Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 9
bari muje yanzu zamu dawo insha Allah, suka nufi motar yazeed ya hau sannan aka bude musu gate suka fita. **************** Can bangaran kuma isah ne shida aliyu a zaune da yake gidan fadede ne kowa harkan gaban sa yake yi, suma haka zaune suke suna hira, nan aliyu yake tambaya ko an zabawa anneesat miji ne, isah kuwa yayi farin ciki da wannan zancen domin kuwa yasan ba a banza aliyun zai mai wannan tambayar ba. "a’a ba wani tsayayye ko a can kauyen ma" “gud” aliyu yace yayi shiru kuma “ko da wani abune isah ya tambaya, a’a ba komai kawai na tambaya ne, “hmm to shikenan tunda kaki fada. Jiniyar motar police suka ji a kofar gida nan take DPO ya fito ya sako deeni a gaba sukayi sallama suka shigo gidan mai gadi kam da yaga police ne kuma ga deeni a gabansa yayi mamaki sossai na ganin deenin, haka shima kawu ya mike yana kallan deeni. Maman deeni kuwa suman tsaye tayi dan farin ciki na ganin yaran nata, amina ce tayi kanta a kidime. Ba tare da bata lokaci ba DPO yaje ya bawa alhaji sanusi hannu suka gaisa sannan yabawa kawu ma, deeni kuwa idan sa a kan mahaifiyar sa yake wanda yana gani ta zube. Kwayar idansa ce ta kai ga masoyiyar sa wato halima, al'amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan, shin wai wannan halima tace ko dai idona ne yake min gizo, saida ya sa hannu ya murza idon dan ya tabbatar da hakan. Alhaji da fatan dai kasan wannan yaran a gagauce, kwarai kuwa wannan deeni kenan shi muke ta faman nema ma a halin yanzu, alhmdulilah inji DPO a halin yanzu ba lokacin batawa ina yazeed da kuma abbansa, yazeed ai yanzu suka fita. “Inalilahhi wa'ina ilaihi raji'un” su deeni suka kama fadi ba'ayi wata-wata ba suka juya tare da cewa alhaji ya biyo su yanzu ba lokacin yi masa wani bayani. Cikin sauri suka hau motar DPO…….. ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 40 Innalilahhi wa'ina ilaihi ra'jiu, abinda ke fitowa daga bakin su deeny kenan, officer yace alhaji zamu iya tafiya yi sauri biyo mu ba lokacin batawa, da sauri alhaji yabi bayan su, wannan karan ma DPO ne ke tuki deeni kuma na nuna mar hanya. Can sunyi nisa sun kusa fita daga gari sai suka hangi motar yazeed sai uban gudu yake ba saurarawa da DPO yayi niyar suje su taresu amma deeni yace kar ayi haka, gwara dai aje har gidan nasu in yaso dama akwai yan sandanku da aka hadani dasu biyu amma dayan wato ogan su tuni an yankasa. “innalillahi kawai DPO ya fada tare da cewa Allah ya gafarta masa, a nan ne alhaji ya dan fahimce su yake tambaya su fada mai me ke faruwa ne. "DPO ne yace yayi hakuri a yanzu ba halin yin hakan, a hankali suke bin bayan motar yazeed shi kam baima lura da wata motar police ba da yake ya dan basu tazara. Abbansa kuwa gani yayi ana ta tafiya dashi har za'a bar cikin gari a yanki daji amma ba'a zo ba, kai yazeed wai ina ne nan zaka kaimu, dad ai mun kusan karaso wa ba nisa. Can bayan sun sake yin wata tafiya mai dan nisa daddy ya kara tambaya domin guraran shi baiga alamar gari bama, daddy nace ka kwantar da hankalin ka mun kosa zuwa. Kai bana san shirme wannan wace kalar shiririta ce, tun minti 20 baya kace min ankusa zuwa sai yanzu ka kara cewa an kusa. Kaga ni bansaka dole ba in dama karya kake min baka da wani uban gida to gwara ka fada sannan ka juya mu koma domin ni zaman motar nan ba wani kaunarsa nake ba na gaji. Ganin baban nasa zai kawo mar matsala ne yasa shi fito da wata yar kwalba ya fesa mai. Ba'afi sakan 30sec ba abban nasa ya hau barci harda munshari. Su kuwa su deeni a baya suke suna biye da su, deeni ne yake bawa DPO shawara a kan a karo ma'aikata in so samu ne har sojoji ma a kirawo domin na tsorata da kalan kartin gidan, DPO yace hmm deeni ke nan zaka nuna mana aikin mune, a’a yallabai ni kawai shawara na bada, kafin deeni ya rufe baki ne suka hangi motan yazeed can zata gangare daga kan titi ta nufi wani daji. Nan ne fa DPO ya fara gaskata maganar deeni nan take kuwa yasa a kira babban office dinsu dake cikin garin kano ya bayyana musu abinda ke faruwa tare da fada musu address din gun da suke a yanzu, saida suka bari yazeed ya mika tukun suma suka gangaro motar tasu suka bi bayan sa, shi kam duk abinda ake bai ma san akwai mota na biye da shi ba, abbansa kuwa nan ya kwanta ya dinga barci na fitar hankali.. Bangaran maman deeni kuwa da aka dauke ta aka kaita daki bayan tafiyan su deeni kadan ta farfado ba abinda take kira sai deeni-deeni ashe dama kana raye ina ka tafi ka barni, duk wanda ya ganta a wannan halin tilas ya tausaya mata. Maryam ce ta ruko hannunta itama hawaye take, itama sai lokacin ta fahimci ashe yaya deeni baya gida boye musu ne kawai akayi, mama kiyi hakuri sunje su dawo tabbas deeni ki ne, nan dai suka shiga lallashin ta. Haleema kuwa wani farin ciki take na ganin sahibin nata, hakan yasa ta tashi ta tafi dakinta ta fada kan gado sai wani kukan dadi take. Aliyu da kawu kuwa duk hankalin sune ya tashi sun rasa abunyi, ba'a musu bayanin abinda ke faruwa ba. *********** A can Kauye kuwa “malam nifa ina jin kamar ba lafiya fa ace har yanzu su anne basu dawo ba”, “haba ke kuwa zuwaira me yasa kin cika garaje ne, kuma ke da zaki dinga musu addu'a, ai addu'a zaki yi ba ki tsaya ki dinga zarge-zarge ba kinsan dai isah yaro ne mai natsuwa bazaiyi abinda zai saka mu a damuwa ko ya bata mana rai, ni banyi tunanin zai kwana a can bama to amma kika sani ko lokacin da sukaje dare yayi ne kuma iyayan yarinyar suce sai sun tsaya sun kwana.” to allah dai yasa a dace kuma Allah ya kare mana su, ameen kinga da tun farko ma haka kika ce, to ai malam abin ne da ban tsoro yanzu fa kaga karfe 10 da wani abu amma yaran nan basu dawo ba, ki kwantar da hankalin ki zasu dawo isha'allahu ya fada lokacin da yake mikewa, to ni zan fita kuma sai na dawo zan biya wajan kaka daga nan in bata sako domin kinga jiya an barta ita kadai a gida, to malam Allah yasa a dace a gayar min da kakar, to zata ji isha'allahu... ************** Yazeed na gaba suna binsa a baya can da suka hangi gidan kuma suka lura nan ya dosa sai suka kara gudu wato dan su isko sa amma ina tuni ya riga ya karasa domin ya musu nisa, a guje suka karasa tun kafin motar ta tsaya yan sanda suka fito kowa da bindiga a hannunsa suka nufi gidan, nan deeni kuwa ya shiga gayawa abban halima abunda ke faruwa............... Abba yayi mamaki sosai ya jinjina kai zuciyarsa cike da tunanin irin wannan yaro wato yazeed duk biyayar da yake wa abban nasa, kenan dama duk kudin da yake da su ta hanyar da ya tara su kenan, banyi tunanin yazeed zai iya yiwa ‘yaya haka ba, ban ma taba tunanin yazeed zai iya kashe ko kwaro ba balle ma ace wai mutu. “Abba to ai shine yayi yunkurin kashe su haleema ma da bakinsa naji yana fada lokacin da nake a tsare a gidan” inji deeni, “Ya allah” abban halleema ya fada tare da dafe kansa da yaji yana irin wata juyawa, dama yazeed fadan da suke da halima ba iya nan ya tsayaba, yanzu ita daya tal da nake da ita yayi niyar hallaka min, kai!! amma da ya cuce mu gaskiya, baza mu taba yafe wa yazeed abinda ya aikata mana ba, Allah ya isa tsakanin mu da kai yazeed. Direct gate din gidan suka nufa cikin irin sallan su na ma'aikata wanda suka san aikin su bibiyu suka kasu inda shi kuma DPO ya bi bangare daya, a hankali suka tura gate din, guda daya ne ya fara kutsa kai can ya hangi motar amma ba kowa a cikin ta, nan ya daga wa na waje hannu alamun su shigo bayan ya leka ko ina baiga kowa ba, haka suka shiga a hankali suke tafiya irin tasu ta ma'aikata , wani daga cikin sune ya tura dakin, sa kafarsa keda wuya sai sukaji anyi harbi ba dan yayi gaggawar dukewa ba da sai ta same shi da sauri yayo baya, sunyi mamaki matuka ta yanda akayi yazeed ya san da zuwan su shin dama ya gansu ne ko kuwa BAYA....... Yazeed tunda yaga abbansa ya fara barci ya fara tukinsa a hankali kwance, can ya lura da motar police amma kawai sai ya basar a cewarsa ai shi ba wani laifi yayi ba me ruwansa da su, kuma ma dan yaga tabbas din hakan sai ya dinka rage sauri domin wai suzo su wuce, can nesa da shi suke abun mamaki kuma duk sanda ya rage gudu suma sai yaga sun rage haka dai ake ta tafiya, ana cikin hakan ne yaji wayarsa na kara yana dubawa yaga dad wato wancan dad din nasa matsafinan yake fadamar cewa daya daga cikin wa yanda muka kamafa ya gudu, yazeed yace garin ya bayan ba wanda ya taba guduwa daga cikin gidan nan ya haka ta faru, dad din yake gaya masa cewa ko ka manta ne sai wanda yaci abincin gidan ne bazai iya fita ba to yaran taurin kai ne da shi ba yanda bamuyi da shi ba a kan yaci amma yaki, ok yanzu miye abunyi domin ga wata motar police nan ina kyautata zatan kuma ni suke bi to amma ni bansa ya akayi ba domin ni kam ban karya dokan titi ba tun tahowata, ok kadai kara kula kuma ka lura sosai yanzu kuna tare da dad din naka? tsohon ya tamabya, eh muna tare gashi nan ma wallah saida na sa mar hodar barci tukuna domin naga ya fara ganowa, ohhh saboda me kasa mar ai da baka sa mai ba domin kasan dokar gunki mu bazai karba kyautan nan ba ko kuma zai raina ne anma da ka kawo shi a hk kasan fa muna da kartai ko da karfi ne da sai mu turasa ga ogan. srry dad ai ina tunanin ma kafin in karaso ya tashi domin bamai karfi bace sosai. ok sai kazo be carefull " ok dad. Yazeed bai tabbatar da su deeni shi suke bi ba saida ya shiga dajin nan, can yayi nisa ya hango su suma sun biyo sa lokacin da har zai waske yayi wani gun kuma sai ya fasa ya sake kiran dad nasa ya sanar da shi cewa police din shifa suke bi, dad yace ba damuwa zasu shirya kafin karaso warsa kawai yazo ba damuwa, haka kuwa yaje ya shiga gidan ya faka motarsa sannan ya kira wasu suka taimaka masa aka dauki abbansa da yake faman barci kamar na mutuwa aka sashi daga ciki. Tuni karti gidan kowa yayi shiri tare da mugayan bindigun su a hannu, amma suna ciki, wato a falo ba su fito ba saboda tsaro, can su kuwa yazeed da ogan tsafin sa kokari kawai suke na su tada abbannasa wato alhaji bashir domin su bawa gunki sa domin kar lokacin ya kure, dan idan lokaci ya kure basu bawa dodan nan abinda yake bukata ba duk sai sun mutu, a wannan ranar ba wanda zai tsira, shi yasa ma basa wasa da du umarnin da ya basu, nan dai suke ta iya kokarin su amma ina yaki ya farka, sun kwara mar ruwa sunyi yaki ya farka balle su jefa sa cikin dakin dodan, suna cikin hakan ne suka ji anyi harbi hakan ya dada tabbatar musu da cewa yan sandan ne suka karaso, nan suka kara azama na tashin alhaji bashir daga baccin. CI GABAN LBR... Su DPO kam da sukaga haka komawa sukayi da baya suna tunanin taya zasu jewa wannan mutanan, gasu su biyar ne, kawai hakan tasa ya sake kiran lambar shugaban su a kan suna bukatar taimakon gaggawa. deeni da sirikinsa da aka bari a cikin mota ba abinda suke sai addu'ar Allah ya fito musu da alhaji basher lafiya ba kamar alhaji sanusi yanda ya damu shi kam kamar ma ya shiga da kansa dan cetan dan uwan nasa. Su DPO kam jinkirtawa sukayi anan suna tunanin wane tsari zasuyi dan shiga gidan nan, saidai fa kuma mu biyar ne gashi bamu san ko su nawa bane a ciki sannan bamu san yanayin makaman su ba dole dai mu jira, wani police ne daga ciki yake cewa oga baka tunanin zasu iya cutar da alhaji kuwa idan mukayi jinkira, to yanzu ya kake tunanin zamuyi kasan fa cewa duk wanda ya shiga ciki sunan sa shekakke domin kaga fa yanda akayi harbi, karan bindigar ma na daban ne ya kamata mu kula. Al'amarin baccin abban yazeed fa zuwa yanzu ya fara basu haushi, to shi wai wane irin maganin bacci ne wannan domin sunyi yan dubarun su na ya tashi amma ina har ruwa mai sanyi suka dinga kwarara mai amma ko motsi yakiyi hakan yasa suka shiga yimai allurai masu kashe wannan ta barcin amma ina shiru yaki ya farka hakan ya fusata wannan tshon shi isa yata dura masa allurai iri-iri ba sassauci, su abinda ba su sani ba tuni ya suma domin sinadaran da suka hada mai sun yi yawa. Yazeed kam tashi yayi ya jigina kai jikin bango bakin ciki ya cika shi, kamar ya karasa kashe abban nasa yake ji sai dai ba halin yin haka, dole suka kyale sa suka nema gu suka zauna a cewar su saiya fardado. Su DPO ne hade da sauran yaransa sun tsaya sai zurga zurga suke domin su rasa abunyi, haka shima abban haleema addu'a kawai yake shi baima iya daurewa ba saida ya shigo gidan ya tambaya wane hali ake ciki yanzu, shi duk a firgice yake kar a hallaka mar dan uwa wanda shine ya rage mai dan uwa na jini a duniya, aka sanar dashi cewa ya kwantar da hankalin sa ba abinda zai faru amma yanzu akwai ma'aikata da aka turo mana da su sun kusan karasowa, sannan DPO yace dashi ya koma mota domin bamu san irin shirinsu dinsu ba. Suna cikin maganar ne sai sukaji karan motoci hakan ya tabbatar musu cewa ma'ikatan ne suka karaso, gabaki daya sukayi waje, sojoji ne da police cikin shirin yaki. Suka fara dira daga saman motar tun kafin a tsaya nan take duk suka zazagaye gidan inda su kuma sojojin da zasu kai kimanin 12 suka nufi cikin gidan, saida DPO ya musu bayani tukunna suka tsaya suna tunanin yanda zasu bullowa al'amarin, ciki kuwa karti ne sama da 50 ko wanne rike da mahaukaciyar bindiga ya saiti kofa, lallai kam duk wanda yayi gangancin shigowa dakin nan zai zama sheqaqqe domin duk a lallabe suke a cikin dakin. Umarni aka bawa mutum 3 su shiga, suna shiga suka ga lokaci daya mutun sama da goma sun fito kafin suyi wani yunkuri tuni an hallaka su duk da rigar harsashin dake jikin su, tabbas suma kartin nan ba'a banza suke ba sunyi training mai kyau. Suna waje sukaji karan fitar harsashin can kuma sai sukaji shiru ko motsi basu kara ji ba, hakan yasa aka kara umartar mutum biyu da su shiga, ba gardama kuwa suma suka kutsa kai, akwance suka is iske abokan aikin nasu, wannan yasa sukayo baya saidai a lokacin ne kuma sukaji kartin nan sun fara harbinsu, nan dai suma suka fara kokarin mayarda martani hade da gocewa, sun ci nasarar harbin mutum daya daga cikin kartan. A tsiyace suka fito da gudu nan suke sanarwa da shugaban nasu irin shirin mutanan, ogan nasu yayi ajiyan nunfashi yana tunanin ta wace hanya kuma za'a shiga gidan nan.. DPO ne ya kawo shawara cewa hanya biyu ne kawai dole a turo mana da kartafila ko kuma tanka domin gidan nan saidai a shige sa ta hanyar rusawa haka ne kawai mafita, no ba sai anyi haka ba inada abinyi..... *************** Maman deeni kam tuni an rarrasheta ta hakura ta dawo hayyacin ta sai dada godewa Allah take yi na bayyana mata duk ya'yan' ta bayan da har tama hakura da su kaddara kenan. Maryam kuwa saida taga hankalin umman nasu ya kwanta tukun ta fito domin tana kewar ganin isah tare da yaya ali ta gansu zaune sai hira suke. Suna ganin ta suka fara tambaya ya jikin umma, da fara'arta ta basu amsa umma kam jiki yayi sauki, ya aliyu ashe kuna nan, eh wallahi maryam muna nan muna dan hutawa bakwan naku ne ya takura a kan wai shi tafiya zaiyi. Maryam kuwa bata fuska tayi jin ance wai ya isah shirin tafiya yake, to ya zaimin haka saida ya sace min zuciya tunanin sa ya hanani sukuni zai tafi ya barni to in ya tafi ma yaushe zai dawo, maryam data sunkuyar dakai tana ta zancen zuci. Ya ali yace yadai naga kin dan bata rai dan ance zai tafi ko dai bakwan sirikin mune ya fada cikin tsokana, dago kai tayi ta kakaro murmushi kai ya aliyu ka cika zolaya ni ina ruwana da shi ya tashi yata tafiya mana idan har zai bar mana annisat din mu, isah da baice komai ba har a lokacin kallanta kawai yakeyi yace “ok haka kika ce ko to ai shikenan indai anne ce gata nan ai sai kucinye an bar muku”, ya kalli ya aliyu lokacin da ya mike tashi ka rakani in hau mota mana tunda kaga dai korar mu ake a garin naku, “aa ba'ayi haka ba gaskiya mu kam mun isa mu kori sirikin mu ai bamu isa ba” aliyu ya fada yana dariya. Maryam kuwa ganin aliyu ya gano komai yasa ta rugawa ciki cike da kunya tana dariya... “Ohh kace kazo zaka dauke mana kanwarmu ko” aliyu yake zolayar isah, ai wannan abun baza mu yarda ba kuwa sai dai ayi chanje, isah murmushi kawai yayi baice komai ba amma kamar ya so ya gane wani abu a cikin zancen aliyu haka shima aliyu yaso yayi mai magana domin ya tabbatar mai da cewa shi fa yana san kanwarsa amma sai yayi shiru, baiji dadin shirun ba. ***************** Shugaban sojojin nan kuwa wasu ya aika mota domin su kwaso taigas..... ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 43 Suna isa asibiti aka yi saurin karban abban yazeed, akayi emergency da shi domin bashi taimakon gagawa, abba da deeni kasa zaune sukayi tsayuwar ma gagara tayi sai zirga zirga da suka hau yi. A can kuma cikin gidan alhaji tsit kake ji ba wani mai kuzari a cikin su domin alhaji sanusi ya kira ya shaida musu halin da ake ciki shi yasa duk suka damu wasu na kuka wasu na jimami, hajiya saratu kam kuka take yi sosai bata taba tunanin wai danta zai iya kashe ko kaza ba balle mutum, uwa uba ma wai yau abbansa zai bayar, cike take da takaici iri iri. Su haleema kuwa dake sun san komai dama basu wani ji mamaki ba, annee kuwa lokacin ta tabbatar da labari da suka bata gaskiya ne, haka dai gidan ya kasance har yamma shiru kake ji ba wani mai walwala a ciki. Su abba kuwa suna asibiti jikin alhaji yayi sauki sosai domin sun hadu da kwararun likitoci, tuni suka magance matsalar. Shidai kawai tsintar kansa yayi a gadan asibiti a kwance gashi baiji wani gu a jikin sa na mai ko alamun ciwo ba, hakan yasa da abban haleema suka shigo ya fara aika musu da tambayoyin cewa wai me ke faruwa da shi, me ya kawo shi hospital ina yazeed nan suka shiga kwantar mai da hankali a kan ya natsu bayada lfy yana bukatar hutu, amna shi ina shifa lfy sa lau yake gaya musu, lokacin ne wani likita ya shigo hannun sa dauke da wasu takardu, nan yake sanar musu cewa an sallame sa zasu iya tafiya dama ba wani abu ke damunsa ba kawai alluran da aka mar ne abun ya wuce ka'ida, nan dai sukayi duk abinda ya dace suka taho gida, duk abinda akeyi DPO na tare da su... Bangaran su yazeed kuwa ranar sunsha azaba iri iri wacce ma basu taba tunanin kalarta ba domin sojojin nan kalan abinda suke musu sun gwammaci mutuwa ma a kan haka. Lokaci daya duk aka canza musu Kamanni, gaba daya ba zaka iya gane yazeed ba, haka suka sako shi a mota suka nufo gida da shi. Su abba kuwa a babban falo gida suka hadu, DPO ya mike yake musu jawabi a kan duk abinda yake faruwa tun daga lokacin da suka kama deeni har zuwa yanzu. Sannan deeni ya mike shima yayi sallama, farinciki cike a ransa, nan ya fara basu labarin duk abinda ya faru, duk yan wajen saida suka tausayawa deeni, mahaifiyar sa kuwa sai kuka take tana dada tausayawa yaran nata, haka itama haleema abin ya kasance. Nan deeny yake fada musu duk abunda yaji a bakin yazeed na cewa shine ya sa a kashe su haleema da kuma kyautar abbansa da yayi ga dodo. Alhaji yayi mamaki sossai da jin wannan zance wato yanzu dama yazeed duk tarbiyar da muka mai a banza kenan ta tashi, dama kudin da suke shigo mai yna fakewa da kasuwanci ashe dama ta wannan hanyar yake samun su, haka dai yaci gaba da tunane tunane, nan shima isah ya mike ya bayyana komai dangane da tsintar halima da yayi haka kuma abin da deeni ya fada shima daidai ya fade shi bai ko saba ba. Nan dai kowa yaci gaba da bada labarin sa duk aka cika da mamaki sai dai har yanzu an rasa wane laifi ne su haleeman suka wa yazeed har da ya kudarci daukan fansa da ransu. Haleema kam tsoro taji ya kara shigan ta, ta kasa fadar gaskiya lokacin da aka tambaye ta meye suka mai, maryam ce tayi bayanin komai cewa dakinsa suka shiga alhalin ya hana kuma suka dauko laptop dinsa to anan ne suka gane cewa ba mutumin kirki bane, taci gaba da cewa kafin mu fito ya ritsemu a daki sannan ya mana duka hade da kashedi karmu kuskura mu bayyana idan ba haka ba kuma duk zai hallaka mu shiyasa duk muka tsorata muka ki fada. Kowa ya cika da mamaki a gun, ba'a fi minti uku ba sai ga yazeed sojoji sun shigo da shi, kallo daya zaka masa ka gane cewa ya lakadu, durkusar dashi sukayi a gaban jama'a, a cewar su wai suyi bankwana da shi. Maman sa kuka ta shiga yi ganin halin da dan nata ke ciki sabanin abban sa da yake jin wata tsanarsa kamar yaje yasa bindiga ya harbe shi a gun, jama'ar wajen kowa yayi Allah wadai da halin yazeed, shima yazeed sai a lokacin yake nadamar shiga wannan kungiyar bayan bai rasa ci ba bai rasa sha ba, kudi suna shigo mai ba laifi amma san zuciya da san tara makudan kudi sun kaishi ga halaka. A lokacin duk wanda ya kalli yazeed zai gane yana cikin nadama, ko bakayi niyar tausaya mai ba sai ka tausaya mai, cikin kuka da wata murya ciki ciki yake cewa ku yafe min dan Allah ku yafe min nasan na jefa rayuwarku ku duka cikin wani hali amma sai yanzu nake cike da nadama wanda nasan ko kun yafe min ba lalai ne in sami rahamar Allah ba, amma yafiyar kawai nake nema a gare ku. Wajen tsit yayi, kowa ya tausaya wa yazeed domin yayi nadama. Halima ce ta fara kada baki tace ni dai na yafe maka duk abinda kamin ya yazeed, Allah ya yafe mana ga baki daya, saida hawaye suka kwaranyo mata, kowa yayi mamaki a gun shi kansa baiyi tunanin halima ce zata fara yafe masa ba, daga jin haka maryam itama ta kada baki tace ta yafe duniya da lahira, wannan ya faranta ran yazeed sossai. Haka yasa kowa ya ta yafe masa, duk kowa ya yafe har ummansa itama, abbansa ne kawai yayi shiru bai ce uffan ba. Abba idan baka yafe min ba bansan halin da zan kasance ba, bana so in tafi ba tare da yafiyar ka ba, abba ni nasani cewa tawa ta kare domin kuwa koda ace basu kashe ni ba ni nasan cewa yau bazan kwana ba domin ka'idar kungiyar mu kenan, mun karya alkawari dan haka bazai kyale ni ba duk wani dan kungiya dole ne yau ya bakunci lahira....................... TAMBAYA IDAN KAINE ABBANSA ZAKA YAFE KO KUWA? ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 45 Hakika yabawa abbansa matukar tausayi baisan lokacin da idanunsa suka ciko taff da kwalla ba, nan ya dinga tuna abubuwan da yazeed yake musu na alkhairi, wannan kawai sharrin shaidan ne, “na yafe maka yazeed Allah ya yafe maka” haka ya furta yayin da tuni hawaye sun gangaro fuskarsa sanda yake kallan yaran nasa cike da tausayi. Cikin wata irin murya mai karkarwa yake cewa na gode abbansa sannan ya fashe da kuka a wajen ba wanda bai tausayawa yazeed ba. Nan wani soja yace kana da magana ko kuwa ka gama, na gama yallabai yanzu abinda zance shine ya kalli abbansa sannan yace a kwashe kaf kayan dakin can ya nuna dakinsa yace gaba daya a kona, haka ma dakina na can abuja shima a kwashe kayan kaf a kona, yana gama fadin haka caf wasu sojoji biyu sukayi sama da shi suka fara tafiya, yana kuka ake tafiya da shi, haka itama mahaifiyar sa kuka take sossai tana yiwa dan nata kallan karshe. Gaba ki daya dai gidan haka ya wuni ranar nan ko abincin kirki ba wani wanda ya samu damar ci saidai tattabawa. Aliyu kam zaune yake shi kadai ya rasa meke mai dadi shifa a gaskiya san anne yake gashi ya kasa gaya mata karfa yayi zurfin ciki, nan ya dafe kai yana tunanin shi ya zaiyi ya bayyanawa wannan yarinyar yana sonta domin kuwa idan ta koma kauyan su baya tunanin zai sake ganin ta, gashi yana ji yayan ta ya takura shi gida yake so ya koma. Tashi yayi da sauri ya nemo takarda da bairo ya rubuta wasika, yar aikin gidan yabawa ta kai mata sannan ya kwatanta mata anne yace ta bata a sirrance kar ta bari wani ya gani. Deeni ma fa haka al'amarin shi duk wannan al'amarin baya damunsa tun dazu bayan sun hadu da maryam da mamansa yaji wani fayau ba abinda ke damunsa yanzu masoyiyarsa kawai yake san gani saidai ya rasa ta hanyar da zai kirawo ta domin su hadu da juna, itama haka taji ba abinda take so yanzu sai ganin deeninta cikin falo suke zazzaune sun kunna tv amma ba wanda hankalinsa ke kan tv kowa ta tasa yake yi. Halima sai yan kifce kifce take hakan yasa ummanta ta gano ta, tace uhm wato gurinsa kike so kije shine kika kasa fada ko to ai ni na ganoki tashi kije wa zai hanaki ganin deeni. Fuska ta rufe ciki da kunya tana murmushi ta yo waje bisa mamaki a kan wani dan dakali ta tarar da deeni inda dama sun saba haduwa a gurin, nan fa aka sha hira irin ta masoya, an dade ba'a hadu kuwa yana nuna kalan damuwar da ya shiga dalilin rabuwa. karfe 10 sukayi bankwana kowa

Chapter 8 of 9