Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 8
masa ido, lokaci daya ta rame kamar wadda ta shekara a kwance. A haka ya share mintuna ashirin ko kwakkwaran motsi ba ya so ya yi don kar ya katse mata bacci,har sai da Hindatu ta fado masa a rai, sannan ya lalubo wayarsa a hankali ya kirata. "Ki yi hakuri Hindatu,mun ciki wata matsala ne,kar ki ji ni shiru". Duk da zuciyarta a jagule ta ke,sai ta daure ta ce. "Babu komai,ina fatan ba jikin ba ne?" Ya ce,"shi ne wallahi". Cikin bayyana damuwa ta ce. "Ayya! Allah ya kawo sauki,ko ni zo akwai abin da zan iya taimakawa? Da sauri ya ce da ita. "Yauwa da na gode miki kuwa". Ta sauke waya da sauri ta zura takalmi ta nufi dakin fatima. Ita kanta hindatu kallo daya ta yiwa fatima ta san lallai tana jin jiki,cikin bayyana damuwa ta ce. 3 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 34 "Subhanallahi,me yake damunta haka?" Ya dan muskuta a hankali yana gyara mata kwanciyar don ya ji dadin zama,ya ce. "Daga zazzabi ya koma ciwon ciki,da kin ganta a dazu sai kin mata hawaye..." Hindatu ta ce masa. "Gaskiya dubi yadda lokaci daya ta rame, wannan ai sai ku tafi asibiti,da me zan taimaka maka? Ya ce,"da ruwan zafi a fulas,wanda zata sha tea sai ki dan gyara mata kicin ki wanke mata kwanuka.idan har kin gama ba ta farka ba,sai ki zo ki dan hada mata ruwan wanka sai na tashe ta". Hindatu har zuciyarta ta ce. "To,babu laifi". Da sauri kuma ta fice kicin din tan aikin da aka sa ta, har ta gama ta je ta hada mata ruwan wanka, sannan ta sanar masa tare da cewa. "Yanzu haka ba ta yi baccin dare ba shi yasa yanzu ta ke fanshewa". Ya ce,"ni ma na yi tunanin haka". Ta ce,"yanzu haka zaka tashe ta? Ya amsa mata da cewa. "Ai ya zama dole, gara ta tashi ta sha magani". Ya sunkuya ya fara hura mata kunne,ta motsa a hankali tare da salati tana dafe ciki,ya dago ta a hankali suna yi mata sannu shi da hindatu,muryar hindatu ta sa ta bude ido da sauri tana binta da kallo,ta sauke ido akansa da tambayoyi a ido iri iri,da ya kasa amsa mata sai ta ja jiki a hankali ta janyo filo ta kwanta.ya suke kafafunsa yana cewa. "Ki tashi ki yi wanka,ki samu ki karya ki sha magani". Ta girgiza kai a sanyaye ta ce. "Ba zan iya ba..."$ "sai na taya ki". Ta tari numfashinta da fatar hakan,amma sai ta yi mursisi ta kara jan bargo tana cewa. "Abdul bar wankan nan don Allah". Cikin tausayawa ya ce. "An bar shi, sai ki wanke baki ki dan kurba tea don ki samu ki sha magani". Ba ta tsinka ba, ya tashi ya kawo mata tasa da brush ya taimake ta ta tashi,hindatu ta dago tasan ta zuba mata ruwa a brush din ta mika mata, tana mata sannu shi kuma ya tsaya hada mata tes din. Da kansa ya dinga ba ta da cokali tana sha tana faman rike ciki,saboda karta da yake mata har ma shan ya gagare ta, dole ta koma ta kwanta tana juyi. Babu shiri Abdullahi ya fice waje ya kira likita a wayarsa cikin tashin hankali ya ce. "Dr akwai matsala fa, ciwon ciki ya matsa mata matuka... Yakamata ka zo ka taimaka ko kuma mu zo." Dr ya tausaya,sannan ya ce. "Hakan zata iya faruwa,a cikin magungunan da na ba ta har da na wannan matsalar me yiwuwa ba ta yi amfani da su ba ne, ka bincike su,amma idan ya ki tsayawa nan da yamma sai ku zo". Ya yiwa dr godiya sannan ya koma dakin da sauri. Ya ce mata. "Ina magungunan?" Da kyar ta amsa masa. "Suna falo" Ya fita da sauri,hindatu kuma ta bude karamin firij din da ke kusa da ita ta dauko ruwa,tun ma kafin ya karsaso ta zuba a tambulan tana jiransa,suka bata ta sha ta yi mata sannu,can ciwo ya dawo sabo,hankalinsu gaba daya sai da ya tashi. Haka suka yi ta fama,abdullahi na faman yi mata add'a a cikin,hindatu ma na tata a cikin zuma har Allah ya kawo sauki bacci mai nauyi ya dauke ta. Wunin ranar nan kusan a haka ta yi,don haka ko aiki abdullahi bai leka ba, hasalima masallaci kawai kan fitar da shi. Hindatu kuma tsurku biyu ya hade mata,ga na tabatar kallon fatima da ciki,ga na lissafin kwatancin matowar da Abdullahi ya yi akan fatima wadda sam ba ta damu da shi ba.tunda hindatu ta ke da Abdullahi ba ta taba ganin hawayensa ba, amma a yau inda tana da bukatar tarar hawayen ko gwanhwanin madara ne sai ta samu, wannan abu yana matukar daure mata kai, sai dai wannan bai hana ta hadiye kishinta ba,suka dinga hidimar fatima tare har dare,bayan iska lokacin da ciwon ya jima bai motsa ba. Wannan kokarin nata da kyautatawar ne ya sanya Abdullahi jarumtar barin fatima hannun Allah,lokacin da dare ya yi, don dai kar ya cika shiga hakkin ita Hindatu,ya yiwa fatima bankwana tare da bar mata daya wayarsa da zummar ko wani abu zai faru sai ta kira shi. Yana dab da ficewa daga dakin ya ce mata. Biyewa shaidan idan ya zuga ki kiran Alh da wayar don wannan laifin yana daga cikin wanda ba zan iya yafe miki ba,zan ma dinga kaiwa ubangiji na kararki". Ta dago cikin matukar kasalar jiki da ta zuciya tana ture wayar gefe,ciki murya mara dadi ta ce. "Zo ka dauki wayarka". Ya bata rai, ya ce. "Ai ba don halinki na baki ba, in don halinki ne ma fadima kallonki na yi? Ko da yake ban sani ba ko a haduwar da kuka yi jiya ya ba ki wata wayar". Kai tsaye ya fice ba tare da ya jira cewarta ba sai ya barta da kwalla da son fadawa cikin tunanin barkatai,mafi ciwo a wajena, shi ne uzurin da ya yi zuwa ga hindatu alhalin tana bukatar kulawa.ga shi ma'abocin iya jinya wanda ba ta taba riskar irinsa a rayuwar ta ba, sai ta ke ji a ranta kamar idan yana tare da ita ciwon zai fi saukaka mata.ta rasa daga inda wannan kishi nata ke bullowa. Yana shiga ya sami hindatu ta fito wanka da walwalarta,ta tambaye shi. "Ta yi bacci?" Ya girgiza kai, ya ce. Har yanzu idonta biyu". Ta ce,"ina fatan ciwon bai kuma tashi ba? Ya amsa,"haka ne". Ta dan ja fasali kafin ta dora wata tambayar, zuciyarya cike da fargaba. "Abu Turaba anya ba ciki ne da fatima ba?" Dabararsa ta fara kokawar tsaida lugunden kirjinsa, ya yi matukar juriya kafin ya yi fuska ya amsa. "Wallahi ba ta taba yi min wannan maganar ba, me yasa kika fadi haka? Cike da mamaki ta kada kai. "Ba hasashe nake na Abu Turab,ina shakkar in fatima ba ta da ciki wata kila salon alakar da ke tsakaninku ne ya hanata sanar maka kunna na yi mamakin da kai ba ka ganshi da idonka ba,ga shi nan ya fito?" Ta kwaso masa rantsuwa,yana dariya ya dakatar da ita. "Ki daina saurin rantsuwa,gara ki bari a tabbatar don haka ina barar sirri,ki kulle bakinki a kan wannan maganar,kar ki sake na ji ta a bakin wani". Ta dan yi kasake,sannan ta ce. "Kana daukaka dai wata magulmaciya ko?" Ya yi saurin girgaza kai yana dubanta kai tsaye ya ce. "A'a na san ki dai da dan banzan surutu, kin san kuma an ce shi zance ado ne, amma kawaici kubuta ne" Sai da ta ja fasali sannan ta dube shi da kyau,ta ce, "Wannan kasheda kasheda suke tabbatar min fatima na da ciki,kuma kasan da shi ko in ce kun san da shi, ban san don me kake son ka boye min ba. Ya jima yana kallonta kafin ya sami abin ce mata. "In rantse miki ba mu taba maganar cikin da fatima ba ki kasa gaskata ni? Ni ma ban san me yasa kike son ki fitine ni akan wannan maganar ba". Ta dinga girgiza kai fuskarya na canjawa,muryarta a sarke ta ce. "Ba laifi ba ne don na nemi in san cewa dama in da sadiya ne ba ma haihuwa ke nan? Ya dinga dubanta cike da mamaki,sannan cikin tara gira ya ce. "Kin saka wannan hasashen naki a magwajin hankali da ilimi kuwa? Ina tantamar haka ban sani ba ko idonki ne ya rufe. To amma ba zan hana ki hasasshenki akan batun don jin wannan maganar a wajen ko cikin gidan ta bakinki na tabbatar miki,ita zata sa na warware amincin da ke tsakanina da ke. Sai kawai ta zura masa ido.bai jira cewarta ba, ya kada kai ya wuce bandaki ya barta da hidimar binsa da kalloZuciya d kwanji 35 ****************************** *********** Kafin ya fita sallar asuba,sai da ya shiga dakin fatima don tabbatar da lafiyarta.sai ya same ta tana bacci mai nun koshi lafiya,ya jima yana kallonta sannan ya farkar da ita. "Ya ya jikin?" Ya tambaye ta bayan ta farka,ta sa masa ido kawai, mamaki da shakkarsa ta ke, ya bude KWANJI da kyau yana kulawa da ita, amma fuskarta ba ta fasa nuna yana fushi da ita ko da yake zargin da yake mata adalcinsa ne ma kawai ke sa shi kular da ita.wai wajen Alh ta je, ita da kanta tana ganin abin tir a zargin duk kuwa da wani bangaren zuciyarta na ganin tsabar iya mulkinsa ke son nuna mata fin karfi wajen rabata da Alh,ba tare da yana da wannan damar ba. Cikin sanyin muryar wanda ya ji jiki a cuta ta ce. "Alhamdulillah". Ya ci gaba da binta da kallo,fuskarsa babu walwala. "Ciwon cikin ya kuma tashi?" Ta girgiza kai kawai.ya kara dubanta a kaikaice cikin tare gira,ya ce. "Amma ina ganin har yanzu akwai matsala daga shi nan a kumbure". Cikin dar dar ta kara jan bargo tana rufe jikinta,sannan ta juya masa baya, shi ma ya fara ja da baya yana hadiye dariyarsa,ya ce. "A'a ki tashi ki yi sallah,in dai bai sace ba nan da gobe dole mu je asibiti,ban san abin da ya baki kika ci ba yake neman kashe min ke,an gama da ciwo ga kumburi,kuma a haka kike masa kallon masoyi..." Ko motsi ba ta yi ba bare alamar zata tanka, don ta dan fahimce shi,idan yana cikin fushi ba ya son yana magana ana mayarwa.tana jinsa har ya gama zungure zungure rigimarsa ya fice. Bai kara waiwayarta ba, sai tara saura ya shigo mata da take away,ya fara da hada mata ruwan wanka,babu walwala tare da shi ya yi mata umarnin ta je ta yi, kafin ta fito ya gyara dakunan tsab ya baza musu kamshi. Ta fito ta same shi yana dube sube a wayar da ya bar mata,fuskar nan tasa a murtuke! Ta dinga satar kallonsa har ta kai ga tankawa cikin dar dar din kirji. "Ko tabawa ban yi ba". Bai ko juyo ya dube ta ba bare ya tanka,ya zura abarsa a aljuhu kawai,sannan ya janyo mata stool ya ajiye gaban mirrow har da bude mata mayukan da ya fahimci ta fi mu'amula da su,sannan ya koma gado ya zauna ya jingina da allonsa sai ta share mirrow din ta nufi can karshen gadon ta zauna ta juya masa baya.ya dan bita da kallo.amma sai ya ki tankawa ya tashi ya kwashi mayukan da karamin kurar kayan kwalliyarta ya ja ya kai gabanta har da kai mata foot stool,sannan ya koma mazauninsa ya kuma zama. Ya dinga komai cikin kasala saboda ciwon jiki da damuwa a rai,idanunsa a kanta tunda ba ta kallonsa,tausayinta na damursa a rai, yana jin ba don yana son nuna mata kurenta ba man ma sai kawai ya shafa mata. Yana ta duban agogo saboda lokacinsa da ke tafiya,amma haka ya hakura ya share ta har ta gama lakakinta.ya fito mata da kayan sawa sannan ya mayar da kayan kwalliyar,ta shirya ta kon sofa ta kishingida, ya fita ya kawo mata abincin,ya zauna kusa da ita da magungunanta a gabansa da ruwa da tambulan a hannunsa. Ta fara karyawa cikin kwalla,gaba daya rayuwar ta yi mata zafi,ta rasa gane wannan masifa in dai Abdullahi na mata fushi sai ta rasa inda zata soma ranta gaba daya sai ta ji kuncin duniyar nan ya ishe ta. Abin takaici ma abin da yake zarginta da shi ba ta aikata ba, kuma abin da ta aikata din ba ta yi nasara ba don ta hakkake likita yaudararta kawai ya yi bai zubar da cikin nan ba. To ina mafita ke nan? Sai ta zabi farawa da maganin wannan fushin nasa da ke kuntata mata Zuciya ba tare da yakamata ya kuntata mata din ba. Bayan ya ba ta magungunan ta sha tana mika masa tambulan din bakinta na rawa,ta ce. "Abdul wallahi shekaran jiya ba wajen Alh na je ba. Ya kwashi sakkani masu dama kafin ya tanka a takaice. "Ina kika je? Ta dan yi wura wura tana neman inda zata ce kamar ta ce kasuwa sai ta tuna kishinsa,ta ce, gidansu ya kira ya tambaye su. Kawu sai ta sami kanta da kada kai kawai ta ce. "Asibiti na je". Ya bita da kallo,ya ce. "Kika yi me?" Sai ta ji tamabayar kamar ta gayya ko ta sanin abin da ta je yi asibiti,don haka ta kasa amsawa. Ya kara dubanta da kyau,ya ce. "Idan ba ki ba ni amsa ba zan dauka akwai wata 'yar burum burum da kike min, in baki sani ba ki sani ina zargin akwai dana ko'ya ta a cikinki, in dai asibiti kika je to ina zargin kin sonm salwantar min da ciki,wanda shi ne abu na karshe da zaki yi min ki cuce ni,shi ne kuma zai iya sa ni jarumtar runtse ido na yi miki rashin mutuncin da zan yi shakkar yiwa wanda na fi ki a filin duniyar nan, a matsayinki na wadda na fi kauna a cikinta. Sai dai kar ki yi zaton rashin mutummcin shi ne saki, har in mutu ba zan sake ki ba, sai dai ke ma ba zaki ji dadin zama da ni ba Fatima. Ta runtse ido sannan ta bude su da ballowar hawaye.tana cikin tsaka mai wuya ke nan, in cikin ya zube ko bai zube ba, duk babu sauki! Ashe Abdul ya rankota! In ta zubar da cikinsa ta shiga aukubar fushinsa tunda ya ce babu saki,in kuma ta zauna da cikin nasa kila har abada Alh ya tsere mata. Ta fara dauke kwallarta sannan ta dube shi, ta ce. "Ni bani da wani ciki abdul,har yaushe na sanka da zan yi ciki da kai... Don Allah ka saurara min ni bana son tashin hankali,in dai fita ce ba zan kuma fita ba har ranar mutuwar tawa kamar yadda ka zaba min.... ,shi ke nan? Sai dai ba zan kasa tun mata cutar da ka yi min ta zama da ni ba tare da so rai na ba". Ta kare da kuka,amma sai ya hadiye tausayin nata da kaunar tata da ke bijiro masa ya kawar da kai,ya ce. "Ni yanzu ta cikina da ke gare ki nake yi ba maganar fit da zaman gida ba. Fita dai ba kin riga kin yi ba,kin kuma ki sanar da ni inda kika je da abin da kika je yi, kin fita cikina yana cikin koshin lafiya,kin dawo min da shi a wahale kina neman jaza min mummumnar asarar da ban taba irinta ba, don tsbar son Zuciya irin naku. Na rantse miki da Allahj fatima idan wani abu ya samu cikina sai na wulakanta ki, kuma si na hada danginki na sanar da su abin da kika yi min..." Ta tare shi cikin masifa. "Malam wai a ruwa zan sha cikin ne? Na fada maka ba ni da shi...." Shi ma ya taso mata da fada. "Ta ya ya zan gaskata bakinki da ya saba karya? Zan gamsu kawai idan na dauke ki na kai asibiti aka tabbar min.... Kar ki dauke ni wani soko kin ji! Ina sa wa abin da nake so ido fiye da yadda kike tsammanin,duk wani motsinki a idona yake fatima.... Saboda haka ki shiga hankalinki". Ya mike ya kwashe kayan gabanta ransa a bace ya fice yana ji tana rusar kuka. Ina mafita? Sai ta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai, hakika tana cikin tashin hankali,Allah ya jarrabe ta,haka ta yi kukanta ya ishe ta,har ta share hawayenta ta goge fuska lokacin da ta jiyo sallamar hindatu.ta gyara fuskar ta mike ta fito falon. Da walwala a fuskarta ta yi mata tayin zama suka gaisa ta yi mata sannu da jiki,suka dan taba hira game da ciwon fatima,ta yi mata godiyar dawiniya har suka shihga wasu hirarakin. Karfe sha daya dai dai sai ga laila ta same su tare da hindatu,suka gaisa sannan ta yi musu sallam ta fice. "Wannan 'yar makota ce?" Fatima ta yi dariya ta ce, "Matar mai gidan nan ce". Laila ta zabgawa kofa harara,sannan ta karasa ragowar akan fatima cikin kaushin murya ta ce. "Kin bayar da mata wallahi. "Da mugun sauki tunda ba maza na bayar ba ... Fiye mayar da allura garmawallahi ba .. Gane wata matsalar danne wata ta ke..." Laila ta gyara zama ta ce. "Wani abu ya faru ne? Nan fatuma ta kwashe mata dukkan labari tun daga ranar da suka dawo har zuwa jiya da yau cikin bayyana takaici da damuwa tare da nuna kaka ni kayi,amma tana saka aya sai laila ta saki tsaki ta dora da cewa. "Ni fada miki tuni akwai sakacin wajen cin kashin da mutumin nan ke miki.... Shi din banza da zaki bar shi ya nemi gadar miki da hawan jini..... Don tsabar wulakantar da kai har da wani fada masa ba wajen Alh kika je ba.... Ba kya barinsa ya tafi a haka in ya ji haushi ba sai ya sake ki ba, idan ni ce ma ba sai na ce masa cikin ma na Alh ba ne tunda dama shi bakarare ne. 2 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 2 36 A sanyaye fatima ta dakatar da ita da hannu amma ta kasa cewa kopmai laila tabude jakarta ta fito mata da wayarta black berry bold 2 sabuwa tana cewa. "Sai ki tashi ki shirya mu komawa likitan ga waya inji Alh,akwai layin Glo a ciki " Abdullahi ya alkwartawa kansa duk runtsin aiki sai ya rinka saurara masa ya waiwayi gidansa,don dora ido akan fatima.kuma daga yau ya fara laila ba ta jima da shigowa ba ya shigo gidan.da hindatu ta nemi ba'asi sai ya ce mata takardu ya manta,cikin dabara ya ce mata. "Fatima ta fito ne?" Ba tare da ba wa maganarsa muhimmanci ba ta ce. "A'a Ya kuma dubanta a nutse ya ce. "Amma dai baki ta yi ko?" Ta gyada masa kai,ta ce. "Eh,ta yi bakuwa kam na ganta lokacin da na je dubo ta". Cikin bugun zuciya ya ce. "Ko laila ce? Ta kada kai,ta ce. "Ita ce". Ya tilasatawa kansa jarumtar hadiye rikitarsa gaban hindatu ya wuce yana cewa. "Ah bari na ganta". Ya yi sallama falon,amma a ciki tsoro da razana suka bayyana karara a fuskar fatima me rike da waya a hannu,wayar da gaba daya hankali da idanuwan Abdullahi ke kanta.... Sai laila ta saki baki tana kallon fatima wadda kamar a ce kyat! Ta zura a guke, sannan ta juya ta kalli Abdullahi wanda ya dogare a bayan kujera fuskarsa babu annuri sam! Cikin sakanin ta yi nazarinda,kamka ntar jikinsa bai kamata ace yana da kwarjini ba, amma ita kanta ya cika mata ido sai ta ji gaba daya ya rude.ta fara gaishe shi a rikice shi kuma ya amsa idonsa akan fatima,ta yi saurin kawar da kai tana hadiye rikitarta. Ya yi kokarin kyautata muryarsa,cikin tsare gira ya ce. "Fatima wannan wayar fa? Ta dubi wayar ta dube shi, bakin ta ya hau rawa,ta kasa kuma fitar da sauti. Ya kara murtuke fuska.lokacin da ya karasa gabanta ya mika mata hannu. "Bani". Bakinrta ya hau rawa ta mike ta boye wayar a baya tana cewa... "Ya ya za a yi na baka... Ni ba tawa ba ce..... Ka ga mai ita". Ya gyara murya,ya ce. "Ai na sani ko laifi ne don kin bani na gani....? Ta yi katfin halin amswa. "Ni ma ba laifi ba ne don na hana ka..." Ya tari numfshinta cikin bacin rai. "Ban fadi haka don ina gudun na yi miki laifi ba, musamman da yake zan iya murde hannunki na kwata... Saboda haka tun ina mutuntaki ki ba ni...." Bai ma jira cewar tata ba ya kamo ta ya murde ya kwace wayar ya zaro ta daga kwali. Ya tarwatsata a bango ya kuma binta ya karasa sannan ya juyo gare su da ko wacce ta shiga taitayinta, ya dubi fatima da kyau.ya ce. "Wace ce wannan,me ya matsayinta a rayuwarki?" Ta yi fuska ta kawar da kai babu alamar zata tanka, sai ya rabu da ita ya fuskanci laila ya ce mata. "Bisa wace hujjar kika kawo mata wannan wayar? Duk firsarar laila sai ta kasa motsi,shi kuma ya ci gaba da yi mata kallonm uku ahu,sannan ya ce. "Ke ce wakilyar babban shaidan da karami ko? Ga shi kuma tuni na yiwa gida nan katangar karfe da shaidanu. Saboda haka duk makircin da kika kullo da abinki za ki koma,kin ga..." Ya nuna mata kofa. "Fita ki bar min gida,kar na kara ganin muguwar kafarki a cikinsa,idan ba haka ba sai na yaga miki dam mutumcin mutuntakar da ya dam fare miki... Annamimiya kawai. Fatima ta sha gabansa cikin yanayin tashin hankali ta ce. "Abdul wane irin cin fuska ne wanmnan...." Ya zabga mata harara yana nuna laila ya ce. "Wannan har tana da fuskar da zan ci? Kin san Allah ba don wulakanta wulakantacce wani nau'I ne na wulakanta kai ba yau sai na wulakanta wannan matar.ban taba gaini wani tsanannen mutum sama da ita ba, sabnoda haka inda tana da fuskar da zan ci sai na cinye tas na hutar da 'yan baya. Don haka ke na ki saurare ni da kyau! Duk ranar da na kuma ganinta a gidan nan taki fusakar zan ci tunda ita ba ta da wadda zan ci... Malama tashi ki bar min gida na ce?" Ya kare da tsawr da ta cika gidan. Laila ta mike cike da mugun takaici,dakin na juyawa da ita saboda bakin ciki,fatima ta rakota cikin kuka tana kallon Abdullahi. "Ba zata fita ba,sai dai in ka kore mu tare..." Ya saki wani uban tsaki,ya ce. "Ita na kora,kuma in zaki bita ai ba daure ki na yi ba, iyakaci in kin bita ki ga nawa KWANJIN.... Ba a haifi shashashar matar da zata kawo min wauta ba..." Laila ta fizge hannunta ta yi gaba tana numfashi ita kuma fatima ta kara kuka,ta ce. "Ni ce shashasha abdul?" Ya share ta ya ci gaba da bin laila da maganganu. "Idan kin je sai ki fadawa shaidanin naki yadda na yi da ke,ki kuma tabbatar masa zai iya nasarar raba fatima da gidan nan matukar ya taba ganin wanda ya mutu ya farko,ki fada masa kuma kurarin da ya yi min jiya sun bi rariya tunda ni ba rago ne kamarsa ba..." Laila dai ko juyowa ba ta yi ba ta fice a salube,inda shi kuma ya sauke ganinsa ga fatima,ya yi tsaki ya ce. "To wace ce ke din in ba shashah ba? Ko yawan shekarunki suna miki amfani? A shashashancin ma ke ba ki shiga layin wadanda suka tara suna ba,idan kuma kina da abin yi sai ki yi.... Mts...! Aikin wofi kawai.." Yana huci ya sa kai ya fice daga falon,ai sai kawai fatima ta yi mutuwar tsaye a wajen,kuka ma ya gagara. 1 · Like · React · Report · May 17, 2015 Amierah S-Man Zuciya d kwanji 2 37Wuni ta yi tana tanadin tashin hankalin da zata yi da shi, wanda zai sa shi sakinta ko da ya fi gyatumarsa kokari,amma ina! Sai tanadinta ya tashi a banza, don har ta kwanta bacci bai leko inda ta ke ba duk kuwa da cewa girkinta ne. Da safe ma tana jinsa ya fice ya bar gidan har rana ta take, yamma ta yi ba ta sanya shi a idonta ba,ya dawo amma kamar yiya bai leko ta ba. Daga nan ne fa hankalinta ya bar kan tanadin bala'inta ta koma na takaicin da neman mafitar yadda zata kukuta daga wannan tozarcin me matukar taba rai da ya kwaso mata a lokacin da ta ke cikin tsaka mai wuya na bukatarsa kusa da ita,ko kuma sallamarta ta bar masa gida tunda ya tare tubalin da ya rike ta a gidansa,wato kirkinsa. Ta yi kuka ta yi abin da ya fi,amma ba ta da mai rarrashi,ita kuma zuciyarta ba a nutse ta ke ba bare ta nemo mata mafita sai ma kirkiro mata wasu sababbin koma bayan ta ke, wato kamar na janyo mata gorin sadiya. Har ta saka kayan bacci ta kwanta karfe goma da rabi,ta mike cikin fushi da zafin rai da zura hujabi ta saka takalmi ta fita zuwa dakinsa, ko kwankwaswa ba ta yi ba murda handle ta shiga. Yana kishingide kan sofa yana karanta kur'ani,yana ganinta ya diga aya yayi addu'a,sannan ya mike zaune sosai ya saka mata ido fuskarsa babu yabo babu fallasa,ita kuma ta yi kicin kicin da ita kamar mai shirin sheke shi da mari. Ya mike a hankali ya isa book case dinsa ya ajiye kur'ani sannan ya juyo cikin dakewa ya ce mata. "Lafiya kuwa?" Ta silale a hankali ta zauna akan hannun kujera saboda fushi ya sanyayar mata gabobi,kirjinta sai harbawa ya ke. Da ya gama fahimtarta sai shi ya saukar da nasa fushi ya mika mata filon kujera da sauri yana cewa. "A'a zauna sosai mana" Sai kwalla ta cika mata ido, ta yi saurin girgiza kai,ta ce. "Malam ni ba zama ya kawo ni ba...." Ya sa mata ido kawai. "Zuwa na yi na fada maka wallahi na gaji da aurenka..... Ni dai na gaji wallahi,kuma dole yanzu ka sake in". A sanyaye ya ce da ita. "Me na yi kika gaji da aurena fadima?" A kufule ta amsa masa. "Dama can a gajiye nake,hakurina ne kawai ya kare da na fahimci sam ba ka da tausayi.ina zaune a gidanka bisa tilas kai kuma kana son rataye ni... To wallahi ba zai yiwu ba, idan ma yajin ne na shirya in yi kuma babu mai matsa min in dawo gidanka". Ya tuntsure da dariya ya na dubanta,ya ce. "Amma dai da kin ji kunya.da shekarun talatin da biyu ne za ki kwashi yaji gida? Yanzu laifi ne dan na zagi zagagge? Haba fadima duk yawo da ke da nake yi watannin kusan takwas ban gajiya ba sai ratayar kwana biyun da na yi miki ce zata kosar da ke? To yi hakuri na tuba ba zan kara ba".$ ta dauke kai tana ci gaba da zubar da hawaye. Ke nan! Su ishe ka da laifi amma ba ka isa daukar mataki a kansu ba sai su ki da rauni da neman a basu hakuri,duk goma da ashirin! Ya tari gabanta ya ruko ta cikin murya mai bayyaya tarin kauna,ya ce. "Ki yi hakuri fadima,horo ba zai taba zama kiyayya ba, musamman a zuxiyar da ba ta da tamkar.... Matsala ta daya ce wadda sai ki min uzuri a kanta, ita ce,KAIFIN SO ba ya hana ni tsawatarwa idan an kauce hanya da zaki guji laifuka da kin tabbatar ba a cika samun masoyi kamata ba". Da muryar da ke nuna son fashewa da kuka ta ce. "Idan shashancina ya hana ni fahimtar ka fa.Ni ka karasa fice min a rai,ba ni da sauran wani abin yi a gidanka... Ni kawai tafiya..." Ya shishige mata sosai da kokarin shigar da idonsa cikin nata,ya girgiza mata kai. "A fatar bakinki wadannan kalaman suka tsaya,kafin na furta miki shashanci fadima sau nawa na furta miki kalaman yabo? Kin taba gode min ko kin mayar min da rabbi? Ki yi

Chapter 7 of 8