Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
nan tsaye, hasken kwan wutar dake makale a kofar gidan ya hasko fuskarsa ta jike jargaf da gumi jikinsa sai rawa yake. Har sa'ar da Hilal ya tuka motar ya bi duhun dare Dakta Sadi na nan tsaye baki bude yana kallonsa. Hilal ya yi imani da cewa dole ne gobe war haka dakta Sadi ya yi jiransa. Koda ya hau kan titi sosai sai wani tattausan murmushi ya subuce masa a ransa ya ce. Sauran matakin QARSHE******** D.P.O din jami'an tsaron ya dubi fuskar kyakkyawan mutumin cikin shakka da zargi amma acan cikin zuciyarsa ya fara zuzzurfan tunani tabbas shekaru ashirin da daya da suka wuce ya taba jin wani kyas me kama da irin labarin da wannan mutumin yake bashi. A gurin tsohon D.P.O na ofishin yan sanda ya taba samun labarin wanda D.P.O din dan uwane a gareshi shi ne ma ya yi sanadiyyarsa shiga aikin dan sanda. "Malam ka tabbata da abin da kake fada? Domin idan fa muka je muka kama mutumin muka ji ba haka bane kai zamu rike?" Hilal ya gyada kai sannan ya ce "Yallabai na yarda ni dai abin kawai da nake son ku min shi ne." Hilal ya fara yi masa bayani da sauri da sauri.******* Sabanin ranakun baya yau tun karfe hudu Zuhuriyya ta caba kwalliya ta fesa turare sannan ta buda kundin hotunan ta ci gaba da kallo tana jiran isowarsa. Tabbas shi ne ni daman na san na taba ganinsa. Zuhuriyya ta ce da kanta sa'ar da ta ci gaba da kallon kundin hotunan. Hoton dake gabanta tsohon hoto ne wanda aka dauka ranar bikin zagayowar shekarunta hudu a duniya. Su uku ne a hoton mahaifiyarta da kuma kyakkyawan saurayin da ya dora ta a cinya yana mika mata BINDIGAR ROBA . A kusa da kan saurayin an rubuta (HILAL) Tabbas in dai har ba shi bane to dan uwansa ne. Zuhuriyya ta ci gaba da nanatawa kanta Hawaye ya subuce mata sa'ar da ta dubi hoton mahaifiyarta. Ina ma tana raye.. Da ta tabbatar min ko shi wane ne. Zuhuriyya ta ce cikin zuciyarta. Sannan ta dada kallon hoton ko shakka babu wannan saurayin da ya dorata akan cinya shi ne mutumin da ta karewa kallo a yammacin jya. In ba shi bane me ya sa zai yi kira na da Zainab. Hakan na nufin ya san mahaifiyata kenan...me yiyuwa kama na yi masa da ita. Zuhuriyya ta ci gaba da zancen zuci. To koma dai wane ne ko ta sanshi ko bata san shi ba ita dai ganinsa ya sa duk kaunar Dakta Sadi ta fita daga ranta cikin kwana biyu kacal. Zuhuriyya ta ajiye kundin hotunan sannan ta dubi agogo karfe bakwai saura. Nan da nan ta ji tsoro ya kamata kada fa ya ki dawowa...shi da muka yi da shi zai dawo. Haka nan zuhuriyya ta yi ta jira har karfe taran dare babu labarin mutumin ta. Daga karshe dai tana share hawaye ta nufi daki za ta cire kayan kwalliyar da ta caba, sai ga shafi'u ya sheko a guje. "Zuhuriy...ga wannan mutumin a waje wai yana kiranki." Hilal ya dubi zuhuriyya, ita ma ta dubeshi. Sai yanzu ka ga damar zuwa." Zuhuriyya ta ce tana dubansa. Cikin damuwa. "Ki yi haku...wallahi mahaifiyata aka kwantar a asibiti." Zuhuriyya ta dafe kirji. Mamanka aka kwantar...a wane asibitin?" "A asibitin mahaifinki mana yanzu ma can zan koma shi ne nace bari na biyo ta nan mu nemi alfarma tun dazu muke can babu likita da zai dubata shi ne na ce me yiyuwa za ki iya hadamu da...mutumin ki...mijinki dakta Sadi." Zuhuriyya jiki na rawa ta ce. "Bari to na shiga gida na fadawa matar babanmu in da zani ka ga dare ya yi, kuma babanmu yau zai sauka karfe goma sha daya na daren nan kada ya dawo ya tarar bana nan ya yi ta fada." "Je ki fada mata." Hilal ya ce sannan sai ya dan hade fuska na karya. Daman mamanki ba a gidan take ba?" Nan da nan ya ga fuskar Zuhuriyya ta yamutse, bai ji dadin tambayar da ya yi mata ba to amma dole ne ya tabbatar. "Ni...babata tun ina karama ta mutu AKA KASHETA******* . Ya ya ka shiga ta nan?" Zuhuriyya ta tambayeshi cikin mamaki sa'ar da ta ga Hilal ya shiga ta kofar da zata kai su rukunin gidajen ma'aikata asibitin. "Na dauka ta gidan Dakta Sadi din za mu bi sai mu wuce da shi cikin asibitin." Zuhuriyya ta dan yi jim, domin ba ta son su je gidan Dakta Sadi din tare. "Na san abin da kike tunani." Hilal ya ce da ita cikin murmushi. "Idan mun je kya iya cewa da shi ni kanen babarki ne." Zuhuriyya ta harareshi ta ce. "Ah, ni dai ba abin da kake nufi nake tunani ba." Sannan sai ta hade fuska. "Me ye to in ma ya ganni da kai din." Suka fito daga cikin motar babu magana sannan sai Zuhuriyya ta wuce gaba Hilal ya bita abaya suka nufi gidan. A daidai lokacin da suka isa jikin jerin bishiyoyin dake gidan ne to Jami'an tsaro suka fito kamar aljanu suka zagaye su. Zuhuriyya ta rike numfashi a tsorace ta dubi masu bakaken kaya dake zagaye dasu bata iya ganin fuskokinsu amma tana iya ganin duzuzun gashin bakin bakin katon dan sandan dake tsaye a gabanta. "Ka da ki ji tsoro yan mata ba wani abu za a yi miki ba." Zuhuriyya ta dubi Hilal a tsorace tana neman taimako. Ga mamakinta sai ta ga Hilal ya matsa daf da ita da murmushi sannan ya ce da ita cikin rada. "kada ki ji tsoro Zuhuriyya, ki yi duk abin da suka ce ki yi yanzun nan ba da dadewa ba za ki ido biyu da wanda ya kashe mahaifiyarki tun kina karama". Hilal na gama fadin haka sai ya ce cikin wata murya kasa-kasa. "Yallabai ka zagaya can bayan da ita inda zaku iya sauraron mu." jikinta na rawa, hawaye na zuba saboda tsoro da rudewa Zuhuriyya ta bi yansandan zuwa bayan gidan, a zuciyarta tana addu'ar Allah yasa ta farka ta ga kawai mafarki take yi.******** Hannayensa cikin aljihu Hilal ya karanta addu'arsa ta karshe ta neman sa'a sannan sai ya danna kararrawar gidan ko dakika goma ba a yi ba kofar ta bude. Dakta Sadi ya dubi Hilal a tsorace. "Shigo daga ciki Hilal tun dazu kai nake jira." Abin ya yi matukar girgiza Hilal saboda jin ya kama sunansa haka nan ya lura babu alamun tsoro sosai a cikin muryarsa. Hilal ya bi shi a baya suka shiga wani matsakaicin dakin shakatawa mai dauke da kujeru sun yi masa kuri sama da arba'in, daga bangaren gabas, wata katuwar talabijin ce mai kamar bango, a kasa da ita (Video) ce da (VCD) da kuma na'urar kamo tasoshin talabijin na duniya. Dakin ya yi matukar tsaruwa. "A kawo ma lemo?" Dakta Sadi ya tambaya. "Hilal ya girguza kai cikin kaduwa. "Na san za ka yi mamaki jin na kira sunanka kai tsaye, to idan kana mamaki ma ka bari, domin a cikin shekaru ashirin da daya da suka gabata babu wanda nake kwana nake tashi da shi a rai sai kai, domin kai kadai ne shaidar ido-da-ido wanda ya ganni lokacin da na kashe TSINANNIYAR KWARTUWAR NAN HAJIYA ZAINAB . ****Wash Nagaji Bari Na Huta****BINDIGAR KWALI-20 . ƘARSHE...... . Kai kadai ne shaidar ido-da-ido wanda ya ganni lokacin da na kashe TSINANNIYAR KWARTUWAR NAN HAJIYA ZAINAB .......A can bayan gidan a tsaye jikin tagar dakin Zuhuriyya ta ji abin da ya ce, dan haka sai ta bude baki za ta kwalla ihu a rude, wani dan sanda ya zaburo ya rufe bakinta da hannu. "Lokacin da na sami labarin an neme ka an rasa na ji dadi domin hakan ya ruda jami'an tsaro masu bincike a wancan lokacin. Sun yi tsammanin kaine ka kashe ta." Dakta Sadi ya dan yi shiru. "Sai gashi yanzu ka dawo da jiya yau. To abin da nake so ka sani Hilal shi ne a yanzu haka idan aka duba tsohon fayil na jami'an tsaro kamannin wanda ake nema naka ne wanda shaidu suka bayar domin kaine mutum na karshe da aka ga ya fita daga gidanta a ranar da na kasheta." Dakta Sadi ya bushe da dariya. "Ka san duniya ba ta rabuwa da yan tsurku irin su DAN BA'U me tireda na kofar gidan Hajiya Zainab a wancan zamanin." Dakta Sadi ya dan yi shiru yana nazarin fuskar Hilal akwai wani abu da ke bashi tsoro a yanayin fuskar saurayin da ya girma ya zama mutum a halin yanzu ko kadan mutumin bai tsorata ba. Dakta Sadi ya ci gaba da cewa. Idan na ga dama yanzun nan sai in damkawa jami'an tsaro kai". A karo na farko sai Hilal ya dubeshi a murmushe ya ce. "Kuma duk da kashe uwar da kayi bai isheka ba shi ne kake son ka auri yar ta itama kasheta din kake son ka yi." Dakta Sadi ya yi murmushi "Wannan duk fadin bakinka ne anan amma baka da shaidar da zaka nuna wa jami'an tsaro su yarda da abin da ka ce ni kuwa yanzu idan na ga dama sai in mika ka garesu domin sun dade suna sane da kai." Hilal ya mike tsaye da faffadan murmushi sannan ya dubi Dakta Sadi ya ce. "Ka san dai ai ba ni na kasheta ba kaine ko ??" "Kwarai kuwa ni na kasheta da hannu na amma ba ka da shaidar hakan ko kana da ita?" "Kwarai kuwa." Hilal ya ce sannan sai ya daga murya ya ce. "Yallabai kuna iya shigowa." "Kafin kiftawa da bismillah jami'an tsaro sun cika dakin shakatawar. Dakta Sadi ya rude a tsorace ya dubi jami'an tsaro. "Kun...kun san dai ba ni na kasheta ba ko...shi ne ga shi nan." "Idan mun je ka fadawa alkali." Shugaban jami'an tsaron ya ce sannan sai ya mikawa Hilal hannu ya ce. "Ba ni abin da na baka." Daga cikin aljihunsa Hilal ya dauko wata yar karamar rediyo baka wacce ke dauke da duk maganganun da suka yi da Dakta Sadi ya mikawa yan sandan. A daidai lokacin da suka bugawa dakta Sadi ankwa sai suka ji motsi a bayansu. Suka juya baki daya. Zuhuriyya ce ta shigo idanunta cike da hawaye ta zo kusa da Hilal tana rike da hannunsa kamkam ta ce. WALLAHI NA GANE KA HILAL" Hilal ya dubeta da murmushi sannan ya dubi dakta Sadi ya nuna shi da dan yatsa ya ce. "Kin ga wanda ya kashe mahaifiyarki yau dubunsa ta cika." Sannan sai ya dubi Dakta Sadi ido da ido ya ce. DA'ACE KANADA SAURAN YANCI DA NA GAYYACE KA AUREN MATANA BIYU 2 . KARSHE . JIKAN SIDI MAI JAKA (YARIMA GANGARIYA) Kasancewar Paper Daya Wacce Kuma ita ce ta karshe a cikin wannan littafi ta bada matsala ma'ana paper din tayi (damage). dan abin da ya saura na daga labarin wanda baku ji ba yana cikin wannan paper din da tayi damage duk da yake ma dai babban abin da kowa yake so ya ji bai wuce yadda Hilal zai auri Mata biyu Rukayya da Zuhuriyya a lokaci daya ba to amma idan kuka yi la'akari da soyayyar da Rukayya take yi masa idan ya zauna ya bata labarin duk abinda ke tsakaninsa da Mahaifiyar Zuhuriyya wacca kuma itace sanadiyyar barinsa gida har tsawon Shekaru ashirin da daya dakuma yadda akayi har aka kama mijin da zata aura bazataki amince masa auren zuhuriyya ba ya hada su tare in yaso tunda Rukayya ce babba sai ta zama uwar gida ya fara aurenta daga baya kuma sai ya auri amarya Zuhuriyya. . ALHAMDULILLAH .... Godiya tabbata ga Allah dayabani ikon gama kamumoku wannan littafu mai suna BINDIGAL KWALI An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7