Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Faruk ya ce, ai haka ake so ka ga yanzu sai ka rike ta da kyau ka nuna mata garanci wanda ba ta samu ba a baya. Haidar ya ce, "Allah dai ya ba ni lafiya amin in ji Faruk yayin da ya zuba musu abincin a filet din da ta zubo suka ci sosai dan shi kansa Faruk ya yaba da dadin girkin nata. Can kuwa Bilki ta mike don tafiya gida, "To ni zan tafi jawahir sai dai gobe zan zo da wuri na raka ki mu sake dubo shi. Jawahir ta hangame baki ta ce, "Don kin ji Faruk ya fada ba kya tsoron mu je a yi mana wani sabon wulakancin da ya fi na yau.? Bilkisu ta ce, "Insha Allahu hakan ba za ta faru ba gwanda ki je, kada su samu kafar raba ki da mijinki ga shi kuma yanzu kuna son juna. Jawahir ta ce, "Shi kenan Allah ya kai mu goben na gode Bilki da kaunar da kike min, da ba ni shawarwari masu kyau da kike yi, Allah ya kara mana dankon zumunci a tsakaninmu amin. Da haka suka yi sallama ta tafi. Jawahir ta shiga dakinta ta kwanta tana tunanin abin da ya faru yau da ita. Faruk ya fita ya yi sallar insha Haidar ya kalli Kausar ya ce ke ba za ki yi sallar ba ne na ga ko magariba ba kiyiba? Ta ce, "A'a ina ruwanka a yin sallah ta ka ga malam kawai ka ji da abin da ya dame ka. Faruk ya turo kofar ya shigo Kausar ta zuba masa harara tare da jan tsaki ta mike ta bar dakin. Faruk ya taimakawa Haidar ya yi Sallah, Haidar ya daga hannu sama ya dade yana addu'a sannan ya shafa ya xuba tagumi. Faruk ya cire hannun tagumin ya ce, "Haba malam menene kuma? Ka yi hakuri a kan larurae da ta same ka, ka yarda da kaddara ko? Haidar ya ce, wallahi ba wannan ne ya dame ni ba halin da jawahir rake ciki nake tunani kada fa ta Gudu gidan Inna ta kuma boye ta ka san ranta ya ba ci dazu da abin da Yagwalgwal ta yi mata. Faruk ya ce, "Ba na jin za ta fita har gida na kai ta kuma na babbata hakuri ka san yarinyar akwai biyayya" To don Allah ka je ka taho min da ita ta kwana a wajena ka ga gidan ba kowa sai masu aiki. "Faruk ya ce, "Ka yi hakuri da safe ai za ta zo ka ga yanzu dare ya yi yanxu haka ma ta kwanta. Haidar ya ce, "Haba Faruk don Allah ka taimaka min ka je ka taho min da jawahir yanzu duk girman gidan nan ta kwana ita kadai sai masu aiki? Faruk ya ce, "Shikenan bari na je amma sai na biya na dau Hafsa don ita ma ta zo ganin likita." Haidar ya ce, "Ko dai ta harbu ne.? Faruk ya yi murmushi ya ce, "To ga mu dai ga Allah don mun sa rai. Ya fita yana dariya ya biya ya dauki matarsa Hafsa suka tafi. Ya ce, Ya ku ka yi da likitan? Ta ce, "Gwaje gwaje ya yi min ya kuma dauki fitsarina ya ce da safe a zo a karbi result din. Faruk ya ce, "To Allah ya taimaka mana ya sa abin da muke nema ne, ta ce Amin. Suka yi wa juna murmushi. Suka yi fakin a harabar gidan Hafsa ce a gaba don ita take buga kofar falon nasu da yake kulle. Jawahir da take takure a falo don zuciyarta cike take da tsoro da fargaba ka sancewar ta ita kadai a sashen ta yi tunanin ko ta kirawo 'yan aikin Kausar su taya ta kwana sai kuma ta fasa, to jin bugun sai ya dada tsoratar da ita. A tsorace ta je gaban kofar cikin rawar murya ta ce, "Wanene?" Faruk ya ce, "Bude mu ne, ta kalli agogo karfe tara gabanta ya fadi, Allah ya sa dai lafiya? Ta bude kofar ta ba su hanya suka shigo Faruk ya ce, "Sarkin tsoro da kin zata barayi ne suka zo sa ce ki?" Ta yi dariya ta kamo hannun Hafsa ta ce, "Wai yaushe rabon ki da gidan nan? Ko da yake ban sani ba ko kina zuwa wajen amaryarku Kausar, "Hafsa ta yi dariya ta ce, Ni ina zan zo gidan nan mutuniyata ba ta nan ta gudu ta bar min abokin miji ya zamo abin tausayi a gari?" Ga ba daya suka yi dariya. Faruk ya ce, "Kar dai a gaji da mu dan mun kuma zuwa da kokon bararmu da karin ban hakuri megida ya ce, a zo a tafi dake don Allah ki kwana a wajensa. Ta yi shiru can ta ce gaskiya ni ba zan je wajensa na kwana ba. Faruk ya ce, "Subhanallahi, kin san hukuncin matar da mijinta ya yi kiranta ta ki zuwa kuwa? Ko kina so ki hadu da fushin ubangiji ne? Jawahir ta ce, "Gaskiya Yaya faruk ba zan je ba, ba Kausar tana can ba? Ai ita ta saba kwanciya da shi ni in na je ina da abin da zan yi masa ne? Faruk ya ce, "Haba jawahir kada ki yi haka mana da iliminki da komai ki yi hakuri ki amsa kiran mijinki mana. Ta ce, "Haba yaya Faruk har ka manta irin zaman da na yi da yaya Haidar a gidan nan ni bani da hakki a kansa sai shi yanzu yake da hakki a kaina har zai neme ni?" Ta sa kuka ta mike tayi daki, "Wallahi ba inda zan je". Ta turo kofar dakinta ta kulle. Hafsa ta ce, "Gaskiya fa ni fa ban ga laifin jawahir ba, don gaskiya an zalinceta" Faruk ya dakawa Hafsa tsawa tare da cewa, "Yi min shiru ana neman sasanta magana kina dada tunzurata. Ya jawo wayarsa ya yi danne-danne. Haidar ya dauka, "Hello" Yauwa Haidar ka kwantar da hankalinka kayi hakuri mun zo mun tarar jawahir tayi bacci amma don Allah kada ka tsayar da hankalinka da safe kafin na tafi office zan biya na dauko maka ita. Haidar kafin ya ce, wani abu tuni Faruk ya katse wayar ya kuma kasheta gaba daya don ya san halin Haidar ba kyale shi zai yi ba. Haidar kuwa tun daga lokacin wata zuffa ta rinka tsiyayo masa, hankalinsa ya yi mummunan tashi, jikinsa sai rawar sanyi yake yi. Ba jimawa zazzabi mai zafi ya rufe shi. Nan da nan jiki ya rikice a ranar da sai Abbansa ne da yaya Abba suka kwana a wajensa. Ba shi da wata magana sai ta ambaton an bar jawahir ita kadai a gidan nan sai masu aiki kada wani abu ya samar masa ita. Yaya Abba ne yake dan karfafa masa gwiwa yana tunasarsa. Yawan ambaton jawahir da Haidar yake yi ya sa Kausar ta yi fushi ta baro asibitin ta dawo gida. Jiyya ta koma hannun yaya Abba da Faruk, amma asibitin kullum cike yake da yan uwa da abokan arziki sai dai rashin matansa a wajen. Duk da haka Yagwalgwal ba ta fasa yada habaici da kananan maganganu ba don haka Anti ba ta son yawan zuwa don ita take yiwa habaicin. Kamar ita ta haifa mata Haidar din Yau kwanan Haidar hudu kenan a asibiti suna zaune a dakin jinyar, Faruk da yaya Abba Haidar ya ce da su, Faruk da yaya Abba ku fara hada kaya ku karbo min takardar sallama." Yaya Abba ya ce, Ah sabo da me? Cikin raunanniyar murya Haidar ya ce, "To kun ki zuwa ku rarraso min jawahir ta zo gareni na ganta ko hankalina ya kwanta. Tun da haka ne gwanda na koma gidan na yi jinyata a can inda zan samu kulawarta. Shi dai yaya Abba ba ya son jawahir ta zo wajen nan ko don sabo da kananan maganganun da Yagwalgwal take yi, don haka ya yi shiru bai ce komai ba. Haidar kawai ya fara hada kaya Faruk ya tausaya masa, ya ce, "Bari Haidar yi hakuri bari na je yanzu na shawo kanta insha Allahu za ta zo. Jawahir tana zaune tana bitar karatun Alkur'ani wayarta ta yi kara. Ta tsagaita da karatun ta dauka, "Hello wa ke magana? Faruk ya ce, "Ni ne daman na bugo na gaya miki Haidar yana cikin dayan biyu ko mutuwa ko rayuwa, don ya rikice an rasa gane kansa sai kiran sunanki kawai yake yi" Jawahir ta gigice, "Na shiga uku yaya faruk yanzu ina yayan yake? "Yana can asibiti a rikice." "Wayyo yaya faruk! Don Allah ka kwantar masa da hankali yanzu zan zo." Ya ce, "Ina harabar gidanku ina jiranki ki fito da hanzari. Kafin ya rufe bakinsa ya ganta ta fito da wayar kange a kunnenta. Ya bude mata bayan motar ta fada, shi kuma ya shiga gaba ya tuka suka yi gaba. Yana tsayar da motar jawahir ta bude ta fito a guje ta shiga dakin da yake tana danna kai ta tarar da shi a gado yana ta faman ihu. "Wayyo Allah! Ya dafe cikinsa yana ta juyi." Ga shi dakin sai shi kadai ba kowa, nan da nan hankalin jawahir ya tashi, tausayinsa ya kama ta sai kawai hawaye taji yana zubowa daga idannuwanta ta zauna a gefen gadon ta dago kansa ta dora a cinyarta tana rike da shi sai sannan take yi masa, gani take da tana da ikon cire ciwon nan ta dawo da shi jikinta da ta yi domin kawai ya huta a abin da yake damunsa. "Sannu yaya na kirawo likita ya ba ka magani. Wayyo yaya cikinka ne yake ciwo? Yaya ko ina ciwon yake yi? Sannu yaya, bari na hada maka tea ka sha ko? Ko za ka iya cin abincin? Don Allah yaya ka tashi. A hankali nishi ya lafa sai kadan kadan daga can ya yi shiru ciwon ya tafi kenan. Jawahir ta rankwafa kansa, "Sannu yaya". Ya lalubi hannunta ya danke a nasa cikin magana sanyi- sanyi irin wanda yake jin jiki ya ce, "Yaushe kika zo? Ta ce, "Ban dade da zuwa ba. Ina yaya Abban ya tafi ya barka kai kadai?" "Yanzu nan kafin ciwon ya tashi ya tafi gida amma yanzu zai dawo."Ta ce "Amma dai bai kamata su rinka barin ka kai kadai ba kana cikin wannan hali." "To ya zan yi jawahir ke ma da kike 'yar uwata matata kin guje ni kin ki jiyyata waye zai jura?" Jawahir ta ce, "Ka yi hakuri yaya ba wai na ki zama a wajenka bane ka san halin Yagwalgwal kar ta zo tana tsinka na a asibiti shi ya sa. Haidar ya ce, "To shi kenan ba komai zan nemi likita ya ba ni sallama sai mu koma gida na yi jinyar a can ko?" Ta ce, "Haba yaya gwanda ka zauna a nan din ka ga sun fi kulawa." To jawahir ai ba zan juri rashin ganinki ba gwanda dai na koma gidan." Daidai nan likita ya shigo ya dubi Haidar ya ce, yanxu ina ganin za mu sallameka ka koma gida tun da Abbanka ya ce kasar waje zai futa da kai. Don haka ga takardar sallama. Jawahir ta ce, "To likita yawan ciwon cikin da yake fa? Likitan ya ce ba komai wannan mun bashi magunguna sai dai a dinga kula wajen ba shi ya sha." Anan yaya Abba ya shigo ya kalli jawahir ya ce wato sai yau kika ga damar xuwa wajen mijinki ko? Kina sane da ba shi da lafiya yana kwance a asibiti amma ba za ki zauna kusa da shi ba, don taimaka ma sa ba ko.? Jawahir cikin biyayya jawahir ta ce, "Kayi hakuri yaya insha Allahu ba zan sake ba, "Faruk ya shigo suka kwashi kaya da Haidar suka yi gidansa. Dakinsa suka wuce da shi suna budewa kamshi ya bige su ko ina a gyare fes kamar yana nan. Jawahir ta hado musu abubuwan ci da na sha suka ci suka sha suka yi kat, sannan suka yi musu sallama tare da kara yi musu addu'ar samun sauki. Jawahir ta shige tolet dinsa ta hada masa ruwan wanka a baho ta zuba turaren wanka a cikin ruwan nan da nan turirin kamshi ya rinka tashi. Ta fito daga tolet din ta durkusa Yaya ga ruwan wanka can na hada maka, ya ce yauwa Babyna na gode. Ya mike ya shige tolet dinshi kansa kamshin da tolet din yake yi dabanne. Yana shiga cikin ruwan ya ji wani dadin ni'ima ya ratsa shi ya fara wankan. Jawahir kuwa ta fito masa da wasu kananan kaya, wando je three Quarter (tiri kwata) da rigar 50 Cent marar hannu ta kara feshe su da turare. Ta debo masa mayukan da zai yi amfani da su da turarukan. Ta ja masa kofar dakin ta sauka zuwa kasa nata dakin. A lokacin kuma Kausar ta dawo ko daga ina take oho ita ta sani. Jawahir ta shiga wanka ta fito ta gyara jikinta sai zuba kamshi take yi kamar wadda aka yi barin turare a jikinta. Riga da wando ta saka da hula mai harafin sunanta. Fuskar nan tata sai sheki take yi, jikinta sumul-sumul gwanin sha'awa kirjinta ya cika fam, da na shanu. Ta bude kofar ta fito Haidar yana kwance a doguwar kujera da karamin kur'ani a hannunsa yana karatu. Kausar tana kujera me zaman mutum daya tana zaune da jarida a hannunta tana dubawa, kamshin da suka ji ne ya sa su saurin dago kai Kausar ta saki tsaki ta mai da kanta ga karatunta. Jawahir ta wuce kicin ta dauko kofin gilas me kyau ta bude firji ta dauko robar ruwa ta Highland ta iso gaban kuherar da Haidar yake kwance ta zauna a kasa kan kafet ta balle bakin robar ruwan ta tsiyayo ta fiffito da magungunan ta mika masa, "Yaya ga magungunan. Ya dan mike zaune ya karbi magungunan ta watsa bakinsa ta kafa masa kofin a baki ya sha ruwan ya ce ta dan danna masa kafafuwansa don ciwo suke yi masa. Ta mike sannu a hankali ta rinka mamnatsa masa tana yi masa tausa. Jin dadin tausar da ya jine ya sa shi fadin wash, wash a hankali tare da lumshe ido. Ita kuwa Allah sarki sai ce masa take yi sannu sannu yaya cikin alamun ban tausayi, shi kuwa taushin fatar hannunta mai kama da atafa shi yake neman dimautar da shi, har yana neman sa shi ya fita daga hayyacinsa, ba dan yana gudun kada girma ya fadi ba ai da ya rungumota. A ka kwankwasa kofar falon jawahir ta kalli Haidar da yake kwance yana lumshe ido don jin dadin tausa ta ce, "Yaya na je na bude kofar.? Kai kawai ya iya daga mata don maganar ta ki fita kanta bude kofar ta ja da baya don ganin Yagwalgwal ce. Jawahir ta durkusa kasa ta gaishe ta, ta ce "Munafuka ba zan amsa gaisuwar taki ba, me kike jira a gidan da baki tafi ba tun da kiyayyar da kike yi masa har ta kai ki sabauta masa lafiyarsa ai za ki iya kashe shi ma, don haka ni gaskiya ban yarda da wannan auren naku ba ka sake ta kawai na gaya maka ba na son gayyar tsiya gayyar jarabawa. Jawahir ta fashe da kuka ta kalli Haidar ta ce, wallahi ba don na riga na yi wa Dadyna alkawarin ba zan kuma fita daga gidan nan ba, ba tare da izininka ba wallahi yau da na bar zaman gidanka. Ta durkusa a gabansa tana kuka, "Yaya don Allah don Annabi yaya ka taimake ni ka sake ni ko ni ma na samu sukuni a zuciyata. Haidar ya sunkuya ya dago jawahir ya hada ta da kirjinsa ya rungumeta yana shafa bayanta alamar rarrashi, ransa a bace zuciyarsa ta yi bakikkirin sai fat-fat take yi kamar ta fasa kirjinsa ta fito waje. Ya kalli Yagwalgwal ya ce, "Yagwalgwal ina ganin girmanki kada ki bari kimarki ta zube a idona, jawahir 'yar uwata ce ko ba aure a tsakaninmu ni me rike ta ne ballantana matata ta sunna ki rika aibata ta a gabana, ai aurena da jawahir mutu ka raba takalmin kaza. Yagwalgwal ta kama salati tana tafa hannu, "Yanzu dan nan ni kake gayawa haka a kan wannan mai kama da sadakar yallan kake neman zagina, to bari na je wajen uban naka in kai ban isa da kai ba ai shi ba zai ki jin maganata ba, tun da ni na haifeshi ko. Jawahir ta zame jikinta daga jikin Haidar ta nufi dakinta tana kuka ta rufe kofarta. Haidar ya kamo hannun Yagwalgwal ya ce, "Yi hakuri matar ta karfen na san du kishi ne yake dawainiya da ke, Ta doke hannunsa ni sake ni me kuma za ka gaya min bayan ka gama yi min rashin kunya. Ya dada kamo hannunta yi hakuri zo mu je sama dakina na gaya miki komai don ki ji yanda abin yake. Da kyar ya shawo kanta suka hau samansa suka zauna a falonsa, duk wannan abin da ake yi Kausar tana zaune a kujerar da take tana kallonsu kawai ba tare da ta tofa komai ba. Haidar ya ce da Yagwalgwal "Wallahi yarinyar nan jawahir tana da mutukar hakuri ga ladabi da biyayya ga sanin ya kamata da hangen nesa, tana aiki da ilimin da Ubangiji ya ba ta, idan aka ce za a yi ta tafiya a yanda a ke yi yanzu, to hakika hakurin jawahir zai iya kai ni wuta." Yagwalgwal ta ce, "Dakata! Don na ce ka rabu da ita kake kawo min wannan bayanin, ka je kada ka sake ta ran da ta kashe ka ai ma zo mu dauki gawarka ko? Haidar ya ce, "Dole dai sai na fasa miki tarihinmu za ki yarda da zancena. Haidar ya faro mata irin tsanar da ya yi wa jawahir tun daga farko da yanda har a ka yi auren da irin zaman da suka yi da dalilin da ya sa jawahir barin gidansa har kawo yau. Yagwalgwal ta saka salati tana cewa, "Ashe ni balokokon vanza nake yi kai ne marar gaskiya? To wallahi ka kula ka rike 'yar uwarka da kyau don tana yi maka son gaskiya. Da haka dai suka yi sallama ya debo kudi me yawa ya bata ta yi masa godiya tare da sa masa albarka ta ce kuma za ta zo ta bawa jawahir hakuri idan ta wuce. Haidar ya juyo daga rakiyar Yagwalgwal ya murda kofar dakin jawahir ya shiga, kamshin dadi ne suka buge shi ya sheka ya karasa cikin dakin. Tana zaune a gefen gadonta hada kai da gwiwa tana shasshekar kuka, ya zauna a gefen gadon ya dago ta ya kara ta da jikinsa ya rungume ta, "Subhanallahi wannan jiki haka mai taushi da dadin kamshi kamar atufa, Ubangiji ka nuna min ranar da zan mallaki komai na yarinyar nan da na nuna mata tsantsar soyayya da kaunar da ba a taba nunawa wata 'ya mace ba. Duk zancen nan a zuciyarsa yake yi wanda har ya so ya shagala cikin tunanin kyan kirar jawahir. Sautin kukanta ne ya dawo da shi hayyacinsa. Cikin taushin murya da magana kasa-kasa kamar mai rada yake rarrashinta yana dan bubbuga bayanta, "Sorry Babyna yi shiru haka kada kanki ya zo yana ciwo kin ji baby na yi hakuri, ta dada shagwabewa tare da langabewa a jikinsa tana kuka kasa-kasa cikin sigar kissa da shagwaba kukan nata me shiga rai da tsayawa masoyi a zuciya. Tuni kirjin Haidar ya fara bugawa fat fat, "Subhanallahi ya salam wai yaushe zan mallaki wannan tsantaararren jikin mai kama da robar balo-balo? Muryarta ya tsinkaya cikin rauni da taushi da dadin murya tana cewa, "Yaya ka sake ni na koma gida tun da kakarka ba ta son na zauna da kai." Haidar ya ce, "A' uxubillahi kada na kuma jin kin furta wannan kalmar kin ji ko, don ubangiji yana tsinewa duk matar da ta nemi mijinta da ya sake ta, kada bacin rai ya sa ki rinka jawowa kanki fadawa cikin fushin ubangiji kin ji ko? Yi saurin yin istigifari." A hankali ta bude baki ta rinka nanata istigifari, ya ce, "Yauwa Babyna Yagwalgwal ta ce a ba ki hakuri. Zumbur ta mike ta shiga tolet don ba ta son maganar don ita a zatonta tanda Yagwalgwal take tsanarta da nuna mata kiyayya ba za ta taba son ta ba. Haidar kuwa binta ya yi da kallo komai nata sha awa yake ba shi komai na jikinta burge shi ya ke yi, wai shi ya zai yi da wannan zazzafar kaunar da yake yi wa jawahir ne? Ta yaya zai yi ya shawo kanta su kwanta gado daya ne da shi? Duk dai da tanxu ba shi da karfin gaban da zai tabuka mata wani abu to amma ko wasanni da sun yi shi da ya ji ta kwance kan kirjinsa yana wasa da wadannan tantsa-tantsan na shanun nata(nono). Duk dai da shi ya yi wasa da damar da ya samu tun farko. Ya dade a zaune yana zaman jira shiru-shiru jawahir ba ta fito ba dole ya mike ya fita, tana jin fitarsa ta fito ta sawa kofarta mukulli. . Abu wasa-wasa jawahir ta kwana ta wuni ba tare da ta fito Haidar ya ganta ba ko ta yi saken kofarta a bude ya shigo. Sai dai wani abin mamaki da safe za ta hada masa lafiyayyen break a kicin din wajenta sai ta leko falon ta ga ba kowa sannan ta jere masa kayan break din ta kuma ajiye masa maganin da zai sha na lokacin da robar ruwan Highland ta koma bangarenta ta kulle kofarta, sai dai in Haidar ya gama shirnsa ya sauko kasa ya hau tebir ya yi break ya dauki magani ya sha ya jira ko jawahir za ta bude ya ji shiru ya taba kofarta ya ji ta a kulle. A lokacin ya juya ya koma sama sannan ya tashi 'yar mulkin tasa wato kausar sarkin 'yan hutu, to wani abin mamakin duk da yau kusan a falo ya wuni amma be ga jawahir ta fito ba bare ya kalli idonta ya ga yanda ta kwana. Sai da ya ji an yi kiran sallar azahar ya daura alwalla ya fita masallaci amma kafin ya dawo jawahir ta fito ta jere masa kayan abinci, tuwon farar shinkafa ya tuku ya yi mulmul da shi da miyar agushi, wadda don dahuwa kazar da take ciki duk ta narke ta dagargaje a ciki. Ta gasa masa naman rago mai ruwa ruwa ya sha kayan kamshi ga tumatir da albasa kai dai kamshi yake tashi. Sai lemon aya da ta hadawa kanta ta zuba masa a jek ta cilla kankara ya sha kayan kamshi, ta jere komai cikin kayatattun fulas masu kyau ta sa farin kyalle mai dauke da falawoyi a jiki ta rufe ta yi saurin juyawa ta koma dakinta ta rufe sashenta ta shiga kicin dinta duk ta gyara kayan data bata, ta wanke komai ta goge ta mai da shi inda yake, sannan ta shige tolet dinta ta saki shaya a kanta ta fara wanka. Karfe biyu da rabi Haidar ya shigo gidan da carbi a hannunsa, "Yan matan kausar ya ga daya a bakin kofar falon tana gadin falon ta yi masa sannu da zuwa ya wuce. Ya shiga falon ya taba kofar jawahir a bame kamar yanda ta kwana. Ya girgiza kansa kawai, shi jin kansa ya hana shi kwankwasawa ya nufi bangaren kausar tana zaune a kan kujera 'yan matanta biyu suna gefenta daya tana yanka mata tufa a kan filet dayar kuma tana zuba mata abinci a daya filet din, wanda ya kasa banbancewa da kuskus ne ko burabusko. Yanda ya gan shi a dundunkule ya sha ruwa ya yi sharkaf. Ya zauna gefen ta 'yan matan suka yi saurin nikewa suka yi waje. Kausar ta dauki filet din abincinta za ta fara ci ta kalle shi ta ce, "Bismillah." Ya ce, "Wa! Ni? Allah ya sauwake na ci wannan abincin, ai sai na yi amai." Ta tabe baki ta ce, "Au kai fa ba ka cin abincin masu aiki ko? Ka sa kanka a wahala don yau na ga abin da za ka ci tun da na ga Sarauniyar taka fushi take yi bare ta zo ta girka maka. Wai ni kuwa yau ka yi break? Don ban ji motsinta ba bare na ji ko ta girka maka Ya ce, "Ke za a tambaya ba tare muka kwana ba, tsakanin ke da ita wa ya kamata ya yimin girki? Ta tabe baki, "Ka san ni ban tashi a cikin wahala ba don haka ba zan iya wani aikin komai ba. Da kake maganar da ni ka kwana ai tausaya maka na yi nake taya ka kwanciya don kada ka kwana kai kadai, me kake iya tabuka min? Ka riga ka zama nakasasshe, in ban da ka ishe ni da tabe-tabe ka tayar min da hankali babu biyan bukata." Ya daka mata tsawa tare da nuna ta da dan yatsa, ke saurara kada ki sake ki kawo min maganar banza a nan, da haka nake? Ko don lalura ta same ni za ki gaya min maganar banza, daure ki na yi ko cewa na yi dole ki zauna idan kin gaji ba dole, ba zan danne miki hakki ba ga hanya nan sai ki san inda dare ya yi miki. A ranta ta ce, "Ba inda zan je gwarzon namiji kamar ka ina zan iya barin ka, idan na yi sake ka subuce min ta yaya zan yi na mayar da kamar ka bare yanda na dandani zumarka ai sai dai na ga ba ka samu lafiya ba tukunna zan ki zama da kai. Ya gama banbamin fadansa ya fice yana tunanin tsananin hakurin jawahir da kawaicinta. Ya ji sallamar Hafsan faruk ya amsa mata cikin fara'a yau ina megidan naki na gan ki ke kadai? Wallahi yana office ka san bai taso ba, yanxu ma gidan yini zan je ya ce na fara biyo wa na ga jikin naka. Haidar ya ce, "Jiki Alhamdullahi." Ta zauna a falon suka gaisa ta ce, "Ina matan gidan ne? Ya ce, "Bari na kirawo miki su. Ya kwankwasa kofar jawahir ya ce, "Ki fito kin yi bakuwa, Hafsa ce ta zo. Ya juya ya nufi dakin kausar ya ce ki zo kun yi bakuwa, "Tace, "Wacece?" Ya ce, "In kin zo kya gani, "Ya juya ya fita. Jawahir ta bude falonta ta fito cikin dammamiyar riga body hook da jeans din wando da ya dame mata cinyoyi daga kasa kuma yake da fadi, kanta ba dankwali sai kananan kalba da ta tufka ta a bayanta ta kwanto guda biyar gaba. Ta yi kyau sai zuba kamshi take yi ta taho da dan gudunta ta fada jikin Hafsa tana dariya. Haidar kuwa ya zuba mata ido kallon ta yake yi yana hadiyar yawu, yarinyar nan kuwa ta san yanda take rikitar masa da hankali? Ta san yanda kirjin nan nata yake dauke masa hankali kuwa? Kausar ta shigo tana yatsina kujerar da Haidar yake kai ta nufa ta zauna masa kan cinya

Chapter 8 of 13