Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
me nauyi an fi so a ci irinsu hadin salak, sharfar taliya me romo gasasshen nama, ko hanta ko zaka, farfesun kayan ciki ko na naman romon kai, ko na jelar sa ko naman karamar dabva, kai da dai duk abin da Allah ya hore muku marar nauyi. To kinga wadannan duk inya ci va za su yi masa bauyi a ciki ba bare su hana shi su kuni su takura shi wajen aiwatar sa sunnah Jan hankalinsa ta suffofin kwanciya kala-kala. Duk abin da kika kula ya fi so to ki lakanci abun duk sanda kuke tare ki rinka kirkiro wasu abubuwan ma da bai san da su ba. Ki saki jikinki da shi ki cire kunya ki rinka sarrafa shi kina dan kukan kissa tare da kiran sunansa a hankali kina hadawa da kalaman soyayya don tafiyar da imaninsa. Ki kasance cikin yawan shan kunun aya, shan zuma, shan rake, lemon zaki, kankana, gwanda, abarba, nono, dabino, cukwi, tufa, inibi, kin ga wadannan ki kasance cikin yawaita cin su ko da yaushe don suna karawa mace ni'ima da amfani sosai a jikinta. Ki nemi garin bagaruwa gwangwani daya, garin kurna gwangwani uku, garin habbatus sauda rabin gwangwani, garin dakakken dabino ki rinka samun busasshiyar aya ki daka sai ki hada su waje guda ki samu lafiyayyen nonon shanu marar tsaki kina diban wadannan kayayyakin da kika hada kina damawa da nonon kina sha, to wannan shi ne sirrin yanda kika ga nonuwanka sun cuccuko sun yi manya suna tsaye ba su da alamar rankwafawa. Jawahir ta ce, "Au Aunty kina nufin garin nan da kike ba ni damamme da madarar shanu yana da nasaba da cikuwar nonuwana?" Aunty ta ce, "Kwarai kuwa shi ya sa kika ga ina yawan gasa mana naman karamar dabba ruwa ruwa da kuma romon kai da farfesun wannan sirrika ne na mata. Duk abubuwan da na lissafo a baya su suke bamu ni'ima a jikinmu mu mata suna sa ihu kyan fata, yawan, amfani da man zaitun da habbatus sauda suna sa fata ta yi mul-mul da santsi kamar ta jariri." Jawahir ta ce, "To Aunty ni da ba a gidan miji nake ba amma kike ta dirka min magunguna da tsumi ina sha. Kuma kullum sai kin sa ni na yi turare na tsugunno da na jiki, meye fa'idar hakan.? Ta dafa kafadarta daya ta ce, "Diyata ke nan, ai duk wannan shiri nake yi miki nake tsumaki don duk sanda Haidar ya kusance ki to haihaita haihaita sunyi sallama da kowacce irin mace don ba me iya gamsar da shi sai ke, na gaya miki Haidar sai ya dawo tafin hannunki, sai yanda kika juya shi. Jawahir ta fada cinyarta tana kyalkyala dariya, "Na gode Aunty sai ya san wadda yake cewa kwaila ko tatsitsiya." . (((((((SALON SO)))))) (((PART 21 TO 24)))): : . Bangaren Kausar kuwa kullum cikin yowa Haidar waya take safe, rana, yamma da dare ma ba ta bar shi ya huta ba kan maganar aurensu tun yana boye mata yana cewa ta jira shi har dai ya fito ya gaya mata gaskiyar batun matarsa. Amma ya ba ta hakuri da ta jira iyayensu su dan samu nutsuwa sai ya tada maganar su zo. Amma da ta kai ta kawo yau da Kausar ta tayar da hankalinta sosai don gani take yi kamar Haidar din sake subuce mata zai yi a karo na biyu, ganin yanda ta samu kanta ne ya sa Haidar ya je yake tuntubar mahaifinsa da zancen. Abbansa ya ce, Yanxu Haidar ba za ka hakura da auren nan ba, kana kallon maganar nan ce ta tayar muku da rigima ga shi ba a san inda 'yar uwartaka take ba ko? Haidar ya ce, Abba ka tausaya min mana, yau shekarar jawahir daya kenan da barin gidan nan. Abba kana kallon kullum ina hanyar gidan nan don cin abinci ni ba na iya cin abincin waje bare na rinka zuwa Otal ina ci. Abba ba ka tausaya min na samu na yi auren nan ko ni ma na samu nutsuwa a gidan? Abba ya ce, "Yanxu kana ganin idan ka yi aure surutun mutane 'yan uwa da abokanan arziki ba za su dinga ganin ba ka damu da batan matarka ba? Ka ga abin zai zama abin surutu ko? Haidar ya ce "Wallahi Abba jawahir tana hannun inna don ita ta boye ta. Ya ce, "Ka tabbata? Daga bakin wa ka ji? Wallahi Abba migadin gidan Inna na ritsa na ce ko ya gayan gaskiya ko na debo masa 'yan sanda shi ne yake gaya min tana gidan Inna to idan na je wa da Inna maganar sai ta koro ni, ni dai ina ganin gwara na yi auren in ta ga na yi auren za ta dawo da ita. Abba ya ce, "To shi kenan Allah ya zaba abin da ya fi alheri, zan je wajen Alhaji ibrahim din duk abin da muka tattauna sai ka ji. Ya ce, "To Abba na gode. Ya mike ya tafi. Abban Haidar ya samu Dadyn jawahir yake gaya masa yan da suka yi da Haidar din, Alhaji Ibrahim ya ce, ai ni tun da na ga hankalin Inna bai tashi ba na san cewa jawahir tana hannunta. To na sha tuntubar Aisha a kan maganar, to idan a ka bar maganar ai anyi zalinci kuma an shiga hakkin Haidar, shekara guda mace ta gudu ta bar ka kuma a hana ka yin aure, ai da zalunci, ni dai kawai ina ganin in Allah ya kai mu jibi mu je gidansu yarinyar a gama maganar komai Haidar ya samu mata kawai Lokacin da suka je Abuja gidan kaninsa Alhaji Aminu suka sauka tukunna sai da suka huta suka samu nutsuwa sannan suka dinguma har Alhaji Aminu zuwa gidansu Kausar. Sai bayan tafiyarsu sannan jawahir ta dawo daga makaranta. Antinta take bata labarin zuwansu Dadynta, Jawahir gabanta ya fadi, "Lafiya kuwa Aunty.? "Eh to, wallahi ban sani ba don sun tafi tare da Ankul dinki kuma be gaya min inda za su je ba ko dalilin zuwansu ba. Jawahir ta ce, "To Allah ya sa dai ba ganowa suka yi ina nan ba. Amin da 'yata, don ba na so a raba ni da ke. Suka yi dariya. Gidan su Kausar an yi wa su Alhaji kyakkyawar karba inda iyayenta suka nuna karamci da dattako. A lokacin mahaifinta ya ce ya yanke ranar aure sati biyu masu xuwa kawai nan fa a ka yi ta murna ana sa musu albarka. To su Alhaji su daga nan suka hawo jirgi suka juyo gida shi kuma Ankul din ya koma gida. Suna zaune da matarsa a falon suna tatraunawa jikin maryam duk ya yi sanyi da jin abin da ya kawosu, Alhajin Abuja. Jawahir ta shigo falon tare da yin sallama ta tafi kusa da Ankul dinta ta zauna dab da kafarsa a kan kafet ta ce, "Ankul barka da dawowa. "Yauwa 'yata sannu "Ankul me ya kawo su Dady? Ko sun san ina nan ne? Ya girgiza kai, "Dady bai san kina nan ba kawai abin da ya kawo su ne, shine na yi musu rakiya. Ankul Dady bai tambayeni ba? "Ai bai san kina nan ba ne shiyasa. "Ankul ko dai maganar auren Haidar ce ta tashi suka zo suka gaya maka?" "In ban da abinki idan auren Haidar ne ai sai su yo min waya ba sai sun zo ba ko? "Eh to, haka ne Amkul'" ya ce, "Kwaso littattafanki mu gani, "Ta mike ta nufi dalinta. . ***** ****** ***** Lokacin da suka isa gida suka shaidawa Haidar halin da ake ciki, a satin suka hada hada kayan lefe da komai da komai mata suka kai, duk wannan halin da ake ciki hankalin Haidar yana kan jawahir don haka ya je ya shirgo mata kayan fadar kishiya akwati uku hadaddun kaya na gani na fada, don tsadaddu ne a ciki ya ai ka wa Inna ya ce a gaya mata tun da ta rike masa mata matarsa ta hana shi to ga kayan fadar kishiya ne don ba a gaya musu da baki ba. Inna ta karbi kayan ta samu waje ta adans su. Biki ya zo bangarensu Kausar sun sharyawa bikin don kalolin fatin da za a yi da komai da komai Kausar ce ta bude bakinta ta yi ta hidimarta ba ta jiran ango don ta san halinsa auren ba dada shi ya yi da kasa ba, ta yi hidima da bidirinta. Fati daya kawai Haidar ya je shi ma, sai da ta dame shi da magiya sannan ya daure ya je. Amarya ta tare a gidan angonta Haidar. Babban falon gidansa na amfanin kowa da kowa ne, a falon akwai kofa da take kallon gabas ita ce in an bude an shiga sashen jawahir da katon falo da dakuna uku a ciki, sai toilet, kicin da suke a ciki. To idan an dawo falon akwai wata kofar da take kallon yamma wato tana kallon kofar bangaren jawahir to ita ma in ka shiga katon falo ne da kicin da tolet shi Amarya Kausar ta shiga, to a tsakiyar babban falon bene ne wanda za ka hau ka je turakar megidan, shi ma falon falo ne, da ya kushi dakuna biyu na bacci da tolet da kicin, sai wata kofa da za ka bi a saman dai, shi kuma makeken fili ne da aka kayatar da shi aka yi masa rumfa don hutawa, to nan saman shi ne na megida Haidar. Zama ya yi dadi tsakanin Ango da Amarya sai dai sabanin halayya da ta zo bamban ta ango da amarya, don ita Kausar ta samo masu yi mata aiki har mutum uku ta cika masa gida da mutane ke nan, shi da yake dan hutu ba ya son hayaniya, to amma duk dawowar da zai yi zai tarar da Kausar uwar lalaci a mike a doguwar kujera ko kan kafet masu aikinta suna yi mata tausa, wani karin abin haushi wai ba ta iya girki da kanta sai dai me aiki ta yi musu wannan dalili shi yake hana shi cin abincin gidan, an gudu ba a tsira ba kenan, don kullum sai ya biya ta gidansu ya ci abinci Karin abin da yake bawa Haidar Haushi da Kausar wai gadon da suka kwanta sai dai ta kirawo me aiki ta gyara, wai ina abubuwan da jawahir take sanya musu a gidan da dakunansa suke kamshi ne, duk yanzu wannan kamshin mai dadi babu. Shi wai shi yaya zai yi ne ya dawo da jawahir dinsa ne, ko don lafiyayyen girkin da take yi masa mai dadi ga ladabi da biyayya, duk yanda ya bata mata rai ba za ta fasa yi masa girki ba ko ta ki gaishe shi, ga shi ya yi auren wayayyiya wadda ta yi karatu a waje amma babu biyan bukata. Don zamansa da tatsitsiyarsa ya fi sau dubu dari, duk hanyar da ya bi don Inna ta dawo masa da jawahir ya bi amma magana daya take gaya masa ita ma ba ta san inda take ba. . Lokacin da jawahir ta ji labarin auren Haidar ta yi kuka sosai ta tashi hankalinta har sai da Inna ta zo Abuja don rarrashinta. Don lokacin Ankul dinta yana legos. Jawahir kuka take kamar rainta zai fita Inna kuwa sai sai rarrashinta ta ke yi tana bata hakuri jawahir ta ce, ni ba wani abu ne ya sa ni kuka ba irin yanda ya wulakanta ni ya yi aure kin ga ya sake nunawa duniya cewar bai damu da ni ba kenan. 'Inna ta tausayawa jawahir don ta fuskance ta kishi ne yake damunta. Inna ta ce, "Ki yi hakuri idan kina so ma yau sai na mayar da ke gidanki. "Da sauri jawahir ta dago kai tare da saurin katse Inna, "Haba-"Haba Allah ya sawake ai sai ya ga na damu da shi ne ya sami hanyar da zai kuma wulakanta ni. Inna ta ce, in dai wannan kike ji kwantar da hankalinki domin kuwa yanzu Haidar ta damu dake wanda ba kya zato, auren nan da ya yi ya yi shi ne don na yi fushi na dawo masa da ke ne, ta ba ta labarin yanda hankalin Haidar ya tashi na rashinta da yanda a kayi auren har kayan fadar kishiyar da ya kai mata da irin korar karen da take yi wa Haidar din, ko ba komai in kalaman Inna ya sanyayawa jawahir zuciyarta har ta ji tana sha awar ta koma gidan Haidar ko dan ta ga wanne irin zama suke yi da Amaryar ta sa. Jawahir ta ce, "Shi kenan Inna ba komai Allah ya kara rufa asiri. Kwanan Inna biyu a Abuja ta juyo zuwa gida, Maryam ta ce da jawahir kada ki damu diyata, ni na san shirin dana yi wa jikinki kowanne namiji in dai ya dandana ki to ba ba zai iya kusanta ki da wata mace ba, ni na fada miki haka kuma ki hakura ki koma gidan Haidar ko don ki ba ni labari gaba, idan ya dandani zumarki. Jawahir ta ji kunya ta mike da gudu ta bar wajen. Bayan Inna ta koma gida washegari ta nufi gidan danta Alhaji Ibrahim mahaifin jawahir, su momy da Abba Nasir zuwa su Auwal da Sani sun yi murna da ganin Inna gida ya rude a na ga Inna ga Inna. Inna ta zauna cikin jikokinta ana wasa ana dariya Momy kuwa tana ta hidimar kawo mata ababan ci da na sha. Momy ta zauna suka gaisa Inna ta ce, "Maigidan kuwa yana nan.? Momy ta ce, "Eh yana nan bari na yo miki magana da shi." Momy ta samu Dady rigingine a kan gado yana kallon sili da alamu tunani yake yi, Ta yi sallama tare da cewa, "Barka da hutawa. Ya amsa da yauwa: Inna ce ta zo take son magana da kai. "Ya mike zumbur ya ce, "To gani nan fitowa. Ya zo ya durkusa har kasa ya gaida Inna, ya ce "Inna da kanki kika taho maimakon ki aiko na zo.? Ta ce, "Kamawa ta yi daman na zo a kan maganar yaran nan ne, ya ce, "Wanne yara?" "Ta ce, "Wanda ka hada auren dole yanzu kuma kuka je kuka yi masa auren da yake so, ita kun hana ta wanda take so ta mutu kenan ko.? Ya ce, "Inna Allah ya ba ki hakuri wallahi ba haka ba ne." Dady ya ce, "Don Allah don Annabi Inna ki yi hakuri kada ki yi haka ba mu san abin da auren nan ya kunsa ba, kada mu yi wa Allah shisshigi a lamarinsa. Yanxu ki yi hakuri ki dawo da jawahir nan gidan gobe sai na sa a mayar da ita gidanta. Inna ta katse shi, "Kana nufin a mayar da yarinyar ya ci gaba da wulakanta ta ko? "Wallahi Inna ni na san ba zai wulakantata ba, in kika yi la'akari da yanda ya gigice da batan jawahir din. Inna ai kun hora shi ya horu ba zai sake ba. Inna 'ya 'yan nan duk namu ne wa za mu ki a cikinsu.? Duk wanda za ta aura ai ba kamar Haidar din ba ko Innata? Ta ce, "To shi kenan ai kokarinka ni ma na fi son a karfafa zumunci. "Yauwa Innata yanxu ina jawahir dina? Tana can gidan kawunta. Dady ya rike baki "Wanne kawun nata? "Tana da wani kawunne bayan Auta Aminu?" Alhaji ya ce, "Ikon Allah yanxu duk binkicen nan da muka yi ta yi tana Abuja.? Sallamar Haidar da Abbansa ne suka shigo nan fa Abban ya nufi Innar ya durkusa gaban Inna yake gaishe ta, "Haidar kuwa gaban Dady ya je ya gaishe shi, shi ya ki kallon Inna. Dady ya ce, "To ni na amsa gaisuwarka ba ka gaida uwata ba.? Haidar dai ya yi shiru bai ce komai ba bai kuma kalli Inna ba. Abba ya ce, "Ai yanzu ma shi ya je ya taso ni dole har da kukansa shi fa sai an nemo masa matarsa jawahir. Tun sallar la'asar ya tashi daga office ya je ya sani a gaba ga shi har bayan issha ya ki tafiya gidansa shine na ce ya zo mu je wajenka ko za a sami wani dan labari." Inna ta ce, "Daman abin da ni ma ya kawo ni kenan na zo a karbo min takardar sakin jikata ita ma ta je ta auri wanda take so." Haidar ya yi saurin tasowa ya rike kafar Inna don Allah don Annabi Inna ina jawahir take.? Ta ce, "Ina ruwanka da inda take ba kayi aurenka ba, to ka ba ta takardarta ita ma ta auri wanda take so." Haidar ya ce, "Don Allah don Annabi Inna ki yi hakuri ki yi min rai ki dawo min da matata wallahi zan kula da ita ba za a kuma samun kuskure ba. "Inna ta ce, "A'a, ka je dai ka rike matarka ita ma sai ta samu wani. Haidar ya ce, "Ki rufamin asiri "Inna wallahi ko cewa kika yi sai na saki Kausar za ki dawo min da jawahir sai na sake ta, don ni jawahir ta fiye min kowace mace. "Inna ta ce, "Ni da kake fushi da ni ba ka kula ni. Ya yi saurin cewa, "To yi hakuri mu shirya don Allah Inna jawahir tana ina.? Inna ta ce, "Jawahir tana Abuja gidan kawunku tun washegarin ranar da ka koro ta daga gidanka na tura ta can. "Tuni Haidar ya mike ya nufi bakin kofar waje. Abbansa ya ce, "Haidar ina za ka ne? Ya ce, "Abba Abuja zan tafi yanzu." Dady ya ce, "Ba ka da hankali ne ka dubi lokaci fa yanxu karfe tara ka baro matarka a gida ba ka gudun hakkinta, ka yi hakuri ka koma gidan na yi wa kawun naku waya gobe za su taho a jirgi insha Allahu a gobe za a dawo maka da matarka." Ya rissuna ya karayi musu godiya sannan ya tafi gidansa cike da nishadi. Daga nan su ma suka gama tattaunawa a tsakaninsu Inna direbanta ya maidata gida. Abba ma ya nufi nasa gidan. Washegari sha biyu na rana a Kano ta yi wa Ankul da Aunty da jawahir da ma tun goma na safe kannan Momy suka tafi gidan Haidar don wankewa jawahir kayanta tare da kade mata kura suka share mata sashinta suka gyara komai. Dady da Momy sun yi mamakin ganin yanda jawahir ta girma haka ta kara kyau da haske kamar ba ita ba. Yaya Abba dai da Nasir sai da suka yaba kyan nata. Da yake Inna ma ta zo nan dai aka hadu da Inna da Ankul da Dady da Momi da Anti Maryam a ka yi ta yi wa jawahir fada da nasiha yanda za ta zauna da mijinta da kishiyarta lafiya, ki ci gaba da yi wa mijinki ladabi da biyayya kada ki yarda wata rigima ta kuma hada ku da mijinki sai mun saba miki. Gaba daya kuma suka yi ta sama ta albarka. Anti Maryam ta ja ta daki ta dada yi mata bayanin yanda za ta yi amfani da magangunnan da ta hada mata. Da magariba suka raka ta gidan mijinta kamar sabuwar Amarya. An dai sake yi mata fada da nasiha daga nan kowa ya fashe ya barta. Ta shige sashenta ta kuwa garkame kofa sai karfe goma na dare Haidar ya shigo gidan. Dakin Kausar ya shiga ya same ta a mimmike a gado ya zauna a gefenta ya tambaye ta jawahir kuwa ta dawo? Ta ya mutse fuska tare da tabe baki kai da ka je ka dawo da ita ba ka san ta dawo ko ba ta dawo ba bare ni da ban san ta ba, ko na taba ganin ta ne? Be kuma ce mata komai ba ya yi tolet don inda sabo ya saba da rashin ladabi na Kausar. Da ya gama shirnsa ya nufi dakin jawahir sai ya ji shi a kulle sai ya haye samansa ya yi dai-dai a gadon bacci. Har ya fara bacci ya ji shigowar Kausar ta bi shi gadon suka kwanta. Da safe jawahir ta riga su tashi don haka ta hada birek dinta iya wanda za ta ci ta gyara babban falon nan da dakunanta kamar yadda ta saba ta turare su kamshi ya wadaci ko ina ta shiga ta tsala wankanta da kwalliyarta 'yar ubansu. Shadda ganila ta saka wadda ta sha dinkin surfani duk bulu da yalow da yake kwambineshin ce, ta sha a don gwal fuskar nan tata sai sheki take tana shainin. Ta zama cikakkiyar mace sosai kirjinta kamar ya fashe don cika. Jikinta kuwa wani fitunan nan kamshi ne yake tashi kamar an yi barin turare a jikinta. Ta fito falonta ta zauna, ba babban falo ba. Ta dauki break dinta za ta fara ci kenan ta jiyo taku an yo sashenta. Haidar har ya tashi ya yi wanka ya gama shirnsa cikin kayatacciyar shiga ta alfarma kamai yanda ya saba, amma gimbiya Kausar ana gado a kwance ana ta sharar bacci. . ((((((SALON SO)))))) ((((((PART 25))))))) : . Yana saukowa babban falon ya ji fitinan nan kamshi jawahir mai har gitsa masa kwalkwalwa ya yi hamdala ga ubangiji yayi godiya ga Allah da jawahir ta dawo hannunsa Bai ganta a babban falon ba don haka ya yi sallama a nata falon ya tura kofar ya shiga. "Subhanallahi! Tsarki ya tabbata ga wanda ya hallici wannan kyakyyawar budurwar yarinya sai ka ce balarabiya. Anya ba aljanu ne suke yaudararsa suna neman bude masa ido ba.? "Me ya sa kika tafi wani wajen ba da izinin mijinki ba har tsawon shekara daya? Kina ganin kinyi dai dai kenan? Ko kin manta aure kike yi? Ya za ki da dumbin zunubin tashin hankalin da kika sa mijinki a ciki.?" Ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka don Allah yaya kayi hakuri ba zan sake ba. Ya ce, "Shikenan ba wani abu sai dai ki kiyaye gaba. Kin ga yanzu ba mu kadai ne a gidan ba kina tare da abokiyar zama don haka ki kiyaye kin san ba na son hayaniya bare abin da zai daga min hankali. Shiru ta yi ba ta ce komai ba don ta san idan ta yi magana hawaye ne zai zubo don wani dunkulallen abu da ya tokare mata makogaro, ni na san ba komai ba ne sai kishi. Ya ce, "Ba ni break din na ci, "Ta mike tsam ta kai masa gabansa ta durkusa tana hada masa shayin ya yi kauri da madara, bonbita, neskofi, da sauransu. Ta bude masa fulas din soyayyen dankali ne da wainar kwai, sai gasasshiyar kaza da ta gasa. Ya ce, "Je ki falo na ki dauko biredi. "Ta dan yi dum ya ce, "Ba ki ji ba ne? Ta ce, "Yaya matarka fa tana saman? Yace, "Ba komai je ki, ki dauko min ai bacci take yi. Haka ta tafi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki shi dai yana tsananin kaunar jawahir yarinya me tsananin hankali da biyayya ga saukin kai ga kuma uwa uba ta hada komai da yake tsananin SO a jikin mace. Jawahir dai har ta hau sama ta sauko ba ta ga matarsa ba. Ta shigo falon ta da siririyar sallamarta ya amsa mata ta zo gabansa ta durkusa ta miko masa, ya ce, "To zauna mu sha ta girgiza kai, ya hada kai tare da cewar ba na son gardama zauna mu sha. Ta zauna suka fara birek Haidar danna birek dinsa yake yi yana ci sosai don yaushe rabon da ya yi break ma a gidansa tun jawahir tana nan. Ita kuwa a yangace ta ke ci kamar mai cin magani ya kalle ta ya ce, "Ke ba za ki bude baki ki ci ba ne? Wato kin fa dawo za ki rinka kin cin abinci ki kuma ramewa ko? Can da yake suna tursasa ki ki ci ai ga shi nan kin yi kiba to ni ma na daina kyale ki dole na matsa miki ki ci ki koshi. Haka ya takura ta ta ci da yawa. Daga nan ya fita ya tafi office cikinsa da koshi. Jawahir kuwa ta rufe kofar falonta ta yi zamanta a dakinta. Dan haka ba ta san wainar da suke toyawa ba. Da ta ji yunwa ragowar birek dinsu na safe ta dauka ta ci ragowar kazar da Yogourt roba biyu ta ji ta koshi kuwa. Shi kuwa Haidar a office duk ya kasa samun sukuni ganin yanda jawahir ta koma. Karfe shida ya tashi daga office ya yi gida. Ya yi sallama falon shiru ba kowa bare a amsa masa. Ya haye samansa ya tube ya yi wanka ya dauro alwala ya yi sallar magariba ya sako kananan kaya ya sauko kasa ya shiga dakin Kausar. Tana tare da 'yan aikinta suna aikin bautarsu na matsa mata kafa wannan abu yana konawa Haidar rai. Suka yi gaggawar fita daga dakin. Ya zauna tare da cewar, "Ina abincina.? Ta ce, "Na ga ba ka cin abincin masu aiki shi ya sa ban ajiye maka ba, ya ce, "Okey kin kyauta. "Ya mike ya fice kawai ya shiga dakin jawahir shiru sai dai ya ji motsin ruwa a bandaki wanka take kenan, don haka ya nemi gefen gadonta ya kishingida yana shakar daddadan kamshin da dakin ya ke yi. Jawahir da ba ta san da mutum a dakin ba ta gama wankanta ta dauko tawul iya gwiwa ta fito gashin kanta duk ya bazu ya manmanne mata a fuska ta bude kofar tolet din ta fito. Tana 'yar wakarta ta nufi gaban mudubi. Subhanallahi! Ai tuni hankalin Haidar ya so gushewa don ganin kyakkyawar kirar jawahir, jiki mulmul da shi ga shi jajir santsi yake yi da sheki, santala santalan cinyoyinta kamar na Baturiya. Ta zauna gaban mudubi ta fito da mayukanta da hadin turarukanta ta fara mulke jikinta. Sam ba ta kula da wani a dakin ba tana shirin yaye tawhul din don shafe jikinta sai ta hango kamar mutum ta mudubin tuni ta razana ta yu kara cikin dimautacciyar murya da takaicin rashin kwancewar tawul din ta ya ce, "A'a jawar meye haka? Ta ce, "To Yaya ai tsoro na ji ban san ka shigo ba, ya ce, "Okey sorry, sorry je ki ki gama shirinki. To

Chapter 6 of 13