Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
yayi bangaransa. Isah kam yaso ya koma gida yau amma ganin halin da gidan yake yasa ya hakura amma yasan cewa iyayansa bazasu ji dadi ba kawai dai yasan idan ya fada musu abinda ya faru zasu yi mai uziri, kwance yake yana wannan tunanin a cikin dakin da suke shi da aliyu da kuma deeni, sai yanzu yama tuna da ya hardace lambar salmanu cikin hanzari ya tashi aliyu yace ya ara masa waya, shima aliyun bai yi barci ba tukun yana nan sai tunanin sahibar sa yake, nan ya miko masa wayar ya kira lambar salmanu amma a kashe. haka ya hakura yabawa aliyu wayarsa shima ya kwanta. Anne kuwa har ta kwanta kuma sai ta tuna da wasikan da aka kawo mata cikin hanzari ta tashi ta dakko tazo ta tashi su halima wai su karanta mata, “kai anne wallahi bakya jin magana yanzu bazaki barmu muyi barci ba mu hutawa ranmu” inji maryam, sannu matar yaya kwanta kiyi barci ni nama isa in hana aunty na barci. Pillow din dake wajen ta dauka ta wurga wa anne hade da cewa wannan kanwar tawa bata jin magana, suka yi dariya gaba daya. Anne ta mika wa haleema takardar, karanta min wannan, haleema ta karba takardar “mene wannan?” lokacin da take warwarewa, “kedai kawai ki karanta” hmm tace sannan ta fara karantawa kamar haka. (( Assalamu alaiki bayan gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan kin wuni cikin koshin lafiya gimbiya aneesat, farar mace alkyabbar mata, yar mutunci da kima. Halima ce ta dan tsaya da karatun ta kalli anne tana mata murmushi, ita ma martani ta mayar mata, maryam ma haka ta matsokurkusa dan jin waye ya aiko wannan wasikar sannan halima taci gaba da karanta musu, a hakikanin gaskiya na fada kogin kaunarki tun kallan farko da na miki nake, tunanin ni dake mun dace, tarbiyarki da natsuwarki da sanin ya kamatar ki sun mini aneesat. Saidai bansan ko zan sami masauki wato gurbi a zuciyarki ba, ki bani dama in nuna miki so da kauna da kulawa, ina san ki zama mallaki na uwar yayana, ki zamo mai share min hawaye, karki sa su zubo aneesat. Nasan zakiyi mamakin jin nine na aiko da wannan wasika amna ta wani bangaran ba abin mamaki bane domin shi so baya buya kuma so makaho ne. Daga karshe dai ina kuma jadada miki so da kaunar da nake miki i love u aneesat. Daga Aliyu zuwa gareki.... ina jiran amsa daga gareki sai anjima... Nan fa anne kunya duk ta cika, zolaya dai ba irin wacce basu mata ba daga baya suka natsu, maryam tace to yanzu fada mana, kina san sa ko kuwa. Haleema ce tasa hannu ta dan bigi maryam tare da cewa ke ina ruwanki, maryam tabe baki tayi sannan tace to miye laifi na ai gwara a fada mana domin musan matsayin mu, haka dai sukaita surutan su ita kam anee bata sa baki ba, bata ce musu ko uffan ba. Nan suka gaji har suka kwanta bata basu amsar eh ko a’a ba. Washe gari tunda sassafe bayan anyi breakfast wajen karfe 8 kowa ya taru a katan falo kawu ake jira kawai ya karaso................ Ayi min afuwa ban sama damar post ba jiya da shekaran jiya ba Shi kuwa deeni gaban sa ne yaci gaba da faduwa wato kawun haleema kenan aka bawa dodo, hawaye keta kwaranya a idaniyar deeni, wai an kashe haleeman shi da kuma kanwarshi shi maryam da yake matukar ji da ita, bashida burin da ya wuce ya farantawa ummansa da kuma yar kanwarsa wato maryam tunda babansu baya raye, wani xazzabi ne ya rufe deeni. Maryam ce zaune kan wani gado na kara ta dafe kumatu wato tayi tagumi, tunanin ummanta kawai take, wasu yan siriran hawaye ne suka kwaranyo, haka haleema ma da take kwance kwakwalwarta sai juyawa take cike da tunani iri iri tama rasa wanne zatayi shin waye mai neman hallaka mu, shin wane hali deeni na ke ciki, shin umma da abba ya zasu ji na rashina bayan basa san yin nesa dani ko kadan, idanun ta cike da kwalla ta tashi zaune ganin maryam a gefan gado ta zuba uban tagumi, “maryam maryam” inji haleema tunanin me kike. Tuni maryam ta dago tare da sa zani tana goge hawayan fuskarta, nan haleema ta fahimta cewa duk ashe daya ne halin da suke ciki. Ta dafa kafadar ta haba my sis ki saka dangana a zuciyar ki mana mu barwa Allah komai shi zai yi mana maganin wannan al'amari ba kuka ne abunyi ba... Aneesat ce ta shigo, ganin su a wannan yanayi ta fahimta tunanin gida suke yi, duk da sun so su boye wa anne amma saida ta fahimta, “haba yan uwana, nan fa kamar gidan ku ne ku kwantar da hankalin ku, dama yanzu daga wajan maman mu nake shawara muke yi yanda za'a maida ku gida, ku kwantar da hankalin ku”... Tabbas sunji dadi sosai da jin kalaman anne gaba daya suka ce “hmm anne kenan haba ba komai amma gaskiya muna so muga iyayan mu domin basu san ko wane hali muke ciki ba, kinga in sun gammu hankalin su zai kwanta. Yaro ya shigo da salamar sa “anne wai ana kiran maryam, bata tsaya ko jin waye ba tace “je kace gata nan”, domin anne tuni ta kyaro su wato tana lura da abunda ke faruwa tsakanin maryam da kuma isa. Ya zaki ce gani nan bayan baki san kowa ke sallama ba, shin waima cikin gari nan waya san ni da har zai aiko kuma wai ace maryam tazo ma. Anne tayi murmushi ai sai kije ki gano mana. cikin zolaya haleema tace “kanwar mu ah gaskiya kinzo kauyan nan a sa'a kinga shikenan sai mu barki anan”. Suka sa dariya gaba daya. Bari inga ko waye tunda kun matsa ta ce, anne ara min hijab dinki. Ya mata daidai kuwa kamar dama nata ne.. A tsaye ta iske shi ya harde kafafu da kara da ya rike a hannun hagu yana wasa da shi, hannun daman kuma yasa shi cikin aljihun wando. “Assalamu alaika” ta fada, wani irin sauti mai dadi yaji a zuciyarsa yace dama haka muryar yarinyar nan take ashe. Amin wa'alaiki Salam warahmatul lahi ta’alah wa barakatuhu: sanda ya cika amsa sallamar cif cif. Gefe daya ta samu ta tsaya nesa da shi kadan, ita kam ta kasa dagowa da kanta domin wannan ne karo na farko nata na tsayawa da wani da namiji .. Maryam kenan sarkin kunya shin ko dai kema yar fulani ce kamar mu, amma ai ke kunyar taki tayi yawa ma. Murmushi kawai tayi domin ta gane yaya Isah ne shi isa taki ma dago kanta domin tsoran abinda take ji in ta hada ido da shi wato faduwar gaba. Ki daure ki dago kanki, ki kalle ni ya fada yayin da ya dan kara matsowa kadan kusa da ita. A hankali ta dago kai “wow” dama haka wannan bawan allah yake da kyau, ashe duk ganin da nake mai zaije farauta ne, amma duk da haka yana da kyau saidai kayan da yasa sun kara fito da zallan kyawun sa wanda haka yasa ta kafe shi da ido shima dai abun ya daure mai kai ta tsaya sai kallan sa take... Um dama so nake in gaya miki…… Kuma sai yayi shiru, ka fada mana a zuciyarta ta fadi hakan, gani tayi ya kalle ta, tayi saurin sunkuyar da kai ashe yaji abinda tace... Maryam ba wani abu bane dama ina so in gaya miki ina sonki, ina kaunar ki, tunanin ki ya hanani sukuni ko ina naje bana jindadi in ban ganki a gunba, idan na rufe ido ke nake gani, nayi tunanin cire haka a zuciyata sakama kwan ni dan kauye ne ke yar birni ce kinga kuwa auran mu bazai yiwu ba amma dai yanda sanki ya addabi raina yasa ni dole in gaya miki ko naji dan sauki... Farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta hakika taji dadin kala man sa, wannan ne na farko da namiji ya taba cewa yana santa abinda ko da wasa ba'a taba gaya mata ba, kalmar so kenan yayin fadarta sai bakin ka ya fara bari duk jarumtakar ka, bama kamar karo na farko haka duk macen da aka furtawa a take a waje sai taji chanji, lalai so halitar Allah ne, juyawa kawai tayi da niyar tafiya ita duk kunya ta dabai baye ta.. “Maryam” tsayawa tayi chik, baki ban amsa ba zaki tafi, ki taimaki zuciyata karta fashe mana. Juyowa tayi ta sakar mai tattausan murmushi mai dauke da sako, saidai shi bai iya karanta iri kalaman din jikin murmushi ba, kawai cikin gida ta juya ta shige. KU KARANTA :- An kama wani Fasto dumu-dumu yana yayyaga Qur`ani yana konawa a jihar Kogi Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da Takwas dan jin cigaba ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 27 Share This: Batun yazeed kuwa da aka tafi dashi dake dare yayi cikin wani daki aka saka shi wanda ake saka masu laifi da safe da suka zo suka duba tarar da shi sukayi ya mutu, bakin sa na zubar da wani abu bakikkirin kamar an daka tawwada haka kuma ya wani kun bura kamar zai fashe, shugaban sojojin DPO ya kira ya sanarwa da hakan cikin gaggawa ya nufi gidan alhaji sanusi, ganin yanda gidan ya cika da farin ciki da murna yasa bai fada musu halin da ake ciki ba, suna gaisawa ya juya zai koma nan alhaji ya kira sa ya mai kyaututtuka, nan ya fahimci su tuni sun ma manta da dan nasu shi yasa ma bai fada musu abinda ke faruwa ba dan karya tayar musu da hankali. Washe gari bayan isah yaje ya bayyana wa iyayansa duk abinda ya faru, sannan ya bayyana musu maganar auren sa da kyaututtuka da abba ya mishi da ma batun anne sannan kuma ya nemi su da su koma birni tunda ba abinda suke yi a kauyen har kaka zasu tafi. Iyayan isah sun amince da zasu dawo birnin, ummansa ce ma taki yarda daga baya kuma da suka bata baki saita amince, a gidan da abba ya basu suka sauka, gida ne isasshe ba laifi ya isa suyi iya rayuwarsu, nan suma suka gode wa abba, bayan sunyi wanka sun huta ne isah ya dauke su a mota da yake dama ya iya da ita yaje dauko su ma a kauye, yan kauyan sun taya shi murna sosai suma, nan ya kaisu gidan alhaji ya gabatar da su, anne tayi murna sossai ganin mahaifiyar tata da kuma kaka, nan isah yake bayyana wa abba cewa iyayan nasa sun amince sun dawo nan domin yanzu na kwaso kayan su ma mun dawo nan, kowa yayi farin ciki sosai da jin haka, nan aka tashi yaran wajen ya koma sai iyayen aka cigaba da tattauna maganar aure yaushe za'asa shi, kawu yace tunda dai yara nasan junan su kuma iyaye duk mun amince dan haka ba sai an dauki wani tsawan lokaci ba kawai asa auran nan sati daya kafin nan kowa yayi abinda ya dace, kowa ya amince da maganar kawu nan aka shiga shirye-shiryen aure, amare kuwa sai gyara ake musu. A kwana a tashi ba wuya wajen Allah yaune sati ya cika kuma yau ta kama asabar daurin aure, anyi taro sosai anyi sha gul gula wanda lokaci bazai bada damar bayyana muku irin abubuwan da akayi a cikin wannan sati ba, anyi komai anyi taro iya taro an daura aure amare uku su duka ukun kaya kala daya suka saka, ba abinda zai burgeka sai ma kaga gidajen da abba ya basu a jere, fenti da komai da tsare-tsaren gidajen duk kala daya ne. Haka ko wacce kawayen ta suka rakata gidan ta, gida dai ya kara girma ya cika da farinciki zaman lafiya suke su duka ukun suna shan soyyaya abinsu. ALHAMDULILLAH!!!!! A nan wannan labarin yazo karshe ina fatan masu karatun kun samu darussa da nishadi a ciki. Muna muku albishir da cewa a yanzu haka akwai wani littafi da zamu fara saka muku shi, kuma muna sa ran zaku ji dadinsa sossai, Musamman ganin yadda wannan littafin na namiji ne kuma shine littafin sa na farko, shi kuma wanda zamu fara kawo muku na mace ne kuma ta dade tana rubutu. Daga karshe muna godiya ta musamman ga wadanda suka bamu lokacinsu wajana binmu har muka gama wannan littafin. BISSALAM ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 48 (KARSHE) BANI NA KASHE TABA Na King Boy Isah Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.co An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9