Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 8
kuma masu kwarin gaske ne,cikin zafin nama ya karyo rassai guda biyu sirara musu tsini.Karar rassan ne yasa kadan ya tsaya cak ya juyo da baya,ai kuwa sai Samazan ya mike tsaye zumbur ya ruga da gudu izuwa inda kadan yake.Koda kadan ya jiyo takun sawun Samazan sai shima ya rugo da gudu izuwa gareshi,inda ace mutum yana nan a lokacin da wannan kada da Samazan suka falfalo da azababben gudu domin suyi mugun gamo dole ne yace Samazan ya haukace saboda in ba mahaukaci ba babu wanda zai yarda yayi gaba da gaba da wannan murgujejen kada.Koda ya rage saura baifi taku bakwai ba suyi muguwar haduwa sai kowannensu ya daka tsalle sama,kadan ya wangame bakinsa yana mai fesar da wannan mugun ruwa da nufin ya hadiyeshi.Koda ruwan ya zuba a sassan jikin Samazan saiya kokkonashi tamkar garwashin wuta aka watsa masa amma bai narke ba.Samazan ya kaucewa hadiyar kadan ya lafo gadon bayan da hannu daya ya dane bayansa sannan ya daga wadannan siraran rassan bishiya guda biyu ya caka su a cikin fasasshen kwayar idanuwan kadan.Take rassan suka lume a ciki idanun suka fasa ta bayan kan nasa.Take kadan yayi wani irin ruri da gurnani mai matukar ban tsoro a lokacin da jini ya kama tsiri sama daga cikin idanun kadan kuma ya fado kasa tim.Ya kama birgima wacce ta haifar da girgizar kasa,shima Samazan saiya fado kasa ya mirgina can gefe daya don kada jelar kadan ta ragargaza shi sakamakon jehota da yake izuwa ko ina.Sakamakon mirginawar da Samazan yayi sai raunin gadon bayansa ya bugu da jikin wata bishiya take ya baje a kasa sumamme.Samazan bai farfado daga dogon suman da yayi ba sai bayan sa'a daya da rabi lokacin da wata irin iska mai karfi ta rinka kadawa,tasa ruwan wannan rafi ya kama yin ambaliya har ruwan ya watso kan Samazan,Samazan na farkawa sai yaji raunin gadon bayansa a daure tamkar igiya akasa ka zagaye bayan nasa.Koda yakai hannun nasa ya shafa raunikan sai yaji an dinke shi,cikin firgici ya yunkura zai mike tsaye sai yaji an danne shi ya kasa koda motsa ko ina a jikinsa.Sannan kuma sai yaji an kece da mahaukaciyar dariya.Take wani irin shudin hayaki ya baiyana tsulum a gabansa kuma sai hasken ya rikide ya zama wan dan guntun aljani wanda baifi a kife shi da kwando ba,kansa rantalele ne yafi gangar jikin girma amma fukafukansa yan kanana ne tamkar na dan tsako,gangar jikinsa siffar jemage ce ba kyan gani abin tsoro.Aljanin sai ya risina ga Samazan ya gaishe shi cikin girmamawa sannan yace gaisheka sarkin sadaukan duniya,hakika ka ajiye tarihin da har abada duniya ba zata taba mancewa da kai ba.Domin ka kashe kashe dabbar data gagari dukkan jaruman aljanu da bil'adama tsawon shekara ashirin.Lokacin da Gimbiya Ulaimatu tazo daidai nan a labarinta rana ta fadi gari ya soma yin duhu don haka sai sarauniya Safirat ta tari numfashinta tace dakata haka bana son kowa yaji karshen wannan labari face ni,zan kira ki ki karasa mini labarin a lokacin da muka kadaita mu biyu jal,A cikin daki bayan na nada muku sabuwar sarauniyarku.Koda gama fadin hakan sai sarauniya Safirat ta mike tsaye nan take gaba dayan dakarun yakin birnin suka zube kasa a gabanta suna masu mika mubaya'arsu.Nan dai taro ya watse kowa ya kama gabansa.Lokacin da Sarauniya Safirat ta shiga cikin turakar sarkin misra ta kwanta akan gadon da nufin tayi bacci sai ta kasa saboda tunanin mutum uku,mutum na farko shine marigayi sarkin misra kuma ba komai take tunowa ba'a kansa face maganganunsa na karshe kafin ya mutu.Mutum na biyu kuwa shine Yarima Musal'Asari wanda akace a halin yanzu ya fito farautarta,gashi da sa'a da kuma karfin sihirin tsafi.To waishin ma ta yaya zata iya kare kanta daga sharrin wadannan jarumai biyu kuma waishin yaya karshen labarin Jarumi Samazan zai kasance kafin ta hadu dashi.Nan take Safirat ta yanke hukunci a cikin ranta cewar ba gudu ba ja da baya a kan nufinta na maishe da dukkan mazajen duniya bayin mata kuma zata cigaba da bincike a cikin hallarar tsafinta domin ta gano hanyar da zata hallaka Yarima Musal'Asari da jarumi Samazan tun kafin su risketa. SHIN SARAUNIYA SAFIRAT ZATA CIKA BURINTA NA SAUKE SARAKUNAN DUNIYA KAF DAGA KAN KARAGARSU TA MULKI TA DORA MATA AKAI? TSAKANIN YARIMA MUSAL'ASARI DA JARUMI SAMAZAN WAI ZAI FARA HADUWA DA SARAUNIYA SAFIRAT KUMA IDAN SUN HADU MENENE ZAI FARU? SHIN YAYA KARSHEN SAFIRAT YAKE KASANCEWA? Mu Hadu A Kibiya Ratsa Maza Littafi Na Shida Don Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen Kayataccen Labari. Alhamdulillah.End Of Kibiya Ratsa Maza (5).Dama Kamar Yadda Na Fada Kafin Na fara Littafin 1-5 ne ya fito.To kuma gashi Allah yasa mun kammala shi.So sai muyi jiran fitowar cigabansa nan bada jimawa ba. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 8 of 8