Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 8
sanyi. Zuwan maryam din ya yi mata dadi,dan tana da tarin bukata kamar na dauke kewa,da wata hidima tata ta musamman da ta shafi sirri. Dan haka ta karbi maryam hannu biyu fiye da zaton mutum,maryam kuma ta canji Abdullahi inda ta dinga yi mata hidima kan jiki kan karfi kusan fiye ma da Abdullahi tun da ita mace ce. Kwanaki ukun da abdullahi ya yi yana jinya,kwana daya a dakin Hindatu,biyu a girkin fatima sai suka zame masa wasu kamar na sallah,ya sami hutu kuma ya sami kusanci da hira tsakaninsa da fatima,domin da ta karbi girki sai ya kwashi jinyar tasa ya tare a can dakinta,babu halin ta daure masa fuska,kuma dole ta dinga yi masa sannu tana nuna masa kulawa saboda idon maryam da ke tare da su. Da dare ma dole suka kwana daki duk da ta takura kanta ne akan sofa. Kwanan sadiya daya da karbar girki ya dawo gida da yammaci ya ci karo da maryam zata shiga gida,sai ya ji babu dadi a ransa,dan malam ba ya son fitar su maryam kamar matan aure yake kullensu,to ina ta je? Tana yi masa sannu da zuwa yana bata fuska da tambayarta. "Ina kika je?" Ta daga masa ledar da ke hannunta mai dauke da tambarin wani pharmacy,ta ce. "Anty fatima ce ta aike ni". Ya bi. Leadar da kallo cikin rashin fahimta,ya ce. "Kika siyo mata me?" Sai ta yi dariya kawai tana cewa. "Oho! Rubuta min ta yi na zaci ma magani ne". Da sauri ya mika hannu ya karbi ledar ya zazzago abin ciki,sai numfashinsa ya nemi daukewa,ya zare ido yana kallon maryam,ya ce. "Me zata yi da pt-strip?" Fuskar maryama ta bayyana tsoro saboda rikitar da ta ganshi a ciki. Ta debo in ina tana cewa. "Ni .... Ni wallahi ... Ban sa.... Sani ba...... Ban ma san na me ye ba". Zuciyarsa ta kara saurin bugu,numfashinsa na son shakewa.da kyar ya dake ya mika mata tare da murmushin karfin hali,ya ce. "Ungo! Kai mata". Maryam ta wuce sukuku shi kuma sai shiga gidan ma ya gagare shi gaba daya,saboda fargabar yadda zai je wa sadiya a rikice, kila wannan ya janyo su tashi dan karamin yaki saboda rudanin da zuciyarsa ke ciki. Fata! Fargaba! Sun hade masa waje daya kawai sai ya shige cikin motarsa ya dinga fama da rigimarsu. Sallar magriba ta tashe shi ya wuce masallaci amsa kiran mahalicci tare da dokin kai wancan fatan nasa gare shi. Sai karfe tara ya nemi gida bayan ya sallaci sallar isha,dadewarsa a wajen bai hana shi shiga gidan a birkice ba, saboda tsannain kaunar hada ido da fatima da ya mamaye ransa,ba kuma hada idon kawai ba har da kaunar sauke mata tambaya daya kacal wadda a ma'auni ta fi dutse dala nauyi. "A kawo maka abinci?" Da tambayar da sadiya ta kori shirun da ke tsakaninsu ke nan, bayan ta gama cikarta da batsewa,shi kuma ya nuna halin ko'inkula.to a nan ma sai aka kuma kwatawa,domin girgiza mata kai ya yi alamar kar ta kawo,tunda bai ga amfanin tambayar ba. Sadiya fa ta zo wuta iyaka! Ta hadiye wani katon kullin bakin ciki,ta ce. "To wai me yasa ba zaka sallama ni gaba daya ba? Ka hada mata kawai da kwanakin nawa,sai ka bar ni gadin dakinka kawai,tunda ba zan ce ka barni zaman 'ya'ya ba". Ya share ta,fuskarsa a hade ya dauki remote ya latso tashar kallon kwallo,sannan ya ajiye remote ya wuce fridge ya dauko fura ya markada abarsa cikin matsakaicin jug ya hado da kofi ya dawo ya zauna ya fara sha hankali kwance abinsa. Da ta kalle shi sai ranta ya kara mungun baci,kamar ta mike ta rufe shi da duka,sai ta zabga wani katon tsaki,ta ce. "Me ye amfanin zama da makiyi don Allah? Na rantse maka yadda kake jin ka tsane ni haka nake jin tsanarka dan dai kawai ba zan iya sakin kaina ba ne". Nan ma ya shanye ya ki tanka mata abin da dama ya dinga gudu ke nan,ga shi kuma bai tsira ba, ya kasa gane wannan bala'in na sadiya wadda ke neman so da masifa. Har ta karaci maganganun cin fuskarta bai tanka mata ba, ta fice daga falon cikin fushi,shi kuma ta ba shi damar fita ya tunkari dakin fatima da nufin yi mata bankwana.ita ma da nata cin kashin ya yi kwankwasawar duniya ta share shi, dan maryam ta yi bacci, dole ya kwashi sassanyar gwiwa ya doshi dakin Hindatu domin yi mata tata asubar ta garin. A ranar bai yi bacci kirki ba saboda tsabar fata da fargaba.ya rasa inda zai aza tunaninsa akan farin cikin cikin fatima ko kuma a farin cikin yadda cikin zai iya matsanta mata zama da shi, ko kuma idan labarin bai kasance haka ba akan bakin cikin yadda zata iya masa wasarere da cikin? 2 · Like · React · Report · May 16, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 2 .20) Da ya rasa mafita sai ya zabi ta tashi kai wa ubangiji kokensa na godiya tare da neman dauki. $ da safe ma bai sami ganinta ba, ya sami shiga falon saboda maryam ta tashi har ta fara hidimominta amma dakin uwar dakin a kulle. Sai ya share ya fice kawai dan ya lura da take takenta idan ya matsa sai ta tsinka shi wajen maryam. ****************************** ****** ************************************ 'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Kawai fatima ke fada tana maimaitawa tana ja da baya da jikin jikin din bayan ta yar da tsinken gwajin da sauri. Tana bin kayan gwajin da kallo tare da shafa cikinta lokacin da ta ke ja da baya kamar su be cikin ta ke son gudar musu ba wanda ke jikinta ba. Ta runtse ido ta girgiza kai da karfi tana dokin abin da ya faru ya zama mafarki,amma hakan ba ta samu ba sai cikin nata ne ya yi mata inkiya da wani karamin motsi da bayar da shaida. Ta sulale cikin jiri zuwa kan mat shower ta zauna cikin kuka da girgiza kai tana hadawa da ambaton,"A'a,a'a insha'Allahu ba zai kasance ba!" Fiye da rabin awa tana fama da kuka da wannan sambatun,can ta mike da wani karfin hali kamar na dan daudun da ya kama kadangare ta kuma farke wata takardar ta canja tasa ta sake wani gwajin.tana tsaye a kansa ba ta ko kifta ido har lokacin ya cika ta zare tsinken shi ma ta shiga gadinsa fiye da mintuna biyar sannan ta daga shi cikin bugun zuciya. Har yau ba ta canja zani ba,yanzu ya fi dazu fitowa rangadadau ma kamar ya san shakka ta ke, kawai sai ta kece da kuka!..21) Tun kafin biyar ta cika Abdullahi ya dawo gida a hikimarsa ta neman dalilin da zai sami ganin fatima,su kebe idan ma da hali ya tambaye ta sakamakon da gwajin ya bayar. Har biyar da Rabi yana zaune a dakinsa sadiya ba ta leko shi ba bare ya hutar da tata zuciyar har ya sami damar tafiya ganin fatima,ga shi kuma yana kyashin binta ya rarrashe ta tunda bai ga laifin da ya yi mata ba. A karshe kawai sai ya fada wanka ya shirya ya zari mukullin mota ya nufi dakin fatima.ya same ta da maryam suna cin tuwon shinkafa miyar danyar kubewa kwano daya. Suna gaisawa shi kuma yana duban agogo,sannan ya sauke ganinsa akan fatima wadda kallo daya ya yi mata ya karanto damuwa a kwayar idonta,ya ce. "Abincin dare kuke ci ko na rana?" Ta yi murmushi yake ta kawar da kai,da haka kuma ta bar tambayar tasa ta bi ruwa, saboda makoshinta ya toshe da haushinsa ba ta ko kaunar bude ido ta ganshi,sai maryam ce da ta ke zaton jikin da fatima ke ji ne ya hana mata magana,ita ta amsa masa. "Na rana ne, Anti ta kasa cin komai sai tuwo". Shi ma ya gyara zama a gabansu ya watsa hannu a kwanon yana cewa. "To Anti sannu,dama yanzu shigowa nayi mu je asibiti. Daga nan sai mu mayar da maryam gida tunda ni na sami sauki". Sai da ta ji fasali, sannan ta amsa. "Rashin son cin wani abinci sai wani, ai ina tsammanin ba cuta ba ce,ra'ayi ne kawai saboda haka ni ba zani wani asibiti na, maryam kuma ban shirya ta tafi yau ba". "Ya kai lomar tuwo uku kafin ya amsa mata ba tare da ya dube ta ba. "Na sani,ni 'yar burum burum ce ba na so.... Sannan malam ba ya son su maryam su yi nisa da gida, idan muna son gaba a bamu ita ai dole mu mayar da ita akan kari,amma dai in ranki bai so hakan ba ki yi hakuri. Ya kare maganarsa da tausasa murya dan son ya ragewa zuciyarta dacin da ta ke ji. Suka yi tsit har suka gama cin abincin maryam ta nemi wanda zai kara Abdullahi ya amsa zai kara,har fatima ta yi musu shiru,sai da maryam na dab da shiga kicin ta dan daga murya. "Shi ma ya koshi dan kadan zaki. Zubo masa. Sannan ta bishi da harara tana cewa. "Ban ga fa dalilin da zaka zo ka cinye min abinci ba, alhalin ga naka can". Ya kura mata ido tare da wayon kallon cikinta,dan haka ya kasa damuwa da ma'anar kyarar da ta ke masa har ta fara tsarguwa da salon kallon nasa,sai da ya ga tsarguwar tata ta yi yawa sannan ya basar yana dariya,ya ce. "Dama kina cin tuwo? Amma kwanaki can da na yi miki kika ce min ba ki san shi ba,jiya kin yi tuwo yau tuwo,mene ne dalilin?" Sai ta juya masa keya kawai har maryam ta fito.ya yi mata sannu da kokari,sannan ya ce. "Ki shirya mu tafi". Ko daya fatima ba ta so hakan ba, dan maryam na matukar ji da ita,tana yi mata hidima tare da tausayawa,ko motsi ta yi sai ta yi mata sannu,kuma ga ta da iya girki,da hidimar yi mata tuwo kullum ba tare da ta cika ta da tambaya ba. Sai da maryam ta shige daki,sannan ta daga kai ta dan yi masa duban rahma. "Idan kai ka ji sauki ni naji ne? In dai don ni ka kawo ta ke nan. Ba tare da ya dube ta ba ya amsa. "Idan ta zauna ni ne zan kuma kwantawa, dan na ga yanzu ne ma kike kan sharafin kina mayar da ni aljihun baya. Gara ta koma gidansu ni kuma na koma bakin aikina,idan kin ji ciwo sai ki kimtsa halinki",. Kawai sai ta share shi, ta mike zuwa dakinta inda ta yiwa maryam sha tara ta arziki har da kudin dubu goma. Suka yi sallama da ciwon rabuwa,ya tafi mayar da ita gida. Da ya ga take taken fatima na sanyawa kai damuwa da neman rigima da shi sai ya watsar kai ita kawai yana jiran ta karbi girki dan su ji dadin yinta su wanye. Ranar da zata karbi girki ta samo amsar lissafinta(-) minu,ma'ana zabar zubar da cikin kawai tun ma kafin ya fashe ya zame mata matsala ta ko wanne bangare,wato ta bangaren Alh da zai san ta ci amanarsa!da kuma ta bangare Abdullahi da zai iya yi mata karan tsayen zubar da cikin,ko kum$a shi da danginsa da za su hau ta yamadidin ta sami ciki. Cikin shirin fita ya shigar mata sanye da fararen kaya kasancewar juma'a ce. Ya same ta zaune falo cikin alamun tunani, amma tana ganinsa sai ta daure fuska,shi ma sai ya dake ya dan bata fuska ya ce. "Me zan yi miki na karin kumallo?" Ta dan biyo shi da kallo tana so ta fassara yanayinsa,sai ya bar mata wajen kawai ya shige dakin baccinta,har da turo kofa.ya dinga nazarin dakin kamar shi zai tabbatar masa da sakamakon gwajin da ta yiwa kanta,cikin kasala ya hakura ya hau gyara mata gadon,ya gyara dakin tsab,sannan ya bude bandaki shi ma ya bi shi da kallo har idonsa ya fada kan dust bin ya hango tsinkayen nan. Ganinsu guda biyu ma ya fara ba shi tabbas din ya yi nasara. Ya hadiye dukkan murnarsa,ya fito falon ya same ta har yanzu tana wajen da ta ke. Ya gimtse fuska ya hau gyara falon,har sai da ya kammala sannan ya kuma dubanta. "Har yanzu ba ki yanke shawarar abin da kike son ki ci ba?" Ta kara daure gira,ta ce. "Kawai ka dafa min ragowar tuwon nan". Bai tanka ba, ya wuce kicin din kawai.ta bishi da kallo ranta na kara yi mata daci. Tana so tilastawa kanta ganin bakinsa fiye da yanzu,amma da ta dube shi sai abin da ke cikinta ya fado mata a rai.da alama zumuntarsa da abin cikin nata ke mata iyaka da kaiwa matakin karshe akiyayyarsa. Kamar yasan hakan ya ki yi mata shisshigi, har ya gama hidimarta ya fice. Karfe sha daya dai dai ta shirya ta baza hijabi ta kullop kofarta,ba ta damu da ta yi wa kowa sallama ba, ba don suna tsakar gidan ba sun dai gaisa da Hindatu har ta ce mata a dawo lafiya. Ta dauki shatar adai daita sahu zuwa asibitinta, inda ta dakatar da shi ta shige. Dr na jin cewa ita ce, sai da ya ji alamun tsoro da fargaba a ransa,saboda tausayin Abdullahi wanda ya kwallafa rai akan samun dan kai. Ya sallami pt da ke gabansa ya share wadanda ke kan layi.ya ce ta shigo. Suka gaisa a gajarce kamar yadda suka saba, shi yana juya kujerar yana kallonta a nutse tare da nazarin cikin dukan ziciya.ita kuma ta yi kicin kicin tana bin office din da kallo kamar wanda ya canja mata. 1 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man .Zuciya d kwanji 2 22) Abin mamaki yanzu Abdullahi ya yi min wauya kuma bai sanar min cewa kina hanya ba". Ta yi saurin dubarsa kamar a rikice, amma sai muryarta ta hadiye rikitarta,ta ce. "Ya yi maka waya akan me?" Sai da ya ja fasali sannan ya canja gaskiyarsa amsar da ya kamata ya ba ta. "Ya tambaye ni izinin zuwa ku ganin game da matsalolinki. Ya sanar da min ba ki da koshin lafiya". Ta yi shiru tana janye kai a hankali,ta jima kafin ta tanka,sannan ta nisa. "Sai ga shi na kawo kaina, sai dai kuma babu hannunsa ko yawunsa a ciki, ni ce kawai da na da yunwar lafiyar zata halaka ni nake son karya a zumin. Ya ci gaba da kallonta kawai da alamar tambaya har ta gaji da shan kamshinta ta fasa. "Ciki ne da ni, amma in so ka fitar min da shi dan ba ni da bukatarsa, sai dai bana so Abdul ya san da labarin". Kallon da yake mata ba zata iya fassara abin da zuciyarsa ke rayawa ba, amma zuciyar tasa ta raya manyan abubuwa,ta ga kuma girman ta'adancin fatima da zaluncinta,wadda ba ta san kowa ba sai kanta.... Me ya yi zafi da ta ke son mayar da zuciyar mutum mai kirki kamar Abdullahi dai dai da bakin tunkunya? Da tambayar da amsar sai ya hada su ya hadiye ,ya kuma boye abin da ke zuciyarsa,cikin sakewa ya ce. "Ayya! Me ya yi zafi? Ni kuma gani nake ko wanne runtsi kika shiga Hajiya barin cikin sai ya fi zubar da shi alhairi". Ta kyabe baki,ta ce. "Ban zo maka da tarihina dan ka yi min gyara ko ka shawarce ni ba, in wannan ne sai in nemi malamin falsafa. Na zo maka ne akan aikinka wanda a kansa kake zaune a wannan kujerar". Ya jima yana wasa da biro cikin kada kai, sannan ya sauke numfashi ya ce. "Wanne nau'in zamu yi?" Cikin farin ciki ta ce. "Mai sauki dai, yadda wani ba zai fahimci halin da nake ciki ba". Ya kuma jan fasali, sannan ya ce. "Wata nawa ne?" Har sauri ta ke,ta ce. "Uku". Nan ma ya jima yana juya al'amuran cikin ransa,sannan ya janyo takarda ya fara rubuce rubucensa, kana ya daga kai ya dube ta. "Idan haka ne,ba ma bukatar gaggawa ke nan,sai mu yi komai cikin dabara,ki yi barinki hankali kwance, yanzu za ki karbi allura da magunguna mu jira sati biyu sannan ki dawo mu dora,kin gane?" Ta kada kai zuciyarta daya. Ya shirya mata file sannan ya yi kiran nose din da zata ji da ita. Bayan allura har jininta aka dauka da ta nemi ba'asi sai nos din ta ce, mata za'a yi wani gwajin ne. Sai sha biyu da rabi ta fito asibitin a gurguje ta shige a dai dai sahun ya ja suka tafi. Da yake juma'a ce yana tashi aiki biyun nan sai ya wuce gida. Sai da ya yi duba ya kara bincikawa amma bai ganta ba, ya fito ya zagaya baya sai su hindatu.ya koma yana mao tsoro da tashin hankali,kar fa fatima ta je ta zubar masa da ciki?" Dan dai ya tabbatar din sai ya kuma zagayawa baya hankali a tashe,ya ce" "Hindatu,fatima fita ta yi ne?" Cikin shariya ta ce. "Eh ba ta dade da fita ba ka shigo". Ya furta,innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a hankali, fuskarsa na kara bayyana damuwa da hasasshen inda ta tafi. A rikice ya kuma duban hindatu. "Dama ta taba fita?" Makira sadiya ta yi saurin amsawa. "Eh mana". Hindatu kuma ta girgiza kai. "Gaskiya ni ban taba ganin ranar da ta fita ba,idan dai ba tare kuka fita ba". Ya yi kwafa da rangaji ya juya.bayan tafiyarsa hindati ta dubi sadiya ta ce. "Me yasa zaki yi mata karya sadiya?" Ta yi tsaki ta ce. "To me ye amfaninta? Da kin bar ni har da sharri sai na yi mata wallahi. Hindatu ta girgiza kai,ta ce. "Kin manta dan sako ne sharri, idan ka yi shi ba ka bukatar rufe kofa dan zai dawo maka da amsa.ba na tsammani makirci zai yi tasiri a lamarin mutanen nan wanda ya wuce addu'a.kina tsammamin duk tabarar da ta ke bai ji haushinta ba sai fitarta ba tare da izininsa ba? Go slow ya hade wa su fatima, ba ta sami isa gida ba sai daya da kusan rabi,lokacin Abdullahi ya hakura da lissafinsa ya fita za shi masallaci,sai suka yi kacibus a tsakar gida. Ya babbake hanyar da zata wuce ransa bace! Tsoro ya bayyana karara a idonta, don haka tayi saurin kawar da kai daga kallon kwayar idonsa. Ya daka mata tsawa ya ce. "Daga ina kike?" Ta dan ja da baya dan rage tazarar da ke tsakaninsu,bakinta na rawa ta amsa masa. "Ina ka aike ni?" Kafin ma ta dire kawo mata mari, wanda hucinsa ne ya sami fuskarta saboda saurin ja da baya da ta yi hadi da dafe kunci, ta bar shi da marin iska. Abin ya ba ta mamaki tare da daure kai, ta dube shi ta ce.23)"Abdul lna tsammanin ka kai martabar da zaka daga hannunka da sunan kai duka a jikina?" Ya cije lebe yana bin gidan da kallo,sannan ya tuna akwai'yan sa ido,kawai sai ya finciki hannunta ya ja ta dakinsa,yana rike da hannunta tana yunkurin kwacewa ya sa makulli ya bude dakin,ya ja ta ciki sannan ya mayar da kofar ya rufe,lokaci daya kuma ya ture ta gefe kamar dama cizonsa ta ke,sai da ta yi namijin kokari sannan ta sami tsaywa da kafarta tana binsa da kallo cikin tashin hankali iri iri. Ya murza hannu yana kallonta da fuskar gargadi. "Da ace akwai abin da ya fi duka kaskanci. Na rantse da na yi miki shi a yau. Na tabbatar kuma ba za a zarge ni ba dan na kaskantar da wanda ya kaskantar da kansa. Ta tare shi da shafakkiyar murya. "Na yarda ni na kaskantar da kaina na aure ka,sai dai kar ka shiga dimunwa wannan bai isheka damar da zaka daki fatar jikina ka zauna lafiya ba". Ya naushi hanunsa yana takawa a hankali ba tare da ya juyo ya dube ta ba da kaukkausar murya,ya ce. "Na rantse miki duk ranar da kika kuma sanya kafa kika bar gidan nan sai na yi miki abin da zaki gamsu kai kake fara kaskantar da kanka kafin a kaskantar da kai, kawai ki rike a ranki duk hakurina da kawaicina ba zai taba shafar dokata kulle kafarki ba tare da izinina ba ki ba ni amsar inda na aiki ki? An fada miki ni Alh ne? $ sai kawai ta saki baki tana kallonsa, bai ja maganar ba ya nufi kofa ya fice bayan ya dubi agogo. Tana layin ta biyo bayansa,ya fice abinsa ita kuma ta bude dakinta ta shige cikin hawaye da takaicin yadda abdullahi ya sami damarta. Babu abin da ya yi mata ciwo irin kalamar da ya fada mata. "Ko an fada miki ni Alh ne?" Ta wuni da takaici da bakin ciki goma da ashirin,ga na cikin jikinta ga na mai cikin. Hagun wani damar wani ita kuma sadiya ta wuni da farin cikin da rabauta da irinsa tun ranar da aka kawo ta matsayin amarya.. A yau ta tabbatar duk ma wata rawar kafa da abu Turab yake akan fatima ta bogi ce, dan duk tsaurin idon da yake mata kirari bai taba gwada dora hannunsa akan fatarta ba. Duk wani kisinme kisime da sadiya ta san zai shugabantar da ita a zuciyar abu turab ayau ta yi shi,ciki har da daukar shawarar kisisina da kawaye suka dade suna ba ta tana watsarwa. Ta yi kwalliya ta kai kala uku,tana baza idon ganin shigowarsa dan ta je ta fanshe nata girkin da yake kai wa fatima idan hargitsi ya hado su. To bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha, kuma abin da ya kusan buga numfashin sadiya kai tsaye dakin fatima ya shige. Ta dinga bulala tuarare tana safa da marwa a tsakar dakinta,kawai sai ta jefar da kwalba ta tunkari dakin fatima. Ya sami fuskar fatima a kode saboda tsabar kuka,sai duk jikinsa ya kara sanyi,ya dinga nacin kallonta yana aika mata sakon ban hakuri da ido,amma ta ki yarda ta dube shi sai faman cika ta ke tana batsewa,ya ajiye jaka ya isa gabanta ya durkushe ya kamo hannuyanta ya rike da sassauci,da sauti a makogwaro ya ce. "Ki yi hakuri fadima.... Kin ji? Ki yi min uzuri akan yadda na rufe ido na yi miki ba dai dai ba. Haka Allah ya yi ni, so ko wani KYALLI ba ya rufe min ido na kaucewa ra'ayina wanda ba na kirkirarsa akan son zuciya,ko babu wata a kasa ba zan iya barinki fita sasakai na saboda kina da sura mai hatsari.... Bari na sami ni dan karo ne kawai a cikin rayuwarki, Allah ne dai ya sallada shugabancinki a hannuna... Amma na sani... Ke ma kin tabbatar min ni ba komai ba ne a cikin rayuwarki.... Sai dai na yi mamaki da na ji wani matsanancin kishi wanda ban taba tsammanin an halitar wa wani bil'adama irinsa ba lokacin da na zo na tarar ba ki cikin gidan nan duk kuwa da na san ni ba wata daraja nake da ita ba a wajen ki ....." Ya dinga kokarin kallon fushin fuskarta, idanunwanta na ga talabijin, ya kai yatsanta bakinsa ya gatsa a hankali,sannan ya hura yana son su hada ido, amma ta ki.ya tausasa murya ya ce. "Kin janyo abin da makota suka ji tsanainmu ko fatima? Yanzu abin da ya fi damuna ke nan, wato samun kofar da za a zaci gibi a cikin son da nake miki... Kila ke ma ki ji hakan a ranki.... Amma kamar yadda na fada miki laifinki irin wannan ba zan iya hadiyewa ba don Allah kar ki kuma,kin ji? Ina kika je? Ina fatan ba wajen Alh kika je ba". Ta tamke gira rai a bace ta juyo ta dube shi, bakinta ya dinga motsi dan canki cankin abin da zata ce masa... A karshe ta samu kalamar ta fito da kyar. "Dama mun yi da kai zaka yanke dangantakar da ke tsakanina da shi ne? To ko wajen nasa na je batawa kai lokaci ne ka nuna damuwa a kai..." Kwankwasa kofar da ake ya hana ta ci gaba da magana,inda suka bi kofar da kallo su duka,a hankali abdullahi ya furta. "Shigo" Sadiya ta shigo kwas kwas tana taunar cingam ta tsira daurin dankwali daurin ture ka ga tsiya,sai zuba yauki ake. Sai da ta karaso rukunin kujerun sannan abdullahi ya zare hannayensa daga na fatima ya mike a hankali,hankalinsa na kan sadiya wadda ta saci idonsa ta watsa wa fatima harara,sannan shi kuma ta hau yi masa gwalangwaso. "Abu Turab talabijina ce ta ki yi, zo ka duba min don Allah,zaman shiru babu dadi". Yanayin yadda ta ke ne ya daura masa kai, don wannan kwarkwasar ba dabi'arta ba ce,ita banda masifa ma ba ta iya komai ba, don haka ma ya ga sam iya yin bai mata kyau ba. Ya saci kallon fatima wadda ta yi suguri tana kallonsu,a hankali kuma sai ta kawar da kai cikin tunani. $ "kin janyo abin da makota suka ji kanmu ko fatima...? Wato samun kofar da za zaci gibi a cikin son da nake miki..." Yanzu ya gama yi mata wannan karatun ga sadiya har ta fara biyawa.... Bayan takaici sadiya har mamaki ta bata,ko ta dauka daga daji ta fito don hala ba zata gane wannan karuwancin ba? Ita da ta ke da dangi fal! Ko wanne gida da nasa tsarin wanne irin shakiyanci ne ba ta sani ba? Bakin abdullahi na rawa yana kuma satar kallon fatima da ta dauke musu kai,ya ce. "To ban da abinki sadiya ni gayaran talabijin na iya? Kin lalata ta kawai sai ki jita gobe na kira miki mai gyara". Laraf fatima ta shiga maganar. "Tun da ka jiyo ta fadi haka ai ina tsammanain gyaran naka ne,sai dai a nan ma ai kana da wani gyaran duk da bai taka kara ya karya ba, gama da shi sai ka yi wanka na rakaka ka duba mata". Tana rufe baki sadiya ta amsa. "Haka ne,wanda ya bata dole ya gyara duk da an baro kari tun ran tubani inji hauswa". Fatima ta yi mata shiru tana saka amsar bata,sai dai da ta tuna mai saurin fushi bai cika cin tiba,sai ta share ta kawai,ta dauki remote tana latsawa tana sauraron yadda sadiya ta dage tsakaninta da Allah tana yiwa abdullahi shagwaba, wai sai ya zo sun tafi. Ya kuma kasa daukar mataki a kanmta,kirjin fatima ya dinga radadi da zogi wanda ta kasa tantance haushi ne ko kishi? Har sai da ta kasa hadiyewa ta hade rai ta dubi sadiya ta ce. "Baiwar Allah nan fa ba club ba ne da za ki ishi mutane da haninya,shi kuma ba yaron kanti ba ne da za ki ishe shi da tayi,ina tsammanin da karanki ya kai tsaiko ba sai kin batawa kanki lokaci haka ba. Na ce ki je zai zo ya gyara miki.... Kin nace,ko sai na janye alfarmar tawa kewar ta lahanta ki?" Zata yi magana abdullahi ya tare ta. "Kin ga sadiya ki je don Allah,wanka kawai zan yi in zo. 1 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 24) Takaici ya ishe sadiya duk da tana ganin ko yanzu ta yi nasara,ta juya ta fita,shi kuma ya rasa da idon da zai dubi fatima wadda ta kara tamke fuska.ya yi 'yan kame kamensa sannan ya shige wanka. Bayan ya shirya ya fara shashantar da zuwa wajen sadiya da maganar abinci,har yana gayyatarta su fita ta sami tuwo ta ci. Ba don son cin tuwo da ya mamaye ranta ba babu abin da zai hadata fita da shi, sai ta yarda, sai dai ba cikin walwalar fuska ba. "Ina maganar zuwa duba mata talabijin?" Ya dinga nazarinta yana son gane abin da ke zuciyarta,darare ya ce. Ta kara tamke gira,ta ce. "Don me? Idan kuma kewa ce ta dame ta fa? Ka san dole akwai ciwo,mace da mijinta mata har biyu su aure matshi,ban da ta uku me haramar zuwa maimakon layin kwanaki hudu da ta ke hawa ta koma na shida.... Ka je ka rage mata kewa kawai,duk da zan dan yi muku cikas a gabana za a yi gyaran, amma na san ko da kallon fuskarka da

Chapter 4 of 8