Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 8
baya izuwa inda fatattakakken tantinsa yake ya shiga kukkullashi yana gyara shi cikin matukar takaici da bakin ciki.Hakika inda ace yayi arba da wanda yayi masa wannan barna da sai yayi masa muguwar azaba ko KISAN WULAKANCI.Samazan ya hado itatuwa ya kunna wuta sannan ya zauna a gaban wutar ya dauko zare da allura ya kama dinke jakar guzurinsa wacce aka fatattakata.Gama dinke jakar keda wuya saiya fara gyangyadi kawai saiya bingire kasa ya kama bacci mai nauyi harda munshari saboda tsananin gajiyar dake jikinsa sakamakon doguwar tafiyar daya sha da kuma aikin sare bishiyar da yayi,tabbas jiki da jini akwai gajiya. MAI ZAI FARU DA WANNAN JARUMI? Sai Mu Hadu a Cikin Littafi Na Biyar Don jin cigaban wannan labari. °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!! Littafi Na Biyar (5) Part Â. BAYAN BACCI YA SACE SAMAZAN DA KAMAR DAKIKA ARBA'IN SAI GA WANI MURTUKEKEN KADA YA TASO SAMA DAGA KARKASHIN WANNAN RAFI.Masana tarihi da masu bincike a doron kasa sun tabbatar da cewa a duk fadin duniya babu wani kada mai girmansa.Wannan daji da Samazan ya shigo ana kiransa da suna Mautul Inzag.Fiye da shekaru dari daya da ashirin baya mutane da dabbobi,tsuntsaye da aljanu basa shigowa cikin wannan daji na Mautul Inzag saboda masifar wannan kada wanda ya kasance sihirtacce.Shi dai wannan kada asalinsa wani boka ne ya taba zama a gefen birnin dake daf da dajin Mautul Inzag ya samar dashi ya barwa mutane annoba.Ba komai ne yasa bokan yayi wannan kada ba sai saboda yar sarkin garin yake mutuwar so bayan ya shafe shekaru goma yana yi mata wahala kuma yana taimakon mahaifinta da birnin gaba daya bisa alkawarin za'a aura masa ita.Sai akayi masa butulci aka aurar da ita ga sarkin wani gari daban.Bakin cikin hakan ne yasa bokan ya kamu da ciwon zuciya.Koda ya tabbatar da cewa wannan shine ajalinsa saiya dauki alkawari cewa saiya haifarwa da birnin mai suna Kaldusa masifar da zatayi ta addabarsu har abada.Bayan kwana bakwai da mutuwar bokan ne kadan mai lakabi da Inzag ya baiyana a cikin wannan katon rafi.Baiyanarsa keda wuya sai duk dabbobi da tsuntsaye da aljanun dake cikinsa suka rinka ratsa ta cikin dajin basa isa birnin Kaldusa face sun zama gawarwaki,komai yawan rundunar mayaka da karfin sihirin su da suke zuwa musamman domin yakar kadan dayansu baya tsira da rayuwarsa.Idan kadan ya taka kasa girman takun sawunsa yana kaiwa fadin zira'i ashirin da kuma zurfin kamu goma.Tsawon Inzag kuwa daga kansa zuwa karshen jelarsa yakai kamu dari da sittin don haka yana iya kanannade jelarsa yayi gammo da ita.Gaba daya jikin nasa kaifi ne dashi tamkar zabira don haka duk abinda ya doka da jelar tasa koda kuwa dutse ne ko karfe saiya rabashi gida biyu ko ya ragargaza shi.Duk abinda Kada Inzag ya ciza da hakoransa indai mai raine take yake rubewa ya rinka fitar da tsutsotsi.Idan ya wangame bakinsa ya feso wani irin ruwa saikaga kamar ruwan sama ne ya sauko kuma duk abinda ruwan ya taba saiya narke ya zagwanye.Daga ranar da kada Inzag ya baiyana sai fari da talauci ya kama birni na Kaldusa ya zamana cewa duk shekara sai anyi mummunan fari,yunwa da cututtuka iri iri suka addabi mutane duk wanda yayi yunkurin yin Hijira kuwa saidai a tsinto gawarsa a bayan gari.Wani abin mamaki shine duk irin cutar da ta kama mutum ba zata kashe shi ba amma kuma baza'a taba warkewa ba koda likitocin duniya zasu taru a kansa.Bisa wannan dalili ne kasashen dake makwabtaka da kasar Kaldusa suke kyamatarsu aka hana su yin huldar komai da kowace kasa ya zamana cewa ba'a shigo musu suma basa shiga wata kasar.Bisa wannan dalili ne harkokin kasuwanci suka dakushe,abincin da ake nomawa a kasar ya daina isar talakawa,ya zamana cewa kowane gida sau daya akeyin abinci,komai rashin imanin mutum idan ya shiga cikin birnin Kaldusa yaga yadda mutane ke fama da rama da bakin talauci dole ne ya tausaya musu.Musamman idan ya dubi kananan yara yaga cewa zai iya kirga kasusuwan jikinsu.Haka ake fama da wannan masifa a birnin Kaldusa tsawon shekaru dari da ashirin kuma a dalilin hakanne kowa ya rungumi kaddara tun mutane na shiga dakin bautar garin suna rokon abin bautarsu akan ya magance musu wannan matsala har saida sukayi fishi suka daina bautawa gunkin nasu aka rufe dakin bautar gaba daya.Lokacin da Kada Inzag ya taso sama daga karkashin wannan rafi ya hango Samazan kwance a can gefe daya yana ta fama shara bacci sannan kuma yaga tantin daya rusge an sake kafashi.Nanfa mamaki ya kama Kada Inzag domin tsawon zamansa a cikin wannan daji shekaru dari da ashirin wannan ne karon farko dayaga bil'adaman daya iya shigowa har yazo bakin gabar rafin da yake ciki,cikin sanda Kadan ya fito daga cikin rafin ya zagaye Samazan har sau biyu yana kallonsa kawai yana nazarinsa.Maimakon ya hallakashi saiya sake ragargaza tantin nasa sannan ya koma cikin wannan rafi yayi nutso izuwa karkashinsa.Duk karfin sautin takun kadan da kuma karar rugujewar tantin bata sa Samazan ya farka daga baccin da yakeyi mai nauyi ba.Har saida gari ya waye,koda rana ta fito da dallare kan fuskar Samazan saiya farka daga bacci a firgice yana bude idanunsa yayi arba da wawakeken takun sawayen kadan kewaye dashi.Tunda Samazan ya fara yawon farauta a cikin dazuzzuka bai taba ganin sawun kafar dabba mai girma kamar wannan ba,abinda ya tsora tashi ma shine ganin zurfin takun sawun,ganin sawun ya nufi cikin wannan kogi ne ya tabbatar masa da cewa halittar ruwa ce.Abinda ya kara fadowa Samazan a rai shine me yasa wannan halitta bata kashe shi ba kuma ya akayi ta fito har ta zagayeshi amma baiji motsinta ba ya farka?Amsar da Samazan ya kasa baiwa kansa kenan.Kawai sai yace a ransa idan ma tsorona dabbar taji ai zamu hadu ne kafin nabar wannan daji(Kunji Gwarzon Namiji).Koda gama fadin hakan saiya dauko jakar guzurinsa ya fiddo da kalaci yaci sannan ya kama aikin sassaka kwale kwalensa.Saida Samazan ya yini yana wannan aiki har doshin magriba saadda gari ya fara duhu sannan ya dakata ya huta.Samazan bai kammala aikin kwala kwalensa ba sai bayan cikar kwanaki uku,kuma a tsawon wannan lokaci kullum saiya jiyo gurnanin wannan kada a cikin rafi amma ko kadan bai fito ba sunyi arba.Abinda bai sani ba shine kadan baya fitowa bakin gabar rafin face sai bayan kwanaki bakwai ko kuma idan wani abu ya fada cikin rafin bisa tsautsayi.A cikin wadannan kwanaki ukun ne kuma Samazan ya sami ™Abubakar Haleefah Physicist™ damar yin yawo sosai a cikin wannan daji har ya gano abinda yayi matukar bashi mamaki kuma ya jefashi cikin tsananin farin ciki.Ba komai ya gano ba face akwai dumbin dukiya mai tsananin yawan da babu kamarta a ko ina cikin duniya.Samazan ya gano cewa akwai tarin lu'u lu'u da zinare a cikin kogunan dajin wadanda za'a iya shafe shekara dari ana hakosu basu kare ba.Lallai idan da akwai kasar dake mallakin wannan daji kuma inda tasan da wannan dukiya da babu kasar da zata kaita arziki.Nan take Samazan yace a ransa ya zama dole na bincika na gani ko da akwai masarauta a kusa da wannan daji domin na nemi hadin kan sarkinsu mu hako wannan dukiya tare.Nikam Allah ya kawo mini karshen wannan rayuwa daga nan na daina yawon duniya don cika burina.Shidai Samazan ya baro kasarsu ne don neman arzikin da zai huce takaicin da dan sarkin garinsu ya kunsa masa kuma bisa alwashin hakanne yayi bankwana da iyayensa abin ya faru ne kimanin shekaru uku baya.Samazan ya kasance haifaffen birnin Hindu kuma mahaifinsa ne sarkin mafarauta na kasar gaba daya amma ya tsufa ainun don haka bashi da wani buri wanda yafi dansa Samazan ya gaje shi,amma inda matsalar take dan kanin sarkin Hindu wanda ake kira Balwan bashi da burin da yafi ya sami wannan sarauta ta sarkin mafarauta saboda da can asalin sarautar a gidansu take amma da akayi wata gasa sai mahaifin Samazan ya lashe gasar ya karbe kambun sarautar daga hannun mahaifin Balwan.Mahaifin Balwan ya kasance kasurgumin attajiri kuma a cikin harkar farauta tasa Allah yayi masa arziki na ban al'ajabi.Shi kuwa mahaifin Samazan bai tara wata dukiya ba ta'azo a gani ba amma yana da rufin asiri.Lokacin da mahaifin Balwan yaga mahaifin Samazan ya kwace sarautarsa sunansa nata daukaka shi kuma nasa na dakushewa sai yayi amfani da dukiyarsa ya rinka gine gine na kasaita a kasar Hindu kuma ya rinka taimakon talakawa da kuma duk wanda yake da wata matsala,ada ko sadaka bayayi bare kyauta.Duk inda aka nemi agaji kafin sarkin Hindu yakai nasa tuni mafarauci Hashmar yakai nasa..Nan da nan Hashmar ya zamo babban mutum a kasar Hindu sunansa ya daukaka ainun,darajarsa ta girmama ya zamana cewa ana girmamashi fiye da yadda ma ake girmama Sarki har takai cewa bisa dole sarkin ke jansa a jikinsa don shima kada tasa darajar ta zube.Nanfa Hashmar ya sami shiga ainun a wajen sarki har takai cewa shima babban mai baiwa sarki shawara ne akan dukkan al'amura kuma duk abinda ya zartar dashi ake zartarwa.Dama tun daga ranar da Imsar mahaifin Samazan ya kwace kambun sarautar a hannun Hashmar sai gaba mai tsananin ta kullu a tsakanin su don haka sai Hashmar yayi amfani da damarsa ta wajen sarki yasa aka hana yin farauta a cikin gaba daya dazuzzukan dake cikin kasar kuma ya hana hako ma'adanan kasa.Dama shima Imsar yana da wannan baiwa irin ta Samazan wato baiwar gano inda ma'adanan kasa suke,koda sarkin Hindu ya hana farauta da hako dukiya ta karkashin kasa,sai tattalin arzikin mafarauci Imsar ya dakushe ya zamana cewa babu wata hanya da yake samun kudi bisa dole ya koma harkar noma,noman ma sai yaki karbarsa,hakkane ya janyo sanadin talauci a gidansa ya zamana cewa da kyar ma suke tsira da abincin da suke ci.Tun Samazan baifi shekara tara ba a duniya suka tsinci kansu a cikin wannan matsala kuma a lokacin ne gaba mai tsananin ta yawaita tsakaninsa da Balwan.Tun suna yaran shida Balwan sun taso da sadaukantaka da iya yaki da farauta.Don haka duk inda suka hadu sai fada da yaki ya kamasu kuma duk sa'adda suka fafata kare jini biri jini sukeyi.Saidai tsananin wuya tasa su rabu bisa dole.Amma dayansu ya kasa hallaka dayan saboda karfin damtsensu dana sihirin tsafinsu yazo daya.Har suka girma a haka suke don hama ma sai suka daina yakar juna aka koma yin kiyayyar zuci,harara da kuma ba'a,sannan duk bala'in da daya yaga dayan a ciki bazai taimaka masa ba.Lokacin da Samazan ya zama cikakken saurayi ne dan shekara ashirin da biyar sai mahaifinsa Imsar ya matsa masa akan ya nemo matar aure saboda shi kadai ne dansa a duniya kuma yanason yaga jikansa.Koda jin wannan batu sai hankalin Samazan ya dugunzuma ya dubi Imsar cikin alamun tsananin damuwa yace haba yakai Abbana ya zaka ce nayi aure alhalin muna cikin wannan hali na rashi,wani lokacin ma abinda zamu ci a gidan nan ni da kai da mahaifiyata wahala yake yi mana,sau tari sai naje kasuwa nayi aikin karfi sannan nake samo mana abinci.Ka sani cewa a cikin zuciyata na dauki wani alkawari guda daya,alkawarin kuwa shine inason na shiga duniya na bazama cikin wadansu kasashen neman arziki.Burina shine na samo dukiyar da tafi ta Hashmar,ya zamana cewa gidanmu ya danne gidansa domin sai nayi abubuwan da suka ninka nasa sau dari.Bakin cikin daya kunsa maka ya dakusar da sunanka ya jefaka a cikin talauci da izinin abin bautarmu Kirishna sai shima ya fada ciki da dukkan zuri'arsa.Lallai saina daukar mana fansa,abinda nake bukata kawai a wajenka shine ka bani izini nayin wannan tafiya.Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa Imsar yace haba yakai dana shin ka manta ne cewa kai ne kadai 'da na a duniya,ta yaya kake zaton cewa zan barka kayi wannan tafiya wacce bansan ranar dawowarka ba,kuma babu tabbacin cewa zaka dawo a raye,gashi na tsufa karfina ya kare kuma ko yaushe rai zai iya halinsa duk da cewa tsufa ba mutuwa bane.Koda tsoho Imsar yazo nan a zancensa sai jikin Samazan yayi sanyi kuma shima yaji ya kamu da tsananin tausayinsa bai san sa'adda shima ya kamu da tausayinsa ba har idanunsa suka ciko da kwallah nan take suka rungume junansu suka kama kukan zuci.Daga wannan rana Samazan ya cire ™Abubakar Haleefah Physicist™ burin daukar fansa akan sarkin mafarauta Hashmar da iyalansa ya maida hankalinsa akan kokarin ruke gidansu da kyautatawa iyayensa da kuma tsare mutuncinsu har tsawon wata uku,ya zamana cewa shida iyayen nasa suna cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali saboda a wannan lokaci Samazan ya zage damtse yayi aikin karfi mai yawa ya samo yan kudade masu yawa don haka sai ya siyo musu abinci mai yawa wanda zai ishesu har tsawon shekara guda kuma ya baiwa mahaifiyarsa yan kudi masu yawa yace ta adana su saboda amfanin yau da kullum.Saboda jin dadin wannan abu ne da yayi musu ya zamana cewa kullum a cikin sa masa albarka suke.Ana cikin wannan hali ne wata rana kwatsam cikin tsakiyar dare Samazan da iyayensa na cikin dakuna suna bacci sai sukaji mutanen unguwar sun rude da ihu.A firgice suka farka daga bacci suka rugo waje suna fitowa sukaga ashe rumbunansu ne suka kama da wuta tuni ma sun gama konewa kurmus babu kwayar abinci guda daya da za'a mora.Koda ganin wannan al'amari sai mahaifiyar Samazan ta fashe da kuka,shi kuwa mahaifin nasa durkushewa yayi a kasa ya durfafi kasa da kansa saboda tsananin takaici,jarumi Samazan kuwa jikinsa ne ya kama karkarwa zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone a lokacin da makwabtansu keyi musu jajen wannan masifa suna tattaunawa ana mamakin abinda ya haddasa wannan wuta saboda ba'a san yadda akayi ba ta tashi.Kawai sai Samazan ya juya da baya ya ruga da gudu izuwa cikin dakinsa yayi damarar yaki ya dauko makamansa ya sake fitowa da gudu ya ruga izuwa inda dokinsa yake ya kwanceshi ya hau yana shirin sakarwa dokin linzamin kenan sai yaga mahaifinsa tsaye a gabansa fuskarsa a murtuke ya dubeshi yace ina zaka je?Samazan yace yakai abbana ka yi sani cewa ba wani bane ya turo aka kona mana rumbunanmu ba face Hashmar ko kuma dansa Balwan.Na rantse da darajarka yanzu zanje na yakesu har cikin gidan nasu na kashe su gaba daya daga matansa har yayansa koda kuwa bazan dawo a raye ba.Koda jin wannan batu sai Imsar ya matso gaban Samazan ya zabga masa mari mai karfi.Samazan ya tsaya yana kallon mahaifinsa cikin mamaki domin ko tsawa mahaifin nasa bai taba yi masa ba tun da aka haifeshiSamazan ya tsaya yana kallon mahaifinsa cikin mamaki.Take alamar mamaki ya baiyana karara a kan fuskar Imsar bisa marin da yayiwa Samazan ya zamana cewa shi kansa yayi mamakin yadda akayi ya mareshi.Take idanunsa suka ciko da kwallah ya dubeshi yace yana da kyau ka iya sarrafa zuciyarka a duk lokacin data fusata domin tsalle daya ke jefa mutum cikin rijiya.Kaman tane cewa duk abinda kake takama dashi walau karfi ko tsafi duk Hashmar da dansa Balwan suna dashi,bazaka iya kawar dasu ba kuma baka da cikakkiyar hujja akan cewa sune suka zo suka kona mana rumbunanmu,baya ga wannan sarkin yawa yafi sarkin karfi zasu iya sawa dakarun sarki su kamaka akan ka kai musu hari kuma kasan cewa sarki nasu ne zai iya yanke maka hukuncin daurin rai da rai a kurkuku,idan kuma hakan ta sameka bakin ciki ne zai zamo sanadin ajalina. Uhm Littafi yafa zo karshe.kamar yadda nace 1-5 ne ya fito. °KIBIYA° °RATSA° °MAZA°!!! Littafi Na Biyar (5) Part B ZAI ZAMO SANADIN AJALINA.KODA YAZO NAN A ZANCENSA SAI HAWAYE YA ZUBOWA SAMAZAN YACE YAKAI ABBANA YANZU KANA NUFIN SHIKE NAN SAIDAI NA CIGABA da zuba ido,ina ganin makiyanmu na dakusar damu,tunda har takai azo a kone abincinmu to tabbas wata rana kuma mu za'a kone.Dajin wannan batu sai Imsar ya gyada kai yace baza'ayi haka ba,abinda nake so dakai shine kayi shiri a yau dinnan ka nausa cikin duniya domin cika burinka.Koda jin wannan batu sai Samazan ya kamu da tsananin mamaki yace yakai Abbana ina dalilin da yasa ka sauya shawara,shin tafiyartawa ba zata haddasa maka wani ciwon ba? Sa'adda Imsar yaji wannan batu sai yayi ajiyar numfashi sannan ya dago kai ya dubi Samazan yace ai tuni makiya sun dade da samini wannan ciwo kuma babu mai cire mini shi,ka sani cewa da ciwon nan har abada gwara wanda za'a rabu dashi watarana.Abinda nake nufi shine idan har na hanaka tafiya neman daukar fansa to dani da kai da mahaifiyar taka duk a cikin bakin ciki zamu mutu amma idan ka tafi muna sa ran cewa watarana zaka cika mana burinmu.Koda ba zaka dawo ka same mu ba raye.Nasa maka albarka da cewa komai wuya komai tsanani zaka sami nasara ko dakuwa zaka kusan rasa rayuwarka.Koda Nazirat mahaifiyar Samazan taji cewa Samazan zaiyi wannan tafiya sai ta rugo da gudu ta fada kan kirjinsa ta rungume shi tana mai fashewa da kuka.Al'amarin daya karya zuciyarsa kenan shima ya kama kuka yace yake ummina bai kamata ki rinka zubar da hawayenki ba saboda tunda kika haifebi daga kuruciyata kawo izuwa girmana bamu taba rabuwa ba sai yanzu.Wannan tafiya da zanyi tana dauke da manyan burika namu,yana daga cikin burin na dawo da sarautar sarkin mafarauta a garin nan tunda yanzu ma gashi an hana yin farautar gaba daya kuma an hana hako ma'adanan kasa.Koda jin wannan batu sai Nazirat ta janye jikinta daga cikin na Samazan da sauri ta dubeshi cikin firgici tace ta yaya zaka dawo da farauta gami da hako ma'adanan kasa agarin nan alhalin masarauta ce ta hana?Sa'adda Samazan yaji wannan tambaya saiya goge hawayen dake cikin idanunsa yace yake ummina idan har na cika burina na samo arzikin dazan fita nema nayi miki alkawarin cewa saina dawo mana da sarautarmu ta gidan nan koda kuwa saita kaini da sauya sarki tunda sarki na yanzu azzalumi ne,lallai saina sake shi daga kan karagarsa na dora kaninsa Ikmal tunda kowa yasan cewa shi adali ne.A gaban dimbin jama'ar dake tare a kofar gidan nasu Samazan yayi wannan furuci a lokacin da ake ta kokarin kashe kudurinsa,jama'a suka tarwatse don gudu kada Samazan ya shafa musu kashin kaji,Ita kuwa Nazirat saita firgita ainun ta dubi Imsar tace yaya kana jinsa yanayin irin wannan ganganci amma ba zaka hana shi ba,Imsar yace ai an wuce lokacin da zan hanashi aiwatar da duk abinda yayi akan makiyanmu tunda sun kaimu makura,ki gane cewa wanda duk baya sonka to baya son ka rayu.Samazan jeka ka gama hado kayanka yanzun nan nake son muyi bakwana ka tafi izuwa cika burinka mahaifinsa yace.Koda jin haka sai Samazan ya sauko daga kan dokinsa da sauri cikin farin ciki ya ruga izuwa cikin gidan ya dauko jakarsa ta guzuri ya budeta ya zuba yan kayayyakin da yake bukata sannan ya sake rugowa waje.Ba tare da bata lokaci ba yayi sallama da iyayensa suna masu sa masa albarka suna kuka shima yanayi,da kyar Samazan ya janye jikinsa daga cikin nasu ya sake kama dokinsa ya hau ya zabureshi da gudu.Su kuwa suka bishi da kallo kawai,a lokacin da Nazirat ta dora kanta a kan kirjin Imsar duk su biyun suna zubar da hawaye.Idanunsu,zukatansu cike da dimbin bakin ciki da alhinin rabuwa da dansu wanda basu da tabbacin sake ganinsa a rayuwa kafin su bar duniya. *Al'amarin Jarumi Samazan kuwa maimakon ya fice daga cikin birnin nasu na Hindu sai ya wuce kai tsaye izuwa gidan Attajari Hashmar.Gidan Attajiri Hashmar ya kasance katon gida kuma kawataccen gaske domin a gaba daya birnin Na Hindu a wannan lokaci banda gidan sarkinsu wanda ake kira Nagur Bin Hunzal babu wani gida kamarsa.Sama da dakaru dubu biyu neke gidan kuma kafin mutum ya isa falon Hashmar na gidan inda ake saukar baki saiya ratsa ta cikin kofofi tara.Tafiyar dakika dari shida.Ba tare da shakkar komai ba Jarumi Samazan ya durfafo wannan gida na attajiri Hashmar.Tun daga nesa da dakarun tsaro suka hango shi sai suka zare makamai suka taso masa,masu takubba da masu masu suka sha gabansa domin a zatonsu yazo ne da nufin yaki,ko gezau Samazan baiyi ba,yana isowa daf da kofar godan sai yaja linzamin dokinsa ya tsaya caki.Sannan ya dubi dakarun tsaron yace banzo nan ba domin na zubar da jinin dayanku,nazo ne domin nayi magana kawai da mai gidanku kuje ku shaida masa cewa gani nan ina jiransa.Koda jin wannan batu sai shugaban dakarun ya mayar da takobinsa cikin kufe sannan ya dubi Samazan cikin alamun girmamawa yace yakai babban jarumi ina mai shawartarka da kayi maganar da kazo da ita a cikin cikinka don nasan cewa shugabana Hashmar dashi da dansa Balwan ba zasu saurareka ba tunda ka sami irin muguwar kiyayyar dake tsakaninku.Ni kaina nayi mamakin abinda yasa ka kawo kanka nan.Kafin Shugaban Dakarun ya gama rufe bakinsa tuni Samazan ya tari numfashinsa yana mai daka masa tsawa yace kaje ka isar da sakona ko kuma na tarwatsaku da karfin tsiya na shigar da kaina har cikin fadar shugaban naku.Koda jin wannan batu sai shugaban dakarun ya juya da sauri ya ruga izuwa can cikin gidan.Jim kadan saiga shugaban dakarun tare da Hashmar da Balwan a cikin shirin yaki a fusace sun fito da sauri.Koda sukaga Samazan a tsaye bisa dokinsa fuskarsa cike da murmushi babu ™Abubakar Haleefah Physicist™ wata alamar damuwa sai murmushi akan fuskar sai suka cika da matukar mamaki.Koda Samazan yaga Hashmar da Balwan tsaye a gabansa sai ya dubesu a nutse yace yaku manyan abokan gaba,kuyi sani cewa nazo ne nan domin naja kunnenku bisa abu daya,yanzun nan zanbar garin nan domin yin wata muhimmiyar tafiya.Bansan ranar da zan dawo ba amma kada ku kuskura ku taba iyayena domin duk ranar dana dawo na iske wani abu ya samesu na rantse da darajarsu mutum daya a cikin zuri'arku kaf ba zai tsita da rayuwarsa ba,rumbunanmu na abinci da kuka tura aka kone ya isheku.Kada a sakeyi mana wani abun.Da wannan furuci nakeyi muku sallama sai sun sake saduwa.Koda gama fadin hakan sai Balwan ya fusata ainun ya yunkura zai zare takobinsa amma sai Hashmar yayi sauri ya rukeshi yana mai kyalkyala dariyar mugunta sannan ya dubi Samazan yace yakai yaro idan takamarka sa'a to nima ban taba sa wani abu a gabana ba ya gagareni.Kaje ka shiga duniyar ka yawata duk inda ka so,duk abinda zaka samo kaje ja samo shi muna nan madakata muna jiranka.Tsakaninmu dakai zamuga wanda zaiga bayan wani.Nayi ma alkawari daga yau bama mu ba wani ma bai isa ya iya cutar da iyayenka ba muddin ina numfashi a cikin garin nan.Domin bani da burin da yafi iyayenka suga irin mummunan karshen da zakayi.Fatana shine bakin ciki da takaicin lalacewar rayuwarka ya zamo sanandin ajalinka.Sa'adda Samazan yaji wannan batu sai shima ya kyalkyale da dariyar mugunta sannan yacr lokaci ne kadai zai warware wannan gardama dake tsakaninmu,yana gama fadin hakan saiya kada linzamin dokin ya juya da baya ya zabureshi da gudu.Cikin kankanin lokaci ya bacewa su Hashmar da gani sai kurarsa.A sannan ne Balwan ya ciza yatsa kuma ya dubi Hashmar cikin alamun tsananin takaici yace haba ya Abba me yasa ka hanani na yaki wannan babban makiya namu yanzu na kashe shi domin mu cusawa ubansa bakin cikin dazai kaishi kushewarsa?Koda jin wannan tambaya sai Hashmar yayi murmushin mugunta irin na manyan azzalumai marasa imani sannan ya dafa kafadar Balwan yace kai yaro ne 'dana,ai shi kisan mummuke yafi kisan farat daya takaici,yana da kyau ka ganawa makiyinka azaba mai radadi kuma ka cusa masa takaici da bakin ciki mai radadin gaske kafin ya gama dashi.Ta haka ne kadai zaka zamo gagarabadau kuma babban dodo ga dukkan makiyanka,muje zuwa mahaukaci ya hau kura zamuga wanda zai gaji.Wannan shine asalin tarihin rayuwar Jarumi Samazan da kuma dalilin da yasa ya baro kasarsu ta Hindu ya shiga duniya.Bayan Samazan ya kammala aikinsa na hada kwale kwale kuma yaci abinci ya koshi a lokacin da dare ya soma saiya shigo cikin tantinsa ya kwanta kamar yana bacci abinsa a cikin gidansu na birnin Hindu.Bai farka ba saida gari ya waye hasken rana ya doki fuskarsa.Cikin hanzari Samazan ya mike tsaye yaje yayi wanka a bakin gabar wannan rafi sannan yayi kalaci ya shiga kimtsawa yana diban kayansa yana zubawa a cikin wannan kwale kwale.Koda ya gama shirinsa tsam saiya janyo kwale kwale izuwa cikin rafin ya shiga ciki ya zauna ya kama tukashi ya nufi cikin rafin kai tsaye,Ba tare da shakkar komai ba.Abinda ya daurewa Samazan kai shine tunda ya fara wannan tafiya a cikin wannan rafi sai yaji gurnanin dabbar dake karkashinsa ta dauke dif tamkar bai taba jinsa ba.Koda jin haka sai shima ya basar ya cigaba da tuka kwale kwalensa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ba tare da fargabar komai ba.Saida Samazan yayi tafiya mai tsawo a cikin rafin ya iso daidai tsakiyar kwatsam sai wannan kada ya faso tsakiyar kwale kwalen da kansa.Take kwale kwale ya dare biyu Samazan yayi sama a dimauce ya fado ruwan tsundum ya lume kasa.Take yayi arba da narkaken kadan a karkashin ruwa.Sa'adda ya waigo gareshi kuma ya durfofoshi.Koda Samazan yayi arba da wannan kada sai ya firgita ainun saboda bai taba ganin kada irinsa ba mai tsananin girma da ban tsoro.A karon farko Sai Samazan ta juya da sauri cikin iyo tamkar kifi da nufin ya gudu ai kuwa sai kadan ya kara karfin gudun nasa a karkashin ruwan domin ya cim masa.Koda Samazan ya waigo bayansa yaga saura kiris kadan ya cimmasa kuma ya ganewa bai isa yakai bakin gabar kogon ba batare da kadan ya cimmasa ba.Gashi a wannan lokaci ransa ya baci matuka bisa ganin yadda wannan kada ya tarwatsa masa kwale kwalensa bayan yasha wahalar sassakashi.Nan take Samazan yaji zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone don haka sai yayi kundunbala ya juya ya tari kadan.Aikuwa sai kadan ya wangame bakinsa da nufin ya hadiyeshi.Wohoho!Karfi da zafin nama suna da rana domin ba don Samazan yana da tsananin zafin nama ba da bai isa ya iya kaucewa hadiyar da kadan ya kawo masa ba.Kawai sai ya kaucewa kadan ya hadiyi iska,Kadan ya wurkila jikinsa ya juyo da baya gareshi,tuni Samazan ya dunkule hannunsa na dama ya gabzawa kadan wannan naushi akan idon na hugu da kukan karfinsa.Nan take idon Kadan ya gwallatse ya tsiyaye.Kadan yayi wani irin mugun ruri sakamakon tsananin zafi da zogin da yaji,ai kuwa saiya makawa Samazan jelarsa a gadon bayansa.Take gadon bayan nasa ya dare jini yayi tsartuwa shima ya kurma uban ihu a lokacin da kadan ya sake daga katuwar jelar tasa domin ya maka masa,cikin bakin zafin nama Samazan ya zare takobinsa ya kare bugun da kadan ya kawo masa.Koda jelar kadan ta hadu da takobinsa sai tarwatsin wuta ya tashi,karfin bugun jelar akan takobin da nauyinsa ya rinjayi Samazan ya juya sau uku kamar katantanwa.Adaidai wannan lokaci ne Samazan yaji numfashinsa na neman karewa tunda a karkashin ruwa suke don haka babu shiri ya dago sama daga cikin ruwa.Ai kumwa sai shima kadan ya dago sama ya sake wangame bakinsa. ™Abubakar Haleefah Physicist™ Ya kawo masa hadiya,Samazan ya goce ya daka tsalle ya fada kan gadon bayan kadan ya datse bakin nasa da hannayensa biyu.Ai kuwa sai kadan ya kama wurkila jikinsa yana katantanwa da Samazan a cikin ruwa.Wani lokacin ma sai yayi nutso dashi kasa kuma ya taso sama.Nan Samazan yaji ya fara fita daga haiyacinsa sakamakon ruwan dake shiga bakinsa da hancinsa.Duk wannan bakin gumurzu da sukeyi Samazan bai yarda ya yarda takobin hannunsa ba.Domin duk sa'adda kadan ya wurkila jelarsa ya kawo masa duka da ita da takobin yake karewa.Ba don haka ba da tuni kadan ya ragargaza jikin nasa.Koda Samazan ya fuskanci kanshi a mutuwa da rayuwa a wannan gumurzu da sukeyi sai yayi sauri ya murza wani gurin tsafi dake jikin hannunsa na hagu take ya rikide ya zama kifi suka kasa tsere da kadan a karkashin ruwan suka nufi karshen rafin inda gabar take.Nanfa kadan ya dage iya karfinsa domin ya cimmasa amma sai ya kasa duk da cewar tazarar dake tsakaninsu bata wuce kamu uku haka ba,suka iso har bakin gabar rafin sai kifin yayi tsalle ya fito daga cikin koramar aikuwa shima kadan saiya dako tsalle ya biyo shi a saman.Kifin na sama ya rikide ya zama Samazan ya juyo da sauri yasa kafarsa ya doki kan kadan,saboda karfin dukan saida kadan ya fado kasa tim a kusa da gabar rafin tamkar giwa ta fadi,karfin buguwarsa da kasa gami da nauyinsa ya haifar da girgizar kasa,amma sai ya shanye dukan tamkar susa akayi masa kuma ya fusata ainun ya jefo doguwar jelar tasa ta kanannade Samazan tun daga kafafunsa har izuwa kafadarsa ta matse shi.Saboda tsananin zafin da Samazan yaji kamar gaba dayan kasusuwan jikinsa zasu kakkarye bai san sa'adda ya kurma uban ihu ba,don haka sai shima ya takarkare iya karfinsa ya fara buda jelar kadan,a hakne kaifin jelar ya fara yankar jikinsa,jini na zuba amma duk da haka saiya nace kuma ya daure ya cigaba da buda jelar har ya samu ya zaro hannunsa guda daya daga jelar yayi wuf ya zaro wata wuka a kugunsa ya cakawa kadan akan daya lafiyayyen idon nasa.Take shima wannan idon ya gwallatse kadan ya kurma uban ruri wanda yafi na farko kuma ya warware jelarsa babu shiri daga jikin Samazan kuma ya fusata ainun ya rinka jefa jelar izuwa gabas da yamma,kudu da arewa,sama da kasa yana kaiwa Samazan mugun hare hare,bisa dole Samazan ya rinka guje guje da tsalle tsalee yana kaucewa harin nasa.Tabbas in badon kadan ya makance ba da abune mayuwaci a wannan karon ya tsira daga sharrinsa.Ahaka ne Samazan ya samu da dan nisanta daga kusa da kadan ya fadi kasa sakamakon jirin dake dibarsa da kuma jinin dake zuba daga raunikan dake jikinsa.Babu raunin da yafi addabarsa sama da wanda ke bisa gadon bayansa domin mugun radadi da zugi yake masa tamkar ana zuba masa barkono a cikinsa kuma bai daina zubar da jini ba.Duk sa'adda Samazan ya shago bayan nasa da hannunsa jini yake gani tamkar a sannan akayi masa wannan rauni.Nan take hankalin Samazan ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace,Ta yaya zan dinke wannan rauni dake bisa gadon bayana?Tabbas idan ban tsaida jinin ba nan da zuwa wani lokaci zan iya rasa rayuwata gaba daya.Adaidai wannan lokacin ne mugun kadan ya durfafo inda Samazan ke zaune kuma a lokacin ne Samazan ya fara ganin dishi dishi wato idanunsa suka fara lumshewa.Ashe kdan yana amfani ne da kamshin bil'adama amma bada idanunsa ba tunda ya makance,kamar Samazan yasan da hakan sai yayi sauri ya dauke numfashinsa domin a wannan lokaci baisan abinda zai yi ba ya kare kansa.Shidai yasan cewa sara da suka basa tasiri a ko ina a jikin kadan,to wai shin wace dabara zanyi amfani da ita na sami nasarar kashe wannan kada? Lokacin da kadan ya iso daf da Samazan saiya daga kansa sama ya shinshina gabas da yamma,kudu da arewa,da yaji babu sautin mutum saiya wuce gaba a lokacin da kafarsa ta hagu ta gaba ta take hannun Samazan na dama.Take yatsun hannun nasa guda uku suka karye Samazan yayi sauri ya toshe bakinsa da daya hannunsa domin ji yayi kamar zai rusa ihu sakamakon zafin da yaji.Koda kadan yayi dan nisa kadan ga barin inda Samazan ke zaune sai hankalin Samazan ya sake dugunzuma fiye da ko yaushe bisa ganin yadda kadan ya fusata ya wangame bakinsa yana furzar da wani irin ruwa mai yawan gaske.Koda ruwan ya zuba akan bishiyoyi sai suka kama narkewa.Take Samazan ya aiyana a ransa cewa wannan cefa damarsa ta karshe da zaiyi amfani da ita ya kashe wannan kada amma idan ya bari kadan yaje ya dawo tofa ajalinsa ne yazo.Inda matsalar take shine ta yaya zai iya kashe kadan? Waishin inane lagon kadan ne? KIBIYA RATSA MAZA!!! Littafi Na Biyar (5) Part C WAISHIN INANE LAGON KADAN NE? Koda Samazan yayi wannan tambaya a cikin zuciyarsa sai nan take wata dabara ta fado masa amma kuma bashi da yakinin cewa dabar zata fisheshi,saidai kuma bashi da wani zabi wanda yafi hakan.Gama aiyana hakan keda wuya saiya waiga bayansa yaga wata yar karamar bishiya mai siraran sassa,amma

Chapter 7 of 8