Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
tace sato ni akayi. nan ta kwashe labarin duka ta fadawa aneesa. anne tayi mamaki dajin wannan labari. ta gyada kai tace tabb aradu kinyi gudun mutuwa. ko kin san daga nan zuwa bakin titi tafiyar wuni guda ce kuwa gamu wanda muka saba ma kenan. maryam ta bude baki tace wuni guda fa kika ce?. annee tace kwarai kuwa. maryam tace allah ne kawai ya cece ni daga sharin su. anne tace yanzu kinga dare yayi tashi mu tafi gida sai mu kwana tare. maryam tayi godiya ta tashi suka tafi.************** acan kuwa gidan kawu, kawu ne yake cewa wai ni shin da ake cewa deeny yayi kisan kai wa ya kashe?. hawaye ne suka biyu ta kan fuskar maman deeny sannan tace halima aka gani a motar shi sannan gawar halima budurwar aka samu a cikin motarsa nan ta kara fashewa da kuka. maman aliyu ce ke rarashin ta tace kiyi hakuri yanzu tashi mu tafi gidan br fadila din dakyar aka samu tayi shiru ita dai abun ya mata yawa ba maryam ba zaharadeen din ta tasa mayafi suka fita suka tsaida nafen sai gidan br fadila. sunyi sa'a tana gida kuwa da yake ba wani aiki suna isa ta tare su hannun bibiyu tasa mai aiki ta kawo musu abinci da ruwa da lemo haka kuwa aka kawo musu abinci aka girke a gaban su ga lemoka kala kala. su duk hankalin su ba'a akan abince yake ba su brfadila suke su ta fito su mata bayani kawai. can after 5mnt sai gata ta fito daga daki fuskar ta cike da murmushi tace a su maman deeny manya ba'a ko ganin ku yanzu yaushe rabo mu hadu. maman deeny kuwa murmushi ta nema ta rasa duk batada sukuni. tace ai kune manya bakwa ko neman mu. kallo daya brfadila tawa maman deeny ta fahimci ba lafiya ba. taga duk ta wani canza. tace maman deeny lafiya kuwa. haba sai hawaye kamar jira suke dama nan ta kwashe labarin duka ta fada wa barrist fadila sannan tace yanzu haka sunce gobe gobe za'a shiga kotu saboda baban halima ya kai kara. brfadila wani a jiyar zuciya ta saki sannan tace tabdi babbar magana. tace yanzu bari in shirya inje mu gana da deeny inji kan lamarin ankama deeny ai bamuga ta zama ba. maman deeny ta dan share hawaye sannan ta kalla brfadila tace yanzu saiki fada mana abunda zamu kawo dan allah ki ceci yaran nan nasan bazai iya kisan kai ba kuma shike daukar dawai niyar mu yanzu in bashi ya zamu yi gashi maryam din ma bamu san inda tayi ba. cikin sauri fadila ta dago kai ta dafe kirji tace maryam ta bata. maman aliyu ce ta bata amsa tace kwarai kuwa tun jiya data fita islamiya bata dawo ba har yanzu. maman deeny kuka take sosai. fadila ta kalle su cike da tausayawa ta taso daga kujerar ta ta dawo kusa da maman deeny ta rike hannun maman deeny sannan tace. ki kwantar da hankalin ki isha'alahu zamuyi nasara kuma kibar maganar kudi deeny ai dana ne sannan ta kara dacewa in allah yayarda deeny zai fito ki bar komai a hannun na yanzu zanje na sama deeny. maman deeny da maman aliyu godiya suke kamar me sun rasa kalan godiyar da zasu mata ma. tace ba komai muje driver ya kai ku idan ya dawo sannan na shirya sai mu wuce da shi station wajan deeny………… 08096831009 →BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng← PART8 na bigboy isah salama tayi ya amsa kanshi a kasa yanata faman zubarda hawaye duk wanda yaga deeny a wannan halin dole ya tausaya masa sbd tsananin duka da yasha. takare mai kallo sannan ta sama waje ta zauna tace sannu deeny da kyar ya dago kai ya kalle ta yace yauwa sannu sannan tace sunana br fadila nice lauyan ka mai kare ka ina san sannan wasu bayanai game da abunda ake zargin ka da shi da fatan ka shirya?. shidai kawai ido ya zura mata sannan ya daga kai alamun eh. nan sukayi yan maganganun su tana tambayar sa yana bata amsa. daga karshe tace zamuyi nasara isha allahu kafin nan ina so in sanar da kai cewa karka yi magana biyu a kotu dan hakan zai iya jawo mana matsala yace toh sukayi sallama ta tashi ta fice. ***** alhj sunusi kuwa wani kwararan lauya ya nema ana ce dashi barristr bashir ya biya shi kudi har 500,000naira da yake shi ya kasan ce mai kudi ne kudin sa kuwa sanadin wani yayan shi ya,same su wani compny da yayan ya bar mishi sunan yayan nashi alhaji bashir matar shi daya saratu. da daya allah ya basu sunan yaran nasu yazeed yaran nasu yana jida kudin uban sa shi kuma uban ya sakar mai duk dukiyar sa a cewar shi shi zai gaje shi ay hajj saratu taita fada idan taga yanda alhj ke sakar wa dan nashi kudi. ******* wata babbar kotu nagani a cike makil da yan kallo da wanda aka bukaci ganin su. kotu tayi shiru. alkali kawai ake jira ba'a jima ba saiga shi ya shigo ai kuwa duk jama'a gaba daya aka mike alkali ya nufi set din sa ya zauna .an fito da zaharadeen cikin ankwa duk wanda ya kalle sa saiya tausaya mai alkali yace assalamu alaikum warahmatul lahi wabarakatuho. duk jama'a suka amsa sannan alkali yaci "court clerk call the case" Court yafara bayaninsa "In the case of murder between zaharadeen kabir and alhj sunusi. yaci gaba da bayanin sa muna bukatar lauyoyi su gabatar muna da kansu. ya koma ya zauna. my name is barrister bashir lauyan mai kara shima ya koma ya,zauna.fadilat ta mike my name is barrister fadila mai kare wanda ake tuguma. sai duk kotu tayi tsit har yan wajan ma kowa yayi shiru. babu wanda bai hallara a wajan ba.maman deeny.amina maman aliyu.alhj sunusi da matar sa. da wanda yaga gawar da duk sauran jama'a dai duk sun halara har da baban yazeed da maman sa duk………… 08096831009 →BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng←PART 9 na bigboy isah br bashir ya nema alfarma ga kotu domin ya fara tambayoyin sa. kotu tamai izini. sannan yaje gaban deeny. yace zanso sanin cikeken sunan ka. ya dago kai yace. sunana zaharadeen kabir. br bashir yace. miye hadinka da halima. deeny yace budurwa tace. duk jama'a suka dago kai suka kurawa deeny ido.kai ka kashe halima?.deeny yace BANI NA KASHE TABA. br yace an tabbatar da anga gawar halima a motar ka muna da sheda ba daya ba ma. yace haka ne. br yayi ajiyar zuciya. sannan yace to waya kashe ta?. deeny yace nima ban sani ba.bashir yace zaka iya fada mana dalilin ka na cewa bakai ka kashe taba kuma bayan antabatar kai kazo har gida ka dauke ta?. deeny ya fara bada labari. ranar washe garin ranar da dare mu kayi waya da halima take cemin dan allah gobe inzo mu tafi yawan shakatawa ita kafin hutun su ya kare tana so ta dan ga gari. da har naki amincewa nace ni ba inda zani yawan shakatawa ay na masu kudine muda muke nema ina mukaga samun damar zuwa wani shakatawa. ai kuwa nan ta fashe da kukan shagwaba wai ita wllh sai yazo ya dauke ta.dai dai nan hjj hauwa ta shigo dakin halima ta isketa da dan kukan ta hada hawaye. da sauri ta karasa tace halima lafiya kuwa.tace momy lafiya lau ba komai. hjj hauwa tace ban yarda ba sai kin fada min. alokaci shi deeny kuwa yana saurarn su. sai halima tayi sauri ta katse call din ta kamo wani video fassara tace momy fin ne nake kallo shine abun ya bani tausayi nake hawaye. momy dariya tayi tare da cewa allah ya shirye ki. sannan ta kama hanya ta fita. tana fita daga dakin. halima ta sake kiran deeny duka daya ya daga wayar kamar dama jira yake. yana dagawa yace kin gama kukan. tace pls dan allah kayi hakuri kazo mu fita gobe. yace kwantar da hankalin ki gimbiyata zanzo isha'alahu ai kuwa dan murna hada tsale sannan tace gobe karfe 10 ka shirya ko anguwar mu sannan baban na ya fita nasan yada zanwa momy ta barni in fita kaji yace to.allah ya kaimu haka taita jin dadi. har allah allah take gari ya waye. ai kuwa gari na waye wa ta yi sallah ta fito farllo sukayi breek sannan momy ta dakowa dady jakar sa zai fita dan har ya makara yanzu karfe 9:30 suka raka shi har mota halima ce rike da jakar sai da ya shiga mota sannan ta durkusa ta mika mai ya amsa yace baby allah ya miki albarka tace amin sannan ya juya yawa maman baby bye bye driver yaja shi suka fice yana su kuma suka koma farllo suna kallo ita kuma halima duk tabi ta damu ta rasa wace karya zatayi ga waya a hannun ta sai jujuyawa take. hjj hauwa ta fahimce ta tace ke me yake damunki ne naga duk kin changer fuska. halima tace momy mun dan sama sabani ne da deeny wai shine yace inje yana kofa zai bani.hakuri. momy tayi murmushi tace kude yaran nan bakwa gajiya da rikici ko shiyasa naga jiya kina hawaye. ta sadda kanta kasa. momy tace hmm shiyasa naga bai shigo ba kenan yasan yau ba a shirye kuke ba ay saiki tashi ki fita. halima a,zuciyar ta cike da farin ciki a fuska ko kamar bata so. ta tashi ta shiga dakin ta tayi yar kulleyar ta sannan ta chanza kaya. wata atamfa ta saka mai kyau green & water riga da siket sun mata cip cip sun kara fito da kyan ta ta dau gyalan ta fari ta yafa sannan taje jikin mirror ta kalla kanta tayi murmushi sannan ta fice a dakin ………… mu hadu a whatsapp→ 08096831009 Group bigboy on-line 17.04 12:52 →BANI NA KASHE TA BA← PART 10 na bigboy isah ta fito tace momy na tafi momy tace to a dawo lafiya kuma kice ina gaida shi tunda shi yau bazai shigo ya gaida mu ba. tace ameen momy zai ji. ta fita da murnan ta ta nufi inda yake a mota ta bude motar ta shiga sannan tayi ajiyar zuciya tace to sai motafi ko ina zamu fara zuwa. wani kalan kallo ya mata mai cike da so da kauna. yace saida kika wahalar dani na zo sai jira nake kinki fitowa. ta mararai raice tace haba sweethr kasan irin faman da nasha kafin in samu a barni na fito kuwa sai da nayi karya fa. gaba daya suka kwashe da dariya. sannan yaja motar yayi gaba suna tafiya suna ta zuba hirar su ta soyayya tana tamai shagwaba kala kala tace wannan yatsaya ya saya tace wancan haka dai suke ta tafiya suna soyayyar su abun gwanin ban sha'awa. sune har wajan la'asar yace tabari tunda ga masalaci a kusa kuma ankira sallah to tabari yayi sallah tunda kinga ko sallahr azahar banyi ba. tace to nifa nima ay banyi ba. yace ai ku mata ne kun saba dama idan ana biki sallar huni guda duk kuke hadawa lol. ta jefo mai bisket din hannun sa ya kare da hannun sa kuma ya fita da gudu yana dariya itama dariyar take. ita kadai a mota shi kuma ya nufi masalaci ya dauki buta ya zuba ruwa ya nufi ban daki. kotu dai tayi tsit deeny kadai ake ji sai zuba labari yake nima ina gefe ina sauraran sa. yace bayan na gama sallah ne na nufi mota ina zuwa na iske halima a kwance ni a tunani na barci take haka nayi murmushi nace yarinya ai gobe bazaki kara cewa a taho yawan shakatawa ba gakinan duk kin gaji har kinyi barcin dole. ni kuwa nace deeny ka kashe yarinya kace barci take ko lol. yaci gaba da jan motar shi bai tsaya ko inaba sai gidan su halima yana zuwa ya tsaya a kofa yakama dan babuga ta yana cewa my luv tashi mun iso my heart ki tashi ko duk gajiyar ce haka. yayi yayi yaga ko motsi taki yi. nan fa duk ya rikice ya shiga gida ya kira mai gadi wai yazo ya tada mai ita ta shiga gida. ni duk a sannan ban fahimci halima mutuwa tayi ba inji deeny. mai gadi yazo yace ban gane in taya ka tadata ba mai ya faru. deeny yace nidai nayi nayi taki tashi kuma daga yin barci. mai gadi ya matsa kusa da ita ya kama hannun ta ya daga ya sake shi yaji hannun ya dawo kamar dai yadda gawa take. shima duk bai gamsu ba tukun ya bude idan halima yaga fari fat ai kuwa dama tsoho ne da gudu ya ban kade deeny ya nufi cikin gida.deeny har zai bishi sai yaji mai gadi na cewa hajiya ya kashe miki yarinya………… mu hadu a whatsapp→ 08096831009 Group bigboy on-line 18.04 18:45 →BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng← PART 11 na bigboy isah deeny da gudu yayi baya duk jikin sa na rawa ya fizgi mota yayi ciki gudu yake ba kaf kaftawa yace ban tsaya ba nabi wani barji a tunani na duk wajan daji ne ba mutane. yace haka na je na tsaya da mota na juya ina ta kallan halima ina kuka a zuciya ina cewa wai yanzu halima ta ta mutu kenan. nan hawaye suka fara zarya a fuskata na fito na dauki halima. wai ni a nufina binne ta zanyi idan na koma gida koma me za'ayi sai ayi. ina tafiya inata sake sake na dan yi nisa da mota ta nan na ajiye halima inata kuka ina jijigata ina cewa ki tashi ki tashi. shiru nine har magariba ina wajan nan fa na gaji sai kawai na fara haka rami da yake wajan ba tauri nayi rami mai dan tsawo nan kuma sai na tsaya ina tunani toh in binne ta anan ko kuma in maida ta gida a mata sallah a sa mata lukafani. inata saka wancan kunce wancan. sai ji nayi ance waye nan ban ankara ba sai ganin kibiya nayi a gaba na ta caki kasa ina juyawa naga wani saurayi ne ya durfafo ni hannun shi rike da kwari da gwafa. ashe wai nan garkar rogwan sune wai yana ce ni barawan rogo ne lol. da gudu na bar waje nayi wajan motata sai na danyi gudu kadan sai na tsaya a zuciyata nace gwara in tsaya in cemai yar uwata ce ta mutu shine zan binne ta. wata zuciyar kuma tace wannan da yake fada a kan rogo baya ko tsayawa a mai bayani toh ina zai tsaya sauraro na.yana cikin hakan sai ganin mutum yayi a guje ya nufo shi yana barwo aradu barawo ne. ni kuma sai nake cewa ka tsaya ka saurare ni. haba ba sai ji nayi ya sako wata ki biyar ba badan na guce ba da sai ta same ni. da gudu na fada mota naja ta da gudu ya biyo ni. yana har bi yana jifa har dai na samu na tsere. can naje bakin titi na ajiye motar sannan na taho a kasa sai dai ina fargaba amma a haka nace kai gwara inje duk abunda zai same ni ya same ni amma sai na dako halimata na nufi garkar na dan bi a hankali na leka nayi zatan yana nan. amma sai naga wayam tun a nesa naji gabani yana faduwa da na hangi wajan da na ajiye halimata ba komai a hajan tun a nesa na dora hannuwa a kai ina isa wajan kuma na iske ba komai a wajan sai dai ga dan ramin da nayi nan. haka nata ratsa daji ina neman saurayin nan ko sama ko kasa na nemeshi na rasa. bana jin kukan komai a wajan sai kukan tsintsaye da na dabobi da yake dare ne rananr dai haka nata yawo ina kuka kamar mahaukaci ina tunanin shikenan na rabu da masoyiyata abar kaunata hasken zuciyata bugwan zuciyata. na fashe da kuka a ranar duk wani tsoro ya fita a raina bana jin ko tsoran duhun dajin nan haka na hakura na koma naja mota na inata tunane tunane. na nufi gida………… mu hadu a whatsapp→ 08096831009 Group . bigboy on-line 19.04 09:54 →BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng←PART 12 na bigboy isah TUN DAGA BAKIN KOFA naji gabana yana faduwa duk tsoran maman mu nake. sai kuma nayi tunanin ay bata san komai ba. kawai na shiga gida na nufi daki na na kwanta. banyi barci ba har safe da asuba nayi sallah a daki dumin bazan iya fita ba duk na gaji saboda yawan da nasha jiya a daji ina gama sallah na nufi dakin momy ai kuwa ina isa kamar ance mata gani nan sai saukar mari naji tass tace ina kakai musu yarinya nasan bazaka iya kisa ba amma ina kakai.musu yarinya.nace mama wllh BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng momy ta zaroo ido dagaske ta mutu. ai kuwa ta shake min wuya tana cewa. me yasa kakashe ta me tama kane da zaka kashe musu ita banyi zatan zaka iya kisan kaiba zaharaddin sannan ta sake ni daga shake min wuya da tayi idanuna duk sun cika da kwala. momy ta koma gefe tana kuka. a hankali na durkusa nace momy wllh BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng ana nan yan anguwa suka zo zasu toya mu sannan police suka kore su aka kamoni akayo nan dani. ya mai girma mai shari'a wllh gaskiyar abun da na sani kenan.mustapah ne yace yallabai wannan ba abun kamawa bane idan kayi la'akari da maganganun sa akwai karya a ciki sannan yace na gode ya mai shari'a. sannan alkali bayan yagama yan rubuce rubucen shi yayi aziyar zuciya sannan yace barrister fadila fa tana da tambaya. tamike tace akwai ya mai shara'a. tace ina rokon kotu data bani izini in kira hjjy karima maman deeny.alkali yace an baki izini. ana bukatar ganin hjj karima maman deeny. ta taso taje ta tsaya a inda aka tana.br fadila tace da farko muna bukatar jin sunan ki dana mijin ki.ta goge dan hawayan dake fuskar ta domin ta tausayawa yaran nata. tace sunana karima mata ga alh kabir . fadila tace wannan fa danki ne kokuwa dan riko ne. maman deeny tace dana na cikina. fadila tace maganar da ya fadi duk gaskiya ne haka sun faru. maman deeny tace duk abun da ya fada dangane da ni haka ne. tun safe ko karin kirki baiyi ba yace min zashi gidan su halima da yake ni nasan tsakanin su shiyasa ban tugume shi mai zaiyi a can din ba. haka naita jiran shi amma shiru bai dawo ba kanwar shi ma kuma haka da ta dawo daga school ta takura min da tambaya ina yaya deeny sai dai nace ya tafi gidan su halima. da yake itama halimar kawar ta ce.har tayi shiri makarantar islamiya amma deeny bai dawo ba abun ya daure mana kai gaba daya. yaran da yake cin abincin rana a sai gashi har 3:30 bai dawo ba.to bayan fitar maryam ne ba'a jima ba sai ga mai gadin gidan su halima da yan sanda wai sun zo kama deeny anan ne suke shaida min wai ya kashe halima. na dafe kirji sakamakon hani mumanan faduwar gaba da naji. sannan na fada musu rabona da shi. amma basu hakura ba suna ce boye shi nayi duk saida suka har gitsa gida suka shiga ko ina amma basu samai ba. suna gidan tun lokacin har bayan isha'i amma bai dawo ba. ni kuwa abun duniya ya isheni dan a lokacin har jini na ya hau. saboda yada abun suka min biyu ga deeny ana zargin shi da kisan kai sannan ga maryam bata dawo ba. hakan yasa na shiga daki na kwanta zazabi ya rufe ni ban tashi ba sai da safe……………… 08096831009 →BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng← PART 13 na bigboy isah barrister fadila. tace mun gode. zaki iya komawa mazaunin ki. sannan br fadila tasa akata kira mutane daya bayan daya. daga kan maman halima har mai gadi duk wanda labarin deeny ya shafa. sai yace eh maganar da ya fada gaskiya ce. barrister fadila. tace ina rokon wannan kotun mai adalci data rike labarin wannan bawan allah karta dauke su a karya. bayan ga shaidu mun samu kuma duk sun tabbatar da zancen sa haka ne. sannan ina rokon kotu da ta tura jami'a tsaro dumin su tafi da deeny ya kaisu har wannan wajan da yayi rami dan tabbatar da gaskyar sa. na gode ya mai shari'a. deeny kuwa duk ya tsure dumin a lokacin bai san ma inda ya tunkara ba balle ya kai wanda za'a hada shi da su yanzu. turkash. alkali yace munji kuma mun yarda da zan can ki barrister fadila gobe za'a hada shi da jami'an tsaro dumin su je su bincika dan tabatar da gaskiyar sa sannan mun dage wannan zama har zuwa jibi. alkali ya buga gudumarsa…………kotu ta watse >>>>> cigaban labrin deeny> lokacin da dan fulani ya dawo wajan sai ya tarar da mutum a kwance kuma ga duk kan alamu wancan da ya kora binne wannan din yazo yi. adan tsorace ya nufi wajan a hankali ya juyo ta sai yaga ashe macece ma daya kula sosai sai yaga da sauran rai da sauri ya sabe ta ya nufi gida da zuwa kuwa gwaggo ta tarye shi suka kamata suka ajiye a kan wani gadan kara ita kuwa har yanzu bata dawo hayyacin ta ba. nan gwaggo take tambayar isah ina ka samu wannan yarinyar gata kamar yar bunni. tana dan jujuyata.isah yakwashe duk labarin abunda ya faru ya fadawa gwaggo gwaggo tace to hike nan allah hukumusa'a. ya tashi yace gwaggo a kula da shi ni na komai dawa. da yabi kwari da gwafan shi yayi ciki. da sasafe halima a hankali ta bude ido ta ganta cikin bukka tayi mamaki sosai. a hankali ta taso jikin ta ba kwari. tana tagal tagal. gwaggo ta taho da gudu ta tare ta daga faduwar da zatayi. ita kuma halima deeny take ta kira tana ina deeny na. deeny nan inane. duk ta wani rikice. gwaggo tace kiyi hakuri mana ki saurare ni nan ba garin ku bane. nan kina cikin rugga ne. halima ta zaro ido rugga kuma. gwaggo tace tabbas kuwa. jika na ne ya tsunto ki jiya a can garkar su wani na kokarin binne ki. halima tayi ajiyar zuciya tace yanzu ko wane hali mamana da abbana suke cikin. hawaye kawai suka shararo mata. gwaggo tace jikin ki ba kware muje ki zauna. ai kuwa haka gwaggo ta taimaka mata a hankali taje ta zauna…………> mu hadu a https://m.facebook.com/ groups/1232550283531628. whatsapp→ 08096831009 Group bigboy on-line 21.04 11:05 →BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng← PART 14 N@ BIGBOY isah acan kuwa bangaran maryam tashe sukayi suka nufi gidan su anne. suna shiga suka iske iyayan anne a tsakar gida suna hutawa suna yar hirar su. suka karasa maryam ta gaishe su suka amsa cikin fara'ar su sannan maman anne tace aneesat wannan fa daga ina haka kamar yar bunni. anne tace yar bunni ce mana yan fashi ne suka sato ta,zasu kashe ta shine ta tsero har allah ya kawo ta nan kuma a dandali muka hadu tataima ka mana ta nuna mana maciji zai sare mu. shine har nake tambayar ta gidan suea tazo sai ta bani lbr shine nace bari muzo nan gidan ta kwana kafin akaita garin su.abban anne yayi murmushi yace allah ya miki albarka kinga dadin zaman birni kenan yaci gaba da cewa ni naso in sama kudi ma a wannan shekarar mu koma birnin nan mu duka har gwaggo da yayan ki ya kalle anne. maman anne tace wllh malam ba inda zaka halan kaje ka likewa wata kace auranta zakayi ko wllh baza mu ba toh. su anne gaba daya suka kwashe da dariya har maryam dariyar take. ai kuwa sai gani nayi. maman anne ta tashi ta shiga bukar su. nan anne da maryam da baban maryam sukaita hirar su. maryam kuwa ta saki jiki.baban anne yace aneesat tashi ku tafi daki kusha fura sai ku kwana daki daya keda bakuwar taki ko. anne tace to abba. suka shiga dakin daga wani gadan kara bazai ci mutum uku ba na mutum biyu ne ko katifa babu sai tabarmar da aka shin fida da kuma barguna. da yake anne mai tsafta ce dakin yar bukkar tata tsaf tsaf da ita. gefe kuma ga yar a kwatin ta. hada nunawa maryam wai yayan tane ya sayo mata. kuma duk ruggar nan babu mai kalan ta. maryam kuwa me zatayi banda dariya. taga an dakko wata tsohuwar akwati wai nan abu mai daraja ne a garin. nan dai suka gama shirman su suka gaji da hira suka kwanta. ai kuwa ranar da dare maryam tasha jifga.daga anjima sai dai taji an laf to mata kafa ta janye ana jimawa ta kara jin an wullo mata. maryam tace na shiga uku wannan kamar mage dai wannan ai mijin ki ya shiga uku. a haka dai har asuba tayi. maryam ta tashi ta fito ta dauki buta dama annee ta nuna mata bandaki. ta fito tayi alwala. sannan taje tayi sallah tayi adda'au. nan fa ta fara tunanin maman ta da kuma yaya deenyta. tana cikin wannan tunanin taji matsin anne ta farka ta murge ido taga maryam a kan sallaya. tana kallan ta. tace ke kuma haka ake a garin ku kita shi kiki tada mutane ko. maryam tace ke tada ki ai sai jirgi ko kuma azo da bulala. anne tace to miyasa baki dakko bulalar ba. maryam tace ba komai ai akwai gobe. da sauri anne tace toh gobe me zakiyi?. tace ahah bulala zan samo mana saboda tada ki ba kince mi isa ban samo bulala ba. anne tace wasa nake miki kinji yar kawata. ai wannan lalausan jikin nawa bazai dauki bulala ba. gaba daya suka kwashe da dariya. maryam tace. katashi ka nema ruwa ka yi alwala kazo kayi sallah. anne tace kai abun hada tsokala ai dai allahn da yasa ni maganar fulanin ma bata kama baki na ba.kinsan mu a burni muka girma. maryam tace wai ina wannan yayan naki yake ne. sai kira kike yayan ki yayan ki. anne tace yayana yana gidan gwaggo gwaggo ta kwace mana shi ay. tace bari dai in tashi wannan hirar ba karewa zata yi ba. ta tashi taje tayi alwala. ta dawo ta iske maryam tayi tagumi sai tunani take. anne tace maryam maryam.firgigit ta dawo hayaccin ta daga tunanin da take. anne tace kinga indai gida ne ki kwantar da hankalin ki. yanzu da muka gaisa da mamana tace gobe zata bawa yaya isah kudin mashin

Chapter 2 of 9