YUSUF ne ya mi'ki "ya ma girma mai Shari'a ina da wata hujja wato mahaifiyar Barrister FAISAL BELLOH RABE kuma yaron sa ma'ana matar Alhaji ,itta kaɗai ce zata zama raba gardama a wanan Shari'ar , ta sosai tayi a kidd'ime ga wasu hawayin dake bin kumatun ta Iliham ce ta gogge hawayen ta da hijjabinta Umma kam idon ta ne ya kafe rafff kamar mara numfashi 'yan jaridu ne ki haska camera nasu da nasu rubbutu don jin irrin bada'kala tsakanin mata da miji.








"HAJIYA LUBABATU ko zaki iya bayanai akan me ya faru da mai gidan ke meke faruwa? gabatar da kanta tayi wa court sanan ta gyara tsayuwar ta ," ya mai girma mai Shari'a miji na da ake zargin bai aikata hakan ba domin sai shidda na dare ya dawo kuma a wanan lokacin ma Iliham ta tafe gidan mahaifiyar ta ne hakan bai faru a gidan na domin ina nan" daram daram gaban jama'a yake fad'uwa tuni wasu suka amince wasu ko kawai ganin ta su kiye ,








Barrister Suhaima ce ta mi'ki "my lord Ina da tambaya ga Hajiya Lubabatu, " izzini a gaba ta , nan ta zaro wayar ta ta kuna record ,"Muryar ce ke magana ta Hajiya Lubabatu tana cewa "wallhi ina cikin tashin hankali idan har na rasa rayuwar yaro na yanzu ," daga cikin wayar ne aka ce "shawara ɗaya ce kiye abinda kike ganin zai fe miki amman ke shaida Allah baya barchi ," kiran ne ya da datse " shi kuma wanan muryar me zaki ce "? COURT ce ta fara hayaniya , Al'kali ne ya buga guduman sa ya fara rubutu,











Ido ne ya kuma bakin 'kofa ganin an shigo da mutum duk jini a jikin sa tuni hankalin mutane ya tashe Barrister Khazeem bne ya mi'ki ganin Barrister FAISAL BELLOH RABE cikin mayuwachin hali, nan ya isa gaban Al'kali akan keken sa " ina mai. bada hakuri bisa rashin zuwa da wuri ," ganin mahaifin sa yayi da ya tsorata da ganin sa bayan a daren. jiya ya bayar da kudaden masu yawa a kama shi a kashe shi " Daddy " ya fad'a cikin narkewa zuciya "ashe zaka iya kashe ne don gaskiya ta ? ashe makirchin ka akan talakawa gaskiya ce ? ashe zaka iya salwantar da rayuwar d'anka dake don ka dawo hanyar gaskiya "? shin Umma ki kuma kin manta da cewa Allah ne mai raya wa mai kashewa har kika yarda zakiye shaidar zurr din tsoron kar a kashi ne ? shin kin manta Allah ya saukar da Suratu tauba , don ya zama izina ga masu laifi ,? shin Umma kin manta aya ta 124 da wasu ayoyyi dake nuna illar shaidar masu 'shaidar sur a gaban hukuma ko mahukunta...?












mi'kiwa Barrister YUSUF yayi "ina da 'korafi yalla'bai Barrister FAISAL yana kawo shi da babo a nan "hararra Al'kali ya buga mai da cewa "korafinka bai amsu ba ".
Hajiya LUBABATU ce ta fashe da kuka "ya mai girma mai Shari'a tabbas nayi laifi kuma bayiba tun kafin na bar wanan kwantar na shaida Allah ya min babban Ishaq ga abinda nake tsoro idan har na karanta Alqur'ani kuma nasan suratul taubat dmto babbo shakka akan gadon sunna ta aka wa Iliham fyad'i " inallillahi wa inna iallhin raji'oun abinda kowa tai cewa kinan nan ta koro dukkan abinda ya faru ta sanar ,





Iro ne ya fashe da kuka take yazo ya 'karyata abinda yace daga farko da cewa barazana aka masa akan hakan don yayi shaidar 'karya , akan wanan al'amarin Isa ma ya dawo da zancen gaskiyan sa ,,











Al'kali ne ya tambaye Alhaji BELLOH RABE take ya tsuguna " tabbas duk @binda ka shuka zaka 'kirba ,duk nisan jifa'kasa zai fad'o, ramin 'karya'korarrari ne ,sanan rana dubu ta 'barawo rana dubu na mai kaya hakkin wane baya barin wane na aikata yalla'bai,,











Rubbutu sosai Al'kali yayi ya d'ago idon sa da yayi ja yace .."








Al'kalamin ƙanwar sojah-----------ce ✍️💞⚖️💧HANYAR RUWA⚖️


💦The way of water💦






Together
By


ƘANWAR SOJA


RUMYN ROYAL


ZAHRA ROYAL.




A heart toching story💔say No Rape❌








In the name of Allah, the beneficent the merciful.








After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).










🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*





*
38 & 39










Rubbutu sosai Al'kali yayi ya d'ago idon sa da yayi ja kowa yayi shuru zuciyoyin mutane sai bugawa take bare ta Alhaji BELLOH sosai zufa ke yanko mai wata irin muguwar nadama tazo mai bai tab'a tunanin cewa akwai irin wannan rana zata zo ba gyaran murya alk'ali yayai kowa hankali ya dawo kan alk'ali Ina sauraran sa ya ce. "a 'karkashin doka ta 306 da 423 sakin layi biyar da d'igo bakwai ,, doka ta haramta fyad'i ga yara 'kasa da shikaru goma sha takwas,, ya k'ara gyra gilashin idonsa ya sake cewa,


"Ga duk wanda ya aikata hakan doka mai bayani akan zaman gidan yarin tsawon shekaru goma ya tabbata akan sa ,


a babbi na ukku mai sake alkalami tana bayani akan court zata ce ta rarka dubu dari biyar , sanan zaka biya yarinayr Naira miliyan goma a cikin dukiyar ka domin tayi jinya ta dogara da kanta idan kayi hakan doka number 306 zata sausauta zama ka gidan yarin zuwa shikkaru biyar 5"


Alk'ali ya sake cewa "idan wadda ake k'ara yana ja akan wannan hukunci zai iya d'aga k'ara", yana gama fad'ar haka ya buga gudumarsa,


Babu wadda ya kai Alhaji BELLOH shiga tashin hankali kuka yake kamar k'ara min yaro hatta shi kansa Faisal sai yanzu ne jikinsa yayi sanyi koba komai ai mahaifinsa ne hatta Hajiya Lubabatu kuka take na tsananin tausayin mijin nata ance mata da miji sai Allah amma wani shashi na zuciyarta tana farin cikin bayyanar gaskiya na kwato ma yarinya hakkinta.


Y'an sadda ne suka tasa k'eyar Alhaji BELLOH suna k'ok'arin fita dashi




Ba k'aramin dad'i Iliham taji ba har Ummah kukan dad'i kawai Ummah keyi tana godiya ga Allah,




Su Barrister K'haseem kuwa murna suke shida Faisal ta nasar da suka samu suna cikin magana Barrister Yasuf ya mik'a masu hannu da cewa "Congratulations ina tayaku murnar nasarar da kukayi" Sosai suka saki fuska suna bashi hannu suma ana musabaha,




BAYAN KWANA BIYU




Sosai su Ummah canjin rayuwa yazo masu kota ina suna samun kulawa sun samu canjin mahalli na kansu da kansu Sosai Ummah take ba Iliham kulawa sosai take sabon lafiya inda Barrister K'haseem yake zaryar kulawa dasu ba dare ba rana inda takanas suka zo shida Faisal wajan Ummah domin nemar ma Barrister K'haseem AURAN Iliham d'in dan kuwa har zuciyar sa yake sonta da tausayinta,




Bayan Ummah ta saurari abinda ya kawo su ta ce "duk naji abunda ya kawo ku bazan iya hanaka auran Iliham ba amma yaro kaga dai abunda ya faru da yarinyata mareniya ce in kaga zaka iya canza mata Nan ga to dan girman Allah ka kyale ta tayi rayuwarta cikin salama Dan bana son inda za'a tuzar tamin yarinya dan kasan mutum Koda yaushe zai iya canzawa" gyara zama Barrister Faisal yayi kwata-kwata baiji dad'in abinda Umman ta ce ba amma da gaskiyar ta ya ce "Ummah kamar baki san waye Barrister K'haseem ba na tabbata bazai tab'a cutar da Iliham ba kisa a ranki ta samu wadda zai kula da ita har k'arshen rayuwarta Ina da yak'inin hakan", sosai suka kwantar ma Ummah hankali kan cewa ba wani abunda zai biyo baya.




Iliham dake sauraran su tazo shigowa domin gaida su da sauri ta ruga cikin d'akin ta tana fad'awa kan gado kuka ta saki mai cin rai wannan tabo da Alhaji BELLOH yayima rayauwar ta bazata tab'a manta shi ba har k'arshen rayuwarta Nan daba su K'haseem bane kowa yazo auranta za'a iya zugesa haka rayuwarta zata k'are da tsamgwamar mutane akan abunda ba laifinta ciki mi yasa mutane basa ganewa ne why why mi yasa sai mace za'a rink'a yab'a mata tabo mi yasa su mazan in sukayi kwata-kwata sai a manta sai mace Koda bata da laifi ne kuka take tana tunanin halayan mutane lallai zata auri Barrister K'haseem kodan ta tsira da mutumcinta,




Ummah dake shigowa da sauri ta k'ara so kusa da ita tana cewa "da alama kinji mi muka tattauna da su Barrister nidai a matsayi na na uwa a gareki Iliham kiyi tunani ki hanke ma rayuwarki abunda zai anfane ki duniya da lahira bazan miki dole ba amma ki sani karkiyi wasa da damar da Allah ya baki dan..... Kamin ta kai maganar Iliham ta fad'a jikinta tana k'ara sakin kuka ta ce "A'a Ummah wallahi na amince to taya za'ai nak'i amincewa Ummah shin wa zai iya aurena a haka da wannan bak'in fattin Ummah yama rayuwata tabon da bazai tab'a gogewa ba", Sosai Ummah ke k'ara kwantar mata da hankali.






A wajan Faisal kuwa zaune suke da Hjy Lubabatu duk ta rame saboda rashin mijinta Faisal cikin kwantar da murya ya ce "Mommy ina so inje wajan Dad" da sauri ta waiga tana kallon sa ta ce "A'a Faisal kana ganin bazai ma wani abu ba" "a'a Mommy na tabbata ba abinda zai faru please Mommy ki bari naje na gansa" cewar Faisal gyara zama tayi dan itama tana son gano mijin nata Amma tana dannewa ne ta ce "hakane shikenan zamuje tare gudun matsala". Sosai yayi farin ciki.










WASHE GARI


Kai tsaye gidan yari su Faisal da Mahaifiyarsa Koda aka fiddo da Alhaji BELLOH sosai cikin kwana d'aya harya rame kuka Hjy Lubabatu ta saki k'ara sowa yayi k'asa yana sakin kuka kamar k'ara min yaro ya ce "dan Allah ku yafe min Faisal ka nemar min yafiyar yarinya nan dan girman Allah" kuka yake kamar zai shid'e sosai Faisal ya rungume sa suna kuka gwanin tausayi Faisal zaiyi magana Alhaji BELLOH ya ce "ina AL'FAHARI dakai lalllai badan kaiba da har yau ina cikin b'ata Allah yayi maka albarka Faisal











Zahrah Royal Star⚖️💧HANYAR RUWA⚖️


💦The way of water💦






Together
By


ƘANWAR SOJA


RUMYN ROYAL


ZAHRA ROYAL.




A heart toching story💔say No Rape❌








In the name of Allah, the beneficent the merciful.








After the successful of
(FARASHIN SO, RABI DANJA) & (FANSAR MACIJIYA), now we are back with (HANYAR RUWA).










🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}


https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_


*Alk'alaminmu 'yancinmu*










*END*








"Allah yayi maka albarka Faisal yasa ka gama da duniya lafiya, yadda kayi silar gyaruwata ubangiji ya baka Ƴaƴa masu albarka da amfani", cewar ALHAJI BELLO RABE, da ameen suka amsa jikkunansu duk sunyi sanyi, hawaye kam ya kasa tsayawa

Please Login or Register in order to submit comment