Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 8
bar addu'a ba, tsawon wasu mintuna sannan ya ce. "Don Allah ki rage sanyawa kanki damuwa fadima,duk abin da muke. Cin karo da shi a rayuwarmu rubutaccen al'amari ne daga ubangiji,damuwa da bacin ranki ko cida zuci na. Ba zai canja komai ba. Nan ma ta yi shiru,ya kara jimawa yana ambaton ismullahil azam cikin ransa, sannan ya ce. "Ki je ki kwanta ki huta,sai ki dan bar min dan guri kadana ma da zan sanya hakarkarina. Duka duniyar ma nawa ta ke,duk burikan mutum wata rana kabari zai sami kansa". Ta mike ba tare da ta tanka masa ba, ta wuce daki. Ya bita da kallo cikin dukan zuciya har mintuna goma bai ji ta murzawa kofar key ba,ya sauke ajiyar zuciya yana hamdala ga ubangiji,shi ya san hakuri da na ci da addu'a sun fara rana. Biyayya ke nan mai kai akuya dakin kura har ta yi mata tausa 1 · Like · React · Report · May 16, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji .14) A nutse cikin tsarkin zuciya ya dauro alwala ya gabatar da nafila raka'a shida tare da neman daukin ubangiji a dukkan bukatunsa na daren yau,ya mallaka masa fatima,ya takaita masa wahalar neman soyayyarta,sannan ya ba shi dan kansa. Da hawayensa ya dinga yiwa ubangiji kirari yana jaddada kokensa.bayan ya sallame ya jima zaune gurin,sannan ya hakura ya ninke sallaya ya shiga bandaki ya wanke baki,ya jefa minti a baki ya tunkari dakin da karfin gwiwa yana ambaton Allah. Akwai alamun idonta biyu,saboda yadda ta takure a can karshen gadon.ta lulluba da wani bargon ta tattare masa na kan gadon gefe guda,ya tura kofa sannan ya kashe gulob,kamar mai tafiya akan ruwa saboda tsabar shauki. Ya tattare bargon da ta ware mai ya ajiye gefe sannan ya janyo wanda ta takura. Sai ta motsa a firgice, ya hana zuciyarta kai matakin karshe a firgitar bare ta dau mataki.a rikice ya ce. 'Au fadima ba ki yi barci ba? Gajiya ko? Bari kawai na yi miki tausa". Bai jira amsarta ba,ya shisshige mata ya nuna mata abin da yake nufi.ta yi iyakar kokarinta na son ta bijire,amma da yake ba a sassakata da karfe ba,ga abdullahi ya kware wajen rikita,sai ta bayar da kai bori ya hau,musamman idan aka kirga watannin da ta kwashe cikin kewa dan ma an halicci mace da kawaici. Dukkansu babu wanda bai taka rawar azo a gani ba suma da minti talatin,amma a karshe sai ga su kace kace cikin kuka. Babu wanda lamarin bai zo masa a bazato ba. Abdullahi na saka ran akwai wannan ranar,amma bai tsammance ta cikin sauki haka ba.... Bai kawo ta nan kusa ba.... Bai taba zaton hadin kai gare ta kamar haka ba..... Ga kuma tsarin likita..... Ga shi cikin yawaita ambaton Allah da kuma neman tsarinsa daga abin ki..... Ga kuma fadima a cikin mata sa'ida...... Kuka ma ya zame masa tilas dan shi yake nuna tukewar farin ciki. Dalilin kukan fatima sun zarce nasa a yawa, sai dai sun fi nasa nauyi sun kuma fi su tauri a rai, dan nata ba su rabi farin ciki ba, na bakin ciki ne da kaico iri iri,ya ya aka yi ta sake haka ta faru? Ta ci amanar Alh ta dandanawa Abdullahi zumarta,kuma matakin ne da zai hana shi sakinta. To da wacce fuskar ma zata ci gaba da kallonsa kuma sa wacce zata yi masa burga? Idan ya ki sakinta ya ya shirin zuwa nan da wata daya da rabi? Kukanta ya tsananta sai shi ya hakura da sheshekar nasa,ya himmatu rarrashinta, da kalaman ban hakuri da na nuna kauna har da wadanda bai taba tsammanin kwakwalwarsa zata iya kirkira ba, bai samu ta tsagaita ba sai da ya tuna mata. "Fatima kin san fa ba mu kadai ba ne a. Gidan nan, wani fa zai iya jiyo wannan kukan naki," Ta yi dif! Illa hawayenta da ya kara gudu saboda fargabar kila sadiya ta jiyota, kuma gobe zata iya ba ta tabbas. Ya rungume ta dan kokarinsa na tsayar da hawayenta,yana ci gaba da karanta mata kalamai masu sanyi wadanda ko kadan ba su yi tasiri akanta badan hankalinta ba ya tare da shi,sai dai da yake Abdullahi jarumi ne mai hakuri neman so da juriya sai da ya jawo hankalinta ta ba shi nutsuwarta har ta dinga jin ranta bai rasa komai da zai iya mallakar soyayyar mace ba, idan aka dauke ta tunda ta riga ta sadakar da nata son ga soyayyar Alh. Sai ta yi masa bacci karya tsawon lokaci yana shafa kanta zuwa bayanta,har ta kata alamar jan numfashin dogon bacci, sannan ya rabu da ita ya tashi zaune musamman yana kallon fuskarta cikin kauna iri iri. Daga karshe ya daga hannun yana rokon Allah. "Ya ubangiji ka saukakawa wannan baiwa taka al'amuranta,ka yi mata gafara,ka bude zuciyarya ta karbi gaskiya ni ma ka bani juriya a lamuranta... Ka gafarta min tsawon kwanakin da zata juyo ta yi min kallon masoyinta... Ubangiji ka albarkace nu da zuri'a ta gari....." Wannan addu'o'I nasa suka dawo mata da hawayenta ba tare da ta yarda ta motsa ba dan kar ya san idonta biyu. tana kallon ya sauka gadon ya shige bandaki,ya fito da wankansa,karfe uku da rabi ya shimfida sallaya ya dubi gabas. Da ta damu da son ta yi kuka,kawai sai ta mike ita ma ta shighe bandakin tana wanka tana kuka har da karamar shesheka. 1 · Like · React · Report · May 16, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji .15) Ta rasa da ludayin da zata kamfato wannan rayuwar da ke neman zame mata dole,wato zama da abduk,zuciyarta ce ke son ta yarda tsakani da Allah abdul ke sonta, sannan ya cika mizanin soyayyar wadda ta isa abin kallo,bayab wannan me ya hadata da shakkarsa? Me ya hadata da shiga wani garari idan ya rabe ta? Ai ba a kansa ta fara auren ki ba, amma Alh bai taba dadata da kasa ba Bayan wadannan tambayoyin da zaciyarta ta kasa amsawa,akwai illolin da za su hana ta zaman auren Abdul ko da kuwa ta hadiye soyayyar Alh. Shekarunta talatin da biyu ke nan a duniya,tsawon wannan lokacin ba ta taba dandanar zakin so ba sai watannin da suka wuce wanda ta ke zargin tana kaunar Alh,duk da ranta na raya. Mata son nasa kawai zata tsira da shi a aurensa, tunda bai dace da muradan ta na mijin aure ba kamar yadda ta shekara goma da auren nasa,amma dai dai rana guda ba ta taba farin ciki da auren ba. To yau tsautsayi ya gamo ta da auren Abdullahi wanda ya girme mata da shekara daya kacal, sai dai ya iyawa dabi'arta kwarai! Ya mallaki kirki da kyautatawa wadda su ne makamashin samun soyayyar mace.kirkin aljihu na fatar baki na bautawa da gangar jiki na hakuri,na sadaukar da lokaci,na nuna damuwa a cikin damuwarta,Duk abdullahi ta yarda ya mallaka wadannan duk da bai mallaki makudai kudade ba,amma duk da wadannan ..... Shekarin nasa babba ne matukar a zuci,tunda gashi ya ajiye mata uku yana shirin kawo ta 4. Wannan shi ne matsalar tata, wadda abin mamaki sa ta fi kona ranta fiye da na katangar da yake shirin ginawa tsakaninta da Alh,da kuma yake shirin ginawa tsakaninta da Alh,da kuma na alfarmarta da ya keta a yau da kuma shakkat ita ce kuwa ta biye masa hankali kwance da hadin kan da sai ta rantse ba ta taba ba wa alh rabinsa ba? Tun tana kuka kamar ta hadiye zuciyarta har ta hadiye din ta koma hawaye,kuma ta bar tunane tunane da hasashe hasshen da suka cika zuciyarta. Ta yi wanka ta fito daure da towel tana ta faman ajiyar zuciya.Ta bude wardrobe ta dauki wasu kayan baccin ta zagaye Abdullahi yana sallah ta fice fala.ta saka kayan sannan ta nemi kujera ta zauna kawai ta zabga tagumi duk da ta yafewa tunani,amma hawaye fa na aikinsa har toshe baki ta ke kar kuka ya kubuce sadiya ta jiyo. Yana sallame raka'o'in da ta fita ta bar shi yana yi ya biyo bayanta,saboda ciwon da kukanta ke masa,me kama da saukar narkakkiyar dalma a gyambo. Tun da ya fito ta sanya masa ido irin kallo na rashin hayyaci,ya zauna kujerar da ke fuskantarta ya zuba mata ido shi ma, amma shi da nasa hayyacin,sai dai zuciyarsa a dame ta ke kwarai da tashin hankali. Ya san wannan tagumin ta yi shi ne kawai amma zuciyarta ba ta aiki bare ace tunani ta ke,ke nan yana bukatar dawo da ita doka da oda tukunna idan ma rarashi zai yi ya sami shiga. Ya koma ahannun kujerar da ta ke zaune ya dafa kafadarta,ya ce. . "Fatima kina son yanke kauna da rahamar ubangiji ko,ko kuma kina son karfi wajen cimma burikan ki?" Ta dago kai ta bi shi da kallo,sannan ta sauke numfashi ta shiga goge hawayenta wanda ta ke son tilastawa kanta tsayar da su,ko don kara su ci gaba da tafiya a banza,lokacin amfaninsu bai zo ba dan tana ji a jikinta in dai zata rayu da auren Abdul,to an budewa rayuwarta kuntataccen shafi. Ganin ya sami hankalinta,sai ya dora cikin hawaye. "Na yi nadamar abin da ya fari da mu yau ba tare da na nemi aminciwarki hakika ba,na yarda abin da na yi bai kamata ba, amma ina rokon afuwan in Allah ya so ba za ki kara kamani da laifi iron wannan ba..... Na miki wannan alkawarin dan ki san ba shi kadai ne makasudin aurena da ke ba,akwai fatan zamowarki uwar iyalan da zan yi alfahari da su manzon Allah(S A W) ya yi alfahari da mu gaba daya,kin ga ke nan kamata na fi nema daga gare ki ba. Gara na nemi amanincinki da yardarki na zamowa iyalina don ta wannan hanyar ne wadannan zasu saukaka gare mu.... Dan haka nake nadama,kuma ba zan fasa neman afuwanki ba fadina..... Idan ma ba ki gamsu ba zan iya janye jikina daga shigowa dakinki har sai kin yi min izin-,.... 3 · Like · React · Report · May 16, 2015 Maimuna Idrees Matawalle Tnx 1 · Like · React · Report · May 16, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 16) Sai a wannan lokacin ta kara dubansa tana hawaye ,ta ce. "Don Allah abdul ba ka ji a ranka ka zalunce ni ba......?" Ya yi saurin tare ta yana gyada kai. "Na ji.... Tabbas na ji!" Ta koma yi masa kallon zargi da tuhuma,ta ce. "Amma ka san da haka kake son ci gaba da rike ni cikin zalunci har kake kirarin mayar da ni kamar wadda aka rataye,kewa da gorin matanka ya kashe ni ko. "Zan yi hakan ne da zabinki, kuma idan har zai faranta miki rai ko da zai bakanta min". Ta fara gyada kai cikin sartun hawaye. "Idan haka ne kana son farin cikin na sallama ni kawai,shi ne kadai abin da zai faranta min rai.ina zargin kuma ba zaka kalubalamce ni da komai ba,ka dora min idda ko? Yanzu ina da damar da zan yi zaman halali da Alh?" Ya yi saratro yana kallonta,har ta fitar da rai zai ce wani abu,ta dora. "Abdul don me zaka yaudare ni? Idan ka san ba zaka yaudare ni? Idan ka san ba zaka iya aurena ka saki ba, don me ba ka sallame Alh da tayin aurena da ya yi maka ba? Ban taba tsarawa kaina miji irinka ba wallahi... Ni ban iya hayaniya ba ban iya bakat magana ba...kusan shekarunmu daya,kai babu haihuwa ni babu.... Da me zamu ji? Ta ina zamu yi tarbiyar da 'ya'yan da kake mafarki?... Ko ta ina ba mu dace da Abdul,ka dubi girman Allah ka sallame ni na tafi inda na fi wayo inda zan iya rayuwar da na saba.... Kar ka zama me son kai Abdul,Alh ya fi ka bukatata..... Ba shi da kowa bai san son kowa ba sai nawa". Ya yi saurin rufe mata bakinta da tafin hannunsa, ya ja ta ya rungume,tsawon lokaci sannan cikin rawar murya ya ce. "Ina da kishi fa fatima,ina hadiye iyakar abin da zan hadiye cikin yi miki kawaici akan Alh, saboda haka kar ki kara ambaton sunansa a gabana,kin ji? 1 · Like · React · Report · May 16, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 17) Ya yi saurin rufe bakinta da tafin hannuwansa, ya ja ta ya rungume,tsawon lokaci sannan cikin rawar murya ya ce. "Ina da kishi fa fatima,na hadiye iyakar abin da zan hadiye cikin yi miki kawaici akan Alh, saboda haka kar ki kara ambaton sunansa a gabana,kin ji?". Sai ta sami kanta da kasa tanak masa. Suka dauki lokaci a haka,sannan ya dagota yana kallon kwayar idonta. "Fatima,ki rabu da zaciya da sakokinta,sai ta saka miki dubu babu alkhairi a cikin daya, lura da ita duk abin da ta raya miki idan babu Allah a cikinsa ki watsar kawai,ki daina barin shaidan na wasa da zuciyarki,shi ne ya raya miki yanzu na dora miki idda kin halatta miki auren Alh? Kin jahilci hukuncin da ya haramta miki auren Alh fatima, manzon Allah (S A W) ya tsinewa mai halattawa da wanda aka alattawa,ko kin manta na san da wannan a tsakaninmu? Da na yi miki shiru sai ya kuma yi miki wasu sakokin. Ba ki iya hayaniya ba... Shekarunmu ba ki shirya auren mutum irinan....... Ashe mutumin da ba shi da wani garanti a rayuwarsa wadannan hujjojin sun ishe uzuri? Dama yadda ka tsara rayuwa kake samunta? Ina tsammanin ke za ki fi bayar da wannan shaidar dan tun kina budurwa kike shiryawa kanki mijin aure. Ga shi shekarunki sun fara nisawa amma ba ki cimma wannan burin ba, me ya hana?". Suka dauki shiru tana jin nauyin nasiharsa cikin ranta,ba ta ga laifinsa ba, amma ta fara tsanar kanta da kaicon yadda ta ke samun rayuwa. Ya lura tana son komawa kuka sai ya dora da cewa. "Ki dan buda min filin a zuciyarki kadan yawan shekarunmu daya wani abin kaye ne a cikin soyayyarmu har nake ji a raina kamar hakan na kara min gardin soyayyarki, wadanda ke sa hasashe kala kala masu yiwuwa da wadanda zasu yiwu ba.na ji raina da ace mutum na da ikon da rayuwarsa,tabbas da na jira wannan lokacin na fi koshi taf! A cikin soyayyarki,zan fi gamasar da ke irin son da nake miki, sannan ni ma zan fi gamsuwa da farin cikin kasancewa tare da ke ko yaushe. Duk da haka zan yi kokari na kwatanta rokona da ke kawai ki bire katangar debe kaunan a tsakaninmu,insh a'Allah sai mun wadata da 'ya'yan kanmu,sauran korafe korafen ki kuma mu kai wa Allah kuka sai ya magance". Yana diga aya ta zare jikinta ta mike ta shige daki har da murza mukulli.bai nemi takura mata ba sai ya bita da kallo kawai.ya jima yana kallon kofar dakin,sannan ya sauke kai ya kishingida cikin jinjina taurin kan fatima,wadda ko kadan ba ta jin rarrashi sai dai tana da saukin jayayya. Da asuba yana dawowa masallaci ya shiga kwankwasa mata kofa yana kiran sunanta a hankali. Dole ta tashi ta bude dan kar sadiya ta sami abun fada. Tana sanye da hijabi ta zauna bakin gado ba tare da ta yarda sun hada ido ba, ya janyo stool ya zauna a gabanta yana ta faman kallonta,sai can ya kira sunanta a hankali.ta daure ta dago kai ta kalle shi sai ta ga kwalla a idanunsa,sai kawai ta yi kasa da ido jiki a sanyaye. Ya kuma tausasa murya ya ce. "Don Allah ki yi hakuri". Ta sauke ajiyar zuciya kawai,ya kara raunana murya,ya ce. "Na fi ki damuwa fatima,don Allah ki yafe min..." Kawai sai ta sami kanta da kada masa kai idonta ya fara zubar da hawaye. Ta fara jan jiki zata tashi ya yi saurin ruko hannunta ya yi kokarin suka hada ido,ya girgiza mata kai. "Na gode,saura ki cirewa zuciyarki damuwa ki saukakawa kanki al'amura,ki karantawa kanki dogon buri da saka karfin wajen cimmasa. Duk wani abu da yake gaibu dan adam bai isa samar da shi ta hanyar karfi da dabara ba fatima balle ya tilasta mai hukuntawa ya hukunta,Allah ba a yi masa dole fatima,kuma ba a laynace masa aikin da aka bayyanar da wanda aka boye. Saboda haka nake shawarartarki zama cikin hankalinki,ki sami lokaci ki yi tunani mai kayu ki raba kanki da wannan kuncin,ki sake ki yi abin da aka halicce ki dominsa,wati bautar ubangiji. Sannan ki ware ki more ni'imar da ubangiji ya samar dominki,ki bude zuciyarki farin ciki ya shiga ki rayu cikin farin ciki da kowanduk abin da zaki so ki so shi dai dai misali.haka ma wanda za ki ki, domin manzon Allah (S A W) ya hore mu da rikar al'amura tsaka tsaki. Don haka ba zan taba matsa miki ki so ni ba, amma zan shawarceki cire kiyayya ta daga zuciyarki saboda har kasa ta rufe idona babu saki a tsakanina da ke, ki kawar da kai ga kallon ni ban cancanci kasancewa mijinki ba, saboda ba ni da kudi duk da na yarda neman dai daito a aure muhimmanci abu ne, amma aurenmu ba na shiri ba ne. Wayar kanmu kawai muka yi cikinsa, kuma da yake ba kutatacce ne ni ba sai na ga kamar zan iya kwatanta dawainiyarki,duk da ko na gaza ubangiji bai janye miki yi min biyayya da kayutata min ba a matsayin bautarsa. Dukiyar nan ta ki ba zata zama uzurinki ba, kuma ba zata cike miki wannan gibin ba... Kin fahimci ni? Ki kaddarawa ranki aure na wata jarrabar ubangiji ce irin ta rashin samun abin da rai ke so,ki yi hakuri mai kyau Allah sai ya ba ki tarin lada kin ji? HafsatZuciya d kwanji 18) Ya kurawa kwayar idonta ido, wadda ke zubar da hawaye, zuciyarsa ta kara rauni,ya ja ta jikinsa ya fara rarrashi. Rarrashi irin wanda babu macen da ke juyar da shi,ya rungume ta sannan ya share hawayenta da harshensa tare da sumbatarta. Tunda kwkwalwarta ba zata iya manyan ayyuka biyu a lokaci guda ba, sai ta saki hawayen ta karbi wannan rarrashin mai kunce lissafi tare da nzarin makin da ya kamata ta ba wa wannan gwarzon lakantar mace da abubuwan da ke dauke hankalinta. Kamar masu shirin komawa ruwa. Sai dai sun mallaki zuciyoyinsa, muradinsu kawai su gusar da tsatsa a zuciyar juna. Abdullahi na son nuna masa ta gamsu da rarrashinsa,suka bata lokaci kafin su hakura da juna,suka hada ido Abdullahi ya sakar mata wani murmushi sace zuciya,sai ta shanye shi ta kawar da kai fuskarta babu yabo babu fallasa, ta ja jikinta gado a kasalce tana jan bargo,ya saurin sa hannu yana taya ta, yana cewa. "Bacci ko? To dan runtsa sai ki yi wanka ki karya,ki kwanta ki huta sosai". Ya fara gyara dakin,sannan ya wuce falo.nan ma ya mayar da komai fes ya fesa freshner ya dure kicin,ranar har wanke wanke sai da ya yi,samar musu karin kumallo,kana ya shige wanka, bayan ya fito ya tayar da ita,ita ma ta shiga wanka. Suka karya kumallo tare kowa shiru idan ka. Dauke sakon murmushi kauna da yake dawainiyar jafa mata ita kuma ta hadiye ta maze har ya shirya ya fice bayan ya karanta mata kalaman kauna masu zaki. Ita kuma ta koma rudadden baccinta mai mamaye da Abdullahi da komai nasa,a numfashinta mafarkinta,hars henta,kunnuwanta da dukkan iskar da ta ke shaka,sun tura Alh wani dan sako mai kama da kurkuku suka zagaye shi da tausayi, wanda ke son kokawa da sabon lamarin Abdullahi wanda zata iya kiransa fin karfin Abdullahi kawai da iya kirkinsa. ************ ********** *********** Tun daga wannan ranar bakin fatima ya mutu, ta daina kirkirar laifi domin ta bakanta masa. Ta daina ja yana ja bare su yi tanki tanka, sai dai ta dauke masa walwalarta,ta rage kazarniya kamar da,sai ya yi kwana biyu bai ji muryarta ba, iyakaci ya yi kidansa ya yi rawarsa sai ta ga dama ta kada masa kai, ko ta girgiza. Shi da kansa ya dinga yabon da dan ta kan kula shi ko da fada ne su yi, ya sami damar shigar da kansa da fada ne su yi, ya sami damar shigar da kansa da fada mata abin da ke cikin zuciyarsa,ko da gwasalewa ne ta yi. Bayan wannan ta kara sakar masa dawainiyar gida,ya yi hidimar waje,ya yi ta cikin gidanta,dauki ajiye ba zata yi ba, kai wanke wanken kansa sai ta daina sai ya ga haza ya wanke, girki ma idan ba ta so ba sai ya yi abincin ta nuna bai mata ba,dole ya canja mata wani. Ga kuma su sadiya da tasu matsin lambar ta tutiyar shigarsa wajen fatima ranar girkinsu da dawainiyar da yake mata ta jiki da aljihu,duk da su kansu albarkacin kaza kadangare na samun damar shan ruwan kasko,amma da yake ba haka aka so ba, wai kanin miji ya fi miji kyau,sai hidimarsa ba ta burge su komai ma ya yi sai a gwasale,ban da kanana maganganu suka dinga yi masa yajin tsakar gida da na daki, ke nan duk inda ya dafa babu dadi. Amma da yake soyayyarsa na kan sharafinta take tare da fatima sai ya zabi soyayarta da kyautata mata kawai ko da ba zata mayar masa raddi ba, shi babban tashin hankalinsa ma bai fice na lafiyar da ta yi mata karanci ba tsawon watan ni biyu ke nan, yau zazzabi,gobe ciwon kai,jibi na ciki, kullum matsaloli sababbi. Ya yi kuma juyin duniya ya kai ta asibiti ta nuna masa ta yanke gita har ranar mutuwarta. Ya san duk cikin muntukus din da ta ke masa ne wato ta kashe kanta ta bar masa duniyar. Ko yanzu zai iya dorar da auren kyakkyawar mace da dawainiyarta wadda ta bambanta da sauran mata,sai dai bai debe kauna ba. Yana saka ran akwai nasara da zai girbi ribar abin da ya shuka. Wata rana ya tashi da zazzabi,hindatu na ta fama da dawainiyarsa kasancewar a dakinta yake, amma shi hankalinsa na kan mai ciyar masa da fatima da yi mata sauran hidimominta. Bayan ya karya da kyar ya sha magani ya dan kwanta yana cike da fatan idan ya farka ya dan ji ya ware ya je ya yi hidimar fatima,amma fatansa bai ci ba sai ma abin da ya karu. Cikin wannan magagin ya samo shawara inda ya umarci hindatu kira masa malam a wayarsa. Wayar na shiga ta mika masa, bayan sun gaisa malam ya yi masa jaje saboda ya ji canji a muryarsa,Abdullahi ya ce. "Malam don Allah ka taimaka min ka ba mu aron maryam ta karasa mana hutun a nan, dan ta dinga taimakon fatima da 'yan ayyukan gida saboda ita ma ba ta da lafiya,yanzu ma muka dawo asibiti gaba daya. Malam ya ce da shi. "Assha! Me ya same ta ita kuma?" Sai da abdullahi ya ja fasali sannan ya shara karya. "Faduwa ta yi a abndaki ta buge kafada". Malam ya jajanta sannan ya ce". "Babu komai,ka yiwa maryam din waya ka ce ta taho in ji ni, dan ba na gida a halin yanzu,kuma sai dare zan koma". Abdullahi ya yi godiya,suka yi sallama ya yi fuska ya kira maryam ya ce mata. "Kin ga maryan kome kike yanzu ki ajiye ki hado kayanki ki taho nan, na tambaye malam ya ce na sanar miki,ki zo yanzu don Allah akwai wata kafa da nake so ki toshe min" Bai jira cewarta ba ya kashe wayar yana jan bargo dan ba ya son irin kallon da hindatu ke masa. Ta gaji da kallonsa dole ta soke kishi da bacin rai ta basar,ko awa daya maryam ba ta hada ba ta karaso,yana jiyo sallamarta da surutanta da su ya tashi zaune yana Allah Allah ta shigo dan karya fita ya cika azarbabi. Can ya ji shigowarta falonsa tare da su hindatu,ya lallaba ya fito falon,ya yi fuska ya zauna dan yasan tsegumi da neman rigima ya kawo su sadiya,a dai sami abin da za a yi masa korafi. Maryam na gaishe shi tare da yi masa sannu, shi kuma idonsa akan jakarta da ta janyo,ya ce. "Ki sauka wajen fatima,ba ta cika jin dadi ba ne. Ga shi nima haka sai ki dinga taimakonta da wasu abubuwan,ina tsammamnin yau ko karyawa ba ta yi ba. Tashi ki je". Da kuzarinta ta mike tana bayyana jimami. "Allah ya sauwake,bari na karasa". Ya koma ya kishingida yana fadin. 1 · Like · React · Report · May 16, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji .19) "Na gode maryam". Ya yi murmushi,maryam na fita sadiya ta hau rafta salati da innalillahi,ya yi kamar bai san tana yi ba. Hindatu ta muskuta ta ce. "To wai me ya hana ba ka zube mata barori ba?" Ya yi shiru kamar ba zai tanka ba, sai kuma ya tanka din. "Saboda ba bakuwar mallakar barorin ba ce, zai fi armashi idan ni na zama baranta". Sadiya zata yi magana Hindatu ta yi saurin tare ta dan san zata hargitsa musu gayyar,ta ce. "Kuma kamar babu riba". Ya amsa ba tare da nuna damuwa ba. "Ke ce kike ganin haka,tunda ba ke ya shafa ba. Amma dai kin san idan babu kwadayi babu dalilin da zai sa a lashi wuta? To ki ji a ranki kokari ke bude kofar da ke kulle". Kufulalliya sadiya ta kasa hadiyewa. "Babu wata riba wallahi, ita ta zo bauta amma ita ake bautawa,to wai ita ta biya sadakin ne ko kai?" Ita ma tana rufe baki ya amsa mata. "Akwai riba mana tunda ba dan ta yi wahalhulun gida na aure ta ba. Abin da na aureta dominsa na samu, don haka babu ruwana da biyan sadakinta. Bautar da nake mata idan akwai lada Allah ya ba ni....." "Idan kuma babu fa?" Inji Hindatu tana kallonsa,ya ce. "Allah ya sa ya zama kaffara". Sadiya ta kara kufula, ta gyara zama ta ce "Abu Turab kana zunguro maganganu fa. Dazu haka ka ce wai ita bakuwar barori ba ce,to mu ne bakin barorin ke nan? Ko ba tasan kai talaka ba ne ta aure ka? Ta sani akwai dawainiya a gidan talaka,kuma tunda ba ita kadai ba ce a cikinsa ta sani tsab dole ta zage damtse ta yi abin da sauran 'ya'yan talakawa suke yi. Kai ma kuma tilas ka dai daita mu tunda alfaharin mace shi ne gidan mijinta ba na iyayenta ba". Ya kara yin fuska. "Idan ta san ni talaka ne ta aura,ina tsammanin na fi ta sanin ba ni da wadatar da zan samar mata jin dadin da ta saba da shi. Idan kuwa babu maganar shiga hakki,na gamsar da kaina hikimata ta zabar bauta mata da karfi KWANJI dan samar da zaman lafiya a tsakaninmu,kuma kar ta tsane ni saboda neman ta rasa,sai dai kawai idan akwai wadda ta haife ni a cikinku,sai kawai ta ladabtar da ni". Sadiya ta mike saboda kai wa bango tana cewa. "Kan na ka kawai ka gamsar,ita dai ihu bayan hari kake a wajenta. Ga shi nan tana son kai ka kabari da bakin ciki,dan ma ba ka da da balle jika,bare ta mayar da shi maraya karfi da yaji. Tana hanyar ficewa yana ba ta raddi. "Da bakin ciki na ajali ai da fatima ba ta tarar da ragowar ruhina ba,naki da tuni ya mayar da ni gawa". Babu yadda ta iya dole ta fice din, sai Hindatu ta bari da 'yan kame kame. "Allah Abu Turab ka mayar da hankalinka. Ba a taka ruwa a daki ruwa. Matsayin sadiya da fatima daya a wajenka,bai kamata ka dinga daga hakarkari a kanta haka ba.... Ga shi kana ta faman numfashi". Ya saki dogon tsaki, ya ce. "Kun damu da lalurar tawa ne hindatu? Hassadarku ta fi ni kima a idonku,saboda haka duk wadda ta ce kulle zan ce cas! In yaso daga yanzu ta yanke ciyar da ni tunda ita ta auro ni,ke kun fara fitina ta wallahi,kullum magana daya ake yi ta yagwangwanata,kun hana kanku sukuni kun hana ni.... Kun koya min masifa,kun koya mata...... Ita ma Hindatu da ta ga abin ba sauki,sai kawai ta bar masa dakin. ****** ****** ****** ******** Duk da a bakin maryam fatima ta ji labarin zazzabin Abdullahi ta yi dabarar hadiye rashin saninta,sai dai dauko mata maryam din da ya yi, ya yi wani tasiri a zuciyarta, har ta ji wani dan

Chapter 3 of 8