Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 9
ya fada. Bari in shigo da bakon, ya kika bar shi a waje. Lokacin ne ya fita ya shigo da shi.. Haleema kuwa sun gama koke koken su taja Anne ta nufi dakin su tace bari in shiga inyi wanka tukun, Anne ta amsa to, halima gani tayi anne ta tsaya a tsaye sai kale-kalle take, ji dallah kamar wata baffalata na ki zauna mana, Hmm abin hada ba'a ko haleema, nan dai tayi dariya ta fada toilet din. Anne kuwa kama baki tayi tace “wai dama halima cikin wannan daular take amma har ta iya rayuwa a gidan mu wai hadda cin abinci, Hmm gaskiya na jinjina miki. Tashi tayi taje gaban mirror tana kallan kayan make-up kala-kala, lokacin halima ta fito, anne Ta kalli haleema, nifa wallahi mamaki kiki kara bani wai dan Allah ya kika ji dan zaman gidan mu da kikayi, Haleema tayi murmushi tace to ke mene nufin ki, ai ni dan banbanci kadan na gani, Hmm kadan fa kika ce? Nan dai sukai tayi. Da suka gaji da surutun sune anne ta shiga toilet itama domin yin wanka. BANGARAN DEENI KUWA: Karfe 11:00 PM Masifar yunwa da yake ji tayi yawa haka yasa shi tashi yaje ya taba kofa, Ya taba kofar kamar wasa yana murdawa ta bude kuwa, lekowa yayi ya duba ko 'ina baiga kowa ba, ya juya ya kalli abokan nasa wato yan sandan nan sunci abinci sun koshi sai barci suke harda minsharin su. A hankali cikin sanda ya fita kamar ba kasa yake takawa ba dan sanda shine har falo yana yi yana waige-waige. Wajan makeken kofar fita ya nufa, zuwa yayi ya kama kofar da niyar budewa bisa mamaki sai ji yayi....................... Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da Shida dan jin cigaba ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 35 Share This: Wata mahaukaciyar dariya yaji an barke da ita "hahahaha" can kuma ya hanga bai hangi komai a gurin bam, hakan ya kara basa damar sake kama kofan da niyan ya bude ta, amma kamar dazu dariyar kartai kawai yaji ya juyo kuma baiga kowa ba, hakan ya basa damar budewa duda yaji dariyan amma yasa hannu biyu iya karfin sa ya ja kofar, ai kuwa ta bude, waige-waige ya dingai a tsakiyan wannan makeken gidan baiga komai ba. Da gudu ya karasa gate in gidan, basa kulle kofa domin tarkon ne su a gunsu na barin gidan a bude, irin dai darkon da su deeni suka fada. Yana fitowa daga gidan yayi wata hamdala “Alhmdulilah” ya juya ya kalli gidan amma baiga koda alamun gida ba, yunwa yake ji matuka, hk ya rinka tafiya jiri na daukan sa domin yau kwanansa uku baisa komai a bakinsa ba. Haushin karnuka ya ringa ji a bayan sa sai matsowa suke, ai kuwa kafin kace me, washi manya-manyan karnuka ya hango sai haushi suke sun nufo shi, ai kuwa yace kafa me naci ban baki ba, take yaji wani sabon karfi a tare da shi tuni yaji yunwar ta baci saboda wani masi fafan gudu suke yi..... ************** Bayan gari ya waye Tun 5:00 su alhaji bashir suka dau hanyar dake alhaji sunusi ya fada musu tun jiya cewa halima ta dawo, shi yasa suke ta zumudi domin su zo taya dan uwan nasa murna. Ban garan su halima kuwa tun a daran ta shaidawa su abban nata cewa tare da yayan anne suke su sun wuce gidan su maryam ne shine ya tsince ta. Sunji dadi matuka, haka dai suka cewa yar tasu taje ta huta domin tana bukatar hutu, ita kuwa duk ta damu tunanin deeni take kuma har yanzu ta tambaye su yafi a kirga amna basu bata lafiyayyar amsa ba domin suma basu da amsar. Haka shima bangaran su maryam Aliyu kam kamar can dama abokai ne shida isah domin daren jiya ma a gado daya suka kwana. Maman deeni tayi farin ciki sosai sai dai kuma in ta tuna har yanzu batasan inda deenin ta yake ba sai taji bakin ciki. Maryam tun da suka dan natsu take tambayam yayanta wato deeni. Amina ce ta kwantar mata da hankali tace ta bari ba yanzu ba tukun sai gobe sayi magana. Tun safe kafin su karya alhaji sanusi ya aiko da mota yace yana bukatar ganin kowa da kowa na nan gidan kawu, kawun deeni yace a bari suyi breakfast mana, amma dan aiken alhaji sanusi yace “yace a gaya muku ya tanadar muku abun breakfast a can”. Haka driver ya tsaya ya jira su suka dan kintsa tukwanan suka tafi. A falo aka hadu gaba daya, ga kayan breakfast nan kala-kala, gasu nan an jejjera sai abinda mutum yake san yaci. A zazzaune suke suna jiran su maman deeni, cikin sacan 30 sai gasu sun iso ko wanne cike da farin ciki fal a zuciyan sa, haleema kam sai dubawa take amma bataga gwanin nata ba, wato deeni. Haka suka je aka jejjeru, kawu da alhj sanusi saiti daya suke, haka maman deeni da maman haleema da amina maman aliyu suma gefan su daya, a kan carpet suke a zaune, haka suma su haleema bangaren daban, suma su isah haka, abin dai abin sha'awa kamar dama family ne. Bayan duk anyi gaishe-gaiishe, Alhaji sunusi ne ya fara magana “Assalamu alaikum”, kowa ya amsa. Yace to a gaskiya baxan iya bayana muku farin cikin da nake ciki ba a yanzu, sakamakon wannan al'amari mai ban al'ajabi da ya faru wato batun mutuwar haleema. To a hakikanin gaskiya wannan jaraba wace daga Allah sannan idan...... Wayarsa ce tayi kara ya fiddo da fara'ar sa ya daga ganin wanda ke kiran nasa, wato yayan sane alhj bashir da suka taho daga abuja. Yace gasu nan sun karaso cikin kano motar su ce ta dan sami matsala a turo driver ya dauko su, cikin farin ciki yace to shikenan yaya gashi nan yanzu zai zo ya dauko ku kuna daidai ina ne? Ya kwatan ta musa. Nan da nan aka kira driver ya tafi dakko su yazeed.. Jin sun taho ne alhji sanusi yace ayi breakfast kafin su karaso, sai muyi duk abinda ya dace. Ba gardama nan aka hau ciye-ciye da shaye-shaye su ya isah kuwa sai satar kallan maryam yake dan kayan da tasa sun mata mugun kyau. ***************** Deeni kuwa gudu yake kamar me dan tsabar gudu ko gaban sa baya tsaya wa kallo ,daga ya juyo sai ya ga kamar karan zai kama kafar sa sai ya kara wuta. Sanda suka share kusan raibin sa'a suna gudun tukunna deeni ya waiga yaga ba karnukan, sannan ne ma ya lura da wai har ya kawo bakin titi, gaskiya ko shi yayi mamaki domin yanda ya tuna irin nisan da sukayi, tsaye yake bakin titi ya kai minti 20 a gun baiga ko wucewar mota daya ba, tukunnan ya hango fitulun mota ta nufo inda yake kamar ya gudu kuma sai ya tsaya. Motar in police ce yaga ta faka, godiya yayi ga allah a tunanin sa ga masu taimakon sa nan sun kara so. Abun mamaki wani kurtu yan sanda ne ya fito dauke da kulki a hannunsa bai tsaya wata-wata ba ya fara kwadar deeni a kwauri yana fadin daga ganin wannan mugu ne, shi kuwa deeni da yake ta faman kare duka kira yake wallahi yallabai ni ba mugu bane ka saurare ni yallabai, ai ina kawai kwadar sa yake saida suka mar likis tukuna suka dauke shi suka jefa a bayan mota, yan sanda uku ne biyu suka hau baya wato inda deeni yake dayan kuma ya tukasu, basu zame a ko'ina ba sai a office in su... ***************** Tuni driver ya kawo su, suka nufi cikin gidan, yazeed ne yaji kirjinsa na bugawa da sauri ya rasa dalilin haka gashi kuma sai karuwa abin yake. Su hajiya saratu ne a gaba, wato alhj a gabanta shi kuma yazeed bayan umman nasa. Baban yazeed ne ya fara shiga da sallamarsa, ganin mai shigowa ne yasa alhaji sanusi washe baki yana wata kalan dariyan farin ciki, sanda duk suka shigo. Yazeed tsayawa yayi tsitt yana kallan wani abu, sannan gaban sa na dada bugawa da sauri. Halima ce da maryam yake kallo shi kam abin gani yayi kamar a mafarki, saida ya ji tana gaida su abban nasa sannan ya tabbatar ita ce ba mafarki yake b,. dama haleema na raye, dama su mugu karya suke ashe basu kashe haleema da maryam ba, hmm tabbas bai cancanta su mugu su kara koda sacan a duniya ba. Ko gaishe da su abba bai tsaya yi ba direct dakin sa ya wuce, bai ko kalli su abba ba ya shige dakinsa dake a gidan. ................... Sai ku biyo mu a kashi na Talatin da Bakwai dan jin cigaba ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 36 Share This: RECOMMENDED ARTICLES BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng PART 37 Na Isah Bigboy Yana shiga dakin a fusace ya duba cikin wata jaka ya dauko wata Pistol ya bude ta ya zube harsashi sannan ya sakata a tsakanin belt din sa na wand, ya sake fitowa a fusace sannan cikin hanzari yazo ya wuce, har ya kama kofa zai bude sai abbansa yace: “yazeed mene haka ina zaka kake sauri haka ko gaida abbanka bakayi ba” daddy ina zuwa abinda kawai ya fada kenan bai jira wata amsa ba ya bude kofa ya fita. Gurin motoci yaje yasa makullin motar ya warce ta kamar wanda zai tashi sama.... Deeni kuwa cikin cell kake hango sa yayi tagumi duk an bubuge masa kafa, tunani yake tayi kala-kala a zuciyarsa, a gaskiya idan ya makara fa yazeed zai kai kawun haleema gidan gunkin su, shi isa duk ya matsu da su sallame sa amma ina sunki wai shi mugu ne sai sunyi bincike a kansa. DPO suke jira kuma wai shi sai 9:30 yake zuwa. Wani makeken gida yazeed ya faka tare da yin hoon, mai gadi ya leko yana ganin yazeed ne da sauri ya bude gate din dake shima yasan yazeed, a millon ya shiga gidan motar ma bata gama tsayawa ba ya bude murfin motar ya fito a fusace ya nufi cikin falon. Ko kwankwasawa bai tsaya yi ba ya tura kofar ai kuwa ta bude. A dinner ya iske su mugu suna breakfast shayi da biredi ne da wainar kwai sai indomei, ko sallama baiyi ba, tsaye cik yayi yana kallan su, a zuciya yana cewa wato na baku aiki bakuyi ba kun min karya kuma gashi sai holewa kuke abinku. Oga ne ya dago kai, Yazeed ya gani a tsaye ya zuba musu na mujiya fuska a murtuke ba ko walwala a fuskarsa.. Ah mai gida yazeed barka da zuwa kana tafe ashe kuma shine ko kira babu ai da mun tanadar maka special break da munsan zaka zo, sai a lokacin ne su mugu suka lura ma da yazeed din take duk suka tsare shi da kallo suna mai wani dan murmushi... Shi kuwa maganar ce ta ogan ta bata mai rai yaji wani tiririn bakin ciki yake ji a zuciyar sa, wata zuciyar tace ya harbe su kawai, me yake jira da su wata kuwa zuciyar tace, ya tambaye su yaji me zasu ce karya zasuyi ko kuwa.. Karku min karya, kunce min kun kashe maryam da haleeema? Dukkan nunsu saida hantar cikin su ta kada domin duk sanda suka firgice domin kuwa sun san tambayar nan ba’a banza ba, ruwa baya tsami banza kuma sun san yazeed ba imani a tare da shi, duk shiru sukayi suka kasa cewa komai, duk sun shiga tunani, ogan cikin sune ya katse tunanin da yin wani dan murmushi, Hmm oga yazeed kenan kaga ya daga hannu, Ni na kasheta Halima.... Harbi uku kawai akaji sai gasu duk a kasa, ya juya da bindiga a hannunsa tana wani tiriri. Fita yayi da waya a makale a kunnan sa, barka da safiya shi ne abinda ya fara furtawa dake mu Journalisms in zamani ne har mgnr wancan in naji. Morning hw ur day shine abunda yce: im 5yn: dad haleema an maryam they ar living. Me kake cewa kasan me kake fada kuwa.yes srry dad wllh nayi da nasani sa su mugu aikin da ni na aikata da duk hkn bata faru ba amma saukin abu ba alamun cewa sun fadi abunda suka gani.gud ka take care of ur self. Ok dad bye. Ya kashe wayan sannan yi shiga motan sa yazo gate yayi oda da nufin mai gardi yaxo ya bude mai gate amma ina yaji shiru. Abinda bai sani ba shine mai gadi yana jin harbi yayi waje da gudu, dole ce tasa sai shi yazeed ne ya fito a motan yaje ya bude gate in. Can gidan su haleema tuni an gama breakfast kowa ya kama harkokin gaban sa su alhaji bangaran su daya su uku, yau dai kawu an kashe mai zuwa kasuwa du da yaso ya fita amma haka bai samu ba, su alhaji sanusi sun hanashi dole tasa shi hakura, yanayi yana surutu a zuciya “hmm wato ku masu kudi ko? kun tara! ku bar bawan Allah ya fita ya nemo na kansa amma kunki ku barni... Haka shima isa yayi niyar jan yar kanwar sa su nufi gida in yaso sai ya dawo batun maganar auran maryam amma alhaji ya hana yace dole ya bari sai gobe domin akwai kyauta ta musamman da zaiyi mai na ban mamaki. Haka ya hakura gashi aliyu ma ya fita ya barsa shi kadai ne a wajan yayi zuru sai kale-kalle yake dake a lambu ne. Ji yayi an rufe mai ido daga baya da wasu tatausan hannaye, wani sanyi ne yaji ya ratsa duk kannin jikinsa, baiji anyi magana ba murmushi kawai yayi tare da cewa hmm anne, to na gano ki. Shiru yaji ba'a tanka ba kuma sai yaji abin zobe a hannun nan ya tabbatar da ba anne bace domin yasan ita bata da zobe............ ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 37 Share This:A GAFARCE MU NA RASHIN KAWO MUKU CIGABA DA WURI Wata zazakar murya ce yaji ta daki dodan kunnansa, ta shiga cikin kwakwalwarsa ta dinga yimar yawo. Tabbas bazai taba mantawa da zazzakar muryar maryam ba, “Hmm maryam” yace, Hmm taya ka gane nice lokacin da ta sake shi tana zagayowa ta zauna a kusa dashi, haba tayaya ne zan ji muryar abar sona in kasa gane wa ai da bakiyi magana bane shine sai in kasa ganewa. Murmushi tayi tare da cewa ya isah baka gayawa su umma abinda ke tsakanin mu ba kuma dazu kake cewa wai zaka tafi, dan marairai cewa yayi tare da cewa ai ko na tafi ma to annesah zan kai in dawo gare ki sahibata, idan ka aure ni a wane gari zamu zauna? Tabbas ta debo babbar magana, shin yanzu shi mema zaice mata ne, shima kansa ba san zaman a wancan kauyen yake ba balle ita da take dama yar birni, kai gaskiya da sake, to yanzu me zaka ce mata. Yana cikin yan sake-sake ne tace “yaya isah ina sanka, so na gaskiya kasani cewa ko a kauyenku zamu zauna zan aure ka. Wani murmushi yayi wanda ya kara bayyano kyawunsa, baice komai ba, hada ido sukayi, sun dade a haka suna kallan juna. Yazeed ne ya shigo ya faka motar sa kafin ya fito, da murmushin sa ya fito ya nufi inda su abban suke ya gaida su da kawu wato baban aliyu sannan yake gayawa abban sa ya shirya yanzu zasu je domin yaga gun aikinsa da kuma mai gidansa. Alhaji bashir ya kalle sa yace to ai a shirye ma nake, yi sauri ka zo mu tafi, amma ina kaje ne naga kana hanzari haka ko karyawa kuma bakayi ba ka fita inji abban nasa. Daddy naje wajansa ne domin ya kira ni namai wani dan aiki ne, ok to allah yama albarka tashi jeka. Tashi yayi ya nufi falo, Haleema da Maryam da Anne su duk ukun suna zaune a falo sun kunna kallo sunayi hade da hira sama-sama. Baima bi ta kansu ba kai tsaye dakinsa ya nufa, “ina kwana Ya yazeed”, Yaji ance. Juyowa yayi bisa mamaki yaga ai haleema ce, lfy lau yace har ya juwa zai bude dakin ya karaji an gaida shi da murya biyu, Maryam da Anne ne, suma haka dai ya cije lebe ya amsa sannan ya wuce dakin nasa. Kan gadonsa ya haye yana jin wani tiriri da zafi a zuciyar sa. Wanni bangaran kuma tunani yake taya zai hallaka su tun kafin su tona mai asiri domin tunani yake sun san ko shi waye, amma yayi mamaki da basu fadawa kowa ba, yaji kamar ya kyale su hallarcin da suka mai na kin tona masa asiri, saidai kash!! Lokaci ya kore dole ya kashe su domin kuwa a duniya banda su ba wanda ya san ko shi waye sai yan kungiyar su. Mutanan gari a yaro mai ladabi mai girmama na gaba da shi, mai kyauta, san addini, kyakykyawar tarbiya kawai suka sanshi, ba wanda yasan mugun abinda yake aikatawa, kuma ya shafe sama da shekaru 4 a cikin wannan kungiya. Tashi kawai yayi rai a bace, ya fito da wayarsa yayi kira wata number “da fatan ashirye kuke domin ina zuwa da mahaifina”. Eh a shirye muke kawai a ka fada ya katse wayar ya shiga bandakin dake cikin daki, yayi brush tukwanan ya dan watsa ruwa ya fito ya chanza kaya, Jeans baki yasa sai wata riga T-shirt mai layika shudi da fari, ya taje gashinsa, yayi kyau sosai tukwanan ya fiton daga dakin. Su haleema da ke zaune a falo suna shiriritar su. Tun kafin ya karaso gunsu kanshi ya cika su,gaba daya kamar hadin baki suka juya suna kallan sa shi kam ko damuwa baiyi da su ba ya wuce waje abinsa. Haleema kam yayi mata kyau yau, tace wa maryam kinga mutumin yau anci gayu ko dai zance zashi, kinga ba ruwana kinsan dai halin sa ... Hhhhh dariya halima tayi au ashe baki manta ranar ba, Maryam ta kama baki tare da cewa hmm wane ni in manta, Anney kuwa tambaya ta shiga yi wai me akayi wancan ranar, suka share ta. Can halima ta dago ta kalli anney "ohh yi hakuri anneesat, bari in gaya miki abin da ya faru wancan rana." Kamar kullum duk weekends maryam na kawo min ziyara ko ni in kai mata............ ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng part 38 Share This:HALIMA TACI GABA DA BAWA ANNE LBR: Ranar wata lahadi maryam ta kawo min ziyara kamar yanda kika ganmu yanzu to haka muka zo falo muka kuna kallo sai hira muke abun mu, yazeed yana gidan wato ya kawo ziyara. Maryam ta tambaye ni miye tsakani na da yazeed da muke faman fada da shi haka, nace mata wai kawai dan na shiga dakin sane kinsan ya hana, “to miye a dakin nashi da yake hana shiga, naga dai ba komai ne a dakin gauro ba daga kati fa sai jakar kaya” inji maryam. Nace mata to shi wannan ba haka yake ba domin shi abubuwa sunyi yawa a dakim nasa domin harda wani abu na gani ma a rufe da wani zane, haka nake gayawa maryam a lokacin, ita kuwa kin ganta nan da karan bani tana jin haka naga ta mike. Nake tambaya ina zata tace wai dakin ya yazeed, wai in taso muje tunda baya gida nace mata wallahi ni bazan je ba kuma kema ban goyi bayan kije ba idan kika je duk abinda ya same ki toh ni ba ruwa na, tace ita dai wai yasin sai taje ta bincike dakin taga wai miye da yazeed baya san a shiga. Ai kuwa kamar wasa maryam ta nufi dakin ya yazeed ni kuwa kallo ya dauke min hankali ban kula ba har ta bude dakin ta shige ba tare da fargabar komai ba domin nace da ita baya nan. Nidai ina nan sai kallo na nake nama manta da maryam ta shiga dakin, ita kuwa bincike-bincike ta hau yi chan ta hango laptop dinsa, ai kuwa taci sa'a ba password a jiki, haka ta haye mai kan gado tana ta danne-danne abinta. Ganin shiru-shiru maryam bata fito ba yasani tashi na bita, abin mamaki a kan katifa na ganta da kwamfuta sai wangale baki take bata ma ko kula da na shigo ba, hakan yasa naje da sauri ke maryam wai me kike yi ne haka, kinzo kin wani zauna a dakin mutum bayan kinsan idan ya dawo ya tarar dake sai ya wulakanta ki gashi kuma kinsan mama bata nan wallahi duka zai miki. Yayin da nake karasa wa wajanta ta dago min wani hoto dake jikin laptop din, yazeed ne cikin wasu jajayen kaya, fuskan sa duk ya shafe ta da wasu zanuka. Nan muka yada zango a kan gadonsa muke ta kallan hotunansu shida wadan su abokan sa, mun kusan share minti 30 muna kallan hotunan amma bamuga karshen su ba haka yasa muka koma wani bangaran. Da nace aje videos amma Maryam taki yadda, haka yasa na kyale ta badan naso ba ta kamo games nan ma mukata bugawa, ni dai na nace a kan sai an shiga videos nashi, “ kin cika naci da yawa wallahi ke da almajira ce da masu masu sun shiga uku wallahi, bari a shiga videos din" Mu kam sai shagalin mu muke yi ba ruwan mu mun ma manta da a dakin wa muke. Nan maryam ta nufi kan videos ni kam nayi mamakin yanda ta iya computer haka ma domin nasan bata da ita, hakan yasa na tambaye ta a ina ta koya tace a laptop din yaya deeni mana, ta shiga bude videos, video farko ya ruda mu gaba daya jikin mu ya fara rawa a tare tuni muka kankame juna domin kuwa abinda muka gani ne yafi karfin tunanin mu. Anne tayi zugum ta saki baki sai sauraren labari take yi, gani tayi halema na waige-waige saida taga ba kowa sannan ta yi kasa kasa da murya sosai sannan take cewa “anny wallahi in gaya miki annesah yazeed ne a videon ya rike wuka yana yanka mutum, kuma dan yaro gashi nan jage-jage duk jini shi kuwa sai yanka sasan jikin wannan yaran yake, yaro ne fa dan shekara baifi 7 ba. Ganin haka ya firgita mu da gudu muka tashi a tare ni da maryam da niyar muyo waje ko laptop din bamu wani tsaya kashewa ba, abin mamaki ina kama kofar yazeed shima ya turo da niyar zai shigo. Karki so kiga yanda mukayi baya a wani firgice ni kam bansan lokacin da na shiga basa hakuri bama, maryam kam tuni ta fara kuka, shi kam da ya shigo tsayawa yayi chak ya kare wa dakin kallo yaga duk an bincike mar daki can ya hango laptop dinsa a kunne tana kallo. Daga jin sautin video ya gane ko wannene, haka yasa shi kulle dakin da mukulli ya koma can gefan katifarsa ya jawo computer ya kashe tukun,ya hada hannuwa biyu ya dora a goshi alamun yana tunani kenan.. Anne in takaice miki labari wallahi ranar mun daku domin samun mu yayi kamar yayan sa ya dinga lafta yana fadin zaku kara, muna kuka muna a’a, saida yayi mana dukan tsiya sannan yace muyi shiru, ya zazzare mana ido tare da cewa wallahi muka sake muka kuskura wannan maganar ta fita duk sai ya kashe mu. Hakika mun tsorata ba yanda muka iya haka ya bude mana kofar muka dawo falo muka sha kukan mu. Kinga zancen nan dana fada miki ko to wallahi ba wanda na fadawa ko ummana da abbana basu sani ba domin nasan wannan mugun zai iya aikata komai, Halima da tazo nan ta juya ga maryam, “ke ko kin taba gaya wa wani”, “ni nama isa” inji maryam. Ai tun lokacin na kama baki na nayi shiru gidama da naje mama tayi kokarin gane miye ya same ni amma naki fada mata nace ba komai. Anne ta rike baki tare da girgiza kai chabb!! Wallahi idan nice sai na tona asirin sa a kan me, ke rufawa kanki asiri idan kika fada akaje kuma ba'a kama sa da hujja ba ya zaki ce? Jikin anne yadan yi sanyi, kinga ba muda mafita ne, kawai kedai ki bari rana dubu ta barawo rana daya ta mai kaya ko ba haka bane? Haka ne inji anne sannan ta mike “matar yaya zo ki dan rakani mana” inji anne take fada mawa maryam, maryam ta mike tare da cewa ina? “Dakin yazeed mana da sauri maryam ta koma ta zauna tare da cewa ba dani ba, ai kuwa duk suka kyalkyace da dariya. ******************* Deeni kuwa yana can sai fargaba yake, shi kam yama rasa me ke mai dadi domin yasan jinkirinsa nada mummunan hatsari indai har yazeed ya samu damar tafiya da abban sa wancan gidan tabbas akwai matsala, domin kuwa dodansu za'a bawa shi, gashi yayiwa yan sandan nan bayani amma ina sunki sauraran sa wai kawai basu yarda dashi ba muna fiki ne. Shigowar DPO ce ta dansa zuciyar sa ta danyi sanyi........ ads BANI NA KASHE TABA daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng daga www.hausaebooks.com.ng Part 39 Share ThCan yaji shigowar DPO hakan tasa ya sami yar natsuwa, saida suka yiwa DPO din bayani tukwanan ya nufi wajan deeni, shi kuwa dama kamar shi yake jira, yana isa deeni ya gaida shi ya amsa tare da karewa deeni kallo, “kai gaskiya wannan ba mugu bane” haka ya fada a zuciyar sa tare da zuwa gab da deeni ya tsuguna a cikin cell din, " kalle ni nan ina so ka fada min gaskiya who ar u? Deeni da hawaye tuni sun cika mar ido ya fara bayani sunana zahradeen kaza da kaza dai ya fada mai kaff labarin sa har mutuwan halima, dama tserowar sa. DPO ya yi wani ajiyar zuciya sannan yayiwa deeni wani kalan kallo yace “ka tabbata?” eh na tabbata, ban maka karya ba, ok yanzu kace yazeed ya bayar da mahaifin sa? kwarai da gaske kuma yallabai jinkirin mu ma ba karamin hatsari bane ya kamata muje ka tabbata da kanka. Bai gardama ba yace a kunce deeni, wani kurtun dan sanda ne yaje ya cire mai ankwar dake sanye a hannunsa, sannan DPO din ya dauki mutum 4 daga cikin yaransa tare da shi da kuma deeni suka hau mota kai tsaye suka nufi gidan su haleema, shikam deeni godewa Allah yake yayi da DPO nan ya fahimce shi, a zuciyar sa da yana tunanin ko DPO in mugune amma yanzu kam yaga sabanin haka.. *************** Yazeeed kuwa yana fita daga falo ya nufi gun da su abbansa suke a zaune, su uku ne suna hira, da baban sa da kuma wan babansa sai kuma baban aliyu wato kawu. haka yaje cikin ladabi (kunsan ance mai san kayan ka yafika dabara) yaje ya sami abbansa yace dad na shirya, “ok mu tafi kenan” a cewar abban nasa, yauwa ai kuwa ina ganin gwara kawai mu tafi mu duka tunda kaga wadannan suma iyayan ka ne ya nuna su kawu, lokaci daya yazeed ya bata fuska yaji ana shirin bata mai shiri, a’a dady kawai gwara dai mu tafi mu biyun kasan mai gidan nawa bai cika san hayaniya da yawa ba, abban haleema ne ya kalle sa tare da yimai dakuwa uku “nace wato mune zamu mai hayaniyan ko, to dai mu nan duk iyayan kane kaji na gaya maka” sunkuyar dakai kawai yayi. Wayar alhaji sanusi ce tayi kara ganin wanda yakira ne yace to ni ga ma kira ya shigo wayana kuje kawai domin wani abokin kasuwanci nane kuma zamu dade muna waya, alhaji bashir ya tashi yana murmushi to ai shikenan

Chapter 7 of 9