Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 8
Ka ga tun da abin ya fara kawo mun irin wannan bakaken maganar kafin ka kai ga sa hannun ka dake ni..... Sallame ni, tunda ba kwai na ajiye a gidan ba, sai ma na ba wa wasu sarari su shigo idan sun ga zasu iya su zauna su haifi kashi,idan ba zasu iya ba su ma su ci taya". Fatima ta gaji da sauraronm wannan hayaninyar sai ga ta zaune tana mutsuke ido,sannan ta dubi sadiya ta ce. "To ke baiwar Allah akwai wanda ya yiwa Ubangiji rawa ya ba shi tsatso ne? Na tannatar kin san inda gadar haihuwa ake da yanzu mun cika gidan nan da ya'ya.mts! Ina mamakinki wallahi, ke babu wani mutum mai mutunci a idonki da ya fi karfin ki dagawa harshe. To tsoronki za a ji ayi miki abin da kike so? Ai duk mutumin da yake jin kowa ya tsane shi,to ya binciki kansa halinsa ne ba shi da kyau". Kawai sai Abdullahi ya nemi guri ya zauna,ransa na yi masa dadi. Fadima ta karbe shi fadan ya san kuma yanzu zai mutu,don tana kulle sadiya da takaici zata tafi ta ba shi guri. Sadiya ta kara bala'I kamar zata cinye fatima danya. "Wai ke ina ruwanki? Ban yi miki kashedin kar ki kara shiga sabgata ba? Ni iskar da ta kwaso ki ma idan ina kaunar shakarta Allah ya tsine min...." Fatima ta yi saurin tare ta da rashin nuna damuwa. "Me yasa za ki ce babu ruwana? Ki saka min miji a gaba kin faman ci masa fuska ki ce babu ruwana. To me ye amfanina? Idan ke ba kya so ni ina so, saboda haka a kansa sai in da karfin ya kare, ke nan kina da bukatar canza tunanin,da ruwanan har da komai nawa". Da sadiya ta rasa abin cewa,sai ta harde hannu cikin rawar murya ta ce. "To daga nan ki sa shi ya sallame ni mana tunda da alama kamar ke ce mijin shi ne matar". Fatima inda zaki, zama zaki yi ki ci gabna da ganin abin da ba kya so, idan kin yi zuciya sai ki canja halinki". Zuciyar sadiya ta tafasa ta juya ga Abdullahi ta ce. "Abu turab kayi min iyaka da matar nan ko kuma ka bude baki ka sanr da ni kai nake aure ko ita? "Allah ya ba ki hakuri". Kalmar da ya fada mata ke nan cikin yanayin cin magani,sai ta yi kwafa ta kada kai ta bar wajen. Tana bacewa fatima ta tashi zaune tana hura hanci,kafin ta yi magana sai ya riga ta, tare da mika mata lemo. "Ungo sha makogwaronki ya bude sai ki sauke taki rashin kunyar". Sai ya ba ta dariya, dole ta koma ta kwanta dan kokarin ta hadiye dariyarta,ta ce. "Kai dai kawai ba ka son na fadi gaskiya, kuma sai na fada,ka kawo ni cikin matanka suna koya min hayaniya,babu gaira babu dalilin ku dinga sa min ciwon kai. "Allah yasa ya zame miki kaffara". Ya fada yana hadiye dariyarsa,sannan ya kwanta rigingine yana so kadaita da tunanin hayoyin da zai canja wadanda za su kawo masa fatima a saukake. Babu jimawa kannen hindatu uku suka zo ta jajibe su falonta tana karrama su dai dai gwargwado,Abdullahi ma ya kwaso kafa ya biyo su,aka yi da shi inda ya fake da murar da ta ke ya sanya su shiga kicin,shi kuma ya ci gaba da more huldar arziki da fatima tunda ba zata saka shi kwandon shara a gabansu ba. Ya dorar da ranar yau don har abinci kwano daya ya ci da fatima.wanda rabin su da hak ahar ya manta. 2 · Like · React · Report · May 15, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 9)Da azahar ya kamo hanyar gida,domin ya kai su gidan suna,ya ce su tsaya zai kai su ne saboda fatima,wadda ya ke matukar kishinta da hujjar fuskarta mai hadari ce ga maza. Har ya zo gida yana tunanin da yadda za ayi ya raba musu tafiyar tunda ta ce ba zata da su ba, sai Allah ya taimake shi ya sami hindatu da kannenta su Rabi duk za su, dan haka.ya fake da cewa motar ta yi musu kadan,idan ya kai su ya dawo ya kai fatima. Ko rabin awa bai yi ba ya dawo ya dauke ta. "Wane sauti zan sa miki?" Da batun da ya kau da shirunsu ke nan bayan ya tashi motar,sai ta juya masa keya, yana dariya a ciki ya ce. "Kar fa in sa wanda raina yake so ki kalubalance ni". Yana rufe baki ta amsa masa. "Sa min dan'anace" Ya tuntsure da dariya,sannan ya latsa sautin wakar bala anas "masoyiya ke ce tawa' yana cewa. "Ai kin kawo kuka gidan mutuwa,kin ji inda na fi kauri". Ta yi banza da shi ta kawar da kai,ya dinga yi mata dan biki yana bin wakar yana inkiya da ita kamar ba tuki yake ba. Sai da suka gota sahad store da ke zoo road sannan ta juyo ta dube shi,ta ce. "Mu shiga zan sai kayan baby". Ba tare da ya dube ta ba ya ce. "Ki ba ta kudin". Ta tara gira,ta ce. "Don me?" Ya bude ido ya amsa. "Dan ba ki yi shirin za ki shiga wani guri bayan gidan suna ba, in kin shirya shiga store sai ki sanyo hijab har da nikab tun da akwai mazan da zaki dinga cin karo da su. Ta ce,"ga ni ga ka?" Ya dage gira,yana mata wani kallo ya ce. "A matsayina na wa dinki?" Sai ta kawar da kai ta share,sannan ta nisa ta ce. "Mu koma sai ka shiga ka siyo min,babu komai...." Abdullahi ya yi gudun gara ya fada zago, domin shigarsa store din ke da wuya fatima ta hango direban Alh na tashin mota zai fita,da sauri ta ya fito shi ya taho jikinsa na bari kamar manta cewa,yanzu ba shugabarsa ba ce. Ya rankwafa sosai ya gaishe ta,a rikice ta saurin katse gaisuwar,ta ce. "Ya ya Alh?" Cikin ladabi ya amsa mata. "Ayya! Alh jiki ya ki Hajiya,yau satina biyu a jamani. Ta fara karanto,'innalillahi wa inna ilaihi raji'un' a zuciyarta, fuskarta na nuna kololuwar tausayawa,Abdullahi na shirin kisan kai, abin da ta dora a ranta ke nan. Tana tuno Abdullahi sai gabanta ya fadi, wanne irin zafin kai zai mata idan ya zo ya tarar da ita da direba? Cikin yanayin tsoron da damuwa ta ce. "Shi ke nan, Allah ya ba shi lafiya. Idan kun yi waya ka fada masa an karbi wayar hannuna ne shi yasa ba ma samun gaisawa". Ta bude jaka ta debo kudi babu ko kirga ta ba shi. Ya yi mata godiya ya bace,yana tunanin wa wannan matar 'yar zafin kai ta ke shakka haka? Matar da ya sani ba a sa ta ba a hana ta, mulkin mallaka har ga wanda ya ajiye ta. Gaba daya ta sauya,wani mugun jin haushin abdullahi ya mamaye mata kirji,tsanarsa ta ishe ta. Ta dinga jin gara ma mutuwarta da rayuwar da ta ke a gidansa, kawai sai ta rafka tagumi cikin hakakin bacin ra. Ya dawo ya miko mata kayan,ta karba a fusace ta watsa baya. Sai kawai ya yi saroro yana kallonta,sannan ya kada kai ya zagaya ya shiga motar. Yadda ya ga yanayinta sai ya sha jinin jikinsa,sai huci kawai ta ke kamar ana taba ta fashewa zata yi. Bai yi shawara da kowa ba ya raba kansa da sauraron'masoyiya ke ce tawa'ya mayar da karatun alkur'ani cikin suratul kahf da muryar Abdullahi madarut.ya dinga bi cikin nutsuwa har suka kai babu wanda ya tankawa wani. Bayan ya faka motar sannan ya koma nazarinta,ya tabbatar kashi hamsin na daga kunci da ta ke ya zabge,ta bar huci ta koma tagumi da zubawa gilas ido fuskarta,ya ce. "Fadimatu me ya faru ne? Ko dan na hana ki shiga store? Haba fadimatu wannan ai karramawa ce gare ki shiga dan ni kuntata miki ba"m Kwallar da ta cika mata ido ta fado,ba ta damu da dauke ta ba ta dube shi ta ce. "To wai don me ma zaka so ni ne Abdullahi? Soyayyarka gare ni karan tsaye ce a farin cikin ban taba shiryawa kaina auren miji irinka ba saboda haka rike ni da kake a matsayin matarka zalunci ne gare ni' Ya yi shiru yana kallonta cikin damuwa da tarin hasshen abin da ya zunguro ta haka. Ya kife kai a sitiyari yana nazarin ta inda zai sha kanta.Rarrashinta zai yi ko kuna mayar da koken nata wasa zai yi kamar yadda ya saba? Duk ciki bai ga na zaba ba saboda shi ma yau kirjinsa ya yi nauyi a kan lamarin. Kimanin mintuna biyar sannan ya dago ya dube ta ya ce. "Fatima so ba ya shawara kafin ya sami muhalli, sai dai ba shi ne mafi a'ala a cikin zamana da ke ba, idan ma ya yi tasiri ba zai wuce na son tsarkake ruhinki da gangar jikinki daga abubuwanki,so ba zai yafe min ba idan na dauke hannu akan tarbiyyarki,ko kuma na sallame ki dan na gaji da dawainiyar neman soyayarki har ki sami damar zaman haramun da alh,kin san wani abu? Ko halali ne aurenki da Alh musulunci ya ba da damar a raba shi,saboda yadda Alh ya shagala da soyayarki,ke kuma kike amfani da wannan damar wajen dama garinki yadda ranki yake so,ko da ba ya kan turba. Kin san tsoron da nake jiye miki? Kar ki zama daga marasa rabo,kyawunki ya zan silar shigarki wuta,kin dauki hakkin Alh a zamanki da shi, kun yi rayuwar saki uku,kuma kun fatalar da hakkin Allah kuna son rayuwa cikin saba masa,na aure ki ina ta faman dawainiya da hakuri da ke,fadima kar ki zama daga cikin matan da ake saka mazajensu aljana saboda hakuri da munanan halayensu. Sin fadima an kagi halittar ki ne ba tare da wata manufa ba? Ki maida hankalin ki fa? Ita mutuwa ba sallama ta ke ba bare ki ce kina da garantin lokacin tuba ki kubutar da kanki,idan Allah a karbi ranki a haka ki ba ki da wani uzuri da zaki gabatarwa ubangijin .......,ki sami lokaci ke da kanki ki yi tunani,duniyar nan da kike ganinta ba ta kai fikafikin sauro daraja ba a wajen Allah,inji manzon Allah(S A W). Idan kyawunki ke rudinki ki farga fatima,ko kina raye shekaru kalilan kike jira ya gushe a sa'in da ido zai mutu kwalli ya kasa tono shi,kuma akwai hadisin manzo Allah(S A W ) da ya ce,'ka mori kuruciyarka kafin tsufanka'. Akwai alamar maganganunsa sun shiga kwanyarta da muhimmanci.hawayen ya tsaya duk ta yi wani wuri wuri da ita,ya jima yana kallonta sannan ya kara tausasa murya,ya ce. "Fatima ki taimakawa numfashinmu,mu zauna lafiya.... Ni an jarrabe ni da kaunarki..... Ba zan iya sakinki ba fatima.... Kuma ba zan daina kaunarki....." Ya kife kai a sitiyari saboda hawayen da ya hana shi magana,kawai sai ta sami kanta da binsa da kallo,abin mamaki sai ta ji kukansa na taba ranta,ita ma sai kwalla ta cika mata ido da dinga goge su suna kara dannowa tare da haifar mata da makaki a zuci, abin ya yi mata yawa,ga damuwar Alh ga ta Abdu 1 · Like · React · Report · May 15, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji .10) Haka ta dinga nade kwallarta tana dokin wannan lokacin ya wuce musamman na damuwar Abdul. Sai da ya yi edabarar goge hawayensa tsab bayan ya dan sami sassauci a ransa,sannan ya juyo mata da murmushin karfin hali,sai ya ganta da hawaye.ya bude ido cikin murmushi na neman ba'asi sai ta kawar da kai tana goge fuskarta. "Ki yi hakuri kin ji, ba a son raina nake bata ranki ba" Ya fada a can kasan makogwaronsa sai ta kasa hada ido da shi,ya ce. "Gyara fuskarki mu shiga". Bata musa ba ta bude jakarta ta fara gyara fuskar.ta dawo fes kamar ba ta yi hawaye ba,sai da ta mayar da kayan jakarta ta rufe sannan ta ta dago ta dube shi suka hada ido ya sakar mata murmushi,sai ta sami kanta da ba shi rabbi,abin da kuma ya so birkita shi ke nan, tare da tabbatar masa ya ciyo wani birni a cikin zuciyarta.bai taba ganin murmushi a kuncinta tsakaninta da shi ba.... Ya shiga damuwar neman sanin abin da ya yi ya samo masa ita haka,wannan ya sa soyayyarta ta kara cika masa kirji,har sai da ta bayyana a harshensa ya furta mata. "Ina sonki fadima". Ta kawar da kai sannan ta balle murfin motar,ya yi saurin ruko hannunta,a tausashe ya ce. "Bari na kira maryam ta shiga da ke" Yana rike da hannunta ya yi kiran kanwaesa maryan ta wayarsa,sannan ya sauke ido a kanta,ya ce, "Karfe nawa zan zo na dauke ki?" Muryarta na rawa ta ce. "Duk santa ka shirya". Tana kokarin janye hannunrta, ya ki sakin hanun nata,ya ce. "Idan na bari sai dare ban takura ki ba?" Ta gyara kai fuskarta na nuna damuwar son ya sakar mata hannu saboda ta hango fitowa maryam,ya ce. "Rufo kofar nan in fito in bude miki kin ji?" Ba ta musa ba ta rufe kofar har maryam ta karaso,sannan ya fito ya bude mata,suna gaisawa da maryam dinmai cike da murnar ganin fatima sai fara'a suke wa juna.ya dauko kayan barkar ya ba wa maryam cikin barkanci ya ce. "Ki kular min da mata kar ki sake ki barta da kadaici.yau in son filin zuciyarta fetal" Maryam na dariya,fatima na kawar da kai har suka wuce irin nishadin nasara a cikin zuciyarsa. Ashe fatima na jin wakazi? Bai samo lagonta ba kuwa? Ya shige mota da sauri ta tashe ta ya bar wajen. Duk da fatima na kasaita da shan kamshi da yake tana da fara'a kuma ga ta da kyau,sai ta yi farin jini a dangin Abu Turab,aka dinga nunata a matsayin amaryarsa a dangi.ita kuma ta ki nuna kosawa duk wanda aka nuna mata sai ta gaishe ahi dai dai matsayinsa da shekarunsa. Maryam da sauran kannen Abu turab din suka dinga hidima da ita,komai sai sun yi mata na musamman tare da jin ta fi karfin wannan,ita kuma tana ta binsu da godiya. Ba ta hadu da su hindatu ba sai daba da magariba da su maryam suka yi mata rakiya dakin maijegon,suka kara gaisawa da muwadda wato mai jegon,tunda sun hadu da ta shiga bangaren iyayen abu Turab. Sannan ta umarci maryam ta ba ta kayan wanda ita kanta ba tasan me ye a ciki ba,ashe kaya masu kayu da tsada har sati biyar,wannan ya sa muwadda ba ta iya hadiye mamakin ita kawai ba,sai da ta nuna wa wata yayar abdullahi haj Asma'u. "Anty kinga kayan da amaryar Abu Turab ta kawo wa baby". Haj asma'u ta yaba ta yi godiya,abinka kuma da dangin miji,karaf sai wata kauwa a wajen abdullahi ta fara yiwa su sadiya da ke zaune yarfe. "Ke dai komai kin hada,ga kyau ga fara'a ,kyauta.wanda ya iya ya huta,kuma babu ruwanki da cika mutane da surutu,gara ma mai abin kanshi tana bade mana". An ce kowa ya yi zagi a kasuwa yasanm da wanda ya ke, hindatu ce ta fara amsawa da cewa. "Ban da abinki ai mikar mutum ba ta wuce tsawon hannunsa". Sadiya kuma na sako baki sai ta huce akan fatima. "Idan ana cin baure ai ba a ton cikin sa,ni ban ga burgewa a cikin sayar da rai dan nemo suna ba. Idan na adana wanda ya zame min wajibi na gama aikina,ko ina tsiya ina matashin kai da bargon da mutum zai rufa ma sai yana wujila wujila da shi? A nan dai an zama kyandir". $ ban da hindatu babu wanda ya san daga inda maganar ta faro bare inda ta samar da ma'ana. Dan haka maganar ta wuce sururuf bayan Haj Asma'u ta tsawata,sai dai ta yi katon rauni a zuciyar fatima.11) Ta tabbatar babu abin da ya fi kishi ciwo,tunda komai bai wuce a canja maka fassara a goranta maka shi ba, zuciyarta ta baci matuka har ta dinga jin hawaye na son zubo mata a ido. Dole ta sna neman tsari da wadannan kananan maganganun sa sadiya wadda ko yaushe kiris ta ke jira ta goranta mata akansa. Cikin dabara ta mike ta bi Haj Asma'u tana cewa. "Anti bari na zo na ga turarukan na akwai irin wadanda nake amfanin da su,marayam ku zo mu je". Suaka fice ta bar wa su hindatu dakin,tana jin wata s'ida a ranta.ita yanzu ko ganin sadiyar bata mata rai yake. A wajen haj Asma'u ta zabi turaruka masu kyau na kimanin dubu talatin,antin ta cire mata wani abu inda ta ce ba ta fito da kudi ba a tura mata wani ta bayar. Tsab ta shiga cikin 'yan uwan abu Turab ta baro su hindatu da ire iren matan yaye da na dangi,don haka yayyen Abdullahi da iyayensa suka dinga yabonta suna jin dadin yadda ta ke daukarsu'yan uwanta, ba kamar yadda sauran surukan sukan yi ba. Bayan sallar magriba aka ce ga ke kadai kika zo". $ ta kare da zolayarta,sai fatima ta yi dariya kawai,ita kuma anti da kanta ta je ta ce,ya fara kai su sadiya,fatima na cin abinci, duk kuwa da ba abincin ta ke ci ba. Shi da ya san dawan garin bai wani musa ba ya hada kan su sadiya ya kai su gida,ko kashe motar bai yi ba ya koma. Farin cikin sa ya kura da ya ga wajen mutum goma su rako masa fatima,har ma da yayyensa biyu, suna ta yiwa juna godiya tana sa su alkawarin kawo mata ziyara. Da haka suka yi sallama ya ja mota,maimakon ya yi baya su hau B.U K. Road sai ya mike amin kano,dole fatima ta kau da shirun da ya ratsa motar. "Ta ina zamu bi ne?" Ba tare da ya dube ta ba, ya ce. "Zan ga likitana ne,kin san ina karbar magani." Ta tara gira,ta ce. "Na me?" Ya juyo ya dube ta,sannan ya mayar da kai ga titi "Na neman tsatso ko zan huta gorin ..... "Ga mamakin kanta sai ta ji kishi ya karci zucitarta,tare da tunano uwar gori sadiya,sai ta kawar da kai tana jin wancan kishin na dan gushewa,yayin da kwanyarta ke karanta mata, ai sadiya damuwa ce, gori kamar a jininta yake. Da suka karaso asibitin ya yi mata tayin ra raka shi, sai ta yi fuska ta ce. "Ka manta ba ka sako min hijab ba?" Dariya kawai ya yi ya fice ya rabu da ita, inda ta bishi da kallo, kirjinta na bugawa wannan asibitin ne na zuwanta,domin likintan ya san aikinsa, shi ya ba ta gwaggwabar gudubmowar hana mahaifarta karbar ciki lokacin da ta ke gidan Alh,ba tare da sanin Alh ba. A lokacin duk bayan wata uku ta ke karbar allura, amma tun bayan mutuwar aurenta ta dauke kafa,don haka ta san yanzu idan ta shiga babu mamaki ya ishe ta da tambayoyi a gaban Abdullahi. Sai dai wasa! Tun tana jiran fitowar Abdullahi da kauna,har ta yi mugun gundura,da ta duba agogon hannunta sai ta tarar goma ta wuce,ke nan ta yi zaman sama da awa daya a cikin motar. Ranta ya yi mugun baci, kawai sai ta balle murfin motar ta fito,kai tsaye ta wuce reception ta dinga bin mutane da ido,amma babu abdullahi sai wasu ma'aikatan da ta sani ne suka dinga kawo mata gaisuwa."Madam kwana biyu". Inji wata nos wai ita sister Rabi,fatima ta yi murmushi kawai domin babu amsar ba ta.ta kuma cewa. "Kuna da appointment ne?" Fatima ta yi saurin girgiza kai. "A'a wani yaro na rako,amma kinga ya shanya ni kawai fiye da awa daya,ina jiransa" Sister Rabi ta bi jama'ar da kallo,ta ce. "Kuma babu shi a nan?" Fatima ta gyara kai, sister Rabi ta kuma cewa. "To ko abdullahi ne? Shi ne ya jima tare da doctor" Fatima ta hadiye takaicinta. A takaice ta ce. "Shi ne" Sister Rabi ta tafi tana cewa. "Bari na miki magana da shi. Ba ta jima ba ta fito ta ce. "Ya ce ki shiga". Dan babu yadda ta iya ne kawai ta tura kofar ta shiga,ta tarar ana yiwa abdullahi allura. Ta hau nazarin ofishin kafin su gama,sannan ta nemi guri da zauna tana harara abdullahi. 4 · Like · React · Report · May 16, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 12) Dr ya koma mazauninsa cike da mamakin ganin Fatima,kuma wai matar abdullahi ce, da me Abdullahi ya rako wannan sarauniyar matan? Tu'ajjinbin ya tuke a nan. Suka gaisa tana wani basarwa ita a dole ba ta san shi ba, shi kuma ya ki yarda da hakan,ya ce mata. "Ki yi hakuri ya karbi wata allura ne, ya zauna zaman jiran rabin awa ya sha magani sannan ya karbi wata" Ba ta tanka ba, kuma fuskarta ba ta bayyana matakin da zuciyarta ta dauka ba, ya kuma tambayarta. "Madam kwana biyu?" Ta yi murmushi kawai nan ma ba ta tanka ba, idanunwanta na kan Abdullahi,tana masa duban tuhu$a. Shi kuma ya ki yarda su hada ido.sai ya mayar da hankalinsa ga likitan wanda ya fara yi masa bayani. "Za mu dinga haka duk bayan wata daya kai kuma Allah ya sa akwai madam a kusa sai a hana ido bacci... Ina mana fatan dawainiyarmu ta zo karshe Abdullahi". Abdullahi ya mike, ya mika masa hannun yana cewa. "Insha'Allahu dr,na gode fa". Sannan ya juya ya dube ta, ya yi fuska ya ce. "Ke kuma mene ne tunda kika shigo kike ta faman harara ta, yi hakuri yarintar tawa ce ta motsa in ba ki hakura ba kuma idan mun koma gida sai ki daki abinki." Ganin likita ya sa ta maida abin wasa. "Abin da ka yi ai ya fice kuruciya,dan na ce maka yaro is good ya ya za a yi ka shanya ni fiye da awa daya? Idan akwai abin da ya fice duka ma ba sai na yi maka ba, ya kamata duk gajiyar da na yi ka kwo ni nan ka dire,a kalla yanzu na yi nisa da bacci. Ya hadiye dariyar ketar da ke tattare da maganar da zata fito bakinsa. "Watakila wata gajiyar ke kiranki". Ta yi masa duban rashin fahimta,amma sai ta share saboda idon likita,suka yi masa sallama suka fice, amma suna shiga mota ya biyo abdullahi da kira ta waya. Sai ya dube ta,ya ce. Don Allah zahara'u minti biyu na manto maganin aofishin Dr". A kufule ta mika masa hannu,ta ce. "Gulma dai kawai na dawainiya da ku. Ba ni key din idan ka fice minti biyu na rantse sai dai ka tarar da filin wajen". Yana dariya ya mika mata,sannan ya falla da gudu. Dr ya rike hannunsa fuska a rikice,ya ce. "Da gaske fatima matarka ce?" Fuskar abdullahi da alamun mamaki ya kada kai,likita ya sauke numfashi ya ce, "A'a tsaya kar muyi haka da warwara.ta amince zata haihu da kai?" Da karsashi Abdullahi ya ce. "Ba ta da zabi" Dr ya dururuce hannu alamar jinjinawa ya ce. "To kar ka yi wasa, ina zaton kukanmu ya zo karshe,don mahaifarta na saurin karbar ciki,sai dai ba ta da juriyar rike shi idan ya yi kwari,idan hakan ta kansace yana da wata uku za mu yi mata wani aiki,sannan mu bi lamarin da addu'a. Abdullahi barkatai suka taru a kwanyan Abdullahi lpkaci guda,albishir din likita da fargabar yadda za su kwashe da yar rikicin ban da minti biyun da ta ba shi. A gaggauce ya yiwa likitan godiya ya fice. Ya dinga jan motar a sannu kamar ba dare ba, ne ma sai da ta yi magana. "Yanzu don Allah a titin nan zamu kwana?" Ya dan yi mata wani duba,ya ce. "Ai na ga kin gaji ne bai kamata na fige motar ba ko? Ta yi shiru ta kawar da kai". "Kin san maganin gajiyar nan taki? Muna zuwa gida ki yi wanka da ruwan mai dumi sannan ki dan ci kayan marmari ki sha zuma kofi daya,tsab za ki ji kin wartsake. Nan ma ba ta tanka ba, har suka je gida yana nemanta da magana tana sharewa, shi kuma bai hakura ya bari ba. Suka shiga dakinta ya ajiye mata kayan da suka shigo da shi zai fice zuwa dakinsa,ita kuma zata shiga wanka. Ta kira shi ranta a dan bace.ya juyo ta ce. "Kar ka kuma shigo min da wanin bargo da filo dakin nan". Ya yi nazarinta da kyau,amma yanayin bacin fuskarta ya sanya shi hadiye tambayarsa,ya yi mata. "Zumar zan kawo miki?" Ba ta tanka ba ta wuce bandaki,shi kuma ya fice ya dan jima sannan ya dawo mata da zumar a kofi,ba tare da shakka ba ya ishe ta har dakin bacci tana zaune gaban madubi daure da towel. Fuskarta ta nuna rashin jin dadin shigowarsa,sai dai bakinta bai furta ba. Ta karba tana dan binsa da kallonm nazari,shi kuma ya birkida tunaninta da siyasa,dan ya nuna bai damu da yadda ya same ta ba. Ya cire riga ya shiga wanka a toilet din cikin dakin. Da sauri ta shirya ta zira kayan bacci masu kauri ta dauki zumar ta fice falo cikin damuwa irin irin ta Alh da ta shishigin da abdullahi ke mata yau 2 · Like · React · Report · May 16, 2015 Amierah S-Man Amun hakuri rashin sa page 5 Like · React · Report · May 16, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 13) Da kuma na gorin sadiya,babu wanda zata iya magani ba tare da ya gagare ta ko in ta yi maganinsa ta cutu ba, wato ba ta da damar magancewa Alh matsalarsa,shishigin Abdullahi kuma makale da gorin sadiya,wanda maganin gorin shi ne ta karbi tayin shi da shishiginshi, a nan ne kuma ita zata cutu. Duk zakin zuma sai dinga shanta kamar magani, har dai ta dire kofin ta dan kishigida a kasalce.ya fito shi ma sanye da yalwatattun kayan bacci, kallo daya ta yi masa ta kawar da kai,shi ne ya dora mata ido,har ya kada kai zuwa kicin ya yanko lemo,abarba,kan kana da gwanda ya dawofalon ya zauna kujera kusa da ita ya sanya kayan marmarin tsakiyarsu kan hannun kujerar,ya ce mata Bismillah". Ko motsi ba ta yi ba, babu kuma alamar zata tanka masa bare ta sa hannun.ya share ta ya ci gaba da shan kayansa yana kallonta ta janyo mayafin ta dora aka, sannan ta kara kishingidawa can gefe,ta juya masakeya. Ya dinga nazarinta yana tunanin inda zai kamo zarenta ta kula shi. Ya yi gyaran murya tukunna ya ce. "Wai fadima me ke faruwa ne nake ganin ranki a bace?" Ta girgiza kai kawai ba ta ce komai ba. Ya dan ja fasali sannan ya ce. "Me yasa kika hana ni shigowa da filo alhalin kina rufe dakunanki?" Ta juyo a sanyaye ta dube shi, idanuwanta sun dan kada alamar ranta a bace yake.ta ce. Sai ka dinga shiga nan dakin ni ina shiga can, kafin Allah ya yi ikonsa akan mu... Mts! Ba na son kananan magana ne, wai babu abin da ya wuce a ci maka fuska a kansa,ai kishi bai yi ba wallahi." (Allah ya yiwa sadiya albarka) abin da ya yi ta maimaitawa ke nan a ransa,amma ya hana fuskarsa nuna farin cikin da zuciyarsa ke yi,sai ya tara jimamin duniyar nan afuskarsa, sannan ya shiga lallabata. "Kofofin da nake ta fatan ki toshe ke nan tun tuni,idan ba ki bayar da kofa ba mutum ma shakkarki zai yi.yanzu me ye ma na sai mun raba dakin? Ko babu komai ai zamu dinga debewa juna kewa..." Ta yi saurin dubarsa,amma saboda fuskarsa na bayyana jimami sai ta kawar da kai,ta ce. "Ban iya yaudara ba" Ya amsa a tausashe. "Dama babi ita a tsakaninmu,na sanki farin sani, kina furta min gaskiyar zuciyarki saboda haka na san matsayina a wajenki, ni ma bana boye miki dukkan abin da ke raina,ya sa ki farin ciki ko akasin haka,ba na damuwa dan in sin tabbatar miki da gaskiyata,ke ma tun kina ganin bekena har ranki ya yarda babu cuta a tsakanina da ke..... Babu soyayya ya isa rike wani gidan auren". Ta yi shiru ba ta tanka ba, kanta na kallon kasa,kwalla duk ta cika mata ido. Ya jima yana kallonta. Harshensa bai

Chapter 2 of 8