Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
tace nasan kana jin yunwa sai ka fara cin wannan ko..?Da jin haka sai takaici ya turnuke sarki Safwan ya tuna cewa shifa sarki ne mai isasshen iko amma wai shi za'a wulakanta haka.Safwan ya dubi Safirat cikin tsananin fishi yace zaifi kyau ki kashe ni domin bazan yarda kici gaba da muzanta ni ba haka sai kace wata dabbar daji,kin kulleni a cikin keji kina bani dan itaciya.Dana cigaba da rayuwa a haka gwara ma na kashe kaina.Koda jin haka sai Safirat ta bushe da dariya lokaci guda kuma ta turbune fuskarta,tace bazan kashe ka ba kuma kaima ba zaka iya kashe kanka ba saboda rayuwarka da komai naka yanzu a hannuna yake.A nan nan cikin wannan keji zaka kwana duk sanyin nan da akeyi a kanka zai kare kuma babu wani abinci da za'a sake baka face wannan ayaba,idan ka cinyeta za'a baka ruwa makurwa hudu kasha saida safe.Koda gama fadin hakan sai safirat ta juya ta koma cikin tantinta taje tayi kwanciyarta.Fitarta keda wuya sai Sarki Safwan ya fusata ainun zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda bakin ciki don haka sai ya yunkura domin ya kama kansa da hannayensa biyu da nufin ya murdewa kansa wuya amma sai yaji hannayen nasa sun daskare ya kasa matsa su kuma yaji wani irin mugun zugi da radadi ya shigeshi bai san sa'adda ya kwalla ihu ba.Kawai saiya bingire kasa.A haka Sarki Safwan ya kasnace yana shan azaba ta radadi har gari ya waye,saida Safirat ta farka daga bacci taci abinci tayi wanka kuma ta gama kintsawa sannan tazo tayi nuni da hannunta izuwa kan Safwan sannan ya daina jin zafin da yake ji.Kuma ya iya sauke hannayensa kasa daga jikin kansa.A wannan lokaci zazzabi ya rufe sarki Safwan sakamakon kwanan da yayi a cikin sanyin.Nan take Safirat tasa aka bude kejin a ka fito da Safwan a matukar galabaice ga yunwa kuma ga rashin lafiya.Nan take tasa aka bashi abinci mai rai da lafiya yaci ya koshi kuma aka bashi magani yasha,gama hakan keda wuya sai aka mayar da sarki Safwan cikin kejinsa aka kulle.Haka dai Jaruma Safirat ta cigaba da wulakanta Sarki Safwan har tsawon kwanaki uku kuma sau bakwai sarki Safwan yana yunkurin kashe kansa yana kasawa.A ranar kwana na ukunne da farko yammaci saiga dodo Gargus ya dawo tare da amayarsa.Koda ganinsu sai Safirat ta ruga garesu cikin matukar farin ciki ta rungumesu kuma nan take tasa akayi shiri aka cigaba da tafiya aka durfafi birnin kisra.Wannan shine Abinda ya faru ga jaruma Safirat bayan ta sami nasarar mallakar Kwari Da Bakanta wanda mahaifinta Boka Saiham ya sana'anta.Kwari Da Bakan da duk wanda ya mallakeshi tamkar ya mallaki duniya ne. *Al'amarin ragowar manyan sarakai kuwa da manyan matsafa da jarumai wadanda suka zo yakar Jaruma Safirat domin su rabata da kwari da bakanta sai kowannensu ya koma izuwa garinsu cikin rashin kwarin guiwa,tashin hankali da matukar damuwa don haka sai sukayita yada labarin rashin nasarar da sukayi.Nan da nan kuwa labarin ya bazu ko ina cikin kasashen duniya.Koda sarakuna sukaji wannan labari sai cikinsu ya fara durar ruwa saboda babu wanda yake son a rabashi da karagarsa ta mulki a maishe shi bawa.Wasu sarakuna kuwa sai suka rinka yin dariya suna karyata wannan labari domin basu ma yarda da cewa akwai wannan kwari da bakan ba a duniya wadda ake cewa jaruma Safirat ta mallake shi.Wadanda bokayensu sukayi bincike suka tabbatar musu da cewa lallai wannan labari gaskiya ne sai suka fara shirya taro na musamman domin susan hanyar da zasu bullowa al'amarin tun kafin abin yazo ya riskesu har gida.Nan da nan sunan jaruma Safirat ya tumbatsa a duniya ya zamanacewa ana kodata fiye da yadda ma take. *A CAN BIRNIN ISTANBUL kuwa wacce ta kasance DAULAR MUSULUNCI,Sarkin dake mulkinsu ya kasance wani dattijon mutum wanda shekarunsa sun haura casa'in,tsufa ta riske shi amma yana da 'da guda daya jal wanda ake kira da suna Musal Asari.Yarima Musal'Asari ya kasance sadaukin jarumi kuma zarto mai tarwatsa maza a filin daga,baya ga haka ya kasance jarumi mai tsananin saa bisa duk abinda yasa a gabansa.Domin tunda ya zama cikakken saurayi duk gasar da aka shirya a nahiyar shike zama zakaranta walau a cikin biranensu na musulmai ko a biranen ma'abota bautar wanin Allah.Bisa wannan dalili ne Yarima Musal'Asari ya zama sananne kuma mai matukar farin jini a wajen yan mata amma ko kadan hankalin Musal'Asari baya kan SOYAYYA da AURE.Burinsa guda daya ne jal a duniya kuma tun yana yaro karami yaso ya cika wannan buri amma sai mahafinsa yaki ya bashi damar hakan.Ba komai bane burin Yarima Musal'Asari face ya zagaye gaba dayan kasashen dake cikin daular larabawa ™ Prince Auwal Auwzab ™ yaga kowacce irin kabila gami da al'adunsu da addininsu kuma ya rubuce shi domin ya zamo abin tarihi.Mahaifin Musal'Asari bashi da kowa a duniya face shi,Mahaifiyarsa ma tun yana da shekara hudu a duniya ta rasu sakamakon wata rashin lafiya.Bisa wannan dalili ne sarki yake mutuwar son Musal'Asari fiye da komai a rayuwarsa kuma ko kadan baya yarda ya nisanta dashi.Ana cikin wannan hali ne fatake suka kawo labarin baiyanar jaruma Safirat izuwa cikin birnin Istanbul inda akayi ta yada jita jitar cewa sai wannan jaruma ta mulki duniya gaba dayanta,a hankali kuma saita maishe da mazan duniya bayin mata.Lokacin da wannan jita jita ta yawaita a gari saisarki Suleman wato mahaifin yarima Musal'Asari ya tara gaba dayan fadawansa a cikinsu harda sarkin Yaki Musal'Asari.Sarki Suleman ya rufe su da fada yana mai cewa yaya za'ayi a bari ana ta watsa wannan jita jita a cikin birninsu na musulmai.Nan take aka kafa doka akan cewa duk wanda aka kama yana wannan magana ma za'a sa dakaru su kamashi a kawo shi fada ayi masa hukunci tunda dai wannan al'amari ne na matsafa da masu hasashen banza.Hakane tasa dole bakin da suke shigowa birnin da wannan zance suka tsuke bakunansu amma duk da haka ba'a fasa yin maganar ba.A boye cikin gidaje ana gulma,ba komai bane ya haddasa hakan ba face a wannan lokaci akwai Ahalilkitabi a cikin birnin na Istanbul kuma sunayin addininsu na lumana tare dasu bisa yarjejeniya.Bayan cikar kwana uku dayin taro sarki Suleman da yan majalisarsa sai sarki Suleman yayi wani mafarki wanda ya girgiza shi kuma ya firgita shi ainun ya zamana cewa hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe a rayuwarsa.Ba komai ne ya jefashi cikin hali ba face tun yana yaro karami dan kimanin shekara shida duk abinda yayi mafarki akansa to sai wannan abu ya faru a gaske.A Cikin mafarkin nasa aka nuna masa baiyanar jaruma inda ta ci manyan kasashen labarawa guda hudu da yaki ta sauke sarakunansu daga kan mulki ta sanya mata a madadinsu.Sannan ta nausa wani bangaren daban na duniya inda ta cigaba da cin kasashe da yaki.Sannan kuma ta sake shirin afkawa sauran kasashen larabawan data bari a baya.A daidai nanne sarki Suleman ya farka daga baccinsa a razane yana mai rafka salati.A wannan rana dai jikin sarki Suleman yayi sanyi sosai matuka,kuma ya kasa cin abincin kirki saida kyar aka tursasashi yaci abincin kadan.Bisa wannan dalili ne yasa aka yi taron gaggawa inda ya baiyana musu labarin mafarkin da yayi.A hakane akai ta kawo hujjoji akan dole a tashi a kare kai.Yarima Musal'Asari ya dubi mahaifinsa yace,Ya Abbana ka bani dama domin na fita izuwa sauran kasashen duniya domin naje na daukaka kalmar Allah.bisa babu yadda za'ayi Sarki Suleman ya amince da maganar dansa duk da cewa yana matukar kaunarsa baya son rabuwa dashi koda ta dakika daya ce.Sarki Suleman ya ce da Yarima Musal'Asari idan har ya dawo gida zai zaba masa matar data dace dashi muddin ya dawo ya iskeshi a raye kuma a sannane zaiyi murabus ya bashi Karagarsa.Koda Sarki Suleman yazo nan a jawabinsa sai hawaye ya subuto masa kawai sai ji yayi Musal'Asari ya rungumeshi ta baya shima ya fashe da kuka,ba komai ne yasasu yin kukan ba face wannan shine karo na farko da zasu taba rabuwa arayuwarsu ta tsawon kwanaki ko watanni tun daga haihuwar Yarima Musal'Asari kawo iyanzu.Kashe gari kuwa da sassafe sarki yasa akayi shela.Fada ta cika ta batse da mutanen gari gami da fadawa,bayan kowa ya hallara sai sarki ya mike yayi bayanin cewa Yarima tare da dakaru dari uku zasu tafi izuwa gabashin kasashen labarawa domin daukaka kalmar Allah.Koda jin wannan batu sai jama'a aka rude da kabbara kuma aka kamu da tsananin mamakin yadda sarki ya sallama rayuwar yarima don tafiya wannan JIHADI.Kuma kowa ya sani cewa daidai da rana daya sarki baya son rabuwa da yarima.Ba tare da bata lokaci ba Yarima da dakarunsa su dari uku suka gama kintsawa dukkaninsu sukayi bankwana da iyayensu da yan uwansu dama gaba dayansu samari ne matasa babu mutum daya mai aure a cikinsu don haka sunaji da samartaka,karfi iya yaki da kuma jajurcewa bisa duk abinda suka sa a gaba.Saida aka rako wannan runduna har izuwa bayan gari,yawancin wadanda suka rako su din yan mata ne masoyansu,wasu ma ansa ranar bikinsu,lokacin da bai wuce shekara daya ba.Kowa ka gani da budurwarsa amma banda Yarima Musal'Asari wanda shi koda wasa ma bai taba cewa yana son wata budurwa ba Kamar ni Prince Auwal Auwzab Auwzab hmmmmm saura wani yace ba haka bane, kuma duk waccce ma tace tana sonsa fa to ta yankawa kanta kazar wahalar da bazata iya figeta ba.Nan dai masoya suka kama kuka da alhinin rabuwa sunajin kamar su fasa wannan tafiya har al'amarin ya fusata yarima Musal'Asari ya dakawa dakarun nasa tsawa,kowa tsoron fishin yarima Musal'Asari yake dan haka dakarun suka haye dawakansu sukayi gaba suna waigen masoyan nasu har saida sukayi nisa a cikin daji suka bace musu da gani.Mafi akasarin wadannan zakwakurun jarumai guda dari uku sa'annin yarima Musal'asari ne kuma abokansa ne domin tare suka taso,tare sukayi wasa don haka akwai shakuwa gami da fahimtar juna a tsakaninsu.Wani lokacin ma idan suna hira da wasa da dariya mutum bazai iya ganewa cewa ko 'ya'yan talakawa bane shi kuma dan sarki.Yarima Musal'asari yana da matukar saukin kai,kawaici,kunya,jinkai da sanin ya kamata,amma kuma baya son zalunci,rainin hankali,girman kai da wulakanci.Sai da wannan runduna ta shafe sa'a bakwai da rabi tana ketawa ta cikin dazuzzuka har yazamana cewa sun fita daga yankin cikin kasar su ta Istanbul sun nausa nahiyar birnin Yemen ba tare da sun yada zango ba ko sun hadu da wani mugun abu ba.Adaidai wannan lokaci sallar Azahar Tayi don haka ™ Prince Auwal AUW.ZAB ™ sai Yarima ya bayar da umarnin a yada zango domin ayi sallah.Nan take kuwa aka tsaya aka kafa tantuna sannan akayi alwala yarima ya shige gaba yayi limanci akayi sallah.Bayan anyi addu'a an shafa ne sai kowa ya fiddo abincin kalacinsa ya kama kimtsa cikinsa,shi kuwa yarima sai ya koma gefe daya ya zuba musu idanu kawai yana lazimi yana murmushi.Koda ganin haka sai shugaban dakarun wanda ake kira da Samhar ya taso daga inda yake zaune dauke da gasasshen nama yazo daf da yarima ya zauna kuma yayi masa tayin naman,yarima ya girgiza kai yace ai ni ma inada irin wannan nama da kake ci amma bana sha'awar cinsa ne.Samhar ya dubi Musal'asari cikin mamaki yace haba ya shugabana rabonka da abinci fa tunda asuba da mukayi kalaci kafin mu baro gida kuma na tabbata cewa kana jin yunwa ko kuwa baka da lafiya ne?Koda jin wannan tambaya sai yarima ya dafa kafadar Samhar ya dubeshi cikin murmushi yace tabbas ina jin yunwa amma bana sha'awar cin komai face sabon nama wanda aka yanka yau ko tsuntsun da aka harbo a yau don haka yanzu ni zan shiga daji na farauto abinda zanci.Gama fadin hakan keda wuya sai yarima ya mike tsaye ya dauko kwari da bakansa ya rataya su a gadon bayansa kuma ya daure takobinsa a kugunsa.Take shima Samhar ya mike ya kama shirinsa bisa ganin hakan sai yarima ya dubi Samhar yace ka sani cewa babu sama dani dakai a cikin dakarun nan,idan babu ni babu kai waye zai basu umarni idan wani bala'in ya taso ba zato? Samhar ya gyada kai yace nasan da haka amma ka sani cewa ba zamu bari ka shiga daji kai kadai ba dole ne mu baka kariya duk da cewa mun san zaka iya kare kanka kuma Allah zai kareka daga dukkan abinki,bisa wanann dalili zan hada ka da mutum hudu ni kuma zan zauna na kula da sansanin.Koda jin haka sai yarima yayi murmushi ya sake dafa kafadar Samhar a karo na biyu yace da kyau abokina,hakika kana da basira gami da hangen nesa shi yasa nake matukar son zama tare dakai.Nan take Samhar ya zabo mutum hudu wadanda suka san sirrin daji kuma manyan barade sha gwagwarmaya a filin daga ya hadasu da yarima suka sashi a tsakiya don tabbatar da tsaro suka nausa izuwa cikin daji.Yarima da dakarun nasa mutum hudu sukayita kutsawa a cikin daji suna dube dube da hange hange amma saida suka shafe kusan rabin sa'a ko dan karamin tsuntsu basu ga giftawarsa ba bare wata dabba.Al'amarin daya basu mamaki kenan,Yarima ya yiwa sauran dakarun nasa hudu inkiyar su tsaya.Take kowannensu ya tsaya a inda yake.Yarima ya dubi gabas da yamma,kudu da arewa da kuma sama da kasan dajin yayi nazarin komai dake wajen,kawai sai yayi murmushi yace akwai mugayen yanfashi a wannan daji kuma mugayen dabbobin da suka hana kananun tsuntsaye da halittu shi yasa muka kasa farauto koda zomo guda daya.Gama fadin hakan keda wuya sai Yarima ya bude bakinsa yana mai cewa idan mutane ne yan uwanmu labe a wannan wuri ku baiyana kanku in ba so kuke taku ta kare ba,ai kuwa kafin yarima ya gama rufe bakinsa sai sukaji an bushe da mahaukaciyar dariya a cikin wata murya mai kauri da kaushi daga sama.Kafin su yarima su daga kawunansu sama suga maiyin wannan dariya tuni dakaru sama da mutum dubu sun sauko daga saman bishiya a cikin shigar bakaken tufafi,fuskokinsu a rufe,idanunsu kadai ake gani kuma kowannensu na ruke da muggan makamai.Nan da nan suka yiwa su Yarima Musal'asari kawanya daga can sai ga shugaban dakarun wani narkeken kato mai siffar mutanen farko ya ratso ta cikin duhuwar ciyayi yana safe da wata sharbebiyar adda bisa kafadarsa babu riga a jikinsa kuma babu takalmi a kafarsa.Dogon wando ne na fatar jimina kacal a jikinsa sai kuma tarin guraye na tsafi a jikin hannayensa da kugunsa,kallo daya zakayiwa wannan narkeken kato ka gane cewa rikakken dan fashi ne wanda bai san wani abu waishi tausayi ba,da ganin kura kasan zata ci mutu.Allah ne kadai yasan iya adadin rayukan da wannan shirgegen mutum ya salwantar.Koda wannan kato yayi arba da yarima Musal'asari sai ya kare masa kallo sama da kasa,daidai ya ganshi a cikin suturu mai kyau mai tsada kuma ya dubi dakarunsa ya gansu a cikin shigar dakarun gidan sarauta saiya bushe da dariyar farin ciki mai kama da kukan jaki bisa ganin karensa ya kama zomo.Lokaci guda kuma saiya turbune fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dakawa yarima tsawa yace yakai wannan kyakkyawan matashi ina mai umartarka daka gaggauta baiwa yaranka umarni da su zubar da makamansu,kuma su tattaro duk abinda kuka mallaka ku zube su anan gabana idan kuna son ku wuce wannan daji a raye,in ba haka ba kuwa yanzun nan zamuyi muku kisan gilla gaba dayanku sannan mu kwashe dukiyar taku da ababan hawanku a matsayin ganima.Koda jin wannan batu sai Yarima ya jiyo ya dubi gaba dayan dakarun nasa yace dasu su zubar da makamansu.Cikin tsananin mamaki da kaduwa dakarun sukayi tsuru tsuru suka rasa abinda zasuyi saboda sunsan cewa indai za'a fafata zasu iya kawar da wadannan yanfashi duk da cewa sun ninkasu sau uku a yawa.Har Hamsar ya bude baki zaice wani abu ga yarika sai ya tari numfashinsa ya daka masa tsawa yace zakubi umarni nane ko kuwa a'a? Dajin haka sai Hamsar da sauran dukkanin dakarun suka cire takubbansu da sauran makamansu na yaki suka zube kasa.Koda ganin haka sai Yarima Musal'asari ya dubi shugaban yanfashin yace yanzu zan baka zabi guda biyu kamar yadda ka bani.Ka umarci dakarunka su duka su yakeni ni kadai ko kuma mu fafata ni dakai kawai.Idan ni da dakarunka ne zamu fafata nayi maka alkawarin cewar da izinin ubangijina dayansu bazai tsira da rauwarsa ba.Idan kuma ni dakaine to zan kasheka kuma ranka fansar na yaranka ne......... °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!! Littafi Na Uku (3) Part C Kuma ranka ne fansar na yaranka ma'ana zan kyale su su rayu a matsayin bayina kuma dole ne su karbi addini na.Koda Yarima Musal'asari yazo nan a zancensa sai shugaban yan fashin da yaran nasa gaba dayansu suka bushe da dariyar mugunta sukayi ta kyalkyala dariyar kamar bazasu daina ba har saida shugaban nasu ya tsuke bakinsa sannan suma kowannensu yayi tsit.Shugaban yanfashin ya sauke lafceciyar addar tasa kas daga kan kafadarsa yana mai gyar tsayuwarsa sannan ya dubi Yarima Musal'asari cikin tsananin fushi gami da kakkausar murya yace ni zan yake ka kuma idan na kashe ka zan kama dukkanin wadannan yara naka nayita gana musu azaba mai radadi,daya bayan daya har sai kowannensu ya riski ajalinsa.Kafin shugaban yan fashin ya gama rufe bakinsa tuni yarima ya zare takobinsa ya ruga izuwa kansa sun runguntsume da azababben yaki,sauran yanfashin da dakarun yarima kuwa sai suka zama yan kallo suka zubawa SARAUTAR ALLAH ido.Yarima da shugaban yanfashin suka wanzu suna kaiwa junansu sara da suka cikin bakin zafin nama juriya da jarumtaka taban al'ajabi.Ana fara wannan gumurzu ne shugaban yanfashin ya cika da mamaki kuma ya gane cewa lallai ya hadu da jarumi abin kwatance saboda wannan ne karo na farko daya hadu da jarumin daya iya tare dukkan hare harensa harma yake iya maida martani.A tarihin gumurzunsa a cikin dakika ashirin yake bazar da mayaki komai karfinsa girmsa da iya yakinsa amma sai gashi sun shafe kusan dakika dari uku da ashirin suna bakina artabu shi da yarima Musal'asari amma ya kasa koda lakutar jikinsa.Idan kuwa ya naushi mutum a mukamukin fuska saidai kaji karar karyewar kashin mukamukin amma sai gashi yarima yana shanye duk naushin nasa kuma yana maida martanin dashi baya ma iya shanye shi domin duk sa'adda Yarima ya gabzawa katon naushi sai yayi taga taga da baya kamar zai fadi,tsananin juriyace take sawa yaki faduwa.Nan da nan suka hadawa junansu jini da majina amma cikin kankanin lokacin shugaban yanfashin ya fara jigata.Al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan a wajen saboda gashi dai a zahiri shugaban yanfashin yafi yarima girma,kaurin gwanji da kwarjini amma sai gashi yarima ya fara luguiguitashi.Har saida takai cewa takobin katon ta subuce daga hannunsa ta fadi kasa,koda ganin haka sai shima yarima ya jefar da tasa takobin ya tsaya suka kama kallon kallo tsakaninsa da shugaban yanfashin sukayi cirko cirko suna kallon juna a lokacin da jini ke diga a hancinsu da bakinsu.Duk wanda ya kallesu a wannan lokaci yasan cewa nazari da tunani sukeyi akan yadda zasu sami nasarar hallaka juna,saida suka shafe yan dakiku kadan suna tunani da nazarin juna cikin mugun nufi kai da gani kasan mugun gamo za'ayi wanda dole ne abu daya cikin biyu ya faru.Kodai ayi ragas ko kuma daya ya kashe daya.Koda ya rage saura baifi taku biyar ba su hadu sai kowannensu ya daka tsalle sama,ashe akwai wata karamar wuka a soke a bayan shugaban yanfashin don haka yana saman sai yayi wuf ya zaro wuka cikin zafin nama ya kirbawa yarima ita a gefan kirjinsa na hagu.Take wukar ta lume a gefan kirjin nasa,yarima ya kwala kabbara da karfin gaske sakamakon mugun zafin daya ji a lokacin da jini yayi tsartuwa daga cikin ramin wukar inda tayi masa rauni,amma saiya daure ya sakalo wuyan katon da kafafunsa biyu suka fado kasa tare.Yarima ya shake wuyan shugaban yanfashin da kafafun nasa a lokacin da jini ke zuba a kirjinsa,nanfa shugaban yanfashin yasa hannayensa biyu ya fara kokarin banbare kafafun yarima daga cikin wuyansa.A lokacin ne kowannensu ya dage iya karfinsa,kwanjin shugaban yanfashin ya kumbura kuma jijiyoyin hannunsa suka tashi sukayi burdin burdin ya kama ruri da ihu irin na manyan mazaje sai yayi kamar zai sami nasarar banbare kafafun na yarima saiya kasa.A haka dai yana ji yana gani Yarima ya cigaba da shake masa wuya har numfashinsa ya fara sarkewa yana karkarwa ya rinka wutsil wutsil da kafafunsa.Yaransa suka yunkuro da nufin kawo masa dauki sai dakarun yarima sukayi wuf suka dauki makamansu suka sha gabansu.A haka dai yarima ya sami nasarar kashe shugaban yanfashin ya zamana cewa jikinsa gaba daya ya sandare ya daina motsi,shi kuwa yarima saiya mike tsaye amma yana tangadi jiri na dibarsa dauke da takobinsa ya nuna yanfashin da ita yace kun yarda ku zama bayina ko kuwa kuma zaku yakemu?Koda jin wannan tambaya sai gaba dayan yanfashin suka zubar da makamansu suka durkusa kasa bisa guiwoyinsu suna masu yin mubaya'a,faruwar hakan keda wuya sai dakarun yarima sukayi sauri suka kwashe makaman yanfashin kuma sukayi musu kawanya suka ritsa su,adaidai wannan lokaci yarima Musal'asari ya yanke jiki ya fadi kasa sumamme,cikin dimauta Hamsar ya rugo izuwa gareshi ya shiga duba raunin nasa kuma ya bayar da umarnin a gaggauta kafa tantin Yarima.Bayan an kafa tantin ne an shimfidar da yarima a ciki kamar gawa,an cire wukar dake lume a cikin kirjinsa aka gano cewa akwai mugun dafi a jikin wukar.Nan take wani badakare masanin dafi ya duba raunin da kyau,nan take gumi ya karyi masa ya dubi Hamsar cikin alamun firgici yace ya shugaban dafin dake jikin wannan wuka daga jikin wani irin maciji na birnin Kisra aka samo shi,dole sai an samo irin macijin sannan za'a sami makarinsa,abin da zan iyayi kawai a yanzu shine na dakatar da dafin daga yaduwa izuwa dukkan jijiyoyin jikin yarima kuma zan iya yin hakanne kawai tsawon kwanaki uku,idan aka wuce wannan lokaci yarima zai iya rasa rayuwarsa saidai kuma wani ikon na Allah.Koda jin wannan batu sai hankalin Hamsar dana sauran dakarun ya dugunzuma ainun cikin alamun ™Abubakar Haleefah Physicist™ tsananin damuwa Hamsar ya dubi masanin dafin yace yanzu daga nan zuwa birnin Kisra tafiyar kwana nawa ce?Masanin dafin daya ji haka sai yace a kalla sai mun shafe kwani hudu da rabi.Koda jin haka sai Hamsar ya mike tsaye zumbur ya dubeshi yace da izinin Allah zamu isa can din kafin cikar kwanaki uku daka ambata.Hamsar ya dubi gaba dayan yanfashin yace yanzu kun zama bayinmu gaba dayanku amma zaku iya zama yantattu bisa sharadi guda,sharadin kuwa shine zaku tuba daga yau kun daina wannan muguwar sana'a taku ta fashi har abada kuma zaku karbi Addinin Musulunci yanzu take,inba haka ba kuwa zamu kashe ku a yanzu take.Koda jin wannan batu sai gaba dayan yanfashin sukace sun amince su karbi Addinin Musulunci.Ba tare da bata lokaci ba Hamsar ya biya musu kalmar shahada suka maimata gaba dayansu.Nan da nan akayi shirin tafiya aka dora Yarima akan dokin Hamsar aka cigaba da tafiya ba sassauci domin a isa birnin kisra kafin cikar kwanaki uku.Yarima yana cikin wani irin yanayi mai kama da dogon suma domin bain san a halin da yake ciki ba kuma bai san wanda ke kusa dashi ba. End Of Book 3. TURKASHI!!! Sai Muje Zuwa Ga Littafin Kibiya Ratsa Maza Littafi Na Hudu (4). °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!! Littafi Na Hudu (4) Part  WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GASU YARIMA MUSAL'ASARI BAYAN SUN BARO KASARSU TA ISTANBUL da nufin yin farautar Jaruma Safirat domin tsayar da ita akan nufinta na kaskantar da dukkan mazajen duniya ta fifita mata a kansu. *Al'amarin Jaruma Safirat kuwa a cikin matukar farin ciki da kwanciyar hankali ta durfafi birninsu na Kisra.Duk sa'adda ta waigo bayanta taga sarki Safwan a cikin keji kuma a wulakance kamar dabbar daji saitaji dumbin farin ciki ya sake rufeta tunda gashi ta sami nasara akan babban makiyinta,kuma tana daf da cika burinta.Haka dai Safirat da dakarunta su dodo Gargus suka cigaba da tafiya tsawon yan kwanaki ba tare da sun fuskanci wata matsala ba har suka iso birnin Kisra.Tun daga nesa suka hango kofar birnin a bude wanwar kuma ko mai gadi guda daya babu a bakin kofar.Koda ganin haka sai Gargus yayi sauri yasha gaban Safirat ya tsaida keken dokinta ya dubeta yace ya shugabata akwai tuggun da aka shirya mana a cikin wannan birnin naku,a ina kika taba ganin an bar kofar gari a wanwar haka babu masu gadi?Koda jin wannan batu sai Jaruma Safirat tayi murmushi sannan ta dubi Gargus cikin nutsuwa tace yanzu mu da muka ratsa cikin dajin Sarkif muka tsallake duk masifun dake cikinsa sannan muka shiga dajin mutuwa muka dauko kuttun baka ashe har akwai wani abu wanda zai iya razana mu?Koda Safirat tazo nan a zancenta sai Gargus yaji babu shakka a cikin zuciyarsa don haka saiya ruga da gudu ya durfafi kofar birnin Kisra.Itama Safirat sai ta karawa keken dokinta kaimi.Ragowar dakarun dodanninta ma suka take mata baya.Saida su Jaruma Safirat suka gama shigewa cikin birnin sai kawai sukaji an rufe kofar garin ta waje an kulle su,Safirat tayi murmushi ta cigaba da tafiya abinta,babban abinda ya daure musu kai shine har suka iso tsakiyar birnin basu ga koda mutum daya ba,garin yayi tsit tamkar babu wani mai rai a cikinsa.Kai ko gilmawar dabbar gida guda daya basu gani ba amma suna isowa tsakiyar garin ne Safirat ta hango mahaifiyarta a daure a can saman jikin wata doguwar dirka tana zubar da hawaye.Nan take saiga gaba dayan dakarun yakin birnin Kisra sun fito da gudu daga cikin maboya sun kewaye su Safirat.Wasun suma sun dana kibiyoyi wasu kuma takubbai da adduna da sauran makamai ne a hannunsu.Sarki Safwan dake cikin keji a daure koda ya hango abinda ke faruwa saiya bushe da dariyar farin ciki gami da mugunta ya dubi Safirat yace kina zaton cewa kada mage yanka ne?To ki sani cewa faduwar zaki a cikin dajinsu ba wasa bane,koda kin kashe ni tamkar kin kashe maciji ne baki sare kansa ba,saboda da akwai wanda ya fiki son wannan karaga tawa kuma ba wani bane face wazirina Hidaisu bin Alkas.Gama fadin hakan keda wuya sai ga waziri Hidaisu ya fito daga cikin wani babban gida a cikin gagarumar shigar yaki gaba dayan yan majalisar kasar na take masa baya.Kai tsaye ba tare da fargabar komai ba waziri Hidaisu ya tunkaro inda Safirat take bisa keken dokinta dauke da sarki Safwan a cikin keji.Saida ya rage saura baifi taku goma ba a tsakaninsu sannan Hidaisu ya tsaya cak ya dubi Jaruma Safirat cikin murmushi yace una godiya a gareki da kika bani dama ta zartar da abinda ya gagareni aiwatarwa tsawon shekaru talatin da biyar.Babu abinda bayi ba akan ganin na kawar da sarki Safwan daga kan wannan karagar mulki na daneta amma na kasa saboda dama can sarautar ta gidanmu ce kakaninsa suka kwaceta,ina da sadaukantaka da jarumtaka irin na sarkiSafwan kuma inda da karfin sihirin tsafi duk irin nasa amma ya zame mini alakakai,yau gashi rana daya kin bani dama nayi masa juyin mulki,kece kadai zaki iya taka mini birki a cikin nasarata,kema kuma gashi inada garkuwar da zata kareni daga dukkan sharrinki,yanzu zan baki zabi guda biyu,zabi na farko shine ki bani sihirtacciyar kwari da bakanki ni kuma na baki mahaifiyarki ki juya ki fice daga birnina kada ki sake dawowa ko kuma na kashe mahaifiyartaki,sannan kema na kasheki kinga dai ko kin hau kan wannan karagar mulki zaki karasa rayuwarki ne a cikin bakin cikin rashin mahaifiyarki har abada,ba zaki taba mancewa da makashinta ba.Koda Waziri Hidaisu yazo nan a jawabinsa sai kawai akaji Jaruma Safirat ta bushe da dariya.Al'amarin daya bawa kowa mamaki kenan,Safirat ta cigaba da kyalkyala dariya kamar bazata daina ba har saida ta fado kasa daga kan keken dokin ta zauna a kasa dirshan tana ta kyakyatawa,idanunta suka ciko da kwallar dariya suma dakarunta su Gargus sai suka kama yin dariya irin tasu ta dodanni mara dadin sautin tamkar saukar arada.Koda ganin haka sai waziri Hidaisu da gaba dayam dakarun yakin birnin Suka firgita cikinsu ya duri ruwa sukaji kamar su watse kowa ya cika wandonsa da iska amma saboda ganin Hidaisu tsaye sai kowa ya tsaya cak.Lokaci guda sai akaji Safirat ta tsuke bakinta tayi shiru ga barin yin dariyar sannan ta mike tsaye ta fuskanci waziri Hidaisu tace ina mai shawartarka daka gaggauta sawa a kwance mahaifiyata daga jikin waccan dirka (Pillar) a sauko da ita kasa kai kuma kazo ka bude wannan keji da sarki Safwan ke ciki ka sanya kanka saboda ba zaka iya kashe mahaifiyata ba,kayi kuskura babba daka bari nazo na risketa a raye,tabbas na raina wayonka da tunaninka,in dama boyeta kayi a wani wurin da zaka iya cutar dani,idan kana shakka a kan cewa zaka iya kashe tan to ka jarraba ka gani.Koda waziri Hidaisu yaji wannan batu sai ransa ya baci nan take ya dubi dakarun da suka dora kwari da baka yayi musu inkiya,nan take dakarun kimanin su miliyan daya da rabi suka juya da saitin kibiyoyinsu suka saita mahaifiyar Safirat suka sake jan ™Abubakar Haleefah Physicist™ zaren bakan suka tabe.Koda ganin haka sai idanun Safirat suka ciko da kwallah har hawaye ya zubo mata a zaton Hidaisu wannan hawaye da Safirat ta zubar na bakin cikin mutuwar mahaifiyarta ne don haka saiya bayar da umarnin a sakarwa mahaifiyarta ta harbi.Kaico hakika masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce rashin sani yafi dare duhu domin inda maharban nan sunsan abinda zai biyo baya da dayansu baibi umarnin Waziri Hidaisu ba.Koda Hidaisu ya bayar da umarnin aka saki miliyoyin kibiyoyin suka tafi da gudu domin suje su cake mahaifiyar Safirat a inda take daure jikin Dirka a can saman gini sai akaga kibiyoyin sun dawo da baya da gudu sun cake wadanda suka harbo su suka rinka zubewa kasa matattu.Nanfa garin gaba daya ya hautsine mutane suka kama guje guje da iface iface.Gaba dayan sauran dakarun yakin ma sai suka dimauce suka zubar da makamansu suka kama gudu suna neman maboya.Suma gaba dayan yan majalisar kasar wadanda suka baiwa Hidaisu goyan baya sai sukayi masa tawaye suka tarwatse kowannensu ya sami wuri ya labe ya zuba ido yaga yadda karshen al'amarin zai kasance.Kafin kace wani abu filin wajen ya zama wayam babu kowa face Safirat a tsaye tare da dakarunta dodanni sai gawarwakin dakarun da sukayi yunkurin kashe mahaifiyarta.Kuma sai Waziri Hidaisu wanda ke fuskantarsu sai kuma sarki Safwan wanda ke daure cikin sarka a cikin keji.Tsawon yan dakiku ana kallon kallo tsakanin jaruma Safirat da waziri Hidaisu cikin tsananin fushi da kiyayyar juna har fuskar Hidaisu nayin gatsine saboda tsabar fushi,sai kawai yayi wuf yayi jifa da alkabbar jikinsa sannan ya zare takobin jikinsa ashe dama a shirye yake ko riga babu a jikinsa sai wani dogon wando na almiski irin nasu na sarakai.Waziri Hidaisu ya cika murjejen kato mai kirar sadaukai domin gaba dayan jikinsa cike yake da tarin tsoka,kwanji da jijiyoyi,a gaba daya mazajen dake filin ma babu mai girmansa da kwarjininsa.Kawai sai ya nuna Safirat da tsinin takobinsa ya budi baki cikin kakkyausar murya yace ke yarinya idan duk fadin garin nan babu wani da namiji dayai saura saini ba zaki firgita ni ba na kasa tunkararki da yaki,ina mai tabbatar miki da cewa ni zaki ne uban dawa don haka faduwata sai anyi da gaske,kibar ganin cewa kin sami nasara akan sarki Safwan kiyi zaton cewa nima zaki iya samu a kaina,kuma idan kin kisa ki ajiye kwari da bakan naki na sihiri mu yaki juna da zallan karfin damtsen,u da iya yakinmu ba tare da karfin sihiri ba ki yadda zanyi fata fata dake a nan wurin,ai komai lalacewar namiji yana gaba da mace har abada.Koda Hidaisu yazo nan a jawabinsa sai zuciyar Safirat ta kama tafarfasa kamar zata kone don haka sai ta cire kwari da bakan dake rataye a bayanta kuma a lullube cikin bakin mayafi ta mikawa Gargus ya rike mata.Koda ganin haka sai idanun Gargus suka zazzrao hankalinsa ya dugunzuma ainun ya dubeta cikin alamun tsananin firgici yace haba ya shugabata saboda me zakiyi wannan ganganci shin kin manta ne da bakar wahalar da muka sha a baya kafin mu sami nasarar hada wannan kwari da bakansa ko kuwa so kike ki mutu a banza ki tarwatsa duk mafarkin mahaifinki?Koda jin wadannan tambayoyi guda biyu sai Safirat tayi murmushi sannan ta matso daf da Gargus tayi masa rada a kunne tace ai abinda baku sani ba shine daga ranar dana dana kwarin wannan baka da hannuna gaba daya sihirin dake jikinta ya shiga jikina don haka babu wani makami da zai iya tasiri a kaina.Koda kuw kuwa zamu kwana arba'in muna yin wannan yki domin bazan taba gajiya ba,koda gama fadin hakan sai jaruma Safirat ta zare takobinta ta juya ta fuskanci inda waziri Hidaisu ke tsaye.Koda ganin haka sai Hidaisu ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa ya rugo da gudu izuwa kanta,aikuwa itama Safirat saita ruga da gudu izuwa

Chapter 5 of 8