Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
masifa. Wani waje aka kaisu babu kowa sabone don ko budewa ba aiba saiyanxu da aka budemusu tanuna musu wani daki tabasu key sushiga xa akawo musu abinci, tatafi kamar jira taketaga fitar baba ta ja tsaki Banjidadin abindakikayimun ba hubba Yakamata kuma kisani sbd karki kara Maimaitawa, Hubba tashareta tana yingaba xuwa bakin kofar dakin da aka nunamusu tasa key tana budewa don itama haushin mowana takeji sbd abindatayi afalon hajia yayi yawa saikace wata sabuwar 'yar kauye yanxu da hajia taganta lokacin datake kallon danta watakila tahanasu aikin ma akoresu gida, taja musu asara, Fadowa dakin mowana tayi itama tana jin xafin shariyar da hubba taimata Suduka tsayawa sukai bakin kofa suna kallon dakin dasetin kayan kamar dakin mace guda gadone kato faffada dakatifa sai cover biyu da bandaki adakin sai fanka maikyau dalabulaye pick window da kofa dakinyayikyau don shima yahadu kuma babbane, Hubba ce ta bude kofar bandakin tashige nanma saidata gama kallon haduwarsa kafin tayi tsarki tadauro alwala tafito dadduma tadauko datagani kan drowan gefen bed din, tashinfida tatada sallar godiya ga Allah dayataimakesu yaugasu sune acikin gida irin wannan, Datayi raka ah 2 taroki Allah yasa abasu aiki maigwabi daxasu sami kudi sutaimaki iyayensu dake famada talauchi, Mowana wacce tanemi gaban gado taxauna bakwari sbd itakanta sama sama take jinta, wani abu mai dadine yake yawo acikin jikinta tare da wani sassanya abu dake xagaye akwakwalwarta daxuciyar ta akan saurayinnan datagani, yatsayamata arai, har ba abundayake wucewa tamakogwaronta bai tintibesa ba yamakyale amakoshinta tanajinsa tamkar yadda take jin yaji idan yafada mata ido, Hotonsa take gani a cikin idanunta yatafi da dik wani tanadinta yarusa dikkan shirinta yakuma dauhanyar chanmata rayuwa, Mowana Hubba ta dafata tana xammanawa kusa da ita Shuru tai tana kallon hubba kamar batasantaba sbd ba ita take kallo axahiri ba ME KYAU take gani, Kiyi hakuri da abindanamiki daxu banaso kibadamune awajen har hajia taganki tafasa bamu aiki saitai tsammanin mudin daga kauyemuke Mowana tai murmushi Bakomai hubba nima nai kuskuren aikata hakan dik da ba laifina bane narasa yaxanyi control inkainane awajen shiyasa Amma nasan bakiga abindana ganiba shiyasa bakiyi kamar yadda naiba, Hubba tace Aa naganshi mana ni baidadani dakasaba kyan nashi shiyasa daharkike furtamasa sunaa da ME KYAU Mowana tai dariya tanayiwa hubba kallonke baki da wayo Kafin tace Humm hubba wlh mekyau yayi kuma daga yau sunansa kenan awajena sbd naji abindabantaba ji akan wani dah namiji ba ajikina danai toxali dashi, Xantai miki addu ah dagayau domin nafuskanchi xaki fara abin daba halinki ba karki manta ke bakowa bace akan shi wannan saurayin dakikagani donhaka karki kuskuren ara ki yafa sbd kar abun yadamemu, Kash! Meyasa baki tuna haka ba sanda muna gida, saida mukaxo sannan idona yaga abincinsa, mai afkuwa ta afku ai tun lokacin dakwaran idanuna suka sauka afuskar ME KYAU, koda baxaki yarda ba wlh nakamu daso yau kuma daxu take! bansanyaya akaiba karki xargeni akan wannan al amarin nayi iya kokarina daxuciyata amma takwace min tunanin yakubce narasa makamin yakar sa koda bamai fahimtata xancigaba da kallonsa a idanuna, amma inason ME KYAU hubba, koda baxansake ganinsa ba daga yau. Hubba dake kallon mowana cike da mamaki da al ajab yau mowana ce kefurta tanason wani dah namiji dakanta, matar da batakaunar wani yafurta mata kalmarso yau ita ke begen wani daga kallo daya tak! Tabdijan lallai akwai wata sabuwa, Sallama wata yar matashiya tayi abakin kofar dakin tare suka taso suka bude kofa tiren abinci tamiko musu hubba ta amsa suka koma ciki itama ta tafi, Bayan sunsa tiren atsakiya wanda kedauke da kuloli biyu masu dan girma sai flet daya da spn biyu sai roban ruwa biyu, Bude daya suka sukaga soyayyar taliya jalb danama manya manyan yanka saidayar kuma farar shinkaface da miya adanwani karamin maxubi,, Cisukayi suka koshi suka sha ruwa sannan sukayi wanka lokacin anyi sallar xuhur sukatashi suka gabatar dasallar saikuma bacci yadaukesu sunyi bacci sosai mai isarsu xuwa karfe hudu darabi suka farka agurguje suka dauro alwala ganin lokacinta har yafice suna tashan bacci sukagabatar da sallar asari suka xauna, karasa abincinsu nadaxu saikayi, sannan hirar gida ta wanxu tsakanin su har akayi mangaruba suna xaune suna hira sallace tatashesu suna idarwa anakawo musu abinci, bayansunyi sallar isha i sika dan taba abincin da aka kawo musu kadan sbd basajinyunwa sunci ragowar nadaxu, Gameda siyam kuwa fitarsa gidansu Adeel yanufa kaitsaye asabuwar motarsa wacce Abba yakawo masa ita daga london jiya, Horn yayi akofar get in gidan lokacin Adeel yafito shima motarsa xaidauka apaking spice, yaje gidan su siyam din saikuma yajisa fitowa yayi kawai yana murmushi yabude gidan maixaman banxa yashiga yana basa Hannu Baxaka shiga kugaisa da mama ba dady mana nan Siyam yayi dan murmushi Xanxo takanas mugaisa yanxu idan muka tsaya ba lokaci sai kaga muncinye time in anan kasan mama dahira musamman tasameni Adeel yayi murmushi yanakara kallon abokin nasa Eh kwarai za ai haka kai mutumin mama, ya nagakamar ranka abace ne Siyam, fuskarka yanuna Key yayima motar kawai yana cillata titi kamarbaiji abinda Adeel din yace masaba Adeel yayi dariya afili Sbd yasan halin abokin nasa da basarwa duk da shidin nadamane duk sirrinsutare suke tattaunawa Ok nagane dik yadda akayikai da mum ne din mune Siyam yaharare sa Wlh donba mai mun irin wannan maganar daxata sosamin rai haka nace banason yarinyar nan banaso amma mumy tamatsamin akanta wlh Adeel banason su'adaat batamin atsarin matar daxan iya aureba. Look! Abokina badai haka kacema mumynba Siyam yana mai sauke wani xaxxafan iska daga bakinshi yace Aa banfadamata ba amma nayi mata magana like hakandin sbd hanninka mai sanda naitamata sbd kar takaiwa Abba xancannan, Adeel ya ce Kabari xamu sanyadda xamuyi kawai kaikam kacigaba dayima mumy biyayya, Ok, Yadagakai yana maikarawa motan gudugudu, Sai wajen karfe tara yadawo kamar yadda yasaba wajensa yawuce yafada toleit yay wanda yafito bayan yagama shafe shafen mai da turere yadauki wayarsa yasa chaji yarufe wajen yayi sashin mum Time din Alj, Abdullateef natare dahjia tana tayashi wani lissafi sbd sufi yin sauri bacci yafara kamasa ga gajiya Bude kofar yayi yashigo bakinsa dauke da sallama Atare suka amsa masa Fuskokinsu cike da nishadi Abba ya miko masa hannu suka gaisa yana jawosa kusa dashi yaxauna "Abba ya aiki? Ya dan bubbuga kafadar siyam Aiki Allahamdulillahi siyam yanaka aikin Abba yanakyau Masha Allah, yau kaxaxxaga gidajen gonan nan ko? Eh ai yanxuma haka daga canmuke natsaya amasallacin gidan su Adeel munyi sallah ne Ok "Mum Barka da dare Barka son yahanya? Yashafakansa momy Allahamdulillahi sakonki ma ankawosu nasa ashiga dasu stor Umhum tohm yayi kyau Abba ganin sunta maganarsu bashi yasa baki Siyam gobe ko xuwa jibi idan kahuta xamu xauna dakai akan maganar gidajen gonancan nasan akwai abun daba arasaba yakamata ayi sbd musamman gidan gonar dake wajen wudil naga kajin ciki kwanakin baya sun murmutu kusan dari uku da wani abu kuma bansa akai wasuba sbd inaso infara fahimta yaya abunyake ne mutanen bangama yarda dasu ba amma yanxu xandoraka akanharkar ne gabadaya,sbd ni harkoki sunyimin yawa Ok Bakomi Yadawo kusa da mome yanarike hannunta Mum masu kula da bangarena yau basu shiga sungyara minba Abba ya amshi maganar Ya akai haka hajia basu san aikinsu bane kome yasa yaudin basu gyaramasa part insaba Hajia tai murmushi Abban siyam maida wukar nimakaina bansan dalili ba kuma baba ke kula da ma aikatan gidannan kaf ita xatasan yaya akai kuma suwaye masu kula da wajen Dasafe asanyadda ya aka akasake maikula dawajen wadanda kuma keyida yau basuyi masaba nakoresu karwanda nadawo nasamu yana nan abasu kudin aikin wata uku sutafi, Hajia takallesa yadda ransa yabaci sbd antaba masa Siyam ita har mamakin irin wannan soyayyar take ta Ahaji da Siyam. Tohm shikenan xanfada mata alaluboko suwaye xa ai abundakace amma kamar hukuncin yayi girma ko Yakalleta tare da tsayar da danne dannen dayake acomputer Aganinki kenan sbd ba sanda yargaban goshinki na nan bane da ita akayiwa hakan natabbata kafin nadawo kinyi seta musu hanya Siyam yarumgumi Abba yana murmushi Thn my heart kamar kwa kasani Abba mum tafi kula dakomi na jawwa badan anmata aureba da har yanxu inakallon banbanci Takallesu tana dariya sbd yadda suke neman suhade mata kai Toh ai jawwa macace kuma tanadajn magana tunda bagashiba tana kanwarka amma hartai aurenta tatafi kaika xauna kana kara wahalar da mata kafison suyi tabinka suna makyalema kana disgasu kana ganin kamar birgewa ne sbd kana da kyau, kul wlh nakusa maganinka siyam Hannun Abba yarike yana bata fuska Abba kaji ta ko kaji mumy abindatake fada Abba yashafa kansa Rabu da ita shi aure ai nufin Allah nekarkadamu kanada kyanne ai shiyasa ake binka kaga tashi Kaje kai bacci kaga dagajiya ajikinka Yayi musu sallama yatafi part insa Tare mowana da hubba suka kwanta bacci har hubba tayi bacci amma mowana bacci yagagara Kwance nake kamar inabacci amma ahakikanin gaskiya ba barci nakeba bakuma najin alamun bacci atare dani, tunanin ME KYAU yadameni ga yadda kunnawa na keta dawo mani da maganansa da sautin murmushinsa inajin tamkar inna bude idanuna xangansa Juyi nakumayi inakara matse fulon dake rumgume akirjina fuska ta kuwa sai murmushi nake tamkar gani gamaikyau nake hangone daxaran narufe idanuna, hannuna nakai wurin da makunnin lantarkin dakin yake ina kunnawa take haske yabayyana duhu yayaye kallona yakai ga hubba dake takwasar bacci bakama hannun yaro nace kinhuta dama nice haka nake baccinnan saikuma naji alamun hawaye nasaukowa daga idaniyinsa Wannan shine karo nafarko danataba ganinka mekyau katafimin daxuciya bansan makomar wannan abundayake shirin faruwa dani ba nibakowa bace face talaka mara karfi da iko mara kyau komai xaisameni banaganinsa mutkar xansameka arayuwata, xanxauna dakai naitakallonka shikadai ya isheni koshin kullum domin abincin yayiminkadan kudi sunmin kadan jindadi yayimin kadan ayanxu kaikadai ne jindadina dafarincikina kump inakara jin tausayinkaina sbd wannan ruwan xafin Dana debowa kaina nafahimci shine silar konewar rayuwata sai Allah yayi xankai lbri, Nakai wajen awa uku ina faman kuka da tunani kafin natashi dasauri nanufi toleit dindakin nadauro alwala nadawo nashinfida darduma nafara gabatar da sallar nafila, bankwantaba saida karfe hudu tayi sannan naji wani bacci mai nauyi yaxo yatafi dani banfarka ba saiwuraren takwas lokacin hubba harta karya ta ajemun nawa sbd in ina bacci ba atashina ko agida, saidai natashi dakai na sallah nayi kafin nagama karyawa an aiko hajia nakiranmu. Donhaka agurguje nakarasa muka tafi tare da baba, Wani hadadden falo nahango yana fuskanto wajen damuka fito anyaye labulen falon anafito dawasu daka dakan kujeru wadanda ni atarihina ma bantaba ganin irinsuba baba dake tare damu nakalla Dan Allah bava can wajen nawaye ko wajen kishiyar hajia ne? Kallona tai kafin tai dariya Aa Ai hajia batada kishiya can wajen dantane Brister Siyam Nai murmushi inacewa Au dan megidan daya ne Naitambayar ne sbd nasan sunan mekyau ko su biyune sunan dayan tafadan bashiba Aa subiyune shida kanwarsa hauwa anace mata jawwa ita yau wata biyu kenan dayin aurenta, Nakalli hubba taharareni nayi mata kyafile maiban haushi inacigaba da maganata nacewa baba Auhoooo yayikyau aikinga gwara mufara sanin kangidan karmuje bamusan komi game da gidanba murinka kuskure Eh kuma kinyi tunani yarinya Lokacin mukarasa kofan falon vaba ce agaba ni abayanta sai hubba saikuma wasu mutun biyu suma mata da akahadomu tare wajen hajia Muka gaggaisa inatabaxa ido domin naga Siyam ME KYAU amma ina abu yagagara har kallon hajia yaxo kaina Tace waccan doguwar nace Ni Tace Eh Nace Na'am Sunanki Nace Mowana Araina inacewa tohhh sanabe jiya jiya muka fadamiki sunanmu amma harta manta humm Tacigabada magana Baba kinunawa mowana wajen Siyam nanne xata rinka kuladashi kifada mata abinda yakamata akeyi Baba ta amsa Niko dan dadi nakusa sumewa wlh Allahamdulillah nace araina ina kara maimaitawa jinwani sabon farinciki nake yana shiga rai na. Sbd tsabar tunani dajindadi bansan wanne bangare aka kai hubba ba saiji nai anacewa mungo de hajia nima nafada kafin duk baba tasamu agaba muka futo muna fitowa naji irin kamshin nan najiya daya daskarar dani yabugi hanchina inajuyawa naga ME KYAU dina xaishiga wajen hajia saura kiris nafadi sbd, wani arnen wanka yasha na shadda wayyo kalar shaddar kalar fatarshi fuskarsa tayi tas saiwani annuri ke futa sbd baya rabuwa da murmushi, badan hubba ta ganni lokacin dana tafi faduwarba tatareni da sauri danasha kasa don xai wahala ace hakorana biyu basu fita ba, atare duk muka kalli kasa wani ramine maidan girma anyi shuken fulawa aciki nakusa ruftawa garin kallon Brister Siyam. Bayan baba tafadawa sauran biyun aikinsu taje takaisu tadawo takalli hubba Kece hubba ko Tace eh Tohm ke xaki aiki ne awajen sirikar hajia dake cancikin gidannan tsohuwa ce akwai mai mata wanki ke abinchi xaki rika mata da kula da ita albashinki dik wata 2000, Hubba taimurna sosai tana godiya sannan baba itama taraka har part din hajia Sanawiyya mahaifiyar alhji Abdullateef. Sannan tadawo wurin mowana wacce harta fara kewar yar uwarta tunkafin wani lokaci, Kekuma kece mai aikin dayafi na dikkansu wahala mowana Dasauri nadago axato na kartace xata chanjan dasauri nace Bakomai ai xan iya baba Takalleni da mamaki kamar taimin tambaya saikuma tafasa Shikenan ai naga aikamar xaki kokari amma saikin hakuri da halin Brister kinji xaki rinka kula dawajensa shara goge goge bawa tsintsayensa abinci yimasa abinci dik wanda yakeso sbd haka xanfara koyar dake girke girke kala kala daga gobe inkikagama aikinki kixo murinka xama Nace Toh Taso muje nagabatar dake awajensa yau lahadi yana nan ba inda yake xuwa haka idan kika fara aiki dik randa yake gida baki dahutu Sbd fitowa yake lanbun gidan yaxauna yafito da tsintsayensa kekuma kita aikinbasu abinci sbd haka ka idarsa take, Na numfasa Toh ai hikanan baba Kekuma albashinki 35000, naxaro ido Wuuuuu baba haka dayawa ai aikin bayawa kuma xa arinka bankudi har 35000 gaskiya dayawa Tai dariya munakarasawa kofar falon baba tai sallama Nidai da kunnena banji sanda aka amsaba amma baba taji saiga ninai tadanna kai tashiga nima nabi bayanta asukwane Tab nace kawai kusan afili sbd agaskiya lamarin mutanen nan yafara bantsoro falo kamar ba aduniyaba bangon kansa nafalon kamar kwalba sbd yadda yake sheki da walwali, ancikasa dakayan kyale kyalen duniya yafi na hajia kyau da kawatuwa sosai sbd sanyin falon ME KYAU da dadin kamshinsa mowana takusa bacci agun da idontakwa yasauka akan sa takusa faduwa daga durkushen datayi, Tsarki yatabbata gareka Allah mahaliccin wannan kyakkyawar halitta, Tafurta aranta tanadan daidata nutsuwarta kar baba ta harbota Bayan sun gaisa da baba Yanacigaba da danne dannen lop'top dama baidago ba balle yaga wacece suke tare bakin mowana narawa tace Ina.... Kw... Kwa... Naaa,,, Kamar baxai amsaba cankuma yace Lafiya Baba tace Wannan itace sabuwar maikula da sashin nan yanxu kamar yadda hajia ta ce nafadamaka, Bat are daya dagoba yace Ok shikenan baba Tamike Nabarka lfy Mowana tamike baba tadaga mata hannu alamun takoma taxauna aikwa takoma taxauna tacigabada kallonshi tunda taga shi baxaitaba kallon kwaran idontaba sbd ko baba baitsaya yakalletaba balle ita dabai san wacce kayan bace, Tamkar babu wani abu awajen haka gun yayi shuru saikarar fnka da eysi ke tashi wajen awaa daya da wani abu tukunna yarufe lop top din yadago kansa sai lokacin suka hada ido shima kuma sbd ita idonta nakan fuskarsa tsowon lokacin datadauka agun, Kasa magana yayi ganin hankalinta baya jikinta aransa yanajin amma wannan mahaukaciya ce inba mahaukaciyaba yaya xakisani agaba dakallo kamar wani tv yayi kwafa amma sam baidawo da mowana ba saima wani sabon salo dakallon nata yasake Kauuuuuuuuuuuuuu Yadauketa da mari maixafin gaske kuma iya karfinsa Wata kara mowana takwallah tanasunkui dakai hannunta dafe da kuncinta barin daya mara amma sbd tsabar xafi dashigar marin dataji hardayan bangaren amsawa yake, Ga mamakin Siyam koda mowana tadago murmushi ne afuskarta saiwasu 'yan siraran hawaye wadanda batasan dafitowarsuba ke bin fuskarta Kanta tasunkuyar kasa karon farko batare data daina murmushin ba "Afuwan Tafurta ahankali cikin nutsuwa kanta akasa Ashe mai hanklice shitsammaninsa ma ko mahauciya ce tashiga yamanta da baiga wacce baba takawo masaba lallaikwa baxai amshi wannan ba sbd saitarika sashi amai Kaudakansa yayi dakallonta Yanatashi afasace " kikoma indakika futa bakida tarbiyyar daxaki iya aiki awajena don axahirancema kinfi kama da mahaukata Tadafe kirji tana janwani numfashi da kyar, sbd yadda yake maganar sacikin salon nutsuwa tamkar baxai motsa bakin ba hakan bakaramin kyau yayi masa ba, Ni ba mahauciya bace dikkan idan dayakasance namai hankali xai fahimci hakan amma bakowa ba, Take siyam yafahimci tanaso tace masa mahaukaci gaskiya tai tsaurin ido domin kuwa ba bu macen data taba masa makamancin wannann abin, lallai wannan ko wacece batasan wayeshi ba kodaga kauye take ko batada hankali ne ma Mike wa tayi xata fita "Dakata! Tatsaya cak batare data juyo ba Shima bai matsaba yana tsaye inda yake Karki sake nakara ganinki acikin gidan nan nafahimci abindake damunki hassada dabakinciki sune suke damunki toh balaifi dama wannan halin namahaukatane wlh kotantama banai bakida hankali kuma kiji ni dakyau inma aiko akayi cikin gidannan domin ki wani abu toh baxa ki iyaba domin munfi karfinki, munrigaki munce Allah. Hawayene xafafa suka shiga xubowa a idanin mowana Sbd bakidaya network inta yadauke kafafuntama sunkusa kasa daukarta Tajuyo daidai lokacin dashima yajuyo xaidau wayarsa yashige ciki suka hada ido saita saki murmushi Tana kiss din hannunta tasa akirjinta tare da lumshe ido, Hakane nidama nasan banida hankali bakaine kafara fadanba ninafara tabbatarwa kaina sbd kasancewa ta haka shiyasa nake neman xaucewa amma koda xanrasa rayuwata natabbata xanrasatane atadalilin ME KYAU, Tafice dagudu siyam kwa banda, DACI da xuciyar sa take masa ba abindayake so irin yaganar da wannan yarinyar kuskurenta tabvas saita gwammace kida da karatu mutkar takara kiransa da ME KYAU, Tanakomawa dakinsu wanda yanxu yazama nata itadaya tafada gado tafashe dakuka Nashiga uku wannan wacce irin jarabtace mekyau inason ka wlh inason ka kaikadai nake so baxantabbatar raye nake ko mace ba saitare dakai xan amince narasa komai matikar xankasance dakai, Kidaina wahalar dakanki domin kuwa siyam akwai wacce take sonshi Naji maganar hubba akaina dasauri nadago kaina ina kallonta sbd bansan yaushe tashigo ba, Wacece kuma hubba nikadai nadace da siyam mekyau kema kinsani wlh nikadai nake sonshi Nafashe dakuka inafadawa jikinta rumgumeni tai tana lallashina Mowana tabbas nafadamikine sbd ke kijanye kudirinki akansa sbd wacce najidin tafiki gata Namike tsaye Mutkar batafini son mekyau ba, toh baxata nunan komaiba sbd sonsa shine baxar danarike xankuma iya xane kowacce mace da ita mutkar ta tinkareshi, kinga hubba karki damu kanki koyanxu kasuwa tawatse dankoli yaci riba koba komi mekyau yasan inasonshi kuma har marina yayi Allahamdulillah naji dadi tunda nasamu darajar da har yatsunsa ke iya kwanciya afuskata , Hubba tasaketa tanaganin ikon Allah wannan abun itakam yafara bata tsoro Shikennan mowana yanxu nixankoma wajen hajia sanawiyya sbd karta bukaci wani abun donhaka inkinyi sallar mangarib kixo can wajen kisameni dan Allah saimuci gaba damaganar hakan xa ai ammafa banfadamiki ba cikin maganar da mekyau yayimun hardata kora yace karyasake ganina acikin gidanma ba wajensa bansan yaxanyi ba yanxu wlh kiban shawara kar tunani yamin yawa kaina yafashe Hubba taidariya tana tausayawa 'yar uwartata har cikin ranta sbd bakidaya yanxu tamanta ma dawani farinciki nata kawai siyam ne agabanta Karki damu kirinka xuwa kinamasa aiki saidai kawai yadawo yatarar inkikai haka baxaiganki ba, Tasaki murmushi Nagode sister hubba Allah yabarki da malam Abubakar Taidariya amin yarabbi kingakwa kojiya munjuma muna waya har yake fadamin yace mlm sadiq ya aikosa kwana biuu idan yakira wayarki bakyadauka lfy? Mowana ta tabe baki tare da jan dogon tsaki Mustww kinji gara fa, ko wa yace masa ma yakira ohoo, hum kinaji kekanki hubba kinsani mlm sadiq ba ajinabane kuma banasonsa nasha fadamasa amakaranta nafadamasa sanda yaxo kofar gidanmu nafadamasa kuma dik kallama daya ce banasonsa bansansa toh anayin so dole ne, wlh banasonsa kuma baxantaba sonsa ba nimatar siyam ce anan gidan duniya harna lahira donhaka kifadawa mlm Abubakar yafadamasa anki adaga wayar tasa idan ya isa da ni da ita ya mayardamu inda muka fito yahuta, Hubba tace Aaa aikinsan baxan iyafadawa darling wannan maganar yafadawa mlm sadiq ba kema kinsan ni inada hankali nakuma san abundanake, wallahi Mowana ranta yavaci wato har anxo gabar da hubba xata iya daukar ta a amatsayin mahaukaciya Idonta cike da hawaye tamike tsaye Nice mahaukaciya hubba akan mlm sadiq dayaxo yasamemu tare kike alakanta ni damahaukata tab lallai natabba ashe akwai abubu masu sauki dasuka fini daraja da kima aidanunki natabbata tunda harxaki iya fadamun kowacce kalma taxo bakin ki , Taficeda guda saiwajen baba Tacisa a bata nandonhaka taxauna tasha kukanta mai isa kafin tashare hawayenta taxauna jiran baba taxo tafara mata terenin akan abincin brister siyam. Donko tai alkawarin kome xaimata saita kasance atare dashi, Mowana bata fahimci hubba daidai ba, domin hubba bataji dadin faruwar hakanba itama ranta abace tafice takoma wajen hajia, BAYAN KWANA 20 Al amura natatafiya kowanne ayadda yake tafiya kamar yadda nadauko muku labarin ciki harda chaftar mekyau da mowana, Tsawon kwanakinnan mowana keyiwa mekyau dik wani abu daya shafi wajensa abinci goge goge bawa tsintsaye abinci gyara masa takalma agoge komidai amma baitaba dagakai yaga fuskartaba sbd yamanta dawancan abun dayafaru dayake Brister Siyam baida ruko ko kwakkwafi akan abu, gakuma wani abu dayake basa mammaki shi ne dik wani abudayakeso shi akemasa ba ayimasa badaidai shiyasa yake jindadin wannan mai aikin nasa,ga kuma yadda akemasa abinci masu dadi irin wadanda yakeso idan yaci abincin mai aikin saiyaji kamar irin wanda kanwarsa take masane kafin amata aure jawwa, donhaka hankalinsa yakwanta yayi, bulbul dashi harwani kara kyau yake sbd yayi kewar abincin kanwarsa gashi yanxu yamarda kamar ita xaiso yaga wannan mai aikin nashi macane ko namiji oho yafada aransa don baxai iya tunawa ba. Xaikara mata albashi maitsoka Mowana xaune akan wani dan madaidaicin benci mekyau kusa dawata yarkaramar bishiyar gwanda cangefenta kuma wasu fararen tattabarune wadanda kodigon baki babu ajikinsu tamkar anai musu wanka kullum Wanikyakkyawan koko ne dauke da abincin tattabarun ahannunta tana watsamusu sunaci inta watsa sai sai suyi farrrrrrr kamar xasu tashi saisu dawo subiyo abincin nasu kasa su ci, Hakan nabata sanyata nishadi kwarai kuma yanadebe mata kewar mekyau dayanxu take kokarin hanakata ganinshi ko jinshi harna kwanaki dayawa wadanda suka shudemata gashi har xa aimusu albashi nanda gobe sutafi gidasukwana biyu sudawo bakaramin kewar tattabarun xataiba dasauran tsintsayen gaxomunta can tanahangowa agidansa saidaga kunne yake taidariyatana dagamasa hannu, kamar tanamagana dawani mutum babba, Ina xuwa dan xomona rabiy dayake haka take kiransa akwai kuma wata katuwar magi awajen siyam itakuma sunan data samata vidya tanakaunarta sosai Abincinsa tadebo taje tabudesa aikuwa yafito dagudu yanatsalle yafado kanta tadagashi tana dariya rabiy ilov wannan kirniyar taka tasaukesa tana dariya, yafara cin abinci yanakada kunnuwa, itakuma saishafashi take tana dariya "Rabiy sarkin tsalle kai baka rabo da gudu kanada jiki mekyau rabiy kana birgeni xankewarka idan natafi gida Rabiy Tamike tana dauko wani boket tadebo ruwa awani babban daro taxo taje kowanne tasa masa ruwa agidansa tukunna tanufi kasan bishiyar wani mango dayayi kasa kasa yayi 'ya'ya sunkuma fara nuna wasukuma sun nuna iskar wajen medadi mesa bacci donhaka taja kujarar roba taxauna tana lumshe idanunta tunanin mekyau yadirar mata baxato batsammani taji tafara yabonsa acikin ranta axahiri kuma tana rera waka macike da shauki, "Xafin nakuda nasa fitar hayyaci amma so yana agabansa gun kullachi,yawan demuwa nasa mutum furgici, sonasa yawan damuwa amma kasa bacci, wanda yasoka dan Allah kasanyashi xuci, kamai agajin kayan tufa har abinci, kimanta shi ko da kudinsa komai talauchi, kawai kalli so gane siffa yafi suna, (Wakar isa ayagi) Hawaye sharrrr suka fara fita a idanunta, magana take afili sbd yadda dakadaicewar datai, Narasa tayayaxancire soyayyar ka acikin raina nayi dik wani kokari amma nakasa kataimakamin kasan inasonka ka kuma amshi soyayyata ME KYAU, tabbas xan iyarasa rayuwata mutkar bansamu soyayyar ka ba, Nikadai nake sonka ina kaunar ka akwai sonka adikkan sassan jikinta, ME KYAU banasonka don kudi kodan wani abu dalilin soyayyarka nake nema nima narasa kawai asanina kyawunka nadumautani Tsaye yake akanta kyam tamkar

Chapter 2 of 11