Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 8
kintsenta kuma ta sanya wadannan takalma da Bandaru ya bata sannan ta fice da sauri daga cikin tantin.Tana fitowa tayi arba da wadannan dodanni guda arba'in.Kowannensu ya goya jakar guzurinsa a gadon bayansa sai kace sun kasance mutane ba dodanni ba.Al'amarin daya baiwa Safirat dariya kenan yayi murmushi,kawai sai ta juya ta nufi arewacin dajin ta dagawa dodannin arba'in hannu tana mai yi musu inkiyar su biyo bayanta.Nan fa Safirat ta falfala da azababben gudu izuwa cikin dajin dodannin arba'in na rufa mata baya suma sunayin gudu na ban al'ajabi don har tashi sama sukeyi saboda karfin gudun nasu.Amma duk da haka Safirat ta basu yar tazara. *** A*H*P *** Sarki Safwan na zaune akan kujera ya zuba idanu izuwa cikin dajin Tsaunin Lauhul Farras a lokacin da alfijir ya keto sai ya fara gyangyadi.Nai ankara ba sai baccin ya kwashe shi gaba daya har da minshari.Ashe suma sauran rundunonin da suka fito farautar Safirat basuyi bacci ba da daddare.Abin kamar hadin baki sai suma suka kama gyangyadi a wannan lokaci da alfijir ya keto.A sansanin sarki Safwan barde Barha ne kadai baya yin bacci a wannan lokaci saboda a daren jiya kwanciya yayi ya hantse abinsa,amma gaba dayan sauran dakaru da hadimansa da kuyanginsa duk bacci sukeyi.Koda Barde Barha yaga kowa bacci yakeyi hatta sarki safwan kuma shi kadai ne idonsa biyu sai hankalinsa ya DUGUNZUMA saboda tsoron kada jaruma Safirat ta fito a daidai wannan lokaci daga cikin dajin Lauhul Farras saboda yasan cewa shi kadai bazai iya cimmata ba ya tare ta.Sannan kuma sai yaji tsoron kada ya tashi sarki Safwan daga bacci ya zamo ya aikata lafin katse masa baccinsa.A karon banza ya fuskanci hukunci mai tsananin.Nan fa barde Barha ya kama kai kawo a gaban sarki Safwan wanda ke fama sharar bacci akan kujera yana tunanin abinda zai fishshe shi.Kwatsam sai barde Barha yaga giftawar wani abu shuu!Ta gabansu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.Kafin ya juyo yaga ko mene ne tuni Jaruma Safirat da dodanninta guda arba'in sun bazu tazara mai yawan gaske.Barde Barha ya wangame bakinsa ya kuma ya takarkare ya kurma wani uban ihu mai tsananin kara da firgitarwa.Take sarki Safwan da sauran dukkanin jama'arsa suka farka firgigit a dimauce.Sarki Safwan ya zare takobinsa koda ya kallo gabansa sai ya hango jelar daya daga cikin dodannin kan tsaunin Lauhul Farras ta kule izuwa cikin daji.Kawai sai sarki Safwan ya falfala da masifaffen gudu izuwa arewacin dajin domin ya gane cewa Safirat ce tazo ta giftasu yana bacci.Nan yake kuwa Barde Barha da sauran dakaru suka ruga suka hau dawakansu suka bi sawun sarki,su kuwa hadimai da kuyanci a firgice suka shiga hada kaya sannan suma suka bi sawu.Kamar yadda su Jaruma Safirat suka gifta su sarki Safwan suna bacci haka suka gifta sauran sansanin na sarakai,jarumi da matsafa,sai bayan sun wuce sannan ake farga dasu a bi bayansu.Nanfa aka kasa uban tsere a tsakaninsu ba sassauci.Amma aka rasa wanda ma zai kusanci su jaruma Safirat.Sai gashi mutum daya jal yazo yana ta wuce jarumai,matsafa da sarakai rike da zabgegiyar takobi a hannunsa.Nan da nan ya baiwa kowace runduna tazara mai yawan gaske har ya bace musu bat da gani saboda masifaffen gudun da yakeyi amma duk da haka shima da kyar yake iya hango dodo na karshen baya daga cikin dakarun Jaruma Safirat masu tsaronta.Haka dai aka cigaba da tseran gudu tsakanin su jaruma Safirat da sarki Safwan tun daga fitowar alfijir har rana ta take a sannan ne kowa ya gaji ainun.Tsananin yunwa da kishirwa suka addabesu.Amma saboda naci anki a daina gudu.Safirat da dakarun nata har tangadi sukeyi kamar zasu fadi kasa.Shima sarki Safwan haka,wani lokacin ma har faduwa yakeyi amma kuma har a san ™Abubakar Haleefah Physicist™ nan takobinsa na hannunsa bata subuce masa ba.Ana cikin wannan hali ne Safirat taga uku daga cikin dodanninta sun sare sun fadi kasa suna haki kamar ransu zai fita,kawai sai ta sharesu ta cigaba da gudunta abinta suna kara yin dan gaba sai dodannu biyar suka sake sarewa suma suka zube kasa.Faruwar hakan keda wuya sai hankalin Jaruma Safirat ya dugunzuma domin ta fahimci cewar indai aka cigaba da gudun a haka to za'a kai munzalin da zata rasa gaba dayan dodanni,alhalin kuma tasan cewa akwai lokacin da zasuyi mata matukar amfani.Bisa sa'a kuwa sai Safirat ta hango wata fadama (korama) a gabansu kadan.Cikin farin ciki ta karasa gaban koramar ta tsuguna ta jika kanta ta sha ruwa.Ai kuwa sai suma sauran dodannin suka rugo izuwa cikin fadamar suna murna suka kama shan ruwan.Adaidai wannan lokaci ne Safira taji takun sawu da gudu an tsaya a bayansu.A nutse Jaruma Safirat ta mike tsaye ta juyo a hankali saboda dama tasan wanda ke biye dasu din.Ai kuwa tana waigowa tayi arba da sarki Safwan a tsaye rike da sharbebiyar takobinsa yana haki kamar ransa zai fita.Ga tsananin kishirwa na damunsa,lebansa ya bushe sai kallon wannan ruwa na cikin fadamar yake.Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin sarki Safwan da jaruma Safirat.Kawai sai dodannin suka yunkura zasu kaiwa sarki Safwan farmaki amma sai jaruma Safirat ta daka musu tsawa tace wannan yaki ba naku bane shi kadai ya iso nan don haka mutum daya ne zai yakeshi kum NI CE!Koda gama fadin hakan sai jaruma Safirat ta cire battar ruwanta daga kwankwasonta ta tsomata cikin fadamar ta cikata da ruwa sannan ta tsuke bakinta ta cillawa sarki Safwan ya cafe.Dama tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku ashirin ba.Safira ta dubi sarki Safwan a lokacin da hawaye ya subuto mata cikin tsananin takaici tace bazan yaki masoyina a lokacin da yake jigace ba,kasha ruwa ka gusar da kishinka.Koda jin haka sai sarki Safwan ya bude battar ruwan ya kafata a bakinsa ya kama kwankwada har saida ya koshi sannan yayi jifa da ita.Ya dubi Safirat fuskarsa a murtuke tamkar yana kallon kumurcin maciji mai shirin saransa.Har ya budi baki zaice wani abu sai ta tari numfashinsa muryarta tana rawa tace ashe zaka iya sayar da soyayyarmu saboda abin duniya? Ina kaunarmu da amanar dake tsakaninu?Shin laifin mahaifina ne ya shafeni har da kakeson ganin bayana?Koda sarki Safwan yaji wadannan tambayoyi sai zuciyarsa ta karaya kuma kunya ta kamashi sannan hawaye ya zubo masa shima ya budi baki cikin rawar murya yace,yake Safirat ki dauki soyayyarmu,kaunarmu,­ shakuwarmu da kuma amanar dake tsakaninmu tamkar wani abu daya faru a mafarkin daya shude tuntuni a baya.Ki sani cewa a halin yanzi bani da wani abokin gaba wanda ya fiki domin mahaifinki ne ya kashe ubana kinga dole ne na dauki fansa akanki.Abu na biyu dole ne na rabaki da wannan KWARI DA BAKA naki domin ceto Rayuwar kasata da jama'ar da kuma mulkina.Idan harna barki kika mallaki wannan kwari da baka tofa sai duniya gaba daya ta koma hannun mata.Sai maza su koma hannun bayin mata.Kinga kuwa duk ranar da mulkin duniya ya koma hannun mata sai komai ya lalace.Zaman lafiya da kwanciyar hankali sun rushe kenan.Saboda haka yanzu bani da wani zabi wanda yafi na kashe ki na dauke wannan baka tunda gaba daya sarakai,jarumai da matsafan duniya hankalinsu na kan baka.Kafin sarki Safwan ya gama rufe bakinsa tuni Jaruma Safirat ta daka masa tsawa tace kaje ka binciki mahaifiyarka kace kana son ta gaya maka ko wanene ya kashe ubana.To ka sani cewa ubanka ne ya siye amintacciyar baiwar ubana ta zuba masa guba a shayinsa.Shin rama cuta ga macuci laifi ne?Hatta uwata bata san nasan wannan sirri ba.Koda jin wannan batu sai jikin sarki Safwan ya sakeyin sanyi a karo na biyu.Amma sai zuciyarsa ta kekashe ya sake murtuke fuskarsa yana mai gyara tsayuwa alamar cewa a shirye yake a gabza yakin.Koda ganin haka sai Hawaye ya sake subutowa Safirat tace tabbas yau ne na tabbatar da cewa NAMIJI BA DAN GOYO bane,kuma namiji butulu ne!Idan har nayi nasara kanka kuma na sami nasarar dauko tuttun kwari na,na rantse da jini ubana saina sa gaba dayan mazajen duniya sun zubar da hawaye.Sai na sauke gaba dayan sarakunan duniya daga kan karagarsu ta mulki na dora mataye akai.Sai kowace matar aure ta daina kwanciya a kasan mijinta,sai dai a samansa.Sannan sai kowace mace ta daina dafawa mijinta abinci tare da yi masa sauran hidima,saidai shi yayi mata ya zamo bawanta.Saina maishe da dukkan mazajen duniya tamkar karnukan farautan mata sai yadda suka so zasu sarrafasu.Safirat na gama fadin haka sai ta dubi dakarun dodanninta tace dasu ko sarki Safwan zai samu nasarar kasheni kada ku tayani yakarsa.Duk wanda ya tayani yakarsa zan kasheshi da hannuna.Nan take Jaruma Safirat ta zare takobinta ta ruga izuwa kan sarki Safwan tana mai kwarara uban ihu da kururuwa,takobinta na kartar kasa tana tashin kura.Suna haduwa suka kacame da wani masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro da ban al'ajabi.Nanfa suka rinka kaiwa junansu sara da suka cikin bakin zafin nama,juriya da bajinta.Su kuwa wadannan dodanni sai suka zuba musu idanu kawai suka zama yan kallo saboda tsoron saba umarnin jaruma Safirat. Toofah!!Nima ganin ana wannan masifaffen yaki yasa na tsaya domin na more kallo. Don't just read and pass,Commenting and Liking Necessary. A yanzu ne labari ya fara dadi fiye da da. KIBIYA RATSA MAZA!!! Littafi Na Biyu (2) Part B Saboda tsoron saba umarnin Jaruma Safirat.Wohoho!Idan jarumtaka ta hadu da takwaranta,naci da juriya suka game tofa dole ne yayi yayi tsamari ainun.Saida Safira da Sarki Safwan suka shafe dakiku masu yawa suna wannan artabu amma dayansu bai samu nasarar koda lakutar jikin daya ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalin kowannensu kenan.Shidai sarki Safwan burinsa shine ya kashe Safirat kafin ragowar rundunonin makiyanta su karaso wajen ya dauke bakan dake goye a bayanta ya gudu.Itama Safirat kokarinta shine ta gama da sarki Safwan kafin sauran makiyan nata su karaso domin ta isa cikin dajin Sharkif in yaso su sameta a can.Koda kowannensu yaga wankin hula zai kaishi dare sai suka sauya salon fada a lokaci guda suka hada da kaiwa juna NAUSHI DA BUGU.Nan take kuwa labari yasha bambam ya zamana cewa sun fara hadawa kansu JINI da MAJINA.Nanfa suka fara galabaita.Lokaci guda kowannensu ya fara ja da baya cikin tsananin fushi sukayi nazarin juna suna mamakin yadda karfin damtsensu yazo daya gami da iya yakinsu.Kamar hadin baki sai kuma suka sake rugowa da gudu izuwa kan juna a karo na biyu suna masu kwala ihu.Koda ya rage saura taku uku kacal su hadu sai kowannensu ya daka tsalle sama ya kaiwa dan uwansa mugun sara.Duk da cewa kowannensu yayi yunkurin kaucewa harin da aka kawo masa,amma sai da hakan ya faskara domin sarki Safwan ya sami nasarar saranta a gadon bayanta,ita kuma ta samu nasarar saransa a kirjinsa.Lokaci guda duk su biyu suka rusa ihu sakamakon tsnanin zafi da zogin da sukaji a lokacin da jini yai tsartuwa daga jikinsu suka fado kasa a matukar galabaice suka kasa koda mikewa tsaye.Adaidai wannan lokaci ne suka jiyo sukuwar dawakai a bayansu.Suna waigawa suka hango rundunonin daruruwan mahaya sun tunkaro su daga can nesa sai kara yiwa dawakansu kaimi suke domin su riskesu cikin kankanin lokaci.Sawayen dawakan nasu na tashin gagarumar kura.Koda ganin haka sai daya daga cikin dodannin ya suri jaruma Safirat ya dorata a gadon bayansa,ya falfala da wani azababben gudu irin nasu.Ai kuwa sai sauran yan uwansu suka rufa masa baya.Kafin rundunonin abokan gabar Safirat su iso wajen tuni dodannin sun kule a cikin dajin tamkar basu taba wanzuwa ba a wajen.Koda sarki Safwan yaga Safirat ta tsere saiya kurma uban ihu na bakin ciki kuma ya dafe raunikan kirjinsa mai bulbulo da jini.Adaidai wannan lokaci ne ya bingire kasa sumamme.Koda dakarun sarki Safwan suka iso sukaga halin da yake ciki sai suka dimauce.Nan tahe aka kafa tanti aka shigar dashi ciki,likitansa ya kama aikinsa.Sauran sarakuna da jarumai da mayakan da suka iso kuwa suka cika da tsananin bakin ciki saboda sun san cewa koda ma sunbi bayan Safirat a yanzu ba lallai bane su risketa kafin ta isa cikin dajin Sarkif.Dajin da babu wani mahaluki da baya tsoransa a duk fadin duniya walau MUTUM ko ALJAN.Nan take gaba daya sarakunan kimanin su arba'in gami da manyan bokaye su ashirin da takwas da kuma zakwakwaran jaruman da suka fito daga manyan birane na duniya su talatin da biyu suka shirya taro na gaggawa aka zauna ana tattaunawa.Sarkin Misra ne ya fara da fadin cewa a halin yanzu babu abinda ya kamata muyi face mu jira farfadowar sarki Safwan na birnin Kisra tunda shi kadai ne a cikinmu ya sami nasarar cimam wannan takadariyar yarinya har suka fafata.Kuma dama shine mafi sanin siriinta tunda tun suna yara suke tare.Shine kadai zai iya bamu shawara da wannan baka kafin ta dauko kuttun kwarinsa.Koda sarkin Misra yazo nan a jabawabinsa sai wani shahararren boka na kasar Yemen ya tari numfashinsa yace kai bazai yiyu ba,domin a bari ya huce shike kawo rabon wani.Kuma da zafi zafi akan bugi karfe.Ba muki ta shawararka ba amma ga wata shawarar.Kowacce runduna ta zabo wakilanta guda goma goma a turasu subi bayan jaruma Safirat da dakarun dodanninta,su cimma kafin su shiga cikin dajin Sarkif.Tunda dai itama Safirat akwai rauni babba a jikinta yanzu,nasan ba zasu shiga cikin dajin Sarkif da ita a wannan hali ba.Dole ne su tsaya suyi jinyarta ta farfado kuma ta dawo cikin haiyacinta.Boka Inzuba ne yayi wannan jawabi.Koda jin haka sai sansanin ya rude da shewa kowa na cewa ya amince da shawarar boka Inzuba.Nan take kowace runduna ta zabo dakaru goma daga cikin mayakanta wanda take takama dasu.Kuma ganin cewa ta yarda dasu,zasu iya yin duk abinda ake ganin ba zai yiyu ba,kowane badakare kallo daya zakayi masa ka tabbatar da cewa ya cika gwarzon mayaki abin kwatance saboda suna da kwarjini,haiba da cikar zati gami da sura irin na manyan jarumai.Kuma kowannensu na dauke da mahaukacin makami.Har wadannan zababbun dakaru sun yunkura zasu bi bayan su jaruma Safirat sai sarkin birnin Farisa ya tsaida su yana mai daga hannu sannan ya dubi gaba daya jama'ar dake wajen yace yanzu a misali idan wadannan wakilan dakaru namu suka sami nasarar karbo wannan baka a hannun Safirat wa za'a barwa Bakan?Koda jin wannan tambaya sai kowa ya shiga taitayinsa aka kama muzurai ana kallon juna.Aka rasa wanda zaice kala.Da ganin haka sai sarkin Farisa yace tunda an rasa mai bada amsar tambayata ni zan baiwa kaina amsa.Amsar itace da zarar an zo da bakan,sai a shirya GASAR JARUMTAKA a tsakanin dakarun jaruman namu,wanda suka yi nasara su za'a barwa bakan.koda jin haka sai aka dada rudewa da shewa kowa na cewa ya amince da wannan tsari.Nan take dakarun wakilcin suka zaburi dawakansu da gudu izuwa cikin daji domin su riske su jaruma Safirat kafin su isa dajin Sarkif. *** * * * *** Bayan tafiyar wadannan dakarun wakilci da kamar kimanin ™Abubakar Haleefah Physicist™ rabin sa'a ne sarki Safwan ya farfado daga dogon suma da yayi.Yana bude idanunsa yaga raunin kirjinsa a dinke kuma ya tsinci kansa kwance a cikin tanti.Take ya gane cewa dakarunsa ne sualka iso suka ceci rayuwarsa.Kawai sai ya tuno da yadda Safirat ta kubuce masa,nan fa bakin ciki ya turnuke shi ya rasa abinda ke masa dadi a duniya.Cikin tsananin karfin hali sarki Safwan ya yunkura domin ya mike zaune daga kwance amma saiya kasa bisa tsananin zafi da zogin da yaji tamkar kasusuwan kirjin nasa zasu kakkarye.Bisa dole ne ya koma ya kwanta.Faruwar hakan keda wuya saiga likitansa ya shigo cikin tantin da sauri saboda dama yi kiyasta iya tsawon lokacin da sarki Safwan zaiyi ya farka daga bacci.Da shigowar likitan yana duban sarki ya gane cewa yayi yunkurin mikewa zaune don haka saiya dubeshi cikin alamun tsananin damuwa da fargaba yace ya shugabana ka sake yunkurin zauna zaka iya rasa rayuwarka gaba daya domin kuwa dukkan kasusuwan jikinka ne zasu kakkarye saboda jijiyoyin dake rike da kirjin naka ne zasu tsintsinke.Kayi sani cewa ka auna arziki daya zamana cewa saran da jaruma Safirat tayi maka baikai ga datsa kasusuwanka ba,naman wajen ya dare kuma ya dan taba kashin kadan.Dole ne a kallah ka sami kwana tara a kwance kana jinya kafin kashin ya hade ka iya motsi sosai ko ci gaba da tafiya.Koda jin wannan batu sai zuciyar sarki Safwan ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda bakin ciki domin yasan cewa kafin cikar kwanakin tara jaruma Safirat zata iya dauko kurtun kwarinta.Idan kuwa har haka ta kasance tofa babu wani mahalukin da ya isa ya tare da yaki don ko mutanen duniya ne da aljanunta zasu hadu a kanta sai ta karar dasu.Koda sarki Safwan ya gama aiyana hakan a cikin zuciyarsa sai sabon bakin ciki ya turnukeshi har kwallar takaici ta cika masa idanu yayi sauri ya kauda kansa ga barin kallon likitan nasa don kada ya gane damuwarsa. *** * * * *** Al'amarin Jaruma Safirat kuwa itama tun sa'adda ta fadi kasa sumammiya daya daga cikin dodannin ya sureta ya aza a bayansa suka ruga izuwa cikin daji bata farka ba sai bayan sa'a uku da rabi,tana bude idanunta ta tsinci kanta kwance akan wata bishiya mai yawan duhuwar ganyaye kuma a cikin wani irin daji wanda ko a labari bata taba jinsa ba.Da farko saida Safirat ta shafa gadon bayanta taji an dinke rauninta kuma an shafa mata wani magani a kansa me maiko.Koda ta dubi gabas da yammanta sai taga ashe akwai wadannan dodannin kimanin su goma akan bishiyar sun yi mata KAWANYA suna gadinta.Bisa mamaki sai jaruma Safirat taga ta iya mikewa zaune alhalin a zatonta ba zata iya mikewa ba zaune sai bayan yan kwanaki.Koda taga ta mike zaune daram ba tare da taji wani ciwo ko wani zogi ba a bayanta sai ta dubi dodannin tace,maza kuzo mu wuce izuwa cikin dajin sarkif saboda na tabbatar da cewar makiya suna biye damu,kuma idan suka riskemu anan ban san yadda karshen gumurzunmu zai kasance ba.Koda jin wannan batu sai wannan dodo wanda ya goyata a bayansa ya dubeta yace,ya shugabata ai dama ba wani abu bane yasa muka yada zango ba anan face ganin halin da kike ciki na suma da wannan rauni dake jikinki.In badon mun kware akan ILMIN LIKITANCI ba da ba zamu iya ceto rayuwarki ba har ma ki iya mikewa zaune.Kuma gani mukayi idan ma muka shiga cikin dajin Sarkif dake a cikin wannan mugun hali babu abinda zaki iya bisa batun dauko kuttun kwarinki.Kinga kenan shigar tamu bata da wani amfani.Koda jin haka sai Safirat tayi murna kuma ta yiwa dodannin godiya bisa ceto rayuwarta da sukayi.Nan take ta duro kasa daga kan bishiyar suma sai suka duro.Nan take taga ragowar dodannin suna fitowa daga inda suka lallabe don tabbatar da TSARO.KAfin Jaruma Safirat tayi yunkurin cigaba da tafiya sai kawai sukaga wadannan dakarun wakilci sun durfafo su a guje bisa dawakai su da yawa suna masu zare takubbansu suna kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa.Kuma tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku goma ba.Har jaruma Safirat ta yunkura zata zare takobinta sai wannan dodo daya goyata yai wuf ya sureta ya sake° goyata a bayansa yace ya shugabata bai kamata kiyi yaki ba yanzu domin raunin gadon bayanki bai gama hadewa ba da warkewa.Dinkin raunin zai iya warewa idan kikayi kyakkyawan motsi.Ki kyalemu da wadannan dakaru zamu iya dasu.Kafin wannan dodo ya gama rufe bakinsa tuni sauran yan uwan nasa sun ruga izuwa inda dakarun wakilcin suke suka tare su.Nanfa aka ruguntsume da azababben yaki sai gashi dodannin suna daka tsalle sama suna shawagi akan dakarun wakilcin suna kai musu yakushi,sara da suka da miyagun faratan hannayensu.Su kuma suka wanzu suna karewa gami da maida martani.Nanfa kowa ya zamewa kowa alakakai domin babu bangaren dake samun wata nasara.Duk saadda makaman dakarun ya hadu da jikin dodannin saikaga tarwatsin wuta na tashi.Da yake suma wadannan dakarun wakilci sun cika jarumai masu karfin sihirin tsafi gami da matukar juriya da tsagwaron iya yaki sai karfi ya kusan zama daya.Koda donannin suka ga haka sai suka rinka huda cikin dawakansu suka rinka faduwa kasa matattu suna kayar da mahayansu.Nanfa aka bude kasuwar KASUWAR YAKI ta gaba da gaba.Abinda ya dugunzuma hankalin dakarun wakilcin shine ganin yadda KAIFI da TSINI baya tasiri a jikinsu.Duk wannan abu dake faruwa dodon dake goye da Safirat yana ta kokarin samun hanyar da zai tsere da ita ne ya nausa cikin dajin Sarkif amma ya kasa saboda dakarun wakilcin sunyi musu kawanya ne.Saida aka shafe sa'a daya da rabi ana yin wannan bakin artabu ba tare da kowane bangare sun sami wata nasara ba.Kwatsam bisa tsautsayi sai tsinin takobin ™Abubakar Haleefah Physicist™ daya daga cikin dakarun wakilcin ya soki idon daya daga cikin dodanni.Faruwar hakan keda wuya dodon yayi wani uban ruri a lokacin da jini ya kama feshi yai tsalle ya runtuma da kasa ya kama kakarin mutuwa.Koda dakarun wakilcin suka ga haka sai suka cika da murna saboda sun gano lagon dodanni ai kuwa sai suka kara kaimi wajen yakarsu.Sai gashi sun cigaba da soke musu idanu suna zubewa kasa matattu tamkar ana sassabe a gona.Nan da nan cikin kankanin lokaci suka kashe kimanin dodanni ashirin da bakwai su kuwa dodanni da kyar suka iya kashe ashirin da daya na dakarun wakilcin.Koda Safirat taga irin mummunar barnar da dakarun sukayi musu saita fusata ainun bata san sa'adda ta daka tsalle sama ba daga kan gadon bayan dodon daya goyata.Tana saman iska ta zare takobinta ta afka cikin dakarun wakilcin ta hausu da sara da suka ba kakkautawa.Take salon yaki ya sauya domin a cikin dakika arba'in ta shaftare makogwaron dakaru kusan hamsin suka zube kasa matattu.Ana cikin haka ne wani badakare mai mugun naci ya sadado ta bayan Safirat ya doki gadon bayan nata da kafarsa guda da dukkan karfinsa.Jaruma Safirat tayi tsalle sama tamkar an janyeta da majaujawa a lokacin data kurma uban ihu sakamakon mugun zafin da taji a gadon bayanta kuma sai fuskarta ta gwaru da jikin wata bishiya ta fado kasa sumammiya.Kafin daya daga cikinsu ya sami damar cafkarta tuni wannan dodo ma'abocin goya Safirat ya dauketa daga wajen ya sake goyata ya falfala da azababben gudu ta tsakiyar dakarun wakilcin yana tarwatsasu da karfin tsiya su kuma suna yi masa lugudan sara da suka suna kokarin hallaka Safirat da dauke bakanta.Amma sai suka kasa saboda dodon yafi gaba dayansu zafin nama da karfin gudu da kuma tsananin karfin damtse.Kafin su ankara tuni ya fice fit ta tsakiyar tasu ya basu tazara mai yawa.Nanfa suka bi bayansa da gudu a lokacin da tsirarun dodannin ma suka rufa masa baya.Haka dai dakarun wakilcin suka cigaba da bin wannan dodo mai goye da Safirat suna karawa dawakansu kaimin gudu wanda gudun nasu gudu ne na SIHIRI amma har dodon ya iso bakin dajin Sarkif basu sami damar riskarsu ba.Koda sukaga dodon ya fada cikin dajin Sarkif da kafafunsa sai suka ja linzamin dawakansu sukayi turjiya da haniniya.Jin turjiyar dawakan nasu ne yasa dodon ya tsaya cak ya waigo yana yiwa dakarun wakilcin murmushin muhunta sannan ya yafutosu da hannu yana maiyi musu nuni da cewar idan sun isa su biyoshi cikin dajin sarkif din.Amma dukkaninsu sai suka noke aka rasa wanda zai saida ransa.Ta gaban dakarun wakilcin sauran dodannin suka zo suka wuce da gudu suka fada cikin dajin Sarkif suka bi dan'uwansu a baya lokacin daya juya ya cigaba da tafiya a hankali cikin Izza,Kasaita da kwanciyar hankali. *** * * * *** Bayan Kulewar Dodannin ne a Cikin dajin Sai..... Tab su Safeerat sun shigo DAJIN SARKIF dajin da kowa ke shakka.Sai gobe maji yadda zata kasance Insha Allah. KIBIYA RATSA MAZA!!! Littafi Na Biyu (2) Part C BAYAN KULEWAR Dodannin ne a cikin dajin sai dakarun wakilcin suka dubi junansu cikin tsananin takaici.Daya daga cikinsu ya dubi sauran cikin alamun matukar damuwa yace bamu da ilimin komai akan dajin Sarkif,duk wanda yayi gangancin shigarsa a cikinmu tabbas mutuwa zaiyi.Yanzu kuzo mu koma sansaninmu wajen shugabanninmu mu sanar dasu duk abinda ya faru,amma dole ne mu dauki gawar dodo ko guda daya ne domin su gasgata zancenmu su tabbatar da cewar munyi iyakar kokarinmu.Gama fadin hakan keda wuya sai dakarun wakilcin suka juya da baya da gudu izuwa cikin dajin da suka baro,wato can inda suka fara yin gumurzun farko dasu jaruma Safeerat. *** * * * *** Al'amarin su jaruma Safirat kuwa lokacin da aka shigar da ita cikin dajin sarkif sa'adda take cikin suma na biyu goye a bayan wannan dodo,tafiyar dakika dari biyu da sittin kacal akayi ta farfado daga suman da tayi.Amma sai taji gadon bayanta yana yi mata mugun radadi da zogi sakamakon naushin da akayi mata wanda ya zama ya fama mata raunin,amma sai taji cewa zata iya yin tafiya da kafafunta,Sai ta budi baki tace ka ajiyeni na taka da kafafuna.Koda jin muryar Safiray sai farin ciki ya kama dodon ya tsaya cak ya sauke ta saboda tsawonsa.Koda ya direta kasa a gabansa yaga ta fara kallon dajin Sarkif tana murmushi saboda ganin irin ni'imar dake cikinsa ta korayen ganyaye,ruwan duwatsu dake kwaranya wanda ya kasance garai garai gwanin ban sha'awa da kuma yayan itatuwa irinsu inibi,baure da sauransu sai yace ya shugabata kyawun wannan daji ya daina birgeki domin kyan dan maciji ne.Idan kinsan masifun dake cikinsa da bakiyi sha'awar shigarsa ba.Mu kanmu a yanzu ba karamin ganganci mu kayi ba da muka biyo dake izuwa nan kawai,don bamu da yadda zamuyi mu kawo kanmu GIDAN MUTUWA,kuma ako yaushe a ko ina ajali zai iya zuwa ya shammacemu a cikin wannan daji.Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama jaruma Safirat tace to wai shin menene abin tsoro a cikin wannan daji?Ni tun da muka shigo cikinsa ko mugun kwaro guda daya ban gani ba.Gama fadin haka keda wuya sai safirat taji wani irin huci a bayanta mai dumi kamar an kunna gagarumar wuta sannan kuma taji wani irin gurnani mai matukar ban tsoro.A firgice ta waiga bayanta da sauri,koda tayi arba da abinda ke bayanta sai taji kamar ta saki fitsari a tsaye saboda tsananin razanar da tayi duk da jarumtaka irin tata kuwa.Ba komai jaruma Safirat ta gani ba face wata irin katuwar macijiya mai girman gaske,amma kuma kanta irin na macen bil'adama ne rafkeke tamkar tunkuyar girki irin ta mutanen da.Tna da idanuwa manya manya kamar tulu,hancinta wawakeke za'a iya zura mutum a cikin kowane kofar hancin.Bakinta kuwa kamar kofar shiga wani gari.Hakoranta gabza gabza ne kamar hauren giwa ne aka jera sama da kasa kuma guda dari ba daya ne.Saboda girman jelarta da nauyinta ko yaya ta motsa sai dajin gaba daya yayi girgiza.Tunda Jaruma Safirat tazo duniya ko a mafarki bata taba tunanin cewa akwai wata halitta mai mummunar siffa irin wannan ba.Nan take sai jikin Safirat ya kama karkarwa.Su kuwa wadannan dodanni abokan tafiyar Safirat tuni sun arce daga wajen sun shige cikin kogunan duwatsu da cikin ramuka sun buya suka bar Safirat ita kadai a tsakiyar dajin a gaban wannan muguwar Macijiya.Lokacin da macijiyar taga yadda jaruma Safirat ta firgice kuma ta dimauce sakamakon yin arba da ita sai ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya mai kama da saukar kwaran kwatsa sannan ta hade bakin a lokacin da wani irin turirin dafi ke fita ta dakawa Safirat tsawa tace ke karamar kwaruwa wane irin taurin kai gareki gami da ganganci da rayuwa har da zakiyi tunanin shigowa cikin wannan daji domin ki dauki wani abu?To ki sani cewa ko shi kansa mahaifin naki boka Saiham daya tabbata shugaban bokayen duniya bai taba shigowa nan ba,saidai ya aiko da abu ta hanyar sihiri shi kansa yasan ya turoki ne izuwa AJALINki.Kafin macijiyar ta gana rufe bakinta tuni jaruma Safirat ta tari numfashinta tana mai cewa ke tsohuwar azzaluma,ki sani cewa koma girman halitta,komai jin kanta da karfinta sai an sami wadda ta fita komai.Tabbas na firgita da ganinki saboda shi tsoro wajibi ne,amma dana gane cewa ke azzalima ce sai naji duk tsoronki ya gushe daga cikin zuciyata.Duk abinda yai farko a cikin wannan duniya yana da karshe,babu mamaki zuwana nan ya zama sanadin karshen zaluncinki.Nayi imani cewa sai na sami abinda nazo nema a cikin dajin nan kuma sai na fita a raye don haka ke baki isa ki hanani daukar abinda nazo dauka ba.Koda Safirat tazo nan a zancenta sai Macijiyar ta wangame katon bakinta ta bushe da dariya a karo na biyu,iskar bakin nata ta daga Safirat sama har saida ta daina dariyar tsuke bakinta sannan Safirat ta fado kasa tim.macijiyar ta dubeta cikin kallon raini tace hakika yaro bai san wuta ba sai ya taka ta.Tunda kikayi mini rashin kunya yau saidai uwarki ta haifi wata amma dai ke taki ta kare.Idan kina da wasiya ta karshen rayuwa ki fadi kafin ki sheka barzahu.Kuttun kwari da bakan da kika zo nema bama ke ba wasunki ma basu isa susan inda yake ba a cikin wannan daji bare su dauka daga nan har izuwa rayuwa idan akwaita.Kafin Safirat ta bude baki tace wani abu ko kuma tayi wani yunkuri tuni majiyar ta shammaceta ta wangame bakinta.Take wata irin iska mai karfi ta fito daga cikin bakin ta zuke Safirat ta hadiyeta.Kawai sai macijiyar ta rufe bakin nata sannan ta daka tsalle ta tsunduma cikin wani tafkeken kogi tayi nutso izuwa karkashinsa.A ka'idar wannan macijiya duk abinda ta hadiye a cikin dakika ™Abubakar Haleefah Physicist™ biyar kacal yake narkewa ya zagwanye saboda tsananin zafin dake cikin cikinta,amma sai gashi Safirat bata narke ba kuma bata mutu ba amma tsananin zafin cikin macijiyar yasa jikinta yayi luguf kuma numfashinta ya fara sarkewa saboda rashin shakar iska.Koda Safirat taji zata hallaka saita mike tsaye a cikin cikin macijiyar ta zare wata wuka dake daure a jikin cinyarta ta hagu ta kama saran hanjin cikin macijiyar.Ai kuwa sai macijiyar ta rinka jin kamar zata mutu don haka bata san sa'adda ta wangame bakinta ba tayi wata irin muguwar kara wacce tasa gaba dayan halittun dake cikin karkashin tekun suka mace nan take,wadanda ke saman kogin suka sume,wadanda ke cikin dajin bisa turba dole suka toshe kunnuwansu,wasu kuwa suka rinka tona kasa suna binne kansu da kansu a karkashin kasa.Safirat ta cigaba da saran hanjin cikin macijiyar duk da cewa kuwa hanjin baya katsewa amma macijiyar bata daina mutsu mutsu da juye juye ba tana ruri da ihu tana gwara jikinta a jikin duwatsun dake cikin karkashin kogin.Sakamakon haka ne Safirat ma ta rinka faduwa tana gwara kanta da jikin macijiyar amma saboda tsananin naci da juriya sai ta cigaba da mikewa tsaye zumbur tana ci gaba da saran hanjin macijiyar,nanfa ya zamana cewa da ita da macijiyar duk sun wahala sun jigata ainun.nan da nan idanun macijiyar suka kada sukayi jawur,suka fara zubar da hawayen wuya,kai da bala'i yai bala'i macijiyar taji cewa tabbas hallaka zatayi sai ta taso sama daga karkashin kogin ta fito bakin gabar kogin ta fito bakin kogin ta kama kakarin amai domin ta watso Safirat waje daga cikinta ta huta da azabar da take ji.koda Safirat taji an zukota za'a wastota waje daga cikin macijiyar don haka saita saki jikinta ta taho da gudu tana fitowa bakin macijiyar saita wurkila jikinta ta haye saman kan macijiyar ta zauna daram.Kafin macijiyar ta wurkila jikinta ta jeho Safirat kasa tuni ta daga wannan wuka dake hannunta ta caka mata ita a tsakiyar madigarta.Nan take jini ya kama tsiri sama a lokacin da macijiyar tayi wani irin uban ruri wanda bata taba yin kamarsa ba.Kawai sai ta langwabe kasa tayi wanwar ko shurawa batayi ba.Ashe ruhin wannan macijiyar a cikin tsakiyar kanta yake cikin madiga.Ita kanta jaruma Safirat da taga ta sami nasarar kashe macijiyar tayi matukar mamaki domin bata san cewa ruhinta a tsakiyar kanta yake ba kawai dai tsananin sa'a ne da rabo ya kaita ga samun wannan nasara.Saboda jikin Jaruma Safiray ya hadu yayi lugub sakamakon tsananin zafin da cikin macijyar yake dashi saita yanke jiki ta fadi kasa sumammiya.Adaidai wannan lokaci ne wadannan dodanni suka fito daga cikin ramuka da kogunan duwatsun da suke boya da gudu suka rugo izuwa inda take kwance.Nan dai suka fara kokarin ceto rayuwarta.Saida suka shafe kusan rabin sa'a suna yi mata fifta da dan yayafa mata ruwa amma bata farka ba.Al'amarin dayai matukar dugunzuma hankalinsu kenan suka fara tunanin cewa lallai ta mutu saboda babu alamar inda yake motsi a jikinta.Nan fa dodannun suka kama kuka suna zubar da hawaye na takaici da bakin ciki saboda a ganinsa bai

Chapter 3 of 8