takutsa kai tareda sallama
Suna zaune dashi da rukayya sunacin naman kaji rukayya saizuba masa shagwaba takeyi shikuma kamar zaimaida itah ciki saboda soyayya""
Bakisake fateema take kallonsu Dan sallamarda tayima abakinta tamakale ganin yanda suke soyewa. Amman kullum rukayya cemata takeyi itakanta muhammad yadaina kwana da itah yadaina sake mata fuska "" wasu hawaye masu zafine suka sauko akan fuskarta
Muryar Muhammad taji yadaka mata tsawa kewacce irin jakace zaki shigomun daki cikin irin wannan yanayin kuma kiyimun tsaye akai
Fateema tagoge hawayenta taduka kanta nakasa tace kayi hakuri nakatsemaku jindadinku wlh banda lafiyane kwana biyu shine nakeso intambayeka gobe zanje inga likita
Yace bazakiba tashi kibacemun daganie"" takalleshi cikin mamaki tace Muhammad bafa wasa nake yiba katausayamun mana damezanji dawulakancin da kakemun koda ciwonda ke jikina???
Afusace yamike yace watoma ninakemaki wulakanci??? Lallai yarinyar nan kinsamu damar rainani dankawai inasake maki fuska tokarshen walakanci kije gidanku nasakeki saki biyu kimaza maza kifitarmun gida kafin nakirga goma
Kwatakwata neman hawayenta tayi tarasa saitayi murmushin takaici tace nagode Muhammad balaifinka bane Nice dalaifi da nanace saina aureka
Babuyanda Yayana baiyiba Amman nace saikai Amman kasani babu inda zanje sainayi idda
Kafinma tarufe bakinta yace agidan ubanwa zakiyi iddar
Tamike ahasale tace agidan uban Yayana kuma babu inda zanje sainayi idda"" yace wlh bazakiyi idda agidanaba ke kijema na iyarda sauran sakin sai inga inda zakiyi iddar tunda ba uwarkice tabani gidan ba
Fateema tace wlh karkasake zagarmun uwa yace idankuma nasakefa "" tace sai inrama ai uwarka bafin uwata tayiba kafin tarufe baki yadaga hannu zaimareta
Tarike hannun tace Karka sake wlh barganin kadakeni ada nakyaleka dajarar soyayyace dakuma aurenka dayake kaina yanzu Kuma babu kodaya danhaka bazanji takaicin ramawaba
Ta sake masa hannu tacije lebonta nakasa zanbarmaka gidanka Amman kasani bazantaba yafemakaba bantaba cutar kowaba nikuma duk Wanda yacutardani bazan yafeshiba wannan alkawarine tanakaiwa nan tawuce abunta Sam kuka yabacewa idonta
Zatafita yace dawo dawo ko kallonsa batayiba yafada dakinta yadauko muktar yana barcinsa yajawoshi kamar Wanda yadauko kayan wankii
Tana kiciniyar bude kofa yace wazakibarwà wannan shegen dannaki tajuyo afusace tace shegen ubansa aibadashi nazoba danhaka babu inda zanidashi inkaga dama kabarshi yamutu tafita dasauri tabanko kofa
Tanafita yajefo muktar waje yarufe kofar gidansa kukanda yakwantsane yasakata waigowa dagudu tadawo tarun gumeshi tahau rarrashinsa gabadaya unguwar tayi tsit kukan karnuka kawai kakeji yanatashi
Tashi tayi tagoye muktar abayanta dukda babu zanie tasoma tafita gabadaya tsoro yafita ranta tayi tafiya mainisa hartabar unguwarsu sosai haryanzu kowa batahadu dashiba "" muktar haryakoma barciii gashi tagaji dole tasamu wani wuri tarabe tacire dankwalin kwanta tashinfida takwantardà muktar tazauna saiyanzu tasamu damar yinkuka
Tasoma kuka maidan sautiii tsayin min tuna kamar ashirin taga anyadomata fitila maihaske hannu tasaka takare fuskarta tacigaba da kukanta
Ahankali mai fitilar yatako kusa da inda take yakashe fitilar yadan rage tsawo yana dubanta yace baiwar Allah mutum ko aljan???
Batareda takalleshiba tace inaruwanka karabudani"" kaje kayi abunda yake gabanka"" yanisa naji Amman amatsayinki Na mace mai rauni baidace inganki anan ba kuma inkyaleki nimafa inada Yaya kamarki bazanso nima Yayana susamu Kansu a irin wannan yanayinba inaso suma ataimakesu
Tace gawanda kebukatar taimako ko??? Toni bana bukatar taimakonka"" kabarni Dan Allah tasake fashewa da kuka""
Mutumen ya murmusa yace shikenan tunda bakyaso Amman bazan bar yaron nan wajen nan ba kinga gidana cen dasafe saikishiga maidakina tabakishi yayi maganar kawai yadauki muktar
Tabishi da kallo komotsi batayiba bayan tafiyar sada jimawa saigashi taredawa ta mata alamu sun nuna matarsace yace kinganta nan yayinuni da Fateema
Matar takaraso wajenta tace haba baiwar Allah kitaso mana kinkosan karfenawa yanzu??? Itakanta matar muryanta ta maibarcice dagaji mijinne yatasheta babu musu kuwa tamike tabi matar hargidan dakinda suka kwantarda muktar nan suka nunamata sukaimata saida safe
Itakuwa babu maganar barci a idonta harsafe bayan tayi sallah tana lazumie saiga matar tashigo dakayan kari tagaida itah sannan ta ajemata tace kisamu kici malam zaiyi magana dake tace to
Duk datasan bazata iyah cin komaiba"" tatashi muktar yayi alwala yayi sallah sannan tabashi abun kari yaci bayan haske yagama mamaye gari rana takunno kai saiga matar tasake dawowa wajenta tace kitaso yana kirah bamusu tamike tabi bayan matar""
Harwani daki tasameshi zaune saman buzunsa gatarin littafai nan agabansa dakuma allo da Qur ani tasamu gefe tazauna kanta yanakasa tagaidashi
Ya amsa cikin sakin fuska duk kunya takama fateema data tuno yanda sukaidashi jiyan yakatsemata shirunta yace yarinya hakika nalurah kamar kinacikin damuwa
Tunjiya la akarida yanda naganki dayaro acikin dare kuma cikin wannan muguwar shiyar'" inaso kisanardani abunda yafito dake daga gida
Shiru tayi nayan dakiku sannan tasanar dashi""komai yace wa iyazubillah Allah yakaremu dasharrin shaidan yata wannan mugun asirine akaimaki domin arabaki da mijinki
Gaban fateema yabada rasss dasauriii tadago kanta idanuwanta sunakawo kwalla tace asiri kuma baba??? Tomena tarewa wani dahar yakeso yashiga tsakanina da farincikina????
Yace yata abubuwa dayawa alabarinki kincemun matarsa bata taba haihuwaba??? Fateema tagyada kai yanisa kekuma gashi kinyi harbiyu ba mamaki itace dawan nan aikin
Fateema tayi shiru tana nazari ta tuna jiya dadare datasamesu dakinsa duk abunda akeyi rukayya kotado kanta batayiba saicin nama takeyi abuntaa fateema tashare hawaye tace bashakka idankuma hakane Anty tacutarda rayuwata tafashe dakuka
Saida matar malamin tasoma rarrashinta tanabata bakii
Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 72
By
Gentle Lady💃🏽
Tundaga muktar har khadija babu Wanda yaruntsa harsafe khadija takwana kuka kafin safe wani zazzafan zazzabine yakamata jikinta yagashe kamar wuta
Sallar asuba kanta dakyar tayi gashi jiya bataci abinciba"" dasafe inna takawo mata abun karinta tatasheta tace takoshi
Babuyanda inna batayiba Amman takici dataga zatadameta tace zataci inna tanafita tasake gyara kwanciya"" tana nan kwance har azahar muktar baishigo dakinba
Inna tasake kawo abincin rana tasamu nasafen bataciba"" ta ajemata tafita dakin muktar tayi saita sameshi zaifito kenan yana ganinta yadansaki ransa yagaida itah
Ta amsa tace idan zaka iyah rarrashin sarkin zuciyar cen kaje wlh yaukoruwa batasha ba rabonta da abinci tunjiya dasafe babu yanda banyi da itah dasafe ba tanuna masa kaga karinta nasafe yanzu danakai narana nadaukoshi
Yayi shiru sannan yace shikenan yajuya zuwa dakinta koda yaturah kofa idonta rufe yake yataka harbakin gadon yazauna yakuramata ido
Yasan tasan shine dangashinan idanuwanta sunsoma zubarda kwalla duk da arufe suke" sunanta yakirah bata amsaba"" baidamuba yace kitashi kici abinci
Nandinma banza taimasa yaturah hannunsa daniyar yatasarda itah mugun zafinda yaji shiyasa yacire hannunsa dasauri batareda yayi niyaba
Cikin tashin hankali yace khadija bakida lafiya Daman??? Meyasa baki sanardaniba duk arude yake maganar dasauri yafita yacewa innah kishirya ta yanzu zandawo da doctor yadubata yafita dasauri yana dauko waya cikin aljihunsa
Abokinsa Abubakar yakirah yasanardashi yana kano yanzu haka yanason ganinsa "" yace toyasameshi gida danyanzu Hutu yake yace toganinan tafe
Yanagama wayar yatari Dan adaidaita zuwa gidan sa bayan yakirasa yace yakaraso saiyafito motarsa sukashiga zuwa gidan
Yashiga yasanarda innah zaishigoda doctor tace to saida yashiga yasamu khadija kwance yagirgiza kansa sannan yafita"""
Yashigoda Abubakar din yagaida innah sanan sukashiga dakin "" yataba jikinta dazafi sosai sannan ya aunata"" haryagama abunda yakeyi muktar yana kallonsa
Yatashi tsaye yana kallon muktar yace me akaimata halan??? Muktar yace mefa akaimata doctor mekedamunta??? Yanisa yawan tunanine yahaifar mata da damuwa gakuma kirjinta yanazafii
Tunyaushe rabonta da abinci?? Jiki asanyaye yace jiya" yace mujeto asiyomata magani dole aimata allurar barci domin tasamu barci ko damuwar zataragu
Yace tomuje yayi maganar yana kallon khadijar taresukaje dashi akasiyo maganin da allurar yabiya sukaje inda masu fura damun injin yasiyamata suka wuce gida
Dakyar yasamu tasha furar sanann akaimata allurah takwanta yanunamasa yanda zatasha maganin idan tafarka yayimasa godiya yarakashi bakin motarsa sundade suna firah sannan yatafi hankalin muktar duk yana wajen khadija
Kodayakoma yasamu tayi barci kusa da itah yazauna yabuga tagumie yana kallonta"" wasu hawayene suka saukomasa yasadan yatsansa yataresu
Yana nan har akayi la asar yatafi masallaci yadawo yazauna ba itah tafarkaba saigoshin magrib yataimaka mata tawatsa ruwa tayi sallah taci abinci tasha maganie takoma takwanta
Sallamar labila sukajiyo tsakar gidan tagaida innah sannan tafada dakin tanakiran sahib bata rufe bakiba sukai ido hudu da muktar yasake tsuke fuskar nan
Itama saita dauke kanta tace inawuni bai amsaba itama batadamuba saman gadon tahau tace meyasameki sahiba???
Khadija saman kafarta tahau saitafashe dakuka nantake labila tafara kukan tace me akaimaki sahiba??? dan Allah kiyi shiru
Muktar yanazaune yanakallon ikon Allah"" innace taji kukan yayi yawa tashigo tozakufara sana ar takuba kuyiwa Allah kuyishiru
Kojinta basuyiba itama tsaye tayi tasaki baki kamardai yanda muktar yayi tsayin mintuna goma khadija tayi shiru saikuma takoma rarrashin labila sahiba kiyi shiru kinji kar zazzabi yakamaki
Saida tagama rarrashinta sannan tace inayan tafiya??? Da murmushi tayi maganar labila tace tunjiya naso inkawomaki da dare harzanfito sainaji raina abace nakoma daki nayita kuka jiya wlh banruntsaba zazzabi yarufeni
Yanzun Karin ruwama akaciremun tanunawa khadija hannunta tace inatashi nacewa hajiya kinzo tacemun ah ah shine nataso ingako lafiya
Khadija tasaki wani kayatacceñ murmushi tana kallon labila tace sahiba lafiyata qalau Nima rashin ganinkine yahaifarmuñ da damuwa Amman yanzu tunda naganki Alhamdulillah
Tace nima wlh sainaji nawarke taresuka sakarwa juna murmushii"" muktar yamike jin ansoma kiran sallah yafita baicedasu komaiba
Aransa yana tunanin wannan wace irin soyayya ce sukewa junansu aidole khadija tace tanason baban labila Kuma batai laifiba Amman anya nizan iyah barinta ta aureshi??? Nifa tsoron matan yanzu nakeyi dawan nan tunanin yatafi masallaci
Inna ma fita tayi domin tayi sallah suma sukayo alwala sukai sallah anan suka zauna sunata labari yawancin firarsu duk akan karatunsune na islamiyya har innah tagama abincin dare sukaci gabadayansu sunware tamkar basuyi ciwoba""
Muktar yadawo yasamesu suna tafirah yadade bakin kofar yana saurarensu basu ganshiba dan hankalinsu baya nan juyawa yayi yabar kofar dakin
Saikusan karfe Tara labila tayi gida saida sahiba tarakata sannan tadawo tanashigowa gidan tasha toka zuwa dakinta batajima dazamaba
Saiga muktar saman gadon yazauna yana kallonta yace sapna kenan wannan fushin duk ni akeyiwa ko??? Gashi kinware tunda kinga kawarki Amman tana tafiya kinkoma kina fushi
Dadago da sirarun hawayenta tace Yayana ciwona azuciyata yake bawai afuskaba nayi kokarin boye damuwa tane saboda labila muddin tasan inacikin damuwa zata matsane saina sanarda itah menene damuwata dakuma silar damuwar
Idanhar nasanarda itah Kaine kake fushidani wlh bazata sake kallonka da mutunciba"" ninasan labila batunyauba danhaka nake boye damuwata duk lokacinda muke tare
Yanisa yanzu khadija ninake fushidake??? Kodai kece kike fushidani"" hawayenda suke kan fuskarta suka karasa saukowa yace please nifa bakuka nace kiyimunba "" tace Yayana taya zanyi mushidakai Kaine ubana kuma Kaine uwata
Kasharemun hawayenda uwayena ne yakamata su shafemun banida wani babban farinciki aduniya Wanda yawuce inga nafaranta maka rai
Yayi murmushi khadija kenan aiyanzu banada wannan kimar tunda har nahanaki soyayya Amman kikayi dama bayada mata dadan sauki Amman khadija mai matafa kuma harya manyanta
Gyara zama tayi tana fuskantarsa tace Yayana duk da bansan dalilinka nafurta hakanba nasan kasan wannan baharamun bane
Shimai mata baza a aureshiba tosabodame??? Koshidin bamutum bane??? Kasani mata sun linka maza sosai idankowanne namiji mata daya zai aurah sauran matan kumafa wazai auresu???
Yayana idan kai aure nan gaba kana bukatar kari kaima saiwacce kakeso tace batasonka tunda kaima kanada mata"" shinzaka saki uwar yayankane saboda kanason Karin aure???
Idan kasaketa ka auri waccen kasake ra ayin karawani aurenfa??? Aganina mai mata bashida wata illarda za ace aurensa bazai yiyuba sai idan ansan shidin ba nagartaccen mutum bane tanisa banyimaka wannan maganarba waidan kabarni Na auri dadyn labila
Tundahar bakasonsa wlh nahakurah dashi zansanarda labila kayimun wani mijin kokuma inbika cen kagama bangantaba ballantana inji damuwa Amman Yayana nasan kanada dalilin fadin haka
Dan Allah kasanardani meye dalilinka
Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
chapter 71
By
Gentle Lady💃🏽
Wayar taketa kallo tana murmushi"" saiga kirah yasoma shigowa cikin kira ar sudes tuni khadija talunshe idonta saboda jindadin karatun tanabinsa ahankali harkiran yakatse
akasake kirah saiyanzu tabude idonta tadauko wayar saitaga ansa hubbina takwalalo ido tace hubbina kuma batasan harta dauki wayarba tanacewa hubbina sai asaitin kunnensa saitaji yace Na am
Wata irin kunya takamata kamar tanitse cikin kasa muryarsa taji yace khadija menaji kinkirani dashi yanzu???
Duk tabi ta daburce tace dad sorry wlh banice nasakashi awayarba sahibace tasaka namanta sainakirah Ashe harnadauka kaji dakyar takeyin naganar kamar wacce akasaka dole
Murmushi yadanyi maisauti yace nikuwa naji dadi danaji kinkirani hakan"" hannu tasaka tarufe fuakarta tace kayi hakuri yace aibalaifi kikayiba khadija
Tace harka kaine saikuma tarufe bakinta da alamu batasan sanda maganar tafitoba"" yace ah konadawo ne bakigaji da ganinaba??? Tace sai anjima dad
Dariya yayi maidan sautiii yace kunya kikejine??? Kamar yana ganinta tanoke fuska tareda daga kanta yace isowata kenan harzan soma aiki nacebari nafarajin muryarki"" murmushi tayi tace tokayi aikinka lafiya dad "mungode batajirah mezaiceba taka she wayar"" yabi wayar dakallo yayi murmushi
Khadija sunagama wayar wani farincikine yalullubeta marar misaltuwa tadade tanajin soyyarsa cikin ranta Allah yakaddara shine mijinta
Kullum Usman saiyakirah khadija Amman baitaba kiranta idan haryana kusa da lubabatu Sam batasan meyake faruwaba tsayin sati daya sannan yakoma kano yasanarda malam garba khadija ta amince..
Yace shikenan yabashi kwana biyu zaikirah muktar yasanardashi komai yace saiya fadamashi"" hakan kuwa akayi bayan kwana biyu yakirah muktar.
Tana fara ringing yadauka tareda sallama malam garba ya amsa muktar yace kawu inawuni yace lafiya kalau ya karatu
Muktar yace karatu Alhandulillah"" yace to Allah yabada sa a yabada abunda akaje nema yace ameeen muktar yace kawu ina sapna??? Yace kaima kasan tana islamiyya ni nadawo gidane indan watsaruwa saboda zafie
Muktar yace kagaidamun inna " yace tana amsawa" daganan saikuma shiru yabiyo baya muktar takawarda shi run yace kawu ko akwai maganane???
Yanisa ah kam muktar akwai magana mai mahimmanci akan khadija shine dalilinda yasakama nakiraka"" jinya ambaci khadija yasaka yasaka muktar yabar abunda yakeyi yatattara hankalinsa duka yana saurarenshi
Yace inajinka Allah yasadai lafiya yace qalaune insha Allah yayidan jinkiri sannan yace watarana ina kasuwa saiga mahaifin Kawar khadija labila kaganeta aiko???
Cikin kosawa yajimeyafaru yace ah nagane" yacigaba yazone akan batun khadijar daganan yakwashe abunda sukai dashi yafadamsa haryanda sukai da khadija tace ta amince
Yana rufe bakinsa muktar yamike tsaye yace ai wannan zancen banzane kawu nawa khadija take dahartasan wata Abu wai soyayya bazata aureshiba!!!
Kawu yace dakata muktar baikamata kahana yarinyar nan cika alkawarinda tadaukarwa kawartaba"" tace daina maganar wani alkwari kawu kawai kacemasa auren nan bazai yiyuba yayanta yace bayaso
Idankuma bazaku iyah sanardashiba nimai iyah fadamasane haba kwata kwata nawa khadijar take 18years fa" Kuma tarasa wazataso sai Wanda yakeda mata !! Never
Malam garba yanisa yace tonidai bansan yazanyi makaba Amman gaskiya zak asani jinkunyar bawan Allah nan tundaga kano yataso
Muktar yace Allah yasa daga saudiya yazo kawu ban yarda Kanwata ta auri mai mataba!! Malam yace to Allah yakyauta sai anjima
Yakashe wayar yanakallon innah yace Dama hakan nayiwagudu shiyasa nacemasa yabari saina sanarda yayanta
Kinji yanda yaceko??? Innah tace lallashinsa zakayi ai saiyayi hakuri Amman magana tagaskiya yarinyar nan tanasonsa "" ninalurah dahakan tunkafin yace yanasonta
Malam yayi shiru yana nazari cenyanisa yace to tundashi yakeda kanwarsa yace bayaso ahakurah mana nibanaso inyi karambani inajin tsoron maimaita tarihi duk da banada laifi
Innah tace to Allah yazaba mana abunda yafi zama aikhairi malam ya amsa da Ameen bangaren muktar kuwa sunagama wayar yakasa zama jikinsa harwani ciccirah yakeyi anyama zai iyah sake kwana a kasar nan karfa yanacen kawu yayiwa khadija aure
Kuma wai baban labila mai mata ai bazaitaba yiyuwaba "" dasauri yasoma hada kayanshi sai filin jirgi
Koda jirginsu yasauka takwas nadare masallaci yafara zuwa yafara ramakon salloli sannan yatari Dan adaidaita zuwa gida
Suna tsakar gida sunacin abinci dayake yanayin zafine saman babbar tabar marnan suke saidai sukaji sallamar sa dagasama
Malam garba yadago da mamaki yana kallonsa lallai abun yayi tsamari suka amsa masa sallama yaduka yagaidasu baiko kalli gunda khadija takeba yatashi yakoma bangaren dakunansu"" yashige dakinsa
Tuni murnar dakuma farincikin fuskarta yagushe takalli innah kamar zatayi kuka mikewa tayi zuwa dakin dasauri da sallama tashiga
Yana kwance saman gado yakurawa silin dakin ido ahankali tataka indayake taduka muryanta tana rawa tace yaya halan bakaganniba???
Atsawace yatashi zaune yace naganki sapna mekikeso inyimaki???? Take hawaye suka jikamata fuska tace wani laifin nayimaka Yayana???
Yadallah mata harara yace kebakisan ma abunda kikaiba tunyaushe nake Jan kunnenki akan karkisake kiyi soyayya??
Asheni bansaniba ihunake bayan hari" nawakike khadija dahar zakice waikinason wani kuma bama saurayiba maimata??? Kinsan sarai natsani mai mata bazantaba bari ki auri mai mataba kodakuwa mazan duniya sunkare
Tanaduke hawaye sunabin kumatunta batacemasa komaiba haryakai karshe cikin sanyin murya tace Yayana baban sahiba tane fa baikamata kajerah shi cikin sahun marasa nagartar mazajeba
Yadaga mata hannu rufemun baki nalurah kedin bakida hankali tokisani gobe gobe dake zankoma sainaga karyar rashin kunya kuma shima zankirashi inji dalilinsa duk matan dasuke kasarnan yarasa wazai ce yanaso ya aurah saike zatayi magana yace kiyimun shiru tashi kibar nan banason ganinki
Cikin muryar kuka tace nidin ya muktar??? Cikin tsawa yace kifita nace tsawarda yayimata cikin wata murya wacce itah kanta batasanshi da itaba
Dasauri tamike tarufe bakinta saboda kuka dagudu tafita tafada dakinta saman gado takwanta tasoma kuka maicinrai meyasa nabata maka rai meyasa??? Danasan hakan zaikona makarai bazantaba bari son dad yashiga zuciyataba
Su inna sai kallo kallo suke sukalli kofa sukalli juna"" sunsan koda sunshiga dakin muktar bazaitaba saurarensuba"" Dan idan yahau dokin zuciya bamai saukardashi
Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
chapter 73
By
Gentle Lady💃🏽
Yayi shiru daga bisani yace khadija tace na am Yayana " yace kinsan bazanso abunda zai cutardake bako??? Tagyada kanta yanisa tundakike bakisan labarin mahaifiyar muba
Babu Wanda tasanar mawa kisani bayanni kinada wani yayan"" dasauri tadago tace Yaya kuma a ina?? Yanisa mu uku mahaifiyar mu tahaifa
Nima naji wannan ne lokacinda zamubar garin mahaifinmu tanasanarda wani malami alokacin ban fuskanci labarin sosaiba bayan nagirma nasake komawa yola
Da mamaki takalleshi duk da inayaro banwani sha wahalar gane gidansaba Amman da tambaya da yake malamine sainayi dace tunda nasan unguwar awajen gwaggo hasana na tambaya
Nasameshi yatsufa sosai baima ganeniba saida nayimasa bayani yanisa kwana na daya agarin hargidan mahaifinnawa natafi Amman baigane niba
Naso sosai nasan inda Dan uwana yake duk Wanda natambaya saiyace babu faruq agidan malamin shine yasanardani labarinda mahaifiyarmu tasanar dashi
Yanisa anan yakwashe komai yafada mata"" duk irin wahalarda tasha dayanda malamin yacemasa asirine akai mata komai baiboye mataba
Yanakai karshen labarin khadija tafasheda kuka baiyi kokarin hanataba saida tayi mai isarta dankanta tashare hawayenta
Yace wannan dalilinne yasaka banaso ki auri maimata Dan bazanso kema hakan tafaru dakeba"" khadija tadago jajayen idanunta takalleshi tace nagane Yayana Amman inaso kasani babu Wanda zaiwuce kaddararsa
Kataba tunanin za ahaifeni???? Duk da kiyayyarda mahaifinmu yakeyiwa mamana dayake akwai rabon saina shigo duniya gashi anhaifeni
Ya muktar kaddarata rubutacciyace bakada ikon sauyata inhar Allah yarubuto nima zansha wahala babu makawa hanawarka bazai kareni dakomaiba""
Kataba tunanin zan iya auren marar matar dagabaya yasake aurowata wacce zatayi nasanin fitana gidan??? Shifa Allah ba aimasa wayo baka isah ka karkare abunda yake arubuceba tunfil azal
Baikamata kayiwa kowacce mace kallon hakaba Dan idanharkayi tonima wani mai irin hangenka dawannan zai kalleni
Kasani ba arasa nakwarai acikin al ummah komai lalacewar zamani zakasamu akwai nagartattuñ mutane acikinsu
Tanisa abunda kawai yakamata kayi kace Allah yakare maka kanwarka daga fadawa hannun irin wadan nan azzaluman matan"" kuma kabawa kanwarka makami wato ilimin Islam Wanda kowayake takama dashi
Dashi zata iyah kare kanta Allah yashiga tsakaninta damiyagun mutane kumani bana zargin mom wlh baruwanta halinsu daya da labila
Idanhar tanada wani mugun hali da awajen yarta zamugani Dan duk Wanda yatsotsi nono bazai yarba kamar yanda naji anafada
Nikuwa nace wannan zancen burr ne inji tusa saunawa uwa take haihuwar Yaya Amman babu Wanda yagadota wani lokacin maishegen fada saita haifi salihar yarinya
Wani lokacin saliha saita haifi masifaffiya danhaka masucewa waisu bazasu auri yayan masifaffuba bawai halin uwar zaku dubaba nayar dankowa da halinsa
Muktar yanisa yana kallon agogon hannunsa yace dare yayi kikwanta kihuta"" kai tagyadamasa tace nagode kaima kasamu kakwanta nasan jiya bakai barciba
Murmushi yasaki maidan sautii yace ya akai kikasan banyi barciba??? Itama murmushin tayi tace gashinan inagani a idanuwanka
Yamike yadauko mata maganinta yace aikece kikajamun kinfita kina kuka badole hankalina yatashiba""" tace ayimun afuwa duk laifin nan dai nawane baice komaiba yabata maganin tasha yayi mata saida safe yakoma dakinsa yadade yaana nazarin maganganunta kafin yayi alwala yana sanarda Allah yazabawa kanwarsa abunda yafizama alkhairi arayuwarta
Washe gari dasafe yana dakinta zaune suna firah saiga wayarta tasoma ringing jikinta yasoma rawa dantasan shine jiya silent tasaka wayar bayan fitar muktar tadauko wajen miss call ashirin tayi mamaki sosai"" saitacireta silent saiyanzu gashi yakirah
Tanakallon wayar tana kallon yayanta yalurah da itah saiyashare yace wayar waye take ringing tsuru tayi alamun rashin gaskiya tace dama dama wayar sahibace tamanta da itah
Dakagan yanda take magana. Kasan batada gaskiya yayi murmushi yace tokidauka kice batakusa dawayar mana"" tadan sosa kanta tace ah ah kawai barta idan yagaji zaidaina kirah kowaye
Wayar hartakatse akasake kirah muktar yamika hannu yadauko wayar yaduba hubbina yaga anrubuta yadaga ido yakalleta saita done kanta yace kinganima inaganin kamar saurayintane yake kirah
Shirudai tayi batace komaiba hartakusa katsewa yadauka tareda sallama dayan bangaren aka amsa "" yace barka dasafiya yace yauwa Dan Allah Khadija nake nema
Muktar yadaga kai sukasake yin ido hudu tasosa kanta kamar wacce zatayi kuka"" yace togata nan tafe yakashe wayar baiko kalletaba yafita rike dawayar
Jikin khadija Yakama rawa tace yaunabani mekuma yakawoshi yanxu??? Saileken kofa takeyi""
Muktar da murmushi kwance afuskarsa yakarasa wajenda Usman yake tundaga nesa yaga matukar kamarda sukeyi da labila kuma tamkarma bai isah haihuwartaba""
Shima yana ganinsa yasaki fara a kafin yakawo inda yake haryasameshi yabashiy hannu suka gaisa "" daganan suka karasa kusa da motarsa
Suka sake gaisawa yace yan america saukar yaushe bayan malam yacemun bakanan"" sosai Usman yayiwa muktar kwarjini a ido Sam yakasa daga idonsa sama yakalleshi""
Yace shekaranjiya nazo"" yace toya hanya inafatar dai lafiya?? Yace ah lafiya kawune yakirani yasanardani sakonka
Usman yatari nunfashinsa yace Allah yasadai yayan namu ya amince"??? Wata kunyace ta sake kama muktar yace ah gaskiya lokacinda naji Sam banyi Na am ba dalilinda yasaka nataso aranar kenan
Nazone daniyar natafi da itah dankawai nace banyardaba saiyarinya tazubemun balafiya jiyama saida tasha allurah Usman yace subhanalillahi yayanmu meyasa zakaimana haka
Muktar yace dad inada nawa dalilin saboda nayi alkawarin Kanwata bazata auri Wanda yakeda mataba saboda shine silar dayasa mukarasa mahaifiyar mu yanisa
Amman sapna tayimun gamsasshen bayani kuma nayarda dahakan yanzu danaganka yasake nisawa yadago yakalli Usman kamar zaiyi kuka yace wlh inason Kanwata sosai itace kawai take debemun kewar mahaifiyarmu
Banaso tashiga tashin hankali da matsatsin rayuwa" yasanne kansa nidama banda natauyemata hakkinta bazantaba bari tayi aureba
Danba zanso wani yacutarda itaba"" Usman yamurmusa yadafa kafadarsa yace nagane abunda kakenufi kuma nagamsu nayimaka alkawarin babu abunda zaisameta inasonta sosai bawai son wasaba dasanina kaima kasan bazantaba bari wani yacutarda itah ba
Muktar yanisa shikenan Allah yazaba mana abunda yafizama alkhairi usman yace Ameen"" muktar yace bari nakiramaka itah
Yayi maganar yanashirin juyawa Usman yasake basa hannu suka gaisa sannan yawuce aransa yanacewa ashedai baban labila haka yake bashida girman kai""
Usman kanshi yaga saukin kan muktar"" yanashiga gidan innah tace wai inakaje naga khadija sai tsautsauniya take"" murmushi yayi yace innah dadyn labila ne yazo"" yayi maganar yana shiga dakin yace kishirya yana jiranki ya ajemata wayar akan dago harzaifita tace Yayana tsayawa yayi batareda yajiyoba tace nidai banason fita bakafadamashi gobe zamutafi dakaiba
Adarare takeyin maganar yajuyo dafuskarsa wajenta dauke da murmushi yace inazanje dake kiyitamun kuka ainalurah soyayyarku hartayi nisako
Tace wlh ah ah ya muktar yace hakane shiyasa naga kinyi serving din numbersa da hubbina
Kafin tace wlh banice nasaba yace karkibata masa lokaci yanajiranki Amman karkidade yawuce abunsa"" murmushi tayi mayafinta kawai tadauko tasaka tasa talkamanta tafito tana leke waiko zataga ya muktar innakuwa sai dariya takemata
Tafito dasauri tafita"" tunda yahangota yasoma aikomata dawani kyakkyawan murmushi Wanda itakanta bazata iyah daukarsaba akarancin shekarunta jitayima kamar kafafuwanta suna hardemata tuni tasanne kanta kasa
Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 74
By
Gentle Lady💃🏽
Ahankali tataka harzuwa wajenda yake tsaye shikuwa haryanzu baidauke idonsa daga kantaba tafiyarta tamkar dawisu natsuwarta kalamanta komai natadai yana matukar burgeshi
Ko amafarki baitaba tunanin wai zaitaba soyayya dawataba saigashi kwatsam ya afka kogin so kuma yayi nitso tayanda baxai iyah fitaba
Da tsadadden murmushinta Wanda yake matukar dimautarda Usman tayi sallama dakyar ya tattaro sauran natsuwarsa wajen amsa mata sallamarta
Tace inawuni dad"" yadan gyara tsayuwa sanann yace lafiya qalau mom" dasauri tadago takalleshi batareda tayi maganaba"" yadaga mata gira yace yes indai bazaki kirani Usman ba nikuma mom zandinga kiranki dashi
Bakinta tadafe 🙊Dan Allah dad karufamun asiri dawanne bakin zankiraka aikuwa danayi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 31