Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 8
idonshi arufe bai budesuba, ahankali ya girgiza kai, dad yace “u will marry her koma wacece”, ahankali ya bude idonshi dasukai ja ya kalli dad da kyar Ya iya bude bakinshi daya bushe sosai yace ” are u sure dad?”, baban ya girgiza kai hawaye yacika idonshi, mum tazo tarike dayar hanunshi tace “Oliver koma wacece zaka aureta,duty every parent ne subama yaransu abunda sukeso, kawai ka warke be strong my little boy”, takarasa maganan da kuka tace”karka mutu shine abunda banaso, kai kadai garemu plz don’t leave us,we promise zamu baka Hiraj,zamu nemota ka aura”, jini ya bulbulo ta bakinshi, da kyar ya zame hanunshi daga hannu dad yakai fuskan mum ya share mata hawaye yana girgiza mata kai, da sauri mum ta kama duka hannayen nashi tai musu kiss tace” I luv yhu my son, I luv yhu so very much”, hawaye ya gangaro daga idonshi bakinshi na rawa yakara cewa ‘mother Hiraj, kice mata tazo’, yana magana bakinshi na fitar da jini, dad yay sauri ya share hawayen shi yace” son don’t talk again kaji, get some rest”. Oliver da yanzu bakajin maganan shi yabude baki yana magana, da sauri baban yakai kunenshi bakin Oliver ahankali yaji Oliver na cewa” dad I want to see ur special adviser sultan of sokoto MALLAM MUHAMMAD KHALIL plz now dad Kafin na mutu,hurry up”, dad ya girgiza kai ‘don’t say dat plz son,bazaka mutu ba,yanzu zan kirashi’, jan mum yayi dake kuka sosai suka fita adakin, Dr yazo zaimai allura Oliver yace “saura lokaci kadan natafi karkamin alluran kabari nafara ganin Sultan, nakusa tafiya”, ahankali likitan yasaki alluran tafadi akasa. Maman Abd Shakur😘 🌸🌺KABILAR MU🌺🌸🌺🌺🌸🌺 34 Yaja kujera yazauna gaban Dr Oliver ahankali yace “sir u have to be strong, karka manta kai Dr ne,dad dinka yace sai nemoma hiraj sir, Dr Oliver da kyar ya bude baki yace “help me with my phone”, Dr din yatashi ya miko mishi, Oliver ya rike phone din da hanun Dr din gam, Dr na ganin haka ya kara kunenshi abakinshi danjin maiyake fada, saida Oliver yagama fada mishi sanan bacci ya daukai, wayan Oliver din naga Dr din yanata danne danne na kusan minti 15,sainaga ya ajiye wayan kan drawer, ko 2min ba’a yiba saiga wayan yafara kuka Director aka rubuta akan screen din wayan, Dr din ya dauka, daga dayan bangaren Director yace “sir naga kamin transfer 20 million naira da account number ka namenene?”,Dr yace” sir yana bacci, but yace nafada ma dazaran result din jamb da waec din Hiraj yafito ka nema mata admission a best university din kaduna state,ka saimusu big house subar gidan dasuke, clothes, da everything da a lady needs, idan kudin bai isaba kafada ma dad dinshi. amma yace karka fada musu shine, kace government ne,takara samun wani scholarship ne,bayason kowa yasan daga wurinshi kudin yazo, hope you understand?” director da sauri yace “yes sir”, daga bisani suka katse wayan. Wuraren 8 aka bude dakin aka shigo Mr president ne,dawani kakkyawan matashi wanda bazai wuce sa’an Oliver dinba,dogo yanada gemu da dingilallen wando,hanunshi na rike da jakan laptop. Dr yabasu waje, Mr president ya sauke ajiyan zuciya yace “AMIR gashinan,bansan mesa yakeson ganin dad dinka ba,but kome yakeso kamishi, help my son”, ahankali matashi yaja kujera ya zauna agabanshi yana karemai kallon shi bai taba ganin ciwon da mutum zaiyi yellow hakaba, Mr president yace “Amir kuyi magana yanzu cos by 10:00 zamu wuce Paris” yaron yace” to” Mr president yafita Dr ma haka yafita. Ahankali Amir yay Bismillah yakama hannun Oliver ya rike gam,ahankali Oliver ke bude idonshi ya saukesu akan Amir, bakinshi daya bushe yake kokarin budewa da sauri Amir ya mika dayan hanunshi ya dauko ruwa yabashi da kyar Oliver ya iya hadiyewa bayan yasha Amir ya ajiye goran agefe yana kallonshi, ahankali Oliver yace “who are you?”, Amir yay murmushi yace “am d son of sultan, AMIR MUHAMMAD KHALIL, babana yay tafiya saisa yace na wakilceshi akiran shugaban kasa”, Ahankali yace “meke damunka?” Oliver da kyar yace “ALCOHOLIC HEPATITIS, da LIVER STONES”,… tari yafara yi najini Amir yajuya zai fita yakira Dr, Oliver ya rikeshi ahankali yace “don’t plz, nasan kan ciwo na, i can control my self, akwai abubuwan danake son natambayeka”, ganin yanda jini ke zuba abakinshi yasa Amir yace “kadena magana bakinka na jini?” Oliver ya girgiza kai yace “I need to know, plz kafada min waye ALLAH?? Ya suffar ALLAH yake?? And menene ISLAM?? Maman Abd Shakur😘 [2/11, 3:49 PM] Aishat muhd: 🌺🌸🌺KABILAR MU🌺🌸🌺🌺🌸🌺 35 Amir ya dade yana kallonshi dan baiyi tunani arne zai taba yimai irin tambayan nanba, ajiyan zuciya ya sauke sanan yace “ALLAH shine ubangijin mu, wanda muke bauta mawa, shiya hallici sammai da kassai,ya hallici mutane,ya hallici Aljanu, ya hallici dabbobi, ya hallici duwatsu, ya hallici komi da komai na duniyan nan,shine ubangijin mu wanda muke bautama,mai saukar mana da ruwan sama,mai azirtamu, mai talautamu”. “ALLAH shine ubangijjn daya hallici ni ya halliceka,sanan yasa mukai girma har mukakai munzilin damuke ayau,ya hore mana ji, gani,feeling dakuma ganewa da fahimta”. Ahankali Oliver yace “so Allah shiya hallice ni, wot about Jesus ubangiji na,bashi ya hallice niba? wanda nake bauta mawa shi waye shi?”Amir yace “Jesus manzo ne, Annabi issa,(AS), messenger ne wanda Allah ya aiko,danya fadama al’umman shi su bautama Allah. Inda ace Jesus shine ubangijin gaskiya ya za ayi yay duk abubuwan damu normal people mukeyi?,mu musulmai munyi imani da Jesus saboda munsan manzo ne wanda ubangijin mu ya aiko”. Ganin Oliver yay shiru kaman yana tunani yasa yace “bari nabaka wani dan misali; zaka karanta book ko novel,zakaso kasan waya rubutashi. Oliver yace “das true”. Zakaga kakkyawan gini,saika fara neman waya ginashi. To kenan sama(heaven) da kasa(earth) babu wanda ya zana su,babu wanda yakera su?”,Oliver yay shiru, sai chan yace “to waya kerasu”?Amir yay murmushi yace “mutum yana gane abune inyay tunani, everything proves cewa ALLAH ne, shine kadai yakeda ikon yin halitta haka, ba mutane ko aljanu ba”, hannushi yakai kan cross din wuyan Oliver yace” take a look at dis cross, wanene wanan da aka nuna a rataye jikin bishiya?”,ahankali Oliver yace “is Jesus”, Amir yace “wanan yay kama da mu ko baiyiba?”ahankali Oliver yace” yayi,munada dsame hanci,hannayen mu iri daya,kafan mu haka komi haka”, Amir yace “inhar kai da kanka u were able to understand hakan,den mutum irinmu baida power halittan sama da kasa,baida power yin sama da kasa, annabi issa annabin Allah ne mu amatsayin mu na musulmai munyi imani dashi. Anybody da baida power halittan sama, baida power halittan mutuwa, baida power rayawa da azurtawa, to dat person is not worthy of worship. ALLAH is d only one dayake da karfin nan saisa muke bauta mishi. Wanan takaitachen bayani kan Allah ne. Ka tambayeni game da ya siffan ALLAH take, ya rike hanun Oliver yana murmushi yace “Kome zaizo zuciyanka akan ga yanda siffar ALLAH take,to bahaka yaken ba,kawai kayi tunanin abunda ALLAH ya hallitta, karkai tunani akan yanda ALLAH yake, dan ALLAH yawuce tunanin ka, ALLAH is beyond our comprehension”. Oliver ya dade baiyi magana ba,saidaga baya yace “to menene ISLAM??”. Maman Abd Shakur😘 [2/11, 4:46 PM] Aishat muhd: 🌺🌸🌺KABILAR MU🌺🌸🌺🌺🌸🌺 36 ISLAM addinimu ne,ISLAM adinine dake koyar damu yakuma sanar damu cewa; ISLAM is a universal addinin da aka turo mana kowa,all humanity. ISLAM addinine mai adalci wanda baya daurama gajiyayyu responsibility dabazasu iyaba. ISLAM adinine mai adalci wanda baya xaban gidan wane ko wance saboda sunfi kudi ko sune duniya keji dasu,ko sune aka sani akoina,ko wanan fari ne,ko baki, a addinin musulunci kowa daya ne,wanda yafi wani a wurin Allah shine wanda yafi tsoron Allah. ISLAM addinine wanda duk abunda aka hanemu,idan zaka duba abun to yanada illa, misali shine Allah yahana shan giya, da sauri Oliver ya kallai, Amir yace “yes addininmu yahana shan giya,and idan kaduba shan giya nada illa akarshe zata iya baka ciwuka kala kala,ta lalatama koda. Yahana zina,kuma shima zakaga ana daukan cutuka kala kala ta hanyar zina. addininmu is d best, anything dazai kawo illa a jikkunnmu adininmu yahana. Jakarshi yabude yaciro wasu books yamika mishi, yace “ka karanta books dinan u will know alot about ISLAM,dukda har yanzu bansan mesa kake tambayana about Islam ba”. Da kyar Oliver ya karba ya daura akan cikinshi. Karfe goma nayi Mr president, 1st lady, wasu escort masu kayan sojoji suka shigo dakin, Mr president ya shafa kan Oliver yace “my son is tym to go”, ahankali Oliver yarike mai hannu yace “dad inason Amir yabini”, Amir zaiyi magana Oliver yace plz,” haka ya yarda. aka saka Oliver a jirgi yana rikeda books din da Amir yabashi mai suna MY BEAUTIFUL RELIGION, wani guard ne yake karanta ma Oliver book din ahankali yana sauraro yayinda Amir ke gefenshi, Oliver yaki bacci,jikinshi yay mugun zafi,kawai littafin yake sauraro”. Abangaren Eraj haka aranan tagama kukan ta takoma cikin gida,zazzabi sosai yarufe ta adaren,Amma ta matukar damuwa,danko bude ido batayi da kyau,sai Amai datakeyi kaman zata amayar da hanjinta. kawu Amma takira washe gari,ganin basuyi bacci ba, yazo yan kudin da yakedashi Amma tahada da nata aka kaita asibiti, gado aka bata wai maleria ke damunta. Washe garin ranan suka isa Paris da safe,direct asibiti aka wuce dashi,har alokacin yaki bacci book din ake karantamai,suna shiga asibitin aka wuce dashi dakin x-ray, aka gano dole amishi aiki yanzu acire stones din,jikinshi yay zafi,idanunshi sunyi yellow, farar fatanshi yay mugun yellow, kaya aka chanzamai aka fito dashi dan yaga iyayenshi kafin ashiga theater, Mr president, 1st lady, da sojoji duk awurin, aka gunguro Oliver akan gadon marasa Lpy, mamarshi ta fashe da kuka ta rungumeshi, murmushi ya mata ya mikama Amir hannu, Amir yatashi ya rikeshi, Mr president ya dafa kafadar shi hawaye ya zubo, wani karfi Oliver yaji yazo mai, ahankali yace “mum dad I want to convert”,zan dawo musulmi, I finally realize kiristanci adinin bata ne,ISLAM is d best religion, addinin gaskiya,addinin adalci, ahankali yakalli Amir yace “Amir I accept ur religion! Nayi imani da ubangijin ka Allah!”. Ni ummu Abdush-shakur nace ALLAHU AKBAR!. Maman Abd Shakur😘 [2/12, 4:52 PM] Aishat muhd: [2/12, 10:27 AM] Aishat muhd: 🌺🌸🌺KABILAR MU 🌺🌸🌺 37 Amir durkushewa yayi yace “sir anya kaine kuwa…?,bai karasa maganan ba yaji anja bayan riganshi,da sauri ya juya yaga 1st lady ce tana huci, tace “leave dis hospital right dis minute, nasan kaine kai brain washing dana, dukkai kasamishi idea musulunci akai”, ta dakamai tsawa get ‘out of here’, ta kalli Oliver wanda ita yake kallo idonshi araunane tace”son are u out of ur mind ko ciwo haukane? baka da hankaline?bakasan enemies dinmu bane? y? mesa zakace kadawo Muslim? u are joking cos dat will never happen”,Allah yasa Ida suke dakine babba su kadai harda kujeru dayake president ne saisa akaimusu karamcin amma da kowa yaji fadan datake, ahankali Oliver yasa hannu ya cire sarkan dake wuyanshi yabama guard din dake tsaye gefenshi yakalli Amir yace “am ready”, Amir da murmushi a fuskanshi yabashi kalmar shahada take Oliver ya fada shima,fass kakeji 1st lady ta wankama Amir kakkyawan mari tace “zaka dawo da dana irinku,yana ajiye wanan gemun kaman na bunsuru da dingilallen wando” ta shake Amir,tana kallon president da jikinshi yay mugun sanyi tace “say something, kana ganin danka yadawo Islam, kuma kasan bamu sonsu,I hate Muslims”, ahankali president yazo yace “sakeshi”, yacire hannunta daga wuyanshi, cikin yarensu yace” honey I know yanda kike feeling yanzu, but dis is not tym to fight or argue, we are after our son’s health, plz calm down, Oliver is an adult, yanada right to choose abunda yakeso ma kanshi,idan he thinks being a Muslim is what best 4 him, dole we have to respect dat,he is our only son,and I as his father zan mishi kome yakeso aduniyan,inhar inada hali da karfin yinshi,Oliver is my pride,my hair, my blood, I will support him, his all I got, at least yanzu operation za’amai we should try nd make him happy, yatafi da murna cikin theater din”. Maman tace” so u are supporting him, honey kamasan maikake fada kuwa?,yaron mufa yadawo musulmi kakosan mai hakan ke nufi?”. Mr president yace”Oliver is morethan 18 years, lokacin dayaro yakai 18 yanada right din kanshi,komi zai iyayi, Oliver is 29 years, ba yaro bane da we have to make decisions 4 him,at least look at his condition now and respect his wish,support him”, hawaye ya zubo a idonta tace “dat will never happen, I will never support u being a Muslim Oliver”, juyawa tayi zata fita escort dinta suka bita, da kyar Oliver yace “mommy”, juyowa tayi ta goge hawayen idonta, tace “dont ever call me mommy,starting 4rm today am not ur mother u are not my son, indai kan musulunci ne dudda kai kadai garen,na yarda na rabu dakai har abada Oliver u are not my son, tasakai tafita daga dakin. Maman Abd Shakur 😘 [2/12, 12:36 PM] Aishat muhd: 🌺🌸🌺KABILAR MU 🌺🌸🌺 38 Oliver ya fashe da kuka,baban ya shafa gashin kanshi yace”shii,nasan mamarka bazata taba iya fushi dakaiba,zata sakko,mubata lokaci kaji my baby boy kadena kuka,be strong 4 ur daddy”, Oliver ya kankame hanunshi yace”I luv u dad”, Baban yamai kiss a goshi yace “luv u too son”,nurses suka shigo dakin dan tafiya dashi theatre, Mr president da Amir suka rakashi har bakin kofan,harza’a shigar dashi Oliver ya rike hannun dad da Amir yace “dad promise me zaka auramin Hiraj,plz promise me idan natashi I will see her by my side a matsayin matata plz dad”, yana maganan yana tarin bakin jini, Mr president kasa daurewa yayi hawaye shar shar shar jiyake kaman ya daukemai ciwon, Amir da shima idonshi ya cika da hawaye yace “in sha Allah zamu nemama aurenta zaka farka ka ganta tareda kai a matsayin mijinta kaji ya girgiza kai,Mr president yace “I promise zan tura a auro maka ita,kome kakeso a duniya saina ma my son”,Oliver yace” Director of ideal international school yasan komi zai kaiku gidansu Hiraj Dina” sakin hanun Mr president yayi aka shiga dashi theater,ahankali bakinshi na furta my baby doll”. President yasamu wuri ya zauna yana why Jesus maisa zaka wahalar min da dana? Amir yay shiru yana mamakin yanda sukeson Oliver haka. Ayaune aka sallamo Eraj,suka dawo gida,kawu da matarshi atine da yarshi sa’an Eraj mai suna Fiddausi duk suna gidan dan saida yamma zasu tafi. Jikin Eraj da sauki dan tadan murmure saidai ta rame takara haske kaman mara jini ajiki, ganin kawu yatafi yin azahar a masallaci,ga Atine da Fiddausi na kitchen yasa Amma ta shiga dakin danyima Eraj magana, tana shiga dakin taga Eraj ta share hawaye da sauri,dan bataso Amma taganta tana kuka, Amma ta zauna kusa da ita tana shafa kanta ahankali tace “Eraj son Oliver kikeyi?” Da sauri tace”ni Amma?,ni banison shi,mezanyi da arne”,Amma tace nasan kin ganshi ranan saisa kika fara ciwo” kuka tafara tace wlh wlh ni Amma ni ni banason shi,dama dama dama aifa kawai ni tausayi yaban saisai” Amma tai kwafa tace gwara karma kifara wahalar da zuciyarki dan arne ne,koda zaki mutu bazaki taba aurenshi ba harsaiya musulunta”. Sallaman kawu sukaji ya kwalla mata kira, Amma fito kinyi baki, tabarma ya shimfida suka zauna Amma ta dau Hijab tasa ta kalli Eraj tace “nadai fada miki”,tasakai tafita, Eraj tafashe da kuka sosai ta rike zuciyarta tarasa meke damunta ita tadaisan batason Oliver to kodai tausayi ne?danta ganshi yana kuka, amma maisa yanzu takejin tanason ganinshi tanason karajin muryanshi. da sauri ta share hawayenta ta dau Hijab tasa jin Amma na kwalla mata kira. Tana fita taga director school dinsu dawani mutum a gefenshi suna sanye bakaken suit, ganin fuskar kawu dasu Amma tayi dauke da murmushi, zaunawa tayi gefen Amma cike da ladabi ta gaida director da dayan mutumin director yay murmushi “yace Congrats Eraj, kinci waec dinki da jamb da kyau government tabaki scholarship harki gama university, wanan shine ma’aikacin da gwanati ta turo. Eraj tafasa ihun murna ta kankame Amma jin zata fara university, Burinta yakusa cika, yamika mata result din ta duba komi A1 a waec, jamb kuma tana 340 marks,saida tagama murna sanan director yace ‘gwamnati tasai muku gida takuma baki mota kirar Benz dan haka yanzu zaku bimu mu kaiku gidan’, Amma kawu kowa yay shiru yana kallonsu, director yamika ma Amma paper yaace “kiduba duka paper din gidan ne dana motan kiyi signing, ki godema Allah yarki Allah yamata baiwan kwakwalwa”,Amma tai shiru takasa signing tana kallo Atine,kawu yace “yi singning Aisha”, ahankali Amma tai signing, duk suka mimmike, sukace sai zuwa gidan,haka suka shiga motan suka kaisu gidan suka wuce. Komi akwai a gidan,ansa musu komi ranan sunyi murna sunyi kuka,sai Albarka suke sama Eraj,da kyar Amma taroki kawu yadawo kaduna da zama taba kawu kyautar motan,da kyar ya karba,yakuma yadda zai dawo. Maman Abd Shakur 😘 [2/12, 3:48 PM] Aishat muhd: 🌺🌸🌺KABILAR MU🌺🌸🌺🌺🌸🌺 39 PARIS. Karfe 6 daidai na yamman kasan Paris, likitoci suka fito daga theatre da sauri Mr president da Amir suka mike, Dr ya gaida Mr president yace “d operation was successful, saura matsala daya shine damuwan dayake ciki, kubashi abunda yakeso,inba hakaba zai iya komawa giya kuma hakan na iya dawomai da Alcoholic hepatitis din,yanzu saidai mujira tashin shi”,Amir yace “Alhamdulillah”,dad ya sauke ajiyan. Haka aka barsu suka shiga dakin, Mr president a asibitin ya kwana,yasa aka tafi da Amir hotel dan yay bacci yahuta, cikin dare har bacci yafara daukanshi yaji Oliver na ambaton Hiraj, Hiraj, da sauri Mr president Ya daura hanunshi akan kan Oliver, ahankali Oliver yarike hanun ya sauke ajiyan zuciya yace “my Hiraj”,sanan ya cigaba da bacci. Da safe Mr president yadau waya yakira 1st lady bata daukaba,yasan fushi take. Kiran Director yayi,director ya dauka da sauri,magana sukayi mai dadewa da Mr president sanan ya katse yakira wani abokinshi dasukai school tare malami babba, shima sukai magana sun sanan ya katse yakoma dakin da Oliver yake. NIGERIA. karfe 11 ne nasafe a katsar Nigeria, awanan lokacin Eraj da fiddausi sun tafi hadda,duk suna zaune a falon kawu suna hira,da Amma da kawu,da Atine,suna mamakin sauyin rayuwan dasuka samu tashi guda,kawu yace “inama yayana (baban Eraj) na raye, yay alfahari da yarshi…knocking gate din gidan akayi da sauri kawu yafita, ba ajimaba ya dawo da baki kusan su goma, sunci manyan kaya,cikinsu harda director,falo dinshi yakawosu,su Amma suka tashi zasu fita kawu yace “kudawo ku zauna”. Bayan an gaggaisa,wani dattijon cikinsu yace “munzo aikan shugaban kasa ne, ku taimaka kubama yaronshi auran yarku Eraj”,Kawu yace “wani shugaban kasa?kuma wani dannashi?ba arna bane antaba aure tsakanin arne da musulmi?”, Ya kalli Amma yace “wata mu’amala tataba hadaku da dan shugaban kasa ne”?Amma tace “nidai mutum daya nasan yataba son Eraj Oliver, kuma ganin ba musulmi bane yasa nace yayahakuri,bansan kodan shugaban kasa bane”. Kirane ya shigo wayan malamin da sauri yadaga naga yace yes mr president, sai yasa wayan a speaker yamika ma kawu,ahankali kawu ya karba. Cikin gwarancin hausan Mr president yace”plz kutaimaka ma yarona karya mutu I beg u,plz”,kawu yay shiru wai anya ba mafarki yakeba kuwa shugaban kasa guda yana rokanshi, da raunanniyar murya haka. Maganan Mr president yaji yace”nasan zaka dinga tunanin bamu yarku aure wlh nai alkawari zan riketa da kyau,zan kula da ita,dana bazai taba bata mata raiba,plz yana gadon asibiti aiki akamai”,Mr president jin kawu yay shiru yasa yakara rudewa yakai wayan saitin bakin Oliver sukaji ahankali yana fadin Hiraj Hiraj,Amma idanunta suka ciko da hawaye saboda tausayin Oliver, kawu da muryanshi ya dishi yace “Mr president addininmu ba dayaba,KABILAR MU badayaba”.. Mr president yace “dana yadawo musulmi, wlh ya musulunta,ga abokinshi ku tambayay”,ya mikama Amir wayan,ahankali Amir ya karba wayan yama su Amma bayanin komi,hakanan kawu yaji ya yarda da maganan Amir, Amma ta matukar tausayama Oliver, Mr president ya karbi wayan yace “plz abama maman yarinyan,Amma ta karba yace” madam ke uwace, kinsan yanda yaro yake inbaida lpy, plz kitaimaki dana, dazaran ya warke zamu dawo Nigeria sai ayi biki da shagali, amma yanzu kubari adaura auren ataho da ita”,hawaye ya tsiyayo daga idon Amma ta kalli kawu ya gyada mata kai tace” Mr president mun yarda” Atake a wurin babban Malami da sauran jama’an dakin suka shaida daurin auren Dr Oliver da Eraj akan sadaki mafi karanci,inda kawu ya wakilci Eraj,dayan malamin ya wakilci Oliver. Maman Abd Shakur😘 [2/12, 4:49 PM] Aishat muhd: 🌺🌸🌺KABILAR MU🌺🌸🌺🌺🌸🌺 40 Director yace “ina Amaryan tamu?”Atine tace “sunje hadda itada yayanta”, haka suka baro falon, sukabar kawu da jama’an suna zaune ana jiran dawowan Eraj. Ahankali Amma tasamu gefen gado ta zauna tai tagumi hankalinta atashe, Atine ta dafata ahankali tace “Amma karki damu wanan auren haka Allah ya kaddaro xai faru,kuma ina keda kanki kince yaron nasonta?,kisa aranki wanan auren auren alkairi ne Wanda zakiyi alfahari dashi nan gaba,Amma tai shiru tace “ya Eraj zataji yarinyar daketa murna tasamu scholarship zata zabi university datakeso taje,Eraj tasha fadamin batason aure yanzu, kwata kwata ban shiryata kan aure yanzu ba,batasan komiba gameda yanda ake kula da miji balle zaman takewan aure ba, auren da yarone kadai musulmi uwa arniya baba arne”. Atine tace “karkiyi tunanin haka, kima yarki fatan alheri abunda take bukata kenan”. Suna zaune duk sunyi shiru Atine tafito da sabon pink lase da bakin takalmi,sai bakin hijab iya ciki ta ajiye akan gado Amma tabita da kallo karfe sha biyu kawu ya shigo dakin yace “har yanzu bata isoba?”Amma tace eh,kawu yace “kodai naje na dauko tane… sallaman Eraj da fiddausi sukaji suka shigo dakin kawu yafita yace “kuyi sauri ku shiryata fa”. Eraj data bisu da kallo tace “Amma zamu fita da kawu ne?”ahankali Amma tace “eh”. Atine tajata takaita bayi saida tabata wasu magunguna tasha sanan tabata wasu tai tsarki dasu tamata wanka da ruwan turare, duk kunya yakamata mai Atine kemata wanka saikace yarinya, sai kallon Amma take,kayan akasa mata Atine tai mata ubansu kwalliya tai mugun kyau sanan tace “zauna da mamanki zata mini magana”, Atine taja hanun Fiddausi sukabar dakin. Ahankali Amma tace” Eraj abu daya zan fada miki kima mijinki biyayya, yanzu ana jiranki kuma kinsan babu kyau shanya mutane amma in kukakai chan zan kiraki zan miki bayanin komi kinji my baby”, idonta yaciko da hawaye tace “Amma aure kuma? wayay aure”… Amma zatai magana kawu ya shigo yace “yauwa mutafi”,Eraj tafashe da kuka tace “wayey aure?” Amma tace “kece,share hawayenki zamuyi magana inkin kai,kima mijinki biyayya”, da sauri Atine tafito da karamin trolley taba Eraj tace “abubuwan ciki ki dingasha kullum magani ne kinjiko” tace to, tana kuka sosai tana kallon Amma da idanunta yacika da hawaye sosai. Waje suka fita kawu yasata a mota shima ya shiga ya zauna sauran jama’an suka shiga sukaja motan sai Airport. Amma tafashe da kuka tana Allah kareki my baby. Eraj kuka sosai take a mota kawu na lallashinta, suna kaiwa Airport din kaduna already jirgi na musamman na jiranta, gabaki daya kanta a dode yake takasa gane komi, kawu har gaban jirgin ya kaita ta kankameshi tana hawaye kawu ina xaku kaini? Yace “paris, ki kula da mijinki baida lpy”, wata mata ne ta sauko daga jirgin ta duka ta gaida Eraj tace” u are welcome ma,aikina shine kula dake da bukatunki har mukai Paris, mu shiga ciki”,saida kawu yay kaman xai bugeta ne tawuce matar ta karbi trolley hanunta tarike hanun Eraj dake kuka kaman ranta xai fita suka shiga jirgin, agaban kawu da sauran jama’a jirgin ya daga sai Paris. Eraj tai kuka har bacci yay gaba da ita. Alamun taping dinta ahankali taji anayi,bude idonta tayi taga matan namata murmushi tace”ma kin dade kina barci harmun iso”,tamika ma Eraj wasu kayan sanyi masu fitanannen kyau riga iya guiwa da wando,ringa pink da baki, wandon complete baki,tace “jekisa kayanan, dan akwai sanyi agarin”, Eraj ta shiga inda matan tanuna mata ta chanza kayan takara maida hijab dinta tafito,matar tai mata make up, tai kyau sosai tace” we are ready to go”,kama hanun Eraj tayi wani soja yazo yadau trolley din,wani babban Jeep ke jiransu, Eraj jin waje sanyi yasa ta kankame jikinta sojoji suka bude mata motan suka shiga sanan aka jazu. Wani baban wuri tagani,ginin gabaki daya glass ne mai kama da madubi,achan wani bangare taga ansa ST MARGIN’S SPECIALIST HOSPITAL. Parka motan akayi aka bude musu suka fito,sojoji hudu agabansu hudu abayansu su suna tsakiya, kankame matan tayi tafara kuka sosai, tana” ina xaku kaini?” Elevator taga sunshiga soja ya danna 17th floor, kawai taga abun yadagasu ihu tayi tarike mata tana kuka, matan ta rike ta tana lallashinta saida sukakai sanan suka fito, wani daki tagani sojoji kusa 20 agaban dakin sun tsaya kyam kaman basu motsi,dakin suka dosa, kara kankame matan tayi tana kuka me za amin? wlh ni bantaba yima sojoji rashin kunyaba”. Ahankali taga wani soja yabude musu kofar dakin matar adaidai nan ta tsaya tace” ma,anan aikina ya kare”, kullo kafan akayi Eraj tafashe da kuka tana bubbuga kofan ku budeni”…. ahankali taji ance “Hiraj”. Maman Abd Shakur😘 [2/14, 7:44 AM] Aishat muhd: [2/14, 6:41 AM] Aishat muhd: 🌺🌸🌺KABILAR MU🌺🌸🌺🌺 🌸🌺 41 Juyowa tayi da sauri jin an ambaci sunanta,idanunta ne suka sauka kan Dr Oliver dake kwance kan wani makeken gado,an lullube duka jikinshi da bargo, hanunshi anyi fixing drip,idanunshi arufe, kama bakinta tayi jin wani irin kuka yataso mata,karasawa tayi gaban gadon ta tsaya tana kallonshi ya rame sosai,kuka tafashe dashi ta zauna kan kujeran gaban gadon takifa kanta tana kuka, wani irin tausayinshi taji yana shiganta. Bude kofa taji anyi da sauri ta share hawayenta tajuya tana kallo mutane biyun dataga sun shigo, babban yay kama da Oliver sosai,dayan kuma taganshi ustaz ne, Mr president da murnanshi yace “welcome my daughter in-law”,sauke kanta tayi tana wasa da yatsun ta ahankali tace “ina wuni”,Mr president yace “kidena jin kunyana am ur dad”Amir ya karaso ya ajiye abunda kehanunshi agabanta yace”sannu da zuwa”kallonshi tayi da sauri jin yamata hausa, Mr president yace”bari mutafi tunda kinki sakewa, mayi hira gobe, yanzu kiyi bacci nasan kin gaji”Eraj ta girgiza kai, karaso wa yayi gaban gadon yama Oliver kiss a goshi, yace “gud nyt son,and wake up soon cos ur wife is here”ya juya yanama Eraj murmushi. Mr president yafara fita,Amir yajuya zai fita,cikin muryan kuka tace “mainake yi anan?me zaku kawoni wurin arne?”Amir juyowa yayi ya kalleta yace “wurin mijinki kikazo, ki kula dashi bakiga baida lpy ba, kuma ya musulunta tunba yauba”,da sauri Eraj ta kallai, ya gyada mata kai, wani kukan takara fashewa dashi ‘to wanene

Chapter 5 of 8