Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
Hilal ya sauke gilashin motar domin ya sami damar ganin irin sauyin da aka samu a birnin kano BAYAN TAFIYARSA BABU SHIRI. Hilal ya yi mamakin ganin irin manya- manyan gidajen da suka dadu a cikin garin idan ban da ya gani a rubuce da ba zai taba imani da cewa nan birnin kanon da ya sani ba ce A zuciyarsa ya yi mamakin irin yadda yan jaridu ke karawa miya gishiri domin a yadda ya ji suna bada labarin yakin mai tatsine bayan tafiyarsa bai dauka zai tarar da kano a haka ba. Hilal ya shafi aljihunsa a hankali domin ya ji ko bindigar rabor tana nan sannan sai ya kalli zoben dake dan yatsansa na hagun ya ce a sanyaye. "Rabon ka da garin nan yau shekaru ashirin da daya. tun wacce ka fi so a duniya tana raye." wani zazzafan hawaye ya fara sartu akan kyakkyawar fuskar da karin shekaru ashirin da daya basu iya dakushe kyawunta ba. Sa'ar da motar ta shiga cikin layin sai Hilal ya miko kansa ta cikin tagar yana kallon gidajen dake layin cikin kaduwa sannan har sa'ar da motar ta ja birki ta tsaya a kofar gidansu kaduwar bata saki Hilal ba badan komai ba kuwa sai don ganin a cikin shekaru ashirin da dayan da ya yi baya nan ba a sami wani kwakkwaran sauyi na gani a fada ba. Wannan ita ta sa motar na tsayawa Hilal ya bude kofar ya fito kana jikinsa na rawa ba tare da ya dubi inda sabuwar katangar gidansu take ba sai ya kalli kudu ya kalli arewa, sannan ya kalli gabas da yamma cikin tsananin mamaki in ka dauke wasu yan tsukakkun benaye guda uku masu kamar hasumiyar masallaci gami da wani katon kwalbati mai tudun tsiya kamar kabarin jaki gami da katangar gidansu da aka sake ginawa babu wani sauyi da aka samu da layin sai tarin bolar data cushe magudanan ruwa da kuma karin kaji da agwagi da aka samu a layin. Jikin Hilal na rawa ya nufi kofar gidan makwabtansu Malam Iliya, sai ya ga har yanzu dai tsohon ginin nan ne mai kamar bukka to sai dai kuma katuwar rumfar kiwon awakin da Hilal ya sani tana kafe a kofar gidan a yanzu babu ita har ma an sumunce gurin wani dan tutturnan saurayi mai doguwar keya da kyawawan idanu farare gami da dogon bakin da ya bashi siffar tsuntsu shi ne zaune a gurin da wani dan teburi yana sayar da kayan masarufi masu rangwamen farashi. "Sannu da zuwa." Dan saurayin ya ce da Hilal, sannan lokaci guda ya matso inda suke ya kamawa direban suka fara sauke kayan Hilal. "Yauwa sannunka dai...sannu da kokari." Hilal ya ce yana duban saurayin sama da kasa domin ko shakka Hilal ba ya yi yasan saurayin dan Malam Iliya ne ko kuma jikansa domin idanunsa da kuma tsayin bakinsa sun nuna hakan. Me yiyuwa bayan tafiyata da kadan aka haifeshi. Hilal ya ce cikin Zuciyarsa domin ya lura saurayin bai fi shekaru goma sha takwas zuwa Sha tara ba. Saurayin da direban suka ci gaba da sauke manyan akwatunan Hilal yana kallonsu gabansa na ta faduwa, bai san abin da zai tarar a cikin gidansu ba bai kuma san ta yadda zai fara neman gafara a gurin iyayensa ba, tabbas ya san ya gama jefa iyayen nasa cikin bakin ciki marar misaltuwa musamman ma mahaifiyarsa hilal ya yi sauri ya share hawayen bakin cikin dake kokarin subuce masa sa'ar da ya tuna da safiyar wannan mummunan rana*********** *** Ranar da ya rasa babbar masoyiyarsa Hajiya Zainab. "....yau ba za ka je makaranta bane ka ke kwance har yanzu ba ka tashi ba... Wallahi bani da lafiya ne..." Maganganun da suka yi da mahaifiyarsa suka fara dawo masa a safiyar ranar. Har yanzun nan da yake tsaye Hilal na iya tunawa da irin matsananciyar kulawar da mahaifiyarsa ke nuna masa a zamanin kuruciyarsa, sai gashi lokaci guda ya bakanta mata, a dalilin subucewar wani abu da ba zai taba daina kauna ba. "Malam mun gama" Muryar direban motar ta katse tunanin Hilal. Cikin lalaci Hilal ya lalubi aljihunsa ya zaro wasu adadi na takardun kudi ya mikawa direban. Cikin ladabi direban ya karbi kudin sannan ba a dade ba ya shiga motarsa ya fice daga tsukakken layin. Hilal ya yi tsaye cikin fargaba yana kallon kofar gidansu, yayin da dan tutturnan saurayin ya kura masa idanu a zuciyarsa yana tunanin duk yadda aka yi mutumin bako ne kuma me yiyuwa ma bai san takamaiman inda ya zo ba. "Gidan wa kake son zuwa?" Saurayin ya tambayi Hilal gami da matsowa kusa da Hilal cikin niyyar taimako. Hilal ya dubi saurayin, sannan ya jefeshi da murmushin yake ya nuna gidansu ya ce. "Nan gidan nazo. mutanen gidan suna nan?" Saurayin ya yi jim na dan lokaci "Ai daman babu kowa a gidan sai Iya me waina." To ina mahaifan nawa suke? Ya tambayi kansa Sannan lokaci guda ya dubi Saurayin. "Taya ni to mu shiga da kayan ciki." Kafin ya rufe bakinsa saurayin ya kinkimi katuwar akwati daya ya nufi cikin gidan. Hilal ya yi kamar ya tsaya ya ga dawowar saurayin, sai wata zuciyar ta ce dashi shiga kawai ka tambayi me wainar inda iyayenka suka koma. WANNAN ITA TASA HILAL YA KINKIMI AKWATI Shima ya bi saurayin a baya. A daidai lokacinda ya shiga zauren gidan ne ya ji wata murya na cewa da saurayin "Hamza wannan katuwar akwatin fa ko tsintuwa muka yi?" Hilal ya ji zuciyarsa ta harba tsakanin hakarkarinsa sa'ar da muryar ta daki dodon kunnensa "Wani mutum ne ya ce na shigo da ita." muryar Hamza ta ce da me waina "Wani mutum? Wane ne?" "Nima ban san shi ba wallahi bako ne amma na ga kin yi kama dashi sosai wallahi" Hilal ya dafe kirji wani zazzafan hawaye ya fara kokarin subuce masa. Ko shakka ba ya yi duk duniya babu mai irin wannan murya sai mahaifiyarsa. Dan haka zuciyarsa na harbawa sai ya shiga gidan janye da katuwar akwati me taya "Ya yi kama da ni fa ka ce, to wannan wane..." kalamin matar ya katse sa'ar da Hilal ya shiga tsakar gidan da sallama cikin rarraunar murya. "Ameen wa'a..." Bata karrasa amsa sallamar ba sa'ar da suka yi ido biyu da mutumin. Hilal ya dubi yamusasshiyar tsohuwar wacce ke sanye da zanen shudin leshi mai tsadar gaske wanda ya sha dinki na zamani duk kuwa da irin tsufan da ta yi. Abin ya bashi mamaki. Koren dan kwalin dake kanta ya zame gefe guda wannan shi ya baiwa gashinta rabi baki, rabi fari da furfura ya sami damar burtsowa ta gefen kyakkyawan dankwalin to sai dai kuma fuskarta duk ta yamutse tunani me yiwuwa da bakin cikin rashin ganinsa sun gusar da kyawun da annurin fuskar da Hilal ya sani shekaru ashirin da daya da suka wuce amma hakan bai isa ya hana Hilal gane mahaifiyarsa ba. "Ummi!" Ya kirata muryarsa na rawa. "Hilal...kaine. ..wayyo Allah...Allah nagode ma da ka dawo min dashi" Tsohuwar ta fashe da kuka. Hamza cikin mamaki da tausayi ya ci gaba da kallon diramar da ake yi a gabansa. Shin ko wannan shi ne dan mai waina da ta sha ba shi labari? Hamza ya tambayi kansa. "Ummi daina kuka dan...Allah" Hilal ya ce duk kuwa da cewa shima kukan ya ke yi. Jikin tsohuwar na bari ta matso kusa da dan ta ta rike hannunsa ta duddubashi tana rafsa kuka kamar karamar yarinya wani sa'in kuma sai ta fashe da dariya kamar tababbiya, motsattsiyar fuskarta ma'abociyar kyau da annuri a wani shudadden zamani ta jike sharkaf da hawayen farin ciki a haka cikin wannan hali tana kuka, yana kuka makwabta suka fara taruwa zuwa gidan domin su ganewa idanunsu abin da ke faruwa. Da mutum ya shigo sai tsohuwar ta dubeshi ta ce. "Wannan shi ne dana da na sha baku labarin ya bata. Gashi yau Allah ya dawo min da shi."********** **** Wannan ita ta sa gidan ya ci gaba da dinkewa da yan uwa da abokan arziki domin duk wanda ya fita sai ya bai wa dan uwansa labari. Wasu ma ba su san Hilal ba wasu ko haifar su ma ba a yi ba sa'ar da Hilal ya bar gida amma sai zuwa gidan suke domin su sami abin kai wa gaba. Ana cikin wannan hargitsi ne, Hilal ya dubi mahaifiyarsa ya ce. "Ummi ban ga BABA ba?" Mahaifiyarsa ta sunkuyar da kai sannan ta ce a sanyaye bakinta na rawa. "Shekararka daya da tafiya Allah ya yi masa rasuwa.. Yan mai tatsine ne suka kashe shi a kofar gidan nan ka san shi da taurin kai!" Ta sake fashewa da kuka.********** ********** Daga ita sai daurin kirji ta shigo kawataccen dakin ruwa na diga cikin tsefaffen gashin kanta wanda ke kwance akan doron wuyanta kafafunta sanye cikin farin takalmin roba marar nauyi fitowarta kenan daga wanka Matar ta yi ajiyar zuciya kana ta nufi kujera ta zauna a gaban teburin kayan kwalliyarta wanda ke dauke da kayan shafe-shafe da manne-manne sama da kala dari domin a duk wata guda na duniya sai ta kashewa kayan kwalliya naira dubu bakwai. Kudi ba komai bane a gurin matar domin ta mallake su an kuma tara mata su a gida. Haka nan a halin da ake ciki kudin da ta tarama a shekaru goma sha biyar da ta yi tana aikin banki sun isheta kashewa har iya rayuwarta ko da kuwa bata gaji komai ba a wajen mahaifinta marigayi Alhaji Alawaisu. Wannan ita tasa aduk karshen mako idan ta bushi iska sai ta hada liyafar sanyaya rai ta gayyaci kawaye irinta shagwababbu su yi ta rakashewa abin su domin talauci ba abokin wasansu ba ne, ba su ma san shi ba sai dai su ji labari. Akwai wata rana, suna zaune ita da wata kawarta sai suka ji wani mai labarai a gidan rediyo yana bayanin irin masifar wahalar da talakawa ke ciki a kasar nan har ma yana cewa mutanen da ke kwana ba su ci abinci ba ba zasu kirgu ba. Jin haka ke da wuya sai matan biyu suka bushe da dariya. Kawar matar ta dubeta ta ce. "Oh! Masu labaran nan ba a rabasu da QARYA. . BINDIGAR KWALI--> 11 . Jin haka ke da wuya sai matan biyu suka bushe da dariya. Kawar matar ta dubeta ta ce. "Oh! Masu labaran nan ba a raba su da karya ki ji fa wai har akwai wadanda ke kwana ba su ci abinci ba." Matar ta yi murmushi ba ta ce komai ba domin ita ta san abin da mai labaran ke nufi a kalla dai koda bata san menene talauci ba to ta taba ganinsa muraran a gidan mutumin da tafi kauna fiye da kowa a duniya. Matar ta dauki wani tattausan shudin kyalle ta fara goge ruwan dake cikin gashinta mai santsi a zuciyarta tana cewa yau dai ya kamata na je wankin gashi duk kuwa da cewa jiya-jiyan nan ta je wankin gashin da safe. Bayan ta gama wanke gashin sai ta mika hannu zata janyo kwalbar mai kusa da ita sannan ne to ta tuna. Cikin sauri ta zabura domin ta tuna da cewa ta manta da al'adar da ta saba yi a duk safiyar duniya. Cikin sauri ta janyo lokar da ke jikin teburin kayan kwalliyar ta dauko wata farar ambulan sannan ta zaro hoton kwaya daya tak wanda a gurinta ya fi komai muhimmanci a cikin dakin domin da kyar ta sami hoton. Matar ta kurawa hoton idanu na tsawon lokaci hawaye na zuba daga cikin fararen idanunta har tsahon mintuna goma sha biyar a zuciyarta tana cewa "Allah...Allah ka dawo min da masoyina Hilal. A daidai lokacin ne to ta ji motsi a bayanta. Bata damu da ta juya ba domin ta san ko wace ce. "Um...hum kin fara abin ba ai sai ki yi ta yi wahalalliya, soyayya da matacce." Muryar mahaifiyar ta ce. "Ke dai Rukayya wallahi kin shiga uku, ni na taba ganin irin wannan masifa ki yi ta fama da son mutumin da ya riga ya mutu haba Rakayya. Yau fa shekarar sa ashirin da daya kenan da barin gida." Ta dan yi shiru sannan sai ta fice a fusace tana cewa. "In kin gaji da zaman haka ai kya koma gidan mijinki." Rukayya ta yi ajiyar zuciya sa'ar da ta gama jin bambamin fadan mahaifiyarta. Ba ta damu ba domin har ta saba da irin wannan fada, dan tun tana budurwa take jin irin wannan fada, har zuwa aurenta na farko wanda ko shekara guda ba a yi ba ta fito daga gidan mijin. Daman sai da ta fadawa iyayen nata cewa ita fa ba za ta auri wani mutum ba a duniya sai Hilal, idan kuwa Hilal ya mutu ba zai dawo ba, to ita da aure har abada. Ba a fi shekara goma ba da mutuwar aurenta na farko, wani dan abokin mahaifinta ya nuna yana kaunar zama da ita. Rukayya ba ta ma san da maganar ba sai bayan da aka daura aurenta da mutumin. A ranar da za su wayi gari na farko da ango nata, ta dubeshi tace.********* "Bawan Allah ka rufawa kanka asiri dan ban taba ganinka ba, ban san da labarinka ba sai ji na yi an daura min aure da kai, ka ga ashe abu ne me wuya na iya zama da kai dan ba na kaunarka." mutumin dan gajere fari kamar zabiya mai katon kai da fadi kamar faranti ya dubeta da dariyar keta ya ce. "Ni ma kaina na san ba kya kaunata, amma ai ni ina kaunar ki dan haka da za ki yi hakuri mu zauna da ya fi domin ina son matata kuma ba zan sake ki ba." A wayewar garin ranar da asuba Rukayya ta rushe katon kansa da kwalbar lemo. Kwanansa goma a asibiti yana jinya. Fitowarsa ke da wuya ya bata takarda yana murna. A shekarar da ta fara aiki a banki ne, aka dada takurawa Rukayya ta auri wani dan kasuwa Alhaji Mahmud. Auren ya so ya yi karko domin Rukayya ta sami damar yin shekara biyu tare da shi daga karshe mutumin ya kamata tana shan maganin hana daukar ciki. "Dan me za ki yi min haka ba ki san cewa son haihuwa ne ya sa na aure ki ba." Rukayya ta dubeshi a yatsine ta ce. "Da ni ka dauka kaunarka ce ta sa ni aurenka? Bin maganar na gaba ne kawai ta sa ni aurenka amma ni ina da wanda ke raina har abada. Idan ba shi ba ba zan iya haihuwa da kowa ba." washegari mutumin ya sake ta. A cikin shekaru ashirin da daya din da suka gabata auren Rukayya biyar a cikinsu babu wanda ya taba wuce sama da shekara biyu. A yanzu da take zaune dauke da hoton a hannunta shekara biyar kenan rabonta da aure. Ba ta da aiki sai hada liyafar kawaye da tsofaffin abokanta yan boko wadanda suka yi mutunci a zamanin zaman su na jami'a. Yaushe za ka dawo Hilal...yaushe ne za ka dawo ka gusar da bakin cikin raina? Rukayya ta ce tana duban tsohon hoton da ke rike a hannunta. Sannu a hankali sai ta mike tsaye dauke da hoton ta nufi madubi kana ta dubi hoton sannan ta dubi kanta a madubin. *HAKIKA KWANAKI NA SHUDEWA *WATANNI NA WUCEWA *SHEKARU NA KARA YAWAITA. *ZAMANI NA DADA NISAWA. *KYAWUNA NA DADA DAKUSHEWA Rukayya ta ce da kanta. Ta lura da cewa fuskarta tafara tsofewa kyakkyawan saurayin dake jikin hoton. Shin yaushe Hilal zai dawo? Rukayya ta kuma tambayar kanta. A karo na farko cikin shekaru ashirin da daya sai ta ji tsoro ya cafki zuciyarta sannan ta fara mummunan tunanin da zuciyarta ba zata iya jurewa ba. "Anya kuwa Hilal bai dade da mutuwa ba?" Ta tambayi kanta da kanta, zazzafan hawaye na zuba akan kumatunta.********* Washegarin ranar da Hilal ya dawo da sassafe misalin karfe shida mahaifiyarsa Asma'u ta nufi dakinsa domin su sami damar tattaunawa dashi. Jiya ba a bar su sun sake ba, don tun dawowarsa yan uwa ke ta tururuwa suna zuwa kallonsa duk kuwa da cewa da yawa daga cikinsu. Sun watsar da mahaifiyar ta sa babu ruwansu da ita. Har karfe goma sha biyun dare jama'a ba su bar gidan ba, wannan ita ta sa sai kusan biyu saura Hilal ya sami damar runtsawa. Sa'ar da Hilal ya shiga tsohon dakinsa a ranar sai ya ji kamshin turare ya bugi hancinsa, sannan ya ji kafarsa ta taka wani abu tattausa, tabbas kilishin dakine. Abin mamaki na uku kenan. Hilal ya ce cikin zuciyarsa. Domin sa'ar da ya fara shiga gidan ya lura duk an gyara ginin gidan an sumunce ko ina an kuma sake fenti, hakika gidan ya sake kyau nesa ba kusa ba fiye da yadda ya bar shi shekaru ashirin da daya da suka wuce. Mamaki na biyu shi ne tufafin da ya gani masu tsada jikin mahaifiyarsa, sai gashi yanzu kuma ga dukkan alamu zai sake ganin wani sabon abin mamakin. Sannu a hankali Hilal ya fara laluben inda makunnan lantarkin take, bayan wasu yan dakiku ya samu sannan ya kunna, dakin ya gauraye da haske Hilal ya dubi dakin a rude......... BINDIGAR KWALI--> 12 . Kamar yadda ya yi tsammani tun farko, tabbas tattausan kilishin daga bangaren arewa a jikin bango wata katuwar katifa ce dindimemiya, me yiyuwa sai ya sa tsani zai iya hawanta. Katifar lullube take da wani irin tattausan zanen gado mai gashi dauke da surar wani kyakkyawan aku launin rawaya zaune akan bishiya. Daga bangaren kudu na dakin teburine na gilashi mai bakaken kafafu, dauke da fulawowi na roba, da kuma sauran yan littattafan Hilal na makaranta wadanda yake amfani dasu shekaru ashirin da daya da suka wuce. Ko da Hilal ya duba bangaren gabas sai ya hangi wasu yan kujeru masu taushi guda biyu. Tsawon mintuna biyar Hilal na tsaye cikin tekun mamaki yana kallon dakin. Shin wane ne da wannan aiki? Ya tabbata a yadda ya ga mahaifiyarsa a motse a kode duk a rame babu alamar jin dadi a gareta babu wata hanya da zata iya kawata wannan gida nasu haka, ga kuma wani abin mamakin shi ne babu alamar kura ko kankane a cikin dakin. Hilal ya zauna akan tattausar katifar. Ga mamakinsa sai ya ji lokaci guda gajiya ta lullube gabobinsa, nan da nan ya fara hamma, sannan ba a dade ba zuciyarsa dauke da tambayoyi masu tarin yawa sai barci ya daukeshi. Tunani na karshe da ya zo zuciyar Hilal a daidai lokacin da barcin ke kokarin dauke shi shi ne, shin me ya sa mahaifiyarsa ramewa da tsofewa, bayan kuma ga dukkan alamu babu wahala a gidan? Wata zuciyar ta ce da shi bakin cikin rashinka ne Hilal? *** "Salamu alaikum...Hilal ka tashi ne?" Mahaifiyarsa ta ce dashi Hilal ya ji wani abu ya lullube zuciyarsa. Wannan shi ne gidansu, wannan shi ne mutuncinsa, wannan ita ce irin kulawar da mahaifiyarsa ke nuna masa tun yana karami. Hilal ya tuna safiyarsa ta karshe a gidan. Hilal ya amsa sallamar a daidai lokacin da mahaifiyarsa ta shigo dakin ta zauna a gaban katifarsa akan tattausan kilishin dakin. Cikin sauri ya gaisheta, kana ya ajiye tasbahar dake hannunsa a gefe guda. "Jiya ba mu sami damar tattauna komai ba jama'a sun yi yawa." Mahaifiyarsa tace tana dubansa. A zuciyarta tana cewa Hilal ya zama cikakken mutum. Hilal ya sake duban kayan dake cikin dakin sannan ya dubi mahaifiyarsa alamun tambaya karara akan fuskarsa, mahaifiyarsa ta lura da hakan, wannan ita ta sa ta dubeshi da busasshen murmushi ta ce. "Na san abin da kake tunani, wane ne ya gyara gidan nan ko? Wane ne kuma ya ba ni sutura ko?" Hilal ya gyada kai cikin mamaki domin kamar zuciyarsa ta karanta. "Kafin na baka amsa zan zo jin inda ka tafi da kuma dalilin tafiyar ka, ba ka dawo ba sai yanzu bayan shekara ashirin da daya." Ta dan yi shiru tana dubansa sannan sai ta sunkuyar da kai ta ce da shi a sanyaye. "Hilal sace ka a ka yi, ko kuwa wani ka yi wa laifi ya yi maka kurciya?" Hilal ya sunkuyar da kai cikin tsananin tunani, bai san ta inda zai fara ba, shin wai zai fada mata labarin ne tun daga lokacin da aka kashe babbar masoyiyarsa Zainab, ko kuwa iya labarin tafiyarsa kawai zai fada mata. Zuciyarsa ta shiga cikin rudani, dole ne in har yana son ta fahimci dalilin barinsa gida ya sanar da ita labarin Hajiya Zainab. Hilal ya yi ajiyar zuciya sannan ya dubi mahaifiyarsa lokaci guda ya dauki tasbahar dake dab da shi ya fara wasa da ita, yana duban koren kilishin dakin. "Ummi...kin tuna da wata Zainab da ta taba zuwa nemana?" Mahaifiyarsa ta gyada kai cikin sauri ta ce. "Ba zan taba mantawa da ita ba, wata kyakkyawar mace da ta zo nemanka a mota ko? Hilal ya gyada kai, sannan ya dan yi shiru yana tunanin kaset din tsohon majigin dake cikin kwakwalwarsa, sannu a hankali sai ya fara tunanowa. Ga shi nan ya fito kan titi cikin sauri a firgice, yana kokarin shigewa duhu domin baya son motocin yansandan dake giftawa ta gabansa a guje su hasko shi. Hawaye na zuba kamar ruwa, ya kasa imani da abin da ya gani shin anya kuwa da gaske ne Zainab masoyiyarsa ya gani a mace cikin jini? Ko kuwa mafarki ne yake. A daidai lokacin da ya raba ta jikin doguwar katangar wani gida ne wani katon kare ya yi masa haushi. Hilal ya yi tsaye cak a cikin duhun jikin katangar. A lokacin ne ya tabbata abin da ke faruwa gaskiya ne ba mafarki ba. "Ka yi min rai don Allah...ka kyale ni na wuce kada ka sa a kamani wallahi ba ni na kasheta ba.." Hilal ya ce da katon karen mai bakin kai da farar jela kai ka ce da mutum yake magana. Tsawon yan dakiku Hilal da karen suna kallon juna, sannan kamar karen ya fahimci abin da Hilal ya ce sai ya fara ja da baya da baya sannu a hankali har ya shige cikin gidan mai katuwar kofar baka. Hilal ya dafe kirji gami da ajiyar zuciya sannan ya zura a guje ya nufi bakin titi a rude kwakwalwarsa a hargitse. Sa'ar da ya kawo daf da bakin titin sai ya tsaya gindin wata katuwar bishiyar dorawar turawa yana mayar da numfashi lokaci guda ya dubi kwan dalelem agogon robar dake hannunsa mai lamba- lamba karfe bakwai na dare saura mintuna. Hilal ya jingina da jikin bishiya yana haki "Na shiga uku! Na shiga uku!! Ya ce a rude Sannan zuciyarsa ta fara tsalle-tsalle tana tunanin abin da ya kamata yayi. Abu na farko da ya fara zuwa zuciyarsa shi ne ya kira yan sanda ya yi musu bayanin cewa abokin mijinta ne ya kashe masoyiyarsa Zainab. "Kai shashasha." wata zuciyar ta ce dashi "Yanzu idan yan sandan suka tambayeka abin da ya kai ka gidan wacce amsa za ka ba su?" Wani zazzafan gumi ya barko akan goshinsa. Sai in ce da su kwartanci ne ya kai ni. Hilal ya baiwa zuciyarsa amsa duk kuwa da cewa ya san har abada ba zai taba iya fadawa yan sanda haka ba. To wacce hujja ma na ke da ita da zan gamsar da su cewa dakta Sadi ne ya kasheta? Hilal ya tambayi kansa. Me yiyuwa ma su yi tunanin cewa ni ne na kasheta rudewa ta sa na kawo kaina. Wannan tunani shi ya sa shi kawar da tunanin zuwa gurin yan sanda daga zuciyarsa. "Ka tafi gida kawai abinka ka ci gaba da addu'ar Allah sa babu wanda ya ga shigar ku gidan tare da ita." Zuciyar tasa ta ci gaba da fada masa. Jikin Hilal ya dauki rawa sa'ar da ya tuna lokacin da suka zo kofar gidan dazu. "Sannu da zuwa Hajiya." Wasu mutane guda biyu suka gaisheta, sa'ar da Zainab ta tsayar da motar a kofar gidan domin kofar a rufe babu kuma me budewa tun da ta sallami duk masu gadin domin ta sami sakewa da tsohon kwartonta dakta Sadi. "Yauwa sannun ku dai. Dan Ba'u" Hajiya zainab ta ce da daya daga cikin mutanen biyu wadanda suka nufo gurinta a rusune cikin fadanci Hilal ya dubi yar rumfar kwanon dake daf da kofar gidan sai ya ga ashe yar karamar tireda ce a gurin mafi yawa-yawan abubuwan dake cikinta biskit ne da alewa kala daban-daban. Me yiwuwa yaran masu hali dake yankin unguwar ne ke saya. Hilal ya ce cikin zuciyarsa. "Bari a bude miki Hajiya ba ma sai kin fito ba." daya daga cikin mutanen wanda ta kira da Dan Ba'u ne yace hakan. Cikin sauri ya nufi kofar ki-ki-ki-ki ya janye kofar gefe guda sannan ya ce. "Bismillah Hajiya." Zainab ta tuka motar zuwa farfajiyar gidan. Bayan ta tsayar da motar sai ta fito daga cikin motar a daidai lokacin da dan ba'u ya ke kokarin rufe kofar. "Dan Ba'u." Ta kira sanansa Cikin sauri Dan Ba'u ya taho inda take ya durkusa "Gani Hajiya" Hajiya Zainab ta mika masa takardar kudi ta ce. "Na gode, ga wannan kwa raba da wannan aboki naka na waje." "Na gode Hajiya." Dan Ba'u ya ce Duk wannan Hilal na zaune cikin motar bai fito ba. A daidai wannan lokacin ne ya ji Dan Ba'u yana cewa da Hajiya Zainab. "Ah.. Hajiya wannan dan uwan Alhaji ne.. naga kamar sun yi kama." Hilal ya ji gabansa ya fadi domin ya san irin wadannan mutane yan zaman sheda ne ba kasafai suke manta fuskar duk mutumin da suka gani sau daya ba. "Oh! Hila....uhm...u hm....abokin... Aikina ne..." Ta fada muryarta na rawa. Hilal ya ji abin da ta ce ya kuma ji irin rawar da muryarta take yi ya kuma tabbata Hajiya Zainab ba gwana ba ce wajen iya karya "Oh....to sai an jima Hajiya." Dan Ba'u ya ce. Sannan ya dubi Hilal ta cikin gilashin motar. Mutanen biyu suka kurawa juna idanu na dan lokaci sannan sai Dan Ba'u ya juya cikin sauri ya nufi kofar gidan ya fita daga waje Ya janyo ta ya rufe Hilal ya lura kamar akwai alamar murmushi a gefen bakin mutumin Tun daga wannan lokaci Hilal ya san a duk inda suka hadu Dan Ba'u ba zai taba mantawa da shi ba Dan haka a lokacin da Hilal ke jingine jikin bishiyar yana tunanin tafiya gida sai ya ga bazata sabu ba wai bindiga a ruwa. Tabbas ya sani idan an dade ba a sami gawar zainab ba kwana biyu inda kuwa har yan sanda suka fara bincike ba za a dade ba su Dan Ba'u zasu bada shaidar cewa sun ganshi da ita sun shiga gidan. Gumi ya ci gaba da sartu akan goshin Hilal tuni har rigar dake jikinsa ta fara mannewa a bayansa. Tunanin mahaifiyarsa ya fado masa. Idan har akwai abin da Hilal yake tsoro to shi ne bacin ran mahaifin sa. Ya riga ya sani idan allurar sojansa ta motsa mahaifiyarsa ma ba kyaleta yakeyi ba ballanta na kuma shi Hilal ya riga ya sani ko da kwartanci za a tuhume shi zai da shi idan mahaifinsa ya sami labari kashe shi zai yi tabbas kashe shi zai yi ! Duk da yake dai mahaifin Hilal kafa daya ke dashi ido daya amma Hilal na da wayo sa'ar da mahaifinsa ya ke cewa sai ya harbe wani saurayi dake yi musu ihu kullum akan kwanar layi in ban da manyan unguwa sun sa baki da abin ya baci Wannan shine tunanin da ya sa Hilal barin gida kano. Har yanzun nan da Hilal ke gaban mahaifiyarsa yana bata labarin tafiyarsa zuciyarsa na tuna lokacin da ya isa tashar motar dogayen motoci dake zuwa kudu. A wannan lokacin dan kudin dake aljihunsa basu taka kara sun karya ba a haka ya isa tashar ba tare da ya san inda zai dosa ba. Ya jima yana zagaye a cikin tashar...... INA KUMA HILAL ZAIJE ??? BINDIGAR KWALI--> 13 . Ya jima yana zagaye acikin tsashar lokaci-lokaci ya kan duba agogo a zuciyarsa yana tunanin me yiyuwa yanzu an tsinci gawar Zainab. a'a me yiwa Zuhuriyya ta farka cikin dare ta sami mahaifiyarta a kwance cikin jini Hilal ya tausayawa Zuhuriyya irin halin maraicin da zata shiga Tsawon lokaci Hilal na ta zagaye- zagaye cikin tashar tuni har hankalin fasinjojim da ke shirin tashi karfe bakwai ya fara kaiwa gareshi. A daidai lokacin ne Hilal ya hangi wani bahaushe dan duniya zaune a gefe guda sanye da shudiyar riga ta "Jeans" da wandonta, gashin kansa ya koma tsakiya goshin na kyalli kamar madubi saboda sanko a hannun mutumin karan sigari ne yana karawa sararin samaniya hazo babu abin da ya dameshi lokaci- lokaci ya kan dubi katon agogon mai kamar ankwa dake hannunsa, ga dukkan alamu ya kosa motar ta tashi. Hilal ya matsa kusa da mutumin jikinsa na rawa ya ce. "Wannan motar ina za ta?" Mutumin dan duniya ya busa hayaki sama kana ya jefar da guntun tabar ya take da katon bakin takalminsa ya dubi Hilal. "Ikko za ta sai ka hanzarta. Ina tsammanin akwai

Chapter 4 of 7