Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 8
kamata ace jaruma kamar Safirat ta mutu ba wacce tasha wannan bakar gwagwarmaya tayi bajintar da ba'a taba samun mahalukin da yayi taba a nahiyar gaba daya,sannan kuma suna matukar bakin ciki bisa ganin cewa duk wahalar da suka sha a baya ta raka Safirat izuwa cikin dazuzzukan biyu da kuma yan uwansu da suka rasa duk sun zamo a banza kenan.Dodannin na cikin wannan tsananin bakin ciki ne ma'abocin goyata a bayansa ya lura da yadda jikin Safirat ya hadu yayi lugub har a sannan tururin zafi bai daina fita ba daga cikin kofofin gashin jikinta.Koda ganin haka sai yayi wuf ya sureta ya azata a bayansa ya runtuma da gudu izuwa wani bangare daban na dajin wanda shi kansa bai san inda hanyar zata kaishi ba.A dimauce sauran yan uwan nasa suka rufa masa baya domin suga inda zai kaita.Haka dai dodon ya cigaba da gudu dauke da Safira yana waige waige da dube dube ko zai ga abinda yake nema wanda yake ganin cewar shine kadai zai iya ceto rayuwar Safirat.Duk da cewar wannan dodo da sauran yan uwan nasa suna matukar tsoron wannan daji na Sarkif sai gashi sunfi jin tsoron mutuwar Safirat akan dajin.Burinsu kawai shine su ceto rayuwar tata koda kuwa zasu rasa tasu rayuwar.Saidai wadannan dodanni suka shafe sama da sa'a guda suna guje guje a cikin wannan dajin Sarkif suna fadawa cikin tsaunuka suna jin raunika a jikinsu saboda komai na dajin daban yake basa iya kare jikinsu.Nan da nan suka jigata ainun suka sha bakar wahala.Duk wanda ya kalli wadannan dodanni a lokacin da suke cikin wannan hali dole ya tausaya musu kuma babu abinda zai burge mutum face yadda suka nuna tsananin tausayinsu da kaunarsu akan jaruma Safirat.Sai bayan sun sha wannan muguwar wahala ne kwatsam suka hango dusar kankara a gabansu a bakin wani kogi.A guje suka karasa wajen wannan dodo dake goye da Safirat ya sauketa daga kan gadon bayansa ya turbutsata a cikin dusar kankarar ya binneta a ciki yabar iya fuskarta a waje sannan suka ja da baya suka tsuguna suka tsurawa gangar jikin Safirat idanu suna jiran tsammani,ba don komai ba kuwa sai saboda sunsan cewa idan Safirat ta shafe kamar rabin sa'a a cikin Dusar kankarar bata farfado ba to ta mutu kenan ba zata taba tashi ba.Koda rabin sa'a ta shafe kuwa sai zuciyoyinsu suka karaya suka fashe da matsanancin kuka kai kace mutane ne su ba dodanni ba.Cikin tsananin bakin ciki suka mike tsaye tamkar wadanda suka tashi daga zaman makoki suka nufi inda Safirat ke kwance da nufin su cirota daga cikin kankarar su haka kabari su binneta.Da isarsu gabanta ™Abubakar Haleefah Physicist™ wannan dodo ma'abocin goyonta yakai hannu da nufin ya zarota sai kawai yaga idanunta sun bude nan take ta yunkura ta taso zaune daga cikin dusar kankarar.Koda dodannin sukaga haka sai suka kaure da shewar farin ciki suka kama tsalle tsalle.Koda Safirat taga yadda wadannan dodanni ke murnar ganin ta rayu bata mutu ba sai itama ta kamu da tsananin farin ciki,nan take ta mike tsaye ta daka tsalle ta fada kan kirjin wannan dodo ma'abocin goyata suka rungume juna kuma sai suka fashe da kukan farin ciki.Saida suka dan jima a kankame da juna sannan dodon ya ajiyeta kasa tamkar ya ajiye yar tsana saboda kankantarta akan girmansa.Kawai sai Safirat ta dubeshi cikin murmushi tace waishin menene sunanka ne?Koda jin wannan tambaya sai mamaki ya kama dodon ya maida mata martani da murmushi yace,ke kuwa menene dalilin da yasa tuntuni baki san suna ba tun a farkon haduwarmu sai a yau? Sa'adda Safirat taji wannan tambaya sai ta sake yin murmushi tace saboda ayau ne na tabbatar da cewa kai masoyina ne na kwarai domin kuwa ban taba haduwa da mahalukin daya taba nuna mini tsantar kauna ba kamarka hatta masoyina sarki Safwan kuwa.Domin shi ya kasa hakuri da komai na duniya a kaina.kai kuwa gashi ka sallama rayuwarka don ceton tawa,kayi kuka ka zubar da hawaye saboda ganina a cikin mugun yanayi.Inda ace kai mutum ne kamarni da babu abinda zai hanani aurenka face mutuwa.Amma duk da haka zan nemi alfarma daya a wajenka inaso idan har na sami nasarar dauko kuttin kwarina zan fara karbar karagar mulkin Safwan na zama sarauniyar Birnin Kisra.A sannan ne nake son ka zama shugaban dakaruna ma'ana ka zama sarkin yakina amma lallai ka koma can mazauninku ka dauko matarka idan kana da ita.Idan kuma baka da mata to lallai kayi sabon aure.Koda Safirat tazo nan a zancenta sai dodon ya bushe da dariya yace suna nan Gargus kuma dama can nine mataimakon shugabanmu Bandaru,Ban taba aure ba amma saboda na faranta miki rai bayan kin cimma burinki zan koma can dajin tsaunin Lauhul Farras na auri daya daga cikin irin matayenmu.Ya shugabata ina ganin zaifi kyau mu nemi inda zamu kwana a cikin wannan daji tunda yanzu dare ya soma yi gashi babu hasken FARIN WATA.Kin sani cewa wannan daji na Sarkif yana da tsananin hadari kuma babu wanda yasan iyakar mugayen abubuwan dake cikinsa.Koda Gargus yazo nan a zancensa sai Safirat tayi murmushi tace na aminta da wannan shawara taka dari bisa dari.Nan take suka dunguma gaba dayansu suka kama neman inda zasu kwanta su huta kuma suyi bacci.Cikin sa'a kuwa basu dade ba suna nema suka sami wani kogon dutse.Saida suka shiga cikin kogon suka cajeshi tsaf suka tabbatar da cewar babu wani mugun abu a cikinsa.Sannan suka yiwa Safirat shimfida ta kishingida.A sannan ne Gargus ya shiga duba ko ina a jikin Safirat domin yaga yadda raunikan jikinta suke yayi mata magani.Bayan ya gama nazarin raunukan ne ya kwanto jakar guzurinsa ya ajiye a gabanta ya shiga yi mata magani a lokacin ne ta kura masa idanu ta shiga zancen zuci.Ba komai bane ya fado mata a rai face tunowa da cewar Gargus shine kadai namiji daya taba jikinta itama ta hada jikinta da nasa hatta sarki Safwan kuwa.Waishin yaushe ne zatayi aure ta sami mijin da zai iya sallama rayuwarsa domin tata kuma ta sami magaji tare dashi?Koda Safirat tazo nan a tunaninta sai hawaye ya zubo mata,takaici ya turnuketa ta sami irin wannan masoyi.Haka dai Safirat ta cigaba da wannan tunani har Gargus ya gama aikinsa bacci ya saceta bata sani ba.Safirat bata farka ba daga bacci saboda tsananin gajiya da jigata saida gari ya waye har rana ta kwalle.Tana farkawa taga tuni su Gargus sun nemo mata abin kalaci na yayan itatuwa kuma ga wani gasasshen tsuntsu a gefe daya a gabanta.Al'amarin daya bata mamaki kenan kuma ya burgeta ainun.Ba tare da wani bata lokaci ba sai Safirat ta mike tsaye taje ta wanke fuskarta da bakinta da hannayenta sannan tazo ta zauna ta kama cin abincin a lokacin da su Gargus suka koma gefe daya suka zazzauna kuma suka kau dakai ga barin kallonta saboda kawaici da girmamawa.Al'amarin daya kara bata mamaki kenan bisa ganin yadda wadannan dodanni sukeyin abubuwa na hankali,tunani da sanin ya kamata tamkar sun kasance bil'adama.Bayan Safirat ta kammala lakacinta ne ta dubi Gargus tace ina bukatar naje nayi wanka.Koda jin wannan batu sai idanun Gargus suka zazzago ya kamu da matukar tsoro ya dubeta cikin alamun firgita yace haba ya shugabata shin kin manta ne da irin tsananin wuyar da kika sha a yayin da mummunar macijiyar nan ta hadiyeki?Shin bakya tunanin cewa za'a iya samun wadansu mugayen halittun a cikin karkashin kogunan dake cikin wannan daji har da kike tunanin kije jiyi wanka a cikinsa?Sa'adda Safirat taji wadannan tambayoyi sai tayi murmushi tace kada ka damu yakai amintaccen sarkin yaki na na nan gaba.Kayi sani cewa ina ji a jikina cewar tunda har na sami nasarar shigowa cikin dajin nan kuma har na kawo i yanzu a raye to akwai alamun tabbacin samun nasara sai burina ya cika.Zo muje kayi mini rakiya izuwa bakin kogin da zanyi wanka.Koda gama fadin haka sai Safirat ta fice daga cikin wannan kogon dutse tana rataye da bakanta.Cikin hanzari Gargus ya take mata baya har saida suka iso bakin wata katuwar korama!!! KIBIYA RATSA MAZA!!! Littafi Na Biyu (2) Part D Har saida suka iso bakin wata katuwar Korama.Kawai sai Gargus yaga Safirat ta yunkura zata cire tufafin jikinta sannan ta shiga cikin koramar.Cikin hanzari Gargus ya dakatar da ita yace haba ya shugabata ai komai saurinki dai kya bari na fara tabbatar da lafiyar cikin koramar tukunna.Ki kula da kanki kafin na fito daga cikin karkashin wannan korama.Yana gama fadin hakan sai ya fada cikin wannan koramar yayi nutsu izuwa karkashinta.Saida ya kure nisan koramar gabas da yamma kudu da arewa ya tabbatar da cewa babu wani halitta mai numfashi a karkashin wannan korama sannan ya fito a jike sharkaf yana yarfe ruwan dake jikinsa sannan ya dubi Safirat yace ya shugabata babu komai a cikin wannan korama zaki iya shiga kiyi wankanki.Tana gama cire kayan jikinta ta fada cikin koramar ta fara wankanta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa tamkar a cikin gidansu na birnin Kisra take.A lokacin da Safirat ta fara wannan wanke hankalin Gargus yakai kan wannan baka wacce ke lullube cikin mayafi,kawai saiya kurawa bakan idanu yace a cikin ransa.Oh! Yanzu akan wannan abin ne hankalin kowa a duniya ya tashi,mu kanmu da mu kayi gadin wannan baka tun daga lokacin da Boka Saiham ya kawota kan Tsaunin Lauhul Farras dayanmu bai taba taba ta ba.Ai kuwa kamata yayi na tabata ko don na barwa kaina tarihi.Tunda dai shekaruna sun kai talatin da bakwai ko Safirat taga ina tabata ba zata zargeni bisa komai ba tunda tasan cewa ban isa na sarrafata ba.Gama fadar haka keda wuya sai dodo Gargus yaje gaban bakan ya yaye mayafin da aka lullubeta.Faruwar hakan keda wuya sai hasken bakan ya dallare wajen gaba daya kuma yayi tsiri yana mai nuni izuwa wata hanya.Baiyanar hasken ne ya janyo hankalin Safirat wacce ke a cikin korama ta juyo da sauri izuwa inda Gargus yake.Koda taga bakanta a hannunsa kuma hasken jikin bakan yayi nuni izuwa wani waje,sai tayi sauri ta fito daga cikin koramar ta sanya kayanta ta karbi bakan daga hannun Gargus sannan ta zare takobinta ta nufi inda hasken bakan keyi mata nuni.Cikin hanzari Gargus da sauran dodanni yan uwansa suka bita a baya suna mamakin yadda bakan yake yiwa Safirat jagora.Nanfa suka rinka shiga cikin sakuna na duwatsu da tsaunuka masu tsananin tsawo da duhu.In badon ma hasken jikin bakan ba da ba zasu iya bin hanyar ba.Duk inda suka shiga sai suga miliyoyin dakarun yaki masu tsananin kwarjini da ban tsoro na aljanu da dodanni masu wata irin siffar da kansu su Gargus basu taba sanin cewa akwai irinsu a doron kasa ba.Komai jarumtakar mutum idan yayi arba da wadannan miliyoyin dakaru dole ne ya firgita kuma yasan cewa komai hatsabibancinsa bai isa ya ratsasu ya wuce ba amma sai gashi Jaruma Safirat dasu Gargus na ratsawa a tsakiyarsu.Dakarun na gudu suna buya.Ba komai bane yake tarwatsa dakarun ba face wannan haske na jikin bakan Safirat domin konasu yakeyi suna narkewa su zama ruwa.Haka dai Safirat dasu Gargus suka cigaba da kutsawa a cikin wani makeken kogon dutse wanda girmansa yakai na birnin Kisra gaba dayansa.Duk inda mutum ya duba a cikin kogon babu abinda zai gani face kwarangwal na kawunan bil'adama da kafafuwansu da hannayensu,sai kuma beraye suna ta guje guje suna shige da fice a cikin ramuka alamar cewa sune suka cinye naman mutanen da suka rube a cikin kogon.Koda Safirat ta dubi Gabas da yamma kudu da arewa na cikin kogon wanda kamar bashi da karshe kuma taga ko ina kwarangwal ne tsubi tsubi har suna tsiri sama sai tayi ajiyar zuciya ta jiyo ta dubi Gargus tace,tabbas nan ne KOGON MUTUWA,Tana gama fadin hakan sai ta cigaba da bin hanyar da hasken bakanta keyi mata nuni tana bi ta kan kwarangwal tana takasu suna ruburbushewa.Su ma su Gargus suka cigaba da binta a baya suna tunkarar can saman kwarangwal tamkar suna hawan saman tsauni.Suna isa karshen tudun kwarangwalolin ne sukayi arba da wani dogon teburi wanda akayi da zallan shudin lu'u lu'u.A kasan sane suka ga an ajiye MAKAMAN YAKI iri iri wadanda gaba dayansu anyi su ne da karafa kala kala kuma kana ganinsu kasan cewa SIHIRTATTUN MAKAMAI ne.A tsakiyar wadannan makamai ne aka dora wani dogon tebur na zinare,akan teburin kuma aka aza kuttun KWARI na Bakan Safirat alamar cewa an fifitashi akan gaba dayan wadannan makaman yaki.Shi kansa wannan kuttun kwari wani irin sheki da walwali yakeyi yana kashe idanu.Koda Safirat tayi arba da wannan kuttun kwarin sai farin ciki ya lullubeta domin tasan cewa KARSHEN WAHALArta yazo.Cikin sauri ta tunkari inda aka ajiye kuttun kwarin domin ta dauka.Koda ya rage saura baifi taku goma ba kacal tsakaninta da kuttun kwarin sai kawai taga sarki Safwan ya baiyana tsulum a gabanta tamkar daga sama aka jehoshi.Fuskarsa a murtuke tana gatsinewa tamkar naman fuskar zai zazzago kasa saboda tsananin fushi.Hannunsa na dama na rike da wata azabgegiyar takobi,hannun hagu kuma na ruke da garkuwa.Kawai sai ya dubi Safirat ya daka mata tsawa yace yake babbar abokiyar gabata kiyi sani cewa a can dajin tsaunin Lauhul Farras munyi RAGAS,har kika sami damar guduwa bayan kin dauki bakanki.To ki sani cewa anan kogon mutuwa dole ne dayanmu ya sami nasarar kashe daya.Idan nine na samu nasarar kasheki na rantse da kabarin ubana saina wulakanta MATAN DUNIYA fiye da yadda kika yi niyar wulakanta maza saina sa mata sun rinka kashe kansu saboda bakin cikin da zan rinka cusa musu wanda zasu gwammace mutuwarsu fiye da rayuwarsu.Idan kuma kece kika sami nasarar halaka ni saiki aiwatar da abinda kikayi niyya akan MAZAJEN DUNIYA.Koda jin wannan batu sai su Gargus suka taso da gudu da nufin su afkawa sarki Safwan ™Abubakar Haleefah Physicist™ amma sai ya nunasu da garkuwarsa take suka kame a inda suke suka zama gumaka!Koda ganin haka sai Safirat ta fusata ainun ta kurma uban ihu kuma ta ruga izuwa kan sarki Safwan suka ruguntsume da masifaffen,azab abben yaki mai tsananin ban tsoro da ban al'ajabi. WAYE ZAI SAMI NASARA A WANNAN YAKI TSAKANIN JARUMA SAFIRAT DA SARKI SAFWAN HAR YA MALLAKI KWARI DA BAKAN YA CIMMA BURINSA? SHIN SU DODO GARGUS SUN HALLAKA KENAN KO KUWA ZASU RAYU? INA LABARIN SAURAN SARAKUNA,MATSAFA DA JARUMAN DAKE FARAUTAR WANNAN KWARI DA BAKA NA SAFIRAT? SHIN SUMA SUNA NAN BIYE DA SAFIRA A CIKIN DAJIN MUTUWA? YAUSHE NE SAFIRAT ZATA CIKA BURINTA NA MAISHE DA MAZA BAYIN MATA A DUNIYA? Mu Hadu A "KIBIYA RATSA MAZA Littafi Na Uku Don Jin Cigaban Wannan Kasaitaccen Kayataccen Labari. Don't Just Read And Pass,Liking And Commenting Necessary. End Of Book 2.Sai Mun Hadu A Book 3 Insha Allah. °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!! Littafi Na Uku (3) via nasir shehu teerlow Part A LOKACIN DA AKA RUNGUNTSUME DA AZABABBEN YAKI mai matukar ban tsoro da ban al'ajabi tsakanin jaruma Safirat da sarki Safwan sai gaba dayan dajin na kogon mutuwa ya kama girgiza.Kasa ta rinka tsagewa bishiyoyi suka rinka kakkaryewa suna zubewa kasa,duwatsu kuwa suka rinka mirginawa suna murkushe yan uwansu da sauran bishiyoyi.Duk wani abu mai rai dake cikin wannan daji na sarkif saida ya dimauce ya fita daga haiyacinsa a wannan rana amma su manyan giwayen biyu wato jaruma Safirat da sarki Safwan ko kadan basu damu da halin da dajin ke ciki ba,kowannensu idanunsa sun rufe bai ma san yanayin da dajin ke ciki ba kawai kokari yake yaga ya kashe abokin fadansa domin ya kare martabarsa kuma ya cika burinsa.Bisa wannan dalili ne suka rinka kaiwa junansu sara da suka cikin bakin zafin nama kuma da dukkan karfinsu.Duk wanda yaga yadda wadannan abokan gaba ke kawai junansu mugayen hare hare dole ne ya firgita saboda kuskure kankani gaba dayansu na nufin Ajalinsa.Saida Safirat da Safwan suka shafe sa'a daya da dakika dari bakwai da sittin suna fafatawa wannan masifaffen yaki ba tare da dayansu ya sami nasarar lakutar jikin daya ba.Wani lokacin sai kaga faduwa suke kasa amma sai suyi wuf su sake mikewa su cigaba da gumurzu,a hakane suka jigata ainun babu shiri suka ja da baya sukayi cirko cirko suna kallon juna suna haki a wannan lokaci ne kowannensu ya tabbatar da cewa lallai karfin damtsensu,iya yakinsu da karfin sihirinsu yazo daya,don haka sai kowannensu ya fara tunanin hanyar da zaibi ya sami nasarar kashe abokin fadan nasa.Bayan sunyi kallon kallo gami da tunani da nazari na tsawon yan dakiku sai suka rugo da gudu izuwa kan juna a lokaci guda tamkar hadin baki suka kacame da yakin suka hada da kaiwa junansu naushi da bugu,faruwar hakan keda wuya labari yasha bambam domin a sannan ne kowannensu ya fara samun nasarar cutar da abokin gwaminsa.Da zarar Safwan ya sami nasarar gabzawa Safirat Naushi a fuskarta ta furzar da jini daga cikin bakinta,kafin ya sake kara mata wani naushi ko yakai mata sara sai kaga tuni itama ta rama naushin da yayi mata jini na feshi daga bakinsa.A hakane kowannensu ya sami nasarar yankar dan uwansa har sau bakwai bakwai.Sai gashi jini na zuba a sassan jikinsu,jiri na dibarsu,suna maye daga tsaye tamkar sun sha giya sun bugu,duk wanda ya dubesu a wannan lokaci dole ne ya tausaya musu domin gani zaiyi kamar gawace taki rami domin a koyaushe zasu iya rasa rayukansu.Har izuwa wannan lokaci dodo Gargus da sauran yan'uwans dodanni a kame suke cikin matsayin gumaka dayansu bai kara motsawa ba.Ana cikin wannan bakin yamutsi ne Safwan ya Shammaci Safirat ya gabza mata wawan naushi a ciki take ta sunkoyo da kanta kas a lokacin da taji cikinta yayi muguwar kullewa.Safwan yasa kafarsa ya doki habarta saboda karfin dukan saida tayi tsalle sama ta fado kasa tim ta baje kasa magashiyan a cikin wani irin mugun yanayi mai kama da suma.Koda Safwan yaga ya sami wannan nasara sai ya sake dako tsalle a sama ya dira a gabanta yana mai raba kafafunsa kuma ya dubeta cikin murmushi irin na mugunta da farincikin samun nasara.Kawai saiya daga takobinsa sama da hannayensa biyu da nufin ya caka mata takobinsa a cikinta.Ba zato ba tsammani sai kawai yaji Safirat ta doki fuskarsa da tafin kafarta ta dama da dukkan karfinta,saboda karfin dukan saida shima yayi sama bayansa ya je ya gwaru da wani dutse kuma ya fado kasa bisa fuskarsa.Take fuskar tasa ta daddauje tayi face face da jini,da kyar ya mirgina gefe daya yana numfashi sama sama kuma ya kasa yunkurin mikewa domin ji yayi kamar kasusuwan bayan nasa sun kakkarye sakamakon muguwar buguwar da yayi da dutsen.Cikin tsananin juriya Safirat ta yunkura ta mike tsaye taje har izuwa kan sarki Safwan tasa hannunta ta lakuci jini dake kan fuskarsa taje ta shafa a jikin Gargus wanda ya kasance gunki.Faruwar hakan keda wuya sai Gargus ya dawo cikin ruhinsa ya juya da sauri ya rinka shafar yan uwansa suma sai ruhinsa ya dawo.Koda Gargus ya gama shafar dukkanin yan uwansa sai ya ruga da gudu izuwa inda sarki Safwan yake kwance da nufin ya karasa kashe shi,amma sai Safirat ta daka masa tsawa ya tsaya cak kuma ya juyo ya dubeta cikin mamaki yace haba ya shugabata ya zaki hanani kashe wannan babban makiyi naki?Ki dubi irin mugayen raunikan da yayi miki kuma ki tuna cewa barinsa a raye hadari ne babba domin a koyaushe karfin jikinsa zai iya dawowa ya cutar damu.Maimakon Safirat tace wani abu sai ta taka kafafunta da kyau ta nufi inda kuttun kibiyoyin yake tana tangadi kamar zata fadi.Tana isa wajen sai ta dauki kuttun ta ratayashi a bayanta.Faruwar hakan a bayanta.Faruwar hakan keda wuya sai wani irin haske mai karfin gaske ya haskake kogon gaba daya yadda ko allura ce ta fadi kasa sai idanu sun gani kuma nan take Safirat taga duk raunikan jikinta sun dinke kansu sun daina zubar da jini,wasu ma sun zama sai tabo tamkar tafi wata uku da samunsu.Safirat taji wani irin gagarumin karfi ya shiga jikinta irin wanda bata taba jinsa ba a rayuwarta domin ji tayi kamar ko duniyar gaba daya aka aza mata a ka zata iya dakonta.Kawai sai ta daka tsalle sama sai gani tayi tayi sama sosai tamkar fikafikai ne a jikinta har tana wani irin shawagi a saman kogon cikin matsanancin karfin gudu tamkar tauraruwa mai wutsiya domin a cikin dakika biyu ta kewaye kogon gaba daya sau goma sha biyu.Hatta sarki Safwan bai san sa'adda ya wangame baki ba yana kallonta a saman cikin tsananin al'ajabi duk da cewar yana cikin mugun yanayi,kawai sai yaga Safirat ta dira a gabansa,karfins a saukarta ya haddasa ™Abubakar Haleefah Physicist™ karamar girgizar kasa tamkar giwace ta diro.Safirat ta dubi Safwan cikin murmushi zuciyarta cike da dumbin farinciki tace na cika burina na mallakan KWARI DA BAKAn mahaifina,ka daina tunanin cewa kasheka zanyi,ina amfanin rayuwa idan babu abokin gaba?Ta yaya zan iya cusa maka bakin ciki idan baka raye?Koda gama fadin hakan sai tayi nuni da hannunta izuwa kan sarki Safwan take wata murtukekiyar sarkar tsafi ta daure hannayensa da kafafunsa.Safwa n yayi iya kokarinsa ya kwance kansa da karfin nasa na sihiri amma saiya kasa.Koda ganin haka sai Safirat ta bushe da dariyar mugunta tace ai yanzu a duk fadin duniya babu wani sihirin tsafi daya kai nawa babu wani jarumi da zai kaini jarumtaka.Babu wani aljani da zai fini karfin gudu ko sauri daga yau duniyar nan kaf zata zamo tamkar kwayar hatsi a kan tafin hannuna sai yadda naso zanyi da mutane da aljanu,kai sarki Safwan yanzu zansa ayi maka magani domin ka warke sosai sannan na sanyaka a cikin keji tamkar dabbar dawa na tafi dakai izuwa birnin Kisra a wulakance domin ya zamo izina ga kowa.Zan haye karagar mulkinka na sauke dukkanin fadawanka na sanya mata madadinsu,zan kafa sababbin dokoki ga ma'aurata yadda maza su zamo bayin mata,sauran sarakuna,jaruma i da matsafa kuwa wadanda suka biyo mu izuwa cikin wannan daji domin su rabani da wannan kwari da baka nawa zakaga yadda zanyi dasu.Koda gama fadin hakan sai Safirat ta dubi Gargus tace dashi maza a yiwa sarki Safwan magani.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya baibaye Gargus da sauran yan uwansa dodanni suka rude da shewar gurnani irin tasu ta dodanni cikin matukar farin ciki suna yiwa Safirat jinjina suna cewa tabbas kin cika burinki kin zama SARAUNIYAR DUNIYA!!! Ba tare da bata wani lokaci ba Gargus yaje ya dinke raunikan jikin sarki Safwan yasa masa magani a lokacin da sarki Safwan ya kamu da mugun bakin ciki hawayen takaici suka zubo masa a lokacin da zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone,aikuwa Gargus na gama yi masa magani sai yayi amfani da sarkar dake hannunsa ya shake kansa da kansa domin ya mutu ya huta da bakin ciki.Koda ganin haka sai Safirat ta sake nunashi da hannunta na hafu take ya saki wuyan nasa wato ya daina shake kansa a lokacin dayaji an zare gaba dayan lakar jikinsa hannayensa sukayi kasa sharaf yaji ko dagasu bazai iya karawa ba bare ya sake yunkurin kashe kansa.Take Safirat ta sake yin tsafi saiga sarki Safwan a cikin wani keji bisa keken doki,Gargus da sauran yan uwansa dodanni basu san sa'adda suka bushe da dariya ba,bisa ganin yadda sarki Guda mai daraja kamar Safwan ya zamo tamkar dabbar daji.(Hmm Gaskiya Safeerat taci mutuñcin Safwañ).Safirat ta dubi Gargus cikin murmushi tace kamar yadda nayi alkawari daga yau ka zama shugaban dakaruna na yaki,wadannan sauran yan uwanka kuwa wadanda muka sha bakar wahala tare da sun zama mataimakanka,ya nzu zamu fita daga cikin wannan daji muje mu fuskanci dubunan jama'ar dake jiranmu a wajensa.Kada dayanku yayi yunkurin yakarsu ba zamu yake su ba da kansu zasu gudu su barmu kuma akwai sakon da nake son na basu.Koda gama fadin hakan sai Safirat ta hau keken dokin da kejin sarki Safwan ke kai ta sakarwa dokin linzami sukayi gaba.Cikin hanzari su Gargus suka take mata baya a guje shi kuwa sarki Safwan dake cikin keji a wulakance babu abinda ya iyayi face cigaba da zubar da hawayen takaici.Kafin su nufi wajen wannan daji na sarkif Safirat ta goya kwari da bakanta a bayanta kuma ta lullube su da wannan bakin mayafin har saida ta fara hango DANDAZOn masu farautarta sannan ta yaye mayafin data lullube kwari da bakan ta ajiye shi a kusa da ita.Koda sauran sarakuna,matsaf a da manyan jaruman duniya suka hango jaruma Safirat daga can nesa ga hasken kwari da bakanta na dallare musu idanu sai hankalinsu ya dugunzuma kuma tsoro ya baibayesu,sarki n Misra ya dubi sauran sarakunan yana mai rike kansa da hannayensa biyu yace shikenan ta faru ta kare Safirat ta sami nasarar hada kwari da bakanta gwara ma kuzu mu gudu tun kafin ta karaso nan domin mu tsira da rayukanmu.Gama fadin hakan keda wuya sai sarkin Misra ya yunkura da nufin ya kada linzamin dokinsa amma sai bokan birnin Yemen yayi sauri ya riko dokinnasa yace yakai wannan sarki menene amfanin gudun da babu tsira,to ka sani cewa koda ka tserewa Safirat a yanzu to nan gaba zata riskeka har birninka ta sauke ka daga kan karagarka ta wulakantaka ta maisheka bawa,shin ka zabi ka zama hakan ko kuwa zaka tsaya yanzu mu hada kai mu kwatarwa kanmu yancinmu?Koda jin wannan tambayoyi sai jikin sarkin Misra yayi sanyi ya fasa guduwa suka cigaba da zuba idanu suna jiran isowar Safirat.Koda Safirat ta matso kusa kowa yaga sarki Safwan daure a cikin keji kuma da Safirat rataye da kwari da bakanta a bayanta sai aka dada firgicewa aka tsorata da al'amarin Safirat ainun.Koda ya rage baifi taku bakwai ba tazarar dake tsakanin Su Safirat da wadannan sarakuna,jaruma n da matsafa masu farautarta sai taja linzamin dawakan keken dokin.Take dawakan suka yi turjiya suka tayar da kura aka tsaya ana kallon kallo tsakanin Safirat dasu har izuwa yan dakiku.Daga can sai Safirat ta dube su cikin nutsuwa tace yaku wadannan sarakai,matsafa da manyan jarumai kuyi sani cewa zakaran da Allah ya nufa da cara tofa ko ana muzuru ana shaho sai yayi abinda kuke ta farautarsa kukeson ku rigani mallakarsa gashi na riga ku mallakar abina,idan a cikinku nan akwai wanda yake ganin cewa zai iya yakata a yanzu domin ya rabani da kwari da bakana to ya jarraba,amma fa ya sani cewa HUKUNCINsa KISA ne.Idan kuma babu wanda zai jarraba yakata a cikinku to ina da shawara gami da sako a gareku gaba daya.Shawarata itace ™Abubakar Haleefah Physicist™ dukkanin sarakunan cikinku da zarar sun koma gida suyi murabus su baiwa matayensu karagarsu,daga sannan kuma su zamo sune masu yin aikin gida kamar yadda mata keyi kuma ko a kan shimfidar ne duk namijin daya zamo bisa matarsa hukuncin kisa ya tabbata a kansa.Kafin Safirat ta gama rufe bakinta tuni sarkin kasar Yamen ya tari numfashinta yana mai daka mata tsawa yace ke yarinya karyarki tasha karya,na rantse da darajar iyayena da kakannina baki isa ki sauya yanayin da duniya ke ciki ba tunfarkon wanzuwarta kawo iyanzu,ina mai tabbatar miki da cewa dole ne maza su zamo gaba da mata don haka ko a yanzu kin sami nasarar aiwatar da nufinki da karfin wannan kwari da baka na mahaifinki,ina mai tabbatar miki da cewa nan gaba sai an sami jarumin da zai dakatar dake koma ya kawar dake gaba daya.A yanzu da ranmu da lafiyarmu ba zamu zuba ido ba muna ji muna gami ki zubar mana da kimarmu da mutuncinmu ba,gama fadin hakan keda wuya sai sarkin Yemen ya umarci dakarunsa na yaki dasu afkawa Safirat su kasheta su dauko masa kwari da bakan nata.Kafin Sarkin Yemein ya gama rufe bakinsa tuni dakarun nasa kimanin su dubu uku sun zare takubba sun sakarawa dawakansu kaimi suna masu kwarara ihu gami da kururuwa sukayi kan jaruma Safirat,ita kuwa saita zaro kibiya guda daya jal daga cikin kuttun kibiyoyin nata ta dana shi a kan bakan ta jashi ta tabe sannan ta saki harbi.Take kibiyar ta fita daga cikin bakan a wani irin azababben gudu da karfi.Kafin daya daga cikin dakarun su dubu uku ya riski Safirat a inda take tsaye tuni kibiyar ta fasa kirazansu su duka sun zubo kasa daga kan dawakansu matattu.Wannan abu ya faru ne a cikin abinda bai wuce dakika biyar ba kuma nan take kibiyar ta dawo da kanta izuwa jikin bakan Safirat ta sake dana kanta.Koda sauran sarakuna,matsaf a da jarumai sukaga abinda ya faru sai dukkaninsu suka firgice basu san sa'adda suka zube kasa ba daga kan dawakansu suna masu yin mubaya'a shi kuwa sarkin Yemen tuba ya kamayi bisa kuskuren da yayi na tura mata dakarunsa su kasheta.Shi kuwa Sarkin Misra saiya mike tsaye ya matsa kusa da Safirat ya risina cikin girmamawa sannan yace yake wannan JARUMAR JARUMAI ki tuna cewa mahaifinki 'da namiji ne don haka bai kamata ki wulakanta maza ba,ina mai rokonki daki janye nufinki na mayar da maza bayin mata.Koda kuwa zaki raba mu da matsayinmu na mulki.Koda sarkin Misra yazo nan a zancensa sai Safirat ta bushe da dariya sannan tace tabbas ina girmama mahaifina amma ka sani cewa sarki dan uwanka ne ya zama sanadin mutuwar ubana,kuma shine namiji na farko wanda na baiwa zuciyata amana,amma sai gashi yaci amanar tawa yayi mini butulci kamar yadda ubansa ya yiwa ubana butulci,bisa wannan dalili ne nayi rantsuwa akan cewa saina dauki fansa akan mazajen duniya,rantsuwa bata tashi face na cikata don haka babu wata alfarma da zan iyayi muku akan wannan al'amari.Kuje ku isar da sakon dana gaya muku ga sauran yan uwanku sarakunan duniya,idan kuma har yanzu akwai wanda yake ganin zai sake jarraba sa'arsa akaina toga fili ga mai doki.Koda jin haka sai gaba dayan jama'ar suka sake zubewa kasa suna masu nuna mubaya'arsu.Saf irat na ganin haka sai ta bushe da dariya ta sakarwa dokinta linzami tayi gaba su Gargus na take mata baya har saida suka kule a cikin dajin sannan kowa ya kama hanya don tafiya garinsa cikin tsananin bakin ciki da sanyin jiki.Lokacin dasu Jaruma Safirat suka iso wata mararrabar hanya sai suka tsaya Safirat ta dubi Gargus tace yanzu ka tafi izuwa can inda jama'arku suke ka auro mace da zamu tafi da ita izuwa can birnin Kisra inda zamu ci gaba da rayuwa.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya kama Gargus ya zube kasa yayi godiya sannan yace ya shugabata kafin naje na dawo nan zai iya daukata kwana uku Shin zaku ci gaba da jirana ne a nan ko kuwa zaku wuce izuwa can birnin Kisra na riske ku a can?Koda jin haka sai Safirat tayi murmushi tace matsayinka a wajena ya wuce na tafi na barka dole ne na jiraka idan ma kana so zan iya raka can din.Gargus yace ai ke yanzu kin zama sarauniyar duniya don haka idan kikayi gaba baza zakiyi baya ba,na yarda zaku iya yada sansani anan din kuma zan gaggauta tafiya can wajen jama'ar tamu na auro mata,na barki lafiya sarauniyar duniya.Koda gama fadin hakan sai Gargus ya yiwa Safirat sallama ya juya da sauri ya falfala da azababben gudu izuwa cikin daji.Kafin kiftawar ido ya kule.Nan take Safirat ta dubi sauran dodanni ta basu umarnin a kafa tanti. Liking an °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!! Littafi Na Uku (3) Part B TA BADA UMARNIN A KAFA TANTI.Nan take kuwa aka kafa mata tanti akayi mata shimfida a ciki tayi kwanciyarta ta kama bacci ba tare da fargabar komai ba a lokacin da dodannin suka kewaye tantin don tabbatar da tsaro. *Al'amarin sarki Safwan kuwa a cikin wannan keji aka barshi a kulle kuma a daure,dare yayi ko ruwa ba'a bashi yasha ba saida Safirat ta farka daga dogon baccin data sha bayan ankawo mata abinci da abin sha tayi hani'an sannan ta tuno da batun sarki Safwan.Nan take Safirat ta dauki Ayaba guda ta tafi izuwa wajen tantin ta isa inda sarki Safwan yake,da isarta bakin kejin da sarki Safwan ke ciki ta ganshi a kwance ya takure jikinsa yana karkarwar dari sai taji ta kamu da tausayinsa amma data tuna cewa ranta fa yake nema sai zuciyarta ta kekashe ta doki kejin da hannunta.Safwan ya mike a firgice zumbur kawai sai yaga Safirat tsaye a gabansa ruke da ayaba tanayi masa wani irin murmushi na mugunta.Kawai sai ta cire ayabar guda daya ta cilla masa ita cikin kejin

Chapter 4 of 8