Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 9
na Talatin dan jin cigaba ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 29 BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng PART 30 Na Isah Bigboy Hajiya maryam kenan laifin me nayi kuma da ba'a min magana, idan laifi nayi ai gwara a fadan dan in gyara laifina ko. Maryam dan kauda kai tayi gefe cike da kunya bakayi laifin komai ba. Yauwa haba har naji zuciyata ta dan sami sukuni... Su halema da suke ta kallan su abun ya bawa Haleema sha'awa, nan ta shiga tunanin deeni ta Allah sarki. Anne kuwa hannuwa tasa ta toshe baki ta bushe da dariya, shima Isah dagowa yayi cike da kunya yayin da ya tashi ya nufi kofa, har zai fita kuma sai ya waigo, ni har na manta ma wallahi kun jani da hira, baba na kiranku dukaku. Dukansu sun hallara gaban abban su isah, Suka kwashi gaisuwa sannan ya dora da bayani. Ba wani abu bane yasa na kiraku sai dan in sheda muku cewa gobe zan hada ku da isa ya maida ku gida domin bamu san ko wane hali iyayan ku suke ciki ba a yanzu Kunsan dai ku ba yara bane. Ya kalli inda su halleema suke yace fatan kundai ji abinda nace... To baba yaushe zasu tafi, kuma dan Allah baba zan raka su inji anne. A’a ai gobe da yamma zasu tafi dan haka kuje ku fara shiri ma tun yanzu sannan kuma ke aneesa badake za'aje ba. Ayya baba dan Allah ka barni inje sai mu dawo da yaya isah. In banda abinki aneesah ai ba yanda za'ayi ki bisu duk da dai kun shaku da juna amma ai sai ki bari wataran kyaje. Hakika ita dai bata so haka ba domin bata jayaya da iyayan nata shi yasa taja bakin ta tayi shiru. To mun gode abba, ba abinda zamu iya cewa sai dai Allah ya saka muku da alkhairi. To ameen ku tashi kuje sai da safe ko. Kai kuma isah goben ka shirya da wuri fa, to abba ya amsa. Ku tashi ku tafi. ***************** Yazeed ne yayi shiri tun da safe ya fito a shirye, a dining ya iske su abba yaje ya zauna bayan ya gaishe su, a nan yake fadawa abba zai koma gida amma yana ga kwana biyu zai yi ya dawo domin ko kaya bazai dauka ba. Abba yace to ai shikenan amma jiya ina kaje ne har na dawo ban iske kaba sai maman haleema ke gaya min kazo. Yadan sosa kai, eh wallahi dad abokanaina ne suka tsare ni, Hmm yazeed kullum in kazo inamaka warning a kan ka kiyaye abokai marar sa tarbiya, to dad ai abokan kasuwanci nane. Karfe 8;00 tuni sun kammala breakfast, 8:30 yazeed ya tafi. ************** Deeni kuwa tunanin hanyar tsira yake yace tabbas dole in bar gidan nan yau ko ta halin yaya, hannu ya daga yana addu’a, ga yunwar da take cin sa domin shi kam yaki yarda yasha ko ruwan gidan. Kamar kullum yauma haka aka shigo karfe 9:00 aka kawowa su deeni breakfast amma shi ko kallan abincin baiyi ba. Mai kawo abincin ne yaje yake gayawa tsohon nan cewa yaran nan fa yaki yarda yaci abinci kuma a dokar wannan gidan sai wanda yaci abinci shine ba zai tsira ba. Ya juya ya kalli wani dake can tsaye kato ne duk jikin sa a murmured, baki ne wuluk kamar gawaye, Kallo daya zakama katan nan ka tsorata domin indai ta bangaran girma da murdewa ne to lalai wannan gardin ya cika. Ya kira shi da wani suna yace kaje ga daya daga cikin yaran can yaki cin abinci kuma kasan cewa a tarihin nan gidan ba wanda ya taba shiga ya fita in ba yan kungiya ba, maza kaje ka tsorata shi, kuma banda duka ko ka tusa mai, domin idan kayi haka ma a banza dole sai in mutum ne ya dauka abincin yaci da kansa, to oga kawai gardin yace, ya juya ya nufi dakin da su deeni ke ciki. ***************** 9:30 su anne ne ke wanke wanke suna tadi, to mu da ake cewa mu shirya bayan ko kaya sai wanda suke na jikin mu, lah kaji min yarinya to da ace bamu wanke na jikin mu din jiya ba to da fada min ya zamuyi yau inji maryam. Yauwa anne wai ke baki da saurayi ne a duk fadin garin nan ko dai babu mashin shini ne, inji maryam. Hhhhh yar sa ido kawai, Inji haleem. Haleema kyale ta yau tsokana take ji, kuma maganar saurayi ke dai tunda kin sami naki kin zo kin dauki hadadden saurayin garin nan ai shikenan. Wata kalan harara ta dakawa anne tace waye? Hmm kedai kika sani. Lokacin da suke tattara kayan wanke wankene anne tace yauwa dan Allah ku taimaka min ku lallabi abba watakila in kune zaiyi hakuri ya barni in biku tunda dai yau yaya isah zai dawo. To mun yarda amma sai kin zagaya damu wannan rigar taku tinda kinga har yanzu bamuyi yawo da rana ba, Ai wannan ba matsala bane yanzu dai kuyi wanka tukun na, to ke fa yaushe zaki yi wankan, Tabb to ni da ba dani za'a ba wankan me zanyi aradu bazanyi ba. Dariya suka kama yi, Mama wai anne bazatayi wanka ba sai za'a je unguwa. Maryam ce ke fadi wa maman. Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da daya dan jin cigaba ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 30 Share This: RECOMMENDED ARTICLEHmm ai kadan ma kuka gani ko dandali idan zata kwaskwarima kawai take sai uban jan baki da take laftawa, wai amma a hk har samari ke bibiyar ta, Hahaha to inna amma naga tunda muka zo ba wanda ke zuwa, inji maryam. Hmm ai in gaya miki duk wanda yazo korar shi take, wai ita dan mai gari take so, Maryam tasa hannuwa biyu ta matse dariyar da ta taho, ai kuwa inna bari in taya ki gyaran dakin nan inje inta tsokanan ta, ah ah maryam da kin bari ku yan birni ai wannan ba aikin ku bane, Maryam tayi murmushi lokacin da take shinfida zanin gadon, lah mama kenan to wallahi wasu yan birnin ma aikin da suke in kika gani sai kin rike baki, a’a maryam ai bazaki hada nan da can ba kinga mu fa nan ko dakan fura aka barki da shi ya isheki, balle ace ke zaki jawo ruwa kuma ki zo kiyi girki kuma fa wani lokacin ke zaki surfa ki kuma daka .. Gabanta taji ya dan fadi lokacin da ta tuno da dan guntun san isah dake makale a zuciyarta, to shi wannan dan mutumin idan ya aure ni a nufin shi ina zai ajiye ni to, al qur'an nidai bazan zauna a kauyan nan ba, wannan uban aiki!!!.To da jan ruwa zanji ko dakan ko girki. Umman anne din ta danyi murmushi ko dai abubuwan ne nan uku kadai dana lissafa sune har suka saki dogon tunani, ta dan zaro ido mama bayan wannan harda wasu ayyukan kuma, Sossai ma ai wannan wai wanda suka zama dole ne kawai na fada miki amma ai akwai saura da yawa ma ko in lissafo miki , a’a barshi wallahi mama karki dada tsorata ni wllh. Ai sai ynz ma na fahimci matan birni hutu kawai suke kinga ba kowa take girki da ice ba wasu cooker gas ma suke aiki da shi, amma a haka ma sai shegen korafi, kuma kinga ruwa mai gida ke siya, haka ma idan kina san fura shi zai siyo. Mama tace kwarai kuwa kinsan fa muma munyi zama a can kusan shekarar 9 a can. Lah allah mama kuma me ya dawo daku wannan kauyan. Mamar tayi shiru kadan sannan tace “kai maryam gaskiya fa yau kina ji da surutu. Dama haka kike ashe”, Maryam ta dan rufe ido wai alamun kunya, tace “mama kenan”. **************** 1:00 Yanzu An sallamo maman deeni, Likita ya rubuta musu magun guna sannan yace musu su kiyaye, kuma a guji abinda zai bata mata rai ko kankani ne. Ya sallame su suka koma gida, gidan kawu kenan, gidan su aliyu. Yanzu karfe 2:00 Yazeed ya isa garin Abuja, ya tsaya a hanya ya danyi sayayya, tsara ba kenan, sannan ya karasa gida. Yana shiga su siyama sukayo kansa, wato kannan sa ne su biyun, dake sun san duk zuwan da zaiyi sai ya kawo musu tsaraba, saida ya bawa kowa nashi tukunna ya karasa ya gaida maman shi. Take tambaya lafiya yace wallahi lafiya kalau, kawai na dawo yin wani abune, ina dad, Bai dawo ba inji hajiya saratu wato mamansa kenan, “Ok” ya fada sannan ya tashi ya nufi kan bene. Su maman anne kuwa da maryam suna daki sai hira suke abinsu lokacin sallah har yayi, Maryam ta fito ta tarar da su anne har sun kusa kammala girki, wato abincin rana. To uwar surutu kin gaji ko, ai muna jin surutun ki har nan, halerma ce ta fada. Cuno baki tayi tace anyi din yar sa ido kawai. Zanyi maganin ki ai yarinyar nan wato ina aunty ki amma kike fadan wannan maganar ko, Eh din anyi ta harare ta sannan ta juya ga anne budurwar dan mai gari ina gaisuwa fa, idan yazo hira yau a mika min gaisuwata. Anne kuwa daga jin haka ta gane mama ce ta fada mata, Tashi tayi ta bita da gudu da kara a hunnu suka hau zagaya gida, Sallamar da sukaji ita ce ta tsaida su.............. Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da biyu dan jin cigaba ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 31 Share This: RECOMMENDED ARTICLESAbban su anne ne ya shigo shine yasa su tsayawa cik daga inda suke suka daina guje gujen, “Abba ina wuni” kamar hadin baki duka suka fada, ya amsa “lfy lau” sannan ya kalli anne ke me yasa bakya ji ne, ai shi yasa nama hanaki ki bi su dankarki je ki kama yi musu rashin jin a can, Kwalla ce ta cika mata idano, a’a wlh abba zan natsu wallahi abba. “Abba dan allah ka barta mu tafi tare” Inji haleema kafin yayi magana maryam ma tace abba dan Allah ka barta ta bimu tunda yau yaya isah zai dawo sai su dawo tare. Jin hakan abba ya danyi jim kadan sannan yace to shikenan ba komai zata iya rakaku. Wani kalan murna da farin ciki ne ya ziyarci zuciyan anne bata san lokacin da ta daka tsalle ta kamkame maryam tana dariyar farin ciki da shewa. Au kun gani ko kunga abinda nake gaya muku ko, Ayya abba farin ciki ne fa, anne ta natsu. Wai ina yayan naku ne, wallahi har yanzu dai bai shigo ba abba, Yanzu fa 1:30 kunga kuyi sauri ku shirya sannan kuyi sallah sai ku tafe can domin kuyi bankwana da gwaggo, “to abba” suka fada. ***************** Bangaran deeni kuwa. Katan yana shiga deeni yaji gaban sa na faduwa, gadan gadan kuwa ya nufi inda deeni ke zaune farantin abinci katan ya dire a gaban deeni ko magana baiyi wa deeni ba kawai ya bata rai yana hararan deeni da jajayan idanonsa. Ganin deeni ya dake ko dan firgita baiyi ba yasa katan nan ya kara turo abinci gaban sa, “Ci dan ubanka” da wata basamudiyar murya yayi maganar, nan deeni ya fara tunanin wani abu, tabbas akwai lauje cikin nadi, to su miye damuwar su dan naki cin abinci to wallahi bazan ci ba, haka ya fada a zuciyar sa, bazan ci ba!! haka kawai ya furta. Katan kuwa ya fusata ai nin, wata kalan tsawa ya dakawa deeni wace saida tasa duka dakin ya rude, sauran police din kuwa su biyu kan kame juna sukayi hade da sa hannu suka toshe kunnuwa domin karan bana wasa bane, deeni kuwa ko kallan sa baiyi ba saidai kawai rufe kunnan da yayi. Kai wallahi badan ance kar in dake kaba da yau saika dandana azabar da baka taba ji ba a rayuwar ka, dan iska kawai wato kai har wani jiji dakai zakawa mutane ko oya zanje in dawo kuma wallahi ka tabbatar ka cinye abincin nan, ya bude kofar in daki ya fita shi kuwa deeni kallan sa kawai yayi yace ai kuwa zaka zo ka dauke abinka yanda ka barshi domin ni azumi nake ma. Su anne tuni an shirya jin ance za'a da ita yasa ta yin wanka, nan taje ta fara kwalliya, duk da ta zauna a birni amma haka baisa ta daina haukan kwaliya ba. Ta dan iya kwaliya haka ta zo ta lafta uwar hoda ja aka zo aka kara da wani janbaki shima ja kai abindai abin dariya. Maryam na shigowa ta kwashe da wata mahaukaciyar dariya sannan ta shiga kiran haleema wai ta zo ta gani, su anne anyi kwalliya. Ita kuwa anne murguda mata baki kawai tayi ta shige, ina ruwanki yar sa ido kawai, lokacin ne haleema ta shigo dakin itama dai abin ya bata dariya amma kawai sai ta basar ta ce anne kyale waccan yar adawa ce. Nan haleema ta dan gyagyara mata, “Wow masha'allah maryam ce ta fadi haka da tayi tozali da fuskar anne, kinga yanda kikayi kyau kuwa annesah, ai yanzu ne kike annesah amma da anne, sukayi dariya. Haka suka fito suka hau zagaya gari ko ina sai kallan su ake can suka hango wani saurayi ya nufo su. Nan take anne ta wani daure fuska gabaki daya ta chanja fuska. Maryam ta fahimci hakan to amma ta rasa dalilin da yasa anne bata rai haka, sun danyi gaba maryam ta dawo baya inda taga wani saurayi wanda zai kai shekara15 ta tambayeshi wancan waye ta nuna saurayin da anne ta gani ta bata rai, “dan mai gari ne mana sunan sa ado”. Kai amma naji dadi wallahi amma kaci sa'a bani da ko kwandala amma da sai nama kyauta. Ta bisu a guje, tana kai ku tsayani mana duk haukan anne yau dai kam ta sarawa maryam domin abinda take yi yau yafi karfin anne ma. Isah ne a labe ashe yana kallan maryam yana binsu a baya duk abin da take yana gani, duk sai yaji ta kara shiga rayuwarsa yaji santa ya kara shiga zuciyarsa, da sauri ya bisu domin shi a yanzu ji yake baya so ya rabu da ita daidai da na sakan daya............. Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da uku dan jin cigabaGida ya bisu saida suka shiga sun dan jima sannan ya bi bayan su. Maryam ce sai zuba uban surutu take domin yau yan haka ne a kan nata. Sallama sukaji anyi. Sallamar da tasa maryam yin shiru a dole, isah ne ya shigo, can nesa da su kadan ya sami wani tsohon tirmi ya zauna, sanye yake da white t-shirt mai kyau ta kama jikinsa sai wando black jeans, ya gyara sumar kansa tayi luf luf duk da yake shi ko aski ba a kauyan nan ake mai ba, yasha gyaran fuska abindai gwanin sha'awa. To ai sai ku gama bankwanan ku zo ma tafi, ya duba agogon dake makale a hannunsa. Oh kunga fa yanzu 3:30 to wallahi minti 10 na baku. Maryam da take uban surutu daga shigowar sa taja baki tayi tsit daga eh sai aa kawai take iya cewa ita gaba daya kunyarsa take ji, kowa ya fahimci haka amma duk sai suka kyale. Isah ne daga can yace haleema wai ni kam me nawa maryam ne, kinga daga shigowata taja baki tayi shiru bayan tun daga waje nake jin sautin ta, Anne tayi farat Kunyarka take ji.. Ya harare ta, ke kuma ina ruwanki, ah su anisa anyi wanka ina za'aje ne. Yo ai dani za'aje, baba bai gayama ba ta wangale baki. Nifa ince kwaliyar nan ba'a banza ba. Haleema ce tace kai gaskiya anne an canfa ki da yawa wallahi ke kowa yasan bakya wanka. Kowa ya kama mata dariya ita kuwa ta wani sha kunu. Maryam dai kadan- kadan take satar kallan ya isah. Shima din kallan ta yake daga sun hada ido kuwa sai ya sakar mata wani murmushi wanda ke karya mata zuciya. Nan dai sukayi bankwana da kaka ta kawo uwar tsaraba irin tasu ta kauye ta basu sukayi godiya, da maryam har tace a barshi, ya isah ne yayi magana shine yasa tayi shiru. Haka suka koma gidan su anne can ma aka yo musu tsaraba har makwabtan su duk sun kawo kayan alheri kunsan dai tsarabar kauye bata wuce irin kayayyakin gona su gyada soyaya, yakuwa, goriba, taura, magarya da sauransu. Su haleema Sunyi mamaki matuka ganin irin karar da yan kauyan nan suka yi musu gaskiya ko nan sunyi abinda yan birnin ma baza suyi ba. Tafiya suke sun nufi hanyar da zata kaisu wajan hawa mota, Maryam a can gefan take, gefan dama, Ya isa kuwa yana gefan hagu, amma saida yayi dabarar da ya koma can gefan da take. Yau kam Alhmdulilah sun danyi hira da ita saida ya kasan ce su anne da halima suna hirar su dabam itama maryam da ya isah hirar su da ban, yaji dadi kwarai yanda ta sakar mai fuska yau, Sun dan yi tafiya mai nisa tukwunnan suka isa wajan hawa motar.... Karfe 4:00 daidai suka shiga Motar kano, Dake dan kauyen nasu ba mutane saida suka danyi jira akayi lodi tukwanan... Bangaran deeni.. Deeni fa ya fara jin maza domin ji yake kamar ‘ya ‘yan hanjin sa zasu fado dan yunwa, tsabar yunwar da yake ji tasa ya fara sallama rayuwarsa ma. Abuja kuwa.. Yana zaune shida yan kannansa a falo suna kallo, shi kuwa yana tunanin ya zaiyi yaja daddy gobe zuwa kano, kuma inma sunje ya zaiyi ya kaishi gidan tsafi tunda ya riga yayi kyauta da shi. Sallamar abba ce ta dawo da shi daga tunanin da yake yi, cikin fara'a ya tashi ya tari abban. Hajiya saratu tazo ta karbi jakar hannun alhaji, shi kuwa hannun yaran ya kamo suka zauna yazeed ya durkusa ya kwashi gaisuwa, sannan ya tashi ya koma kan kujera. Kai kuwa yazeed me ya dawo dakai wannan karan kai da kake yin kwana2 ko 3 wallahi dad na manta wani abu ne amma gobe zan koma, kuma sannan ina so goben in ba damuwa mu tafi tare domin mai gidan mu yace yana san ganin ka.. To masha'allahu nayi murna sosai kuma naji dadi domin kuwa na dade ina san in san aikin ka, wato dayan business din da kake, kaga kuwa gobe ko inada aiki, dole na barshi mu tafi tare tunda ba dadewa zamuyi ba, ai har momyn ka zamu iya tafiya da ita, ya kalli hajiya saratu yace ku shirya gobe zamu tafi kano domin kuwa kinga batan halleema yau kusan kwana shida bamu je ba kullum sai faman waya. To alhaji Allah ya kaimu kawai tace, shi kuwa yazeed wani irin farin ciki ne ya lullube zuciyar sa domin kuwa ya sami hanya mafi sauki da zai ja abban shi gidan sheqewa..... Karfe 7 su maryan suka iso garin kano, Alhmdulilah sun zo lafiya...... Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da hudu dan jin cigaba A tashar mota suka sauka, a daidaita suka hai basu zame ko ina ba sai kofar gidan su haleema. Wani irin farin ciki ne da azarbabi ke azalzalar haleema tun kafin su sauko da zata ruga cikin gidan, yau fa 6 days rabona da gidan nan, zuwa sukayi suka kwankwasa gidan daga ciki mai gadin ke tambaya waye, “Haleema tace nice..” Sautin murayar haleema ne ya daki dodan kunnan sa amma shi ya karyata haka domin shine yaga gawar haleema, wata zuciyar tace mai haleema ce wata kuma tace mai wannan mai kalan muryar tace. Kara bubugawan da akayi ne ya dawo dashi daga tunanin da yake, su anne kuwa ana tsatsaye sai waige waige take domin anguwar masu kudi ne komai a tsare yake a anguwar.. Dan budewa yayi a hankali, ganin haleema a tsaye tana kallan sa yasa yin sauri ya tura kyauran ya rufe, da gudu ya nufi cikin gida yana kiran fatalwa fatalwa, su ahaji sanusi ne da kuma maman haleema a falo ya kunna kallo, wai dan ya dan rage musu damuwa amma ina, ai duk lokacin da ta tuno yar tata sai ta fara zubar hawaye alhaji ya hau lallashi. Adamu mai gadi ne ya shigo a sukwane domin masifar gudun da yake abin ya baci da kyar da alhj ya daka mai tsawa ya hadawa kansa birki. Kana da hankali kuwa adamu ya zaka shigo mana gida haka da gudu kuma ko sallama babu. Wallahi alhaji abin ne ya tsorata ni, alhaji fatalwa na gani yau kiri kiri da ido na. Kai bana san shirman banza a ina kaga fatalwar, Alhaji wlh wlh karku je fatalwa ce tayi shigar yar ku haleema ta zo gidan nan domin ni nasan ba haleema bace haleema tuni ta mutu. Jin an anbaci haleema jikin maman haleema ya dau rawa duk ta kidime, tana ina muje ka kaimu, tana fada cikin wata murya mai gargada. Alhaji wallahi karku je, yi min shiru matsoraci kawai, maman haleema tuni ta fita waje ta nufi gun gate. Shiru shirun da sukaji ne yasa gaba daya maryam ta kosa taga mahaifiyarta dole ta takura musu da ita fa tafiya zatayi in yaso da safe tazo, Ya isah kuwa da jin haka yace to yanzu yanda za'ayi su su tsaya a nan kafin azo a bude, mu muje gidan naku. Haka aka bar anne da haleema a gun, su kuwa suka tafi gidan su maryam da yake unguwar ba nisa a tsakanin su. Tafiya suke suna hira ya isah ne keta jaddada soyayyarsa a gareta, ita kuwa ba abin da take so a yanzu da ya wuce taga mahaifiyarta. Tun daga nesa ta hango gidan a rufe alamu dai ba kowa kenan, basu tabbatar da hakan ba saida suka karasa suka iske gidan a garkame da kwado. To ina mum ta tafi kuma ma ai ya kamata mu iske ya deeni a gida domin a gida yake yin sallar maghriba, shidai isah ya tsareta da kallo sauraran zazzakar muryarta yake, ji yake kamar karta daina domin kuwa bazai gaji da jin muryarta ba. Kallan shi tayi duk da dare ne hakan bai hanata gane ita kawai yake kallo ba dake akwai fitulu a layin nasu. Murmushi tayi “ya isah wannan wane irin kallo ne haka kamar baka taba gani naba sai yanzu, a kunyace yace ina wani tunanine maryam idan na rasaki a matsayin mata bansan wane hali zan tsinci kaina a ciki ba, bama wannan ba, abinda yake kara bani tsoro shine ni fa dan kauye ne kuma a halin yanzu ma bansan ya matsayina yake a gunki ba.. Hakika zantukan sa sun sata jin tausayin sa, “Ya isah kasani cewa tun haduwar mu ta farko dakai na gane cewa kaine mijin da zan aura badan komai ba ma ko dan faduwar gaban da naji a lokacin”, Ya isah duk abinda ake nema a jikin namiji ka mallake shi, sannan duk macan da ta same ka ta wuce gori, tabbas ina sanka har cikin zuciyata ba wanda zai rabani dakai da kai ya isah, kai ne kuma namijin da ya fara furta kalmar so a gare ni ba shakka ina sanka ina kuma kaunarka. Wanni farin ciki ne da baya musaltuwa ya ziyarci zuciyar ya isah bai san lokacin da hawayan farin ciki suka zubu daga idanon sa ba. Sun dade a tsaye sunawa juna kallan kauna. Sai can maryam tace yaya isah muje gidan kawu nasan maman mu bazata wuce tana can ba, murmushi yayi tare da cewa to muje Ko... Da sauri tazo ta kama gate tana kokorin budewa. Alhaji ne ya karaso wajen “haba safiya ya zaki zo ki dinga kokarin bude mana gida bayan baki san ko waye ba, kisawa zuciyarki natsuwa mana”. Suna cikin haka ne sukaji an kara buga gidan tare da cewa ado ka bude mana nice, haleema ce fa, Jin muryarta ne ya kara rikita gaba daya iyayan nata sai ya zama ana rige rigen bude kofar ma. Suna budewa “haleema ce alhaji wlh ita ce ko dai gizau take wa idanuna” hajiya ce ke fadan haka lokacin da take nunawa alhaji sanusi. Abin tausayi yanda hajiya safiya ta kidime da ganin yar tata haleema, itama kukan farin ciki ta fara da sauri ta zo ta rungume maman nata tasa kanta cikin jikinta tana kuka tana cewa mama nice fa. Ta kasa cewa komai kuka kawai take, Aneesah dake gun ita kanta saida tayi kwalla shima alhaji hk. Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da biyar dan jin cigaba adsHaka suka shiga gida rungume da juna sai kukan farin ciki suke yar da aka fidda rai da ita gashi ta dawo, murna ai yau a gurin su hajiya safiya bata faduwa, haka shima alhaji, Anne dai bayan su tabi kawai wanda su basu tambaya ko wacece ba haka itama bata fada musu ba... Direct su maryam gidan su kawu suka nufa, ita kam maryam duk da dai tana cikin zullumin ganin ummanta haka baisa ta share isah ba, haka suke tafiya a jire sai hira suke irin ta masoya kamar dai wanda dama can sun shaku da juna. Sunzo wuce wa ta wajan wani mai lemu ne isah yace bari a sayawa umman tsaraba, Uhmm kawai tace, Lemun 300 ya saya aka zuba a leda. Basu dade suna tafiya ba suka karaso layin su kawu. Maman deeni yau jiki yayi sauki zaune take a kan tabarma a tsakar gida ita dai yau ta rasa me yasa gaban ta ke faduwa lokaci zuwa lokaci, haka dai ta wuni yau tun tana tsammanin wani abu yanzu har ta daina, ta kammala sallar isha’i tayi addu'o'I, maman aliyu ce take jira domin suci abinci karya huce. Su maryam sun karaso kofar gida, shi isa yace bari in tsaya ki shiga idan kin sanar da su sai in shigo ko, tace tom. Assalamu alaikum, karima wato maman deeni kafe mai sallamar tayi da ido lokacin da take kokari tashi, itama maryam daga inda take ta tsaya cik tana hawaye dan farin ciki, haka dai sukayi cirko cirko kowa sai sharar hawaye yake. Ita dai maman deeni bata gaskata abinda idanuwanta ke nuna mata ba, shi yasa ma bata karasa gun maryam ba. Suna cikin haka ne amina ta fito daga dakin lokacin da ta gama saller, daga inda take ta tsaya hade da cewa wa zan gani haka, maryan kece kuwa, lokacin ne ma maman deeni ta fahimci idanuwanta ba karya suke mata ba. Mama amina nice. Haba a lokaci guda maman deeni ta taho da gudu ta rungume maryam tare da fashewa da wani kuka mai tsuma zuciya tana fadin “maryam ashe kina raye, maryam ina kika tafi kika barni” cikin kuka take maganar, itama maryam kuka take yi mai tsanani tare da farin ciki, maman amina ma zuwa tayi ta rungume su, haka suka kankame juna ba abinda suke sai kukan farin ciki.. Isah dake kofar gida a tsaye tuni shi yafara gajiya da tsayuwa ba abinda yake ji sai sautin kuka dake tashi a gidan, shi yasa ya yanke shawarar cewa idan yaga yaro ya aika shi ya kirawo maryam.. Ana cikin hk sai ga aliyu da ya dawo daga wajan abokansa, ya iske mutum a kofar gida yayi masa isah sallama sannan ya mika mar hannu suka gaisa, har aliyu ya juya zai shiga gida sai isah yace yauwa dan Allah idan ka shiga kace anawa maryam magana, cikin rashin fahimta yace wace maryam kuma, ai mu bamu da maryam a gidan nan, eh ba yar nan gidan bace ai zuwa tayi, bai ce mai komai ba yasa kai ya shiga cikin gidan, yayi sallama yaji shiru sai sautin kuka, Ganin halin da suke ciki ne yasa shi karasawa da sauri, maryam Alhmdulilah

Chapter 6 of 9