Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
can kan wata kujera ya hakimce ga wani dining table a gaban sa duk kujeru ne a zagaye da table din, sannan sai wata kujerar mai kama da tasa a kusa dashi, kai tsaye yazeed ya wuce dayar kujerar ya zauna. Sannan ne suma manyan cikin kungiyar sun zo duk an zazauna kowa da plate a gaban sa, abun dake cikine zaisa idan ka kalla sau daya baza ka kara ba, sasan jikin mutum ne kala kala a ko wane plate ba kyan gani, “welcome my son” inji tsohon juyawa yayi ya kalleshi hade da cewa :thank you” sannan tsohon ya tashi yana wasu gwalan gwalantun tsafinsa sannan yace muna maraba da babban yaro na kuma shugaba magajin wannan kungiya wato yazeed (bad man) ya dora da cewa kun sani cewa a cikin mu ko jikokin dan kungiya bazasu yi talauci ba, bazasu taba sanin miye babu ba kuma baza mu yi sasauci ba ga duk wanda ya bujirewa umarnin mu, sannan ku sani dole ku kula da dokokin kungiya sannan ya juya ga yazeed yace dodon mu yana bukatar jini kuma daga gareka wato a cikin dangin ka, dole ka bamu jininn ka domin tun farko kayi alkawari cewa a wannan shekarar ne zaka bayar. Chan kuma cikin dakin ajiya wato inda aka saka su deeni sun matukar gala baita yunwa ma ta ishe su gashi anki kawo musu abinci, wadannan yan sandan biyu sun sha kuka kamar ransu zai fita sannan suka hakura sukayi shiru, domin ba maganin da kukan ke yi musu ba. Deeni ne ya tashi ya nufi kofar fita sakamakwon magana da yake ji sama sama, lekawa yayi ta wata yar kofa, da sauri ya dago ya dan kama baki alamun yana so ya tuna wani abu, a ina yasan waccan fuskar kamar ya taba ganin ta, kunne ya kafa yana saurare me suke cewa.. .. Yazeed ne ya mike yayi gyaran murya, “a matsayina na mataimakin shugaban mu kuma babana gashi a zaune ya nuna wannan tsohon. Inaso in muku bayani wato dan takaitacan tarihina domin kusan cewa a harkar nan ba imani idan kanada imani bazaka ci muriyar mu ba... Ni dai na kasance fuska biyu ne domin idan ka ganni a gari bazaka taba cewa ni mugu bane, yanda nake al'amura na sakin fuska, kyauta da sauran halaye masu kyau. Ina so ku sani yan matan da na kawo nan aka hallaka sun fi a kirga kuma duk a matsayin saurayi nake gare su, abinda baku sani ba shine duka ba wacce mahaifanta suka sanni, hatta unguwa sai naje nesa da tamu sannan nake yin budurwa, ku sani cewa yan matan yanzu ba ruwansu da SOYAYYAR GASKIYA kawai sudai abin hannunka suke bukata, laifin iyaye kuwa da suke barin yaran su wato mata suna fitowa zance alhalin basu san saurayin ba. Ya danyi shiru tukun yace karfa ku zata wannan nasiha ce, no ni da kuke gani ba alamun imani ko tausayi tare dani, ni na hallaka haleema ya fada tare da kawarta maryam sakamakwan tona min asiri da suka so suyi..... Gaban deeni ne yayi mumunar faduwa sai yanzu ya gane yazeed din sakamakwon sau daya ya taba ganin sa, ya dafe kai da yake sara mai da karfi, “yanzu yana nufin ya hallaka min maryam dina, no no no, haleema na da gaske kin mutu kai ban yarda ba karya kake karya kake” ganin zasuji yayi saurin control din kansa ya natsu sai hawaye sharrrr! Can ya sake kafa kunne dan jin me yazeed ke cewa... Sannan ina so in fadawa kungiya cewa lallai ni mai cika alkawari ne dan haka naba kungiya babana (mahaifina) ranar Friday zan kawo shi domin baya garin nan amma tabbas nasan yanda zanyi in kawo shi, wannan babbar kyauta ce nawa kungiya... Gaba daya suka fara tafi......................... Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da bakwai dan jin cigaba ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 26 Share This:Shi kuwa deeni gaban sa ne yaci gaba da faduwa wato kawun haleema kenan aka bawa dodo, hawaye keta kwaranya a idaniyar deeni, wai an kashe haleeman shi da kuma kanwarshi shi maryam da yake matukar ji da ita, bashida burin da ya wuce ya farantawa ummansa da kuma yar kanwarsa wato maryam tunda babansu baya raye, wani xazzabi ne ya rufe deeni. Maryam ce zaune kan wani gado na kara ta dafe kumatu wato tayi tagumi, tunanin ummanta kawai take, wasu yan siriran hawaye ne suka kwaranyo, haka haleema ma da take kwance kwakwalwarta sai juyawa take cike da tunani iri iri tama rasa wanne zatayi shin waye mai neman hallaka mu, shin wane hali deeni na ke ciki, shin umma da abba ya zasu ji na rashina bayan basa san yin nesa dani ko kadan, idanun ta cike da kwalla ta tashi zaune ganin maryam a gefan gado ta zuba uban tagumi, “maryam maryam” inji haleema tunanin me kike. Tuni maryam ta dago tare da sa zani tana goge hawayan fuskarta, nan haleema ta fahimta cewa duk ashe daya ne halin da suke ciki. Ta dafa kafadar ta haba my sis ki saka dangana a zuciyar ki mana mu barwa Allah komai shi zai yi mana maganin wannan al'amari ba kuka ne abunyi ba... Aneesat ce ta shigo, ganin su a wannan yanayi ta fahimta tunanin gida suke yi, duk da sun so su boye wa anne amma saida ta fahimta, “haba yan uwana, nan fa kamar gidan ku ne ku kwantar da hankalin ku, dama yanzu daga wajan maman mu nake shawara muke yi yanda za'a maida ku gida, ku kwantar da hankalin ku”... Tabbas sunji dadi sosai da jin kalaman anne gaba daya suka ce “hmm anne kenan haba ba komai amma gaskiya muna so muga iyayan mu domin basu san ko wane hali muke ciki ba, kinga in sun gammu hankalin su zai kwanta. Yaro ya shigo da salamar sa “anne wai ana kiran maryam, bata tsaya ko jin waye ba tace “je kace gata nan”, domin anne tuni ta kyaro su wato tana lura da abunda ke faruwa tsakanin maryam da kuma isa. Ya zaki ce gani nan bayan baki san kowa ke sallama ba, shin waima cikin gari nan waya san ni da har zai aiko kuma wai ace maryam tazo ma. Anne tayi murmushi ai sai kije ki gano mana. cikin zolaya haleema tace “kanwar mu ah gaskiya kinzo kauyan nan a sa'a kinga shikenan sai mu barki anan”. Suka sa dariya gaba daya. Bari inga ko waye tunda kun matsa ta ce, anne ara min hijab dinki. Ya mata daidai kuwa kamar dama nata ne.. A tsaye ta iske shi ya harde kafafu da kara da ya rike a hannun hagu yana wasa da shi, hannun daman kuma yasa shi cikin aljihun wando. “Assalamu alaika” ta fada, wani irin sauti mai dadi yaji a zuciyarsa yace dama haka muryar yarinyar nan take ashe. Amin wa'alaiki Salam warahmatul lahi ta’alah wa barakatuhu: sanda ya cika amsa sallamar cif cif. Gefe daya ta samu ta tsaya nesa da shi kadan, ita kam ta kasa dagowa da kanta domin wannan ne karo na farko nata na tsayawa da wani da namiji .. Maryam kenan sarkin kunya shin ko dai kema yar fulani ce kamar mu, amma ai ke kunyar taki tayi yawa ma. Murmushi kawai tayi domin ta gane yaya Isah ne shi isa taki ma dago kanta domin tsoran abinda take ji in ta hada ido da shi wato faduwar gaba. Ki daure ki dago kanki, ki kalle ni ya fada yayin da ya dan kara matsowa kadan kusa da ita. A hankali ta dago kai “wow” dama haka wannan bawan allah yake da kyau, ashe duk ganin da nake mai zaije farauta ne, amma duk da haka yana da kyau saidai kayan da yasa sun kara fito da zallan kyawun sa wanda haka yasa ta kafe shi da ido shima dai abun ya daure mai kai ta tsaya sai kallan sa take... Um dama so nake in gaya miki…… Kuma sai yayi shiru, ka fada mana a zuciyarta ta fadi hakan, gani tayi ya kalle ta, tayi saurin sunkuyar da kai ashe yaji abinda tace... Maryam ba wani abu bane dama ina so in gaya miki ina sonki, ina kaunar ki, tunanin ki ya hanani sukuni ko ina naje bana jindadi in ban ganki a gunba, idan na rufe ido ke nake gani, nayi tunanin cire haka a zuciyata sakama kwan ni dan kauye ne ke yar birni ce kinga kuwa auran mu bazai yiwu ba amma dai yanda sanki ya addabi raina yasa ni dole in gaya miki ko naji dan sauki... Farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta hakika taji dadin kala man sa, wannan ne na farko da namiji ya taba cewa yana santa abinda ko da wasa ba'a taba gaya mata ba, kalmar so kenan yayin fadarta sai bakin ka ya fara bari duk jarumtakar ka, bama kamar karo na farko haka duk macen da aka furtawa a take a waje sai taji chanji, lalai so halitar Allah ne, juyawa kawai tayi da niyar tafiya ita duk kunya ta dabai baye ta.. “Maryam” tsayawa tayi chik, baki ban amsa ba zaki tafi, ki taimaki zuciyata karta fashe mana. Juyowa tayi ta sakar mai tattausan murmushi mai dauke da sako, saidai shi bai iya karanta iri kalaman din jikin murmushi ba, kawai cikin gida ta juya ta shige. Salam Alaikum masu bibiyar wannnan labari, muna baku hakuri sakamakon rashin kawo muku cigaban labarin har na tsahon wasu kwanaki, hakan ya biyo bayan wasu kalubale da muka fuskanta amma yanzu insha Allahu zamuci gaba daga inda muka tsaya. ************** A baya mun tsaya ne inda “Maryam” tsayawa tayi chik, baki ban amsa ba zaki tafi, ki taimaki zuciyata karta fashe mana. Juyowa tayi ta sakar mai tattausan murmushi mai dauke da sako, saidai shi bai iya karanta iri kalaman din jikin murmushi ba, kawai cikin gida ta juya ta shige. *************** Cikin rashin gamsuwa isah ya koma gida yana ta tunane tunane shin me yarinyar nan ke nufi, ai a so ba’a dole idan bata so na ba saita fada ba kawai a wuce gun, Isah ne shi kadai yana tafiya yana zancan zuci.... Maryam kuwa tana shiga dakin duk suka gyara zama wato haleema da anne wai sai ta fada musu waye yazo gunta, ai kuwa fa fur taki fada, sukayi sukayi anma tace kawai bata sanshi ba. Anne tace to ai nasan dole ya fada miki sunansa, to ya sunansa ai nasan ko wane saurayi a duk fadin garin nan. Bai fadi min suna ba... Suka hau dariya wai bata da gaskiya, haka dai sukai ta zolayar maryam wacce ita kuwa tunani ne duk ya addabe ta.. ************ “Ina kwana umma” “lfy lau aliyu” a cewar mamar tasa, sannan ya juya ga maman deeni suka gaisa.. Wai aliyu har yanzu ba batun ko daya daga cikin su ne? Wllh mama babu wani labari a cewar aliyu haka makarantar su maryam ma sun ce bata je ba ranar. Maman deeni ta yi shiru hawaye ne suka fara zarya a idanonta a bin tausayi, kanta ne ya fara sarawa da karfi dafe, kanta tayi tana inalillahi. Kwatsam sai gani sukayi ta fadi, da sauri sukayi kanta, a kidime suka kwasa sai asbiti akayi Emergency da ita, duk a gigice suke sun ma kasa zama da kyar aka lallashe su da cewa jinin tane ya hau yanzu tana bukatar hutu anjima zasu iya shiga domin ganin ta .... Bangaran yazeed kuwa ******************* Naman suka hau ci kallo daya zaka musu ka fahimci ba imani a tattare da su gaba daya yanda suke cin abinci da sassan dan adam a ciki amma su ko a kansu, tsohon cikin su ne yace gaskiya badman kayi mana asara kasan fa dodanmu yafi bukatar jinin yan mata amma ka bari su mugu suka kashe su. Dad ba haka bane a duk cikin yaran ba wanda su mugu suka samu damar kubutar da su, a inda suka iske su a nan suke sheqe su. Thats gud, Kasan fa Allah ne ya kawo mana dakwale har hudu police 3 da kuma wani 1 dan karamim cikin su. Dad kace naman police ne shi isa na ganshi da baki baki. Hahaha sukayi wata irin dariya tasu ta marasa imani wacce suka saba. Tashi muje ka gansu inji tsohon nan, Ya kalli wasu dake tsaye yace kuje ku kaiwa wadan can naman abinci mana, ko so kuke sai sun rame sun zama kashi ne. Su yazeed ne suka shiga dakin ajiya wato inda su deeni suke, kallan deeni yake kamar yasan shi saidai ya rasa a inane, gaba daya kan yazeed ya daure to shi a ina yasan wannan. Zuwa yayi gaban deeni ya tsuguna yana so ya tuna wani abu amma ya kasa kai kamar na sanka, denni kuwa kallan sa kawai yake, “a ina?” Inji deeni. Shiru kawai yazeed yayi dai dai lokacin ne aka shigo musu da abinci, plate uku ne aka bawa deeni daya suma sauran aka jiye musu nasu, kamar jira suke dama suka fara aika abincin nan, deeni ne ya yi kokarin da katar da su “kudaina cin abincin nan” ya fada. Wata irin harara dan sandan ya dakawa deeni alamun ya kyale su, deeni kuwa da ya karewa abincin kallo tsaff sai ya ga akwai nama mutum da sauri yasa kafa ya hankadar da abincin ya zube .. ************* Assalamu alaikum. Suka amsa mai gaba ki daya yan majalisar, Zagayawa yayi bangaran abokinsa da wato salmanu ya zauna kan dan guntun iccan da yake a zaune, abokina waya tabo ka ne naga duk ka wani canja fuska, ya tambayi isah. hmm abokina zo muja gefe ina san magana dakai, salmanu ba gardama kuwa ya tashi suka koma gefe, isah ya kwashe duk abunda ya faru tsakanin sa da maryam tun daga farko har karshe, yace to amma naga alamun yarinyar ba sona take ba jifa yanda na dame ka a kanta ko da yaushe tunanina gareta ne amma kaga fa abinda ta saka min da shi kenan. Dariya salmanu ya kyakyace da ita harda su rike ciki, “bana san haka fa kai wato nazo na fadama damuwata, wato abinda zaka min kenan ko kasan fa na tsani dariya” isah ne ke fadan haka. Salmanu ya dafa kafadar sa yace kwantar da hankainka abokina nasan baka fahimta bane kawai, amma a hakikanin gaskiya ina tayaka murna abokina domin na tabbata ta amshi soyayyarka. Wani irin dadi yaji baisan ma lokacin da ya rungume salmanu ba dan tsabar murna, “ka tabbata”, eh mana domin kuwa murmushi ta shine tabbacin haka sannan ba yanda za'ayi in mace bata sanka ta maka murmushi a lokacin da ka furta mata so saidai ma ta bata rai. “Yaya isah wai ance in kira ka”, Wani yaro ne dan makwabtan su aka aiko, “Wake kirana” isah ya tambayi yaran, “abban ku” inji yaron “jeka ce gani nan zuwa” yauwa salmanu ina godiya da jin wannan gagarumin albishir naka sannan yanzu taya zan gane haka gaskiya ne idan naje gidan. Kawai abinda zakayi shine ka mata murmushi in kuka hada ido sai kaga kalan martanin da zata dawo maka dashi inji salmanu. Nan sukayi bankwana, Isah ya nufi gidan nasu. Assalami alaikum ya maimaita har sau uku amma shiru kake ji gidan kamar ba mutane. Saida ya zo wucewa ta matattakala sannan ya fahimci akwai mutum a falo. Ta dora hannuwa biyu, Haba hajara miye haka ne yasa zaki dorawa kanki damuwa da yawa bayan haka allah ya kadarta, haka yayi niyya ya faru gare mu, kisawa ranki dangana mana. Sai lokacin ma tayi farat ta dago alhaji ashe ka dawo, tana goge hawayan fuskar ta. Haba maman deeni yanzu dama duk wannan kugin da nake faman yi bakya jini hakikanin gaskiya ta bashi tausayi domin yanda take ji da yar ta, rabuwa da ita dole yasa ta cikin rudu. Rungumota yayi a jikinsa yana share mata hawaye kamar yarinya, Ita kuwa sai shesheka take tana cewa yanzu shikenan haleema na yanzu shikenan. Ta kara kakame alhaji tare da kuka mai tsuma rai, shi kuwa yaci gaba da lallaban ta yana lallashin ta........... Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da Tara dan jin cigaba ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 28 Share This:Salam Alaikum masu bibiyar wannnan labari, muna baku hakuri sakamakon rashin kawo muku cigaban labarin har na tsahon wasu kwanaki, hakan ya biyo bayan wasu kalubale da muka fuskanta amma yanzu insha Allahu zamuci gaba daga inda muka tsaya. ************** A baya mun tsaya ne inda “Maryam” tsayawa tayi chik, baki ban amsa ba zaki tafi, ki taimaki zuciyata karta fashe mana. Juyowa tayi ta sakar mai tattausan murmushi mai dauke da sako, saidai shi bai iya karanta iri kalaman din jikin murmushi ba, kawai cikin gida ta juya ta shige. *************** Cikin rashin gamsuwa isah ya koma gida yana ta tunane tunane shin me yarinyar nan ke nufi, ai a so ba’a dole idan bata so na ba saita fada ba kawai a wuce gun, Isah ne shi kadai yana tafiya yana zancan zuci.... Maryam kuwa tana shiga dakin duk suka gyara zama wato haleema da anne wai sai ta fada musu waye yazo gunta, ai kuwa fa fur taki fada, sukayi sukayi anma tace kawai bata sanshi ba. Anne tace to ai nasan dole ya fada miki sunansa, to ya sunansa ai nasan ko wane saurayi a duk fadin garin nan. Bai fadi min suna ba... Suka hau dariya wai bata da gaskiya, haka dai sukai ta zolayar maryam wacce ita kuwa tunani ne duk ya addabe ta.. ************ “Ina kwana umma” “lfy lau aliyu” a cewar mamar tasa, sannan ya juya ga maman deeni suka gaisa.. Wai aliyu har yanzu ba batun ko daya daga cikin su ne? Wllh mama babu wani labari a cewar aliyu haka makarantar su maryam ma sun ce bata je ba ranar. Maman deeni ta yi shiru hawaye ne suka fara zarya a idanonta a bin tausayi, kanta ne ya fara sarawa da karfi dafe, kanta tayi tana inalillahi. Kwatsam sai gani sukayi ta fadi, da sauri sukayi kanta, a kidime suka kwasa sai asbiti akayi Emergency da ita, duk a gigice suke sun ma kasa zama da kyar aka lallashe su da cewa jinin tane ya hau yanzu tana bukatar hutu anjima zasu iya shiga domin ganin ta .... Bangaran yazeed kuwa ******************* Naman suka hau ci kallo daya zaka musu ka fahimci ba imani a tattare da su gaba daya yanda suke cin abinci da sassan dan adam a ciki amma su ko a kansu, tsohon cikin su ne yace gaskiya badman kayi mana asara kasan fa dodanmu yafi bukatar jinin yan mata amma ka bari su mugu suka kashe su. Dad ba haka bane a duk cikin yaran ba wanda su mugu suka samu damar kubutar da su, a inda suka iske su a nan suke sheqe su. Thats gud, Kasan fa Allah ne ya kawo mana dakwale har hudu police 3 da kuma wani 1 dan karamim cikin su. Dad kace naman police ne shi isa na ganshi da baki baki. Hahaha sukayi wata irin dariya tasu ta marasa imani wacce suka saba. Tashi muje ka gansu inji tsohon nan, Ya kalli wasu dake tsaye yace kuje ku kaiwa wadan can naman abinci mana, ko so kuke sai sun rame sun zama kashi ne. Su yazeed ne suka shiga dakin ajiya wato inda su deeni suke, kallan deeni yake kamar yasan shi saidai ya rasa a inane, gaba daya kan yazeed ya daure to shi a ina yasan wannan. Zuwa yayi gaban deeni ya tsuguna yana so ya tuna wani abu amma ya kasa kai kamar na sanka, denni kuwa kallan sa kawai yake, “a ina?” Inji deeni. Shiru kawai yazeed yayi dai dai lokacin ne aka shigo musu da abinci, plate uku ne aka bawa deeni daya suma sauran aka jiye musu nasu, kamar jira suke dama suka fara aika abincin nan, deeni ne ya yi kokarin da katar da su “kudaina cin abincin nan” ya fada. Wata irin harara dan sandan ya dakawa deeni alamun ya kyale su, deeni kuwa da ya karewa abincin kallo tsaff sai ya ga akwai nama mutum da sauri yasa kafa ya hankadar da abincin ya zube .. ************* Assalamu alaikum. Suka amsa mai gaba ki daya yan majalisar, Zagayawa yayi bangaran abokinsa da wato salmanu ya zauna kan dan guntun iccan da yake a zaune, abokina waya tabo ka ne naga duk ka wani canja fuska, ya tambayi isah. hmm abokina zo muja gefe ina san magana dakai, salmanu ba gardama kuwa ya tashi suka koma gefe, isah ya kwashe duk abunda ya faru tsakanin sa da maryam tun daga farko har karshe, yace to amma naga alamun yarinyar ba sona take ba jifa yanda na dame ka a kanta ko da yaushe tunanina gareta ne amma kaga fa abinda ta saka min da shi kenan. Dariya salmanu ya kyakyace da ita harda su rike ciki, “bana san haka fa kai wato nazo na fadama damuwata, wato abinda zaka min kenan ko kasan fa na tsani dariya” isah ne ke fadan haka. Salmanu ya dafa kafadar sa yace kwantar da hankainka abokina nasan baka fahimta bane kawai, amma a hakikanin gaskiya ina tayaka murna abokina domin na tabbata ta amshi soyayyarka. Wani irin dadi yaji baisan ma lokacin da ya rungume salmanu ba dan tsabar murna, “ka tabbata”, eh mana domin kuwa murmushi ta shine tabbacin haka sannan ba yanda za'ayi in mace bata sanka ta maka murmushi a lokacin da ka furta mata so saidai ma ta bata rai. “Yaya isah wai ance in kira ka”, Wani yaro ne dan makwabtan su aka aiko, “Wake kirana” isah ya tambayi yaran, “abban ku” inji yaron “jeka ce gani nan zuwa” yauwa salmanu ina godiya da jin wannan gagarumin albishir naka sannan yanzu taya zan gane haka gaskiya ne idan naje gidan. Kawai abinda zakayi shine ka mata murmushi in kuka hada ido sai kaga kalan martanin da zata dawo maka dashi inji salmanu. Nan sukayi bankwana, Isah ya nufi gidan nasu. Assalami alaikum ya maimaita har sau uku amma shiru kake ji gidan kamar ba mutane. Saida ya zo wucewa ta matattakala sannan ya fahimci akwai mutum a falo. Ta dora hannuwa biyu, Haba hajara miye haka ne yasa zaki dorawa kanki damuwa da yawa bayan haka allah ya kadarta, haka yayi niyya ya faru gare mu, kisawa ranki dangana mana. Sai lokacin ma tayi farat ta dago alhaji ashe ka dawo, tana goge hawayan fuskar ta. Haba maman deeni yanzu dama duk wannan kugin da nake faman yi bakya jini hakikanin gaskiya ta bashi tausayi domin yanda take ji da yar ta, rabuwa da ita dole yasa ta cikin rudu. Rungumota yayi a jikinsa yana share mata hawaye kamar yarinya, Ita kuwa sai shesheka take tana cewa yanzu shikenan haleema na yanzu shikenan. Ta kara kakame alhaji tare da kuka mai tsuma rai, shi kuwa yaci gaba da lallaban ta yana lallashin ta........... Sai ku biyo mu a kashi na Ashirin da Tara dan jin cigaba adsAliyu ne ya shigo dauke da ledoji guda biyu a hunnunsa, ya ajiye ledojin tare da dagowa yace mama ya jikin maman deeni, da sauki ai, Alhmdulilah saidai doctor yace ta rage tunani domin duk shi yake kara zafin ciwan . Yaja nunfashi tare da cewa to Allah ya bada lafiya ga abinci nan ai sai ki bata ko, kema ga naki ya mika mata ledojin sannan ya mike ya fita, maman deeni kuwa duk ta wani rame tana jin su duk abinda suke kuma idan ta a bude amma bata iya cewa komai ba... ****************** Deeni kuwa tunanin tserewa yake domin kuwa yaji yazeed yace zai kawo baban sa. Yace a ransa ai gwara in fita ko ba komai da zan taimakawa kawun haleema kuma zan sake ganin ummina ko sau daya ne kafin a zartar da hukunci a kaina. Juyawa yayi ya kalli yan sandan nan yaga sai barci suke abinsu, shi kam kwana 2 da yayi a gun ko gyan gyan di baiyi ba.. . *********************** BAN GARAN ISAH KUWA.. Shiga yayi dakin baban nasu da sallama abban nasa ya amsa. Bayan sun gaisa yace mai dama ba wani abu ne yasa nace a kiraka ba illah in fada maka maganar da mukayi, dazu muka tatauna da mahaifiyar ka a kan maganar yaran nan kaga yau kwana 2 kenan bamu san wane hali iyayan su ke ciki ba ya kamata mu maida su ga iyayan su dan haka ina so zan baka kudi gobe da yamma ka kaisu gida domin suna cikin hayyacin su, zasu ganne gida. Isah kuwa gabansa ne ya fadi ji yake ai shikenan zai rasa maryam dinsa idan suka koma, domin shi har ya sakankance ma dan baiji ana maganar koma war su ba, dan haka sam shi baiji dadin maganar Abba ba. “To Abba” yace, Sannan yace baba kabar kudin ka ai ina da kudi zan sa yanzu su shirya goben sai mu tafi. To Allah yamaka albarka, yanzu tashi ka kira min mahaifiyar ka tare da su yaran. To baba ya tashi ya nufi dakin umman nasu ya isar da sako sannan ya nufi dakin anne, su maryam da suke zaune sun gama cin abinci sai hirar duniya suke, maryam ce aka bari a kwano sai sude kwano take wai miyar tayi dadi wato taji daudawa. “Hmm ni wllh wani abu ke ban mamaki” maryam ta fada, Anne tace miye kuma wannan maryam, Wai wannan baiwar Allahr mana ta nuna haleema da yatsa cewa tayi fa bata cin tuwo miyar kuka in ba nama. Zumbur haleema ta tashi daga dan ringisawar da tayi “kiji yarinya da sharri to waye ya gaya miki? yaushe mukayi dake?. Kai haleema kiji tsoran Allah kin manta ranar da kika zo gidan mu nace in zubo mana kika ce wai bakya ci, ko dai ranar a koshe kike. To ai ni ba wannan yake ban mamaki bama ji fa yanda kuka ware kuna cin tuwo, amma fa ni gani nake ba dan Allah kuke cin abincin garin nan ba sai dan yunwa inji anne. Gaba daya suka kwashe da dariya. Gaban maryam taji ya dan buga shi yasa ta sasauta dariya, sai suka ji sallama wannan ya sasu rage dariyar amma duk da haka a cikin darayi suka amsa sallama, isah ne ya shigo dakin ya tsaya yana kallan sarauniyar tasa so yake ta juyo ya aika mata da sako, amma taki juyowa sai su anne ne suke gaishe shi... Ya amsa itama sai daga baya ta gaishe shi, ina wuni yaya isah a cewar maryam. Su haleema ne suka hada ido alamun dai akwai wani abu kenan a kasa. Shima kam cikin wata sanyayar murya ya amsa mata tare da cewa anne an sama kawaye wato ba ko futa dandali, murmushi tayi tare da cewa yayana kamar ka sani kuwa domin ni har nama manta da fita zuwa dandali, zuwairah ma kaga taki biyo min, ni kwana biyu ma bansan me na mata ba taki zuwa nan gidan... Ai ke da ita ba’a san waye mai laifin ba domin kuwa ke ya kamata ki neme ta domin kinsan tallah take ko yanzu ma tana can ta fito tuwo a dandali... Haleema tace wai me ake a dandalin dan Allah, yaya isah ka kaimu mu gano, yayi murmushi, me kike ci na baka na zuba bayan ga masu dandalin nan a kusa dake.ya nuna anney. Ya dan dafe kai, itafa wannan kawar taku bata magana ne. Tana magana mana, wannan hmm uwar surutu kenan inji haleema, watakila kunyar ka take ji shi isa taki magana. Maryam ce ta dakawa haleema uwar harara. Ah ai wallahi gaskiya ta na fada kaji min yarinya. A cewar Haleema. Kinga kyale ta bari inzo ni kusa da ita in tambaye ta me ya hanata magana, zuwa yayi gab da maryan inda take zaune ya tsuguna. Yace.................... Sai ku biyo mu a kashi

Chapter 5 of 9