Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuma sai ta kasa shirin a gabansa sai daya dakin ta shiga ta karasa shirinta ta fito cikin doguwar riga. Tsarki ya tabbata ga Allah, wannan yarinya da kyau take ga iya diresin kamar aljana. Abun da Haidar yake fada kenan a zuciyarsa. Har ta zo gabansa ta durkusa ta ce, "Sannu da zuwa yaya." Ya ce, "Yauwa jawahir kin ci abinci? Ta girgiza kai ya ce, "To me kika ci.? Ta ce, "Yogourt da ragowar naman daxu. Ya ce, "Shi ne zai rike miki ciki? Me ya sa kike son sakaci da cikinki ne? Me ya sa baki girka kin ci ba.?" Ta ce, "Ai gani na yi ba ni kadai ce a gidan ba. To in ban da abinki jawahir ke da gidanki sai an girka an ba ki? Ke da na san ki da kyankyami, za ki rinka cin abincin me aiki ne?" Ta girgiza kanta, ya ce, To kin gani ki rinka girkinki kina ci kin ji ko. Yanzu me za ki ci, ko za mu fita muje mu sayo wani abin ne ko kuma mu je gidan abinci. Ta girgiza kai, "A'a zan girka wani abu yanxu Ya dube ta ya ce, "Dare be yi miki ba. Ta ce, "A'a ba komai. Tun da ta soma magana yake jin wani abu, zil-zil yana tsarga masa don jin dadin muryarta da shaukin begenta. Ya mike ya fita jikinsa a sanyaye kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya fito ya hau samansa sai ya tarar da Kausar a kwance a kan gadonsa tana nishi. Ya isa kusa da ita da saurinsa ya ce, "Lafiya?" Menene ya faru? Ba yanzu na barki a dakinki ba. Ta ce, "Wallahi fama nake yi da ciwon mara tun safe daurewa kawai na ke yi ka daure ka kaini asibiti yanzu." Haidar ya ce, "Yanzu ya dace mu fita asibiti mu bar jawahir ita kadai a gidan? Kausar ta ce, "Haba Haidar me yake damunka ne me zai same ta, ba ga masu aiki nan a gidan ba, ko ka fi so ni na kwana ina murkususu?" Ya ce, "To shikena tashi muje. Lokacin da suka fito don tafiya sannan jawahir ta fito falon za ta shiga kicin wannan shi ne karo na farko da jawahir ta ga Kausar ita ma Kausar ta ganta. Ba su yiwa juna magana ba sai Haidar da ya ce zamu fita yanzu zamu dawo. Jawahir ta shiga kicin kamar ba ta ji me yake cewa ba, suka fice jawahir ta zauna a babban falo ta kunna kallo, salkamar da taji ce ta sata saurin juyowa. "Lalala Bilki yau ke ce a gari?" Gaskiya ba ki da alkawari, ni na za ta ma kin manta da ni." Bilki ta ce, "Haba jawahir ya zan yi na manta da ke, kin san tun ranar da muka zo nan gidan Haidar ya kore mu nake jin tsoron kada nazo na jawo miki wata fitinar. To sai da na ji labarin aurensa na so na zo sai na ji tsoron kada ya cire min kafa daya shi ya sa na hakura na fasa zuwa. Jawahir ta ce, "Yanzu ya aka yi kika zo? "Uhm ke dai bari, tare muke da direba munje gidan kawar Hajiyarmu kusa da ku ne na ga ba zan iya wuce gidanki ba. Jawahir tayi murmushi, "Amma gaskiya na gode na kuma ji dadin zuwanki, don akwai labari da labarai ma sai dai ga shi dare ne da za ki daure da kin zo min da rana mun wuni muna hira. Bilki tayi ajiyar zuciya ta ce, "Kina ganin in na zo babu wata matsala ko Haidar yana nan." Jawahir ta ce, "Ba komai wallahi ba zai ce miki komai ba. To shi kenan jawahir na fita kin ga dare ya yi sai na zo din "Okey Bilki na gode don Allah ina sa ido kada fa ki ki xuwa." "Insha Allahu zan zo" Tayi sallama ta tafi. Jawahir ta soya indomie da kwai ta gasa masa kifi ta hada masa lemon kwakwa da madara ta zuba a jug ta cilla masa kankara ciki ta jere komai a kan tebir din falon ta shiga sashenta ta ci na ta ta watsa ruwa ta wanke bakinta ta je ta yi kwanciyarta. Sai goma na dare su Haidar suka dawo. Kausar ta wuce dakinta Haidar kuwa ya nufi tebur din da abinci yake don yunwar da yake ji tun break din safe da ya yi a dakin jawahir. Ya bude komai ya ci ya yi kat, ya rinka shan lemon kwakwar nan yana nishadi a kasan zuciyarsa kuwa sai shiwa jawahir albarka yake. Da ya gama ya murda kofar dakinta yau ma a rufe gam, ya koma dakinsa yau ma ya kwanta yana murkususu da ya rufe idonsa kyakkyawar surar jawahir yake gani. Ga wata muguwar sha'awarta da tayi masa mugun kamu haka ya rinka juyi yana murkususu. Sai da asuba ya tashi ya yi alwala ya yi Raka'atainil Fajri ya yi ta karatun Alkur'ani ya yi addu'arsa ya shafa. Ya dade yana lazimi sannan ya sauko falon kasa ya zauna ko zai ga jawahir ta fito ya samu ya ganta ko zuciyarsa ta lafa da tsananin radadin kaunarta. Ya yi sa'a kuwa ta bude kofarta ta fito tana sanye da abaya da karamin farin hijab, da ya sha adon bakin les, tana rike da carbi a hannunta ta yi kyau kamar ita ta yi kanta. Duk motsin da tayi sai komai na jikinta ya motsa. Yanda jikinta yake girgiza shi yake dada motsawa da Haidar sha'awarta. Jawahir ta yi mamakin ganinshi a falon, don haka ta karasa gabansa tayi saurin xubewa ta gaisheshi. Ta mike ta nufi kicin idonsa na kanta. Ya ce, "Jawahir" Ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya ce, "Don Allah idan break za ki hada ki hada da mu."(HMMM GASKIYA JAWAHIR AKWAI HAKURI DON NA TABBATA A IRIN KISHI NA MATA BA KOWACCE XATA IYA GIRKI TA BAWA KISHIYAR DA ITA BA XATA YI BA). . (((((((SALON SO)))))) : (((((PART 26)))))) : . Ta yi dan dum kamar ba za ta yi magana ba sannan ta ce, "Kai da wa?" Ya ce, "Ni da Kausar" Ta ce, "Ko a musulunci dakin da ka kwana nan ne yake da hakkin yi maka abinci. To amma tun da hakan ba ta samu ba ni ya zama dole na hada maka, amma ita kuwa wadda ka ambata ban ga dalilin da zan girka mata wani abu na ba ta ba, don ba zamanta na ke yi ba, kuma ni na ajiyeta ba. Kafin ya ce, wani abu ta juya tayi komawarta dakin. Jawahir bata fasa hada break din ba don idan tayi kamar za tayi fushi sai ta tuno abubuwan da Anti Maryam ta gaya mata to sai ta daure tayi ko ba komai yanzu tana ganin nasara don kulawar da Haidar yake yi mata ba kaman a farkon aurensu ba. A babban falon ta shirya masa komai ta koma daki ta tsala wanka ta yi kwalliya ta gani a fada da wani tsadadden material ta yi kyau har ta gaji da kyan, ta sha adon gwala-gwalai kamar ka sace ka gudu. Kamshi ne yake tashi a kowacce kafa ta jikinta. Ta fito falon Haidar yana bisa tebir yana break shi ma ya sha tsantsarerren adonsa da shiga ta alfarma. Yana hango jawahir ya fara sambatu a zuciyarsa, "Subhanallahi! Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi kyakyyawar halittar yarinyar nan, ko yaushe zan ga fuskar da zan latsa jikin yarunyar nan, har na gani gado daya da ita? Kai wannan rana da na suma dan dadi Tina daya daga cikin 'yan aikin Kausar ne ta zo ta kama kafar benen Haidar za ta hau, jawahir kuma sannan ta fito daga sashenta shi ne ta doka mata tsawa, "Ke zo nan Tina ta taho jikinta na rawa ta durkusa kasa a gabanta, jawahir ta ce, "Uban wa ya ba ki ikon hawa benen nan? Ko dakin sa'anki ne a ciki? Me za ki yo? Wa ya aike ki? Tina ta ce, Anti ce ta ce na hau na share. Jawahir ta ce, "Wacece Anti?" Tina ta ce Kausar Jawahir ta ce, "Ke dabbar ina ce ko na ce mahaukaciyar ina ce da za ki zo ki haye dakin megida? Ko ku hudu aka auro ne ban sani ba? Tina ta girgiza kai, "To wallahi ki sani wannan ya zamo na farko na karshe ko falon nan kada na kuma ganin dayar ku ta zauna a ciki, da kun shigo ku yi wajen uwar dakinku ko kuma ku yi zamanku can bangaren masu aiki don ni ba zan yarda da kwashe kwashe da tarkace ba. Tina ta ce, "Ki yi hakuri Anti zan kiyaye gaba." Jawahir ta ce, "A'a ni ba Antinku ba ce, ga Antinku can wadda ta kwaso ku ta zo ta zube ku. Ya kamata a ce kuna gidan mazajenku kuna bautar aure amma ga shi kuna zaune kuna bautawa wata katuwar banza, don kwadayi, wato kun fi kwadayin abun duniya da rahamar Ubangiji ko? Tina ta girgiza kai, jawahir ta ce "To ki gayawa ragowar 'yan uwanki ku yi kokari ku fito da mazaje a yi muku aure ku je can ku samu 'yancin kanku ku yi wa Allah bauta. Tina ta rissina tana cewa, "Mun gode Anti insha Allahu za mu gabatar da masoyanmu. Jawahir ta yi mata izinin tafiya ta fita. Haidar yana zaune yana jin su ko ba komai zuciyarsa ta yi dadi da kalaman da ya ji jawahir tana yi yana alfahari da hankalinta. Gefe daya kuma yana tunanin ko dai jawahir ta fara son sa ne don ya ga kamar tana kishinsa, to Allah ya sa haka ne. Kausar ta bude kofar sashenta ta fito tana yamutsa fuska ta dokawa jawahir harara ta nufi wajen Haidar tana yamutsar fuska irin ta marasa lafiya ta ce, "Darling cikina fa ya ki daina ciwon kuma sai na rinka jin kamar yana harbawa ko cikin wata biyu yana fara motsi ne? Haidar ya kamo ta ya zaunar da ita kan cinyarsa, "Kausar kada fa ki wahalar min da baby, ba kya son cin abincin ne yunwa ce take sa shi motsin dole bude bakinki na ba ki, ki ce. Ta bude ya zuba mata, "Yauwa kausar ko ke fa ai gwanda ki ci. Jawahir ta ji wani katutun bakin ciki da kishi ya tokare mata makoshi, lallai ma tsanar da mutumin nan yake yi min ta kai tsana, duk tsawon lokacin da na dauka a gidansa ya kasa kusantata amma daga zuwan wata har ya ba ta ciki, wallahi ba zan yarda ba sai dai a yi wacce za ayi." Ta nufi gun su gadan-gadan a lokacin da Haidar ya sa mata cinyar kaza ke nan a baki jawahir ta tankwabe tare da dankar wuyan Kausar ta ce, "Wallahi sai ta yi amansa, ai ni ba baiwarta ba ce da zan yi mata girki ta zo tana ci." Haidar yayi yayi ta sake ta taki shi kuwa ya fitar da hannu ya shara mata mari. Jawahir ta yi saurin cika Kausar yayin da ta dafe kuncinta zafin marin ya gigita ta inda ta rarumi faramtin tangaran me nauyi ta kwadawa Haidar a gabansa tuni Haidar ya dafe wajen ya kwalla kara ya zube kasa. Hankalin jawahir ya yi mutukar tashi da ganin halin da Haidar yake ciki sai ta sa kuka na shiga uku yaya, Yaya don Allah kayi hakuri wallahi ba da sanina na yi maka ba, Yaya ka yi hakuri ka tashi na tuba na daina ba zan sake ba. Kausar kuwa kofa ta nufa ta kirawo megadi da yaron gidan suka kama shi suka sa shi a mota ta shiga ta tuka motar suka tafi asibiti. Aka kama shi aka shigar da shi daki suka tsayar da Kausar a waje can likitan ya fito ya ce ta je ta nemo dan uwansa namiji. Kausar ta mike ta shiga motarta ta yi gidansu Haidar. Ta yi salllama falon inda ta samu Abbansa da Anti ta durkusa ta gaishe su ta ce, "Daman Haidar ne ba shi da lafiya har an kwantar da shi a asibiti shi ne na zo na fada Cikin hanzari Abba ya mike ko direba bai jira ba ya fita ya hau motarsa ya tafi inda Kausar ta shiga tata motar ta rufa masa baya. Anti ta ce mata, "Duk halin da ake ciki ta yo mata waya ta gaya mata. Ta ce to. Lokacin da su Abba suka isa sannan Haidar yana bacci don haka Abban ya wuce office din Doctor, likita ya mike tsaye ya mikawa Abban hannu suka gaisa, sannan suka zauna. Likita ya ce, "Daman Alhaji larurar da take damun Haidar ce abin babba ne. Cikin firgita da dimauta Abban ya ce, "Me ya same shi? Likitan ya ce, "To dai a bincikenmu mun gano buguwa ce mai tsanani ya yi a gabansa wadda har ta jawo masa mutuwar gabansa, don ba shi da wani kuzari da zai iya kusantar mace bare ya iya biya mata bukatarta. Abban ya dafe kai tare da fadin, "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yanzu shi kenan dana ya nakasa? Likita me ya jawo masa buguwar.? Likitan ya ce, "Kada ka damu Alhaji za mu yi bakin kokarinmu na ganin ya samu lafiya ya dawo normal. Abba ya yi masa godiya ya koma dakin da Haidar ya ke ya zuba masa ido yana bacci. Jawahir kuwa tun bayan tafiyarsu Haidar asibiti ta kasa samun sukuni sai kuka take yi tana tunanin a wane hali Haidar yake yanzu, ta kasa samun sukunin zuciyarta. Kawarta Bilki ta yi sallama ta shigo, "A'a lafiya jawahir na ganki haka? Jawahir ta ce, "Kyale ni Bilki na bi ta dokin zuciya na aikata abin da zai dame ni. "Me yake faruwa ne?" Jawahir ta kwashe komai ta gaya mata. Bilki ta ce, "Wallahi ba ki kyauta ba, don yanzu Haidar son ki yake yi sosai da kin sani ba ki yi masa wannan dibar albarkar ba, don ba mutunci ba ne mace ta kai hannu kan mijinta da niyyar duka. Tace, "Uhm kyale ni Bilki zafin marin ne ya gigita ni ban san lokacin da na kwada masa ba, karar da ya yi ce ma ta dawo da ni hayyacina." Bilkisu ta ce, "Yanzu ba surutu za ki tsaya ba tashi mu je asibitin ki ga yanda jikin nasa yake. Ta ce, "Kai anya kuwa na je?" Ta ce, "Kwarai ma kuwa, ai tashi kawai mu tafi. "To ai ban san asibitin da ta tafi kai shi ba. "To bari na gano idan direban ya dawo sai mu tambaye shi wanne asibitin ne, ta yi waje. A can asibiti kuwa Abba ya koma gida Kausar tana waje, Haidar ya farka Faruk ya gani a gefen gadonsa a zaune, Faruk ya ce masa, "Sunnu ya kake jin jikin naka? Ya ce, "To da sauki zan ce, "Haidar ya yi tsu can ya ce Faruk ina jawahir?" Cikin mamaki Faruk din ya ce, "Me za ka yi mata? Haidar ya ce, "So nake na san halin da take ciki." "Me ya same ta?" In ji Faruk, Haidar ya kwashe yanda abin ya faru ya gaya masa, Faruk ya ce, haba Haidar me ya sa za ka mare ta? Ai kai ma ba ka yi dai-dai ba. Wallahi yanxu jawahir tana tsananin son ka tun da take yi maka duk abin da kake so, kuma take tsananin gudun bacin ranka, ga shi har ta kasa jure kishinta ta nuna karara. Haidar ka rage zafin zuciya in ba haka ba wata ran zai kai ka ya baro ka. Haidar ya ce, "Ai yanxu ya ma kai ni ya baro din, ni dai don Allah so nake yi ka je gidan ka gano min halin da take ciki inda hali ma don Allah ka rarrashe ta ku taho tare." . SALON SO ♡♡♡♡27 ♡♡♡♡ . Faruk ya ce, "Ba ruwana babu inda za ni bare ta zo ka ci mata mutunci ta zo ta rinka ganin h rashin kirkina. Haidar ya ce, "To ni ka kai ni wajen ta na ganta, Faruk ya yi murmushi, Haidar ko dai ka so ma son ta ne?" Haidar ya rintse ido ya ce, "Wallahi ban san lokacin da son yarinyar nan ya yi min dirar mikiya ba, ya shige ni. Inna kwanta da daddare Allah Allah nake gari ya waye don na ga kyakkyawar fuskar matata kuma kanwata, wallahi ni kadai na san yanda tsananin son jawahir yake raina, kai abin da na yi wa Kausar a gananta ma na yi ne don na auna na ga tana so na kuwa ko ni kadai nake shirme na. Faruk ya ce, Ka ga irin abin da na so ka gane tuntuni ka ki, to yanzu kuwa in ta ji halin da kake ciki sai ta ce don ka ga ba za iya kwanciya da ita ba ne, shi yasa ka nemi shiri da ita. Haidar ya ce, "Ai likita ya ce zan warke fa". Ko da yake yanzu ne lokacin tantance wanda take sonka don Allah da wadda a kayi auren sha awa. "Haidar ya ce, Ni dai don Allah ka je ka taho min da sahibata ko don na ga halin da take ciki. Faruk ya ce, "Zan je ai yanxu Kausar ta turo kofar ta shiga fuskarta a murtuke babu alamar fara'a, ta je gefe daya ta zauna ba tare da ta kula wani a cikinsu ba. Faruk ya mike Haidar bari na je in dawo ko? Duk yanda muka yi zan zo ka ji. Ya ce, "Don Allah ka je fa yanzu kada ka ki zuwa ka ji. Faruk ya ce Insha Allahu kuwa yanzu zan je. Faruk ya fita ya bar su Haidar ya juya ya kalli Kausar ya ce, "Me ya same ki ne na ga kamar ranki a ba ce? Ko cikinne yake ciwo?" Ta zumbura baki, "Kai yanzu har ka manta da barnar da Jawahir ta yi maka a jikinka har kake cewa a je a taho da ita? To wallahi ni ba zan yarda ba don ta ga ita ba ta da amfani a wajenka shine za ta nakasta min kai, wato ka zamo marar amfani, to wallahi ba zan yarda ba don ita ma sai na nakasta ta, sai dai duk abin da za a yi a yi." Haidar ya daka mata tsawa ya ce, "Ke ki shiga hankalinki kina ganin duk da son da nake wa jawahir da ta yi miki abu sai da na yi mata marin da ta gigice, to wallahi ki shiga hankalinki idan kika sake kika taba min mata wallahi sai kin yi mugun raina kanki, don sai kin yi mamakin abin da zan yi miki." Ta mike ta yi waje tana kunkuni ta zari mota ta nufi gidan Yakumbon Haidar wato kakarsa ta wajen uba, ta je ta zayyane mata maganganun karya da gaskiya ta gaya mata, Yakumbo ta hau sababi ka ji mu da tsinanniyar yarinya don ba ta son sa shine take neman hanyar kashe shi, to wallahi bi ba yarda zan yi ba, tashi ki koma asibitin gani nan zuwa yanzun nan, "Kausar ta koma asibiti ta tarar su Anti da Momy da su Yaya Abba sun cika asibitin taf, ana ta jajen abin da ya faru. Shi kuwa Faruk da ya je gidan Haidar yayi sallama falon, su jawahir suna daga kicin suka amsa sallamar suka fito falon, Faruk ya nemi waje ya zauna jawahir da Bilkisu suka gaishe shi, faruk ya ce, Haidar ne ya turo ni na zo na ga halin da kike ciki in kuma da hali ki zo mu je yana son ganinki. "Jawahir ta sunkuyar da kai ta ce, "Gaskiya Yaya Faruk ba zan je inda yaya yake ba, don in na je ban san irin wulakancin da zai yi min ba, ka ga kuwa da na je ya bata min rai ai gwara ban je ba. Faruk ya ce, "Wallahi Haidar yana wani hali na mutuwar sonki kin san miskilancinsa ya rasa ta hanyar da zai bi ya nuna miki Kaunar da yake miki don yanzu da kin ga irin magiyar da lallamin da ya rinka yi min sai na zo gare ki dakin tausaya masa. Kafin ta yi magana Bilki ta ce, "Faruk bari mu karasa girkin da za mu kai masa sai mu fito mu je." Faruk ya ce, to shi kenan bari na je na dawo. Bilki ta zuzzuba komai a fulas ita kuma jawahir ta je ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin atamfa ja! Super Holland dinkin filet ne ya kama jikinta sai zani da dankwali da ta daura, farar hoda kawai ta shafa a fuskarta sai dan man leben da ta shafa ta dauko jan mayafi da jan takalmi ta saka, kunnanta fashon din yari ne me jan dutse a tsakiya. Bilkisu ta tafa mata "Amma yarinyar nan kin yi kyau, kwalliyar taki ta burge ni sai dai kash kin manta a shafa hadin turarukanki. Jawahir ta yamutsa fuska, "Kin san fa inda za mu je za ki ce na shafa hadin turare. Bilki ta ce, to meye ba wajen mijinki za ki ba, ai gwanda ki shafa turarukan da kamshinsu zai gigitar da shi kuma ga karin lada a wajen Ubangiji, don duk sanda mace ta yi abun da zai farantawa mijinta har ya ji dadi a ransa to Ubangiji zai ba ta ladan da ba ta san adadin yawansa ba. Jawahir ta ce, Haka ne bari na shafa don na fuskace shi yana son kamshi. Sun jejjera fulas-fulas din a dan kwando me kyau ta lullube shi da farin yanki me adon bakin les da fulawoyi a jiki. Faruk ya dawo suka dunguma a motarsa zuwa asibiti. A lokacin ba kowa duk sun tafi sai kausar kawai da take zaune kan kujera tana karanta jarida, ba ta daga kai ba balle ta kalli wani a cikinsu. Faruk ya ce, "To ga ta nan na cika alkawari ko, ga ta na kawo maka Haidar ya yi murmushi ya ce, "Ai kuwa na gode Bilkisu ce ta fara gaishe shi tare da yi masa ya jiki. Cikin fara'a ya ce, "Ai jiki Alhamdullahi." Jawahir ta durkusa cikin dari-dari da rawar murya Kamar mai shirin kuka ta ce, "Yaya ina wuni? Ya jikin? Ya ce, "Lafiya lau jawahir ya naki jikin.? Ya sa hannu ya dago ta daga tsugunnun ya shafi kuncinta, ya ce, "Wai haka kuncinki ya tashi hannuna ya fito radau na marin da na yi miki, sorry Babyna ki gafarce ni, "Kafin tayi magana aka turo kofar aka shigo tare da sallama, Yakwalkwal ce ta shigo rike da hannun Sayyid. Sayyid ya fincike da gudu ya nufi jawahir yana cewa, "Anti na anti na, shine rannan kika gudu unguwa kika bar ni ina ta kiran ki ba ki zo kin tafi da ni ba. "Jawahir ta dauke shi ai yau da kai zan tafi kai ta kwana a can ko? Jawahir ba ta ankara ba ta ji saukar mari a kuncinta, Yagwalgwal ce ta kuma hau fada, "Annamimiya me kuma ya kawo ki wajen jikana kin so ki kashe shi, Allah bai baki nasara ba shi ne kika biyo shi nan ki karasa shi ko? Haidar kuwa tuni ya diro daga gadon jinyar ya tare jawahir yana cewa, "Haba Yagwalgwal ya za ki doke ta ita ma fa ba lafiya ce da ita ba, me ta yi miki?" Yagwalgwal ta ce, "Ubanka ta yi min, shege sallamamme so kake yanda uwarka ta mallake Alhaji kai ma jikan mallake ka za ayi, "Yagwalgwal ta ci gaba da nuna jawahir da dan yatsa tana yi mata sababi, daga yau na gaya miki ba ke ba Haidar in ke mayya ce ki ci kanki da kanki, haka kawai hankalinsa ya kwanta yana zaune da matarsa lafiya za ki zo ki bata musu zama. Jawahir ta mike jikinta ba kwari za ta fita Haidar ya yi saurin riko hannunta yana cewa, "Haba Yagwalgwal ya za ki zo ki korar min matata ki ce sai ta tafi? Ai ba ita ta kawo kanta ba ni na sa a je a dauko ta in ta tafi waye zai yi jiyya ta? Kawai mutum da matarsa a nemi raba su. Kan ya rufe baki bakinsa Yagwalgwal ta ba shi nasa marin ya dafe kunci ita kuma ta ci gaba da sababi tana nuna shi da dan yatsa, "Ka shiga hankalinka ka san da wacce kake magana, idan ba ka san ciwon kanka ba ai ni na san ciwonka, yarinya ta nakasa ka ka zamo marar amfani amma ba za ka guje ta ba, wata rana ma ranka za ta raba ka da shi. Jawahir ta fincike hannunta ta yi waje cikin sauri Haidar ya yunkura zai bi ta Yagwalgwal ta rike shi, Bilkisu ta bi bayan jawahir yayin da Faruk ya rufa musu baya. Da kyar da ban hakuri ya shawo kan jawahir ta shiga motarsa don ya mayar da su gida. Faruk ya ce, "Don Allah don Annabi jawahir ki yi hakuri da abin da tsuhowar nan ta yi miki. Jawahir ta yi saurin katse shi, "Haba yaya Faruk ka fi kowa sanin ta yanda a ka yi aurenmu da yaya, ba son sa nake yi ba na aure shi don biyayyar iyayena na zo nake zaman hakuri da shi, ya tashi ya dankaro min kishiya ni duk hakurin da na yi a kansa ba a gani ba kenan. Fashe da kuka Faruk ya ci gaba da rarrashinta ki yi hakuri jawahir ki tuna aure kike, aure kuwa bautar Ubangiji ne kada bacin ran wasu ya sa ki sabawa megidanki kin ji?" Yanda na san ki da hakuri da ladabi da biyayya ki ci gaba da yi komai me wucewa ne wata rana sai labari kin ji?". Ta daga kai ya ce, "Yauwa ko ke fa gobe ku shirya da wuri sai na zo na kai ku ta ce to. Ya sauke su a gidan shi kuma ya koma asibitin shi kuwa Haidar tun bayan fitarsu jawahir da Yagwalgwal ta rike shi don kar ya bi su gado ya koma ya kwanta ya yi rigingine ya rufe idonsa. Maganar duniya babu wadda ba a yi masa ba amma ya yi musu shiru ko motsi bai yi ba dole suka gaji suka hakura suka bar masa dakin. Faruk ya shigo ya dinga lallaminsa yana ba shi baki tare da va shi hakuri sannan ya tashi ya jawo kwandon da jawahir ta jero masa kayan abinci. Dakakkiyar sakwara ce lukui da miyar agushi mai wadataccen nama, sai jalof din taliya da lemon kwakwa. Haidar ya ce, "Ka ga yarinyar nan da zan bata mata rai ba za ta ki yin abinci ba don gudun kada ta bar ni da yunwa."

Chapter 7 of 13