Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 8
sawu a bayansa.Cikin kaduwa da mamaki ya juya bayansa da sauri.Kawai sai yaga ashe Jaruma Safirat ce ta durfafo shi rike da makamanta tana tafiya da kyar kamar zata fadi.Al'amarin dayayi mutukar daure masa kai kenan domin bai taba nashin wani mahaluki ba ya iya tashi tsaye.Kodai mutum ya mutu nan take ko kuma ya kwantar cutar ajalin da zata iya zama sanadin ajalinsa.A takaice dai har abada mutm bazai mike ba saidai ya mutu yana jinya koda kuwa zai shekara dubu a duniya.Jaruma Safirat ta cigaba da tunkarar Bandaru ba tare da shakkar komai ba.Tana isowa dab dashi ta rinka kawo masa sara da suka cikin mugun zafin nama na zato.Koda ya fara kaucewa hare haren nata yaga tana neman taba jikinsa domin wannan karin da karfi na musamman tazo masa dashi.Ba shiri ya zare takobinsa mai tsananin girman gaske ya shiga karewa duk daya san cewa ko ta sami nasarar saran jikinsa ko sukar jikinsa bazai ko karcewa ba.Nan fa suka cigaba da kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta ta ban al'ajani.Suka tayar da kura akan tsaunin.Haduwar makamansu ta haifar da tarwatsin wuta gami da wata irin kara tamkar ana kwasa tsawa,sannan wani irin tururin hayaki ya rinka tashi,kai kace wuta ce keci akan tsaunin.Tabbas Bandaru yayi mamakin yadda akayi Safirat ta samu wannan gagarumin karfi alhalin yana ganin cewa yama gama da ita,babu wani sauran tasiri da zata iya yi.Saida aka shafe kusan ranin sa'a ana yi wannan dauki ba dadi tsakanin Jaruma Safirat da Bandaru amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba.Koda Bandaru yaga wankin hula zai kaishi dare saiya sauya salon fada ya hada dakai mata naushi da bugu.Ai kuwa sai ta rinka gocewa tana karewa kuma tana maida martani,amma fa duk sa'adda suka hannaye sai taji kamr karfe take duka tamkar hannunta zai karye,amma saboda tsananin naci gami da tsananin juriya taki ja da baya ko ta daina kai hari.Duk sa'adda ta samu nasarar naushin jikin Bandaru sai taga ya shanye dukan koda kuwa akan fuskarsa ne.Kuma sai taki yarda ya samu jikinta da naushi ko bugu.Koda Bandaru yaga haka saiya shammaceta ya jeho mata jelarsa ya kanannade kugunta da nufin ya dagata sama ya rotsa da kasa don ta ratattake kamar yadda yayiwa wannan bishiya.Koda Jaruma Safirat ta gane nufinsa sai tayi wuf ta cilla addarta cikin katon bakinsa,al'amarin da yasa ya kasa dagata sama kenan ya makata a kas.Kafin ya zura hannunsa cikin bakin ya zaro addar saboda tatokare masa numfashi da hadiyar miyau sai Jaruma Safirat ta rugo da gudu ta daka tsalla sama ta doki kotar addar tata data leko wajen bakinsa.Take addar ta wuce izuwa cikin makogwaronsa ta tsaya cak ita bata wuce ciki ba,kuma bata fito waje ba.Ba shiri Bandaru ya warware jelarsa daga cikin kugun Safirat ya durkusa kasa ya fara kokarin amai.Damar da Safirat ta smu kenan ta rufe shi da sara da suka gami da naushi da bugu ta ko'ina domin ta gano lagonsa.Amma sai taga kamar ko'ina a jikinsa baya jin sara da suka ko naushi da bugu.Ko kallon Safirat Bandaru baiyiba kawai kokari yake ta amayo addar data shuge masa baki.Nan take Safirat ta gano cewa ai bakinsa shine lagonsa,don haka sai ta shammaci Bandaru a lokacin daya wangame bakinsa ya zura hannunsa guda nufin ya zaro addar,cikin zafin nama ta sake soka takobinta cikin bakin,itama rabinta ya shige makogwaronsa.Ai kuwa sai Bandaru ya kurma uban ihu ya fadi kasa yana birgima da ihu ya fadi kasa yana birgima da ihu sakamakon tsananin zafi da zogin dayake ji yana mai ci gaba da kakarin mutuwa.Wannan itace babbar damar da Safirat ta samu ta wuce izuwa inda aka ajiye wannan baka.Tana isa tasa hannunta guda ta dauki bakan.Bakan na barin kan karfen da aka dorata sai gaba daya wajen ya haskake da wani irin haske na musamman.Ihun aljanun dake dajin gaba daya ya cika dodon kunne.Ashe aljanu ne suka rinka kumbura suna yin bindiga suna tarwatsewa izuwa kwayoyin zarra saboda an karya tasirin sihirinsu na tsafi wanda ba'a taba karyashi ba tsawon shekaru dari uku da daoriya,tun daga lokacin da aka kirkiki wannan tsaunin aka zuba abubuwan dake kansa.Saida Jaruma Safirat ta ratata wannan baka a kafadarta sannan wannan haske na musamman ya bace bat.Ihun aljanun ya dauke dif tamkar daukewar ruwan sama.A daidai wannan lokacine Safirat ta juya da baya cikin tsananin farin cikin samun nasarar dauko bakan.tana dingishi gami da dafe kirjinta kuma tana yin kakin jini tana tofarwa saboda tsananin zogin da take ji akan kirjin nata sakamakin naushin da Bandaru yayi mata.Har Safirat ta wuce ta gaba Badaru wanda ke kwance a kas magashiyan cikin gigtar mutuwa.Sai ta dawo ta baya ta sunkuya a kansa ta zura hannayenta biyu cikin bakinsa ta zaro takobinta da addarta daga cikin makoshinsa.Faru war hakan ke da wuya Bandaru ya furzar da ruwan dafi daga cikin bakin nasa a lokacin da numfashinsa ya dawo daidai.Ya bude idanunsa da kyar wadanda tuni sunrune sun zama farare kal.Sannan a hankali idanun suka dawo yadda suke da,sannan ya tashi zaune da kyar ya budi bak ya kirawo sunan Safirat.Maimakon ta waigo ta dubeshi sai ta tsaya cak a inda take sannan tace shin kana da wani abin fadi ne a gareni?Koda jin wannan tanbaya Sai Bandaru ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubi Safirat yace,saboda me kika ceci rayuwata?Koda Safirat taji wannan tambaya daga gareshi sai ta juya ta dubeshi tayi masa dan guntun murmushi tace,tace saboda kafin mu fara yin gumurzun yaki ni da kai kayi min alfarma guda biyu.Alfarma ta farko itace ka shawarceni da kada nayi yunkurin daukar wannan baka na hakura na sauka kan tsaunin saboda baka son ka cutar dani.Alfarma ta biyu kuwa itace ka nuna mini zahirin karfinka domin na tsorata dakai na fasa yakarka domin na tsira da rayuwata.Wannan duk alamun ne na tausayi da jin kai.Nagode amma na biyaka tunda ba ceci rayuwarka a yanzu,amma ka sani cewa kai ne namijin karshe da zan yiwa taimako ko jin kai a rayuwata.Koda gama fadin hakan sai Safirat ta yunkura da nufin ta sauko daga kan tsaunin amma sai Bandaru ya sake kiran Safirat yace zan sake yi miki alfarma ta karshe a rayuwata.Idan kika sauka daga kan wannan tsaunin kiyi matukar taka tsantsan da wannan Baka taki kuma kada ki yarda da kowa domin masu son su rabaki da ita suna da yawa.Ke hatta sarkinku a haukace da farautar wannan Baka na hannunki kuma zai iya kashe ki domin ya mallaketa!.Banda shi a yanzu haka akwai jarumai guda dari biyu da arba'in gami da matsafa dari uku da sittin da kuma manyan sarakai tara wadanda suka biyoki izuwa cikin wannan daji suka yi lamfo suna jiran ki gama shan wahala ki dauko bakan sannan su shammaceki su rabaki da shi,domin su karasa can dajin Sarkuf su isa kogon mutuwa su dauko kurtun kwarinsa.Shawarar farko da zan baki itace ki lullube wannan baka naki cikin mayafi domin haskensa ne zai tona asirinki duk inda kike.Shawara ta biyu ki daureshi tamau a jikinki ko barci zakiyi ya kasance akansa zaki kwanta yadda ko yaya aka tabashi zaki ji.Shawara ta uku itace kada ki kuskura kiyi gaba da gaba da wadannan jarumai,matsafa da sarakan da suka biyoki izuwa cikin wannan daji.Kiyi iya kokarinki wajen boye musu har ki fice basu ganki ba,idan kuma suka farmaki kar ki yadda ki shafe sama da rabin sa'a kina yaki dasu.Ki tsere ki barsu ki bace mus da gani.Na sani cewa babu wanda zakiyi mamakin cin amanarsa a gareki sama da sarkinku wato Safwan wanda tun baki fi shekara tara ba a duniya kuke yin gagarumar soyayya.To kada kiyi mamaki domin tun sa'adda ya gano batun kwari da bakan da mahaifinki ya sana'anta a cikin shekaru talatin yaji ya tsaneki kuma ya zamana cewa bashi da wani buri da yafi ya hallaka ki ya rabaki da kwari da bakan.Koda Bandaru yazo nan a zancensa sai Jaruma Safirat ta kamu da tsananin bakin ciki har hawayen takaici ya zubo mata saboda tsananin son sarki Safwan.A yanzu haka akwai alkawarin aure a tsakaninsu,itace ta dakatar da batun auren bisa cewa sai bayan ta dauko kwari da bakanta a inda mahaifinta ya adana mata sannan za'a daura musu auren.Boka Saiham wato Mahaifin Jaruma Safirat ya kasance aminin mahaifin Sarki Safwan,domin Saiham ne mai bashi tsaro da kariya daga dukkan abin ki da makiyansa.Kauna da amanar dake tsakaninsu tafi gaban kwatance don haka tun sarki Safwan da Safira suna yara kanana suka shaku ainun har suka fara girma soyayya ta kullu.Daga ranar da mahaifin Sarki Safwan ya gano cewa boka Saiham ya fara sana'anta wannan kwari da baka wacce in ya kammalata zai iya mallakar duniya gaba,ya mulki kowa da komai.Sai kishi ya turnukeshi,yaji babu abinda ya tsana sama da boka Saiham din.Da farko kafin ya tsane shin babu irin shawarar da bai bashi ba cikin hikima da basira akan ya tsayar da sana'anta wannan kwari da baka amma sai Boka Saiham yaki har shima ya fusata ya daka masa tsawa yace,saboda me zaka tsayar dani akan sana'anta abinda babu wani matsafi daya taba yin kamarsa tun daga farkon wanzuwar duniya kawo izuwa yanzu?Shin kana ganin cewa idan na kammaka hada wannan kwari da baka zanyi amfani da ita ne wajen cutar da sarakai irinka?To ka sauya tunani ni na kirkiri wannan kwari da baka ne domin na kare kasata kawai daga sharrin abokan gaba.Burina 'yata ta gajeni akan wannan kuduri ko a bayan raina.Kga kenan idan danka ya auri 'yata zata zamo mai baiwa sarautarsa da kasarsa kariya ta zamo tamkar sarkin yakinsa.Koda jin wannan batu sai Mahaifn Sarki Safwan ya tari numfashin Boka Saiham ya daka masa tsawa yace,yakai tsohon aminina kayi sani cewa masu iko da isa basa zama waje daya,idan har ka mallaki wannan kwari da baka tamkar ka zamo sarki ne,kaga kuwa ba'ayin sarki biyu a cikin gari guda.Ko mutuwa kayi idan 'yarka ta gaji wannan baka ta zama sarauniya,domin dole ne jama'ar gari su rinka tsoronta suna girmamata kamar yadda za'aji tsoron dana a girmamashi.Saboda haka dole ne cikin abu biyu ka zabi daya,kodai ka fasa sana'anta wannan kwari da baka ko kuma ka dauki alkawarin cewa idan ka kammalata niko daya ne zasu mallaketa.Idan kuma ba haka ba kuwa zumuncin dake tsakaninmu zai rushe mu zama abokan gaba na har abada.Idan kuma har hakan ta faru na rantse da girman karagata sai ka fini nadama da bakin ciki kuma burinka bazai taba cika ba bare na 'yarka ya cika.Koda mahaifin sarki Safwan yazo nan a jawabinsa sai hawayen takaici da bakin ciki ya zubowa Boka Saiham yace,na sani cewa duk irin sihirin tsafin danake takama dashi kaima kana dashi.Haka kuma duk irin jarumtakar da nake da ita ta karfin damtse da iya yaki kana dasu,danka ma uana dasu kamar yadda tawa 'yar take dasu.To amma ka sani cewa mu zuri'armu muna da tsananin sa'a da rabo bisa duk abinda muka sa a gabanmu.Saboda haka ina mai shawartarka da kada ka kuskura ka bari mu zamo abokan gaba,zaifi kyau mu ruke zumuncinmu gami da kaunar juna izuwa kan 'ya'yanmu da jikokinmu.Koda gama fadin haka sai Boka Saiham ya mike tsaye ya fice daga cikin fadar ba tare da yayiwa mahaifin sarki Safwan cikakkiyar sallama ba.Ai kuwa daga wannan ranan mahaifin sarki Safwan ya shiga shirye shiryen yadda zaiyi ya hana Boka Saiham cigaba da sana'anta wannan kwari da baka amma sai ya kasa samun nasara.A karshe ne ya yanke shawarar kashe boka Saiham ya hada baki da wata amintacciyar baiwarsa aka zuba masa guba a shayinsa yasha.Boka Saiham ya sani cewa na zuba masa guba a shayinsa kuma yasan cewa sarki Ne yasa aka zuba masa amma saiya dauki kofin shayin a lokacin da hawaye ya subuto masa yasa a bakinsa ya shanye shayin.Yana gama shanye shayin sai ya danki makoshin baiwar tasa da hannun guda ya shaketa ta fara kakarin mutuwa tana kokarin cire hannunsa daga kan wuyan nata amma ta kasa.Boka Saiham ya kurawa baiwar idanu yana mai cigaba da zubar da hawaye yace,yake wannan baiwa tawa amintacciya,yau shekara arba'in da daya kenan kece ke yimin bauta.Tun kina da kuruciyarki na siyoki a matsayin baiwa na rene ki harkika girma.Daidai da rana daya ban taba sabanin ba ko cin amanata,amma yau gashi saboda kwadayin matsayin da sarki zai baki gami da dukiya,kin yarda kisa mini guba a shayi na nasha na mutu.Kin manta da duk halaccin danayi miki a baya.To ki sani cewa nasha gubar kuma zan mutu,amma bazan mutu ni kadai ba,kema zaki mutu kuma shima sarkin tabbas mutuwa zaiyi kuma nine zan kashe shi.Wannan guba daku ka zuba mini a cikin shayina bazata zamo sandain ajalina ba,sai nan da cikar kwana ashirin da daya,kuma a halin yanzu saura kwana takwas kacal na kammala sana'anta Kwari da Bakan nawa.Gama fadin haka ke da wuya sai hawayen nadama ya zubowa wannan baiwa ta boka saiham sannan farar dafara ta zubo daga bakinta kuma idanunta suka kafe jikinta ya sandare ta zama gawa.Take Boka Saiham ya rungume gawar baiwar ya fashe da matsanancin kuka na bakin ciki.Saida ya shafe sa'a uku rungume da gawar yana ta gunjin kuka sannan matarsa Zaituna ta shigo cikin falon gidan.koda taganshi rungume ta gawar baiwarsu yana ta faman rusa kuka sai itama ta kama kuka.Tazo ta cireshi daga cikin jikin gawar ta dubeshi cikin tsananin kaduwa da bakin ciki tace wane ne ya kashe mana baiwarmu ta amana,wacce muka raineta tun kuruciya tamkar 'yar cikinmu? Koda jin wannan tambaya sai Boka Saiham ya rungume Zaituna a kirjinsa ya kankameta har sai da yaga ta sami yar nutsuwa sannan ya bata labarin duk abinda ya faru tsakaninsa da sarki da kuma gubar da sarki yasa wannan baiwa tasu ta zuba masa a cikin shayi ya sha.Ya tabbatar mata da cewa nan da cikar kwanaki ashirin da daya zai mutu kuma tare da sarki zasu mutu tare.Yayi wani kakari sannan ya zubar da kumfar gubar,daga bisani ya cigaba dacewa,amma idan Safirat ta cika shekaru sha takwas a duniya ki... KIBIYA RATSA MAZA Littafina na daya(1) Part C Amma idan safirat ta cika shekaru goma sha takwas a duniya ki bude akwatina ta karfe ki dauko mata kundina ki bata ta karanta.Bayanin duk abinda zatayi ta gajeni yana ciki kuma ki gaya mata cewa ta adana wannan kundin da kyau cikin sirri.Kuma ta tabbatar da cewar dare da rana tana tare dashi.Koda gama fadin haka sai Zaituna ta sake rungume Boka Saiham ta fashe da sabon kuka.Al'amarin daya karya zuciyarsa kenan shima yaci gaba da kukan.Kamar yadda Boka Saiham ya fada haka al'amari ya kasance sai da ya kammala sana'anta kwari da bakansa sannan kwanakinsa daya diba na ajalinsa suka cika yace ga garinku.Shima Mahaifin Sarki Safwan a wannan rana ya mutu ba tare da wata cuta ba domin lafiyarsa kalau yaje fada ya dawo gida.Koda ya shiga turakarsa ya kwanta akan gado domin ya huta shi kenan sai fito da gawarsa akayi.Amma kafin ya mutu ya barwa dansa Safwan wasikar cewa yayi taka tsan tsan da Safirat 'yar boka Saiham ya cire sonta daga cikin zuciyarsa a asirrance ba tare da ya nuna mata ba a zahiri.Wannan batu ba karamin girgiza tunanin Safwan yayi ba,bisa wannan dalili ne ya tsananta bincike a cikin hallarar tsafinsa har ya gano cewa a mutuwar mahaifin nasa akwai sa hannun boka Saiham kuma dama yasan da batun kwari da bakan da boka Saiham ya sana'anta kuma ya baiwar 'yarsa Safira gadonta.Tun daga wannan rana ne sarki Safwan ya dauki alkawarin cewa saiya kashe Safira ya rabata da wannan kwari da baka.ko dan ya dauki fansar ran mahaifinsa.Abinda bai sani ba shine mahaifin nasa ne ya fara zubawa Boka Saiham guba a shayi yasa aka bashi ya sha. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ Jaruma Safira na kuka cikin tsananin bakin ciki ta sauko daga kan wannan Tsaunin Lauhul Farras,tana saukowa rataye da wannan baka sai taga ragowar dodannin nan sun kura mata ido suna kallonta cikin tsananin mamaki kuma suka kamu da tsananin tsoronta.Ba shiri suka rika darewa suna bata hanya.Ta rika kutsawa ta tsakiyarsu tana tafiya cikin tangadi saboda tsananin gajiya kuma ga hawaye na zuba a idonta a lokacin da take tuno da duk abubuwan da suka far a baya tsakaninta da sarki Safwan.Safira ta tuno da irin shakuwarsu da kuma soyayyarsu tun suna yara kawo izuwa girmansu da yadda suka kasance kullum a tare dare da rana babu abinda yake raba su face kwanciyar bacci.Ta tuno da alkawarin dake tsakaninsu na aure kuma ta tuno irin amincin dake tsakanin iyayensu.Koda tazo nan a tunaninta sai tace kai bazai yiyu ba ace yanzu Safwan ne ya zamo makiyinta ba.Safwan ba zai taba yunkurin kasheta ba ko yaci amanarta saboda kawai ya rabata da wannan kwari da baka.Wata zuciyar kuma sai tace da ita ke dai kiyi taka tsan tsan dashi domin masu iya magana sunce namiji ba dan goyi bane kuma akan mulki ko dukiya mutum na iya sauya halinsa.Haka dai Safira ta tsaya cak a kusa da bakin tsaunin Lauhuk Farras tana tayin tunani.Koda taga tunanin nata yaki karewa kuma gashi ba zata iya ci gaba da tafiya ba,domin raunukan dake jikinta sai damunta suke da zogi da radadi saita zauna a kasa ta bude jakar guzurinta ta dauko zare da allura ta dinke raunikan da yayi dan zurfi sannan ta shafa magani akan sauran.Tana cikin yiwa kanta magani ne taga Bandaru tsulum a bayanta yana kallonta cikin murmushi.Kawai sai ya tsuguna bisa gwiwarsa ya dubeta cikin girmamawa yace,Ya shugabata nazo ne gareki domin na baki wata shawara gami da taimako guda daya.Zaifi kyau ki kwana nan tunda rana ta fadi gari ya soma duhu domin idan kika ce zaki fita daga cikin wannan daji a cikin wannan dare sai makiyanki sunfi samun damar cimmaki tunda ko yaya kika motsa zasu ji sautin tafiyar tunda darene.Kuma na gaya miki cewa suna nan a lallabe a gaba kadan sunyi lambo,kawai jira suke suga fitowarki tunda su bazasu iya karasowa ba nan.Taimakon da nake son na miki kuwa shine ina son na baki yara na guda arba'in wadanda zasu taimaka miki wajen yakar makiyanki duk da cewa bazasu iya da makiyan naki ba saboda tsananin yawansu,karfinsu da shirinsu,amma zasu rage miki masifarsu.Inda ace ina da ikon barin wannan tsauni dana biki na zama babban mai tsaron lafiyarki ko don rabani da wannan bauta da nake ciki ba har ta tsawon shekaru dari uku da doriya face bayan kin hada kwari da bakanki.Ina son kiyi min alkawarin cewa idan kin kai ga wannan gaci zaki kizo ki rabani da wannan tsauni na zamo shugaban dakarunki tunda kaf duniya babu jarumi mai karfin damtsena da iya yakina.Da jin wannan batu sai Jaruma Safirat tayi murmushi tace shi kenan nayi alkawari indai na cika nawa burin zanzo na tserar daka daga wannan bauta kuma na baka shugabancin dakaruna.Koda jin haka sai farin ciki ya lullube Bandaru yayi godiya.Nan take ya umarci dodanni biyu suka hau kan tsaunin Lauhul Farras suka dauko tanti,shimfida ta alfarma gami da kayan abinci na alfarma suka zo suka shiryawa Jaruma Safirat.Bayan sun gama kafa mata tantin ne ta shiga ciki ta zauna ta ci ta sha tayi hani'an.Koda ta hau kan shimfidar da ka yi mata taji taushinta sannan ta dubi kayan alatun da aka shirya mata a cikin tantin sai ta gyada kai cikin murmushi tace,hakika dole ne mutane su so mulki da dukiya a cikin wannan duniya.Nikuwa idan na gama hada wannan kwari da baka nawa zan dandana dadin mulki naji yadda sarakai keji.Tana gama fadin hakan sai ta kwanta akan shimfidar ta mikar da kafafunta.Abinka da gajiyayye wanda yaci ya koshi,nan danan barci ya saceta bata sani ba. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ Rundanace ta manyan jaruman da duniya ke takama da ita,tun daga nesa idan ka hango wannan runduna zaka yi zaton gaba dayan mutane da aljanun duniya ne suka fito yaki.A gaban wannan runduna wani hatsabibin sarki ne mai tsananin mummunar kama da girman jiki ga manyan damatsa.Kakkarfa ne na gaske haye akan toron giwa.Sarki Haimarul Dainun ya kasance daya daga cikin manyan sarakunan duniya wanda yake mulkin daular kasashen nahiyar Habasha gaba daya.Wannan fitowa da Sarki Haimarul Dainun yayi tane da nufin cewa bazai koma gida ba har sai ya mallaki kwari da bakan da boka saiham ya sana'anta a bisa kudurinsa na ya mallaki duniya.Sarki Haimarul Dainun ya sha alwashin kawar da dukkan wani mahaluki dayake da irin kudirinsa.Akan wannan dalili ne ma yasa ya debo gaba dauan rundunarsa ta yaki izuwa dajin Lauhul Farrasa.Lokacin da Sarki Haimarul Dainun yayi wannan fitowa baya barin duk wani karamin kauye damanyan birane face ya yakesu ya hallakasu gaba dayan masu rauni daga cikinsu kamar mata,tsofaffi da kananan yara,sannan ya kona gidajensu gami da rushe sauran ginin garin.Jarumai dake cikinsu kuwa ya kamasu su zama daga cikin rundunarsa ta yaki bisa tilas.Abinda sarki Haimarul Dainun bai sani ba kuwa shine gaba dayan manyan sarakunan duniya suma sunyo tattaki izuwa dajin Lauhul Farras domin mallakar kwari da baka.Lokacin da sarki Haimarul Dainun da rundanarsa suka zo wani katon fili ma'abocin dogayen itatuwa tun daga can nesa suka hango wani jarumi da takubba guda ya juya bansa.Jarumin yana sanye da wani kwalkwali ne ba bakin karfe wanda a dalilinsa ne babu mai iya gabe kowaye shi.Koda ganin wannan jarumi sai Sarki Haimarul Dainun ya daka masa tsawa yace,yakai wannan dan matashin jarumi ma'abocin boye fuskarsa wane dalili ne yasa kazo ka tare min hanya?Ko ka gaji ne da rayuwarka ta duniya? Sa'adda sarki Haimaruk Dainun yazo nan a zancensa sai wannan jarumi ma'abocin boyayyiyar fuska ya bushe da wata mahaukaciyar dariya sannan ya juyo ya fuskanci sarkin gaba da gaba sannan ya maida masa martani da cewa.Ya kai sarki Haimarul Dainun kayi sani cewa nazo gareka ne domin na gargadeka bisa wannan kudiri naka Ina mai shawartarla da ka koma gida kai da jama'arka domin kuwa har abda ba zaka iya jurewa tarin masifu da bala'in dake tattare da mallakar kwari da bakan nan ba.Idan kuwa kaki yanzun nan zan yake ka na tarwatsa wannan aniyar taka.Ka sani cewa ni Jaruma Safirat 'yar boka Saiham wadda mahaifina ya sana'anta wannan kwari da baka dominta.Nasha alwashin bazan bar kowane mahaluki darai ba muddin yace zai mallaki wannan kwari da baka dana fito dominsu.Koda Sarki Haimarul Dainun yaji wannan batu take ya kamu da mamakin kasancewar wannan jarumi ba namij bane ashe mace ce.Kuma ya kamu da tsananin farin ciki hadauwa da safira cikin sauki haka domin kuwa a dalilinta ne ya fito daga masarautar kasarsa.Takeyi duba izuwa safira yace,yake safira ki sani cewa na kasance a gaba dayan rayuwa komai na tunkara ina mai samun nasara a cikinsa don haka naek baki shawara da kiyi gaggawar miko mun wannan kwari dake dake tare dake domin ki samu ki tsira da rayuwa.Yayinda Sarki Haimarul Dainun yazo nan a zancensa sai ran safira ya baci ainun take sai safira ya zare takobinta ta afka cikin kakkautawa koda ganin haka sai Sarki Haimarul Dainin yayiwa dakarunsa tsawa yace me kuke jira da ita maza ku ciro min kanta ku kawomini nan,ai kuwa fadar hakan keda wuya sai gaba dayan dakarun suka yi mata rufdugu.Nan ga wuri ya hargitse aka kaceme da masiffaen yaki ya zamana cewa duk inda safira ta kai sara saidai kaga maza na zubewa kasa tamajar ana sassabe a gona.Wohoho! Aika ga mai kareka lokaci guda safira ta bazar da gaba daya dakarun dake gabanta ta falfala da azababben gudu ta tunkari inda sarki Haimarul Dainun yake bisa toron giwarsa.Kafin yayi wani yunkuri ta daka uban tsalle sama kamar daga cikin baka aka harbota kawai sai gani akayi ta fille masa kai.Koda sauran dakarun nasa suka ga kan sarkinsu a sama cikin iska sai suka dimauce suka zubar da makanmansu suka cika wandonsu da iska suka bazama izuwa cikin daji,taje safira ta koma inda ta baro Bandaru da sauran Yaransa. SHIN SAFIRA ZATA SAMI NASARAR HADA KWARI DA BAKAN HAR TAYI AMFANI DA ITA? INA LABARIN SARKI SAFWAN,WANE TANADI YAKEYI AKAN FUSKANTAR JARUMA SAFIRA? YAYA SAURAN MANYAN SARAKUNA DA BOKAYE ZASU FUSKANCI SAFIRA. Muhadu a littadi na biyu domin jin cigaba wannan kasaitaccen labari. KIBIYA RATSA MAZA!!! Littafi Na Biyu (2) Part A A CAN BAKIN DAJIN TSAUNIN LAUHUL-FARRAS kuwa runduna ce ta sarakai,matsafa,jarumai da manyan bokayen duniya suka kakkafa sansani tsubi tsubi a wurare dabn daban.Kowace runduna ta fito ne domin farautar Jaruma Safirat ta kasheta sannan ta rabata da wannan baka data dauko a kan tsaunin Lauhul Farras.Wannan shine kura da shan bugu gardi da kwashe kudi.Daga cikin rundunar sarakan da suka zo har da sarki Safwan tare da dakarunsa na yaki mutum dubu goma kuma suma sun kafa sansaninsu wanda shine mafi kusanci da tsibirin Lauhul Farras.Lokacin da rana ta fadi ne sarki Safwan tare da shugaban dakarunsa wani barde da ake kira Barha na tsaye a bakin tantin sai sarki Safwan ya dubi Barha yace amma nayi mamakin abinda yasa har yanzu Safirat bata fito ba daga cikin wannan daji na tsibirin Lauhul Farras.Koda jin haka sai Barha yayi gyaran murya yace haba ya shugabana ai bai kamata kayi mamaki ba tunda ka sani cewa babu wani mahaluki daya taba hawa kan tsaunin Lauhul Farras ya sauko kasa a raye.Babu mamaki itama ta mutu ne a lokacin hakan.Sarki Safwan ya girgiza kai yace Safirat bata mutu ba kuma nayi bincike a cikin madubi tsafina naga cewa zata rayu bisa duk irin gumurzun da zatayi da dakarun dake kan tsibirin har ta sami nasarar dauko wannan sihirtaccen baka na mahaifinta.Sa'a dda barde Barha yaji wannan batu sai yayi ajiyar numfashi sannan ya dubi sarki Safwan cikin alamun tsananin damuwa da karayar zuciya yace ya shugabana yanzu dai da idanunka kaga runduna sama da guda arba'in a bayanmu ta manyan sarakan duniya,matsafa da jarumai masu ji da kansu.Yanzu koda ka sami nasarar kashe Safirat ka dauko wannan baka dake hannunta ta yaya zamu iya ficewa daga cikin dajin nan da bakan ta gaba wadannan miyagun rundunoni alhalin suma abinda suka zo farauta kenan?Dajin wannan batu sai sarki Safwan ya bushe da dariya.Al'amari n daya kara baiwa barde Barha mamaki kenan.Daga can sai sarki Safwan ya hade fuskarsa yace ai raba Safira da wannan baka yafi tsare bakan wahala.Duk wadannan rundunoni da kake gani na banza ne muddin daya daga cikinsu bata rigamu karbar bakan ba.Bisa wannan dalili ne yasa kaga ni nayi kundunbala nazo daf da bakin dajin tsaunin Lauhul Farras saboda ya zama nawa da zarar Safira ta fito ya kasance nine mutum na farko da zatayi arba dashi.Ninasan cewa indai zamuyi GABA DA GABA da ita to saina rabata da bakan tunda bata finin KARFIN DAMTSE ba dana tsafi kuma bata fini iya yakio ba.Duk abinda take takama dashi nima ina dashi ko mafiyinsa.Kuma muna haduwa zan shaida mata cewa ubanta ne ya kashe mahaifina don haka ina son na dauki fansa a kanta,kaga bata da ikon cewa naci amanar soyayyarta.Kao bari na gaya maka gaskiya,koda Mahaifinta bai kashe nawa ba zan iya zuba idanu ba ina kallonta ta fini matsayi ba da daukaka tunda nine sarkinta.Dole ne ka kawar da batun soyayya na ceci mulkina da kasata tare da duk al'ummata.Babu sani ba sabo a tsakanina da Safira saidai KAIFIN TAKOBI ya rabamu.A yanzu haka ina zargin cewa Safirat zata iya fakar numfashinmu ta fito daga cikin dajin Lauhul Farras a cikin wannan dare ta sulale ta gudu ba tare da wani ya gantaba.Koda jin wannan batu sai Barde Barha ya gyada kai cikin alamun shakku yace haba ya shugabana ta yaya Safirat zata iya wucewa ta gabanmu ba tare da ka ganta ba tunda bata da wani sihiri na bata wanda baka da shi.Nidai kawai shawarar da zan baka itace kada ka kuskura kace zakayi bacci a cikin daren nan domin ta bakin kane a ko yaushe zata iya fakar numfashi ta fito din.Koda jin haka sai sarki Safwan yayi murmushi yace tabbas maganarka dutse ce.Dole ne hakura da bacci gaba daya a daren yau.Ai kuwa sarki Safwan bai yarda ya kara shiga cikin tantinsa ba.Kujera aka kawo masa ya hau ya zauna a waje yana mai fuskantar cikin dajin tsaunin Lauhul Farrs kuma takobinsa nakan cinyarsa ya dafeta da hannunsa guda sannan kuma yasa wata kuyangarsa ta dafa masa shayi aka zuba masa sinadaron hana bacci a ciki yasha.Har gefen asuba idanun sarki Safwan a bushe suke ko alamar bacci babu a tare dashi. *Al'amarin Jarum Safirat kuwa tunda ta kwanata a cikin tantinta ta kama bacci ko kyakkyawan motsi bata sakeyi ba har asuba tayi.Kawai sai ji tayi ana tashinta kamar a mafarki.Safirat ta mike tsaye Zumbur a dan firgice.Tana bude idanunta sai taga ashe Bandaru ne tsugune a gabanta kansa sunkuye don biyayya.Ba tare daya dago kansa ba ya dubeta yace ya shugabata yanzu ne daidai lokacin daya kamata ki shirya ki fice daga cikin dajin nan ki durfafi hanyar da zata kaiki can Dajin Sarkif domin ki isa kogon mutuwa don dauko kuttun kwarinki.Kamar yadda na gaya miki a baya cewa masifar dake cikin dajin Sarkif ta ninka wacce ke cikin wannan daji namu sau goma don haka saiki jajurce kuma kiyi matukar juriya da hakuri.Duk tarin rundunonin makiyan da suka biyoki izuwa nan ba zasu iya binki ba izuwa dajin Sarkif amma ina zargin cewa mutum daya zai iya binki.Koda Bandaru yazo nan a zancensa sai Jaruma Safirat ta tari numfashinsa tace nasan kowane ne ba wani bane face sarki Safwan babban masoyina a da yanzu kuma babban makiyina.Koda jin haka sai Bandaru yayi murmushin murna yace ina farin ciki da kika fahimci hakan duk da cewa har iyanzu nasan zuciyarki tana miki wasu wasi akan hakan.Amma dai na san cewa lokaci zai tabbatar miki da gaskiyar alamari.A yanzu haka tuni dakaru arba'in da nayi miki alkawari sun gama shirin tafiya ke suke jira.Kamar yadda na gaya miki a baya,kada ki fita daga cikin dajin nan goye da bakanki tsirara face kin lullubeshi cikin mayafi saboda hasken sane zai fara ™Abubakar Haleefah Physicist™ tona miki asiri.Yanzu ga mayafin da zaki lullube bakan na kawo miki.Nan take Bandaru ya daga hannunsa sama saiga wani bakin mayafi ua bayyana tsulum a hannun nasa kawai sai ya mika mata ta karba yace wannan ne kadai mayafin da zai iya boye hasken wannan kwarin naki.Maza ki lullubeshi yanzu.Ba tare da wata gardama ba kuwa sai Safirata ta mike tsaye ta ciro Bakan daga bayanta wanda ta daureshi tamau kuma ta kwanta a kansa tayi bacci tun a daren jiyaSafirat na ciro bakan sai ta lullubeshi da wannan mayafi.Nan take kuwa taga hasken nasa ya bace bat.Cikin sauri ta mayar da bakan bayanta ta goyashi kuma ta daureshi tamau.Faruwar hakan keda wuya sai Bandaru ya sake daga hannunsa guda sama saiga wani takalmi fade na fatar damisa ya baiyana tsulum akan hannun nasa.Kawai sai ya mika mata yace ungo wannan ki sanya a kafafunki.Indai har da wannan takalmin a kafarki babu yadda za'ayi wani yaji sautin tafiyarki ko gudunki.Abinda nakeso dake shine daga nan ke da dakarun dana baki guda arba'in zaku fice da gudun tsiya ku nufi arewa nan ne hanyar da zata kaiku izuwa dajin Sarkif.Kiyi gudu iya karfinki da iyawarki.Ta gaban makiya zaku wuce amma babu mai iya cimmaku saidai a riskeku a can dajin Sarkif inda kowa zai shiga cikin tararrabin rayuwarsa.Ni kaina ba zan baku tabbacin cewa zaku tsira da rayuwarku ba acan.Da wannan furuci nake yi miki bankwana yake sarauniyar Duniya ta gobe.Kuma inayi miki fatan sa'a da nasara bisa wannan gagarumin aiki dake gabanki.Ina fatan zaki zamo mai cika alkawari a gareni bayan bukatarki ta biya.Bandaru na gama fadin hakan saiya juya domin ya fice daga cikin tantin amma sai Safirat ta kira sunansa da sauri tace nagode bisa duk irin wannan taimako da ka bani kuma lallai zan zamo mai cika alkawari a gareka.Koda jin haka sai Bandaru yayi murmushi ya fice.Fitarsa keda wuya sai itama Safirat tayi yan kintse

Chapter 2 of 8