Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jaye kuma wani hasken fatane dashi mekyau shiba fari bane kaitsaye tas aa tsabar hutu dajin dadine yasa fatar tasa tayi haske take daukar ido duk family mlm umar siyam yafisu kyau yanada doguwar fuska da dogon hanci sai idaninsa manya sundan lumshe kadan yadda ko kallonki yake saiki tsamman bacci yakeji ko kicema dan iskane sanda yana yaro malmar makarantarsu tasha xaneshi tace kallon soyayya yakemata ko tace wannan yaron dan iskane harsaida Abba yaje makarantar yayimusu bayani 'yan matankwa dasukeson Siyam kuwa sunadayawa domin kuwa mutum ne mai farin jini sosai gashi da daukar hankalin 'yanmata akwai wani lokaci dayaje wurin hutawa sbd yasha iska lokacin daya gama karatunsa ne yadawo nigeria yashiga awani shegen mota kalan shaddan sa yelo ne amma maikamar xuma xuma dinkin yamasa kyau glass ne a idonsa fari tass kawa medical wasu yanmata dake tsaye gefen ruwa suna Shan askirim kowacce kallonsa take sna santin kyau irin nasa kafin kice me saijinsu sukayi acikin ruwan tummmmmbullllllllllll aikwa wurin dayake najama ahne sai dariya hhhhhh itakuma wata tashigo damotarta kafin taisata parking space idonta yagano Mata Siyam tadafe kirji woww bakidaya tamanta da tuki take aikuwa motar tatafi tadaki wani runfa saura kadan tataka wata budurwa hakuri tabata sannan tagyara parking in tafuto tana iyayi tanufi inda Siyam yaxauna yana latsa wayarsa Assalamu alaikum Baidagoba barema yakalle ta kamar baxai amsaba saikuma ya amsa chankasan makoshinsa bawani jitayiba Wa alaikisalm Tai murmushi Sannu mlm yahutu Lfy ya amsa atakaice yanamike xaikaraba tasha gabansa Pls koxansan sunan SA nisunana sufiyya sulaiman kabeer Yakalle yawatsar yana gyara xaman glss insa Mexan toh dasunanki kinga inkingama xubar sai anjima Takuma Shan gabansa Bangamaba banajin kuma xangama pls inasonka wlh tunda nadora idanuna akanka nakamu da masifar soyayyarka Sauke Mata wani wawan mari yayi Wanda yadauki hankulan duk mutanen gurin yaja tsaki yafuce Sufiyya sulaiman kabeer tai murmushi tana cewa Saikaxo hannu xanrama wlh baka ci blss ba Tundaga wannan lokacin sufiyya sulaiman kabeer tasa brister aranta dakudurin aurensa Kota halin kahka. Abudaya yataka mata birki shine karatu, ...... Farinciki ne yabayyana aa fuskar mummy tarike hannun Siyam tana murmushi Agaskiya naji dadi Siyam sannan kuma nayi farinciki mutika dajin cewa Mowana kakeso axahirin gaskiya wannan abu yayi mun dadi kuma insha Allahu xata xama mallakin kace ita din yanxu inaso kafadamun yadda kukayi da ita idankaga kuma kundai daita shikenan Abbanka ashirye yake kodayaushe dayanemo maka aure Yafara sosakai Ai mummy tana sona natabbata sbd mundai daita Tohm allahamdulillahi ai kaga shikenan xanma Alhaji magana Tohm mummy na ADEEL Yau kam natashi cikin farinciki da kuma wani shauki wanda bansan namayeba momma tace keko yau bansan wanda abun farinciki ne yasamekiba duk kincikani da wakoki tundaxu daga wannan kikama wannan Tai dariya Ai momma kedai bari inaga kudifa xansamu sbd wannan farincikin nawa yayi kama dahaka Momma tai dariya Kai kedadina dake surutu kudi ajiyewa toh kikayi da xa kidauka toh memazakiyi dakudi naga kina da na kashewa wadanda yaron kirkin nan ya baki Adeel Eh nasani amma saura dubu biyu kuma ni kudin siyan babbar waya nake magana yanxu shiyasa kikaga nake ta farinciki Tohhh babbar waya kuma Mowana tohm Allah yakawo mebaki Amin sallamar Adeel ce tasa nafada daki dasauri nasako hijabi sbd best ce ajikina kuma batawani rufemin jiki sosaiba Araina ina addu ar Allah yasa baiganni ba Nafuto mukagaisa bayansungama gaisawa da momma yakalleni momma inasonyin magana da Mowana awaje inbadamuwa, Aa bakomi Adeel aikamar yayanta kake tashi anakiranki Yafuta nabi bayansa inadan tsuke fuska Meyabata miki rai Yatambayeni Babu komi tunsafe natashi ahaka Tohm kisaki ranki inason magana dakene kuma tanada muhimmanci Xuciyar mowana har wani fat fat take sbd sanin abundaxai futo daga bakinsa lallai tanacikin fargaba batajin sonsa aranta amma tanajin kaunarsa amatsayinsa namai tausayinsu ita da mahaifiyarta kuma Adeel mutumne maikirki dasanin darajar mutane. Naga kamar xantakura miki bari naxo nakoma kicewa momma natafi Tatsinci maganar Adeel gab daxai bude motar yashiga tarike murfin Babu takura atsakanin yaya dakanwarsa kayi hakuri banaso kabata ranka Yakalleta yanakara kallonta kamar yadauketa yagudu sbd dadin jin abundata fadamasa saiyaji tamkar yafurta mata kalmar sone ta amince bude motar yayi yashiga yananumata itama data shiga Bayansun xauna yakalleta tadan sunkuyar dakai Mowana kifahimceni dakyau dan Allah akan maganar daxanfadamiki nayi iya kokarina domin ingacewa najure nadanne abun araina amma wlh abun yagagara babu wani dabara agareni tunda banida damar hana kaina yi, amma ina tsoron wannan ranar dataxo yau gashi har taxo ranar daxan sameki damaganar bansan amsataba bansan makomar kaina ba agareki daxaran kinji komai kimin alfarma wacce ita kadai nake nema kimin yahada hannuwansa guri daya tamkar mairokon wani abu awajenta "Mowana inasonki wlh inasonki so irin wanda yafi karfi arufe sa. Dan Allah ki amshi soyayya ta koda bankai yadda kike fatan mijin daxaki aura yakasance ba, nasan akwai wanda kike so wanda xuciyata har yanxu tagaxa chanko sa amm,,,,,,,, Tadaga masa hannu tanajuya masa baya tare da dafe kanta daduk hannayenta "Yaya Adeel ada naso wani amma ayanxu babu wanda nakedashi axuciyata, wacce alfarma kakeso nema agurina inyimaka sbd cancantarka Tamkar yaxuba ruwa akasa yasha dan dadi Ki amince ki aureni sbd inasonki kuma xan iyarayuwa dake har abada Bude kofar motar tayi tana sauka sannan tajuyamasa baya tana rufe fuskarta Indai wannan ce alfarmar nayimaka amma kabari xangayama momma sai yadda tace sbd itace gabadani kuma uwata ubana ahalin yanxun, sai kuma hawaye taruga gida dagudu Tana shiga tafada jikin momma tanamai cigaba da kukan Menene dalilin kukan mowana yakunfita tare da Adeel yanxin kuma kindawo min kina kuka meyafaru ko kinmasa wani abun yamareki danbajin magana kikeba Yagirgixa kai Momma baduka na yayi ba cemin yayi wai yanaso na xai aure ni idan na amince Farinciki yabayyana afuskar momma tadagota tana murmushi Allahamdulillahi ai abu yayikyau Adeel aiyaron kirki ne kuma duk inda yafuto dan mutanen kirki ne mekikacemasa ke Tana sharar kwalla tamike xaune sbd ganin yadda momma ketafarin ciki dajin xancan saitaji bataso taga farincikin yadauke xataso mahaifiyarta tadauwa ma acikinsa sbd tadade bataga haka atare da itaba kusan tunkafin babanta yarasu. Momma dama kafin yafadamun yacemin alfarma xainema awajena nikuma jin haka sainace na amince sbd yafi karfin haka awurinmu, xamu xama butulu mutkar nakaucewa bukatarsa amma yanxu kome kikace shixa ayi saikin amince wancan alfarmar yaxama anyi inbaki aminceba nima haka. Aa na amin ce Allah yasa haka yafi alkhairi sannan kuma Allah yabarku tare kinji saiki takatsantsan karkuma yaga kamar dan yanada kudi muka amince masa Nima naitunanin haka dafarko amma kuma naga kamar daga wajensa baya tunanin haka shiyasa nima nashare kuma shima aiyasan bamuda kwadayi tunda saunawa xaibaki kudi kiki karba saidai ya aje ko yakawo mana kayan abinci ni bana ganin haka atare dashi kawai dai inatsoron ahlinsa bansan wa 'yan da iri bane kobasa son talaka nashiga cikinsu naxo naxama nama, Momma tai dariya Banataba jinhaka ajikina mowana akan Adeel ki kwantar da hankalin ki xantamiki addu ah kema kirinkayi Allah sai yaxama gatanki ako ina. Toh momma Awatan da Adeel yafurta ma mowana soyayya yachanjamasu gida maikyau dan madaidaci maidakuna uku daya ciki da falo biyu kuma falle fallene ciki da falone na momma yasamata kayan daki masu kyau Falle dayankuma nagefen ta na mowana ne itama kayan daki yasa seti kalar blu komi har labulenta da bedshit sannan yasissiyo mata kaya masukyau kala kala mayamayan shafawa masu kyau kafun sutare watarana yaxo yadauketa amota yace xata rakashi gidan abokinsa bayansuntaho ne yakawota gidan tanata bude ido taga matar gidan amma bataga kowaba yace taleka dakin bayanta tabude tana lekawa taga dakin yayikyau harda yar kamar tv amannne abango komai nadakin blu ne takallesa Yaya Adeel wai gidan wanene kakwoni saidariya kakemun tunda muka shigo kanunamin nan kanunamin can kanacemin yayikyau nacemaka eh yayi amma banga matar abokin nakaba Yakuma sakin dariya yana xuwa inda take dayake akwai taxara tsakaninsu Karki damu xakisani muje namaidake gida Ko kallonsa batasakeyiba ta wuce tana waige waige Saiyadan biyota da gudu gudu kamar wanda xaikamata yana mika mata hannu aikwa takwasa dagudu tana dansakin kara mara sauti Yaya Adeel karkajafa nafadi Toh sarkin faduwa dayake kece audiga ko sainatare ki yaxanyi ni dakayana Takyalkyale dadariya tanaharararsa tashige mota yaxagaya shima yanadariya yatayar sukatafi yanajanta da hira, Balaifi tasake dashi kuma tana masa soyayya kuma tafara sonsa amma ana tufka tana warwarewa domin kuwa haryanxu Siyam shine aranta shikuma takeso hakikanin so tahakurkurtar da xuciyartane akansa sbd taga ciwonso xai iya kasheta Momma bakara min sawa Adeel albarka tayiba dayadebesu ko cokali baibari sundaukaba yace yaxubamusu komai sabo tayi kuka sosai nafarinciki Mowana ma taji dadin abundayayi musu sbd gidansu wancan din yakusa rushewa duk bangwayen sun tsatstsage ga damuna datashigo yanxu abun haryafara damin momma. Hubba harda kuka dadi ganin yadda rayuwar aminiyar tata tasauya dandanan taxama freesh taikyau tamkar ba itaba, hubba taitasawa Adeel albarka kwana tayi biyu agidan su mowana dayamma adeel dayaxo sukagaisa taita yabon kyansa wa mowana tana cewa aiyafima ME KYAU kyau wannan Mowana ita dai dariya kawai take ganin yadda hubba duk tabi tarude da Adeel amma taji dadin yadda aka koda mata shi itama saitaji yakara shiga ranta anan take tambayarta tadaina xuwa gidan hajia bera'u aiki tace tana xuwa har yanxu amma ml. Abubakar yace xaihanata sbd aurensu daya matso MOWANA taji dadi da hubba xata tafi tadauko kaya kala biyar tabata masu kyau dakudi 3000 sannan tarakota bakin titi tahau napep Adeel yafito daga office suka hadu da Siyam xashi wurinsa komawa ciki sukayi sbd ganin kamar siyam din akwai damuwa atare dashi bayansun xauna yadauko masa roban ruwa yamika masa tareda xaunawa kusa dashi Aida natashi gida xanyi kawai saigaka Yabude roban ruwan yakafa abaki yafara sha saidaya sharabi ya ajiye yanamaida numfashi kamar wanda yasha gudu yagaji. Koda kaje gida aixanxo gidan sbd kwana biyu bamasamu muhadu dakai tsawon satifa yau bangankaba saiyanxu bamu saba hakaba tunkafin mugirma adeel shiyasa yau nayi takanas nace bari naxo office inka inga lfy kuwa Adeel yayi murmushi yanajindadin yadda abokin nasa yanunamasa kulawa Wlh Lfy klau kawai harkokine sukayimin yawa kaga yanxuma abuja daddy xaitura ni gobe akan wasu kaya daxa ashigo manadasu ni inata Allah Allah inxo insameka amma abun bai yuwuba duk da nabari akan yau xanxo gida mugaisama da mummy kwana biyu tajini shuru Harararsa Siyam yayi yana mikewa tsaye Tohm ai shikenan yayikyau nibari nakoma kawai Adeel yabiyo bayansa bayan yakulle kofar jikin motar Adeel suka jingina yanacewa Inafa sane dakai Brister bakataba bina kaje kun gaisa da my kanwata ba kuma kodayaushe tanajin labarinka awajena tanaso ma taganka sbd tace dagani kanada muhimmanci awurina Siyam yayi dariya Karka damu xanje ai nikasan bason irin wannan harkokin na nanaye nakeba amma karka damu insha Allah inxakakoma xanbika Tohm shikennan ai shekaran jiyama su daddy harda abbanka sukaje suka nemo auren ranar sha uku ga watan gobe xa asamana rana kuma ni nace wata uku xa asa amma ita kanwartawa tace wata 6 takeso asa sainace mata aa duk bamu xamu saba kaixakasa saita ce tayarda ahaka mukarabu jiyafa Brister yayi murmushi Aikaima kasan inavayan tako tam donhaka yadda tafada xa ai kawai wata shida xa asa sbd bakasan menene uxirinta ba Adeel yafashe da dariya yana bude motarsa yashiga Kai Brister bakadadama aiwannan sonkai akenunamin nagode hakan xa aikawai nabi taku tunda kunfini yawa, Shima Siyam motar sa yahau yana cewa Ahto aitafika gaskiyane Daganan Adeel gidan su mowana yayi acan yayi sallar mangaruba sannan yatadamusu da jen. Tana kallon sa yana mata nuni databiyoshi kofar gida amma taimasa dariya tashige dakinta tanafadawa saman gado Biyo ta yayi yana tsayawa akofa yarike kyaure Kanwata Tadan tashi xaune tana murmushi Na am yaya Adeel ainaxata katafi danaga kayi hanyar kofar gida Wlh kinmaidani kakanki donnaga kinamantawa cewa kinkusa xama matata ko Tadan rufe fuska Bana mantawa ai yayana saboda wannan airanace tadaban kuma babbar rana agaremu nidakai ranar daxan daga kai na kalleka amatsayin mijina Yaji dadi yasa yahura mata kiss da hannu Kefa akwai baki da jera magana kinga yanxu wannan kyakkyawar maganar taki kadaitasa naji tamkar nikadai ne namiji aduniyar so, yakamata nabaki tukuici kanwata Mikewa tayi dasauri takaraso gabansa Aa bari bari tukuicinka bayanxu ba don baxankarbaba, xanjira har sai lokacin da namaka abundaxaka bani tukuicin kanka bakidaya toh saina karba sbd shikadai yarage mun namallaka agurinka insoyayya ce nasamu har bansan tayaya xanfara kwatanccen taba, Dadi yarufe sa Gaskiya samunki arayuwata yahayfarmun da farinciki maikyau indai kainane aikinsamu dama ainidin nakine kuma kema kinsani amma jan magana irin naki yasa kike kawo shakka acikin kyautar dana dade dayimiki ita, toh xankara fadamiki domin baxangajiba inasonki kuma namallaka miki kaina Ta rufe fuska tana tsalle Xahiri kai abinso ne da alfahari agurin dikkan 'ya macen data sameka arayuwarta Kece ai sbd kitabbatar dahakan nake kara addu ahta kullum akan Allah yamatso da abunnan ayi ayi ahutakawai muma musamu 'yanci ko. Juyamasa baya tayi tana diddira kafa Nibana so gaskiya kadaina addu ah banaso narabu da momma haka dawuri pls Yayi dariya tare da tsokanarta Aikwa yaxama dole yarinya donkwa saikinrabu da ita kuma kwanan nan Aikuwa taxube kasa tana kuka tana turturja kafa Nafadamaka ni baxan rabu da momma ba dawaxata xauna nice kadai takeda ita Share mata hawayen yayi tare da lallashi maicike da soyayya aikwa saigata tana dariya sosai momma ce takirata awaya taje tadauko masa abinci yaxauna yafaraci yanasanti itakuma tana masa dariya tana tsokanarsa Saiwajen karfe 10:00 yatafi sina kewar juna, Yaukwana biyar kenan dasa ranar Mowana da Adeel shakuwa tsakanin su kara karuwa take musamman daga wajensa Mahaifin hubba da malm garva liman din masallacin juma ar su ne suka amshi kudin Mowana suka tsayamata amatsayin waliyyanta, momma taji dadi kuma tayimusu godiya sosai. Game da gidan kuma su Adeel bamatsala domin kuwa Adeel baiboye musu komai bagame da mowana kuma dady ya amince akayi komai saudaya ta taba xuwagidan su Adeel yakawota suka gaisa da mama mamatayava da mowana sosai hartaji cewa danta yayi dacen mace maikunya kuma dagani xatayi kirki Aslamiyya kuwa dayafadamata taji dadi dagalokacin xuminci tsakaninta da mowana yakullu sosai Adeel yasiyama Mowana waya babba Iphone 6, faratas aikuwa ranar murna wajen Mowana ba acewa komai. BAYAN WATA UKU atsaye yake tamkar wani soja yafi awa daya xagaye gurin yake kawai yana tunanin yadda rayuwansa yachanja bakidaya yajinginata ga soyayyar wacce tabacewa rayuwarsa bat! Baikara ganintaba. Har yanxu ciwon sonta yakamasa iyakwatanta sa bakaramin aiki bane domin yayi yawan dayasha masa kai, yadda Siyam yakejin Mowana aransa yanxu bakaramin rubutu bane wanda xa agama yanxu so nabar wa maikaratu ya auna yaga kamar yaya makaho yake son yasamu idanunsa yake kasancewa toh Siyam yafisa bukatar son sake ganin mowana arayuwarsa kodakwa baxata taba amsar soyayyarsa ba, burinsa yasake ganinta. Aranar bai iyatabuka komaiba a office din haka yadawo gida bayan yayi wanka yashiga wajen momma Tare yasameta da Abba ransu abace sai momma datai tamkar taikuka tana ba Abba hakuri shigowarsa tasa duka sukadawo da hankalin su kansa yadurkusa xaigaidasu Abba yadagamasa hannu Basai kagaisheniba kabar kayarka natabbata alfy kaganni tunda gani atsayema toh ya isa baxansake amsa gaisuwarka ba Siyam mutkar......... Siyam yaruga yana rumgumesa tare da rufe masa baki yafashe dakuka yayin mummy ma shitakeyi Dan Allah Abba kayi hakuri dan Allah da annibin sa Annabi muhammadu (s. A. W.) Me na aikata haka Abba daxan kasance haka yau agurinka komi namaka kayi hakuri kayafemin baxansake ba wlh Abba nayimaka alkawari Xakasake mana tunda kadan daga cikin aikinka kenan baxan hakura ba kuma ina kan bakana wlh mutkar bakanemo matar aure asatinnan ba wlh bani bakai xanfita aharkokinka duka saikuyi ta komi da mahaifiyartaka tunda naga bakinku daya sokuke kumayar dani karamin mutum a idon jama ah bila adadin tohm nakyaleku dik yadda maxakuyi kuyi nadaifadamaka sati daya Yafuce yabar falon ransa abace yahaye sama, Juyowa Siyam yayi wurin mummy wacce hawaye keta bin fuskarta kamar ba gobe durkusawa yayi yana kama kafafinta yafara rera nasa kukan Dan Allah ki yi hakuri mummy kije kiba Abba hakuri naga ransa yabaci sosai Sakani kasakarmin kafa Siyam nadawo daga rakiyarka nima wlh wannan mugun halin naka nawulakanta 'yanmata gashi yau yajawo maka mummunar fahimta tsakaninka da babanka abin harya shafeni wannan wacce irin rayuwace nadauko mana Siyam wlh baxanhanasa hukunta ka ba kowanne hukunci yadauka akanka amma kasani baxakahadani da mijina ba tunkafin na haifeka lfy nake dashi chachar baki wannan bantaba yida shi ba silarka xakajawomin matsala ko, toh xakwa kurasa ni duka dagakai harshi baxan iya rigima ba niban iya tashin hankali ba siyam da wanne xanji dasu mariya matansu kawu ko da rigimar Alhaji. Ga kunyar maman Ismat dako ita ta isheni kajawo wargajewar abotar mu da ita. Siyam mekakesoni kaxama ashekarunka yanxu bakai aure ba toh sai yaushe karkamanta yanxu fa kakai 35 ys, sokake sai duniya tagama xaginmu akan munsa maka ido yau kimanin wata uku kenan kaxo kasameni da maganar Mowana na amince amma bansake jinmaganar ba. Kadubeka kaga yadda karame kaxama tamkar wanda yarasa wani muhimmin abu. Bakason magana abinci ma mai aikin wajenka takawomin korafin bakason chi mutuwa kakeso kayi ko mekake nufi wanda mumuka kasa ganewa. Yafashe dakuka yanafadawa jikinta Abunka da uwa da dah. Ta rumgume sa tana share masa hawayen Kai jarumine Siyam tunkana karami duk shagwabarka kai barago bane duk abin daxai saka kuka toh kwa saiyakasance babbane kuma mai muhammanci bayan wannan abun dayake faruwa yanxu tabbas akwai wani akasan ranka wanda ka ajiyesa kakasa fada, dago kafadamun komi xakayimin dig girman laifin daxaka aikata agareni baxai hanani na aje makami nasaurareka ba sbd bakada kowa saimu shima Abbanka xaisauko ne yanxun ransane yariga dayakai kololuwar baci Mummy abundayake damuna yanada nasaba da maganar dakuke da Abba mummy ni mailaifine awajen mowana baxata taba amincewa dani ba sbd nacutar da ita kafin ta farga tabar rayuwata nanemeta harbansan adadin inda naje nemanta ba amma bansameta ba tayi nisa dani sosai harna fara yanke tsammani, Me kakeson fadamun Siyam dama bakasan wacece Mowana ba bakudai daitaba Kwarai mummy bansanta ba sai anan gidan nafadamikine sbd hankalin ki yakwanta kibar maganar Ismat, mummy Mowana kadai nakeso wlh xan iya mutuwa mutkar banganta ba, Mummy tai shuru tana tunani kafun tace Tabbas akwai lokacin dasukaxo neman aiki kuma su biyune dawata budurwar ita har yanxu tana nan Yayi wani xabura yana rike hannun mummy Dan Allah mummy Batare data kallesa ba tajanyo wayarta takira baba sukayi magana ta aje wayar baifi minti 20 ba dakiran baba tashigo tare da hubba abayanta suka xauna akasa mekyau yakalli hubba saiyatuno lokacin dayataba ganinsu tare hubba najan hannun mowana itama tana cijewa. Mummy tabbas wannan itace tare suke tasanta Hubba tatsorata tana xubewa kasa tagai da hajia bakin ta narawa taxata wani laifin tayimasa Kinutsu bakomai kinji tambayarki kawai xamiyi ina wannan 'yar uwar taki dakukaxo tare da ita dafarkon xuwanku gidannan Hubba tasunkuyar dakai Hajia Mowana Eh ita mekyau yayi saurin amshewa hajia tadalla masa harara Yawwa dan Allah xaki kaimu gidan sune yanxu Tasunkuyar dakai tana cewa Hajia Mowana tabani sako tunkafin wannan lokacin yaxo tace karnataba nunawa wani gidansu ko mace ko namiji Dasauri Siyam yamike yana daka mata tsawa Kaga malm dakata kaine wai kakirata ko kuma nice nakirata bafa nason wannan xafin ran naka fa, yakoma yaxauna yana harhade rai axuciyarsa kuwa dadi yakeji sbd ansamu wacce tasan inda Mowanan sa take donhaka komin tsiya saiyaje. Hajia bansan dalilin taba wlh amma ranar nan damuna hira danaje gidansu take fadamun cewa tunda ankusa aurenta nafadamiki bikinta dan Allah nace tohm xanfadamiki Kan Siyam ne yasara mummy kuwa takalli hubba kina nufin anbada ita kenan Kwarai mummy don bikin Mowana yarage wata uku saura kawai in Allah ya yarda kafun sukuma wata magana Siyam yafi kuma akan dan glas table din dake tsakiyar dakin gefen cikinsa yayanke da hannunsa sannan kuma ko motsawa bayayi Ehu mummy tasaki tanayo kansa hubba kuwa kuka tafarayi tana tashiga uku, Abba ne yafuto da gudu yana ganin halin da Siyam keciki shima yarude yadagosa mummy takamasa hannayensa suka futa dashi sai mota Abba dakansa yake tukin. Hubba kuwa waje tayi tatari mota saigidansu sbd baxataje tafadawa Mowana ba tata mata da hankali ansamu talafa har xata auri wani. Game da su'adaat kuwa tafara sarewa da lamarin Siyam domin kuwa taga kota kanta baya bi tasha vinsa har office tabashi hakuri amma ko kallo bata ishesaba haka xatasha kuka tataso. 😢😢😢 Umma baxanfa iyaba abundakike so ayi vadin nan sbd brister yafini gaskiya acikin abun dayafaru kuma, wlh baidahakinmu Kinga Ismat kifito fili kifadamun gaskiyar abundakike boyemun idan bahaka ba wlh nisainadau fansar abun da Hajia taimun itada danta domin ba a isa atabani akwana lfy ba sbd wulakanci nixata wulakanta a idon duniya ta toxarta mu agama magana suxo ace anfasa maganar aure akanme saida nadora burina akansu wlh dasake anbaiwa maikaxa kai, Ismat hawaye suka xobo mata tarike hannun umma Umma banida kirki bankuma kyautama kainaba daku iyayena kuma umma duk sharrin shaitan ne da makircinsa son xuciya da nuna xalama afili shine yajawo dik wannan abun dayafaru umma nice na aikata laifi wa brister Nan takwashe duk abundayafaru tsakanin ta dashi ranar dataje gidansu na karshe Wani wawan mari umma tasauke mata tana huce tafara magana cike da masifa kincucini kinkuma cuci kanki don bayan burina naganin mun mallaki dukiyarsu kema ai kinasonshi kinyiwa kanki nikuma kinbata min bajat cemiki akayi kowa kedaukar irin wannan iskancin. Banxa shashasha. Umma kiyi hakuri dan Allah niyanxu nahakura da brister har munyi magana da ixxiddeen akan xaituro yace nafadamuku Harara umma tadokamata Dama ai abunda kika taka kenan kekikajiyo danni banga abin da ixxiddeen yake dashiba wanda xairikeki narayuwaba amma tunda haka kikaxaba nibadamuwa ta bace xanfadama babanki inyadawo duk yadda yace xanfadamiki saiki gayamasa amma wlh kincucini Ismat banxaton xaki min haka ba yanxu shikenan wasune xasu mallaki dinbun dukiyar da iyayensa xasu mutu subar masa. Ismat wacce yanxu tayi nadamar abundatayima brister tamike tana ba umma hakuri harta shige dakinta. Yau kwanan brister biyu a hospital anyi masa tritimnt din gurin dayasamu rauni gefen ciki da hannu Adeel ne agefensa mummy da Abba sunfuta xuwa gida sudawo Lokacin da jawwa takirani awaya take fadamun ai munfito daga meeting din kenan hankali na yatashi nayi kokarin tahowa alokacin amma wani uxirin yafado banjidadi ba brister yajikin Siyam dake dan kashin gide yana daddanna waya yadan motsa yana cije baki sbd wani mugun xafi dayaji agefen cikin nasa dasauri Adeel yarikesa yanagyara masa xaman Nagode ainasamu sauki ma Wayar Adeel ce tafara kuka dasauri yaduba sbd jikinsa yavasa Mowana ke kiransa aikwa yar halak din itace yafada axahiri yana dariya katsewa yayi yakirata Dagawa tayi tare dasallama cikin sanyin murya Yaya Adeel muntashi lafiya Yasaki murmushi Lfy klau kanwata ya gida Tarangwadar dakanta kamar yana kallonta Yaya gida lfy kalau amma kadawo ko Yakalli Siyam dake kallonsa tundaya fara wayar Saikin canka kawai naga kamar kinfara duba fa Yakyalkyale da dariya Kai yaya duba kuma aa wlh kawai jikina ne yabani sbd yau inatashi dakai nafarka acikin raina saikuma na fara jin kanminshin nan naka maidadi akusa dani ina kiranka awaya wannan alamar ne yanuna kana kusa dani Annurin fuskarsa yakaru kwata kwata yamanta agaban Siyam yake shikwa Siyam sai mamki yake game da yadda Adeel rayuwarsa ta chanja taikyau kodayaushe yanacikin nishadi. Kai kanwata amma najidadi hakan yanuna kodayaushe ina xuciyar ki daxu daxunadawo ko gida banshigaba naxo wajen brister hospital nadubasa yasamu rauni Wata uwar raxana tayi tananeman saka kuka amma sbd karya fahimci abundata boye wa saita dan nutsu amma muryar ta tayi mugun rauni Yaya Adeel me yasameshi Wlh yayankene da glas amma bansan garan yaya ba sbd kinsan tsautsayi baya wuce ranar sa Hakane Allah yabasa lfy kace inayimasa sannu Tana maganar tana hawaye amma taduntse tayadda baxai gane kuka take ba Kallon Siyam yayi Kanwata nayimaka sannu Siyam yadauke kai Kace mata ina amsawa amma bana amsar mike Dariya Adeel yayi yanafadamata Tadanyi murmushi sbd taji lokacin da Siyam din yake maganar saitaji gabanta nafaduwa taji abundaya dade da wuce mata yana neman dawowa Kanwata bari nabasa wayar kidubasa ko Aa yaya Adeel kabari inkadawo kaki rani nadubasan

Chapter 6 of 11