Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
na yanzu a fakaice,don haka da ci da zuci ta ce mat. "Wannan ce hujjarki ta share guri ki zauna a wannan kejin gidan,kuma don tsabar zubar da aji tare da wasu mata har biyu wadanda ba su wuce 'yan share sharen ki ba a matsayin kishiyoyinki?" 1 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 2 29) Sai yanzu ne ma zuciyar fatima ta kuntata da lamarin Abdullahi,wanda ta tabbatar ba zai wuce na tuna su sadiya ba, ta kyale baki ta ce. "Ko daya,ya kankane ni ne,amma kullum ina iyakar kokarina,yanzu ma da kika ganni asibiti zani a yunkurina na zubar masa da ciki". Laila ta zaro ido gami da dauke numfashi ta dafe kirji,ta ce. "Ciki fatima? Da wannan kazamin yaron kika yarda kika sami cikin?" Ga mamakin fatima sai maganar laila ta yi mugum bata mata rai,musamman ta kiran Abdullahi kazami. Ta jima tana kallon laila sannan ta kawar da kai tana bin talabijin da kallo cikin tunanwan abdullahi da suka karade mata kwanya musamman a safiyar yau. Ta juyo ta dubi laila da bindin ido,ta ce. "Wai cewa aka yi miki gardi na aura ne?" Laila ta tare ta da cewa. "Kwarai da gaske! Ba na ji an ce wani dan malam ba ne da ya ki halin malam... Duk tsiya kuwa na san duk inda gidandanci yake a nan ya yi gida ya tare...." Fatima ta tareta da dariya. "Gaskiya to kin jahilci waye malam,ni dai zan iya ba ki shaidar malam ya fi ko wanne namiji iya soyayya,watakila don shi ya karanta ya san wace ce mace,ke nan ko kazami ne zai iya ribatata masu rikita lissafi kamar Abdullahi,idan ban rufe ki ba fa ke nan!" "Ya kamata na ganshi". Da kalmar da laila ta fanshe mamakinta ke nan,fatima ta ce. "Sai ki sami yammaci ki zo,ko kuma wani week end" Laila ta sauke gwairon numfashi ta ce. "Shi ke nan,mu ajiye maganarsa gefe mu yi ta alh.bayan doguwar jinyar da ya sha a dalilin cin amanar da kuka yi masa,jiya ya dawo da alama kuma ya kasa ganin laifinki,shi har yanzu sabuwa kike cikin zuciyarsa,ya bukaci na zo ki sanar da ni bakin zaren idan akwai hanyar da zai fara warwara bayan nasa matakin da yake shirin dauka wai duk dan a samu wannan kallagaggen yaron ya sahale miki...." Fatima ta yi murmushin yake,ta ce. "Wallahi ni babu wani mataki da zan iya dauka akan Abdul laila... Ya fi karfina,kawai sai. Dai mu taru a bangaren Alh....,sai dai ina rokonki abu daya,kar ki sanar da kowa maganar cikin nan shi kuma alh kun hadu ki sanar masa matakin da yake shirin dauka in dai zai fallasar da maganar auren kinsan wutar da na yi,to ya canja wani dan ba karamin hatsari maganar nan take da shi a kunnen kawu ba.... Kuma bana son abin da kawu zai la'ance ni.... Dan bai taba wulakanta diyancina ba, na tabbatar idan ya tsine min sai ta bi ni". A sanyaye laila ta ce. "In Allah ya so haka ba zata faru ba, da kanki ma zaki iya sanar da Alh,zo na kai ki asibiti ba sai mu biya gidansa ba idan mun dawo...." Fatima ta tare cikin zare ido. "Kina da hankali laila? Idan tsautsayi ya hado ni da abdul ya ganni fa... Ko kuma ya dawo gidan bai tarar da ni ba...." Cikin rashin ko'inkula laila ta ce. "Sai ya yi miki abin da muke so kawai..." "Tunda ba shi kadai ne matsalaha a lanurana ba, ina son hada dukkan burikana a lokaci daya,sakina da kuma rufin asirina,da kuma rabuwa da Abdul salin'alin ba tare da na tafi da kewarsa ba, na tabbatar idan na rantse ba zan yi kaffara ba, Abdul ya fi Alh sadaukar min da rayuwarsa,don shi mai kadan ne, yake kuma sadaukar min da kadan din ya hada min da lokacinsa da KWANJINSA, sannan da asarar farin cikinsa ta hanyata batare da ya nemi fansa ba. Amma Alh fa! Duk kofar kishin bakuta da yake toshe min da kudi yake toshe min, wadanda ya mallake su babu adadi,kuma yana fanshea da abin da ya aure ni dominsa,wato kyau na da nunawa duniya da abokansa kyakkyawar matar da ya aura". Laila ta rasa abin da zata ce mata,sai ta dau jaka tana cewa. "Taso mu tafi in yaso idan mun dawo asibiti sai mu biya a sai waya wadda za ku dinga tattaunawa da Alh,sai kuma ki san hanyar da za ki boye ba tare da ya kamaki da kokawa ya karbe ba". Fatima ta san magana ta fada mata, amma sai ta kyale ta ta buge fa murmushi kawai ta mike ta yafa mayafi suka fice ba tare da ta yiwa su Hindatu sallama ba. 2 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 2 30) Bayan laila ta sami wurin ajiye motar,ta fito ta rufe tana kallon yadda fatima ke waiwaye waiwaye ta kasa fitowa cike da mamaki laila ta ce. "Wai wa kike son gani?" Fatima ta balle murfin motar ta fito tana cewa. "Ko dai waye bana son gani,ina fargabar kar na ci karo da Abdul". Laila ta yi dariya ta ce. "Ina mamakin yadda kike shakkar wannan mutumin wanda ke yakamata ya yi shakka musamman da yake son zama da ke karfin hatsi....". Suka jera zuwa cikin asibitin fatima na cewa. "Har yau ni ma wannan shakkar ke damuna,mutum sai ka ce wanda ya yi min sihiri,gaba daya ya mayar da ni wata kidahuma". A kufule laila ta ce. "To wa ya sani?" Sakon zuwan fatima na isa ga likita,kafin ya ba ta izinin shiga sai da ya kira Abdul a waya. "Fatinma fa ta iso". Zuciyar Abdul ta buga,ya ji labarin kamar wani sabo a kunnensa da sha'aninsa da fatima A rikice ya ce. "Dr da gaske fatima ta ke zata zubar min da ciki?" Likita ya yi ajiyar zuciya ya ce. "Ya wuce wai, tunda ga ta ta zo...." Suka ja shiru saboda likita ya rasa abin cewa,Abdullahi kuma yana kokawa numfashinsa da ke son ya tsaya cak! Har sai da ya sami fitar da kwalla,sannan ya sami bakin magana. "Likita ba za a iya yi mata aikin daure bakin mahaifar a yau ba? Tunda kwanaki suka rage ya cika watanin hudu?" A nutse likita ya amsa. "Za a iya". Abdullahi ya yi ajiyar zuciya ya ce.$ "to taimakon da zaka yi min ke nan, yi mata wannan aikin a matsayin na zubar da ciki,ku rabu lafiya in ta dawo gida sai mu hadu,duk da ina son shigowa asibitin yanzu".. Da karsashi likita ya ce. "Shi ke nan ka kawo shawara mai kyau,Allah kuma ya saukaka mana al'amuran...ya inganta abin da aka samu, ya albarkace shi".$ Abdullahi na nade kwallarsa ya ce. "Amin na gode". Suka sauke waya,sannan likita ya kira abokin aikinsa,suka dan yi tattaunawar sirri,kana ya yiwa fatima izinin shiga. Ko gaisawa ba su yi ba ya mike yana tattara takarda ya ce mata. "Ina fatan yau ba ki ci komai ba?" Ta gyada kai cikin shan kamshi,ya ce. "Kin tabbatar?" Ta gyada kai,laila ta yi karaf ta ce. "Ai na yi zaton allura zaka yi mata". Ba tare da ya dube ta ba,ya ce. "A'a aiki za a yi mata a fitar da shi kawai". Fatima ta zaro ido cikin dukan zuciya a tsorace ta ce, "Anya likita babu matsala? Ni da nake so ka yi min komai yanzu na koma gida,zaka kinkimo min aiki,ya ya zai zama sirri, maigidana yana da matsala fa Dr..." Ya yi mata wani duba na mamakin zuciya ya kawar da kai tare da shanye mamakin,ya ce, "Kar ki ji komai za ki koma gida nan da karfe biyar ko hudu..." Ta tare. "Lallai da sake,to ai hudu zuwa biyar din yake dawowa... Ba ni da wani uzuri da zan iya gabatar masa na gamsar da shi". Cikin basarwa likita ya ce. "Ni kuwa da ina masa kallon wani sassaukan mutum..." Ta yi karamin tsaki ta ce. "Ganin kitse kake wa rogo, tsabar son mulki ke sanya shi hayaniya,mutum da kafarsa sai ace sai ya nemi dama kafin ya fito.ita ma sai an ganta za a ba shi...yanzu dai me ye abin yi?. Ya kada kai ya ce. "Babu wani canji,sai dai da yake kina tare da wannan malamar,karfe uku sai ta mayar da ke gida ki karasa wartsakewa a can. "Har yanzu fatima ba ta gamsu ba,da yanayin jimami ta ce. "Kana ganin mai gidana ba zai fahimci halin da nake ciki ko wani na kusa da ni ba?" Likita ua amsa da cewa "Ina ganin ba wannan me mafi a'ala tare da ke ba, kin sani cikin da ya kai watanin hudu aka cire shi dole yanayinki ya canja,sai dai kawai ki san hikimar da zaki yi wajen sanar da mai gidanki zubewa cikin,ko bai san da shi ba?" Sai ta gyada kai. Laila kanta sai da ta ware ido tana kallon fatima, kafin ta girgiza kai ta ce. "Sai dai kawai ki ce kun nunke juna kawai cikin fa ya turo sosai, sai idonsa ya kasa gani? Ke dai kawai ki zubar komai ta fanjama fanjam!" Da haka suka rufe tattaunawar aka fara shirye shirye shiga da ita dakin tiyata31) Abdullahi na tsaye kan fatima a dakin da aka turo ta bayan kammala tiyata fana baccin nan mai kama da mutuwa. Ya kurawa fuskarta ido sai zubar da hawaye yake na ciwon ran yadda fatima ta dage da sai ta salwantar da musu dan da suka yi shekaru sun tsumayi daga shi har ita,wannan wanne irin son zuciya ne? Anya kuwa a duniya akwai fitiniyar mace irin fatima? Tun yana karfin halin dauke hawayen nasa har ya hakura ya bar shi yana ta zuba. A haka likita ya kama shigowa ya same shi,ya ce masa. "Hakuri zakayi Abdullahi,insha'Allah komai zai zo da sauki baby ciki koshin lafiya cikin mu kuma ya yi nasara. Abdullahi ya nacewa kallon fuskar fatima sannan ya dubi likita yana goge hawaye,ya ce. "Mata lamarinsu na da wahalar da numfashi. Wallahi! Musammam kuma irin su fatima,na rasa abin da yarinyar nan ta ke shiryawa rayuwarta,kina gidan mijin ki ki dinga gudun haihuwa,alhalin ba ki da damar yankar wani tikitin sabuwar wata rayuwar.ga wadda ke hannunki kuma shekaru na shurawa,ko don ta ga ku da zabi kyawunta zai hana ku ganin munin aikinta in ma kun gani kun rabu da ita akwai masu rububinta? Abdullahi bai musa ba,sai dai ya yi tawili. "Haka ne! Kuma da taimakom son wanda ke hana ganin aibu. Amma duk wadannan dalilin biyu ba su hana ni dora da KWANJI a cikin tarbiyyarta ba, nake kuma hadawa da addu'a don haka nake ji a raina,zan iya toshe duk wata kafar da zata fandare hanya,wanda ya fi karfinma kuma na san ubangijina zai min". A sanyaye Dr ya ce. "Na ga wannan alamar". Yana tuno kalamanta na dazu. "...maigidana yana da matsala fa Dr". "..... Ba ni da wani uzuri da zan gabatar masa na gamsar da shi. "..... Tsabar son mulki ke sanya shi hayaniya". DuKkan wadannan maganganun nata suna bayyana shakkarsa ne,wanda da ba ta yi ba karamin cin kashi zata yi akan sa ba. Likita ya yi ajiyar zuciya,ya ce. "Yakamata ka tafi dan ta kusa farkowa,me rakota ma na tabbatar ta kusa dawowa". Abdullahi ya kara zubawa fatina ido, sannan ya dubi Dr ya ce. "Dr idan ta farko ka ga tana cikin wani hali kar ka sallame ta, ka yi mata dabara ka ce zaka sanar da ni ta dabara,ya da za a barta cikin wani hali ba," Dr ya dafa kafadarsa yana cewa. "Kar ka ji komai,in dai hakan ta faru wanda ba a fata zaka ji wayata". Suka yi sallama ya fice. Bai iya komawa wajen aikinsa ba sai kawai ya wuce gida cikin bacin rai da tashin hankali.ya tsaya masallaci ya sallaci la'asar sannan ya shiga gida. Jin shigowarsa ya sa sadiya ta ji kamar ta zuba ruwa kasa ta sha saboda murna. Ta dinga tsaiwa jikin taga don ta hango shi yana rankwashin dakin fatima,sai ta ji shiru ya bata a dakinsa. Ba ita yakamata ta je dakinsa ba don Hindatu ce mai karbar girki,amma kawai sai ta yi shahada ta mike ta tafi dakinsa. Ta same shi zaune yana karatu kur'ani fuskarsa a jagule,don ko kallonta bai yi ba, ya fake da karatun da yake. Don tsabar tsuguddi abin da ta jima ba ta yi masa ba sai ga ta tana yi masa,wato ta tsuguna gabansa ta zare masa safar kafa,ta kunce masa neck tie ta zare masa coat sannan ta wuce da su dakinsa ta fito ta kawo masa lemo da ruwa.ta nemi guri ta zauna tana jiran ya diga aya.ya gama haka ya ki tsayawa ya tanka ta,sai da ta zauna sosai sai murmushi ta ke masa, shi kuma ya yi fuska. Ya rufe kur'ani yatsunsa na inda yake ya dube ta yana kokarin hadiye bacin ransa,ya ce. "Kun wuni lafiya?" Ta muskuta ,ta ce. "Lafiya kalau.ko dai ka ce na wuni lafiya. Tunda Hindatu ba ta nan, fatima ma haka". Ya yi saurin duban agogo fuskarsa a bace. "Au Hindatu ba ta shigo ba? Kamar ban ce kar a dinga fice karfe hudu a waje ba?" Ta tari numfashinsa da cewa. "To ai ita ma fatima ba ta dawo ba" Cikin rashin kulawa ya dauki wayarsa ya fara dubawa,ya ce. "Mun yi zan je na dauko ta,ban sami dama ba amma na yi waya a kawo ta yanzu. Takaici ya lullube sadiya,ta zura masa ido da duban tuhuma. "Tunda idan na je unguwa kana zuwa ka dauko ni ko ka dauko Hindatu ko?" Shi ma ya zura mata ido. Ba tare da fuskarsa ta karbi korafinta ba,ya mokade lebe ya ce. "Ko a gadon baya na zanm daukota bai kamata ranki ya sosa ba,matar da ta ke da motocin hawanta na hana ta kawo su gidan nan ke kin ga yakamata na barta tana yawan motar haya? Wani lokacin idan kika tashi korafinki sadiya ba kya hada shi da hankali wallahi... To kin ga ba na son hayaniya,ki tashi ki koma dakinki kar ita ma waccan ta shigo ya zama wani korafin na daban ku da kullum abin neman masifa ba ya yi muku kankanta. Kafin ma ta sami bakin magana ya tashi da alkur'anisa ya shige daki,n ta fice dakinta. 2 · Like · React · Report · May 17, 2015 Ummee Amina hmm Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 2 32"Dr wannan wanne irin Abortion ne na ga cikin nata kurcici?" Tamabayr da laila ta yiwa Dr ke nan lokacin da ake ta faman cike takardun daukan fatima zuwa gida,wadda ke kwance tana mayar da numfashin. Dai dai. Dr ya ki nuna damuwa da korafin na laila.,ya ce. "Zai sace nan da kwanaki bakwai,illa dai a kiyaye dokokin nan kar ta yi aiki mai wahala, ban da shara,ban da daukar ruwan wanka.ke ban da komai ma sai dai ta ci ta kwanta,abincin ma kar ta ci me nauyi...kin gane?" Ta gyada kai idon ta na kan fatima wanda ke tambayarta lokaci da hannu,laila ta yi tsaki ta ce. "Wai dafa ki zai yi ne kika damu haka? Wannan ma tsabar zubar da aji ne ki dinga tsoron namiji haka". Dr ya dinga nazarin laila a fakaice sannan ya ce mata. "Malam laila ke nan,ashe zubar da aji ne don mace ta yi shakkar abin da ran mijinta zai sosu.... Ko kin manta abin da ta yi laifi ne babba?" Ba tare da laila ta dube shi ba, ta ce. "Mazan ma suna suka tara,in ni ce da wannan mijin na rantse ki zagina ya yi sai na rama" Murya a shake fatina ta daga mata hannu,ta ce. "Ba na son cin fuska laila". Dr ya dube ta ya dubi fatinma,ya ce. "Anya kuwa kin san abdullahi da kyau?" Laila ta yi tsaki kawai ta kawar da kai tana son maganar ta bi ruwa,shi kuma dr ya nace a yi ta, ya ce. "Laila kin fin kanwar nan taki zafin kai" Ta amsa masa da cewa$ "Ba kanwata ba ce,kawata ce". Dama abin da yake son sani ke nan,don kai wa Abdullahi tahoto,wanda ya tabbatar laila ce ke zuga matarsa. Da haka ya sallame su da taimakon nurse suka kai fatima ba cikin hayyacin ta ke sosai ba,dukkan sambatunta na fargabar kar su tara da abdullahi a gida ne, tare da rokonm Allah kar ya sa ma kar ya san ta fita. Sai dai kash! Sai ga ta a zaune bayan sun shiga harabar gidan ta ga motarsa,numfash inta sama sama ta dafe kirji ta ce. "Na shiga uku laila,ya dawo wallahi". Laila ta zuba mata iso cike da takaici. "Kin fara kai ni bangi wallahi,wai rufe ki da duka zai yi ne? Iyakacin ya ce ki koma nida kika fito,ba shi kenan ba,dawa ta yi nama...." Fatma ta tareta da cewa. "Zai iya dukan nawa,ko ma abin da ya fi dukan,in koma inda na fito din ne kuma na tabbatar ba zai fada ba". A kufule laila ta ce. Wannan fargabar ta kori jirin da ke damunta,bakin fal addu'ar su shige suruf ba tare da sun ci karo da abdullahi ba.ta taka da kafarta suka shiga cikin gidan. Abdullahi na tsaye ta taga yana kallonsu har suka bude dakin fatima suka shiga.ya saki labule ya tafi gadi da sauri ya zauna lokaci da ya ji shi ma jiri na kwasarsa,ya ma rasa irin matakin da zai dauka akan fatima bare laila. Fiye da mintuna goma yana zuba idon ganin fitowar laila,sai da ya ji buruntu kicin din fatima ya san kila ghirki ta ke mata. Zuwa wannan lokacin zuciyarsa ta rage tafasa,ya shawarci kansa yin hukunci a nutse,ba da fushi ko gaggawa ba. Har yanzu hankali fatima bai gama kwanciya ba, tana sha tea a hankali idonta a kofa, kunnenta a kan juyo motsin bude tasa kofar.can ta ji sallamar Hindatu.lokacin daya da bude kofar dakin nasa ya fara juyewa hindati nata sababin da kakkausar murya. "Duba agogon hannunki karfe nawa?" A ladabce ta fara in ina. "Ka yi hakuri... Wal wallahi go slwo ne ya rike ni.amma tun uku da kadan na fito". A zafafe ya ce mata. "Da ya rike ki ai sai ki kwace ki koma inmda kika fito tunda na ce in dai an san za a wuce karfe hudu a waje gara a tambaye kwana. Ta kuma kwaso wata magiyar. "Don Allah ka yi hakuri Abu Turab.." Ya kuma tarewa da bala'I. "Kin ga Hindatu kar ki kara fado min wata magana, da hakuri da rashin jin maganar tawa duk ki ci gaba da tanadar min su ai dan inyi ta fama da su na zo duniyar". Ta yi shiru kanta a kasa,ya kuma sauke huci,ya ce. "To ki sha kuruminki idan ma kin yi haka ne don ki bata min rai, to tare da naki kika hada wallahi na da wata daya da wasa kar inji kin tambaye ni fita". Gaban fatina ya ci gaba da dukan uku uku ta yi kasake da tea a hannu,laila kanta sai da ta ji abin a jikinta,ta ce. "Fatima,wannan wane irin dan sababi ne?" Hankali fatima kamar ba ya tare da ita ta ce. "Laila rufo mana kofar nan kar ni ma ya zo ya sauke min nawa wanda na tabbatar sai ya fi nata tsauri". "Insha'Allah ba zai shigo ba". Sai ga shi kuwa addu'arta ta karbu,don ficewa ya yi daga gidan sai tashin motarsa suka ji. Fatima ta sauke ajiyar zuciya kila wa kalanci,wato ko dai Abdullahi bai san ta fita ba,ko kuma cikin nata hukuncin ke nan. Laila ta yi ta kwantar mata da hankali,sannan suka yi sallama da zummar gobe zata dawo ta dubata kuma zata taho mata da waya. 2 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man ndalin hausa novels Zuciya d kwanji 2 33 Sai da bacci ya fara fizgarta a nan falo ta ji bugun kofa. Ta dubi agogo da sauri cikin bugun zuciya, agogon ya nuna tara da rabi,ta yi baccin rabin awa ke nan,domin ta ga tsinken agogon akan tara dai dai saboda kasa kunneb shigowar abdullahi bai shigo ba, har baccin ya dauke ta. A tsorace ta ke, don haka ba ta bude masa ta dawo falon ta zauna tana jiran tasa karsasowar. Bai ko dubi inda ta ke ba, fuskar nan tasa a murtuke! Ya dinga shiga da kayan masarufi store dinta, har ya gama ya dawo falon ya kwashe kayan tea din da ta shi da gwangwanayen lemon da suka sha ita da laila,ya wuce da su kicin. Sannan ya dawo ba tare da ya dubeta ba ya ce "Me za ki ci?" Ta dube shi da kyau,sai ta ji shakkarsa ta kara rufe ta, tana in 'ina ta ce. "Na ..... Na sha tes ya gamsar da ni" Ya mokade lbe, idonsa akan talabijin ya ce. "Kin yi wanka?" Girgiza kai kawai ta yi, amma da tasan ba lallai ya san ta yi ba, tunda ba kallonta yake ba, a hankali sai ta ce. "A'a Kawai sai ya wuce dakin baccinta zuwa bandakin ciki, ya tanadar mata ruwan wanka mai saukin dumi,sannan ya kirata daga cikin dakin ya yi kiranta da murya babu walwala. "Ki shigo ki yi wankan". Ya kamata ace ta taya shi wannan danyan kan nasa, amma ita ma sai ta ji a ranta gara ta lallaba shi tunda ta riga ta yi laifin,laifin da ya sha fada mata hukuncinsa zai iya zama ba fallasa sirrinta ga kawu,wadda ta ke jin gara mutuwa akan haka. Ta mike da kyar ta shiga dakin a hankali saboda ciwon da dukkan gabobinta suke babu ma abin da ya fi damunta irin yadda cikinta ya dameta da watsal watsal,sai ka ce akwai dan da ke mata busharara shi ba a cire shi ba. Ta same shi gaban dressing table yana feshe kayan baccinta da turare,daga nan ua fara ware mata bargon kan gadon yana rage fulullaka yadda dai zata sami komai cikin sauki, wannan kyautatawar tasa ce ata sa ta rashin ganin aibun fushinsa,har tausayin sa ya sata jin kwalla ta taru a idanunta. Yadda ta ke jan numfashi ya sa dole ya dan dora mata ido a fakaice,ita ma tana satar kallonsa ta yi saurin daure numfashin ta shige bandakin ko kayan jikinta ba ta rage ba. Har man wanke baki ta yi wankan ta gama cikin hawaye don haka har ta same shi zaune kan stool cikin zurfin tunani,cikin dar dar ta wuce ta dauki kayan baccin,ta juya baya ta saka ba tare da ta nemi ko shafa mai ba, ta haye gado ta ja bargo ta lumshe ido. Kamar daga sama ya jefo mata tambaya muryarsa a cushe. "Zan iya sanin inda kika je yau?" Ta ji numfashinta na neman sarkewa saboda fargaba da neman amsar da zata ba shi don haka suka kwashi lokaci yana jiran amsarta har ya kuma cewa. "Wai ba ki ji ba ne?" Rukani ya sa ta tashi zaune ba tare da ta shirya ba, tana dubansa kai tsaye ta ce. "Ni babu inda na je". Ya kara tara gira yana dubanta,ya ce. "Ko? Amma na dawo ban tarar da ke ba,kuma ina cikin gidan nan kika shigo. Ta kawar da kai daga gare shi,ta ce. "Gaskiya ba in ba ce, don ko kofar daki ban je ba". Ya sauke nufashin yana girmama karfin halinta,ya kawar da kai cikin cije lebe,ya ja fasali sosai sannan ya kike tsaye ya dubi tsabar idonta ya ce. "Fatima kai ki mayar da ni dan iska kin ji! Kar kuma ki taba tsammanin sonki ya yi min runtsewar idon da zaki ci kashi a kaina na zuba miki ido... Na ce dole ya zama da izinina, kuma dole hakan ce zata kasance wallahi ban fada da zummar waka ba! Shugabancina a kanki da matsayin aurenmu kamar sauran aure a musulumci ba zai taba canja salo da ka'idoji ba wai do ba kya sona ko ba kya son ki zauna da ni ni da nake shugaban da KWANJINA nake motsi. Kamar yadda ba ki da ikon sakin kanki haka zalika ba ki da ikom canja matsayin biyayyarki gare ni zuwa yin komai na radin kanki.... Na rantse miki ba ki isa ba wallahi.... Kin yi na farko kinyi na biyu, kuma kin yi na karshe,duk ranar da kika kuma saka kafa kika bar gidan nan sai na yi miki rashin mutumcin da har ki mutu ba zaki manta da ni ba. Kin fara fitina ta wallahi,hakurina ya fara taba bango a lamarinki... Na fada miki na kuma har abada babu saki tsakanina da ke, hakan kuma ba zai sa na laminci abin da raina ba ya so a cikin lamarinki ba. Idan ma kin sami dan iske ki sanar wa Alh da kike zuwa wajensa... Kuma idan kun ci amana ta Allah ya saka min...." Bai saurare ta ba sai ya fice ya bar ta baki bude kekkece saboda kuna. Ta yi kuka, ta yi kuka ba ta da me rarashinta,har sai da zazzabi ya rufe ta sannan ta koma ta tasa inda kudundunar tana faman makyarkata.ina ma daga haka ta zarce,ta huta da wahalar wannan rayuwar da mutum na ya samun abin da yake so. Haka ta kwana tana makyarkyata,ga dukkan jikinta yana ciwo,mararta ma ta kulle tana ciwo, sai ta rasa inda zata tsoma ranta,Allah Allah ta ke gari ya waye ta nemi dauki,don haka da ta yi sallah asuba ta dinga kasa kunnen shigowar Abdullahi har zuwa lokacin da zai shigo mata.... Amma bai shigo gidan ba sai da rana ta fito bakwai da rabi,wanda wannan lokacin ma ya gama shirin fita ofis. Yana shiga dakinsa Hindatu ta cimmasa ta durkusa har kasa ta gaishe sji,sannan ta mike a ladabce ta ce, "Abu Turab wai duk fusjin ne? Don Allah ka yi hakuri". Ya girgiza kai da sauri da son ya yi murmushi,ya ce. "Ya wuce wallahi" Ta ce,"ban ga alamar hakan ba,jiya fa baka yi baccin kirki ba, ka fice sallar asuba ba ka shigo gidan ba sai yanzu. Ina ganinka ka shigo babu walwala,sai na ga me ya yi zafi?" Ya share fuska yana kawar da kai,ya ce. "Ba wannan matsalar ba ce,akwai abin da ke damuna... Ku saka ni cikin addu'a". Cikin tausayawa ta ce. "To Allah ya warware". Ya ce,"amin, yi min afuwa na ga fatima ba ta da lafiya" Ta yi saurin gyada kai tunda tana son ya huce,ta ce. "Babu komai". Ya yi mata godiya ya juya ya fita. Ya same ta kudundune a gado tana ta faman kuka da makyarkyata,ya kara daure fuska don ya yi tsammanin kukan rikicin da ya yi mata jiya ta ke, don haka ya yi mata banza ya fara abin da ya kai shi, wato gyaran dakin, amma makyarkayartar da ta ke ya sanya dole ya sanya mata ido,murya a cushe ya ce. "Wai wannan kukan na jin dadi ne ko na me? Ni ya kamata na koka don ni kika cutar,me yasa kike son nuna ke aka cuta?" Ta girgiza kai cikin wahalalliyar murya,ta ce. "Abdul ba ni da lafiya,zan mutu wallahi! Da sauri ya yar da sallayar da ke hannunsa ya isa gabanta,ya ture bargon ya dago ta a rikice ya ce. "Me yake damunki?" Ta cije lebe cikin sartun hawaye tare da rike hannunsa da kyau ta ce. "Cikina Abdul zazzabi kaina.." Ya yi saurin tattarota jikinsa yana rungumewa,cikin nuna damuwa ya ce. "Ciki kuma fatima... Wanne irin ciwon ciki? Sannu.... Ko mu je asibiti?" Da sauri ta girgiza kai tana kara jankane shi. "Ka yi min addu'a kawai... Idan ya yi min sauki ina da magani zan sha..." Ya ce,"to... To shi ke nan.... Dai dai ina ke miki ciwo a cikin?" A rude ta ce masa "Ko ina abdul" Ya dagota ya yaye cikin yana kallo,hankalinsa ya rabu biyu da addu'ar da kuma kallon yadda cikin nata ke ta faman motsi alamar dai an kuntata shi. Suka kwashe lokaci mai tsawo a haka,cikin ikon Allah sai ga sauki ya samu har ta yi bacci a cinyarsa. Ya kara damke hannunta cikin nasa yana bin fuskarta da kallo,kwalla ta fara cika

Chapter 6 of 8