Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kowanne yanayi da kowanne lokaci. Abu na bakwai gwana ce wajen iya tsafta da gyaran gida tun daga dakunnansu falukansu zuwa kicin bandaki harabar gida ko'ina da launin turaren da take kamshinsa da yake yi Abu na takwas ta riga ta gano makamar kama Haidar domin ta fuskanci abin da ya fi so a jikinta wata kirjinta, don haka koda yaushe ta kasance cikin gyara kirjinta tare da sake kaya masu fito mata da surar kirjinta. Abu na tara ta iya tarairayarsa tana ba shi kyakkyawar kulawa ta siye zuciyarsa da kyawawan halayenta, abu na goma na karshe kuma, ta san sirrinkan kwanciya yanda duk yanda ya juyata haka take binsa kowanne kokaci kuma akwai sabon samfarin da zata gudanar masa a makwancinsa. Ba ta gajiya da shi tana dauriya da jure bukatarsa har sai ya gamsu don kanshi ba ta da korafi bare ta nuna gajiyarta, ko ta ce ya fiye fitina Wa'yannan halaye su ne suka ingiza kaunar jawahir take dada ruruwa a zuciyar Haidar. Kwance tashi wajen Ubangiji babu wuya, ga shi cikin jawahir ya shiga wata tara komai na haihuwa sun tanada sai jiran haihuwar kawai suke yi. Wata sabuwar sangarta jawahir take yiwa Haidar saboda ganin yanda take bata tsantsar kulawa. Cikin nata ya yi nauyi duk da haka ba ta yi sakaci da girkin megidan nata ba, bata sakaci duk yanda Haidar ya kai da lallaminta da lallabata baya son yaga tana wani aikin wahala don haka duk safiya yake shiga kicin ya hada musu break. Ya taimaka ma ta ta yi wanka shi yake yi mata kwalliya, ya sa mata kayan da ya san baza su yi mata nauyi a jiki ba, ya rungumo ta zuwa falo kan kafet ya zauna tana rungume a jikinsa yana bata break a baki, sai daki ya kwantar da ita a gado kamar wata jaririy yana yi mata tausa da matsa sannu a hankali sai ya ga ta yi bacci sannan zai shirya ya tafi office. Sha biyu na rana jawahir ta tashi daga bacci sannu a hankali ta mike ta nufi kicin ta fara hada abubuwan da zata dora girki, duk wani yanke yanke da dake dake ko markade a bulanda me take yi mata. Ita kuma tana kula da girkinta da kuma hada lemummukan da ta san mijinta yafi so da sha'awar shi. Karfe biyu taje ta yi salan wayar Haidar ta sake shigowa bugowarsa ta hudu kenan bayan tashinta daga bacci. Ta dauko "Hello Honey, na baka gajiya da yo waya ko"? . SALON SO PART 40 . . Bebyna ya za ayi na gaji da jin muryarki hasken zuciyarta tare da jin lafiyarsu ita da bebyna. Ta yi shashshekar dariya cikin kissa da jan hankali ta makale murya tare da lankwasar da murya ta yi masa magana cikin yanga da marairaita. "Honey na ka kwantar da hankalinka kalau muke ni da bebynka, sai dai muna kewar dumin jikinka na dan lokaci." "Okey, beby na kada ki damu karfe hudu zan dawo gida mu kasance tare zuwa wayewar gari ko beby na?" Ta ce "Um hum thank you Honey na, sai ka dawo muna jiranka. Ya sumbaci wayar ya huro mata isa ta cikin wayar, ta shashshekar dariya da ta saukar wa da Haidar matsananciyar kasala yayi saurin ajiye wayar tare da jan diguwar ajiyar zuciya. Jawahir ta mike ta koma kicin ta debo fulas fulas dinta ta malmala tuwon farar shinkafarta da ya tuku ya yi luku luku da shi, kowanne ta malmala sai ta sa alaida sannan ta jera acikin fulas din. Ta juyo hadaddiyar miyar wake da ganye wadda ta dahu da hanta da koda da manja sai dan man kuli kadan lallai jawahir kin iya hada abin da zai kara muku jini da lafiya. Ta juye farfesun kifi irin ragon ruwan nan ta zai zuba kamshi yake yi, ta bude oben ta zaro gasashen naman ta da ya ji tumatir da albasa gashi yayi ruwa ruwa sai zuba kamshin kayan kamshi yake yi. Ta hada lemon kwakwa da madara sannan ta hada lemon abarba. Kowanne ta zuba a jug ta cilla kankara ta rufe ta kwashe kayan taje ta jere su a kasa yanda suke yi yanzu saboda girman cikinta. Iya ce ta gyara mata kicin din da duk wajen da ya baci. Jawahir ta shiga toilet ta tsalo wanka tare da tsala kwalliya ta shafe shafe da hadaddun kamshi na tururuka daban daban, simpil doguwar riga ta saka me rubi biyu sai walwalin dutsunan jiki ne suke ta zuba sheki. Ta dora sirrin mayafin akanta, ta futo falo ta zauna akan kafet ta mimmike kafafuwanta ta wara su yayin da ta jawo rumote ta latsa TV ta kama, ita kuma ta jingina da kujera tana kallo. Haidar ya turo kofar tare da sallamar tasa, ya yi saurin karasowa in da take ya zube a gabanta, ya tarairayo ta jikinsa "beby na" ya shafa mararta ya ku ke ya beby na yana dawo na same ku beby na komai lafiya ko?" Cikin murmushi take daga kai tana amsa masa tare da shafar sumarsa ta kansa. "Sannu beby na zauna anan kada ki tashi na hau sama na watso ruwa na zo mu fita muje mu ci abinci ko, ta daga kai. Ya mike ya yi sama da sauri ya fada toilet be jima ba ya fito ya shirya cikin kananan kayansa ya sakko, ta mike ta taro shi ya rungume ta a barin damansa "Muje restaurant mu ci abinci ko.?" Ta langabe a jikinsa "Haba my love da raina da lafiyata na kasa yi maka girki har sai ka fita waje ka ci? Honey na na yi mana girki." Ya rike baki "Bebyna bana hana ki wahalar da kanki ba? Daidai sanda suka zauna gaban kayan abincin yana bubbudawa, ta ce "Wallahi Honey na ba na son naga ka ci girkin waje ko na wani wajen, shi yasa nake daurewa na yi maka da kaina." "San kyau bebyna, na gode Allah ya yi miki albarka, ya raba ku da cikin nan lafiya" Amin Honey na gode." Suna cin abinci Haidar yana zuba santi, jawahir tana kyalkyala masa dariya. Da haka suka gama Haidar ne ya kwashe kayan, ya dawo ya same ta ta kwanta kan kafet ya durkusa kanta yana yi mata tausa sannu sannu yake matsa mata jikinta tare da mulmula mata bayanta a hankali ta ke fadin "wash, wash, tana limshe ido na son yin bacci. Karar wayarsa ce ta sa ta bude ido, ya dauka "Hello Inna kina lafiya kwana biyu?" Inna ta ce, "Lafiya lau nake ina jawahir din?" "Ga ta kusa da ni." "Yauwa daman dai kan maganar da nafara yi maka ne, zan zo na taho da jawahir don ta yi wankan gida". "Haidar ya katse ta da "Haba Inna saunawa zan gaya miki ne ni matata babu inda zata duk girman gidan nan bai ishe ta wanka ba sai kun dauke min ita, wanne hali kuke son saka ni?' Ta daka masa tsawa "Kai marar kunya bana son shashanci, haihuwar farin zaka yi wa wauta yaushe zamu barta ko mu ma wayaye ne irin ka.? Ta kife wayar tana mita. Jawahir ta dora kanta akan cinyar Haidar tana shafa fuskarsa. "Honey na me yake faruwa ne, don Allah ka daina damun kanka." "Bebyna ba dole na damu kaina ba, suna kokarin raba ni da ke, bebyna wai za ki iya tafiya wankan gida ki bar ni a nan har tsawon kwana arba'in da 'yan kai? Ta girgiza kai cikin yanayi na tausayi da son ta yi kuka "Honeyna ba zan barka ba bazan yarda su raba ni da kai ba, babu in da zan bi su." Daidai lokacin da ta dafe cikinta tana wash, wash!, yayi saurin rungumarta cikin rikita yana cewa, "Bebyna menene, me ya faru da cikin nawa.? My love bayana, cikina, kuguna, duk ciwo suke yi." Da sauri ya buga wa direbansa waya ya ce ya fito da mota zasu asibiti. Ya dakko jawahir direban ya bude musu bayan mota suka shiga, ya rife ya ja suka nufi asibitin, abinka da lafiyayyen asibiti tuni suka shigar da ita dakinta daban ita kadai a ciki Haidar ya furgice ganin yanda jawahir take wahala, gani yake kamar ciro cikin ya dawo da shi jikinsa shi ya yi nakudar ya haihu. "My love" ta kirawo shi maganarta kasa-kasa ya durkusa kanta yana jinta "My love kayi waya su Mama su zo kada na mutu basu ganni ba. Ya sake rungume ta yana ta mulmula mata bayanta, "Ki yi hakuri bebyna, ba za ki mutu ba kin kusan haihuwa. Idan ki ka haihu sai na yi musu waya su taho da kwarin gwiwarsu yanzu kuwa idan na gaya musu hankalinsu tashi zai yi su zo su cika asibitin ai ta damunki. "Wayyo Honey." Ta kankame shi tana nishi likitocin da suke kanta suna gaya mata ta yo nishi suna danna mata cikin a hankali tana yo nishi jariri ya fado tare da tsala kuka. Haidar ya yi saurin daukansa a cikin jinin ya na ta murna. Likitar ta yanke masa cibiya ta karbe shi ta mika wa nas don su gyarashi Wata sabuwar nakudar jawahir ta kama ba jumawa ta sunkuto 'ya mace ba da jimawa ba wani da namijin ya kuma futowa. Ikon Allah, Allah mai baiwa, Allah mai kyauta, har da kari jawahir ta haifi 'yan uku maza biyu mace daya, 'ya'yan kyawawa kamar 'ya'yan indiyawa don kyau da ja, Haidar duk ya rikice don murna waya yake ta bugawa kawai baya tsayawa gaisuwa sai dai ya basu labarin jawahir ta haifa masa kyawawan 'ya'ya har guda uku. Kafin ki ce meye wannan, tuni asibitin ya cika ya zama filin barka barka tare da murnar samun wannan kyawawan karuwar da aka yi. Kwanansu daya a asibiti aka sallame su don ba sa mun hutun suke ba saboda jama'a da suke ta tuttudowa ganin wannan kyauta da Allah ya yi musu da ba kowa ake ba wa ba. Nan kuma gaddama ta kaccame in da Inna ta daga gida za a yo da jawahir da jarirai shi kuma Haidar ya ce babu in da za 'a kai masa mata da 'ya 'ya, sai da Abbansa ya daka masa tsawa ya nuna masa bacin ransa a zahiri sannan ya bari aka tafi da su jawahir da yaran gidansu. Shi kuma Haidar ya yi fushi ya yi nasa gidan ransa a bace, yana shiga gidan yaga bakinsa yau ba jawahir a ciki can kuma ya rinka hango ta tare da 'ya 'yansa 'yan uku, haba wa, tuni wani sabon farin ciki ya sake mamaye shi ya shiga wanka ya sake sabon wanka ya zira farae shaddarsa sabuwa kal mai laushi sai sheki take yi kamar boyel. . SALON SO PART 41 . . Ya debi makudan kudi wanda ba zan iya cewa ko na wane ba ya zuba a jaka ya fice ya kulle ko ina na gidan ya fito ya kara gaya wa megadi ya kula da gida sosai Ya shiga mota da kansa yake jan motar cikin farin ciki da annushuwa wani tsadaddaen hadadden kanti yaje wanda duk kayansu da ga waje suke shigowa da shi. Nan da bude bakin aljihu ya runka jidar kayan jarirai su tawul, da shawul da riguna famfas su safa da takalman jarirai komai iri daya guda uku yake kwasa, sai da ya cika but da kayan jarirai har da gadaje set me uku na jarirai. Haidar ko ya manta ne da dinbin siyayyar da suka yo daga kasar waje ta jariran ne? Oho. Ya je ya siyo katon ragonsa wanda za a yanka saboda naman gashi ya siyo kwandunan tattasai da tumatir da attaruhu albasa da kaji da zabi saboda girkin 'yan barka ya yiwa direbansa waya ya taho da wata motar kwashe wasu kayan suka nufi gidan su jawahir. Tirkashi! Wani aiki sai masu da shi, aka rinka jidar kayan da Haidar ya kawo ana kaiwa sashen momy Haidar ya shigo yana ta gaisawa da jama'a suna yi masa barka. Ya karasa falon Momi ya gaida su Momi su Anti Babarsa da su Inna da kannansa 'yan biyu. Dangi dai rankacakaf kowa ya zo, jariran suna hannunsu sun sha ado, da tsadaddun kaya 'yan kantuna masu kyau. Sayyada ce take gaya masa ai jawahir tana sashenta ta ce kada abar kowa ya shiga bacci zata yi, shi yasa aka kwaso jariran ma aka yo nan da su, saboda yan barka. Haidar ya ce ai suma jariran suna bukatar hutu da a kyale su aka yi a jikin uwarsu suna jin diminta suma suyi vaccin iya in an jima su ka tashi duk me son ganinsu sai ya gansu. Anty babarsa ta watso masa harara yayin da ya mike sum-sum ya bar falon ya nufi sashen da aka ware wa jawahir. Ya tura kofar falon ya shiga ko ina a gyare sai uban kamshi da yake tashi, yana kai cikin dakin wani kalar kamshin ya ja mai dadi da sanyaya zuciya. Ya hangota kan makeken gado tana ta baccinta hankalinta kwance. Ta yi kwanciyarta cikin jar sup me zanen ganye ta kara kyau da haske sai dai ta rame. Ya karasa bakin gadon ya sumbace ta yana shafa fuskarta tare da hura mata iska a kunnanta. Ta bude ido tare da fadada murmushinta "Lah, Honey ka daina fushin ka zo? Ta tashi ta jingina a jikinsa ya rungume ta yana shafarta tare da shakar ni'imtaccen kamshin da yake jikinta. Ya ce "Bebyna ai ba zan iya fushi da ku ba, ina zan iya bacci ba tare da naji diminki ba, ai ba ni da kwanciyar hankali in banga 'yan ukuna ba. Aka kwankwasa kofar jawahir ta yi saurin kwace kanta ta matsa can gefe, ta yi izinin a shigo. Inna ce da sajida suka shigo dauke da kwanukan abinci. Inna ta sakko mata da filo kasa ta ce zauna anan ta bude mata kwanon tuwon dawa yana turiri ta bude miyar kubewa danya da aka burge kaza ciki. Daya kwanon kuma gasasshen nama ne ya ji kayan kamshi da yajin daddawa. Sai kunun kanwa a kwanon sha Inna ta debo man shanu ta zuba mata amiyar ta ajiye mata yajin daddawa, ta ce "Sakko ki zauna maza ki cinye." Idon jawahir ya yi rau rau zata yi kuka, Haidar ya ce "Haba Inna daman dan ki yi mata izaya da badin tuwo da kunu shi yasa kika dage sai ta taho nan.? Inna ta ce, "Da Allah i min shiru ku me kuka sani wannan ai shine gatan me jego shi zai sa mata koshi ta sami wadataccen ruwan nono da 'ya 'yan zasu sha su koshi ko kasan har yanzu yaran basu sha komai ba sai zam zam da dabino? Cikin tashin hankali Haidar ya ce "Inna saboda me? Bayan an siyo musu katon din madara.? Inna ta ce, "Ai duk wani abu da za'a basu shi yanxu shirme ne in dai va su fara shan nonon uwarsu ba, nonon uwa shi ne abu mafi mahimmanci ga jariri. Don shi yake sa su kuzari yake kara musu lafiya kuma don haka ki sauri ki ci ga ruwan wanka can yakusa tafasa, idan an daki nonon da ganye zai temaka wajen zuwan ruwan nonon da sauri Haidar ya ce "A to ta so maza ki ci tuwon nan ki sha kunun. Jawahir ta kalli Haidar a marairaice alamun tsoro a faskarta. Haidar ya kamo hannunta "Yi hakuri ta so na taya ki ci kin ji kada ki damu. Ta zauna kan filon shi kuma ya zauna kan kafet din suka zuba yajin daddawa da man shanu suka fara cin tuwo. Yanda suka za ce shi ba haka suka ji ba, ashe dai shima tuwon dawar da dadi. Tun suna ci suna hira har abin ya kaisu da shiru sai dai gyada kai, kawai suke yi suna kai loma tare da zuba santi. Inna tana zaune tana kallon su sai da suka kusa cinye tuwon nan, Inna ta zazzuba musu kunan a kofina ta tura musu gasashen naman shima sun ci amma ba da yawa ba saboda koshin da suka yi. Cikin kwana biyu ruwan nonon jawahir ya watada tana shayar da 'ya 'yanta su koshi sosai. Daddare dai ba sa shan nono sai madara yau kwana hudu da haihuwar an kawo kayan barka akwati biyar na me jego da jirajirai. Bayanin kayan da suke ciki zai cika min dan lattafin nawa ban gama ba, hade da mukulun dankareriyar mota jif, me ruwan ganye wadda Haidar ya yiwa jawahir kyautarta da takardun dankareren gida da yake a Nasarawa GRA shima gift ne ya bata duk saboda haihuwar 'yan uku. Sai takardun filaye guda uku kowacce da sunan yaran mallakarsu ce kyautar ubansu Haidar da yake ba su. Kowa ya kalli kayan sai ya yi murna tare da son barka da wannan hidima da Haidar ya yi. Ranar suna an sa wa jariran mazan sunan baban Haidar da baban jawahir macen kuma an sa mata sunan Inna. Amma duk an boye musu sunan ana kiransu da Salim, Sadat, Salma, Alhamdulillahi taron suna ya yi kyau ya kuma kayatar ya burge kowa da yamma aka je dan Haidar da jawahir sun yi shigar kaya iri daya jawahir ansha gwala gwalai hannu da wuya da kunne har da sarkar kafa, sai sun jero a gurin fatin suna rike da hannun juna suna tafiya sannu sannu suna murmushi tare da hira kasa kasa a tsakaninsu sai sheki suke yi kamar taurari, Bayan su kuma Sayyada ce da Sajida sai Auwalu a tsakiyarsu suna dauke da jariran yaran an yi musu kwalliya ta ke ce raini Salma ta sha adon gwal har da siririyar sarka ta kafa da ta hannu masu bidiyo da hoto sai haskasu suke yi Sa'adu Bori ya saki kida yana wake su cikin wakar soyayya ta yi dadi Jawahir da Haidar. Allah ya raya Salim, Salma, Sadat, 'yan uwa kuwa suka balle bakin jaka sukai ta yi musu ruwan kudi. 'Yan uwa da abokan arziki suka rinka ba wa jawahir kyauta iri iri ta kayan jarirai da kudi da sauran su da haka taro ya watse. Kowa ya nufi gida, jawahir tana zaune a gidansu ita da jariranta da Inna sai kakar babarta wadda ita take yi mata wanka. Anty Maryam kuwa ta dage da sake hada wa jawahir sababbin sinadarai na matse 'ya mace da kara mata ni'ima mace ta koma kamar bata san namiji ba. Haidar kuwa kwana kawai yake yi a gidansa da safe da ya gama shirinsa gidan su jawahir zai taho ita zata hada masa break ya ci ya dauki yaransa ya yi musu wasa sannan ya tafi office. Haka in ya dawo ma nan zai zo jawahir ta shirya masa abinci ya ci ya yi kat yai ta rainon 'ya 'yansa ya na yi musu wasa sai shadayan dare sannan zai koma gidansa. **** **** ***** Bari mu waiwayi Kausar don muga wace rayuwa take y ne." Kausar tun ranar da ta bar gidan Haidar ta sauka a gidansu Abuja. Iyayenta sun tare ta da murna amma ganinta da shirmin akwatuna sai jikinsu ya yi sanyi suka shiga tambayarta da lafiya? Kausar ta gaya musu karya da gaskiya na ciwon Haidar sannan ta mika musu takardar sakin da ya yi mata. Ba su ji wani zafin sakin da ya yi mata ba don su a ganinsu gwanda hakan da 'yarsu ta takura, 'yan aikinta suka shiga gyara mata wajen zama. Kwanaki kalilan a tsakani mahaifanta suka tura kano gidan Haidar don kwaso kayan Kausar suka tarar da gida a kulle sai megida ne yake yi musu bayanin ai ba kasar, sai gidan su Haidar din suka je suka yi wa Anty bayanin zasu kwashi kaya. Anty ta yiwa Yaya Abba waya yazo ta bashi mukullayen ta ce ya je ya bude musu gidan ya tsaya su kwashi iya kayansu. Haka kuwa aka yi, ya je ya bude musu ya jira suka gama kwasar kayansu ko tsinke basu bari ba, bayan yin iddar Kausar ta bude shafin zawarci in da manema kuwa suka yo mata ca! Ganin ta fito daga gidan mekudi ga ta kuma 'yar mekudi. Kausar abinka da goggiyar tuni ta kuma wanke fata ta tsunduma cikin zawarci. Manema da yawa sun firfito mata sai dai rashin sa'ar da ta yi, duk cikinsu babu saurayi, daga me mata daya sai me mata biyu. Hakan ne yasa ta riki Bomboy dinta. in da ya fito ya kawo kudin aurenta ba dadewa ba aka sa ranar biki an sha shagali da casu kamar na budurwa. Ta tare a gidan ta dake nan K/Maiyaki. Bomboy dai ya dauki matar sa kauthar kamar wata sarauniyaba abin da be ajiye mata ba na jin dadin rayuwar dan Adam. Ba ruwanta da girkin gidan kullum sai dai ya dauke ta zuwa hotal su ci abin da ransu yake so, ruwa sai da na roba wato swan. Kowanne lokaci firji dinta cike yake da kalolin abincin gwangwani da kalolin lemummuka. Tuni Kausar ta kara gogewa jin dadi da hutu ya kara samun mazauni kome sai dai 'yan aikinta su yi mata bata katabus koda yaushe aikinta kwanciya ko ci. Ana cikin haka ne aiki ya kuma mayar da iyayen Kausar kasar America. A lokacin kuwa Kausar da Bomboy ba sa kasar don haka bata sani ba don iyayen nata sun ta lalubenta a wayarta ba su same ta ba, sai sallahu suka bar mata gun 'yan aikinta suka daga zuwa America. . (((((( SALON SO )))))) : KARSHE! PART 42. . Ranar da Bomboy da Kausar suka dawo da ga tafiya, 'yan aikinta suka gabatar mata da sakon iyayenta. Kausar har kuka ta yi don bakin ciki gashi wayarta da lambobin iyayen nata suke ciki ta fadi a wannan tafiyar da ta yi, don haka ba wata hanya da zata ji su ba damar ta yi musu waya kenan, ko su yi mata? Ga shi bata san address din su a American ba, bare wata rana ta kai musu ziyara dole ta dauki dangana da hakuri ta na me fatan Allah sa su zo nan kusa don ta ji cikakken address dinsu ko ta bisu su tafi tare. Ba dadewa Kausar ta gama da laulayin ciki me wahalar gaske bata iya cin abinci sosai ga azabar ciwon ciki da ciwon kai. Hankalin Bomboy ya tashi da ganin rashin lafiyartata. Ya kwashe ta suka nufi asibiti akayi mata tes da gwaje gwaje daga karshe likitan ya dauki fitsarinta ya ce, gobe a dawo a karbi ruzol suka taho a hanya ya yi mata siyayya fal irin na marasa lafiya ya dawo da ita gida. Da gari ya waye Bomboy da kansa ya je ya karbo sakamakon gwajin da aka yi mata hankalin Bomboy yayi fari da ganin wannan sakamakon Murna a gun shi da Kausar kuwa kamar su hadiye juna don murnar samun ciki Kausar ta fara kawowa Bomboy tsarabe-tsarabe, ta ce wannan ta ce wannan haka Bomboy zai je ya kwaso mata. **** **** ****** ***** Sannu sannu rayuwa ta juya ta juyawa Bomboybaya domin kudin hannunsa tas sun kare 'yan aikinta wuya ta ishe su duk sun gudu sun barsu, sai ga Kausar ta je ta na rokon matan yayun Bomboy da su taimaka su rinka sammata abincinsu, su kuma suka ce muddin tana so ta rinka cin abincinsu sai dai ta fito ta rinka girkawa don babu bawanta da zai rinka dafawa yana bata tana ci. Dole Kausar ta fito tana girkawa da safe koko ne za'ayi shi tsilulu saboda babu wadatacciyar gasara, rafin kofi ake rabawa kokon ga ba kosai da rana a jika garin kwaki a yayyafa a kasan roba yaro ma baya koshi bare babba. Da daddare datsar dawa za a tuka bakikkirin da koriyar miyar kuka wadda daga daddawa sai barkono a ciki. Kausar ga fama da ciwo ga shi yanzu cikin nata ya kai wata shida ya yanzu cin abinci ne da ita saboda cikin yana sata masifaffiyar yunwa. Ga abincin da ake bata baya isarta, ga rashin dadi haka take hakura ta tattura, ga shi duk ta yi baki ta rame ta kanjame ke ba kya ce 'yar hutu Kausar din da ba ce. Duk ta bushe sai kashin wuya da tsinin ciki gashi bata iya yin tuwon ba duk ranar da ta yi sai yai danye ko ya yi gudaji. Ga matan yayye da 'yansu si yi mata masifa sun dungure mata kai suna yi mata ba la'i, dole ta jure ta hakura take zaune don bata da gurin zuwa in ma ta fita ga iyayenta har yau bata samu labarin su ba, to ina zata samu kudi xuwa American ma bare ta binciko in da suke. Don kayan dakinta kaf ta sai da su ta ci abinci duniya kenan me juyi juyi. **** ****** ****** Jawahir watanta biyar kenan da haihuwa ita da 'ya 'yanta sun kara kiba da haske sun yi kyau jajir da su kamar 'ya 'yan Turawa. Kowa ya kalle su sai ya yi sha'awar cewa da ma dai iyalinsa ne. Haidar arziki ya ci uban na da, ya tanfatsa musu wani tsantsareren gida na gani na fada wanda duk wanda yaje gidan kallo abinda yake fadan shi ne aljannar duniya. Gidan ya tsaru iya haduwa ya hadu, yanda Haidar ya hadewa jawahir falonta da dakunanta ko na sarauniyar indiya albarka Dakin 'yan uku kuwa ke kya ce kamfani ne tsadadde na kayan wasan yara saboda kayan alatu da suke ciki, Haidar ya kara girman da murjewa ya zama Alhaji me tsananin kyau da kwarjini. Jawahir ta zama big madam cikakkiyar mace ga kyau ga hutu ga kwarjini 'yan 'ya'yayansu guda uku abin sha'awa tubarkalla, bul bul da su jajir da su gashinsu akanannade kamar 'ya'yan turawa. Mijinta ya sakar mata naira sosai don duk wasu takaddun kamfanoninsa da gidajensa da filayensa da duk wasu kadarorinsa suna hannunta. Baya yi mata geji akan komai duk wani abu daya kamata ya yi na game da biyan ma',aikatansa albashi na kamfanoninsa zuwa na gidajensu, ya ce Abbansa ya kwanta ya huta shi yake komai na gidansu. Jawahir ta kasance me taimakon talakawa da kaskantattu wadanta basu da watada, don haka gidan nasu kullum yake cike da 'yan neman alfarma. 'Yan uku suna da shekara daidai ta yaye su sun yi girma sunyi wayo gudunsu suke yi ko ina ga surutu kamar Aku. Suma hadadden falonsu duk sun ci kwalliya kamar masu shirin zuwa fati, Haidar yana ta wasa da 'ya 'yansa ya ta da kai da cinyar jawahir Salim da Sadat shiga iri daya akayi musu ta jins da T shirt fara da aka yi rubutu da ruwan gwal a gaban rigar. Salma ma tana sanye da dan jins dinta da 'yar riga, kunnanta da wuyanta yana sanye da yari da sarka kirar daimond 'yar xire, kanta ya sha kananan kalba da kanan ribon a jiki yaran

Chapter 12 of 13