Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 7
kuma shi ne, ya yi masifar kamuwa da ciwon sonta, irin tsananin kaunar da ko rabuwa da ita bai son yi, katsam sai ya ji haka kawai ya tsani mijinta, ba a dade ba kuma sai zuciyarsa ta fara raya masa cewa dama ace kada Hamisu Jumare ya dawo garin, da ma ya makale a can... Zuciyarsa ta buga, domin ya san abin da take nuna masa, ko shakka ba ya yi, fata yake yi dama ace mijin zainab Alhaji Hamisu Jumare ya mutu a can. Zuciyarsa ta ci gaba da kawo masa hanyoyi kala-kala, mota ta yi karo da shi a ciki wata zuciyar kuma ta ce dashi dama jirgi ya fashe dasu a sama.. "Tunanin me kake yi ne? Hilal ba ka ce dani komai ba, ko ba ka kaunata ne?" Hilal ya juyo firgigit ya yi ajiyar zuciya ya dubeta "Ina... Kaunarki Zainab, sai dai kuma duk a banza." Zainab ta dubeshi cikin kaduwa ta mike tsaye ta dafa hannayensa. Hilal ya yi sauri ya janye hannunsa. Ta sake rankwafawa ta ce. "Me kake nufi da cewa kana kaunata a banza?" "Saboda kina da miji". Zainab ta ji kamar ya watsa mata wuta. "Amma ai duk da hakan dai kana kaunata ko?" "Ki dubi idanuna Zainab kin san ai ina kaunarki". Ya shafi fuskarsa a hankali. Suka dan yi shiru na dan lokaci, suna duban juna, sannan sai Zainab ta ce. "In dai kana sona, to za mu ci gaba da haduwa ko da kuwa mijina yana gari" Hilal ya dubeta cikin mamaki ya ce "Ta ya ya?" "Ta hanyar da ta ke bi idan tana son yaudarar mazaje" Wata kakkausar murya ta ce dasu daga baya, sannan sai muryar ta dada da cewa. "Ja da baya Zainab kada ki sumbaci kaninki, ba kya ganin kin girmeshi" Hajiya Zainab ta ji wani abu kamar ruwan kankara ya surtato daga goshinta . Mutanen biyu suka yi sororo kamar wadanda suka yi gamo da aljanu Abin da ya fara zuwa zuciyar Hilal shi ne kashinsa ya bushe domin ko shakka baya yi ya san wannan muryar Alhaji Hamisu Jumare ce To amma a bangaren zainab abin ba haka yake ba domin ita ta fi kowa sanin mai muryar Ta juyo a hankali tamkar sitiyarin mota sannan suka yi ido biyu da mai kakkausar murya. Dakta sadi ya yi murmushi. "ki yi hakuri Hajiya Zainab na saki kaduwa ko? Wallahi nima ba haka na so ba to amman dole ne na ce wani abu in dai har zan yi la'akari da irin kalaman abin kunyar da ke fita daga bakinki shin ke ba kya girma ne da hulda da yara? "Fuskar Hajiya Zainab ta sauya launi tun da take ba a taba fada mata maganar raini irin wannan ba "Fice daga gidan nan' Ta ce cikin fushi tana duban dakta sadi. Dakta Sadi ya yi murmushi sannan ya dubi Hilal wanda ke zaune kamar gunki gumi na kwarara ya ce. "Dan samari tashi ka fice daga gidan nan tun kafin mijinta ya rutsa da kai ni zan iya rufa maka asiri a matsayina na abokin mijinta" Nan da nan Hilal ya mike cikin gaggawa bai ko dubi Zainab ba ya nufi kofar gidan jikinsa na rawa Dakta Sadi ya bushe da dariya Zainab ta bi abin son ta Hilal da kallo cikin takaici domin kwakwalwarta ta kasa tunanin komai sannan sai ta dawo da kanta ga duban Dakta Sadi tsana da kyamarsa karara a fuskarta Sadi ya yi mata murmushi ya ce. "LOVER WOMAN" Dubanni da kyau ko ki so ni ko ki kyamace ni duk a banza domin ni yanzu na gama dake kudin ki kawai nake so "Idan na ubanka ne ba sai ka dauka ba na ce dakai ka fice daga gidan nan ba na son sake ganin fuskarka ko da kuwa a mafarki ne idan kuwa ka ki wallahi zan sa a yi maka dan banzan duka a fitar min da kai Dakta Sadi ya sake fashewa da dariya. Ka da ki yi haka Zainab abin ai bai kai da zage-zage ba na san duk abin da kike fada ai ba ki isa ki sa a aikata haka a kaina ba yanzu ke kya so na bada labarin holewar da muke yi ni da ke? Hajiya Zainab ta ji jikinta yayi sanyi ta dubeshi cikin takaici ta ce "Na ce da kai ka fita "Na ce da ke ba zan fita ba" Dakta Sadi ya ce yana zazzare idanu. "To zan sa kuwa yanzun nan a yi waje da kai" Dakta Sadi ya dada bushewa da dariya Hajiya Zainab ta ji zuciyarta kamar za ta rabe gida biyu. "Na san duk abin da kike fada da barazanar da kike yi wai za ki sa a yi waje dani duk bindigar kwali ce, harsashin ruwa, domin baki da hujjar aikata haka a kaina dan ke kika fara gayyata ta da na zo gidanki, na tayaki jin dadin rayuwa to kuma dan yanzu kin samu dan kyakkyawan saurayi da ya fi ni kuruciya sai ki a wulakantani. To bari ki ji ko dai ki saurari zancen da na zo miki dashi yanzu ko kuma na bata ruwa" Ya yi mata murmushin mugunta "Kin san abin da nake nufi da bata ruwa?" Ta kalleshi cikin takaici ba ta amsa ba ya ci gaba da cewa "Sai na raba ki da dan kyakkyawan saurayi Hilal. Na san kin mutu da kaunarsa ba za ki so na rabaki da shi ba ba kya ganin tuni ya fara tsorona ya dauka ni fa da gaske abokin mijin ki ne." ya dan yi shiru yana dubanta. "Idan kuma kina son ki fitar da kanki, to sai ki ce dashi ya daina tsorona, ni ba abokin mijinki ne ba masoyin ki ne a boye. Za ki iya? Ya dubeta ya sake bushewa da dariya ya buga kafa tim kamar dan bori.*** "Yan sauran tsirarun samari da yan matan da har yanzu suke holewarsu a farfajiyar gidan suka mimmike tsaye daga mazaunansu. Suka daga kawunansu kusan lokaci guda suna masu duba izuwa ga sararin samaniya cikin mamaki. Hakan na da nasaba ne da rugugin aradun da suka ji babu zato ba tsammani ya ratsa shirun dake makale a sararin samaniyar. Duk da yake dai suna da masaniyar cewa a tsakiyar damina ake to amma ba su tsammaci za su fara jin rugugin aradu ba maimakon iska. Hajiya Zainab ta dubi Dakta Sadi shima ya dubeta, a daidai lokacin da suka ga samari da yan matan sun nufo inda suke. Daya daga cikin yan matan dauke take da Zuhuriyya. Dakta Sadi ya dubi Zainab ya jefeta da fatalwar murmushi ya ce da ita cikin murya mai karancin amo. "Ki sameni a dakin shakatawa kafin Hajiya Zainab ta ce dashi wani abu, tuni ya bi jerin fulawowim da suka yi sahu-sahu tun daga inda suke har zuwa kofar da zata kai shi kofar shiga babban falon gidan. Hajiya Zainab ta ji wani abu mai kamar gare-gare ya fara mirginawa wur! Wur!! Wur!!! A cikin kwakwalwarta kadan ya rage tasulale a gurin ta fadi kasa saboda bakin ciki. Ta zargi kanta da kanta domin ita ta janyowa kanta duk abin da ya faru. A haka samari da yan matan suka sameta kyakkyawar fuskarta sharkaf da gumi kamar wacce ta yi ido biyu da ifiritu. "Hajiya mu za mu tafi". Anti Zaliha ta ce da ita sannan lokaci guda kuma ta mikawa Zainab Zuhuriyya wacce tuni ta fara gyangyadi akan cinyar Zalihar. "To Zaliha na gode wallahi" Sannan ta juya ga sauran samari da yan matan BINDIGAR KWALI--> 5 . "To Zaliha na gode wallahi" Sannan ta juya ga sauran samari da yan matan wadanda mafi yawa daga cikinsu duk malaman asibitin su ne. Ta mika godiyarta a garesu. Sannan ta sallamesu da alakoron tattausan murmushin da bai kai idanunta ba domin ba su bane a ranta*** Ba karamin kaduwa ta yi ba lokacin da ta shiga dakin taga Dakta Sadi zaune akan daya daga cikin luntsuma-luntsu man kujerun alfamar da suke falon sigari a hannunsa, hancinsa da bakinsa na ta fitar da hayaki kamar salansar jirgin kasa bugu da kari kuma hannunsa na hagu rike da kofin tangaran mai dauke da tsaftataccen lemon alfarma yana kurbawa abinsa. In ya busa hayaki sama sai ya kurba lemo kai kace gidan ubansa ne. Zainab dauke da zuhuriyya a kirjinta ta dubeshi cikin takaici ta ce. "kana da gado a gidan nan ne? Wai me ka dauki gidan nan ne? Bariki kome? Dakta Sadi ya yi murmushi sannan ya kurbi lemonsa ya ce. "To me ye marabarsa da barikin ? Ko kuwa ni mijin ki ne ?" Cikin kunar rai ta wuce zuwa dakin zuhuriyya ta kwantar da ita sannan ta dawo fuskarta a murtuke ta ce. "Tashi ka fita tunda ba gidan ubanka ba ne!" Dakta Sadi ya fashe da dariya.*** Tsawon lokaci suna duban juna babu wanda ya ce da wani kala Bugu da kari kuma gidan ya yi tsit kai ka ce yan sa'o'i kadan da suka wuce gidan ba a cike yake da jama'a ba. Lokaci-lokaci shuke-shuken gidan da iska ke kadawa su suke bata shirun, haka nan kuma suke dada sa Hajiya Zainab kara tsanan Dakta Sadi wanda ke zaune yana yi mata fatalwar murmushi Zainab ta dubi Dakta Sadi irin duban da za ka yiwa kyankyason da ya fada cikin abincin buda bakinka yayin azumi "kada ki ci gaba da yi min irin wannan kallon zainab." Sadi ya ce yana dubanta. "Haba zainab, kin manta cewa nima masoyinki ne, ki tuna ba ki da kowa da zai taya ki jindadin a rayuwa, na mika kaina garekim na dauki dukkan hadarin dake tattare da al'amarin duk fa wannan domin jin dadinki ne amma duk da haka ba zaki gode min ba shi ne za ki saka min da haka?" "Hauka ne ya sameka?" zainab ta ce jikinta na rawa. "Ba hauka bace Hajiya Zainab ki saurari abin da nake son fada miki*** "Na ce ba zan saurara ba ko kuwa dole ne?" Ta ce dashi tana zazzare idanu. "Ka da ki ci gaba da daga muryarki har jama'a su jiyo na san ba zaki so a sameki da mijin da ba naki ba cikin wannan daren". Ya dan yi shiru yana dubanta. Akwai wani abu a yanayin kallonsa dake kara damun zuciyar zainab. "Zainab maganar kudin nan da nake so ce ta dawo da ni kin ga dai ke Allah ya sa kina daga cikin mutane masu sa'a." Ya yi shiru yana dubanta sannan kuma yana jira ya ji abin da zata ce. "Zainab kin kasance daga cikin mutane masu sa'a, domin tun da kika tashi ba ki san wani abu wai shi talauci ba sai dai ki ji ana fadar sunansa ko kuma ki ga wasu a cikinsa. Zainab ina son ki sani cewa ni kuma ina daya daga cikin marasa sa'a, domin tun da na tashi nake shan wahalhalun duniya iri daban-daban, a haka har na fara karatu," Dakta Sadi ya dan yi shiru yana duban sigarin dake cin wuta a hannunsa, tokar sai murmushewa take tana zuba a kasa. Ya yi kamar zai zuki sigarin to sai kuma ya fasa ya ci gaba da cewa. "Ka da ki tona ki ga wahalar da na sha lokacin da nake karatuna na likita a jami'a, na sha wuya ta fitar hankali, Allah ne ma ya sa da rabona, da tuni ma karatun ya gagareni, zaki yi mamaki idan na ce miki da kyar da kyar da taimakon abokina na gama karatuna. Wasu lokuta kudin motar da zan koma makaranta sai abokaina na gida suke bani, haka nan kuma idan na je makarantar ma to a gurin abokaina nake dan samun abincin da zan jefa a bakina. Kada fa ki yi tunanin bani da yan uwa zainab, ko kusa ba haka bane ina dasu, to amma ganin cewa bani da iyaye sai duk suka watsar dani, bayan kuma a da can wani zamani da ya shude duk a gindin mahaifina suke a tattare kuma..."**** "Malam ya isa haka, ni ban tambayeka tarihinka ba, ka tashi kawai ka fice min daga gida!" zainab ta katse shi fuskarta a murtuke. "kada ki yi min korar kare zainab, da sannu zan zo miki da manufata domin kin ga irin wannan hali naki shi ya sa lokacin da na gama karatuna da kyar sai na gane cewa lallai mutane basu da tausayi ko kadan, don haka nima daga ran nan na kudiri aniyar duk wanda ya fada cikin tarkona ko kuma ya hadiyi fatsa ta, to ban bari ya kufce min ban kuma tausaya masa." Dakta Sadi ya dubi zainab ido da ido ya ce. "Zainab kin riga kin shiga tarkona, domin tun sa'ar da na gane manufarki, sai na ga dama ce agareni ta karshe. Ban ga kuma dalilin da zai sa na tausaya miki ba, domin kema cin amanar mijinki kika yi to mene ne aibu kuma dan ni na ci taki amanar ? Ina fatan dai yanzu kin gane manufata ?" "Ban gane ba!" Zainab ta ce. "To abin da nake nufi shi ne ina bukatar kudin nan da na bukata gareki a kwanakin baya, Miliyan uku kacal nake bukata Sai ki zaba tsakanin miliyan uku da kuma dan kyakkyawan saurayi HILAL wa kika fi so ? Na ba ku kwana uku ki yi tunani" Dakta Sadi ya mike tsaye sannan ya fara matsawa kusa da zainab "Zo mu tafi daki ko" Ya kai hannu zai kama hannunta Zainab ta kai masa duka ta buge hannunsa "Kada ka taba ni shege dan iska" Sadi ya fashe da dariya. "Au yau kuma har da duka to ai iska bata da guda Ya sake matsawa kusa da ita Dakta Sadi bai kula ba a hankali sai kyawawan siraran yan yatsunta suka fara matsawa izuwa kan teburin dake tsakar dakin "Kada ka tabani Zainab ta ce cikin karaji lokacin da ta ga Dakta Sadi da gaske yake yi sannan sai ta yi wuf ta zari kwalbar Dakta Sadi ya ji wani abu fus! Kamar kofaton doki ya daki tsakiyar kansa ya kwalla kara cikin gigita ya rike kansa da hannayensa nan da nan jini yafara rine hannayen "Ni...fice min daga gida" Zainab ta ce bakinta na rawa har yanzu akwai sauran wani bangare na kwalbar da bai fashe ba a hannunta. "In kuma ba haka ba in kara ma shege dan iska" Dakta Sadi ya dubi Zainab cikin tsana rabin fuskarsa a rine da jini ya ce. "Na gode....zainab amma ina tabbatar miki da cewa wannan shine zai zamo karo na karshe da zaki sake dukan wani da namiji a doron kasa." Dakta Sadi ya juya a fusace ya fice daga dakin kansa rike a hannunsa "Na tsaneka!" Zainab ta sake cewa dashi cikin karaji Rugugin aradun bai bari Dakta Sadi ya ji abin da take cewa ba**** Kyakkyawan saurayin Hilal ya motsa a hankali sannan ya turar da zanin mayafin dake jikinsa ya dafe kansa da hannaye biyu ya rintse idanu gami da cije lebe. Da farko ya dauka ciwon kan dake sara masa na da nasaba ne da tashinsa daga nannauyan barcin to amma sa'ar da ya tashi zaune ya jingina bayansa jikin bangon dakin sai shakkar hakan ta darsu a zuciyarsa Tun sa'ar da ya baro gidan Hajiya Zainab kansa ke ta sarawa Dum Dum! Kamar ana kidan duma a ciki shi kansa bai san ta yadda aka yi ya karaso gida ba zuciyarsa cike fa tunane-tunane dauke kuma da fargaba kala biyu. Fargabar farko dake damun Hilal ita ce ta mijin Hajiya Zainab. Duk da ya ke mutumin da ya samesu a daren jiya shi da Hajiya Zainab ya ce zai rufa masa asiri amma hakan ba ta sa ya daina fargaba ba domin Hilal bai san mutumin ba me yiyuwa ma kawai ya yi masa haka ne domin ya yaudareshi ya bar gidan kafin kuma a zo daga baya da jami'an tsaro. Hulda da matar babban mutum kamar Alhaji Hamisu Jumare ba karamin hadari ba ce. Hakika na zama wawa wayona da hankalina duk basu amfaneni da komai ba domin in ba haka ba me zai sa na fara soyayya da matar aure? Hilal ne ke tambayar kansa. So! Amsar kenan da kwakwalwarsa ta shimfida a faifan tunanin zuciyarsa. Wannan kalma ta "SO" ita ce babbar fargaba ta biyu da ta mamaye zuciyar saurayi Hilal. Matsanancin so da begen Hajiya Zainab ya gama mamaye bargon jikinsa cikin dan kankanin lokaci dan haka duk da tsoron mai gidanta da yake idan ya tuna da cewa ba zai taba mallakarta ba sai ya ji duk duniyar nan ta dagule masa. Hilal ya zuro kafafunsa kasa daga kan gadon sannan ya dubi agogon dake makale a jikin bangon dakin a daidai lokcin da aka sake kwankwasa kofar dakin a karo na biyu. Hilal bai damu da ya amsa ba bai kuma yi wani yunkuri na ya bude kofar dakin ba koda yake dai daman jiya da daddare bai iya kulle kofar dakin ba turo ta kawai ya yi Rashin yunkurin bude kofar dakin na da nasaba ne da ciwon da kirjinsa yake yi. Hilal ya dafe kirjinsa sannan kuma lokaci guda ya ji wani abu mai kamar kibiya ya soki kwakwalwarsa nan da nan sai wani zazzafan gumi ya fara wanke kyakkyawan fuskar saurayin. Abin ya fara damunsa domin Hilal bai taba gamuwa da irin wannan matsala ba sai da ya hadu da Hajiya Zainab kuma ya lura da cewa kansa da kirjinsa suna takura masa ciwo ne a duk sa'ar da tunanin Hajiya Zainab ya fado masa Irin wannan kauna wacce iri ce? Hilal ya tambayi kansa A daidai lokacin ne to aka turo kofar dakin a hankali. Hilal ya dubi kofar dakin zuciyarsa cike da masaniyar wacce za ta bude kofar dakin. Bai yi kuskuren tunani ba wacce ya ke tsammanin ce wato mahaifiyarsa "Wacce irin lalatar banza ce kuma wannan Hilal ? Da girmanka da komai ace makaranta ma sai na tasheka za ka dubi fa karfe takwas da kwata" Ta nuna agogon dakin da hannunta "kuma yau na lura ko sallar asuba ba ka yi ba yanzu kana jin idan mahaifinka ya ji za ku kare da dadi? Ko kuwa dai kafi son ka harzukashi ya zo ya yi ta fadan nan nasa ba kai ba gindi." Ta yi shiru tana duban Hilal wanda ke yamutsa fuska. Ko kusa bai fahimci yawa-yawan kalmomin da ta fada ba abin da kawai dake yawo cikin kwakwalwarsa shi ne tausasan kalamanta in da take cewa "KAUNAR KA NAKEYI HILAL" BINDIGAR KWALI--> 6 . Ko kusa bai fahimci yawa-yawan kalmomin da ta fada ba abin da kawai dake yawo cikin kwakwalwarsa shi ne tausasan kalamanta in da take cewa "KAUNAR KA NAKEYI HILAL" "Ko ba ka jin abin da nake fada ne ? Hajiya Asma'u ta buga masa tsawa Hilal ya yi firgigit cikin tsoro ya dubi mahaifiyarsa ya ce bakinsa ba rawa. "Wal..Wallahi Ummi yau bana jindadi" Kamanin fuskar mahaifiyar tasa suka sauya Ta matso kusa dashi "Me ke damunka?" "Kaina ne ke yi min ciwo tun jiya da daddare" Hajiya Asma'u ta dada matsowa kusa dashi ta dafa kansa kamar za ta yi kuka duk bambamin fadan da take ya kare Ko kusa ko alama ba ta son abin da zai taba mata dan tilon danta tuni daman ta yanke kauna da samun Don haka sai hankalinta da na maigidanta malam zubairu ya tattaru gaba daya akan dansu kwaya daya wato Hilal sabanin wasu daga cikin mutane su basu bata nasu dan ba duk kuwa da cewa shi kadai suke dashi sun tarbiyantar dashi sun bashi ilimi na muhammadiya da kuma na zamani. Malam Zubairu tsohon soja ne koda yake wannan tsohon zancene domin yana daya daga cikin tsofaffin sojojin da suka hadu da rashin sa'a a lokacin yakin basasa hakan ce ma ta sa yanzu kafa daya ce dashi kuma ido daya to amma duk da haka idan allurarsa ta motsa to fa ran nan gidan babu kwanciyar hankali kenan. Malam Zubairu dan karere ne motsattse yana da tarin gashin baki fari tas kamar gashin tinkiya idanunsa jajaye ne sakamakon kokinon da aka zuzzuka a da duk da yake dai yanzu girma ya kama shi to amma lokaci-lokaci akan dan taba shan kokino domin wai a cewarsa maganin mura ne. Da yawa daga cikin abokan aikinsa a zamanin suna soja da DUJAL suke kiransa.*** Hajiya Asma'u fara ce doguwar bafulatana kyakkyawa kana ganinta ka ga Hilal mutane da yawa sun sha tsurku akan cewa yaushe za a ce kyakkyawar mata kamar Asma'u za ta auri wannan kyamurarren tsohon sojan mai kamar zanen yan koyo? To amma kuma ai an ce matar mutum kabarinsa. Mutane musamman yan uwan Hajiya Asma'u sun yi farin ciki lokacin da aka haifi Hilal suka ga sam-sam ma shi bai yi kama da ubansa ba domin wai a cewarsu da ya yi kama da ubansa da zai yi wuya in zai sami matar aure a duniya. "Sannu Hilal" Mahaifiyarsa ta ce dashi kamar wani dan kankanin yaro. "Gashi kuma jarrabawa ya za ka yi kenan?" Hilal ya dubi mahaifiyarsa ya yi murmushi yake ya ce 'Zan kokarta na tafi a haka na san me yiyuwa in na shiga dakin jarrabawar na warware." "To ai sai ka hanzarta tun da kana ganin za ka iya kaga fa har tara ta kusa kuma ka ce tara kuke farawa" Hilal ya mike tsaye zuciyarsa na ta zayyana masa kyakkyawar fuskar nan ta Zainab mai lallausan murmushi. "Idan ka yi wanka sai ka je falo abin karin kumallonka yana can gashi ma ko sallah ba ka yi ba." Hajiya Asma'u ta nufi kofar dakin ta janyo ta a hankali zata bude can kuma sai ta juyo firgigit kamar wacce ta tuna da wani abu ta ce. "Af, na manta wai wata yarinya a waje tana sallama da kai ta ce wai yar makarantar ku ce." Hilal ya hade fuska ya dubi mahaifiyarsa ya ce "RUKAYYA CE ko?" Mahaifiyarsa ta girgiza kanta ta ce. "A'a ai na san Rukayya wannan fa ina jin har da mota ta zo wai sunanta ZAINAB." Hilal ya ji kamar an jefa masa gwauron dutse a cikin zuciya. Hilal ya fito tsakar gida dauke da littattafan makarantarsa guda biyu. Jarrabawa ce ta hana shi dauko jakar makarantar baki daya. "Ummi ni zan tafi". Ya ce da mahaifiyarsa wacce ke tsaye bakin famfon dake tsakar gidan tana daukar ruwa a tukunyar karfe. "To Hilal yi sauri kada ka makara yarinyar na nan waje tana jiranka, nayi-nayi ta shigo ciki ta ki". Ta dan yi shiru sannan ta ci gaba "Da zarar an tashi kuma sai ka nufo gida kada ka tsaya zafin rana ya sake tada maka ciwon kan". "To Ummi". Hilal ya amsa sannan ya nufi kofar gida cikin sauri, kirjinsa na dakan uku-uku. Tun sa'ar da mahaifiyarsa ta ambaci sunan Zainab sai ya ji duk zaman gidan ya ishe shi, dokin sake ganin kyakkyawar fuskar nuna bai iya barin sa ya sa ko da loma daya ba a bakin salatinsa to amma Hajiya Asma'u bata takura shi da sai ya ci abinci ba domin a tunaninta rashin lafiyar daya tashi da ita ce ta hana masa jin dadin dandanon abincin. Fitarsa ke da wuya, shekin jikin dankareriyar marsandin fara ya dauke masa idanu kofar motar ta bude Hajiya Zainab ta fito tana murmushi. Yawun bakinsa ya kafe kamar yadda itama nata yawun bakin ya kafe domin a lokacin ko cikakken numfashi bata iya yi sosai. Ga mamakinsa sai ya sami kansa yana mai yi mata murmushi. Masoyan biyu suka dubi juna, daya matar aure daya kuma saurayi dan makaranta Zainab ce ta fara magana bakinta na rawa "Hilal....ka yi hakuri dan Allah". Halil ya yi mata murmushin yake sannan ya juyo ya dubi kofar gidan su domin tsoro ya ke ji kada mahaifinsa ya samesu gurin "Mu shiga mota". Hilal ya ce yana duban kofar gidan. Hajiya Zainab ta nufi motar ba ta yi musu ba domin ta fahimci abinda yake nufi. Suka fara tafiya a hankali a daidai lokacin ne to Hilal ya ji kamar an zungureshi ta baya yana juyawa sai ya ji an fashe da dariya. Zuhuriyya ta dubeshi tana kokarin sake zungurinsa da bindigar wasanta. "Ah, Zuhuriyya kada fa ki harbeni". Hilal ya ce yana dariya. Zainab ta yi murmushin yake ta ce "Ke....kyaleshi haka kada ki dameshi mana ke fa fitinarki kenan". Zuhuriyya ta bata fuska ta ce cikin shagwaba. "To Mama ya dawo baya mana mu zauna." Hilal ya fashe da dariya gami da mamakin irin wannan wayo na wannan yarinya Zuhuriyya, sannan sai ya dubi fuskarta mai sheki ya kuma dubi ta mahaifiyarta sai ya ga tamkar taurari ne biyu a sararin samaniya masu hasken gaske babba da karama. "Hilal dan Allah abinda ya faru jiya ka yi hakuri zan yi maka bayanin duk abin da ake ciki." Hilal ya dubeta sannan sai ya jefeta da wani irin murmushi na kauna mai narkar da zuciya. "Zainab ina son ki sani cewa duk wani bayani da za ki yi min a yanzu in dai har ba na kaunarki to ba zai sa na taba son ki ba. Haka nan kuma an ce so hana ganin laifi dan haka duk abin da ya faru jiya bai isa ya hana ni kaunarki ba in dai har ina yi din". Hilal ya mayar da numfashi sannan ya yi kasa da muryarsa ya ce. "Zainab ina sonki fiye da duk wata halitta dake doron kasa a yanzu dan haka koda ba ki yi min bayani ba begenki bai taba girgiza a zuciyata ba Hajiya Zainab ta rage gudu sannan ta sa hannunta ta share hawayen farin cikin jin cewa yana kaunarta daga kan fuskarta. "To amma kuma ina jin daga yau mun rabu kenan ni dake domin haduwar mu dake ba alheri bace." kadan ya rage sitiyarin motar ya kwace daga hannun Hajiya Zainab saboda girgizata da kalamin ya yi "Haba Hilal kada ka yi min haka kai fa yanzun nan ka ce kana kaunata da bakinka to kuma mene ne ya kawo zancen Rashin alheri a haduwarmu kana sona ina kaunarka fiye da kaina to mene ne aibun" Hilal ya muskuta sannan ya dubi agogon dake gaban motar tara saura minti bakwai. "Aibun haduwata dake shi ne ke ba matata ba ce matar wani ce ki tuna fa duk haduwar da muke dake hatta zama da hirar da muke dake a halin yanzu duk haramun ne" Hajiya Zainab ta dauke wuta na tsawon dakiku tana ta karatun jaki hakika bege da kaunar dan kyakkyawan saurayin sun fitar da ita daga cikin hayyacinta kai dama duk hankalinta gaba daya. Tara da minti daya suka kawo farfajiyar makarantar tuni har barci ya dauke Zuhuriyya wacce ke kwance a bayan motar dauke da bindigar robarta. "Kafin ka fita Hilal ina son ka taimakeni dan girman Allah ka zo gidana yau da daddare ina son magana da kai" Hilal ya dubeta sannan ya girgiza kai yace. "A duk sa'ar da na dubeki sai kaunarki ta dada mamaye zuciyata ni kuma tunanin hakan na da matukar hadari ga rayuwata domin ba zan taba mallakar ki ba tun da kin kasance matar wani ki yi hakuri Zainab ni zan tafi sai wata rana." ya juya ya fara tafiya. "Hilal dan Allah ka taimaki rayuwata, dan Allah" Ya girgiza kai "Ki yi hakuri ni da ke har abada" Ya nufi dakin jarrabawa da gudu-gudu. Har ya kule tana kallonsa sannan sai ta kifa kanta akan sitiyarin motar ta fara matsanancin kuka. "Mama kukan me kike?" Zuhuriyya ta tambaya daga bayan motar.***** Tun kafin duwawunsa ya gama taba kujerar sai talafon ya dauki ruri. Kamannin Dakta Sadi suka sauya ya dubi talfon din cikin takaici. Wane ne kuma wannan ke son damunsa a daidai lokacin da yake kokarin hutar da ransa ya dan sha iska. Tun sa'ar da ya fito daga dakin tiyatar jikinsa ya fara bashi cewa abubuwa yau ba sa tafiya yadda ya kamata. Koda yake dai daman tuni ya gane cewa sabanin da suka samu tsakaninsa da asirtacciyar masoyiyarsa Hajiya Zainb ba karamin taba harkokin rayuwarsa ya yi ba. A da can kafin su sami sabani Dakta Sadi ya dauka shi Hajiya Zainab take so bashi yake sonta ba kuma yana iya yi mata duk abinda ya ga dama domin shi ne (Master) dan shi ake so. Bai gane kuskurensa ba sai a daren shekaran jiya irin yadda Hajiya Zainab ta ruguje shi da kwalba kuma ta koreshi fata-fata kamar kare shi ya karya zuciyarsa sannan kuma ya aza zuciyar tasa akan wani tsini na tsananin FARGABA DAKUMA BINDIGAR KWALI--> 7 . Irin yadda Hajiya Zainab ta ruguje shi da kwalba kuma ta koreshi fata-fata kamar kare shi ya karya zuciyarsa sannan kuma ya aza zuciyar tasa akan wani tsini na tsananin FARGABA DA MAMAKI Lokacin da ya dawo gida sai ya kasa fitar da tunanin kyawunta daga cikin ransa sannan sai ya sami kansa yana mai zubar da hawaye domin ya san ya yi rashin masoyiya a take a nan sai ya gane cewa ashe tuntuni ya kamu da ciwon sonta bai sani ba sai da rabuwarsu ta zo Dakta Sadi ya zargi kansa akan hadama ta son mallakar abin da bai kai ya mallaka ba Da ya san haka ne da bai tambayeta kudin ba da kuma yanzu zamansu suke lafiya A washegarin ranar

Chapter 2 of 7