Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
sauraron muryarka kawai zata iya rage wasu kewar". Da zolaya ya ce da ita. "Idan aka fasa maganganun nan naki fa tarin ma'anini ne da su". Ta kada kafada tare da dauke kai. "Na sani,amma na san duk yadda za a fassara maka wasu ba lallai ka fahimta ba, saboda bambancin dabi'u da ke tsakaninmu ta dalilin jinsi". Ya tari inda ta mayar da kanta yana cewa. "Ni kuma sai na ke ji a raina na fahimce ki fiye da yadda na fahimci tafin hannuna,duk da kawu a fuskokinki kin fi nacin nuna min daya". Cikin rashin fahimta ta ce. "Waccec?" Da sauri ya amsa mata. "Bayyana abin da ke cikin zuciyarki, ko da bayyanawar zata ci karo da burinki". Ta yi kasake,sannan ta ce. "Me kake nufi?" Ya ce,"ki tambaye kanki yadda kike jina a ranki game da sadiya. Ni dai irin wannan na daga cikin abin da ke kara min karfin gwiwa a cikin soyayarki.ina ji a raina duk ranar da sauran fuskokinki suka zama 'yan gida a tawa fuskar da wuya a sami namijin da zai kai ni farin ciki". Ta jima tana nazari,amma ta kasa cankar inda ya dosa,kawai sai ta yi masa shiru,ya jima yana kallonta sannan ya ce. "Ki tashi ki shirya kafin sannan na dawo daga duba mata talabijin" Ta mike a kasalce tana cewa. Jirani zaka yi na shirya,k duba mata mu wuce". Ba ta dami kanta da wata kwalliya ba, ta baza hijab suka fice,tiryan tiryan har dakin sadiya. Ta sami kujera ta harde tana kallonsu,sadiya na satar watsa mata harara tana yiwa abdullahi bayani cikin yanga. "Wani film nake kallo na tashi sallah,wai ina dawowa na kunna sai ta ki samuwa". Ya kunna talabijin din yana cewa. "To ke ce ba ki da aiki sai na kallo ba dole talabijin ta buga ba?" Ta kara karya murya,ta ce. "To Abu Turab ba sai da kallon mutum zai kara gane inda duniyar ta sanya gaba ba, kai ka ga film din da nake kallo yanzu? Labarin wata tsohuwar mace ce ta gama cin nata zamanin kawai ta sami yaro ta aura,kuma don zalunci ta raba shi da matarsa da 'ya'yansa.ta karade danginsa da kinibibi kowa ta mallake,shi kansa sai yadda ta so ta ke juya shi, ga ta yarinya sabon jini a gefe,kai! Ai zawarawa ba su yi ba wallahi". Da yake Abdullahi ne bai gane inda tuggun yake ba a maganar sadiya,sai ya amsa mata da gaskiayar ransa. "To ina ruwan so da tsufa? Sai nawa za ki ga tsohuwa ta yi abin da yarinya ta kas,su 'yanmata me suak sani ban da tsabar girman kai da son iyawa,amma kwakwalwarsu girman kai da son iyawa,amma kwakwalwarsu empty. Sadiya tana juya idanu ta ce. "Koma dai yaya suke sun fi daraja tun da manzon Allah(S.A.W) ya yi umarni a aure su. Ya kuma amsa mata. "Sai kuma kika manta shi da bazawarar ya fara,wadda ta yi abin arzikin da ba a sami budurwar da ta yi abin arzikin da ba a sami budurwar da ta yi kamarsa ba. Gudunmowarta a tarihin muslunci gagaruma ce. "Ai ba zaka taba hadata da matan yau ba, masu auren mai kudi su tatse shi tas! Daga bisani su fita su sami yaro karami su aure,su ma yaran da rashin sanin ciwon kai sai kwadayi ya rude su su afka,sai ka ga sun dawo a hannu,babu wan babu kanin, babu kuma kudin kuma babu KWANJIN su kuma an sha da kuruciyarsu". Abdullahi ya sunkuya yana duba yadda ta hada wayoyin ya ke amsa mata cikin dariya. "Ai gaba daya sun yi min dai dai,da tsohuwar da yaron. Ai ba a hana mace ta auri sa'an dan cikinta ba ma, shi ma kuma an ba shi damar aure saboda kudi,idan kwadayin ya kai shi auren tsohuwa mai kudi ai ba kauce hanya ya yi ba, sai ki ga ma ta fiye masa fakiriyar budurwar da babu kudin,babu kuma kyan hali.yana fama da talauci yana fama da rashin tarbiyarta.ita kuwa tsohuwa ta san darajarsa,ya san tata, shi ke nan ungulu ta biya bukata sai balbela ta tafi da farinta. Sadiya ta yi iyakar kulewa,dan ta yi zargin da gayya ya yaba mata wadannan maganganun, musamman da ta ga hankalin fatima kwance tana murmushi. A kuntace ta ce. "Amma dai ba haka aka so ba". Ya ce,"wa ya fada miki? Aure fa wuce duk yadda kike tsammaninsa.duk tsufan mace da wahala ta rasa abin da zata burge wani namiji da shi,bare a yi kirarin ya zauna da ita bisa tilas,kin jahilci labarin ne sadiya,amma a mata babu babba babu yarinya,mai hikima ce kawai zata iya samun kan mijinta". Sadiya ta yi dif! Ranta duk ya baci. Ganin ta yi shiru ya sanya fatima sako baki cikin hirar tasu. "Kayya abdul! Ai duk wanda ya rigaka bacci dole ya riga ka tashi,kuma da kokari ake samun daukaka ba da kake ko uba ba, amma fa ga wanda ya gane cewa shi zaman bariki ba gayya ba ne, kowa da kafarsa ya zo, kuma halinsa ke janyo masa jama'a". Sai yanzu abdul ya fara caftar karatun,ya saki wayoyin da suka harde yake gyarawa da fuskar damuwa,ya ce. "Haka ne. To mu bar maganar". Sadiya ta fashe. "Don me za a barta,dan kar in fadi gaskiya rai ya yi daci? Ai duk wanda bai ji kunyar hawa jaki ba, to kuwa jaki ba zai ji kunyar nana shi da kasa ba". Nan da nan abdullahi ya bata rai. Ya tsuke ido,ya ce. "Bana son rashin mutunci fa sadiya, dama don haka kafa da kafa kika je kika rakito mu?" Cikin tabe fuska ta ce. 2 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man INA HANYA GOIN BACK TO KADUNA FROM ABUJA.... Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man .Zuciya d kwanji 2 25) "A kaddara ma haka ne, idan ba ta yi kasadar biyo ka ba zata ji abin da ba zai wa ranta dadi ba ne? Ko tana ganin kafata a dakinta da zata ganni da kai ta ce zata shiga tsakani, kuma da zata yi min maganar zaman bariki ba gayya ba ne,da fa ma ba a san asalin ungulu ba sai ta yi burgar daga masar ta zo. Na ga kina amaryaki ma shar kofar danki ma bai ishe shi kallo ba, sai da aka shiga aka fita aka wasko kansa shi ne yanzu za ki yi min maganar hali? To jiya ma me ta yi bare yau, kin san auren fari shi ne auren so,ke kuwa kin watsar da naki ladan sai dai ki ga ana yi.... Kin fara ganin shaida dazu da kuncinki ya kusa diban yatsu biyar....!" Abdullahi ya zuba mata ido cikin bacin rai har sai da ta dire sannan ya kada kai, ya ce. "Shi ke nan sadiya,kin kyauta sai dai ki sani ba fatima kika wulakanta ba, ni kika ci wa fuska... Fatima zo mu tafi." Ya yi gaba fatima ta mike tana murmushin yake,ta ce. "A'a ka tsaya ka gyara mata talabijin mana kar dukan ya yi mata yawa. Na kwace mata miji kuma babu abin dauke kewa, sorinki yarinya tunda kika rasa abin da zai hana yaron mijinki daga kai ya auro tsohuwa sa'arsa,ke dai kurunciyarki ba ta amfane ki ba wallahi,dole ki dau hakurin rungumar filo idan kina kan layi,dan ma kin ci sa'a na kulle kofar bare ki fada layin kwana shidda..... Wata kila da wata rana karfe biyun dare za ki burmo mana kofa..." Sai da abdullahi ya hada da jan fatima suka fice daga dakin suka bar sadiya da hayaninya har da ashar. Cikin mutuwar jikin bacin rai yake,don haka babu wanda ya tanka wani har suka isa gidan abincin,suka yi odar tuwon biski da miyar taushe da farfesu tare da kayan marmari,suna ci kowa bakinsa a dinke,kafin ya ci rabin nasa har ta share nata sai fili,ta fara shan kayan marmarin cikin yanga,ya tsura mata ido cikin tunanuwa barkartai. A nutse ya ce. "Kin koshi kuwa?" Ba tare da ta dube shi ba,ta ce. "Idan ban koshi ba cewa zan yi a karo min?" Ya yi saurin girgiza kai, ya tura mata nasa. "Ki ci wannan,bari na ji da farfesun tunda ba kya ta tasa". Babu musu ta ja farantin da kwanon miyar ta ci gaba da ci. Bai gaji da kallonta ba, ya hada da kallon nata da shan farfesun,ya zuba mata ruwa ya tura mata. "Yau ba ki ci abincin rana ba ko?" Ta yi shiru ta ci gaba da sha'aninta, shi ma farantin ta ture,a sannan ne kuma ya jefa mata tambayar da ta makale masa makoshi,tun kwanaki da suka gabata. "Fatima me kika yi da pt-strip?" Ya ce,"wanda na gav maryam ta siyo miki kwanaki,kuma me ake yi da pt-strip?" Ta yi fuska,ta ce. "Ina tsammanin gwajin ciki ake da shi,ni kuma a ina zan sami ciki?" Ya yi dariya,ya ce. "To fadima mace da mijinta sai a tuhumeta inda za ta sami ciki? Fadima wannan hausar ai ba ta hadu ba". Ta fara goge hannu sannanta matsi santizer tana cewa. "Masu auren shiri ke nan, ni yanzu aka ganni da pt -strip ma ba sai a gudu ba, mu shafe wannan maganar,wajen yara zaka ga pt-strip ka nemi ba'asi sai ka bari idan mun koma gida ka saka damba,ka kai mata kwanan dan nasan ta fi ni bukatarsa". Ya cije lebe yana dariya ya kada ido,ya ce. "Da alama kama kin fi ta himma,tunda ga shi ba a ga pt strip a wajenta ba aka ganshi a wajenki,ko ma mene ne ke yake shirin yi wa lamba,kuma idan ba ki tabbatar min an ga pt- strip wajenki ba to in tabbatar miki yau zan saka dambar da za a ganshi a wajenki wani makon". Ta ji batun a jikinta,amma sai ta hadiye ta tabe baki,ta ce. "Kamar kana da wannan himmar ka ajiye yaran mata shekaru rututu babu labari..." Ya tare ta da cewa. "To himma biyu ai ta fi daya,yanzu ba ga shi da himmar tawa ta sami karfin gwiwar taki ba suna shirin bayar da mamaki har duniya ta gani....ai ko cikin miliyan na mata dole in na kira ki jaruma". Ta ja kujerar saboda rasa amsar ba shi. Ta ce "Kan ka ake ji, ni zan tafi gida". Dole shi ma ya mike yana dariya,ya ce. "Wato ke dai ba za a taba jan hirar arziki da ke ba ko? To za ki yi guzurin biskin ne,ko kuma gobe kin dawo?" Ta yi tafiyarta ta kyale shi, sai da ya sallame su ya tarar da ita jikin mota suka yi gida yana kwasarta da maganganu,ita kuma hankalinta na ga lissafin yadda zata kubuta daga tarkonsa na sa wa cikinta ido. Sai fita cin abinci tare ya zame musu dabi'a,duk ranar girinta tunda ta fi son dukkan abincin da ya danganci tuwo,shi kuma ba shi da sukunin girka mata, sai ya dinga jifan tsuntsu biyu da dutse daya,wato ya samar mata farin ciki ta hanyar ba ta abincin da ranta ke so, da kuma samin damar hira da ita ko zai samu ta fasa masa cikinta dangane da abin da yake zargi. Shi yasa yake dokin ta karbi girki,yayin da yake shiga damuwar abincin da zata ci duk ranar da ba ta da girki,dan ma ya samo dabarar siyo mata ya kai mata. Sai wanan ma ya zama wani kaso a cikin abin da ke dagawa su sadiya hankali,shi yasa wata safiyar da zata fita girki yana ta hanzarin ya fita saboda siyowa fatima karin kumallo,ita kuma sadiya ta kankare shi dan tsabar neman rigima wai sai ta raka shi,ya ce. "Sadiya wacce tsirfa za ki tsiro idan zan je gaishe su sai na tafi da ke?" Ta ce,"ina jin ai ba a kaina aka fara ba, ranar da ka kwaso fatima ka kawo min ita wai ta rako ka duba min talabijin ita ba ta yi tsirfa ba?" Dole ya hadiye ya ce. "Shi ke nan mu je". Suka fara ta dakin Hindatu,ita kanta Hindatu sai ta ga wani sabon abu, ranta ya yi mata babu dadi, musamman da yake tana da bukatu na tambayar fita da ana tambayar kudi. To ga sadiya ta tsaye mata kerere kamar wani badogariya,sai shi Abdullahin ne ya zauna har ya sanya mata albarka a abincin da ta ke ci ba tare da ta yi masa tayi ba. Hindatu ta yiwa sadiya kallo tara ahu da murya kasa kasa ta ce. "Sauda ke nan" Sannan ta mayar da kai ga abdullahi,ta ce. "Ina ta neman wayarka tun jiya ban same ka ba, sam na manta da maganar dubo Anti siyama...." Ya yi fuska ya ce. "Tunawar yanzu ma ba zata amfane ki ba, tunda kin karya ka'ida". Ta yi dariya ta ce". "Haba Abu Turab,uwa daya uba daya ai ya fice wasa, hakuri zaka yi a kawar wa da ka'idar nan kai.... Ba zan kuma ba". Ya ce,"haka dai kullum maganarki ke nan,ni dama tun jiya da na ga uban turaren da kika yi na san yau sai kin tambaye ni fita. Wai har yaushe zan dinga maimaita a daina tambaya ta fita ranar da za ayi ta?" Ta kara dagewa. "Hakuri zaka yi Abu Turab,antu ba zata ga kyautawar mu ba, ace sai an kwashi kwanaki zan je dubo ta...". Ya tare ta. "Kar ki hada ni da ita,a dawo lafiya. Ya zaro dari biyar ya mika mata. "Ga kudin mota". Ta shiga juya dari biyar din tana bin aljihunsa da kallo. "Abu Turab... To kudin da na yi maka magana jiya fa.... Ka ce yau zaka ba ni..." "Ni da kaina?" Ya fada ba tare da ya jira ta ba, ya ce. 3 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 2 26) "Sadiya mu je". Hindatu ta biyo shi har da gayyar ture sadiya tana yi masa magiya,sai da ya ce. "Idan kin yi cinikin turaren ki ara min." Dole ta hakura ta kyale shi cike da haushin sadiya wadda ta tabbatar idonta ne ya hana ya bata. Cikin magagi fatima ta bude musu kofar ta koma ta zauna da bacin rai,dan tana ganin kamar gayya ce ta sa ya kwaso mata sadiya dakinta. Ta yi kicin kicin shi kansa ko kallonsa ba ta yi ba. Tunda ya ga haka sai ya shafa mata lafiya, kai tsaye ya wuce kicin yana cewa. "Me za ki ci yau?". Ta yi masa banza,sai da ya shiga kicin din ya fito ya kuma tambayarta,kamar dole ta amsa. "Ba ni da zabi". Ya dube ta da kyau,sannan ya dubi sadiya da ta tsaye musu,ya san kuma ganinta ne ya tunzura fatima,duk sai ya ji haushinta ya turnuke shi,dole ya hadiye ya kuma wucewa kicin ya jima tsaye ya ma rasa abin da zai yi fiye da mintuna biyar,kawai sai ya fito yana cewa. "Ko za ki koma baccin,bari idan na je office zan turo a kawo miki abinci,yanzu in na tsaya zan makara".. Sai ta kasa tanka masa,bare sallamar da yake mata, suka fice sadiya biye da shi tana jin kamar ta yi fifike don farin ciki.ta ga ma ashe ita ta sake tun tuni ta ba su damar shigar mata hakki. Fatima ta dauke kai daga kallon kofar da suka fice tana cije lebe,tare da gyada kai, cikin tunanin mafita tare da alkawarta wa kanta daukar mataki. Haka kuwa washegari sadiya ta ga hanyar ya gama shirinsa yana ta faman kunci dan kar ta sami kafar cewa zata yi masa rakiya kamar jiya,ita kuwa ta share shi yana mata sallama ta makale jakarsa a kirji ta biyo shi,babu yadda zai yi da ita suka tafi tare,don haushi Hindatu daga bakin kofa ta sallame su, don tana bude kofa ta ganshi sadiya ko gaishe shi ba ta yi ba ta ce masa". "A dawo lafiya,Allah tsare. Ba ta ko jira cewarsa ba ta rufe kofarta. Ya yi murmushi kawai ya kada kai, suka doshi dakin fatima. Ya sa key din hannunsa ya bude,amma sai ya ji alamar sakata cike da mamaki ya fara kwankwasawa dan bai taba riskarta karkama masa sakata ba. Babu jimawa ta zo ta bude bayan ta tabbatar tare yake da sadiya. Ba Abdullahi da ta danawa tarkon ba, hatta sadiya sai da ta yi turus da ganin fatima a haka, tana sanye da farar rigar bacci sol mai zubin net,iyakar rabin cinya wadda da kadan ta zarce babu saboda babu abin da bai bayyana ba a jikinta har da kalar pant din da ta ke sanye da shi wanda shi ma yake fari. Da alamun kasala ta jagorance su cikin falon,ta yi zamanta kan kujerar tana doguwar hamma. Da kyar Abdullahi ya gama kokawa da numfashinsa da kwakwalwasa mai hajijiya da shi saboda ta gano masa hakikanin fatima da ganin da bai taba mata ba.ya samu ya zauna a kujerar da ke fuskantarta kamar wani mutu mutumi. Ya kokarta ya ce. "Sannu da bacci". Ta yi masa wani duba da wutsiyar ido, sannan ta kawar da kai ba ta tanka ba. Ya dan yi kasake yana lalubar ta inda zai sami ganin dariyarta. Ta sake dan kishingida bayan ta yi doguwar hamma,ya ci gaba da nacin kallonta,muryarsa na rawa yana kokarin dai daita. "Wai duk baccin ne, yanzu kike tashi ne?" Ta sauke numfashi cikin yauki ta ce. "Wallahi,kin tashi lafiya,sadiya ya ya dawainiya?" Ta sauke ganinta ga sadiya ke nan wadda ta yi mugun muzanta sai kikkifta ido ta ke tana kallon Abdullahi wanda ta ke jin ma zata iya makanta Abdullahi yanzu ta hana shi wannan kallon maitar da yake wa fatima, har ma ya kasa magana sai kallon kawai,ita kuwa gimniyar ta yi kamar ba ta san yana yi ba. "Ina ka saka min kayan da ka wanke rannan?" Ta tambaye shi cikin tsura masa ido fuskarta da walwala. Bakinsa na rawa ya ce. "Ba ki gansu ba?.... Ta tare shi da mikewa ta nufi daki. "Ban gan su ba". Kai tsaye ya tashi ya bita yana cewa. "Bari mu gani." Ya bar sadiya da gyaran murya dan ta tunatar da shi ya san da ita, yana shiga ya turo kofa. Har da murda key dan yana zaton sadiya zata biyo shi. Sai fatima ta juyo suka fuskanci juna fuskarta na baYyana alamar tuhumarsa da rufe mata kofa. Ya kama hannayenta a rikice ya ce. "Fatima,me yasa kike saka irin wadannan kayan baccin ni a tare da ki?" Ta yi masa kallon rashin fahimta,sannan fara bin rigae jikinta da kallo. Ya fara yi mata shishigi,yana cewa. "Ki dinga sanya kaya masu kauri idan kina ke kadai dan yiwa shaidanu riga kafi... Ko ba ki san kina da kirar da za a kalla a kasa kawar da kai ba..? Ni kima ina da kishi musamman a kanki,kin ji fatima. Kamar dama bai fada don ta amsa masa ba, ya fara sumbatarta cikin gigita da shauki,kamar a majigi sai ta biye masa suka bata hankalin dare matuka! Fiye da mintuna goma sha biyar,ita kanta da ta dana tarkon ta manta tarko ne,ta manta da sadiya bare shi da ya fi ta zakewa. Suka samar da wasu guraba masu muhimmanci a zukatan juna,Abdullahi ya ba ta assigment mai zafi na neman dalilin da ta ke kasa mallakar kanta,idan sun shaki numfashi juna.... Ta kasda sanin dalilin tana ji kuma a ranta ko rabuwa da shi zata sha wannan kewar.... Abdul ya iya da mace ya iya bayyana mata kauna 2 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 2 27) A yau ta samar wa zuciyarsa nutsuwar da ya jima cikin damuwa da tantamar matsayinsa a zuciyarta, ya yarda ya sake ne shi yasa fatansa ke nisa farin cikinsa na binsa a baya. Tabbas duk lokacin da fatima ta karbi soyayyarsa sai ya shiga sakun mazan da suka yi sa'ar auren kyawawan mata wadanda suka karanci so. Ya dago ta da riko kafardarta jiki a sanyaye. "Fatima,kin tuna cewa cikin wata nan bakwai mu ke da aure?..... Dadewa tare na nufin sabo da komai ma idan ta kama har da gajiya..... Amma ni har yau ban saba d sonki ba don kullum In wayar gari da wasu sababbin sonki wanda ban taba dandanar irinsu ba, saboda ganinki ba ya hana in ganin kyan fuskarki kullum,yau fiye da jiya, yadda kike mu'amalanta ta ba ta sa ni yanke kaunar za ki shugabantar da ni cikin duniyar wata rana ba kuma ga shi ina zama wani sabon shiga duk san da na shaki numfashinki...... Amma na san ba komai ba ne sai tsananin kaunarki da ta cakude da jinina,fadima ban taba jingina kaunarki da wani dalili ba.... Kin amince min? Ki yarda da ni..." Ya ci gaba da kura mata idanunwansa da suke fitar da kwalla suke son su yi tasiri a zuciyarta su sanya ta yin abin da babu niyyarsa a burikanta, sai ta yi kasa da ido,ya dago kanta yana nuna mata agogo,a sanyaye ya ce. "Kin ga kin sani na makara fadima,duba agogo me zaki ci? To taya ni mu gyara dakin ko" Ba ta tanka. Shi ba, kuma ba ta taya shi ba, sai ma ta nufi ward robe ta dauko after dress ta maka ta yi zamanta kan sofa tana kallonsa har ya gama da dakin ya fice falo,sai can jimawa ya shigo mata. "Zan tafi fatima". Ta dago ta bi shi da kallo, ya daga gira ya ce. "Ki yi hakuri,zan turo miki break fast kamar jiya,na makara...ki yi min wannan uzurin". Sai ta sami kanta da daga masa hannu da sarkarkiyar murya,ta ce. "Babu komai ka je,ba sai ka ka turo ba zan nemi abin da zan ci". Ya yi kaske yana kallonta, murna duk ta cika masa zuciya.... Da ya rasa abin da zai ce mata sai ya debo mata sambatu. "Dama ace ke za ki karbi girki,da da wuri zan dawo na yi miki tuwo da kaina". Ta ci gaba da sa masa ido kawai har ya gama sambatunsa ya fice. Ta mayar da kai a hankali,tare da son fadawa cikin tunani,sai a sannan sadiya ta fado mata,da sauri ta fito falon sai ta ganshi wayam! Sai Abdullahi da ke ficewa. Ta zube a kujera cikin tsananin dariya tare da furta. "Yarinya kin kuma kiran me alewa ba ki da kobo". Shi kansa Abdullahi sai a lokacin ya tuna wai fa tare da sadiya ya shigo.dan haka a tsorace ya silale ya bar gidan. 1 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 2 .28) A gaggauce fatima ta yi wanka zuciyarta cike da fargabar yadda zata fita ta dawo ba tare da Abdul ya san da fitarta ba,ita kanta sai ta dinga mamakin tsoron da ta ke masa, wadda ta ke jin ba tsoron ne kawai ba har da rashin son bacin ransa, da kuma hangen matakin da zai iya dauka wanda ta ke canke canke akai.da fadawa kawu sirrinta zai fanshe ko kuma da yi mata dukan shan gishiri? Bayan wannan komai nasa ya karade zuciyarta, tana tuna shi a muhimman lokutansu,da jarumtarsa wajen bayyana mata kauna yadda ya kware wajen gigita fuskokin shaukinta, sannan ga bautar da yake mata jiki da jini. Wadannan dalilan suka sanya ta jin kamar tana son ta ci amanarsa a yunkurin ta na zubar masa da ciki musamman a matsayinsa na me neman haihuwa ido rufe. Wannan alhini bai hana ta shiryawa tana duban agogo ba,wanda ya nuna sha daya da 'yan mintuna. Tana tsaye a falonta ta jaka da mayafi a hannu,sai ga kawarta laila kuma tafinta tsakaninta da Alh a lokacin da ta ke zaman gida. Ta yi farin ciki da ganinta sosai,suka gaisa sannan suka zauna suna bincikar labarin juna. "Sai yau nake ganinki a gidan nan laila kin watsar da ni kin barni ni kadai da azancina. Abdullahi na ta samun nasarori a kaina,ina Alh? Laila ta dinga bin dakin da kallo cikin tabe baki, sannan ta ce. "To in zo in yi me a wannan bakin gidan? Ai da alkwarin na yi har ki bar shi ba zan tsomo kafata mai daraja a cikinsa ba. To da alama ke ba kya ganin duhunsa da kuncinsa,tunda na ga har wata 'yar kwarya kwaryar kiba kika yi.... Kin bar Alh na can yana fama da jinya,to jiya ya sauka kasar nan kuma shi ya buga sammako da kansa ya same ni har gida ya ce lallai na zo na ji inda naki lissafin yake,ya ya aka yi kika bace haka... Fatima ina wayoyinki?" Fatima ta dan yi walai da ido alamar bayyana jimami,sannan ta nuna kofa tana cewa "Ya karbe". Laila ta ji batun gingirin,ta tsule gira ta dubi kofar sannan ta dubi fatima ta ce. "Ya karbe?"Wanne sale dan kwadago ya samu haka har ya sami wannan zakewar,ke kuma wuka ya dora miki a wuya ya kwaci wayoyin ko kuma barazana ya yi miki da bindiga cewa,in kika kuma wata wayar zai harbe ki? Fatima ta yi murmushin yake tare da sauke ajiyar zuciya mai bayayyana gajiyar zuciya,ta ce. "Ya faki idona ya kwashe,sannan ya toshe hanyar da zan fita bare in mallaki wata wayar,tsawon watannin nan bakwai fa da muka yi tare ban yi fita ta kai goma ba, kuma ga kafata ga tasa,sai sati biyun da suka wuce na saci hanya na je asibiti, shi ma ba ki ga dan bikin da ya yi min ba, har fa da mari...." Labarin ya girgiza laila kwarai,ta jinjina "Mari?" Fuskar taki ya mara fatima? To dan ganye ne?" Fatima ta yi murmushi,ta ce, Ko daya idan ma yana sha ba zai wuce giyar sona dake bugar da shi ba. Na rantse miki na kasa gane wanda ya fi so na tsakanin sa da Alh....." Laila ta yi saroro kawai tana kallonta,tara gira ta ce. "Da alama kuma kin biye masa.... Soyayyar da yake miki ba hujja ba ce da zaki yi zaman watanni bakwai a gidansa.... Ke ni gani nake ma tsaurin ido ne mutumin bai fice baranki ba ya iya furta soyayyarki". Fatima ta jima shiru tana juya maganganun lailan,ta yarda a ranta laila ba ta san waye Abdullahi ba,koda yake suna da bambancin dabi'u da alkibla ita da laila. Ma'ana kudi sun runtse idon laila,yayin da ita ta ke son rayuwar'yanci da rayuwa da abin da ta ke so wanda kuma ta. Zabar wa kanta da kanta da dalilan da ko kusa baba kudi a cikinsu. Sai ta sami kanta da kwalla,ta dubi laila ta ce da ita. "Ki yi farin ciki laila da Allah bai yo ki kamar ni ba,kyan tarnaki ne a cikin rayuwa wanda mafi yawan lokuta yake hana mutum zabar abin da yake so ake hada shi da zabin wasu,sakamako an yi masa shigar sauri don a rayu da shi dole! Na tabbatar yawancin kyawawan mata ba sa auren mazan da suka dace da burinkansu". Cikin fuskar rashin fahimta laila ta ce. "Me kike nufi?" Fatima ta yi saurin amsawa. "Ba ki ga aya a kaina ba? Na zauna da Alh bisa kaddara ta kara hadani da Abdul..... Wanda nake ganin kamar ya fo Alh zafin so na... Kamar ya fi shi sadaukarwa..." Laila ta tare a kufule. "Idan kin zauna da Alh bisa dole,wallahi ba ki fadi ba zahra'_ don ya isa ya ajiye kamarki a gidansa,sannan ya mallaki wani abu da zai rage miki takaicin kiyayyarsa....'Udi ai su ne a yanzu,don haka ban ga dalilin da za ki zauna da mai gidan nan ba, me ya ajiye,da me ya cancanci mallakar mace kamar ki... Da me za ki karasa ragowar rayuwarki..." Fatima ta yi saurin tare ta fuska a hade. "Wannan ra'ayinki kike fada laila, akwai muhallai da yawa wadanda ba kudi ke taka rawa a cikinsu ba, musamman na dadada zuciya ba, laila ni ban fifita darajar kudi a cikin raina fiye da bukatun da suke gina zuciyata ba, idan dai zan samu in ci kuma in nema dai dai gwargwado in samu ba zan rasa ba, wannan ya wadatar da burina,don haka ki cire min maganar kudi a zamana da Alh na baya,ko hasashen na gaba". Laila ta yi tsuru tana kallonta cikin bugun zuciyar fargaba yadda fatima ke son ta fifita mijinta

Chapter 5 of 8