Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sun yi kyau kamar 'ya 'yan turawa. Gaba daya yaran suna kan Haidar suna ta tsalle tsallensu a jikinsa, wayar ku sa da jawahir ta yi kara ta daga ta kara a kunnenta, "Hello yauwa Anty jawahir wallahi wata bakuwa ce tazo ta kafe lallai tana son ganinki. Jawahir ta ce "Okey ba damuwa kawo ta muna falon sama Ta dire wayar, bakuwar da tun shigowarta ta saki baki tana ta kalle kalle a cikin gidan babu abin da ya fi kayatar da ita irin tsantsara tsantsaran falon da suka rinka wuce su, jikinta bai kara yin sanyi ba, sai da suka shiga wani tsantsareren falo wanda ya hadu da kayan kyale kyale sai wata hadaddiyar matattatakalar bene wadda aka yi ta kamar da ruwan gwal. Kasan matattakalar shimfide yake da kafet, suka hau suka yi sallama falon suka shiga. Jawahir ta dago kai tare da amsa sallamar ta zuba wa matar ido, tana tunanin ina ta santa. Matar ta zube a gabansu tana kuka Haidar kuwa yana ta wasa da 'ya 'yansa be ma dago kai ba bare yasan wacece. Jawahir ta ce a'a baiwar Allah me kuma yake faruwa daga zuwa sai kuka ba tare da kin yi wani bayani ba." Ta kwanto yan kwananniyar'yarta daga baya wadda shimi ce kawai a jikinta saboda rashin sutura matar kuma atamfa da take jikinta duk ta kode ta jeme ga hadin baki a jiki matar ta ce "Ban yi mamakin yanda baku gane ni ba ni ce Kausar. Jawahir ta yi zumbur ta mike tana rike da baki cikin mamaki ta ce "Kausar ke ce rayuwa ta maida ki haka me ya faru dake Kausar ina iyayenki da mijinki.?" Kausar ta goge hawayenta ta shiga basu labarin iyayenta da halin da take ci, ta juya tana kuka tana rokon Haidar gafara Haidar ya ce "Ni wallahi ba komai don rabuwa da ke alheri ya zamar min don da ina tare da ke da ban sami zaman lafiya da kwanciyyar hankali haka ba." Ya mike goye da Salma ya dauki Salim da Sadat a kafadarsa ya shige ciki. Kausar ta bisu da kallo tana me sha'awarsu shi da 'ya 'yansa da matarsa da ta yi hakuri da yanzu itama tana cikin wannan daular. Jawahir ta girgiza kai zuciyarta cike da tausayin halin da ta ga Kausar. Lallai duniya zancan banza ce kana takama kai wani ne lokaci daya sai Ubangiji ya mayar da kai ba komai ba. Jawahir ta ce Kausar "Ki yi hakuri lamarin duniya kenan don haka ba a son daukan duniya da zafi. Ta mike ta shiga daki ta debo sababbin riguna kala takwas da turamen atamfofi kala hudu da dinkakku kwance kala shida, da kudi naira dubu hamsin ta kawo mata ungo wa'yannan kije ki yi amfani da su zan kuma sa abinciko min koda lambar wayar iyayen naki ne kin ji ko." Kausar ta rissina ta rinka godiya tana kukan murna. Jawahir sai da ta sa aka hada mata kayan abinci fal bayan but din mota tasa direba ya kaita har gida. Kausar tana komawa ta sai rishonta ta sai kananzir galan guda ta kai dakinta take girkinta ita kadai ita da mijinta suna ci ta daina kula abincin gidan Nan fa matan gidan da 'ya'yan gidan suka tusa ta agaba da habaici da bakaken maganganu ita dai bata kula kowa sai ta rinka kulle wajenta ma ta daina sauraronsu. Sati biyu a tsakani jawahir ta ba wa direbanta waya sabuwa da kudi dubu goma a ciki da lambar wayar iyayen Kausar ta ce ya kai wa Kausar. Direba ya kama hanya ya kai wa Kausar ta rinka murna tana kwarara wa direba godiya ta ce ya mika mata godiya wajen jawahir din kafin tazo. Direba yana tafiya, Kausar ta kulle dakinta ta buga wayar bugu uku ana hudu aka dauka. Muryar babanta ta ji ta fashe da kuka, "Dady, Dady nice Kausar kun gudu kum barni cikin halin kunci da wahala. Tana kuka tana gaya masa halin da ta ke ciki da ita da mijinta tace yanzu mijinta bashi da komai suna cikin kuncin rayuwa hatta lokacin da ta haihu bai yi mata komai ba, da yunwar da ta sha da bautar girkin da take yiwa matan gidan da irin tsangwama da cin mutuncin da ake yi mata har kawo irin taimakon da jawahir take yi mata da binkicen da jawahir ta yi ta samo mata lambarsu ta kawo mata sabuwar waya da kati na dubu goma a ciki duk ta gama gaya masa. Hankalin babanta ya tashi ransa ya damu ya ce mata kiyi hakuri da man kwanan nan muke son mu zo mu duba ki ganin mun shekara daya da baro Nigeria. Amma kisa idonmu a cikin satin nan muna tafe." Hankalin babarta da 'yan uwarta ya yi masifar tashi da jin halin da Kausar ta ke ciki, ai basu iya hakuri ba kwanakin ba cikin kwana uku suka dira a Nigeria. Iyayenta da 'yan uwanta har kuka suka yi jin halin da Kausar ta shiga, nan fa aka shiga bata kashi tsakanin Bomboy da iyayen Kausar da kyar suka samu ya sake ta. Bayan ya sake ta ne, ya shiga daki yai ta kuka har da ihu shi ya shiga uku. Yanzu yaya za ayi ya kuma wani auren?" Da kyar su Amal Junior da Jauhar M. Nas suka rarrasheshi. Suka zo suka ta yiwa jawahir godiya tare da sa mata albarka. Suka roki kuma Haidar gafara a bisa abin da Kausar ta yi masa ya ce "Ba komai ai ya yafe mata. Nan fa kyakkyawar alaka da zumunci ya kullu tsakanin jawahir da Kausar da kuma iyayensu. Satinsu uku a Nigeria suka daga da Kausar da 'yarta da iyayenta zuwa America. Cikin lokaci kankani Kausar ta murmure ta murje ita da 'yarta ssuka shiga shafe shafen da ya bayyanar masu da kyansu. Bata dade da gama idda ba manema suka fito mata in da ta sake auren wani mai mata daya da 'ya'ya uku. Ya riki kausar da 'yarta cikin gaskiya da amana in da suke zaman lafiya da abokiyar zamanta. Haidar da jawahir linkafa ta ci gaba sun zamo abin kwatance da sha awa a Nigeria suna da 'ya'ya biyar kenan 'yan uku Salma, Sadat, Salim sai Nana khadija da Mohammad auta. Rayuwarsu me burgewa da ban sha awa kowa ya shiga gidan baya son fita don ganin irin rantsattsiyar SALON SO, ya yarda suke shimfidawa a gidan. KASH DAMA ANCE LAIFIN DADI KAREWA. DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA UBANGIJI DA YA BANI DAMAR KAMMALA KAWO WANNAN LITTAFI KAMAR YADDA MUKA FARA. TSIRA DA AMINCI SU KARA TABBATA GA SHUGABA ANNABIN RAHMA (S.A.W), ALAYEN SA DA SAHABBAN SA. DA FATAN MUN KARU DA DARUSSAN DA MUKA GANI A CIKIN WANGA LITTAFI, ALLAH YASA MUYI KOYI DA MASU KYAWAWAN HALAYEN DAKE CIKIN SA YA KUMA TSARE MU DAGA AIKATA MUNANAN AYYUKA MAKAMANTAN NA WASU DA MUKA JI A CIKI. TOHHH!!! INA FATAN NIMA XAKU TAYA NI ADDU'AN SAMUN WATA MATAR TUNDA MAFARKI NA TA SUBUCE MIN WATO KAUSAR. SAI MUN HADE A WANI SABON LITTAFIN INSHA ALLAH.. MU NA GODIYA KWARAI GA MARUBUCIYAR LITTAFIN WATO, _*HADEEZA SALISU SHAREEF*_ SAI NI DA NA KAWO MU KU, _*SULAIMAN BOMBOY_* NA KE MU KU, WASSALAM. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 13 of 13