halinki innabiye maki manyan kaya zakidauka duka tayi maganar tana mikewa tabude drawer tajawo akwatin kayan khadija
Tahau duba kayan ciki kananun kaya tayita shiryawa khadija saboda Usman yasiyamata kananun kaya masu masifar kyau
Mini sket da kananun kaya gasunan kamar kazanta""" manyan kaya kala uku kawai tasakamata"" takoma hadamata kayan kwalliya komai saida tasaka tace sauran kuma idan kinje karkiyi kwalliyar""" nasan halinki"" danzankirah inji waima ina wayarki???
Khadija tace nafadawa dad fa yakarbomun gida namanta ta wlh kuma inason yin magana da Yayana Amman nakasa tambayarsa koya karbo kumashi baicemun komaiba"" labila tace kinsone wlh dakinason wayadashi aidasaikice inbaki Aron wayata saiki kirashi""
Tamere baki inna hardace nomber din kokuma inbar hardaceba"" labila tace kumafa hakane Amman aidason ranki lanbarda batawuce ashirinba keda kikeda kwakwalwa maikyau kikasa hardacewa
Tace kwakwalwata ta karatuce bawai danna hardace tarkacen numbers ba""" labila tace hakanefa ustaziyya Amman kinsan hardace number yanada amfani kodan watarana
Bawai ina fataba kisamu kanki inda kike neman agaji abaki Aron waya baki hardace number kowaba yakenan gashima dai yanzu karamin misali kinason waya da ya muktar Amman bakisan number saba
Khadija tace kinada gaskiya zanyi kokarin hardace tamutum biyu"" labila tace Yayana dakuma daddy ko ???
Murmushi khadija tayi labila tace bakomai mukoda ba a hardace tamuba badamuwa Amman inafatardai abunda nafadamaki dazun kinkwasheshi afaifan kanki wlh sahiba inajimaki tsoron wata baturiya takwace makishi
Aikuwa khadija tahade rai labila tahauyi mata dariya tatashi tabita sukahau zagayen dakin karshedai labila tafada saman gado tana hakiii tace tubanake small momy🤗
Khadija tace aisaikinsha rankashi aka"" labila tarumtse ido takankance kai tanadafe dakai tanajiran saukar rankwashi khadija tahauyi mata dariya tazube saman gadon tace waike atunaninki rankwashinki zanyi aka???
Ainibazan rankwashi kainaba idan dady yasamu baturiya aibanice zanyi kishiba kece dannasan kinfison farincikine fiyedani Kaina yanda kika damu dani nibandamu dakaina hakanba """
Labila tace aisaboda kinsan hakan shiyasa kikemun abunda kikaga dama takwanto saman kafafuwan khadija tace wlh sahiba jinakeyi kamar aduniya bazanso kowa sama dakeba
Idan akacire Allah da manzonsa da sahabai dakuma ahalal baitiii idan za akuma tambayana wanakeso bayansu kinsan wazanfada???
Khadija tagirgiza kai labila tace wlh sahiba sunanki zankirah !! Jinake tamkar sabodake akayini kullum soyayayrki sake shiga rainatake bansan daliliba kodan kinason babanane
Khadija tayi murmushi tace dama haka Allah yake ikonsa soyayya gamon jinice""labilata tashi zaune takurawa. Khadija ido kamar mainazarin wani abun saikuma tafashe dakuka data tunoda kudirin lubabatu akan Khadija
Itama batasan sanda tafara kukanba suka hade kai sunata kuka akarasa Wanda zai rarrashi wanie
Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 85
By
Gentle Lady💃🏽
Saida sukai mai isarsu sukadawo rarrashin juna""" labila tace zanyi kewarki sosai sahiba idan kikatafi khadija tace nima haka wlh sahiba Amman karkidamu ga wayanan ai zamudinga waya kodata daddy ce
Nibandama wani Abu mezaihana kicewa daddy kema zaki wlh zanfi sakewa idan inaganinki"" labila tace naki wayon aiko nan gani nane yasaka kika sakankance gobe aurenki sati dayafa Amman bakitaba zuwa wajen mijinkiba saikace haka akacemaki anayin auren"" wlh kebandah wani Abu dasaina hadaki da inna airanarda za akawoki bahaka akace kiyiba
Khadija ta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace daddy nefa yace inbari yafadamaki kizo kirika tayani kwana kokuma haka kurum baikiraniba nidadi miji sai inkai kaina""
Labila tace ayya sahiba kinada gaskiya aibandauka hakan akayiba koni banbaki goyon baya kiyimasa rawar kafaba dole mudanja ajinmu irin namata aikingane dannafiso yagane akwai banbanci atsakaninku """ mudin bamasu arha bane
Khadija tace kedai akeji wai mahaukaci yafada rijiya kinga kitashi muje muyi alwala dare yayifa sosai musamu ko hizifi uku mukaranta"" labila takalli agogon dakin yabuga shabiyu da kwata tace hakafa aiyau babu maganar barci hirar bankwana zamuyi
Khadija tace nanfadai wlh saina kwanta kinsan bantabaa shiga jirgiba karnaje nayita kwasar barci ayimun dariya tayi maganar tana mikewa labila tace dariyadai waye zaimaki dariya Wanda ya aikeki bayankuma kowa da abunda yashamasa kai babu ruwan kowa dawanie
Khadija tace to suda muje muyi alwalar tana dariya tatashi khadija tafarayin alwala sannan labila sukasoma karatu sai uku saurah suka kwanta
Washe gari tunda sukai sallar asuba basu komaba sukahau shirya kayansu harda labila dantacemata itama kano zatawuce dazaran tarakasu
Bayan sungama suka gyare dakin "" dasauran inda suka bata"" sukai wanka suka shirya sannan suka fita falon kasa Usman yanakusa da lubcy sai shagwaba takemasa kamar wata karamar yarinya shikuwa saibiyemata yake
Haka kurum khadija taji wani iri aranta tayi saurin soke kanta ahankali labila tace kinga yanda akeyi itama data tsufa ballantana keda kike sabon jinie yanzu kike lokacin ganiyarki ta rayuwa
Sam Usman baisan dazuwansuba lubcy ce kawai talurah kuma batadaina abunda takeba saima tayi tamkar bata gansuba""
Usman ne yaji kanshin khadija ya yawaita afalon yadago yakallesu dasauri yayi saurin saita kanshi yajanye lubcy daga jikinsa sosai yake jin kunyar labila
Khadija tagaidashi bayan sunkaraso ya amsa cikin dakewar murya "" tagaida lubcy itama ta amsa labila tagaidasu sannan suka karasa saman dinner haryanzu Khadija batadago kanta sunyi ido hudu dashiba
Tunda suka fara cin abincin yakeson tadago kanta danyakafeta damayun idanuwansa Amman taki dagowa dukda tanaji ajikinta yana kallonta
Bayan sun kammala yakirah habu driver labila tafitomata da kayanta sannan takulle bangaren tarike key din"" lubcy ce tafitoda kayan usman driver yakwashe duka yasa mota suka rankaya dukansu
Yace banga kindauko mayafinkiba kokina nufin iyah nan zakiyimana rakiya??? tana dariya tace inalaifi aiga yarkunan zata rakaku basainajeba Allah yakai lafiya yace Ameen
Takalli khadija tace Amarya asha amarci lafiya khadija tasanne kanta dakansa yabudemata baya"" harzata shiga tadafe kanta"" innalillahi"" wlh nayi mantuwa
Usman yace mantuwar me kumata dama haka shirinku yake kosati zakuyi kuna shiryawa karshe saikunje kunmanta wani abun
Labila tace kabarta mana tadauko mekika manta??? Tace wlh littafaina da Qur ani kumafa dankar namanta Na ajesu kusa kusa
Lubcy tayi karaf tace kekuma banda abunki Kanwata kudazakuje yawon amarci mezakiyi da littafai aikyabaridai harkudawo shima maigidan abashi lokacinsa
Labila tace sabodame zatabàrsu dankawai zatayi tafiya sai akace kabar addininka agida kejeki dauko sahiba tamika mata key wlh kar shaidan yarinjayeki ko inakikaje rike ibada saikace dai su oi daba ta dauki addinin dakimaba"" khadija tawuce cikin gidan
Lubcy tace aike komai saikin nunawa mutane kinfi kowa """ saikifadàman dawakike??? Labila ta marairaice fuska tace waini meyasa mom batasona daddy yanzufa dawata Yar makarantarmu nake tafashe dakuka
Usman yace haba lubabatu yarkiicefa baidace kinamata hakanba"" tace alhaji kanajinfa abunda takefada itah yadace tayihàkà?? Nifa mahaifiyartaçe
Yace aibadake takeyiba tafadamaki dawatà Yar skull dinsu take
Bandama abinki aikinaji batakirah sunaba koda ma takirah suna tundakedai kinsan bahaka kikeba aishikenan saikibarta"""
Tanisa shikenan alhaji yace yauwa kokefa yarnan dai takice komai lalacewarta nibansan dalilinda yasaka bakwason yayan fariba
Ainikam hajiya batayimun irin yanda kikemata karfanaje nadawo nasamu kinhanamun ya rawar gaban hantsi"" labila tace aini dad wajen hajiya zankoma saikundawo zandawo
Yace shikenan ma dama abdul sai Rigima yakewa hajiya waisaita kawoshi inda kike yauma naso turawa shima adaukoshi yadawo nan
Tace idan yadawo dad karatun shifa ??? Daidai kawowar khadija yace kece kikasan hakan Amman wlh danaje kuka Yakama saiya biyoni nakawoshi wajenki"" shibaima tunanin kowa saike
Khadija taimasu sallama suka amsa tamikawa labila key din bayan mota sukashiga shikuma dashi da driver suka shiga gaba tana tsaye tana daga masu hannu harsuka wuce sannan tajuya cikin gidan tana sake sake aranta sama tahau taduba inda ake ajemata sako tasamu layar wani murmushi tasaki tana juya layar labila kenan aiduk kame kamenki saina raba Usman da khadija saidai kuma kiyi hakuri
Tasheke da wata mahaukaciyar dariya irin wacce *hatsabibin boka* yakeyi saida naja baya dannatsorata nadaukama shine yabayyana agabana""
Tunda suka shiga mota labila saizuba takeyi harsukakai airport sunsamu jirginsu Saura minti talatin yatashi
Anan suka zauna zaman jirah duk abunda za ayi akagama lokaci yanayi suka soma shiga jirgi sai lokacin labila tasoma sharar hawaye tana kallonsu harsuka shige tana tsaye saida jirginsu yadaga tanasharar hawaye tana daga masu hannu""
Saida tadaina ganin jirginsu sannan tacewa habu suwuce ganin wani guy yanata kallonta"" tunda sukashiga motar tayi shiru sai sake sake takeyi aranta""
Sunakaiwa gida tace yajirata tashiga gidan lubabatu tana falo tayi sallama tahau sama tadauko jakar kayanta tasauko sannan tace ni mom zantafi
Tanisa kigaishesu"" labila tace zasuji hartajuya saita tsaya tace nasan kinturah dad da sahiba Dubai ne akan wani mugun nufin naki kisani Allah yafiku kibarganin bokanki yanacin nasara kidauka komai kika nema aduniya zakisamu awajensa shikanshi damace Allah yabashi domin yayimasa takunkumi kiji tsoron Allah Mom kidaina biyewa wanann bokan tafashe dakuka maitsuma zuciya lubabatu tamere baki
Idankundago kai tagado takalli indama labilar take saida tasakecewa please mom badanniba kidaina abunda kikeyi kinemi gafarar Allah
Tadago takalleta ahankade tace kingama??? Labila tayi shiru tace totunda kingama nagode da nasiharki muna gaidasu tamike tahaye sama tabar labila tsaye
Tabita dakallo saida tabace mata sannan tashare hawayenta tajuya taja akwatin kayanta
Tafita"" habu yabude mata tashiga yaja motar akabude masu get sukafita"
Fitarsu babu jimawa lubcy taciwo kwalliya tafita itama"" tashiga tanta tsetsiyar motarta akabude mata get tafita tasoma yawo cikin unguwanni kozata samu inda akeyin dahuwar abinci tunsafe har dare abunfa dawahala kuma ance karwani yaganie danhaka badamar tabawa wani kwangila dole dakanta zata binne""
Haka tayita yawo""" duk inda tatambaya daga masuyi dasafe saimasuyin da rana"" kuma tafison ahanya Dan agida tayiyu ba a cika wutar yanda zatayi zafie
Su khadija kuwa tunda jirgi yatashi takankame idanunta kamar zatayi kuka sai addua takeyi hakan yasa usman yajawota jikinsa yakwantar harsuka lulaya cikin gajimare"" ahankali tasoma saukarda ajiyar zuciya ba awani dadeba tasoma barci maidadi asaman jikin Usman
Dayalurah tayi barci yagyara mata kwanciyarta ajikinsa yarufemata fuskarta danbayaso ana kallonmasa puska tuni shima yasoma saukarda ajiyar zuciya yajingina kansa jikin kujerar jirgin yana tunani
Lubabatu tana tsaka dayawo tabaro unguwarsu Danisa indama taje batasan sunan unguwarba bama tataba zuwaba wata yarkasuwace Dan kusa da bakin titi take komai anasiyarwa awajen wata maisuyar doya taganie da dankali da awara
Tatsaida motarta tafito zuwa wajenta matar tanaganinta tawashe baki tanamata sannu dazuwa lubcy ta amsa suka gaisa tace nawa doya matar tace hamsin ashirin dankali kuwa goma biyar "" haka awara
Lubabatu tace kullum kina fitowa??? Tace tomezaihana hajiya aizama gida banamu bane munada marayu agabanmu
Lubcy tace Allah sarki aiyanada kyau kanemi halak dinka kamar dayaushe akesamunki anan??? Matar tace ai hajiya kaman karfe bakwai nake fitowa indorah koko idan yakare zuwa yanzu shabiyu nasoma suyar doya da dankali saidare nake tashi inbarwa yata inkoma gida inyi tuwon dare infito dashi
Takwas muke tashi watarana harmunakai Tara"" lubabatu tace kainaji dadi bani doyar ta dubu uku kisa dankali Na dubu daya zandinga aiko driver na yana karbar Mani
matar tawashe baki tace kaiii Amman naji dadi hajiya tanata wasar baki tazubawa lubabatu doyar tabata tafiddo kudi sabbi hull Tamika mata sukai sallama takoma motarta hartabar wajen matar tanadaga mata hannu saikallon kudi takeyi
tana juyasu bayan lubabatu tayi nisa tatsayarda motar tafito da ledar doya dantasan koda tajeda itah gida bazata iyah cintaba danmaituyar doyarma kyankyaminta takeji tasoma rabon ido kozataga wasu almajirai tanakiran wani
Yarugo kamar daga sama tajiii ance banda sadakaaaa aikinki zai lalace dasauri tajuya bayanta bataga kowaba tamiyarda doyar yaron yanazuwa tacemasa wanigida take nema kuma tagane tashiga motarta tawuce daniyar dadare zatadawo ta saka layar
Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
chapter 86
By
Gentle Lady💃🏽
Doyar datasiya da dankali saidai tazubar shara"" tana zauna sai sake sake takeyi aranta"" tamatsu dare yayi"""
Su khadija basu suka saukaba sai dayamma"" dama usman yana yawan zuwa Dubai bayazama a hotel gida yake kamawa haryagama zamanda zaiyi Amman gidan kusa dawani babban hotel yake"" mamallakin hotel din shiyakeda gidan yayishine dama saboda saukar baki""
Gidan tsab tsab dashi Dan akwai ma aikatanda suke shareshi su goge kullum saboda irin haka karbako yafado kokuma Wanda zaidauki hayarsa yazamana yanada datti""
Bayan sun aje kayansu saman kujerar falon khadija tazube saboda zaman jirgi Usman haryanzu yakasa gane kanta kumashi yakasa yimata magana
Idan tunaninsa gaskiyane Deejarh tana kishinsane"" murmushi yasaki ahankali ganin ko kallon inda yake batayi
Rigarsa yacire yabar wando sai farar singlet dinsa"" kusa da itah yazauna yajawo hannunta yace zo injimana Deejarh na wannan cin maganin duk na menene???
Kanta yanakasa haryanzu takasa dagodakai takalleshi"" yanisa please Deejarh na kisaki ranki dan Allah kodai garin nan ne bakyaso??? Kaita girgiza masa alamar ah ah
Yace towani abun akaimaki??? Nanma tace ah ah yace shikenan kitashi kiwatsa ruwa nibari insiyo mana abunda zamuci yayi maganar yana mikewa yadauki rigarsa yasaka yafita
Tabishi da kallo aranta tace meyasa hakan mezaisa inyi kishi matar sacefa??? Nibataji haushinaba danarikemata miji saini
Haba zuciyarta baikamataba mahaifiyar sahibar tawa saurin mikewa tayi tayishirin wanka "" tashiga toilet da addua aljanie haruzzal yana biye da itah saboda cika umurnin shugabansa""
Allahumma inni a uzu bika minal hubusi wal haba isi sannan tashiga take haruzzal yamakance baya koganin gabansa haka yayita bin hanya baiganin komai
Khadija kam batasan wainarda ake toyawaba bayan tagama wanka tadauro alwala tanafito wa Usman yana shigowa da sallama ta amsa masa sallamarsa ledarda take hannunsa takarba shima yayi shirin wanka maikawai tashafa sai powder tasaka wasu Riga da siket sundan matseta bakamar siket dinma""tafesa turare tasa hijab
Koda yafito hartasoma rankon sallarda take kanta shima yashirya cikin jallabiya yatada sallah bayan sungma sukai addua"" tajuyo da fara a tacemasa inawuni
Yasaki murmushi koba komai yaga fara arta yace qalau sarkin zuciya dariya tayi tace nifa dad bafushi nakeyiba kawai yanayin zaman jirginne yasaukarmun da gajiya
Yace kedai fadi gaskiya ainalurah dake tungida kiketa shan wannan kamshin harcikin jirgi kinkasa bari muhada ido
Ledarda take gefensu yajawo yajata jikinsa yace nasan yunwa kikeji bari kici abinci kozakifi sakewa danni banason ganinki cikin damuwa
Sinasir ne damiya dakuma jelof din shinkafa yace wanne kikeso dagaciki??? Dahannu tanuna masa jelof din
Yace to inazuwa yatada itah daga jikinsa yaje kitchen din gidan yadauko plate da cup da chokali yazuba jelof din sannan yazuba ruwa dakansa yarika bata abaki tanaci hartakoshi""
Yace ga ferfesun tace nidaikam Alhamdulillah yace tonidai bari naloda yadauki chokalin zaici tarike yakalleta yadaga girah alamar mene???
Tace nima dad zanbaka"" yasaki murmushi tonaji Amman banda katuwar loma kinga bakin yanda yake very small
Dariya tayi tanarike baki"" yace yidariyarki an jima nima zanrama"" tadibo abincin tasoma bashi yace wannan saiyawuna suntsinke kafinma tabanie kiyi dasauri kinsanfa cinedani kamar gara
Tayi dariya kai dad tobari nadinga baka dasauri tayi maganar tanaciko chokalin harbaka"" yace bafa cewa nayi kidibo Wanda yafi karfin bakin nawaba tace to sannan tarage tabashi baiwani cidayawaba yace yakoshi tace kaifa kace cinedakai
Yace aiwanda naci bakici korabinsaba""" murmushi kawai tayi tace shikenan jin ansoma kiraye kirayen magrib yamike bari naje sallah"" bayan yafita itama tayi alwala tayi sallah Usman baidawoba sai bayan isah koda yashigo yasamu hartayi barci saman abar sallah tada itah yayi yace takoma akan gado
Takoma takwanta sai lokacin yabude wayarsa yashiga wanka yanafitowa kiran labila yana shigowa yadauka da fara a tayi sallama ya amsa yace nasan tundazu kinyita kirah kikajita kashe
Tace wlh kuwa kunkai lafiya??? Yashafo Kansa Wanda yake jike daruwa yace qalau muka sauka aitundazu """ muka sauka mantawa nayi ban bude wayarba"""
Tace ayya ina sahiba""" yakai kallonsa wajen khadija wacce tasake juya kwanciya saboda jindadin iskanda yake kadata""" yasaki murmushi yace tayi barci ko atada itah..
Tace no barta tahuta nasan gajiyace kawai gobe kaafada mata nakirah yace shikenan harkinje kano??? Tace ah ganima kusa da hajiya tace tana gaidakai yace kibata mugaisa mana tace to""".
Sannan tamika mata"" takarba tareda sallama ya amsa hajiya inawuni tace lafiya qalau babangida"" ya khadijar yace qalau take harma tayi barciii
Tace ayya aidole Tasha hanya idan kuntashi kagaisheta "" yace zataji hajiya ina Abdul"" tace Abdul Dan Rigima aidarensa yayi yanacin abinci yayi barci""
Usman yace ainahuta kullum nazo saiyadameni anty labila hajiya tace aibakasaniba dayaganta shareta yayi waiyayi fushi saida tanuna masa sweet sannan yaje wajenta usman yayj dariya yace sarkin rigima ai hajiya kina fama" " tace toyazanyi tunda yanace saini aidole inyita hakuri kafin yasamu sabon jini kuma ni awatsani kwandon shara
Labila tasomayimata dariya sundade suna fira sannan yayi masu saida safe yashirya cikin kayan barcinsa masu taushi yahau gadon addua yayi masu sannan yakwanta yajawota jikinsa yakura mata ido kamar maitunanin wani abun daga bisani yasaki murmushi yasunbaceta saman kananun labbanta sannan yajata jikinsa barci maidadi yadaukeshi
Lubabatu tanaganin karfe Tara nadare yayi tayi shigar ta kamardai almajirah tahau motarta zuwa kasuwar nesa da kasuwar ta aje motarta tataka dakafa zuwa wajen tayi sa akuwa maidoyar tatashi dadan karenta taje Wanda zata tona koda akwai zafi wajen
Babu mutane wajen duk anwatse tawuce kamar tana Neman wani Abu daidai wajen mai doyar ta duke taduba babu mai kallontaa wajen kuma akwai ragowar wuta
Tajaye garwasun tayi gina tajefa layar tamiyarda toka tarufe tajawo gawayi maiwuta tazuba tamike"" takarkabe jikinta tawuce saida tayi nisa tatsaya taga kodawani bakowa awajen tasakai takoma wajenda ta aje motarta tashiga tatada mota tawuce gida ranta fariii tasss hankalinta kwance bayan tagama abunda zatayi takwanta""
Makale yake da itah kamar Wanda yaji ance za arabasu cen cikin barcinsa yaji kaamar dakinne yakecida wuta
Al amarinda yafaru da khadija. Kenan kusan tare suka farka kowanne yaja gefe sukahau kallon kallo"" Usman yamurza idonsa ahankali yasake kallonta yace waibakida lafiyane???
Tayimasa duban rashin fahimta tace mekaganie dad??? Yace jikinkine yayi zafi rau kamar wutaa hannu tasa tashafo jikinta bataji komaiba tace nima naji zafin Amman banyi tunanin jikina bane"" yace shikenan tashi yayi yasake kara gudun ac sannan yacemata sukwanta
Sake kwantawa tayi yasa hannu yajawota daniyar tamatso jikinsa zafin dayaji yanzu tamkar anwatsamasa ruwan tafasasshiyar dalmace hakan khadija ma tajiii Amman dukkaninsu gefe sukah koma suna jefar juna da kallo"""
Usman yadade zaune sannan yajuya nesa da itah yakwanta yana mamakin wannan suracin dayakeji yana fesowa jikin khadija haryanzu baidaina jin zafinba dolensa yamike babu shiri yakoma falo
Yanafita yajishi wasai yasaukarda ajiyar zuciya yana kwantawa saman kujera barci yayi awongaba dashi
Bayan fitarsa khadija tadago tabishi da kallo aranta tana mamakin wannan lamarin barcin ma saiya kauracewa idonta ganin kamar tunani zaidameta tamike tadauro alwala tatada sallah
Saida asuba tafita falon daga nesa tatsaya tatadashi sannan tajuya dakin bayan tagama sallah saman abar sallar barci yakwasheta bayan tagama azkar
Sauri takeyi danyau tadan makara bata tashi dawuriba"""bayan tagama hada kayan kokon tabawa yarta tace taje tadorah kafin tazo tace to sannan tadau itacen dakomai tawuce
Dayake banisa daga gidan zuwa kasuwar tanazuwa tazube kayan tashirya itacen tahurah wutaa"" tadorah dahuwar ruwanda za adama koko""
Usman yana kusa da khadija tanabarciii yakuramata ido yana nazarinta firgigit tatashi daga itah harshi kusan taresuka mike
Usman yarasa inda zaisa kansa dasauri yajuyaa yabar dakin Amman baiji sassauciba dole yafita gidan yanatafiya dasauriii
Saida yayi tafiya mainisa yadainajin komai ajikinsa bakin wata bishiya yazauna yadafe Kansa yanamaida numfashi
Bangaren khadija ma saida Usman yabargidan tadainajin zafiii ajikinta""" natsuwa tana dawomata tasoma furta innalillahi wa inna ilaihir rajiun
Harkusan azahar batasake ganin Usman ba"" shikuma yanacen dazaran yatunkaro gidan saiyajie kamar anasake huromasa zafii atakaicedai wani hotel Yakama nesa dagidanda khadija take
Harzuwa yanzu bakin Khadija baidaina addua ba"""
Al amarin mai doya kuwa tunda yarta tadorah koko hartasiyar Amman badukaba tadorah doya harkusan marece hajiyar jiya batazoba gashiyau tayi dayawa kumayau bakasuwa"" kawai saita saukartà tallen suya tajaye wutaa tadauko wuka tahau Gina kasa
Saida tayi Gina maidàñ zurfiii saiga layu sunyi jajirr sunata fesarda wutaa"" aikuwa tacirosu tawatsar tadibo ruwa jikinta yanarawà zaninta kamar zaifadiii tawatsawa layarnan sannan tacewa karamin danta yayiwa layar fitsarii
Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 87
By
Gentle Lady💃🏽
Mutane sunfara taruwa sunaganin ikon Allah matar tafashe dakuka tace haba nikam nace tunda naga yauba wani ciniki Nasan nasamu wani dan bakinciki wanda yake hassadata yakaini wajen boka😩
Kaibawa ana bakincikin agakana samu saiwani yayimaka munakisarda karasa komai adawo daya to aniyarku tabiku insha Allah babu abunda zaisameni
Wani dayake gefenta yace asabe lafiya??? Tace inafa lafiya malam mudi jiyajiya daga ganin masu mota sunfara hwakawa wajena anamun gosulo shine wani Dan banza irin tsiya yakaini wajen wani matsafiii tanuna masa layar tace tunda nadorah kokon safe naga yaunayi kwantai jikina yayi sanyi dama nasaba tona murhuna kafin nahasa wuta yauma tsautsayine ganin mun makara saina turo "" batula ashedai darabon inga wannan Bakar ranar to Allah yafiku inazaune lafiya daku Ashe akwai wadanda sukejin haushina nibanajin haushin kudinda kowa yakesamu Amman yan wadanda nakesamu inciyarda Yayana sune suka tsolemaku ido""
Mutumen yace kiyi hakuri bani ruwa ruwa tadibomasa yayi addua yawatsawa Layun saiga wani hayaki baki kirin yatashii sama"" nan take sailayun suka kama dawuta asabe tabuga salati tace kaganiko malam mudi wato so akayi talauciii yakashemu dani da yayana saitasake fashewa dakuka""
Saida layun suka kone kurmus tokar tabi iska "" malam mudi yace tayi hakuri komai ya war ware tayita masa godiya tace ainasan kaf kasuwarnan babu Maisona da arziki Saikai"" Allah yabar Kauna nagode yankasuwar sukaita mata jaje tace wlh inakallon kowa duk Wanda baizo yayimun jajeba shine tsohon munafukin"" ina kallace dakowa kai yinin ranardai akarasa gane kan"" asabe kowayayi mata yarmagana waccema batakai takawoba saitahayeshi da masifa
Hmmm bakutam bayeni meyasa har asabe tasan dakwai laya akasan madafin doyartaba"" asabe babbar macece kuma yarkasuwa maineman nakanta ammanfa akwai masifa batashiri dakowa idanhar ba sana arta akazo siyaba"" tanada wata Kawa jummala dukkansu mazansu sunmutu sunbarsu da marayun yayansu asabe yayanta shida biyar duk matane dayane kawai namiji karamie
Jummala Kuwa yayanta bakwai biyar mata biyu maza dayane mailafiyar dayakuwa bashida lafiya komai sai anyimasa ankwantar atayar sunkullah"" abota da asabe tunsuna yammata harsukai aure dasukafara sana a bayan rasuwar mazajensu shine sukezuwa saran doya wajen wata bayeraba
Idan sunsiyar sumiyarmata dakudi Sukarbi wata"" anahaka watarana dataje siyen doya maman cinedu take tambayarta wai ina jummala sati biyu batazo karban doyaba kuma bata kawomata kudintaba
Asabe tace jummalar??? Maman chinedu tace itafa tazo saubiyu takarbii doya bakudi gashi Nima inadau kotane Dan Allah kishemata takawomun kudina asabe tace Amman da mamaki nimadayake nadan kwana biyu bamuhadu da itah ba Amman bazatarike maki kudiba haka kurum baridai nabiya gidanta injiko lafiya sukai sallama damai doyar tadauki doya tatari Dan adaidaita tafadamasa unguwarda zaikaitaa
Bakin kofar gidan yasauketa tabashi kudinsa sannan tashiga gidan tanakwada sallama yayan jummala sunaganinta sukahau gaisheta dayake gidan ba bakonta bane"" tawuce uwardaka jummala tanaganinta tasaki fara a tace maman batulace yau agidanmu shigomana
Ta aje doyarta tashiga dakin suka gaisa takirah yarta zulai tace takawowa mamanta ruwa tace to bayan tadibo ruwan tabata tashaa"" tayi Hamdala tanakallonta tace dagawajen maidoya nake tace satinki biyu bakije daukan doyaba kuma baki kaimata kudintaba meyafaru jummala kinsanfa matarnan abunda takemana babuwanda zaimanashi kiituna bashifa takebamu kuma idanbamuda kudi tasake karamana
Nifa aganina kodan uwanka bazaiyimaka hakaba wannan zamanin da akeciki"" jummala tace hakane wlh asabe harkunyar zuwanake wajenta bansan yazance mataba kaddarorine idan sun tunkareka bakada maganie sai abunda Allah yayi
Asabe kinsaidai akofar gidana nake tuyar doyar nan wlh kullum saina siyar har ana nema watarana kuwa baifi natashi daguda biyuba saina bawa wani kare dayake zama kusa danie kusan kullum saiyazo idan yakwatanci nakusa tashi
Kinsan komai marayunda suke gabana dan Adam sai addua keni asabe naga takaina wai Ashe wannan cinikinda nakeyi wata tahademun yawu
Tana bakincikina Allah yarufamun asiri dani dayarana babu Wanda yajini akofar wani gidan ina yarmurya ataimakamun natashi nanemi nakaina Amman kuma anajin haushina
Kedai bar mahassada watarana nadorah tallen suyana harnagama wlh asabe ko kuda babu Wanda yazoma kusadani gashi nasoye doya Amman babuwanda yasiya ke ingajarce maki labari karenda nakebaiwa doya koshi bairabo inda nakeba inazaune natasa doya gaba inkalli gabas inkalli yamma inazaune hardare sauro yayita cizona harkarfe goma shadaya dole nakwashe kaya nakoma gida ganin kafa tadauke.
Tace kinga wajen nan tanunawa asabe dayatsa tace umm nagani inajinki jummala wlh harkinsa jikina yasaki tace hmm kedai bari wlh nan nadorah bokitin doya nayi zaune inata rusar kuka""
Yayana dasukaga haka suma sukaita kuka akarasa Wanda zai rarrashi wanie asabe doyarma kasa cinta mukai kafin safe ta Lalace dole nawanketa tacire kwan nashanya
Nasake komawa wajen maman chinedu nakarbo wata nabata hakuri"nace kudinne basu haduba dazaran nasiyar zanhadomata kudin nakawo mata tadauko doya tabanie
Nazo nasake daura talle wlh asabe abunda yafaru jiyan shiyakuma faruwa wannan karonkam banyi kukaba nabawa yarana doyar mukaci muka kwanta washe gari muka karya da itah sauran nashanya
Najikunyar komawa wajenta sainayi tunanin kodai sungaji da doyarne nazo nakwashi yan kayana dawadanda nafarayiwa zulai cikon aure najinginar dasu Na auno wake nayi awara ke dai bantsiraba danjarin yabalgace
Tsawon satii danaga yunwa tanashirin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 31