Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
gareshi suka tari juna suka ruguntsume da masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro da ban al'ajabi domi kuwa kowannensu yana kai sara da suke ne cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta.Da farko sai yakin ya nuna kamar karfin damtse yazo daya,domin saida suke shafe kusan dakika dari da ashirin sunayin bakin gumurzu ba tare da dayansu ya sami nasarar koda lakutar jikin daya ba,amma kuma sai kwatsam akaga Safirat ta fara yin wata irin gagarumar jarumtaka taban al'ajabi ya zamana cewa tana tashi sama kamar tsuntsuwa tana shawagi akan Hidaisu tana kai masa mugayen hare hare cikin bakin zafin nama daya ninka na farko sau uku,wurin ya dare jini yayi feshi,Hidairu ya kurma uban ihu sakamakon tsananin zafi da zogin da yaji amma saiya taso a fusace ya kawai Safirat wani mugun sara,saura kiris ya zabtare Mata Allon kafadarta ta dama,amma saita goce takobinsa ta sari iska ita kuma ta daka tsalle sama ta jera masa lugudan naushi da kafarta a fuskarsa da kirjinsa sau goma sha biyu,Tun Hidairu na layi daga tsaye kamar wanda yasha giya ya bugu sai kawai akaga ya bingire kasa sumamme.Koda ganin abinda ya faru sai gaba dayan fadawa da dakarun yakin kasar suka zube kasa bisa guiwoyinsu suna masu mika wuya ga Safirat.Nan fa Farin ciki ya lullube Safirat tayi nuni da hannunta izuwa can inda aka daure mahaifiyarta dake dirkar da aka daureta a jiki ta jijjigo daga cikin kasa gaba dayanta ta taso a sama tazo gaban Safirat.Cikin tsananin farin ciki Safirat da Mahaifiyarta suka rungume junansu daga can sai Safirat ta dubi Dakarun tace a kirawo likita ya yiwa Hidairu magani sannan a kama shi shida sarki Safwan akai su kurkuku a kulle.Koda jin wannan batu sai Gargus ya dubi Safirat cikin alamun tsananin damuwa yace haba ya shugabata ya zaki bar makiyanki a raye,ba kya tsoron nan gaba su cutar ™Abubakar Haleefah Physicist™ dake?Koda jin wannan tambaya sai Safirat tayi murmushi tace ai idan na kashe su ban more ba,burina shine bakin ciki da takaicin yadda rayuwarsu take ya zamo Ajalinsu.Gama fadin hakan keda wuya saiga jama'ar gari mata da maza suna firfitowa daga cikin gidajensu,manya da yara babu wanda ya rage.Koda ganin haka sai Safirat ta tashi sama kamar tsuntsuwa taje ta dira akan babbar ganuwar dake fuskantar jama'a akayi tsit tamkar mutuwa ta gifta.Adaidai wannan lokaci ne Safirat tayi gyaran murya tace yaku jama'ar birnin Kisra kuyi sani cewa yau ni Safirat 'ya ga marigayi Boka Saiham na zamo GAGARABADAU a wannan nahiya tamu gaba daya kuma da sannu zan zamo SARAUNIYAR DUNIYA!Tabbas na cika burin mahaifina domin na sami daukakar da babu wani mahalukin daya sameta a wannan zamani ina so ku sani cewa sarkinmu na da wato mahaifin sarki Safwan shine ya kashe mahaifina saboda kawai mahaifina ya sana'anta abinda da babu kamarsa.Bayan nan kuma sai dansa Safwan ya shiga farautar rayuwata domin ya kashe ni ya mallaki wannan kwari da baka.Haka kuma manyan sarakunan duniya suka hado dakarun yaki suka fito farautata domin su mallaki kwari da bakana bisa son zuciyarsu,duk wanda ya mallaki wannan kwari da baka zai gabatar da mulki ne na zalunci.Kowa yasan tsakanina da sarki Safwan domin tun muna yara mukeyin SOYAYYA amma sai gashi yayi mini butulci saboda son duniya,yayi kokarin hallakani da kuma rabani da abinda mahaifina ya shafe shekaru kusan arba'in a cikin kogon tsafi yana kirkirarsa.Wannan ya tabbatar mini da cewa maza azzalumai ne kuma ba yan goyo bane,saboda haka daga yau namiji ya daina mulki a nahiyar nan gaba daya,a yau dinnan zan hau karagar mulkin Birnin Kisra na zama Sarauniyarku.Gaba daya fadawan kasar nan zan tuje musu rawaninsu na baiwa mata.Duk namijin da yake da adawa akan wannan batu to ga fili ga mai doki ya fito mu fafata.Hatta dakarun da zasuyi tsaro a birnin nan daga yau mata ne.Koda Safirat tazo nan a jawabinta sai mata suka rude da shewa gami da tafi suka kama yiwa Safirat jinjina da kirari,wuri ya hautsine,maza kuwa sai hankalinsu ya DUGUNZUMA ainun suka rasa abinda yake musu dadi,nan take aka cika umarnin Safirat aka kai sarki Safwan da wazirinsa Hidairu izuwa kurkuku aka kulle.Koda Hidairu yaga an kulleshi a cikin kurkuku saiya fara kokarin amfani da sihirin tsafinsa domin ya balla kofar dakin da aka kulle su a ciki amma sai sihirin yaki yayi tasiri.Al'amarin da yayi matukar fusata shi kenan ya wangame bakinsa ya kwarara uban ihu cikin tsananin takaici sannan ya fashe da kukan bakin ciki,kawai sai yaji sarki Safwan ya bushe da dariya,cikin kaduwa da mamaki Hidairu ya dubi Safwan yace menene kuma amfanin wannan dariya taka alhalin ni da kai duk tamu ta kare.Sa'adda Safwan yaji wannan tambaya sai yayi shiru ga barin dariyar ya dubi Hidairu cikin nutsuwa yace wannan duniyar da muke ciki ce ta burgeni saboda tana nunawa mutum sakamakon abinda ya aikata ya gani da ransa da idanunsa.A hankali mahaifina ya yaudari Boka Saiham kuma yaci amanarsa ya kashe shi don kada ya mallaki wannan SIHIRTACCIYAR KWARI DA BAKA amma a karshe shima mahaifin nawa ya rasa tasa rayuwar,kuma bukatarsa bata biya ba ni ma gashi na yaudari Safirat naci amanarta bukatata bata biya ba,kau ma kuma gashi kaci amanata bukatarka bata biya.Yau dana karbi soyayyar Safirat na aureta a matsakin ABOKIYAR RAYUWA ta da yanzu kuwa na zauna cikin kwanciyar hankali kuma da yanzu ban janyowa sauran sarakunan duniya bala'in da suke fuskanta ba.Koda sarki Safwan yazo nan a zancensa sai ya fashe da kuka na bakin ciki da nadama.Yana cikin wannan hali ne yaji Waziri Hidairu ya dafa kafadar a lokacin daya mike zaune da kyar sakamakon zogin da raunikan jikinsa keyi masa.Sarki Safwan ya juyi ya dubi Hidairu yace me kake son ka gaya mini alhalin kaci amanata kuma ko alamar nadamar yin haka babu a tare da kai. ¶TRIPLE Ŷ Hidair ya gyada kai yace ai ita nadama a cikin zuci take indai ta gaskiya ce ba sai na nunata a zahiri ba,abinda zan sanar dakai shine ka kwantar da hankalinka ka sani cewa komai nisafan jifa kasa zai fadi.Tun farko duniya kawo i yanzu namiji ne bisa mace don haka koda Safirat ta sami nasarar aiwatar da wannan cin zarafi a garemu mazan duniya a yanzu to akwai lokaci da zaizo alkadarinta ya karye,ina mai tabbatar maka da cewa dole ne wata rana sai ta dawo karkashin 'da namiji tunda dai 'ya mace akayi ta su kuwa mata sun kasance masu rauni a kanmu.Yayin da Hidairu yazo nan a jawabinsa sai jikin sarki Safwan yayi sanyi kuma ya kurawa Hidairu idanu yana tunanin da nazari daga can saiya kyalkyale da dariya yace. Sai mun hadu a part B. LIKING AND COMMENTING NECESSARY. °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!! Littafi Na Hudu (4) Part B. SAIYA KYALKYALE DA DARIYA YACE,yakai abokina kayi sani cewa na sauya shawara bisa hukuncin dana yanke akanka wanda ke cikin zuciyata da nayi niyar na kashe ka a nan a cikin kurkukun sannan na kashe kaina domin mu huta da takaicin wulakancin da Safirat zata cigaba da yi mana har izuwa karshen rayuwarmu,amma a yanzu dakayi mini wannan jawabi sai na gane cewa lallai akwai bukatar muyi hakuri mu jira lokacin da wani jarumi zai zo ya share mana hawayen bakin cikinmu.Koda gama fadin hakan sai sarki Safwan ya rungume Hidairu suke bushe da dariyar mugunta a lokaci guda,adaidai wannan loka cine sukaji birnin ya kaure da kade kade da bushe bushe da kuma raye raye alamar cewar an fara gudanar da bikin nadin sarauniya Safirat.Saida aka kwana ana bidiri a cikin birnin Kisra mata sukayi ta sharholiyarsu suna cin zarafin mazajensu sai yadda sukayi dasu wato suka rinka juya su tamkar waina a kas,Daga wannan rana maza suka zama bayin mata mace batayin komai saidai ta kwanta taci tasha.Amma hatta aikin gida mazajensu keyi musu saidai idan mijin ya kasance attajiri ne ya debo maza bayi su yiwa matarsa aiki.Duk laifin da mace ta yiwa mijinta tayi a banza amma da zarar namiji ya yiwa matarsa laifi nan take za'a yanke masa hukunci mai tsauri.Ko'a ci shi tara mai yawan gaske ko kuma a dina masa watanni ko shekara a gidan wakafi.Haka dai sarauniya Safirat ta cigaba da gudanar da mulki wanda babu adalci a cikinsa ko kadan ya zamana cewa rayuwar maza ta shiga kunci,takaici da bakin ciki,kai sai dama takai cewa sarauniya Safirat na kwace dukiyar mazaje tana dankawa matayensu suna juyata saidai a rinka sam musu wani abu daga cikin abinda aka samu.Duk wani aikin karfi kona wahala maza ke yinsa a cikin birnin Kisra,yara da tsofaffi ne kadai basa fuskantar wannan wulakanci na sarauniya Safirat.Bisa wannan dalili ne mazajen birnin wadanda ba zasu iya jure wannan wulakanci ba suka fara sulalewa suna yin Hijira a sirrance ba tare da an sani ba suka rinka hakura da matansu,yayansu da dukiyarsu.Wadansu matan da suke matukar kaunar mazajensu sai suka rinka binsu suna gudu tare.Koda sarauniya Safirat ta gano hakan sai tasa aka datse duk hanyoyin fita daga garin ya zamana cewa babu mai fita sai an bincike shi an tabbatar da cewar ba hijira zaiyi ba.A cikin sati uku kacal sarauniya Safirat ta sauke gaba dayan yan majalisar kasar,hakimai,dakatai da masu unguwanni akan mukamansu ta dora mata a kai.Sannan kuma ta tara dakarun yaki na mata gudu dubu dari bakwai da saba'in da bakwai,Gargus ne ya baiwa wadannan mata horon yaki mai tsananin gaske naban al'ajabi kuma sarauniya Safirat ta basu sirrikan tsafi don kare kansu gami da zama jajurtattu.Bayan sarauniya Safirat ta tabbatar da cewa wadannan dakarun yaki nata guda dubu dari bakwai da saba'in da bakwai sun sami cikakken horon yaki irin wanda take so sai ta tashi manzo da wasika izuwa birnin Misra.Da rana tsaka sarkin Misra na zaune a fada tare da dukkan fadawansa da sauran mutanen gari ana tafiyar da harkokin mulki kamar yadda aka saba saiga manzo daga birnin Kisra wadda ta kasance mace ce a cikin gagarumar shigar yaki bisa wani bakin ingarman doki.Saboda isa da jin kai har cikin tsakiyar fadar badakariyar ta shigo da dokinta dakaru na kallonta amma aka rasa wanda zai taka mata birki har ta iso kusa da sarki ya zamana cewa tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku goma sha ba sannan ta sauko daga kan dokinta ta dan risina kadan ga sarki sannan ta dago kai ta dubeshi cikin nutsuwa ba tare da shakkar komai ba tace sunana Lubbatu daya daga cikin dakarun yakin sarauniya Safirat ta birnin Kisra,ni manzo ce a gareka ta bani wasika na kawo maka kuma tana bukatar amsar wasikar yanzu domin na kai mata.Koda jin wannan batu sai hankalin kowa a cikin fadar ya dugunzuma ainun saboda rashin sanin abinda wasikar ta kunsa,shi kuwa sarki sai yayi murmushi sannan ya dubi Lubbatu cikin gadara yace fito da wasikarki ki karanta a fili kowa yaji abinda ta kunsa.Ba tare da gardamar komai ba kuwa sai Lubbatu ta zura hannu cikin aljihun sulkenta na yaki ta dauko zungureriyar wasika ta warware ta sannan ta fara karanta sakon dake cikinta a fili kamar haka:Takarda daga hannu sarauniya Safirat mai kasar Kisra wacce ke shirin zama sarauniyar duniya kaf.Zuwa ga sarkin birnin MisraIna mai sanar da kai cewa nan da cikar kwanaki kadan zanzo kasarka tare da dakaru na mutun dubu dari bakwai da saba'in da bakwai kacal wadanda gaba dayansu mata ne zalla da zarar na iso ina so kazo kayi mubaya'a a gareni domin na sauke ka daga kan karagarka sannan nayi binciken mace data dace da matsayinka a cikin birnin ta maye gurbinka.kamar yadda ka sauka daga kan mukaminka haka nakeson gaba dayan fadawanka da duk masu mulkin kasar ka su sauka su baiwa mata matsayinsu,idan ka amince da hakan zaka tsira da rayuwarka da kuma mutuncinka idan kuma kaki zaka rasa komai naka.Koda Lubbatu tazo nan a karatun wasikarta tuni jikin sarkin Misra ya dade da fara karkarwa,zuciyarsa tana tafarfasa kamar zata kone fuskarsa kuwa ta kama gatsine kamar zata zazzago kasa saboda tsananin fishi,kawai saiya doki kasa da hannayensa biyu yayi sama tamkar da majaujawa aka janyeshi yana saman ya zare takobinsa ya kaiwa Lubbatu mummunan sara a wuya da nufin ya cire mata kai,cikin bakin zafin nama taja da baya amma duk da haka saida kaifin takobin ya yanketa a saman kirjinta jini yayi tsartuwa a lokacin data daka tsalle can gefe daya kuma ta mike tsaye zumbur cikin matukar juriya tana mai zare takobinta gami da dafe raunin nata.Cikin tsawa sarki ™Abubakar Haleefah Physicist™ ya baiwa dakarunsa umarninsu afka mata su kasheta.Nanfa fadar ta hargitse aka ruguntsume da azababben yaki ya zamana cewa dakaru sama da dubu uku sun rufarwa Lubbatu ita kadai suna kai mata sara da suka ta ko ina domin su hallakata ita kuwa ta wanzu tana mai kare kanta gami da maida martani da kuma kokarin samarwa da kanta hanyar da zata tsere.Saida aka shafe sama da sa'a guda anayin wannan bakin gumurzu da kyar da sidin goshi Lubbatu ta sami damar fasa kofar fadar da karfin sihirin tsafinta ta gudu daga cikin fadar bisa dokinta cikin matsanancin gudu na fitar hankali.Bayan anyi mata mugayen raunika guda uku a jikinta.Jini na zuba a jikinta kuma jiri na dibarta ta nausa cikin daji.Duk da haka saida sarkin Misra tare da dakarunsa suka biyo sawunta suka cigaba da farautarta a cikin daji.Ba don tana da karfin sihirin tsafi ba da sai sun ganta sun hallakata.Saida Lubbatu tayi jinyar kwana bakwai a cikin daji ta boye kanta sannan ta sami lafiyar data cigaba da tafiya ta isa birnin Kisra a matukar galabaice.Da shigowarta cikin fadar sai sarauniya Safirat ta mike zumbur ta ruga gareta ta rungumeta cikin tsananin takaici sannan ta dubeta tace naga duk abinda ya faru a gareki a can birnin Misra kuma inaso ne na zuba ido har kika kwace kanki daga sharrinsu domin su gane cewa ke kadai ma sun kasa kawar dake bare ni da kaina naje.Tabbas kin cika jaruma a bar kwatance don haka na baki matsayin mataimakiyar shugaban dakarun yakina Gargus kuma na baki dukiya da dinare miliyan sittin tare da babbar gona guda daya daga cikin manyan gonaki na na bayan gari.Koda jin wannan albishir sai Lubbatu ta sulale kasa sumammiya saboda tsananin farin ciki saida aka kawo ruwa aka yayyafa mata sannan ta farfado nan take Safirat ta dubi Gargus tace aje a fara shirin yaki gobe da safe zamu tafi izuwa birnin Misra ina mai bayar da umarnin cewa muna shiga birnin mu kashe duk mazajensu,yara da tsofaffi kadai za'a bari da rai.Gargus ya risina yace an gama ya shugabata. *Acan birnin Misra kuwa tun daga ranar da aka bi sawun Lubbata ta tsere aka nemeta sama da kasa aka rasa sai sarkin Misra ya fara shirye shiryen yaki don ya tabbatar da cewar sarauniya Safirat nanan tafe.Nanfa yasa aka rinka binne mugayen tarkuna a cikin dajin da dole sai an ratsa ta cikinsa sannan za'a iso birnin nasa sannan kuma ya aika da sakon neman agajin dakarun yaki daga kasashen dake makwabtaka dashi,wasu sarakunan sai suka aika masa da gudunmawar dakaru wasu kuma sai suka noke saboda tsoron kada fishin Safirat ya shafe su.A wannan lokaci da yawa daga cikin sarakunan kasar sun yanke shawarar suyi mubaya'a ga sarauniya Safirat domin su tsira da rayukansu da mutuncinsa wasu kuma sai suka zuba ido domin suga yadda zata wakana a tsakaninta da sarkin Misra saboda shima ansan cewa ba karamin jarumi bane kuma babban takadiri wanda baya gudu ko ja da baya a filin daga.Kwanaki goma sha daya na cika sarauniya Safirat ta sauko a kofar birnin Misra tare da dakarunta na yaki guda dubu dari bakwai da saba'in da bakwai da kuma dodanni guda talatin da uku dukkaninsu suna karkashin jagorancin dodo Gargus.Lokacin da labari ya riske sarkin Misra cewa ga sarauniya Safirat can tare da dakarunta sun iso kofar birninsa su duka ba tare da dayansu ya hallaka ba saiya cika da tsananin mamakin yadda akayi suka tsalle shirin duk tarkunan da aka binne musu.Nan take ya dauko madubin tsafinsa ya shafe shi saiya ga ashe gaba dayan tarkunan Safirat ce ta lalatasu da karfin sihirin tsafinta.Nan take ransa ya baci,da yake zuciyarsa ta kekashe ga barin tsoro kuma ya cika zarto mai kishin kansa da kasar sa sai ya mike tsaye zumbur ya kirawo gaba dayan dakarun na yaki yace ayi shiri aje a tare sarauniya Safirat a kofar gari.Duk mayakin daya tsorata yayi yunkurin guduwa a bakacin ransa.Nan dai ya cigaba da karawa mayakan nasa karfin guiwa yana mai cewa ku sani cewa wannan yaki da zamu fita yaki ne na kare mutuncinmu,rayukanmu da darajarmu ta 'ya'ya maza,da dai a wulakantamu a maishemu bayin matayenmu gwara mu mutu a FILIN DAGA.Ko ba komai zamu bar tarihin cewa mun mutu mazaje ba mata ba kuma jaruman da baza'a taba mancewa dasu ba.Koda jin wannan batu sai gaba dayan dakarun nasa sukaji dukkan tsoro ya kau daga cikin zukatansu suka kama kurma ihu tamkar ma sun sami nasarar yakin da zasu fita suna yiwa sarkin nasu jinjina gami da kirari.Ba tare da bata wani lokaci ba aka daurawa sarkin Misra damarar yaki yahau dokinsa ya jagoranci miliyoyin dakarun yaku suka zaburi dawakansu da gudu a lokacin da aka bude katuwar kofar birnin suka fice daga dayansu sannan aka mayar da kofar aka rufe.Ai kuwa suna fitowa suka hango sarauniya Safirat tare da tsirarun dakarunta a tsaitsaye bisa dawakai daga can dan nesa kada.Tazarar da bata wuce kamu arba'in ba.Nanfa aka fara kallon kallo tsakanin rundunar biyu har izuwa wadansu yan dakikai.Daga can sai sarkin Misra ya sakarwa dokinsa linzami ya taho a hankali ya fito daga cikin tasu rundunar alamar cewa so yake ya tattauna da sarauniya Safirat kafin a fara yaki.Koda ganin haka sai itama Sarauniya Safirat ta sakarwa nata dokin linzami ta durfafeshi har saida suka isa tsakiyar filin sannan suka tsaya cak suka sake kallon juna.Koda Safirat ta karewa sarkin Misra kallo tsaf daga irin halittar da Allah yayi masa ta sadaukantaka,kwarjini da kirar karfi sannan ta dubi miliyoyin dakarun yakin dake bayansa saida taji zuciyarta ta dan sosu kuma ta tabbatar da cewa in ba don ta sami sirrin wannan kwari da baka na mahaifinta ba da bata isa ta iya tarar wannan runduna da yaki ba.Bayan anyi kallon kallo na ™Abubakar Haleefah Physicist™ tsawon yan dakiku kadan tsakanin sarkin Misra da sarauniya Safirat saiya dubeta cikin tsananin fushi yace yake wannan azzalumar sarauniya kiyi sani cewa na sani cewa kece zaki sami nasara a wannan yaki da zamu fafata amma ina alfahari da zan mutu a matsayin sarki mai kishin kasarsa da jama'arsa kuma jarumin da bai mika wuya ba ga 'ya mace,nayi miki alkawarin cewar kafin ki kaini kas a wannan yaki da zamu fafata sainayi miki raunin da har abada tabonsa bazai bace ba a jikinki saidai akaiki kabarinki dashi,saboda ba na son ki manta da takaicina bayan mutuwata. ¶TRIPLE Ŷ Koda sarkin Misra yazo nan a zancensa sai sarauniya Safirat ta bushe da dariyar mugunta sannan ta murtuke fuskarta tace hakika ka burgeni daka kasance jarumi mai kishin kansa,amma ka sani cewa baka kishin jama'arka da kasarka tunda idan har muka gwabaza wannan yaki saina kashe gaba dayan wadannan mayaka naka na yiwa kasa ado da jininsu kuma saina kone dukkanin kyawawan gidajen nan naku na ruguje su.Idan har kana kishin jama'arka da birninka to zan iya sauya shawara na baka zabi guda.Zabin kuwa shine zamuyi wannan yaki mu biyu rak ni da kai,idan na sami nasarar kashe ka nayi alkawarin bazan kashe ko mayaki daya ba daga cikin dakarunka kuma bazan rushe gida daya ba a cikin birninka kona koneshi amma kuma dole ne alkawarina ya cika a kan mazajenku wato dole ne na maishe su bayin mata.Koda jin wannan zabi sai sarkin Misra yayi shiru yana tunani daga can kuma saiya juya da baya yayi kuskus da shugaban dakarunsa na yaki sannan ya sake dawowa wajen sarauniya Safirat yace,na amince da wannan zabi da kika bani na muyi wannan yaki a tsakaninmu mu biyu rak,idan kin sami nasara a kaina ki idda nufinki,idan kuma nine na sami nasara a kanki saina murkushe birninki kuma namai da nufinki akan matayenku.Dajin haka sai Safirat tayi murmushi tace na amince da hakan,nan take Safirat ta zare takobinta taja da baya kadan da dokinta,shima sarkin Misra saiya zare tasa takobin yaja da baya kamar yadda tayi.Lokacin da suka tasamma juna a guje suna ruri da kururuwa sa'adda kofaton dawakansu ke kartar kasa suna tayar da kura kai kace wadansu manyan giwaye ne biyu zasuyi karo da juna saboda kasar wajen ce ta kama girgiza,ai kuwa suna haduwa suka kacame da azababben yaki na gaban kwatance,suna kan dawakan nasu suka rinka kaiwa juna sara da suka cikin bakin zafin nama,ya zamana cewa kowannensu na kare hare haren yana maida martani.Duk sa'adda takubbansu suka hadu saidai kaga tarwatsin wuta na tashi,saida suka shafe rabin sa'a suna wannan bakin gumurzu ba tare da dayansu ya sami wata nasara ba.Al'amarin dayayi matukar baiwa Safirat mamaki kenan kuma ya daure mata kai saboda sanin cewa tunda ta mallaki wannan kwari da baka babu wani jarumi da yake iya tare hare harenta saboda zafin namanta da kuma karfin saranta,ya akayi sarkin Misra yake iya karewa? Tambayar da Safirat tayiwa kanta kenan kuma ta kasa baiwa kanta amsa. °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!! Littafi Na Hudu (4) Part C. KUMA TA KASA BAIWA KANTA AMSA.KODA SARKIN MISRA DA SAFIRAT SUKA GA SUN shafe kusan sa'a guda suna wannan bakin artabun ba tare da dayansu ya sami wata nasara ba sai duk su biyun suka fusata ainun suka soke dawakan nasu da takubba suka durkushe kasa dasu suka zubar da su kasa.Take dawakan suka mace,nanfa Safirat da Sarkin Misra suka sake ruguntsumewa da sabon azababben yaki mai tsananin tashin hankali domin wannan karon sun sauya salon fada sun hada da kaiwa junansu naushi da bugu da hannu da kafa.Nanfa karfin yazo daya ya zamana cewa kowa yana rama abinda ake masa.Nan da nan suka hadawa junansu jini da majina.Amma duk sa'adda suka sari jikinsu da takubba saidai kaji kara na tashi tamkar karfe da karfe.A sa'a guda ya zamana cewa duk su biyun sun jigata ainun.Gaba daya rundunonin biyu sun zuba ido kawai suna mamakin yadda wannan gumurzu ya kasance haka.Har saida kowannensu ya jigata ainun,bisa dole suka ja da baya sukayi cirko cirko suna haki da kallon juna tamkar zakaru.A wannan lokaci ne kowannensu ya fara tunanin abu na karshe da zai yi ya cutar da abokin gwaminsa.Kamar hadin baki sai suka mike tsaye tare suka juyawa juna baya,sukayi tafiya taku bakwai bakwai sannan suka juyo da sauri suka rugo da azababben gudu izuwa kan juna suna ruri da kururuwa kai da gani kasan cewa mugun gamo za'ayi wanda dole ne dayansu ya bakunci lahira.Koda ya rage saura baifi taku uku ba su hadu sai Safirat tayi wuf ta zare bakin mayafin dake lullube jikin kwari da bakanta dake goye a gadon bayanta.Shi kuma sarkin Misra saiya ambaci wadansu kalmomin tsafi guda uku,ai kuwa suna haduwa sai Safirat ta sami nasarar lumawa sarkin Misra takobinta a cikinsa.Take takobin ta faso gadon bayansa ya kurma uban ihu,kawai sai Safirat ta tsaya cak tana murmushin farin ciki amma kuma sai taji wani irin mugun zugi a jikin karamin dan yatsanta na hagu.Koda ta dago da hannunta ta dubeshi sai taga ashe sarkin Misra ya sami nasarar guntule danyatsanta da kaifin takobinsa jini na zuba.Take bakin ciki da takaici suka turnuketa.Sarkin Misra ya dago kansa da kyar a lokacin da yake kakarin mutuwa ya dubi Safirat kawai saiya bushe da dariyar mugunta.Al'amarin da yayi matukar girgiza Safirat kenan kuma ya bata mamaki ta dubeshi tace saboda me kake yi min dariyar mugunta alhalin mutuwa zakayi?Koda jin wannan tambaya sai sarkin Misra yayi kakin jini ya tofar a lokacin da idanunsa ke lumshewa sannan ya sake bude bakinsa da kyar yace ina yin dariya ne bisa dalili biyu,dalili na farko shine na sami nasarar cika alkawarina a kanki na guntule miki dan yatsan hannunki guda,lallai da wannan tabo zaki tafi har can kabarinki.Dalili na biyu kuwa shine a cikin binciken danayi a hallarar tsafina akwai wadansu jarumai guda biyu da zasu bayyana nan bada dadewa ba a wannan nahiya tamu,sune kadai jaruman da zasu iya tsayar dake akan wannan buri naki na maishe da maza bayin mata.Jarumi na farko ana kiransa da suna Yarima Musal'Asari daga birnin Istanbul.Bani da cikakken tarihinsa amma jarumtakarsa da karfin addininsa gami da sa'arsa sun nunka naki sau biyu.Jarumi na biyu ana kiransa Samazan kuma zai fito ne daga kasar Hindu,Jarumi Samazan ya taba zuwa har nan kasar tamu kuma munyi abota ta tsawon wata uku,kuma a wajensa na sami horon yaki kuma ya bani kaso daya a cikin kaso uku na sirrikan tsafinsa.A yanzu haka tunda mutuwa zanyi bazan iya baki labarinsa ba amma ki nemi matata Gimbiya Ulaimatu zakiji cikakken tarihin rayuwarsa a wajenta.Lallai haduwarki da jarumi Samazan da Yarima Musal'Asari shine karshen tasirinki.Gama fadin hakan keda wuya sai sarkin misra ya langwabe kansa ya mutu tsugunne batare daya fadi kasa ba.Safirat taci birnin misra da yaki a saukake kuma ta zauna da gimbiya Ilaimatu inda ta fara bata labarin jarumi Samazan.Kafin ta fara bata labarin saida gaba dayan mutanen birnin maza da mata suka hadu a babban fili sannan ta fara basu labarin kamar haka:-Dajin yayi tsit tamkar babu wani abu mai rai a cikinsa,babu sautin kaduear iska kuma babu sautin takun sawaye walau na mutum kona dabba,babu kukan tsuntsaye dana halittun daji.Komai jarumtakar mutum idan ya shigo cikin wannan daji sai yaji tsoro kuma sai yayi mamaki saboda akwai ni'ima sosai a dajin.Tarin bishiyoyi da yayan itatuwa kuwa ga sun birjik wasu ma sun gaji da nuna sun rube,koramai da fadamomi kuwa gasu nan cike da ruwa garai gari mai dadin dandano gwanin ban shaawa.To waishin menene ya hana tsuntsaye da dabbobi zama a cikinsa ba tare daya fuskanci wata matsala ba,wannan itace tambayar da bakon mafaraucin yayiwa kansa.Mafarauci Samazan matashi ne dan kimanin shekaru talatin da biyu,ya kasance dogo mai kirar sadaukai kuma kyakkyawa ne wanda duk mace datayi masa KALLO DAYA saiya burgeta.Idan ya fita yawon farautarsa yakanyi shekara uku bai koma kasarsu ta Hindu ba.Bayan haka yanayin tafiya mai nisa ya shiga cikin dazuzzukan wadansu kasashen.Tunda Samzan ya fara yin farauta a rayuwarsa bai taba yin dogon zango ba irin wannan domin yanzu ya shafe shekara guda da wata bakwai yana ratsawa ta cikin dazuzzuka iri iri.Samazan ya hadu da masifu iri iri akan hanyarsa domin ya fafata da mugayen dabbobin daji,yanfashi da mugayen aljanu,in badon yana da jarumtaka matuka ba kuma yana da karfin sihiri da tuni ya hallaka.A wannan doguwar tafiya da yayi tunda yana shaida inda ya nufa har saida kansa ya juye ya rasa ma inda ya nufa,shidai a saninsa bangaren birnin Misra ya durfafa daga can birnin Hindu to amma yanzu ya gane cewa ya kaucewa hanya ya shiga nahiyar da bai taba shiga ba ma. ™Abubakar Haleefah Physicist™ Samazan ya kasance dan baiwa domin tun yana yaro karami duk abinda yasa a gabansa yana samun sanara sannan kuma yana da basira gami da hasashen akan abinda zai faru a gaba,sau tari ba sai yayi amfani da tsafi ba yake gano inda ma'adanan kasa suke ba don haka yana amfani da wannan dama tasa ya sami dukiya mai yawan gaske,bisa wannan dalili ne ko kadan Samazan bai damu da kudin da yake samu ba a farauta.Wannan ce tasa Samazan yake son ya yawata a duniya domin binciken inda ma'adanan kasa suke,idan yayi nazarin wuri yaga cewa bazai iya hako dukiyar ba shi kadai saboda sai anyi haka mai zurfin gaske,saiya nemi sarkin garin su yayi yarjejeniya akan cewa za'a biya shi wani kaso idan akaga dukiyar.Duk sa'adda akayi hakan kuwa sai an samu dukiyar.Hakance tasa mutane suke matukar mamakinsa suke ganin kamar da aljanu yake aiki.Ko kadan babu sa hannun aljanu a cikin al'amarinsa baiwace kawai da kuma sanin sirrin kasa bisa huldar yau da gobe.Lokacin da Samazan ya tsinci kansa a cikin wannan daji mai ban al'ajabi sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi kuma yaji kamar ya juya da baya ya fasa shiga dajin.Amma daya tuna doguwar tafiyar daya sha da irin bakar wahalar daya fuskanta da kuma rashin sanin irin albarkar dake wajen sai yayi kundunbala ya saida ransa ya cigaba da kunna kai ciki,dama kuma yana da wani babban buri a cikin zuciyarsa.Saida Samazan ya shafe sa'a uku yana tafiya a cikin wannan daji yana ratsawa ta cikin kwazazzabai,duhuwoyi da surkuki iri iri batare daya hadu da wani mugun abu ba.Kwatsam sai yayi kicibus da wani katon rafi wanda dole saiya ratsa ta cikinsa sannna zai iya wucewa.Koda ganin haka sai Samazan ya karasa daf da rafin ya tsugunna ya kara kunnensa akan yashin dake gabar rafin,take ya gane cewa rafin yana da zurfi sosai,kuma babu mamaki a cikinsa a iya samun mugayen halittu duk da cewa bashi da tsawo mutum zai iya hayeshi a cikin rabin sa'a.Dan haka akwai hadari a shige shi,Kai tsaye ba tare da anyi amfani da kwale kwale ba.Nan take tunanin sassaka kwale kwale ya fado masa a rai.Daya tabbatar da cewa ba aiki bane na rana daya sai ya sauke katuwar jakar guzurinsa dake rataye a bayansa ya kafa tanti sannan ya dauki gatarinsa ya tafi neman bishiyar da zai saro yazo ya sassakata yayi kwale kwale da ita.Saida ya bata dan lokaci mai dan tsawo kafin ya sami bishiyar data dace.Yana ganin bishiyar ya kamu da farin ciki saiya ajiye gatarinsa sannan ya kwabe rigarsa.Wohoho kirar jiki irin ta Samazan dole ne ta burge mutum saboda Allah yayi masa damatsa,kwanji da jijiyoyi iri daban dana sauran sadaukai.Kana ganin siffarsa kasan cewa dole ne ya kasance GAWURTACCEN SADAUKI.Batare da bata lokaci ba Samazan ya dauki gatarinsa ya kama saran bishiyar aikuwa nan da nan ya kaita kasa a cikin kankanin lokaci saboda karfinsa da kuma kwarewarsa.Mafi akasarin irin wannan bishiya sai karti mutum biyu sun far mata suke iya kaita kasa a cikin sa'a guda,amma sai gashi shi Samazan ya kaita kas a cikin lokacin da bai wuce dakika dari tara da arba'in ba.Koda share zufar dake jikinsa baiyi ba saiya ciccibi bishiyar ya dorata a kan kafadarsa ta hagu ya ruketa da hannu daya sannan ya ruke gatarinsa da hannu ya juya ya nufi can bakin wannan rafi inda ya kafa tantinsa.Tun daga nesa mamaki ya turnuke Samazan kuma ransa ya baci,ba komai ne ya haddasa hakan ba face hango tantin daya kafa baje kas an yayyagashi.Koda ya hango hakan saiya rugo da gudu a fusace a tunaninsa zaizo ya iske wanda yayi masa barnar.Yana zuwa daf da wajen tantin sai yayi wurgi da bishiyar daga kan kafadarsa ya buda hannunsa mai ruke da gatarinsa sannan ya dubi gabas da yamma kudu da arewa kuma ya kasa kunne amma baiga kowa ba kuma baiji motsin komai ba.Al'amarin daya fara fusata shi kenan ya kurma uban ihu nufinsa ko ma menene yayi masa wannan barnar ya jiyo muryarsa ya dawo gareshi su fafata amma sai yaji shiru,koda ya dubi jakar guzurinsa sai yaga an fatattakata tamkar zabira aka sa aka yanyanka ta.Sai ransa ya kara baci fiye da koyaushe.Ya kama muzurai da numfarfashi kamar zakin daya fito farautar abinci yana fama da yunwa.Tsawon yan dakiku Samazan na tsaye yana huci kamar bakin kumurci kwatsam sai ya jiyo wani irin gurnani mai karfi daga cikin karkashin wannan rafi,nan take ya gane cewa abinda yayi masa wannan barna a cikin rafin yake.Cikin hanzari Samazan ya matso gaban gabar rafin kuma ya zare takobinsa wato ya hada makamai biyu a hannunsa ya zuba idanunsa akan cikin rafin yana jira yaga abinda zai fito daga ciki amma sai yaji sautin gurnanin ya dauke dif!Tamkar bai taba jin sa ba.Nanfa Samazan ya tsaya yana shawara da zuciyarsa akan ya shiga rafin yayi nutso kasa domin yaga ko menene a ciki ya kashe shi ko kuwa dai ya bari sai ya gama yin kwale kwalen sannan ya shiga.A karshe saiya yanke shawarar ya bari saiya gama kwale kwalen don haka saiya koma da

Chapter 6 of 8