Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 8
min uzurin waccan kalmar na janye ta tunda ta bata miki rai kin ji? Na san ba zan taba fita ranki ba mun riga mun zama jiji da tsoka... Gidana gidanki ne ba zaki taba barinsa ba..." Ya hanata ci gaba da kallon tuhumar da ta ke masa ta hanyar rungume ta yana karadeta da sumba kawai sai ta sa masa kuka don ta san kawai ya gama da ita. Tabbas ta yarda ta fada taekonso wanda ko ta sami dama zata gaza fita da kashin kanta... Wato tarkon sonsa wanda ba ta gaskata ba sai da rikice rikicen nan nasu suka bullo,idan ya yi fushi sai jininta ya nemi hawa.da ya kaurace mata jiya da yau sai zuciyarta ta nemi bugawa,yanzu ta zo ta tuhume shi ya cika mata ido har dadin bakin da yake mata sun samun muhalli a zuciyarta.da ya rungume ta sai zuciyarta ta warware kullaci ta sami aminci ta ji kamar dukkan matsalarta ta duniya ta warware. Ta fara kokarin kwacewa daga gare shi,sai ya yi dabarar zare makullai din hannunta ya tura aljihu, sannan ya ja ta kujera ya zauanar yana cewa. "Ki yi hakuri fadima!'Yan kwanakin nan sai bata miki rai nake ko? Ki yi hakuri aski ne idan ya zo gaban goshi ya fi zafi... Bari na kawo miki ruwan sanyi ki sha. Ya wuce ba ta . Da ya ji ta bakinta ba. Ta bi shi da kallo tana shakkar halin da ta tsinci kanta tsakaninta da shi. Haka ya dinga janta da maganganu na nuna kauna da sanyaya rai, yana ba ta labaran ban dariya, amma ta ki sakewa damtse ya kawo musu abinci ya yaudare ta suka ci tare yana labarta mata rabonsa da cin abincin kirki,tun shekaran jiya. Ko a ranta ba ta karyata shi ba don ta ga alamar rama a fuskarsa. Ta dubi agogon da ya nuna sha biyu da kwata, sai ta fara neman makullanta ya yi dariya ya ce. "Na adana miki su,ai na yi tsammanin za ki taya ni kwanan a nan". Sai ta kasa musa masa, shi kuma ya ci gaba da himmar dauke damuwa daga zuciyarta,har ya sami rage kaso mai tsoka.musamman da ya ke ya share ta da maganar ciki,kuma hakan ne ya sa ta nutsuwar rai,ta yi bacci har da saleba a kirjinsa. Yaya da ta barshi da tunanin shaukin nasarar da ya samu a kanta.tabbas saura kiri ya gama mallakar zuciyarya,zuciyar da babu wani kaunarsa da ya raba samunta. Ranar bai runtsa ba, don sai sulu sin daren bacci ya rika fizgarsa,amma ya daure masa ya tashi ya gurfana gaban mahalicin shi khushu'I dauke tarin bukatunsa. Sai bayan ya dawo masallacin suka hau rama baccin tare son dama gaba dayansu sun ci bashinsa,kwana biyu,Allah kuma ya yi musu gamon katar week end na,ba su tashi ba sai sha daya ta haura. Haka suka wani yana lallabarta tare da nuna mata kauna,ya share maganar cikin tsab! To ita ma duk da ba ta ba shi raddi to ba ta gwale shi ko kuma turbune masa fuska,sai ya zamana ya sami kansa da farin cikin da bai taba samu daga gare ta ba, tunda ya aureta. Da yamma ya lalaba ta suka fita da zummar ya kai ta su gayar da kawu da momi,kuma ya kirkiro fitar ne don ya faranta mata,sai daiba ta yi farin cikin ba,don ba ta kaunar su ganta da ciki har su fara yamadidi da ita a dangi zancen ya fito Alh ya zatar mata cin amana.Amma babu yadda ta iya tunda abin kunya ne ta nuna masa ba ta son zuwa danginta,sai ta yi shahada ta bi shi suka tafi. Me zai faru? Karbar da suka yi mata ta kada mata ciki kwarai,har ta fara zargin ko dai Abdullahi ya tona mata asirri ne? Kallon arziki ba ta samu daga kawu ba, gasuwar tata ma ciki ya amsa,dukkan kulawarsa da fara'arsa tana ga Abdul,momi kuma sai wani irin kallo ta ke mata,don haka a tsorace ta bar musu wajen ta tafi wajen su safiyya. Babu jimawa momi ta aiko akayi kiranta,ta same ta dakinta.ta nemi gurin zama tana satar kallonm idon momi,wadda sam babu annuri a ciki. "Me ne ne matsayi laila a wajenki da kika yarda ta fi mu sonki,ta fi mijinki sonki,sannan ta fi mu sanin dukkan abinb da zai amfane ki? Tambayar da momi ta jefo mata ke nan cikin kaushin murya wadda sai da ta janyo cikinta ya juya. 1 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 2 38 Saboda firgita don haka ta kasa ko motsi bare ta amsa sai da momi ta kara daure fuska ta ce. "Ko ba kya ji?" Ta muskuta ta kwaso in'ina da rashin ma'anar zance. "Wallahi... Wal... Momi kururuta lamari ne kawai irin na Abdul..... Ba ki ga cin kashin da ya yi mata ba rannan.... Wai kar ta kara zuwar masa gida.... Ni ban ga laifin da ta yi ba....' Momi ta bude ido da kyau tana kallonta cike da takaici,ta ce. "Kin ga kin kara bayar da shaida a kanta da kuma abin da kanwar uwar Alh ta zo mana da shi gidan nan,don kwata kwata babu Abdullahi cikin wannan maganar,tsoro na daya Allah ya sa bai san da maganar kin kai wa likita cikinsa ya cire ba... Haka ne? A kalolin tashin hankali babu wanda bai birkito a zuciyar fatima ba, yanzu ta fahimci lamarin babba ne,sai kawai ta yi zuru numfashinta na bugawa dai dai. Momi ta koro bayani cikin bacin rai. "Jiya har kusan iyanzu Haj sa'adatu kanwar uwar Alh tana nan tana zuba mana tijara iri iri da kashe kashede saboda yunkurin kashe aurenki da kike don ki koma gidan dansu,wai har da yunkurin zubar da ciki... Fatima wacce irin busa duniyar na ke yi miki? Da kin mutu wajen wannan yunkurin naki me za ki fada wa Ubangijiki...? Fatima ta dade kirji cikin tsoro da tashin hankali ba na batun ta zubar da ciki ba, na ta inda maganar ta fita har ta isa kunnen dangin Alh. A rikice ta ce. "Momi inji wane gwanin sharrin? Ni ina ma na ga cikin da har zan zubar?" Momi ta yi mata wani mugun kallo ta ce. "Ko? To wa kike da shi wanda ya wuce kawarki laila? Idan sharrin ne ma ita ta yi miki don ta tabbatar da ita kuka je asibitin.... To ko sharri ne dai ni da kawunki mun gaskata don mun san za ki aikata,ke fa tuni mun fahimci yunkurin kashe auren da kike daga inda Abdullahi ya hana ki waya ya hana ki mota,ya hana ki kula da sauran kasuwanci ki muka san akwai wata akas. To karkade kunnenke da kyau,daga cikin kalaman cin mutunci da sa'a ta yi mana ta furta cewa,idan ma zafin talauci ya fara ratsa ki kike son komawa gidan dansu,to ki yi magana za su dinga yankar miki wasu kudade masu kauri duk wata, su dai ba sa kaunar zamakin cikin a halinsu don ke ba alkhairi ba ce a rayuwar dansu. Sai kuma sakon prof.ya tabbatar miki in sanar miki daga inda kika kaso aurenki shi kuma wallahi ya sallame ki,sai dai ki nemi wani uban ba shi ba. Ni ma kuma na goya masa baya fatima,ki nemi wata uwar ba ni ba, Allah ya gani mun yi iyakar namu kokari har fitinarki ta gajiyar da mu.... To bai kamata a yi mutuwar kasko ba, ke kin sarayar da naki mutuncin da kimar,mu kuma mu yarda mu sarayar da namu ta dalilinki ba... Ina amfanin wulakancin da sa'a ta zo ta yi mana jiya?" Kawai sai momi ta fara hawaye. "Innalillahi wa inna ilaihi raju'un" kawai fatima ke maimaitawa a cikin ranta lokacin da ta ji. Zuciyarta ta yi nbala'in kuntato,tsoro,b acin rai da bakin cikin sun cika ta tafi ita ma sai hawaye ta ke ta kasa tankawa. Sai da ta ga momi ta mike zata bar mata falon sannan ta yi saurin ruko ta ta fara fitar da sautin kuka mai tsuma rai. "Momi ku yarda da ni akwai sharri cikin maganar nan...." Momi ta tare ta a kufule. "Ai daga maganarki ta farko kika kankare sharrin don me? Ko daya babu Abdullahi cikin maganar nan, amma ina fara magana kika kokar kare,babu dalili zai kore ta? Ko kiransa zan yu na ji daha gare shi?" Da sauri ta girgizxa kai cikin kuka,momi ta yi tsaki ta dora. "Sannan kin ce ina ma kika ga cikin da za ki zubar, wannan na jikinki me ye? Ko don kin tanadar masa zubewar kike nufin za ki iya nunke mu bai bai? To me kike shakka ne bayan ke kika haifi kanki? Ai kawai ki yi dukkan abin da ranki ya. Kawata miki, mu mun zama 'yan gani da ido a cikin rayuwarki" Ba ta jira cewarta ba ta yi tafiyarta ta barta tana cikin matsananciyar damuwa don haka ya kyale ta tayi tunani a nutse har zuwa gabar da zai sami abin ce mata. Duk da dare ne hasken fililun titi da na motoci suka sanya shi gane motar da ke gabansa, wato ta Alhaji ce direba na jan Alh da kuma wata mace. Ya juya ya dubi fatima,sai ya lura hankalinta ba ya jikinta,ta rafka taguni kawai fuskarta da alamun hawaye. Ya ciji lebe cikin murmushi keta,ya ce. "Fadima kin gane motar nan da ke gabanmu?" A sanyaye ta dago ta kalli gabanta, kallo daya ta gane abin da ke faruwa,sai kawai ta kawar da kai da sauri,Abdullahi ya sauke numfashi yana kallonta a kaikaice,ya ce. "Dama ya yi aure ne?" Ta yi dif har ya gaji da kallonta ya mayar da kai zuwa titi, har lokacin da motar alh ta saka siginal zata shiga wani gida kayan sanyi,kawai sai abdullahi shi ma ya sanya siginal ya take masa baya. Da sauri fatima ta dube shi bakinta na rawa amma ta kasa magana. Ba tare da ya dube ta ba,ya ce. "Waccan matar ce ta yi min kama da laila, Shi ne nake so in tabbatar". Ambaton sunan laila kawai wani katon rauni ne a zuciyar fatima bare batun wai ga ta tare da Alh,da kuma wannan daren, sai ta ji numfashinta ya fara sasarfa tana bin motar da kallo har ta yi fakin,su na ma suka yi fakik nesa da su. Direba ya fito ya bude wa Alh,sannan laila suka fito suka shiga ciki tare. Abdullahi ya dauke kai yana kada kai hade da rera wakar cin amanar kauna,fatima ta yi dif saboda zuciyarta ta kara wani zafi,ji ta ke ina ma yanzu ta hadiye zuciyar ta bar duniyar gaba daya, wanne irin tashin hankali ta ke tsintar kanta a ciki yau? Sai da abdullahi ya koshi da yarfeb da yake mata,sannan ya yaficeta ya balle murfin motar yana cewa "Zo mu shiga mu ga abin da suke yo don kar mu yanke musu hukunci da zato". Kawai sai ta sami kanta da zuciyar balle murfin motar ta fito ta bi shi suka jera. Alh da laila an kama kujera ana ta kurbar fresh milk cikin annashuwa, Abdullahi ya zarce karbo musu na su kason,amma fatima idonta rufe ta nufi wajen su kai tsaye. Alh na dora ido a kanta zumbur sai ga shi a tsaye cikin tsnannin rikita,da ambaton. "Fatima! Ya ya aka yi kika san ina nan? Cikin tsananin fushi ta ce. "Ba kai na biyu ba, wannan muna fukar na shigo in gani da idona.." A dan kunyace laila ta ce. "Da na yi miki me? Don kin ganmu a nan tare? Ai matsalarki muka zo tattaunawa a sirri". A tunzure fatima ta ce. " Ai ni ba ni da matsla wallahi,ke da shi ku. Ne masu matsala don ba ku ganni ina ketare gwadabe na ba..." Alh ya yi dira dira cikin rudewa,ya yi kamar zai ruko hannunta, ta yi saurin ja da baya. Dai dai lokacin Abdullahi ya iso da ice cream a hannunsa na dama yana sha,yana kuma rike da wani a hannunsa na hagu,da alamin ko a jikinsa hayaninyar da ya tarar.ya mikawa fatima daya ice cream din yana cewa. "Ashe abokin arziki kika hango kik barni ni kadai? Ta runtse ido alamun tsanarsa bacin rai ta bude idop tana duban ice cream din da yake nuna mata,ta ce. "Abdul ba zan sha ba. Sai kawai ya ja kujerar ya zauna yana lasar ice cream dinsa,ya ce. "To ku gama gaisawa mu tafi" Nan fa alh ya zo wuya,cikin shakewar numfashi ya ce. "Abdullahi har ka kai tsawon da zaka yi min wannan cin mutuncin,ka san kuwa ba ka isa ba? Me ya hado ka fita da fatima....? Karaf cikin masifa fatima ta tari numfashinsa. "Kai da girmanka me ya hadoka fita da wannan tsinanniyar?" A rikice Alh ya zaro ido,ya ce. "Fatima goyon bayansa za ki yi, kina nufin abdullahi ya fi ni matsayin a wajenki...? Fatima kin san kuwa muhimmancin ki a rayuwata...? Na rantse miki zan iya komai don na tsira da ke, ciki kuwa har da kisan kai idan ta kama... Saboda haka kai ka shiga taitayinka". Yasa kai ya fice a fusace. Fatima ta janyo wani dogon tsaki ta dauke kai kai daga kallonsa ta sauke akan laila wadda ta yunkuro ta ke son ta wanke kanta. "Fatima ni kike kira tsannainya...? "To me ce ce ke? Mijin aurenki ne ya kwaso ki a bayan mota kuka nufo nan don ku sha minti, da wannan daren ko? Kawance da ke ai bai yi ba laila..." Ita ma laila ta zo wuya don haka ita ma ta yunkuro cike da bacin rai. "Ai babu bambanci tsakanina da ke, shi wannan matsiyacin da kika dauko kuka taho nan me ye a tsakaninki da shi...? Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 2 39 Fatima ta tare ta. "Akwai abin da tsinancewar ki ta hana ki taka matsayinsa,wato aure,kin san kuwa ko banza masa ta fi kashin shanu,don ko me wankin takalminsa kika samu ya adana ki a dakinsa ya fi wannan gantalin da kike... Ko da yake ina tsammanin kin yi zaton gulama da sharrinki ya ishe ki taka matakan da na taka, kika kwashi kafa dangin Alh tsugudidi..." Jin fatima ta debo fasa mata ciki ya sanya ta tarewa da nufin tona mata asirin gaban mijin da ta ke shakka. "Auren naki na gaibu,mara ma'ana da manufa... Ai in dai bariki ne, to tare muka kwaso shi da ke,ko kin taba ni zuba da ciki? Ni kuwa satin da ya wuce ma na raka ki zubar da ciki,a uare kika sami cikin kika zubar?" Sai a lokacin fatima ta tuno akwai Abdullahi a wajen.ta yi saurin dubarsa cikin tsoro da firgici amam sai ya dauke kai,fuskarsa kuma ba ta fassara mata komai ba,ya koma bin laila da kallo wadda ta ke ficewa daga wajen. Fatima ta yi tsaye kawai a wajen cikin yanayi na kila wa kalan yadda rayuwa zata cinmata. Abdullahi ya dake ya karasa shan ice cream dinsa ba tare da ya dubeta ba,ya ce. "Zo mu tafi" Inna lillahi wa innan ilaihi raju'un,ta ambata a ranta ta sa kafa ta biyo shi cike da fargabar ruwan bala'in da zai sheka mata idan sun koma gida,ko kuma kalar fushin da zai mata wanda ta tabbatar wanna dole ne daga yadda ta fahimci takunsa a yanzu. Bai ko jira ta sun jera ba ya wuce mota,ita kuma ta bi shi kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, ya shige mota abinsa ba tare da ya bude mata kamar yadda ya saba ba. Jikinta na bari ta bude ta shiga ya tashi motar ya fice a fusace. Suna fitowa daga harabar wajen suka wuce laila tsaye tana ta faman tare adai daita sahu,suna wucewa saboda daren da ya fara yi. Har sun dan gota ta kadan sai Abdullahi ya sauka titi a hankali,ya yi fakin bai tankawa fatima ba ya fice daga motar.ta bi shi da kallo cikin dukan zuciya,sai ta ganshi kai tsaye laila ya nufa. Nan numfashinta ya fara yin sama sakamakon hargitsawa da cikinta ya yi,ciwon cikinta ya dawo mata sabo. Duk da haka ba ta kasa dauriyar tattara hankalinta ka su ba. Kafin ya karasa laila ta fara tafiya,don haka yana tarar da ita suka jera. A nan zan dakata sai mun hadu a littafi na uku taku..... Amierah S man meh copy n paste. .... Compelled by hauwee jidderh abdulkadir AKA mss jidderh An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 8 of 8