Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 8
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels KIBIYA RATSA MAZA Littafi na Daya(1) Part A Gudu takeyi iya karfinta domin ta ceci rayuwarta saboda bala'in daya biyo ta, babu abinda za'a kwatantashi dashi face ajali. Babu abinda zai baka mamaki face wannan budurwa dake wannan azababben gudu,kyakkyawa ce abar kwatance,kuma cikin shigar yaki take,ga takobi a hannunta tsirara ba'a ciki kufe ba. Saboda karfin gudun da takeyi tamkar tafin kafarta zai tabo keyarta,amma duk da haka waige waige takeyi a cikin alamun tsoro,duk da cewa kana mata kallo daya zaka gane cewa jarumace ta kwarai mai kirar sadaukai. Kai bama ita ba hatta aljanu da tsuntsaye dake cikin wannan daji da take gudu a cikinsa tsoron dajin sukeyi da abinda ya biyota saboda masifu da bala'in dake tare dasu ballantana kuma bako irinta wanda bai taba shigowa dajin ba. Ba wani abu bane yake bin wannan budurwar ba face wadansu irin dodanni masu kirar goggon biri.Kawunansu da fuskokinsu irin na biri ne amma kuma kirazansu cike yake da gashi tamkar zaki.Suna da tarin kwanji a hannayensu tamkar na bil'adama,amma banda a kirazansu babu inda mutum zai ga gashi koda kuwa a kan kawunansu.Saboda tsananin karfin gudun wadannan dodanni har tashi sama suke tamkar tsuntsaye saidai kaga suna tsallake mutum, amma dukda haka sun kasa cimma wannann kyakkyawar jaruma saboda karfin gudun nata ya ninka nasu domin duk sa'adda dodannin suka yi taku biyar bisa turba to a madadin nata taku guda yake.Ko makaho ne yaji sautin gudun wannan jaruma yasancewa gudun nata ya wuce na hankali da tunanin kwakwalwar bil'adama saidai a kirashi da gudun sihiri. Kokarin wannan jaruma shine takaiga wani katon tsauni wanda ake kira da suna Lauhul- Farras. Su kuwa wadannan dodannin suke gadin tsaunin sama da shekara dari uku da arba'in da uku. A tarihin wannan tsauni babu wani bil'adama daya taba samun damar hawansa.Hatta Aljanu da suka sami hawansa ma ba'a taba samun dayansu ya sauko a raye ba,saidai aga an jeho gawarsa daga kan tsaunin. Shidai tsaunin Lauhul-Farras duk wata cuta ta duniya akwai maganinta a kansa. Duk abinda mutum yake so ya samu a duniya indai ya hau kan wannan tsaunin sai ya sameshi, to amma fa ba hawansa ba saukar.Shi kansa hawan ba karamin masifa bace dole sai mutum yana da gagarumar jarumtaka ta kwatance gami da tsananin karfin sihirin tsafi. Mafi akasarin jaruman da sukayi kundumbala suka siyar da rayuwarsu suka durfafo wannan tsauni da nufin su haushi sun kasance 'ya'yan manyan bokayen duniya wanda suka yarda da kansu.Lokacin da ya rage saura baifi taku ashirin ba tsakanin jarumar da bakin tsaunin Lauhul-Farras,sannan kuma tazarar dake tsakaninta da wadannan dodanni baifi taku ashirin ba,sai ta tsaya cak ta waigo ta fuskanci dodannin tana mai bude hannayenta alamar cewa a shirye take ayi duk abinda za'ayi. Ai kuwa suma dodannin suka tsaya cak akayi cirko crko aka fara kallon kallo tsakaninsu da jarumar.. Ba komai bane yasa dodannin suka tsaya suna kallonta ba face itace bil'adama ta farko data taba samun damar shigowa har cikin wannan daji tazo tafkin wannan tsauni don haka basu san iyakar shirinta da karfinta ba. Baya ga haka kuma komai yawan dakarun aljanu gami da karfin gudunsu walau a a sama ko a kasa basa iya tserawa wadannan dodanni face sun karkashesu sun karar dasu,amma yau gashi mutum daya jal kuma ma wai 'ya mace ta gagare su kamawa bare su kasheta har saida ma ta tsaya da kanta. Ita kuwa wannan jaruma a tsorace take da wadannan dodanni saboda itama duk irin tsananin jarumtakarta da karfin sihirinta bata taba haduwa da masifaffun halittu ba irin wadannan masu karfin gudu,bakin naci,kwarjini da ban tsoro. Kuma ba karamar kundumbala tayi ba data tsaya ta fuskanci wadannan dodanni ba,sai saboda tasan cewa idan ta basu baya a lokacin da zata fara kokarin hawa kan wannan tsauni to tabbas komai zai iya faruwa gareta. Kodai suyi mata mugun raunin dazai iya zama sanadin ajalinta ko kuma su kasheta farat daya. Abinda ya kara firgitata dangane da dodannin shine a lokacin data shigo farkon dajin ta kasa tseren gudu dasu. Duk sa'adda ta waiga bayanta taga yadda suke bangaje duk abinda ke gabansu suna tarwatsa shine ya rugurguje,walau bishiya ko dutse,shi yasa ta razana ainun don tasan cewa ta gamu da gamonta duk kuwa da cewa itama tun tana da shekara goma sha daya a duniya mahaifinta boka Saiham ya fara bata horon yaki,horon gudu a cikin duwatsu,kwazazzabai,­ rairayi har da cikin rabo. Tasha bakar wahala wajen koyan wadannan abubuwa ramkar ranta zai fita har mahaifiyarta ta rinka ganin kamar cewa boka Saiham bai damu da rayuwar 'yarsa ba duk da cewa kuwa ita kenan kadai gareshi. Saida takai cewa kafin Jaruma Safirat ta saba da wannan horo kullum sai tayi matsannanciyar rashin lafiya ta zazzabi da kumallo bayan sun dawo daga daji ta karbo horon. Sannan a hankali bayan kwanaki arba'ain da daya jikinta ya saba da wannan tsananin wahala,yake iya jureta ya zamana cewa ko ciwon kai baya sata. A ranar da boka Saiham ya kammala baiwa Jaruma Safirat wannan horo ne kuma ya danka mata gaba daya sihirinsa na tsafi.Ya dubeta a lokacin da idanunsa suka ciko da kwallahh har hawaye ya subuto masa yace,yake 'yata yau kwana arba'in da daya kenan ina baki wannan horo mai tsananin wahala tamkar zaki rasa rayuwarki. To ki sani cewa ba komai bane ya sani nake baki wannan horo ba face saboda tsananin SO DA KAUNA, kuma saboda ina son nan gaba ki zama sarauniyar duniya.Wani babban matsayi nake son ki samu wanda ni bani da ikon samunsa domin damar ta wuce. Koda Boka Saiham yazo nan a jawabinsa sai Jaruma Safirat ta kamu da tsananin mamaki ta dubeshi cikin alamun rashin fahimta tace,haba yakai Abbana saboda me zaka dami kanka kan cewa sai na zamo sarauniyar duniya? Ka tuna fa cewa ko mutuwa kayi yanzu ni da mahaifiyata kabar mana dukiya mai tsananin yawan gaske da har mu mutu bamu isa mu iya karar da ita ba koda kullum zamu rinka dibarta muna rabar da ita ga mabukata. Ka bani jarumtakar da komai dandazon mayaka zan iya kutsawa ta cikinsu na tsira da rayuwata.Sannan komai isar matsafi bazai iya cutata da karfin sihirinsa ba.Koda jin wannan batu sai Boka Saiham yasa hannu ya share hawayensa sannan ya rike 'yarsa Jaruma Safirat ya rungumeta a kirjinsa yace,haba yake 'yata shin kina son na bata shekaru talatin danayi a cikin kogon tsafina a banza kenan? Koda jin haka sai Jaruma Safirat ta janye jikinta daga cikin na boka saiham da sauri ta dubeshi cikin kaduwa tace,yanzu dama duk shekarun daka bata cikin kogon tsafinka tun kafin a haife ni wani babban al'amari ka kirkiro? Boka Saiham yace kwarai kuwa.Yake 'yata kiyi sani cewa ba komai bana sana'anta ba face KWARI DA BAKA wacce duk jarumi ko sarko ko kuma matsafin daya mallaketa zai iya mallakar wannan duniya gaba dayanta. Amma inda matsalar take na gano cewa ni bazan iya sarrafa wannan Kwari da baka ba saboda shekaruna sun haura ashirin da biyar.Kuma bisa binciken danayi babu wani bil'adama da zai iya sarrafata ko kuma aljani face wanda shekarunsa suka haura ashirin da biyar ko kuma suka gaza goma sha takwas bai isa ya iya sarrafa kwari da bakan ba.Babban sihirin wannan KWARI DA BAKA shine idan har tana hannun mutum tofa koda gaba dayan mayakan duniyar nan zasu taru a kansa ba zasu iya kaishi kasa ba ko su cishi da yaki.Kuma KAIFI KO TSINI ba zai iya tasiri a kansa ba.Idan kuma har ya harba kibiya daya daga cikin kibiyoyin dubu nata,kibiyar zataje ta kashe mutum biyar a cikin dakika biyar kuma ta dawo ta koma cikin kuttunta. Kinga kenan a cikin kankanin lokaci mai wannan kwari da baka zai iya karar da milyoyin abokan gaba.Saboda ganin cewa bazan iya sarrafa wannan kwari da baka bane wacce na sana'antata da hannuna,bayan na gama tane na fashe da kuka na bakin ciki amma dana tuna cewa zaki iya mallakarta sai na kwalkyale da dariyar farin ciki.Abinda ya sanya kuwa kika ga na baki wannan horon yakin kuwa mai tsananin wuya shine a lokacin da kika cika shekara sha takwas na san matsafa,jaruma da manyan sarakunan duniya zasu kwallafa ransu akan wannan kwari da baka.Idan baki da wannan horon dana baki zasu iya rabaki da ita bayan kin sha wahala wajen daukota a inda zan boyeta.Koda jin wannan batu sai mamaki ya sake turnuke Jaruma Safirat a karo na biyu tace, Haba Abbana saboda me zaka wahalar dani ka biye wannan KWARI DA BAKA a inda nima sai nasha bakar wahalar daukota? Koda jin wannan tambaya sai Boka Saiham ya numfasa cikin alamun takaici a lokacin da idanunsa suka sake cikowa da kwallah yace,yake 'yata kiyi sani cewa bana son ki sha wahala daidai da dakika biyar,amma idan na bar wannan kwari da baka a gida ko a kogon tsafina a yanzu wasu takadaran matsafa ko bokaye,jarumai ko sarakai zasu iya zuwa su saceta a lokacin da bana raye kafin ki kai munzalin da zaki iya mallakarta a hannunki ki iya sarrafara. Bisa wannan dalili ne na yanke shawarar na raba kwari da bakan na kaisu wurare daban daban inda babu wani mahaluki daya isa yaje ya dauko su face ke. Da farko zan dauki Bakan na kai shi can dajin Sharjul inda tsaunin Lauhul Farras yake na dorata a kansa. Ki sani cewa babu wani bil'adama ko aljani daya taba hawa kan wannan tsauni ya sauko a raye.Kuma duk abinda mutum yake nema a cikin duniya indai ya hau kan tsaunin Lauhul Farras tabbas saiya sameshi,amma fa va zai sauko a raye ba.A matsayina na sarkin Bokayen duniya a yanzu na gano cewa da horon dana baki yanzu gami da sihirin tsafina dana mallaka miki da kuma sa'arki zaki iya hawa kan tsaunin Lauhul Farras ki sauko lafiya.Shi kuwa kuttun kwarin zan dauke shine nakai shi dajin Sarkif na adana shi a kogon mutuwa,kogon da ake adana dukkan kayan yakin duniya tun daga farko har izuwa na karshe. A tarihin wannan kogo na mutuwa duk abinda ya shiga cikinsa tofa bazai sake fitowa ba saboda tsananin tsaron dake cikinsa, amma na gano cewa ke zaki iya shiga cikinsa ki dauko duk abinda kike bukata. Bazan iya sanar dake komai ba akan wadannan wurare biyu ba,da kuma irin bala'in dake cikin dazuzzukansu ba. Amma bayan na mutu zaki karance komai a cikin litattafan tarihin rayuwata da zan bar miki wanda shine zai jagorance ki a cikin duk abinda zaki yi na rayuwarki. Duk abinda ya shige maki duhu zakiga mafitarsa a cikin wannan kundi dazan bar miki gado. Kada kiyi wasa da wannan kundi kuma kada ki kuskura ki bari yaje hannun wani mahaluki walau mutum ko aljan,domin tamkar kin bayar da dukkan sirrikan sihirin tsafinki ne. Sannan ki kasance tare da wannan littafi a tare dake ko yaushe. Dare da rana ki kasance mai juriya bisa duk irin yanayin da kika tsinci kanki domin ba'a zama wane a banza ba. Nima nan da kika ga na sami wannan matsayi na sarkin bokayen duniya ban same shi a banza ba saida na sha gwagwarmaya da manyan mazaje kuma na tara makiya marasa adadi. Tsananin sa'a da rabo ne suka sa na tsira da rayuwata na kawo a yanzu. Tunanin wannan abu daya faru ne yasa jaruma Safirat take samun kwarin gwiwa ta jure duk irin wahalar data tsinci kanta a ciki.Kafin Jaruma Safirat ta iso bakin tsaunin saida tasha gwagwarmaya da mugayen bakaken aljanu,muggan dabbobin daji da mugayen kwari.Tasha bakar wahala da taji kamar ta fasa zuwa tsaunin Lauhul Farras ta koma da baya,amma data tuno da wasiyar da mahaifinta ya bar mata cewar ba'a zama wane a banza kuma ta tuna cewa idan fa bataje ta dauko wannan kwari da baka ba ba babu wanda zai iya daukota kuma duk kokarin da mahaifinta yayi ya zama na banza kenan. Sa'a daya kawai jaruma Safirat bata sani rauni ko daya ba a jikinta amma ta jigata ainun. Bayan anyi kallo kallon kallo tsakanin jaruma Safirat da wadannan mugayen dodanni sai ta sake zaro wata gajeriyar adda a kuibin cinyarta ta hagu ya zamana cewa makami biyu ne a hannunta,sannan ta gyara tsayuwarta.Koda ganin haka sai dodannin suka kama yin wani irin mugun gurnani mai ban tsoro da firgitarwa suka rinka dukan kirazansu alamar cewa suma sun yarda da kansu kuma a shirye suke a fafata ba gudu ba tsira. A wannan lokaci ne jaruma Safirat ta lura da faratan hannayen dodannin taga ashe zara zara ne masu kaifin tsiya gami da tsini yadda duk abinda suka karta ko suka tsira take zai dare ko yayi huda mai zurfu. Duk jarumtaka irin ta Jaruma Safirat gami da dakewar zuciyarta da kuma rashin tsoro amma saida taji gabanta ya fadi sosai domin taji a jikinta cewa karo da wadannan halitta ba wasa bane. Amma data tuna cewa bata da wani zabi wanda yafi ta tunkare su sai kawai ta daka tsalle sama izuwa tsakiyarsu tana mai kurma uban ihu mai tsananin firgitarwa ta dira tsakiyarsu ta hau su da sara da suka. Suma suka wanzu suna masu maida martani da gabas da yamma,kudu da arewa. Cikin kankanin lokaci sai gashi tarwatsin wuta na tashi sakamakon haduwar makamanta da sassan jikinsu. Ya zamana cewa KAIFI DA TSINI baya tasiri a jikinsu. Koda Jaruma Safirat taga haka sai ta hada da kai naushi da bugu.Ta rinka karkadesu tana zubar dasu kasa tana tarwatsa su. Amma kuma sai taga duk irin dukan da takeyi musu suna iya shanyeshi su mike tsaye zumbur su cigaba da yakarta ba tare da sunji jiki ba. Haka suma wadannan dodanni sunyi mutukar mamaki irin jarumtakar Safirat gami da tsananin zafin namanta gami da juriyarta. Domin itace jaruma ta farko wacce ta iya shefe sama da dakika goma tana yakarsu a tsawon shekarun da sukayi suna tsaron wannan tsibirin.Saida aka shafe rabin sa'a cif ana yin wannan bkin gumurzu tsakanin wadannan dodanni da jaruma Safirat. Ita bata samu nasara ba akansu,suma basu samu ba. Koda ganin haka sai hankalin jaruma Safira ya DUGUNZUMA ainun saboda dalilai guda uku. Dalili na farko shine tasan cewa ita batada maganin kaifi da tsini irin na wadannan mugayen dodanni,domin ga dukkan alamu sun fita karfin sihiri. Dalili na biyu shine ita bil'adama ce mai kashi da jini da tsoka mai saurin gajiyawa,don haka idan aka ci gaba da wannan fafatawa izuwa wani lokaci zata iya sarewa,a sami galaba a kanta. Dalili na uku kuwa shine dole ne tayi iya kokarinta ta gano inda laggon wadannan dodanni yake kafin ta gaji. To amma ta yaya zata iya gano hakan,alhalin babu inda bata soka ba ko ta sara ba a jikinsu,amma shiru babu wata nasara. Ai kuwa nan cikin hakane wani dodo mafi naci da jarumtaka daga cikinsu ya shammaci Safira yayi mata wani wawan dundu a gadon bayanta.Take taji kamar bayan nata ya burma kasusuwan wajen sun kakkarye. Ta kife kasa da rub da ciki tama mai yin aman gudan jini.Koda ganin haka sai gana dayan dodannin sukayi caa izuwa kanta gaba dayansu da nufi su ciscisgeta filla filla kowa yaja rabonsa. Ba zato ba tsammani sai suka ga Jaruma Safirat ta wurkila kafafunta tayi wata irin katantannuwa a tsakiyar tasu ta mammake kawunansu ta tarwatsa su da karfin tsiya. A haka ta cigaba da yakarsu cikin mutukar karfin hali tama cigaba da kare hare harensu ta hana dayansu samun nasarar sake taba jikinta da faratan hannayensu. Amma kuma sai suka rinka yin tamola da ita a tsakiyarsu.Nan da nan Jaruma Safirat ta fara fita daga haiyacinta,ya zamana cewa jini na yoyo ta cikin hancinta da bakinta. Take Jaruma Safirat ta aiyana a cikin ranta cewa tata ta kare,domin nanda cikar yan dakiku kadan gaba dayan karfin jikinta zai kare a cita da yaki. Domin a wannan lokaci jiri ya fara dibarta ta fara ganin dishi dishi.Ana cikin hakane taga wannan dodo mafi naci da karfi ya dako tsalle a sama tamkar an harbo shi daga cikin baka,ya bude hannayensa biyu da nufin ya soke wuyanta da tsinin dukkan faratan 'yan yatsun hannayensa guda goma. Koda Jaruma Safirat taga zata hallaka muraran bata san sa'adda ta yunkura ba cikin bakin zafin nama ta sunkuya kasa hannayen dodon suka caki iska.Kafin dodon yayi kasa ya sake kawo mata wani harin tuni ta doki kasa da kafafunta tayi sama tamakra itama daga cikin baka aka harbota.Nan take ta soke idanun dodon biyi da takobinta da kuma addarta.Nan take ruwan idanun ya fashe,jini ya kama tsiri daga cikinsu. Alokacin da dodon ya kama ruri da kuruwa sannan ya kama birgima a kasa yana kakarin mutuwa.Kafin cikar dakika biyar komai na jikinsa ya sandare ya zama gawa.Koda ganin haka sai farin ciki ya lullube Jaruma Safirat saboda ta gano inda ruhin dodonnin yake. Ai kuwa sai ta cigaba da soke musu idanu cikin tsananin jarumtaka da zafin nama na ban al'ajabi ya zamana cewa karfinta ya dawo tamkar ma a sannan ta fara gumurzun.Da bala'i yakai bala'i sai gashi dodannin sun fara ja da baya saboda ganin yadda take ragargazarsu suna zubewa kasa matattu tamkar ana sassabe a gona.Sai gashi duk tsananin yawan nasu ya zama na banza saboda ta zame musu alakakai sun rasa yadda zasuyi da ita. Ita kanta Jaruma Safirat tayi mamakin yadda ta cigaba da wannan yaki cikin kuzari da dacin rai. To amma ba komai bane ya bata wannan kwarin gwiwar ba face gano lagon dodannin. Wohoho! idan kaji ana ga ki gudu to lallai sa gudu ne bai zo ba!! Saida aka shafe sama da sa'a uku Jaruma Safirat nata karkashe wadannan dodanni amma da kyar suka samu suka yanketa sau biyu.Yanka na farko akan damtsen hannunta ne na hagu,wajen ya dare jini ya zuba.Yanka na biyu akan cinyarta ne ta dama. Duk da cewar a wani faffadan kwalkwalin karfe akan cinyar tata saida kaifin tsinin farcen ya darashi ya yanke ta.Ta kurma ihu saboda tsananin zafi da zogin da taji.Amma a hakan dai ta cigaba da yakarsu tana cigaba da karkashe su. Koda dodannin suka ga jaruma Safirat ta kashe kusan kaso daya cikin kaso ukunsu,ga gawarwakinsu nan birjik a wajen tamkar yabanya sai gaba dayansu suka ja da baya suka daina yakarta. Amma sai sukayi cirko cirko a gaban tsaunin suna numfarfashi da gurnani suna kallonta kawai.Koda ganin haka saita juya tana tangadi gami da jan kafa a lokacin da jini ke diga daga jikin raunikanta.Cikin karfin hali ta kama hawa kan tsaunin tana waigen dodannin saboda tasan cewa a koda yaushe wani daga cikinsu zai iya dako tsalle sama ya kawo mata harin bazata. A haka dai cikin matukar karfin hali ta cigaba da hawa kan tsaunin a hankali da kyar amma bata isa saman tsaunin ba sai bayan sa'a guda.Tana isa kan tsaunin sai ta baje a kasa tana kallon sararin samaniya tana numfarfashi tamkar ranta zai fita saboda tsananin gajiya da jigata. Saida ta dan jima a haka sannan ta mike zaune ta kalli saman dutsen ta hango inda aka ajiye bakan da tazo dauka.Koda tayi arba da bakan sai ta cika da tsananin mamaki domin bata taba ganin baka mai kyansa ba wanda aka kawatashi ainun. An dora bakan ne akan wani madauki na karfe mai siffar gwafa wanda aka soka shi cikin tsaunin.Kai da gani ka san cewa dama anyi wannan madauki ne musamman saboda wannan baka. Cikin tsananin farin ciki Jaruma Safirat ta mike tsaye.Mikewarta keda wuya sai ta hango wadansu miliyoyin makamai da kayan kawa iri iri da kuma garin magunguna dana ruwa a cikin kwalabe da mazubi iri iri.A jikin kowane magani an rubuta irin cutar da yake magani kuma gaba dayansu a bayan wannan baka suke. Nan take Jaruma Safirat ta tunkari inda wadannan abubuwa suke tana dingishi da jan kafa da nufin ta isa inda Bakan yake. Tsulum! ba zato ba tsammani sai ga wani narkeken mutum ya baiyana a gabanta rike da wani mashi na lu'u lu'u.Shidai wannan mutum tsagin rabin jikinsa na dabba ne,rabin kuma na bil'adama ne,tsawonsa ya ninka na Jaruma Safirat sau uku.Jelarsa doguwa ce kakkaura wacce yana iya jefata gabansa ko bayansa da tazarar taku arba'in ya cafko abinda ke wajen. Ya kasance kakkaura mai tarin kaurin kwanji tamkar dutse aka cusa a cikin tsokar wajen.Fuskarsa mummuna ce mai matukar kwarjini da ban tsoro cike da saje gami da dogon gemu kamu uku,idanunsa jajaye ne ba kyan gani.Koda Jaruma Safirat tayi arba da wannan mutum mai siffa ta dabba sai ta firgita ainun.Taja da baya a tsorace taji tamkar ta ruga da baya ta hakura da dauko wannan baka. Amma data tuno irin bakar wahalar data sha a baya akan tafarkin dauko wannan baka sai ta fasa gudu.Ta aiyana a ranta cewa dadai ta koma gida babu wannan kwari da baka kamar yadda tayiwa mahaifiyarta alkawari gwara ta rasa rayuwarta gaba daya. Nan take Jaruma Safirat ta gyara tsayuwarta duk da cewa har a sannan jini bai daina diga ba daga jikin rauninkanta ba,ta fuskanci basamudan katon jarimin mai ban tsoro. Kawai sai basamudan katon ya dubeta ya daka mata tsawa wacce ta razanata.Taji hantar cikinta ta kada kamar zata faso cikinta ta fado kasa,sannan ya dubeta yace,yake Safirat 'ya ga sarkin bokayen duniya.Kiyi sani cewa mahaifinki ya tafka babban kuskure daya kawo ajiyar bakansa nan kan tsaunin Lauhul Farras. KIBIYA RATSA MAZA Littafi na daya(1) Part B Kiyi sani cewa mahaifinki ya tafka babban kuskure daya kawo ajiyar Bakansa nan kan tsaunin Lauhul Farras domin duk abinda yazo nan baya daukuwa.Nan ne matattarar maganin dukkanin cututtukan duniya,kuma nan ne matattarar arzikin duniya.Babu mai samun su anan saidai a kasan tsaunin idan ya san sirrinsu.Ina mai shawartarki daki hakura da batun daukar wannan baka idan har kina son ki tsira da rayuwarki kuma na kya son a manta da tarihin matsayin gidanku.Koda narkeken katon nan mai siffa biyu yazo nan a jawabinsa sai Jaruma Safirat ta tari numfashinsa tana mai daka masa tsawa tace,ya kai wannan mummunan halitta kayi sani cewa kalamanka ko mummunar siffarka bazasu tsorata ni ba,ko luma su cire min kwarin guiwa akan tafarkin da mahaifina ya dorani na kokarin mallakar wannan duniya koda kuwa gaba dayan mutane da aljanun duniya zasu taru su yake ni.Babu abinda zai hanani daukar wannan baka wacce mahaifina ya sana'anta da hannunsa domin ni.Ina mai baka shawara akan ka kauce ka bani hanya in kuma ba haka ba kuwa kai ma zaka sayu ajalinka da kanka.Koda jin haka sai nan taje katon ya bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da kukan jaki saboda rashin dadin sautinta.Take idanunsa suka kada sukayi jawur kuma jikinsa ya kama tsuma ya dume da zafi har kakofin gashin jikinsa suka kama fitar da tururi saboda tafarfasar da zuciyarsa keyi.Koda ganin yadda yanayin narkeken katon ya sauya,nan take sai Jaruma Safirat ta razana ainun amma sai ta dake ta sake daga makamanta sama tana mai gyra tsayuwarta.Koda ganin haka sai mutumin ya wurga murtukekiyar jelarsa izuwa saman Safirat ta tsallaketa taje ta kanannado wata katuwar bishiya dake bayanta mai kauri da tsawon gaske,jelar ta tumbukota daga cikin karkashin kasa tayi sama da ita sannan ta dokata da kasa.Take bishiyar ta ragargaje tamkar a cikin turmi aka sanyata aka dake.Koda ganin wannan al'amari sai Jaruma Safirat ta firgita ainun,amma sai ta sake dakewa taki sakin makamanta kasa kuma taki gusawa daga inda take tsaye.Ita kanta tasan cewa shi wannan shugaban masu tsaron wannan tsibir yayi hakan ne domin ya firgitata ta hakura da batun daukar wannan baka domin ta tsira da rayuwarta.Amma shi kansa bisa tsananin mamakinsa sai yaga ko gezau batayi ba bare ta janye manufarta.Duk da haka sai ya sake dubanta yace,yake Safirat kiyi sani cewa ni sunana Bandaru bin Sandamu.Mahaifina mutum ne amma Uwata dodanniya ce,shi yasa kika ga an haife ni da siffa biyu.A matsayina na shugaban dakarun dake gadin wannan tsauni tsawon shekara dari uku da doriya ban taba ganin mahaluki mai taurin rai da karfin zuciya tamkarki daga cikin dukkanin aljanu da manyan jaruman bokaye da suka zo nan domin daukar wani abun.Kece jaruma ta farko wacce bata firgita ba kuma bata canja shawara ba bisa yin arba dani.To zan taimake ki na baki dama ta karshe na sanar dake sirrina kafin mu fara gumurzu domin bazaki taba samun nasara ba akaina bare har ki samu damar daukar Baka na mahaifinki.Da farko dai a halin yanzu duk fadin duniya babu wani jarumi daya kai ni tsagwaron karfin damtse,zafin nama da karfin naushi.Babu wani sihirin tsafi da zai iya tasiri a kaina.Babu wani kaifi ko tsini dazai iya huda jikina.Idan zan kwana dubu ina yaki bazan gajiba.Ta yaya kike zaton cewa zaki iya gamawa dani har kije ki dauki waccan baka?Sa'adda Bandaru Bin Sandamu yazo nan a jawabinsa sai Jaruma Safirat tayi masa dan guntun murmushi irin na manyan jaruman dasuka yarda da kansu.Sannan ta dubeshi tace,babu wani bil'adama ko aljan ko dodo ko wata dabbab wacce bata da lago a jikinta.Na yarda ka fini komai da komai a bangaren karfi da iya yaki amma ban yarda cewa kafi ni sa'a da rabo ba.Wadannan abubuwa biyu sai an jarraba su akan san na kwarai.Koda jin wannan sai Bandaru yaji zuciyarsa ta dan sosu kuma ya kamu da matukar mamakin yadda akayi Safirat tasan cewa kowanne mahaluki yana da lago.Tabbas yasan cewa shima yana da lago,to amma yana da yakinin cewa bata isa ta gano lagonsa ba kuma koda ma ta gano din kafin ta cutar da shi ya gama da ita.Jaruma Safirat ta dubi Bandaru cikin izza tace,kayi sani cewa tun kuruciyata zuwa yanzu dana cika shekara goma sha takwas,duk abinda nasa a gabana sai nayi nasara,ban taba samun rashinta ba,komai wuya da hadarin al'amari kuwa zuciyata bata taba karaya ba,ka sani cewa ba wai na kwallafa raina akan wannan baka saboda kawai na samu mulki ba ne ko dukiya ko wata daukaka,sai saboda kawai ina da wani babban buri a karkashin zuciyata.Bazan bayyana wannan buri ba sai a ranar dana gama hada wannan baka da kuttun kwarinta a hannuna.Koda jin wannan batu sai Bandaru ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa yace,ke wannan yarinya,abida kike son ki cimma daidai yake da tatsuniyar yara ko kuma ince mafarkin da bazai taba zama gaske ba.Ina son ki sani cewa koda kin sami nasarar daukar wannan baka yanzu,to bazaki taba iya zuwa dajin Sarkif ba har ki shiga cikin kogon mutuwa ki dauko kuttun kwarin bakan nan saboda tsananin bala'i da hadarin dake can ya ninka na nan sau goma.Sannan matakan tsaron dake can fiye da shekaru dubu ma ba'a taba samun jarumi ko mayaki ko bokan daya ratsa su ba ya wuce har izuwa cikin kogon mutuwa walau mutum ko aljan.Kafin Bandaru ya gama rufe bakinsa tuni Jaruma Safirat ta tari numfashinsa tana mai cewa idan na gama dakai na dauki wannan baka zaka gane cewa zan iya zuwa can kogon mutuwar.Tana gama fadin haka sai ta daka tsalle sama ta dira a gaban Bandaru takai masa da makaman nata biyu a lokaci guda da nufin ta cisge masa kai.Cikin bakin zafin nama na gaban kwatance Bandaru ya sunkuya,makaman nata suka sari iska.Kafin ta kai masa wani harin tuni yasa kafarsa ya doki kirjinta.Saboda tsananin karfin dukan sai da tayi sama da baya tamkar an janyeta da majajjawa ta fado kasa tim da tazarar kimanin taku ashirin daga inda yake,ta kama aman jini da sarkakken tari a lokacin da taji kamar murhun wuta aka cusa a cikin kirjin nata saboda tsananin zogi da radadin bugun da yayi mata.Koda Bandaru yaga halin da Safirat ta shiga sakamakon naushi daya jal da yayi mata sai ya bushe da dariyar mugunta yace,tabbas yaro bai san wuta ba sai ya taka ta! Iya wannan naushi da nayi miki ya ishe ki masifa domin sai kin shafe wata uku a kwance kina jinyar raunin da nayi miki.Shawarar da zan baki yanzu itace ki rarrafa ko da jan ciki ne ki sauka daga kan wannan tsauni kije kiyi jinyar jikinki a can birninku na Kisra.Ko ba komai kin ajiye tarihin da sauran jarumai suka kasa.Koda gama fadin haka sai Bandaru ya juya mata baya ya nufi inda aka ajiye bakan yana murmushin samun nasara.Yana cikin tafiyar ne yaji motsin takun

Chapter 1 of 8