Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
iyayensa amma dakyar suka amince daya aurenta, akadauramasa aure da maryam watansu biyu suka daga makka acan yakaita danginsa yanunata amatsayin matar da ya auro daga nigeria amma Dangin kabeer basason maryam hasalima tsanarta sukayi sosai basa shiga harkarta shima sukadaina kulashi, dahaka har maryam tahaihu biyu dashi dik yaranta maxa, sulaiman shine babba sai shureim, kuma alokacin tanada ciki na uku, mahaifiyar kabeer tadage saiya kara aure tanemo masa wacce xai aura din balarabiyace budurwa kyakkyawa da ita, aikwa dalavari yaxoma maryam hankalinta yatashi tafara kiraye kirayen waya gida nigeria suka fara asiri amma abin nan bayiba saida kabeer ya auri wannan budurwa mai suna Tasleem akayi aure lfy tatare nan soyayya taballe tsakaninta da kabeer kuma yana kokarin adalchi atsakaninsu kwarai da gaske amma maryam batagani fadan yaudaban nagobe daban, takasa kuma tafara jifan Tasleem da mugwayen asirai kala kala alokacin itama Tasleem din kuma cikine da ita yakuma kai wata biyu, wata shida da auren kabeer maryam takuma haihuwa 'yar mace taci suna Xaienab, bayan kwana goma tanemi taxo gida Nigeria wanka, ya amince taxo aikwa suka dukufa asiri itada mahaifiyarta harsaida sukauima kabeer asirin dasaidaya tattaro yabar kasarsa mkka yadawo Abuja da iyalinsa Tasleem da harkokinsa duka nasai da gwalagwalai. Dawowarsu Abuja yasa kabeer yasauya yaxama wani mijin tace komi xaiyi sai maryam. Tasashi, gacikin Tasleem yatsufa amma baya bata kulawa sbd anjanye masa hankali haka rayuwar su tacigaba da tafiya akarkashin maryam da dokarta, har tasleem tahaihu danta namiji, haushi agurin maryam saima kungani kwana bakwai akasama dah suna Tijjani kyakkyawane nesa bakusaba sbd dik yafi sauran yaran maryam kyau sbd kakarsa yayo tawajen kabeer, donhaka maryam tadauki tsana tadorawa tujjani musamman yadda taga ubansa naji dashi yanakaunarsa sosai domin yanafita dashi yawo da office ko ina sunatare da tujjani Bayanshekara 26, Alokacin ne 'yayan maryam suka kawo karfi sbd sulaiman da shureim sunyi aure xainab ma tayi aure sai kannensu guda uku shahed arfat salima Baiwar Allah kwa tasleem batakara haihuwa ba gashi har tujjani yaxama babban saurayi domin yakai shekara 27 dinnan amma baruwansa damata sai Abbansa kabeer ne yagadacewar yayimasa aure donhaka yace yafitar da mata yayimasa aure yaji kunya sosai lokacin da Abbannasa yaxo masa da maganar auren, amma haka yadaure yace xaiduba. Watarana yaje shopping muka hadu dashi yaxo shima siyayya daga wannan lokacin yakamu dasona yatambayi suna nace masa iyami yayi dariya sbd yafuskanci kamar nidin bayerabiyace soyayya maikarfi takullu tsakaninmu da tujjani harta kai da iyaye sunsani amma iyayena sukace baxan auri musulmiba shima babansa yace bai aminta ba ya auri arniya wacce bata sallah ba, amma tasleem ta amince nima nabijerewa iyayena akancewa xan musulunta na auri tujjani aikwa sukace mutkar na musulunta sai sunfita daga rayuwata basu bani harkarshen duniya haka na amince sbd alokacin nafara sha awar addinin musulunci, haka nasamu tujjani inakuka nafadamasa narabu da iyayena baran baran akan inaso namusulunta ayi aurenmu ya Jin hakan yasa ya rarrasheni sannan yadaikeni yakaini gidansu mamansa ta amsheni da mutumci kabeer daya dawo shima jin labarin xan musulunta yasa ya amince da auren bayan na musulunta akasakemun suna xalihatu. Akasa lokacin auren mu mama tasleem ce taimin komai na aure kabeer yayimana katon gida awata anguwa tamasu kudi yakashema gidan kudi domin dik wanda yaxo bikin saiyatafi dasantin gidan abakinsa anyi aure lfy muka tare, Cankuwa takasa maryam da 'yayanta sunhadu sunfara magana akanmu da mijina, Tijjani mutum ne mai hakuri da soyayyar 'yan uwa amma shi basa kaunarsa sbd uwarsu tacusa musu kiyayyarsa aransu donhaka suka tsananta kiyayyarsu da hassada akansa, takaida ko gaidasu yayi basa amsawa saidai fada da xage xageke rabasu, akwana atashi har nasamu ciki nahaifi yata mace aikuwa tijjani yace sunan mamansa xaisa na amince damaganarsa akasamata suna Tasleem sainace murika kiranta Mowana. (Mahaifiya) shekarar mowana goma sha biyu aduniya kakanta yafadi yamutu kabeer yayin da kamar sulaiman da shureim da xainab da shahid jura suke suka rufa akan dinbun dukiyar da kabeer yabari suka mamaye komai ciki harda compuny auduga dayake hannun tujjani yanakulada shi, suka ciresa daga manajan compuny, suka mamaye hakan baisa yaji wani abuba yasamu wani babban shago yaxuba kayan sanyi yafara sayarwa amma hakan baimusuba saida suka karyasa suka samasa cutar komi yataba baxai albarkaba, ganin yadda rayuwa takoma mana, yasa mama Tasleem takamu daciwon xuciya wanda shine yaxama sanadin mutuwarta mutuwar mama Tasleem yasaka tujjani dani cikin mawuyacin hali narayuwa ga tsanani da masifar wadannan yan uwannasa abinci naci saimun nema dakyar muke ci wataran ganin halin damuke ciki kara ta axxara yake yasa nashirya naje wajen iyayena amma sukayi min korar kare sunce basu bani kanwata emeka taitakuka tanaso taxo wajena amma sukace xasu tsinemata mutkar takulani haka nadawo jikina bakwara nasamu tujjani rike da mowana balafiya hankalina yakara tashi muka kaita asubuti akace karin jini xa amata leda biyu, bamuda kudin hakayaje wajen yan uwansa amma suka wulakantashi yadawo yanakuka nadauki gwal ina nasayar akakara mata ruwan, Danaga idan mukacigabada xama a Abuja watarana xanwayi gari narasa mijina da 'yata sbd yadda suke farautar Mowana tamkar wata abokiyar gabansa, donhaka nacemasa musayar da gidan mukoma kano, ya amince mukasayar da gidan milion 10,sbd bakaramin gida bane, ana igobe xamu tafi suka samu lbari da daddare munakwance saiganin 'yan fashi mukayi akanmu Allah yataimaka tujjani ranan yaje wani guri neman aiki sbd yafisu yaxauna anan wajen yanwansa duk da suna cutarsa yace indai yasamu aiki baxamu tafi kano ba gobe, aikuwa sukayimin dukan tsiya suka kwace kudin gidan amma badukaba sbd nakwashe wasu naboye cikin kwalbar bandaki daya dawo yasha kuka ganin halindayasameni donhaka dasanyin safiya mukayi sammakon xuwa tasha, bamu dade daxuwaba mukasamu motar daxataje kano Allah yakawomu lfy mukafara cigiyar gidan siyarwa dakyar akasamomana maisaukin kudi wannan muka saya muke xaune sauran kudin muka fara cin abinci dasu kullum tujjani xaifita neman aiki amma baya samu watarana yafita kenan saidawomana da gawarsa akayi mota tatakeshi ko motsawa baikumayiba awajen, ranan munga bakinciki baxantaba mantawa da wannan bakar ranaba, Adeel Tafashe dakuka tana rumgumar Mowana itama kukan take Adeel ma haka lallai akwai mugwayene mutane aduniya wannan xalinci yayi girma dayawa, Kiyi hakuri momma Allah yana bayan maigaskiya kuma insha Allahu xakuji dayadda suma xasu kare. Nikuma xancigaba da taimakonku har tsawan rayuwata momma Taitamasa godiya tanakuka Mowana ma kukan take saiyaji ransa badadi ashema yarinyar nan jinin arxikice kuma 'yar dangi Allah yasamiki abundasuka muku yace aransa, Ranar monday hubba tashiry, tsaf taxo tayima Mowana sallama xata tafi gidan hajia bera'u aiki, hankalin mowana yatashi gashi kafarta tafara sauki amma batada ishashhsiyar lafiyar tafiya aiki donhaka tadauko xingureriyar wasika tabawa hubba aboye tace takai dakin siyam harxataki karba amma taji tausayinta ganin yadda ta marairaice kamar xatayi kuka, takarba taima momma sallama tatafi Mowana tana dangashi tarakota kofar gida tanaji kamar tabita kotagano mekyau. amma xata hakura harta gama warkewa tunda yanxu kadan take dangashi, Sunsha kyau kam kamar xasuje gasar kyawawa, dik shaddace ajikinsu yaluwa amma maiduhu, ta amshesu sosai musamman Brister Siyam tamkar domin sa akayi shaddan wata kyakkyawar mota naga sunnufa kalar kayansu dikkansu abaya suka xauna sai direba yaja suka fice, mummy ce kewa direban kwatance ta waya yanatafiya harsuka karasa gaban wani tabkeken gida hadadde amma ko rabin na su Siyam baiba brist, Siyam yatabe baki yanajan tsaki Adeel yakallesu Yakamata ka seseta kanka tunda munshugo gidan Hummm wlh dole mummy taimin amma ni wlh tunkan naga yarinyar naga alamar baxataiminba Adeel yace Look fa malam bakyaleka xa ai axubama maka ido kawai ba girmafa kake kullum sokake abarka katsofe ba aure aa baxaiyuwuba mummy da gaskiyarta ku biyu kadai ta mallaka aduniya dole xataso ganin jikokinta daga gareka karkAga laifinta Humm yaharari Adeel daidai lokacin da direba yayi paking yafito yabude musu kofa amma saida sukadau lokaci sannan suka fito sbd Adeel yaxauna rarrashin mutumin nashi, Cikin wani kyakkyawan falo akayi musu iso yasha turare saikamshi ketashi ga abincinan an ajemasu da kalolin lemuna basufi minti biyar da xamaba saiga wata budurwa tashiga saikamshi take jikinta sanye da wani material anyimasa dinkin doguwar riga sitretgwin tamatseta matika ko ina yabayyana ajikinta tasawani takalmi maitsini saiwani banxan mayafi dayatsaya iya wuyanta dayake dama cillasa taikawai anyi kitsan atacch kala ba yaxubo bayanta da gefen fuskarta dankwalin annadashi ansa agoshi fuskarta kuwa kwalliya akaxo hargida akayimata tadubu goma, ko ba afadi yanayin kwalliyar ba, dajin kudin da akayita ansan taxanu. Saiwani fari take tana yanga tashigo dasallama ahankali kamar baxatai magana, Siyam kallo daya yayi mata yakusa fashewa da dariya sbd yadda take tawani karairaya kamar wata mara lfy, Adeel ne ya amsa sunagaisawa tagaida Siyam dakyar ya amsa yana kara kaudakai, Fatan munsameki lfy Tai murmushi lfy kalau sunana Ismat xulkifulu Siyam yatabe baki Adeel yaxunguresa Sannan yayi magana Siyam, Abokina kuma Adeel kinga namiki xaki iya aurena shine yakawo ni kawai gurinki sbd baxan iya yawon xuwa xance ba Tasaki dariya bawani kaminkai 😁😁Laaaa xan aureka mana bakada makusa sosaima naga hotonka awayar mamana kuma tun lokacin anayimun maganarka naji ka kwanta mun araina Siyam yaji wani haushinta aransa kamar yarufeta da duka bakidaya batada kamun kai tab Shikennan mu xamu koma yamike Adeel yafara fita Aa baxakuci komiba Bakomi mungode yanafadan haka yafice dasauri sbd idan yatsaya yacigaba dakallonta xai iya sibutar baki ya wulakanta ta baisaniba dariya Adeel yake masa ganin irin hade randayake kamar an aiko masa da sakon mutuwar mummy, Kai wannan wanne irin wulakancine xa kaxo xakasani agaba kaitamin dariya Siyam yay maganar afasace kamar yadaki Adeel Rufe bakinsa yayi yana cewa Hhhh yo badole nayi dariya ba wannan soyayya haka kagakwa yadda kuka dace da Ismat kuwa woow masha Allah Duka Siyam yakaimasa yarike hannun nasa yana dariya Au dukana kuma xakai kawai don nafadi gaskiya dadina dakai kin gaskiya Brister Siyam yayi kwafa yana janye hannunsa Yarinyar kokadan batayimin ba hasalim ma ni haushi tafarabani kafin komi gawata futsararriyar shiga da tayi amatsayinta na 'yar musulmai, nikam batamin ba amma mummy tayi rantsuwa akan saina aureta tace kuma dole namata biyayya wannan karon mutkar itace ta haifeni, Adeel yarike baki yana cewa Ya Allah toh gaskiya kuma yakamata kanunama mummy ka haifu kanunamata tabbas kai dahne me biyayya kayi wannan auren pls tunda konan gaba kana dadamar kara ukuma bayan ita, yes! Kana da kudinka bamacen daxakanema takika saimara rabo, Siyam idansa adan lumshe yajingina dabayan kujeran motar Bani da ra ayin aje matannan agidana kamar wasu awakai balle su fitineni, kaganni nan dik wacce na aura xan xauna da ita kawai itadaya, inxaman yaki ne kawai sai insaketa ko na hakura da auren duka, Adeel yana daddana wayarsa yace Nima wannan ra'ayin naka yakusa kama da ra ayina amma ni sai indai nah nah na aura toh saina kara aure kaga kayiwa mummy boyayya kawai ka amince Bris, Siyam yace Yaxanyi na amince Adeel xanfadamata hakan idan nakoma gida inason mummy na banason dik wani abudaxai tabamun ita, shiyasa jiya rikici yakusa shiga tsakanina da kawu salim da kawu babba, Adeel yagyara sbd yasan tsimammiyar kiyayyar dasukeyiwa hja bera u, Toh wai su maye matsalarsu da baxasu hakura hakaba yakamata ace yanxu sunsaki ransu, gaskiya laifin kawu babbane sbd shine babba dole shixaifadawa kawu salim da Aminu suji wlh dai sunji kunya dik yadda Abba ke kyautatamusu basa gani burinsu kullum saisun tayarmasa da hankali, Siyam yaja tsaki Ai kabarni dasu wlh dik sainakoresu daga gidannan dik wanda yakara dagawa mummy yatsa acikinsu ni babban bacin raina Adeel shine yadda mummy takwada mun mari agabansu sannan tace duk lokacin dana kara tankawa kawu salim ko kawu babba ko Aminu batayafemun ba nabarsu komi xasuyi mata suyimata ni amatsayin iyayena suke wannan fa rigimar ita takara tunxura mummy tace naxo nanemi wannan yarinyar idan tayimun awannan watan xa ayibikin nabar gidan, baxan iyabarin mummy acikinsuba Adeel sbd basa kaunarta gashi Abba baya iyamasu magana sai siyomasa cha dama nidin suke shakka kuma mummy tayi mun birki, wasu 'yan uwa Abba kedasu kamar shedanu Hawaye suka shiga futowa aidanunsa Adeel yafara rarrashinsa Kayi hakuri amma gaskiya abindaI ya ta axxara kuma ahakan da shi kawu babban yakeso saika auri 'yarsa su'adaat gaskiya yayi tsaurin ido, Humm ba abundafa suke bukata aduniyarsu iirin Abba yafadi yamutu sumamaye dukiyarsa shiyasa ai suke tadagewa saisun cusamin su'adaat na aura, mummyna dah tayarda fa dagabaya ne yanxu datagane manufarsu ta bujire shine suka kara birkicewa ta inda suka shiga batanan suke futaba toh cikin watannan suke so suhadu sutsai daranar aure Abba kuma ya amince amma yace innafito dawacce nakeso kafin lokacin xa afasa inkwa banfuto dakowaba xa asada su'adaat, itakuma mummy saita yanke shawarar inxo insamu wannan 'yar kawartata, duk basauki domin wannan ma basonta nakeba amma gwara ita da waccen dabbar 'yar mutanen banxa. Haka sukacigaba da tautanawa gameda matsalolunsu harsuka karasa gida wajen hajia bera u sukawuce anan ma sundade suna hirakuma taji dadin yadda yanuna amincewarsa donhaka Alhjia yana dawowa xatasanr masa ranar juma ah idan anxauna family day yasanarwa 'yan uwansa aje anemo auren, domin acikin watan nan takeso ayi auren, donhaka murna awajen hajia bera'u ba acewa komi Ganin mangaruba tadoso yasa Adeel yayiwa Siyam sallama yatafi, Bayan yayi wanka yafuto yagabatar dasallan mangaruba sannan ya matsa ga tafkeken merorr dakin nasa yayi shafe shafen mansa da turaruka yayi tsaf yasauko kasa nan yasamu anshiryamasa abinci adani, yanabudewa yaga soyayyiyar taliya da gashashshen nama sai shinkafar Ghana, yaci abincin balaifi yamike yakarasa ga kujera yakwanta tare da mimmikewa sbd yadda kafafunsa kemasa yama yama ba abundayake bukata kamar bacci fadowa akayi falon dagudu saiji yayi anfada jikinsa ana dariya Helloooo yaya siyam nadawo koka nemeni toh gani ai ni na nemeka ko hutawa banba nace sainaxo naganka Tsaki yaya jin wacece yanamikewa xaune dauke da ita akirjinsa yana dagota yamatsa Kemiyasa wai bakya girmane kullum su'adaat kifado kaina kawai basallama kamar ba 'yar musulmai ba Ta tura baki tana ruko hannunsa Yanxu ni yaya Siyam maye laifina anan don nayi murnan ganinka, sallama kuma ai mantawa nayi Yadauke kai daga kallon ta domin shagwabarma datakeyi din ba birgeshi take ba saiwani tarin haushinta dake daskaremasa amakoshi, Toh ke amatsayin ki na musulma inba sakaciba daganganci miyasa xaki rinka sake harki manta sallama kinga kigyara dabi unki tun wuri sabd wannan dabi ar ta turawa dakike dauka ba indaxata kaiki domin nangaba aure xaki haka xaki koyama yaranki? ko miji nagari inkinason samu toh saikin xama tagari tukunna xaki samu nagari Tai dariya Yaya aini banda matsalar miji nagari tunda nakama nawa kuma natabbata nagarine tunda tun inakarama nasan koshi waye atabangaren halayya dakyautatawa dasanin yakamata yaya aidik wani abu da ake bukata awajen wani dah namiji aika hada shiyasa nake jidakai fa, ga son kyautatawa talaka kanataimakon marayu, bakada kyamar talaka rayuwarka duka abarsoce. Yakalleta kafin yamike Xanje nakwanta yanxu yakamata kema kije ki hutu sbd kinsha hanya Kosauraronta baiba yawuce dakinsa yana rufewa sbd tafaradamunsa kuma dayawa Hubba dasanyin safiya tasalallabo bangaren siyam ta aje takardar da mowana tabata sannan takoma wajen aikinta, Daf daxaifuta yaga takardar yadawo daukayayi saiya danna a aljihu sbd yanasauri office yau akwai wani case daxaikarba. Bayan bakin sunxo suntafi yadansamu nutsuwa sannan yadauko takardar yafara dubawa, 💜💜Sallama agareka yarda da Aminci daso da kauna sutabbata ga ruhin wanda nake bege kullim, kakasance nutsuwar jiki da sirrin ajiyar karuwar farincikin xuciyana nafuskanci dukkan wani jindadina yanaxuwane Adaidai lokacin danake atare dakai, dikkan jinina yana aikine tare da taimakon kaunarka, tabbataccen farinciki marar karewa yakara tabbata agareka ME KYAU wannan rubutaccen sako ne daga wannan dai masoyiyartaka wacce bakada kamar kab wadanda keta furtamaka kalmarso, nafisu sonka nafisu bukatar kasancewa taredakai, sunana TASLEEM (MOWANA). Yadukufar dakai xuciyar cike datunani wannan yarinyar tana danaci wannan wanne sone takemin ne tun abunkwa dayafaru gidan lamgu baisake ganinta ba agidan toh waye yakawo wasikar ya aje lallai akwai ayar tambaya awannan abun Yatabe baki yana dage kafada alamun baidamu ba, wayarsa yadauka yafara dannawa numban ismat yakirawo suka gaisa sbd mummy tace yarika kiranta suna gaisawa, kuka take sosai tana burgima ajikin momma Idan baki barni nakoma gidan hajia aiki ba wlh xan iyarasa rayuwa momma ki kyaleni naje baxam iya rayuwa batare da aikin danake agidan hajia ba, Momma ita kam ma abin na mowana yafara bata tsoro wannan wanne irin aikine da baxata rayu inbabushiba yanxu anataimaka musu da abinci da kudin kashewa Adeel yadauki nauyin abincin nasu amma tace saitatafi aiki bayan yabarmata sallahu akan kartabarta takoma aiki. Kinga mowana fa dake nake dago kanki nan kikalleni Tana sharar hawaye tadago tana turo baki gaba, Kinajina me kika aje agidan hajiar da harkike ikirarin baxaki rayubabu shiba Abu mai muhimmanci arayuwata Tafada tana kara tura baki kamar yataba kasa tana matso kwallar dole Toh kinajina vaxaki koma aiki can ba amma na amince miki yauki shirya kije ki dauko abin naki kidawo kikuma gaida hajiar kifadamata kindaina aiki, Dasauri tamike tana murna tafara tunanin wanne kalar kaya xatasane acikin kayan da Adeel yasiyomata taje taxabi wata falleliyar atamfa baka mai xanen blu dafari dinkin riga da siket da mayafi blu saiwani takalmi shima blu flet ne dayake Mowana doguwace Wanka tayi ta sa kayanta wayyo Allah xansu kuga yadda atamfarnan taxauna ajikin Mowana tayi mata das siket inyakamata daga sama daga wajen kasa yabude sosai rigarma mairafa akasa ce sai dogon hannu wanne yamatse dayaxo gwiwar hannu dankwalinta babba donhaka taninkashi tai daurin aysha buhari, tasa takalminta da mayafin agurguje tadauki dubu daya dagacikin kudin da Adeel yabata, tafuto tana kara jinta tamkar wata sarauniya sbd yaune xataga Siyam dinta wanda tadau tsawon lokaci bataganshi ba, Momma taitakallon yartata tana yaba kyawunta da dirin da Allah yamata acikin ranta kamarta sak da kakarta har dirin lallai Mowana bakibar gidaba Momma kamar yaya kenan banbar gida ba aiyanxu xantafi Momma tai dariya Aa bawannan ba na kamanni saiyanxu nakara ganin tsantsar kamarki da kahkarki Ta wangale baki tana rike kafadar momma Kaii dan Allah momma wlh xagina kike mama tasleem itafa balarabiyace cikakkiya, kuma farace tas nifa kallani nibanason kina tsokanana irin wannan Momma tai dariya Ahaka din domin da mahaifinki yanada rai dashiyafadamiki kumadama ai tunkina yarinya itakikadauko duhun fatane kuma ni kikayo shiyasa amma ai ahakama kinfini haske fatarki mekyauce Ta rumgume ta tana jindadi Tohm momma bari naje sainadawo Adawo lfy Allah yamiki Albarka Allah yabaki abindakike so Tajuyo tanadariya aranta tace kamar tasan abundanakeso xani nema Amin momma Ta amsa tanaficewa dasauri. Sosai maxan anguwarsu ke kallonta yadda take tafiya gashi kuma sunganta tasauya tayi kyau gawasu kaya dake jikinta masu kyau datsada kai amma ta hadu yarinyar nan Cewar wani gaye yana karemata kallo taja tsaki tana saurin karasawa titi tatari napep. Lokacin datasa kafarta acikin gidan wani sabon farinciki yamamaye dikkan ilahirin xuciyarta ba abundatakeso ayanxu datafara gani sai mekyau donhaka bangarensa tayi kaitsaye tana maikara fadada murmushinta axuciyarta kuma tana tabiya irin kalaman daxatai amfani dasu wajen yimagana dashi, daf daxata shiga falon taji dariya da magana gabanta yafadi jin muryar Adeel datayi tadaki dodon kunnenta rabewa tayi sbd dama tagama gane cewa Adeel abokin siyam ne tabbas amma tayaya xata shiga wajensa maganar dasukeyice taja hankalin ta tatsaya sauraronsu. Kanaji na ai bansan ma tayaya xanfadamaka bane wlh amma nakamu dasoyayyar yarinyar nan sosai saidai akwai masala sbd kamar akwai itama wanda takeso daban agefe shiyasa banmanunamata ba sbd kartaki amincewa datawa soyayyar nashiga wani yanayi amma Siyam tabbas inason ta sosai wlh, Siyam yayi murmushi Ai damasalane irin wannan soyayyar mutkar kasan yarinya tana da wanda takeso kace xakaje kaima kace kanasonta baxata yarda dakaiba kasan mata fa Adeel idan suna son abu sai sunji uwar bari suke hakuri ko tatsiya tsiya su samu, Sukayi dariya tare Adeel yace Nidai inasonta kuma xangwada sa ahta nagani yarinya fa poor girl ce amma tanada tarbiyya da ilimi mahaifiyarta ga kirki marainiyace mahaifinta yarasu Gaban Mowana yafadi jin abunda Adee l yafadawa Siyam, kenan Adeel sona yake wayyo Allah raina wlh baxantaba barinsa yafurtamunba sbd yanada kwarjini a ido na gashi yayimana halaccin dabaikamata nawatsa masa kasa a idoba idanyaxo dakokon barar soyayyata ba, yasalam! Dik tabi tadamu Siyam taji yace Haba malm kafada kawai nakegayama karkawani tsaya duba talauchinsu ka aure yarinyar nan sbd kasamu mata tagari saikataima kesu, nima mai tarbiyya nake nema, dik dayanxu anyi kurinkus mummy tayi aiki Suka tafa tare dakyakyacewa dadariya Adeel yace Kai mutumin bakada dadifa toh kagatundaxu akayi sallar juma ah amma kananan kadakata tatawa sai hira muke bakaje family day innakuba yanxukuma nasan harsu kawu babba an xauna fa Siyam yayi dariya Ahhhh hmmm aikamar kasani musamman yadda yake ji da ya isa yafadawa kowa yaji babbane kwarai ajiki, amma kwata kwata baisan meyakeba Adeel yamike Aaa fa babane karkabari shetan yasaka karaina kawunka dayawa Yaharari sa Nanawa kuma saidai kar akara amma tunda bayakaunar mummy wlh nagamada tsanarsa tunyaushema, Jin Adeel xaifuto yasa naruga bayan wani katon fulawa nalabe inakllonsa yafuto yanaduba agogon hannunsa yasha kyau sanye yake cikin wani blu in yadi maisantsi yakarbesa sosai takalminsa baki da glass a idanunsa shima baki hularsa baka agogon hannunsa baki yYi matakyan dabaitaba yimataba. Batasan dafutowar mekyau ba aikuwa dasauri tafuto daga inda tabuya tatari gabansa kayan jikinsa sak irin na Adeel har hular da agogon, amma fa Siyam dabanne tace aranta Assalamu alaika ya habibi Idanunsa suka sauka akan fuskar kyakkyawar budurwar dake gabansa dabaya yaja yanaso yatuno me irin fuskarnan tabbas yasan fuskar nan tayi murmushi Au bakaganeni ba nicefa wannan dinnan wacce keta sonka kana korarta toh nadawo amma badaxama ba kakusa kadaina ganina kaga xancika maka alkawarin alfarmar danace karoka kuma karoka ko, nicefa wacce tayo ma sako TASLEEM (MOWANA) CIKAKKEN SUNA KUMA TASLEEM TUJJANI KABEER. Kafin yamotsa dashirin yimata magana tafuce dasauri tana kuka itakama kanta tarasa dalilin wannan kukan nata tabbas lokaci yayi daxata daina son siyam lokaci yayidaxa tasan mesonta dole ma tayakice soyayyar mekyau acikin ranta taso Adeel shine wanda yakemata soyayya tagaskiya, amma ta inaxata fara, kaitsaye wajen hajia bera'u ta nufa. Maikyau yadade atsaye yana tunanin yarinyar nan mowana kafin yagirgixa kai yana jin wani abu game da ita kamar tausayi tausayi kamar kuma yadainajin haushinta, yanxu kuma yagane cewa dagaske Allah jarabtarta yayi dasoyayyarsa Lokacin da ta isa falon hajia mai aikinta tasamu tatmbayeta hajia tace tana taron gidasai anjima xatadawo donhaka tanemi gu taxauna sbd yau inbataga hajia taimata sallama ba hartatafi toh batasan ranar kuma dawowartaba, Cankuwa katon falon da suke taron kujerune hadaddu masu tsada gaya ra kuma awajen part din sunata wasa dakayan wasa shugowar siyam yajawo hankalin duk mutanen falon kansa har yaxauna sannan su'adaat tasauke kanta daga kallon sa kawu babba ne yafara bude taro da addu ah sannan kawu salima yayi magana akan matsalolin yara game da yadda tsarin 'yan aikin gidan xa asakesa, nankowa yakawo korafe korafensa ciki harda siyam yadda yace yakamata akarawa mai kulada bangarensa albashi Alhaji Abdullateef ya amince bayan andan ci ansha ana dan taba hira duk da hajia bera'u batafiye maganaba, hakanyasa matar kawu salim Sakina da matar kawu babba mariya da matar aminu Suwaiba sukai masifar tsanarta basa shiga harkarta sbd suna ganinta kamar tana nuna tafisu wani abu tanajidakanta, kumadama hassada alamarin nasu, Bayan annutsu Abba yayi gyara murya yana duban dukkan mutanene dake wajen yana cewa Toh allahamdulillahi dama wannan rana tajuma ah nake jira taxagayo kamar yadda mukasaba xama gashi Allah yakawomu tohm yayi dama wata magana nakeso nasanar muku musamman kaiyaya babba dasalim da Aminu Kawu babba yagyara xama sbd tsammanin sa maganar auren Siyam xaimasa da 'yarsa su'adaat Siyam yasamu matar aure kuma nabincika nasama kwakkwaran bayani akan ahlin gidan shine nace toh xansameku damaganar saikusa lokacin dayakamata kuje anemo masa aurenta, yay........ Dakata kawu salim yatare masa numfashi Lallaine Abdullateef kacika mara kunya daharxaka iya duba idanunmu dawannan maganar wlh, kai yanxu harkanada idanundaxaka iya dubanmu ka fadamana wannan maganar kodayake balaifinka bane sbd aidabahaka kakeba yanxu jinin dan uwanka kake gudu menene laifin su'adaat anxauna anan damu dakai akayanke maganar nan akan xa ahada shi Siyam da su'adaat kuma ka amin ce kawu babba ma ya amince au

Chapter 4 of 11