Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
ne to wata dabara ta fado masa. "Sannu abokina." Hilal ya ce da yaron sa'ar da ya kawo dab dashi. Yaron ya tsaya a daidai tagar motar yayin da karensa ma ya tsaya yana sunsuna jikin motar. "Sannu da zuwa...ina wuni." Yaron ya ce cikin zazzakar murya. Hilal ya lura da cewa yaron kamshin alewar cakulan ya ke yi. "Lafiya lau abokina." Hilal ya amsa sannan sai ya dubi yaron ya ce "Dan Allah abokina, ko ka san wata...ah anan layin ana ce mata Zuhuriyya?" Yaron ya dubi Hilal ido-da-ido ya ce "Ni ma yayata sunanta Zuhuriyya." Hilal ya ji zuciyarsa ta harba tsakanin hakarkarinsa. "Uhm...ita yayar taka babba ce ?" Yaron ya gyada kai cikin sauri ya ce "Kwanan nan za a yi aurenta ma." Hilal ya dan yi jim, kwakwalwarsa na ta tunanin gaggawa, wannan al'amarin caca ne, bari kawai na yanki cacar me yiyuwa a dace. "Idan ka kirawo min yayar taka za ta zo?" yaron ya karkata da kai gefe guda sannan ya shafi bayan karensa ya ce "Uhm to, bari in je na kirawo ma ita, in ta ga dama tana iya zuwa." yana gama fadin haka sai ya juya da baya ya nufi cikin gidan da ya fito karensa na bin sa a baya. Hilal ya ji yawun bakinsa ya kafe...tabbasa in dai har ba kuskure ya yi ba gidan da yaron ya shiga bangarensu daya da inda gidan marigayiya zainab yake a wancan lokacin. To ko ma dai mene ne, shi dai ya aika a kirawo ta. Hilal ya lumshe idanunsa gabansa na faduwa, zuciyarsa na ta sassaka abin da zai ce da ita idan tafito. Tsawon mintuna goma yana nan zaune cikin motar, a zuciyarsa yana cewa. Me yiyuwa ma ba zata fito ba. Sannan ne to ya ji motsin an bude kofa. Yaron ya ruga a guje shi kadai babu karensa, ya zo inda Hilal yake, ya leka ta tagar motar ya ce. "Wai ta ce ka karasa kofar gida." jikinsa na rawa, kafafunsa sun koma kamar na roba sun yi rauni, a haka Hilal ya bude kofar motar sannan ya ce da yaron "Muje ko" Yaron na gaba Hilal na bin sa a baya har suka kai daidai katuwar kofar launin toka-toka. Tun daga kofar Hilal ya ji wani tattausan kamshi ya bugi hancinsa sannan ba tare da tsammata ba sai kofar ta bude sannan kyakkyawar surar ta fito. Hilal ya dafe kirji a firgice da abin da ya gani numfashinsa ya dauke, yawun bakinsa ya kafe. A tsaye a kofar gidan, sanye da riga da siket matsattsu, na wani irin yadi mai santsi mai launi jaja- jaja, kafafunta sanye cikin farin takalmi, wani dan siririn gyale mai kamar rawani a saman gashin kanta me shiki a cikin hasken fitulun kofar gidan Kyakkyawan bakinta shan zuciya na taunar cingam tana dubansa a gatsine..... . Marigayiya Hajiya Zainab Hilal yake gani. Na shiga Uku. tun da nake ban taba ganin fatalwa ba a zahiri sai yau. Hilal ya ce cikin wata murya shakakkiya shin ko daman bata mutu ba? Sannan sai ya dubeta a rude ya ce bakinsa na kyarma. "Zainab..." Budurwar ta dubeshi cikin mamaki sannan ta ce dashi cikin wata murya mai taushin gaske. "Rufa min asiri bawan Allah...Zainab sunan mahaifiyata ne, ni sunana ZUHURIYYA!." kusan mintuna uku suka yi tsaye suna kallon juna. Budurwar na cewa cikin zuciyarta. Wannan kyakkyawan mutumin kuwa kansa daya? Ko shakka ba ta yi mutumin dake tsaye a gabanta kyakkyawa ne na hakika haka nan akwai wani abu a tattare da mutumin da ta ji tana so, ita kanta ba ta san komene ne ba. Hilal, na tsaye yana dubanta sama da kasa, tabbas babu maraba ita da marigayiya Zainab, to sai da sa'ar da kaduwar ta dan sake shi ya lura shekarunta a yanzu basu kai shekarun marigayiya Zainab ba a wancan lokacin. Ko shakka ba ya yi wannan budurwar dake tsaye agabansa yar yarinya Zuhuriyya ce da ya bari kwance tana barci sa'ar da aka kashe mahaifiyarta Zainab. "Malam kai nake sauraro ka sa an yi kirana kuma ka yi shiru." Hilal ya yi firgigit. Tattausar muryarta ita ta dawo da shi cikin hayyacinsa. "Ki gafarce ni ranki ya dade." Hilal yace gami da haske ta da faffadan murmushi lokaci guda kuma zuciyarsa na dawurwuri tana nemo masa abin da ya kamata ya fada mata. "Shiga gida Shafi'u...yanzu nima zan taho." Zuhuriyya ta ce da yaron da ya cewa Hilal shi kanenta ne. Cikin sauri Hilal ya dubi yaron "Abokina tafiya za kayi...na gode to." Ina ma ace ina da daddadar cakulan da na bashi. Hilal ya ce cikin zuciyarsa. Yaron ya wuce cikin gida karensa na bin sa a baya kamar inuwa. "Uhm hum ina sauraronka." Zuhuriyya ta ce dashi. Irin muryarsu daya da mahaifiyarta sai dai tata ta dan fi taushi kadan. Hilal ya gyara tsayuwa. "Ah, kin san dai yadda al'amarin Allah ya ke...ran nan ne zan wuce na hange ki...shi ne to na ga ya kamata na tsaya mu dan gaisa." Zuhuriyya ta jingina da jikin kofar kanta a sunkuye ta tsuke baki ta ce. "To ai mun gaisa din ko, na iya tafiya..." Hilal ya ji kirjinsa ya buga "Eh, to abin ya wuce da haka Zuhuriyya...dom in na ji a raina ina kaunarki." Ya dan yi shiru yana duban yanayin fuskarta sannan sai ya dada da cewa. "Allah sa dai abin da na fada ba zai sosa miki zuciya ba." Ga mamakinsa sai ya ga ta girgiza kai da murmushi. "Ya ya mutumin da ya ce yana kaunarka zai yi laifi, ni ko kadan baka yi min laifi ba, sai dai kawai ina fargabar ka zo a makare." Hilal ya dubeta ido da ido "Me kike nufi da na zo a makare?" "Ina nufin an yi min miji domin nan da kwana bakwai za a yi mana baiko dashi." Abin da ta ce bai zo masa a bazata ba, tun da daman kanenta ya ce dashi an kusa aurenta. "Lallai na fi kowa rashin sa'a aduniya." Hilal ya ce yana duban fuskarta me sheki. Da kyar yake iya hadiyar yawu domin gani yake yi kamar da marigayiya zainab suke tsaye, to sai dai ko kusa ko alama wannan budurwar dake tsaye agabansa bata nuna alamun tama gane shi ba. "Me ya sa ka ce haka? "Saboda na rasa kyakkyawa kamar ki." Hakan da ya ce shi ya sa ta dubansa da wani faffadan murmushi. "Kada ka damu kaima Allah zai baka wacce ta fi ni." "To Allah ya sa." Hilal ya ce yana duban zoben dake dan yatsanta ko shakka ba ya yi zobensa ne da ya sa mata a daren da aka kashe mahaifiyarta. "Ni zan tafi ka ga dare ya fara." "To amma kafin ki tafi zan so ki yi min wata alfarma daya." Zuhuriyya ta dubeshi ta ce "Wace alfarma kuma, na fada maka na riga na zabi mijin aurena." "Na ji, na kuma fahimce ki, amma idan babu damuwa zan ringa zuwa lokaci-lokaci muna dan gaisawa...a matsayina na dan uwanki." Zuhuriyya ta danyi shiru. Ta san cewa idan ta sake mijin da zai aureta ya gansu tare ransa ba karamin baci zai yi ba, to sai dai kuma akwai wani abu mai karfin gaske, wani abu mai kama da mayen karfe tattare da kyakkyawan mutumin, wanda ke fizgarta, ta ji kuma tana son ta sake ganinsa takuma sake jin wannan daddadar murya. Zuhuriyya ta yi mamakin jin yadda hankalinta ya kwanta da mutumin don ji take yi kamar ta dade da saninsa. "Ba komai...dan dai gaisuwa kana iya zuwa idan ka sami lokaci." Zuhuriyya ta ce dashi. "Godiya nake ranki ya dade." "Ni ke da godiya, da ka taso ka zo har gurina." Zuhuriyya ta ce, sannan ga mamakinsa sai yaga ta bar jikin kofar gidan da ta ke jingine ta fito waje sosai. Ganin haka sai ya dauki haske, ya juya ya nufi inda motarsa take. Zuhuriyya ba biye da shi a baya. Ko da suka je daidai da inda motar take sai ya bude motar sannan ya dubi zoben dake hannunta ya ce. "INA SON ZOBEBINDIGAR KWALI--> 17 . Ya bude motar sannan ya dubi zoben dake hannunta ya ce "INA SON ZOBEN NAN DAKE HANNUN KI WALLAHI" Zuhuriyya ta dubi zoben cikin murmushi ta ce "Allah ko? Tsohon zobene nima nake ta fama dashi." Hilal ya yi kamar ya tambayeta inda ta sami zoben sai dai ya sauya shawara. "To Allah ya kiyaye. ni na tafi." Ta juya tana rausaya ta nufi kofar gidan sannan ta tsaya tana hangensa. Hilal ya tashi motar ya fara tukawa sannan ne to ya hangeta ta cikin madubi tana daga masa hannu. Koda Hilal ya fara tafiya sai ya yi ajiyar zuciya. Bai yi mamakin rashin gane shi da Zuhuriyya ta yi ba domin yasan shekaru ashirin da daya sun yi yawan da za ta iya manta Hilal dinta. To amma duk da haka ya lura akwai wani boyayyen abu da ke janyo su yana kokarin hadasu. Hilal ya yi tsaki sa'ar da ya tuna da cewa kusan zuwan banza ya yi domin bai ko kama hanyar da zai bi ya nemi azzalumin da ya kashe mahaifiyarta ba.************ **** . Washegari da safe misalin karfe goma sha daya, Rukayya da Hilal suka isa gidan cikin marsandin Rukayya. Rabon Hilal da gidan tun wata rana da suka zo da yan ajinsu gaba daya domin su yiwa mahaifiyar Rukayya ta'aziyar wani karamin kanin Rukayya da ya rasu. Aka shiga da Hilal wani katon dakin shakatawa. "Zauna anan na kirawo maka ita ku gaisa." Rukayya ta ce cikin murmushi. Hilal ya gyada mata kai. "Ya ya na ga duk kana gumi kamar ka hadiyi kunama?" Hilal ya dubeta da murmushi ya ce "Ke fa ba kya rabuwa da tsokana dan Allah je ki kirawota din an gaya miki tsoro nake ji...sai ka ce wani karamin yaro." Tana rausaya ta shige zuwa cikin gidan. Ba dade ba sai ga ta ita da mahaifiyarta. Bayan sun gaisa, sai Hilal ya lura ashe itama kamar Zuhuriyya, Rukayya kamar hoton mahaifiyarta take. Suka yi yan surutai a kunyace sannan Hilal ya yi sallama da mahaifiyar Rukayya suka fita. Lokacin da Rukayya ta dawo daga rakiyar Hilal ne to ta sami mahaifiyarta zaune a falon tana jiran dawowarta. "Rukayya....wan nan kuma daga ina kika samo shi?" Rukayya ta sunkuyar da kai. "Mama ba ki gane shi ba, shi ne fa dan ajin nan namu da kike ganin hotonsa kullum a gurina." Mahaifiyarta ta dubeta cikin mamaki ta ce A'a ha, iko sai Allah saurayin da ake cewa ya mutu shi ne kuma ya dawo?" Rukayya ta gyada kai cikin farin ciki sannan ta sunkuyar da kai ta ce "Mama...kwanan nan zan yi aure." Wani zazzafan hawaye na farin ciki ya subuce daga idanun mahaifiyarta tata. Wannan ita ce kalmar da a kullum kwanan duniya take fatan ta fito daga bakin diyarta Rukayya. "Shi din za ki aura? Rukayya ta gyada kai a kunyace.******* **** Daga ita sai doguwar riga mai shara-shara shudiya kanta babu dankwali hakan shi ya bai wa siraran gashin kanta masu tsayi da sheki bajewa akan doron matashin kan da take kwance. Duk kusan minti guda sai ta yi juyi, ta kasa barci kusan sa'o'i uku kenan tana ta mutsu-mutsu akan gadon kamar kifi a cikin koma, da ta rufe idanunta sai ta ganshi tsaye a kofar gidan yana yi mata murmushi. "Na shiga uku!" Ta ce da kanta "Me ke damuna ne?" A daidai lokacin ne agogon dake kan dan teburin dake dab da gadon Zuhuriyya ya dauki jiniya. Karfe goma sha biyu na dare. Tun sa'ar da mutumin ya bar kofar gidan ba ta sake samun sukuni a zuciyarta ba abin kamar asiri haka kawai sai ta ji babu abin da take so sai ta sake ganinsa. Za ta so ace ya sake dawowa, domin su yi ta hira tana sauraron muryarsa tana kuma kallon fuskarsa kyakkyawa. Zuhuriyya ta zargi kanta da wauta dan me za ta bar shi ya tafi ko sunansa ba ta sani ba. Abin da ke damun zuciyarta shine, tun sa'ar da ta kalli mutumin ta fara tunanin kamar ta san shi, kamar sun taba haduwa a wani guri daban, to sai dai kuma har ya tafi bata iya tunano inda ta taba ganin nasa ba. Zuhuriyya ta mike zaune akan gadon, sannan ta janyo littafin hoton dake daf da ita, ta bude shafin da hoton mijin da zata aura yake ta kura masa idanu, a tunaninta wai ganin surar mijin da zata aura na iya kawar mata da tunanin mutumin. Ga mamkinta sai ta ga kamar fuskar mijin da take tunanin auren ta yi mata tsufa sosai sannan ne to ta tambayi kanta tambaya mai tsada. . "WAI SHIN ME NA GANO AJIKIN MUTUMIN NAN DA YAYI KUSAN SA'A DA UBANA ? KUDI ? AI MUNADA SHI KYAU ? AI BASHIDA MA KYAUN..." . Tunaninta ya katse domin ta san ganin mutumin dazu ne ya munana mata mijin da zata aura. Zuhuriyya ta rufe littafin hotunan, ta dada kwanciya rub da ciki akan gadon sannan ta fara bijiro da surar mutumin cikin zuciyarta tare da kokarin ta tuno inda ta taba ganinsa. A haka barci ya dauketa a cikin barcin ne to ta yi mafarkin mahaifiyarta a ranar da ake bikin zagayowar ranar haihuwarta.**** ******** "Kada ka yaudari kanka Hilal, bakin rijiya ba gurin wasan makaho ba ne, wannan budurwa ba ta dace da kai ba in ma ta dace din ba wani damuwa ta yi da kai ba gara ma ka cireta daga cikin zuciyarka ka auri me kaunarka tsawon shekaru ashirin da daya gami da kyautatawa mahaifiyarka." Duk wannan dogon bayani zuciyar Hilal ce ke yi masa cikin wata boyayyiyar murya da shi kadai ne ke iya jin ta. Fitowarsa kenan daga wanka ba a dade ba ya sanya doguwar riga launin kasa tazarce ya dora hula irin kayan sannan ya fesa turare kana cikin sauri ya jefa kafarsa cikin wani bakin takalmi na yan birni mai daukar ido kamar madubi ya nufi kofar gida inda dankareriyar motarsa take. Cikin sauri ya shigo, sannan ya tuka motar ya fara tafiya yana duban agogon cikin damuwa. Kamata ya yi fa ace yanzu gidansu Rukayya zani. Hilal ya fadawa kansa. A daidai lokacin da ya hau kan babban titi ya karawa motar gudu. Hilal ya gama yanke shawara a zuciyarsa, tabbas Rukayya zai aura to sai dai kuma abu biyu ne ke damun zuciyarsa a yanzu. Na farko dai shi ne ya riga ya dauki alkawarin in dai mutumin nan da ya kashe zainab yana raye sai ya gano duk in da yake, to ga shi kuma har yanzu nan bai sami ko da hanya daya ba da take nuni da inda zai bi ya gane mutumin. ...dan samari tashi ka fice daga gidan nan tun kafin mijinta ya rutsa da kai ni zan iya rufa maka asiri a matsayina na abokin mijinta... Hilal ya tuna da kalaman mutumin a ranar da ya kama shi a gidan marigayiya Zainab Wannan ita ce hujjar fitowar Hilal a wannan lokaci domin in dai har abokin mijin Zainab ne akwai yiyuwar Zuhuriyya ta iya saninsa. To sai dai kuma akwai abu na biyu dake damun zuciyar Hilal, shi ne Zuhuriyya. A daren jiya da kyar ya runtsa, domin da ya rufe idanunsa sai ya ga fuskarta, tunaninta ya fara yawaita a zuciyarsa. Hilal baya farin ciki da haka domin ya riga ya yankewa zuciyarsa cewa ba shi da wata matar aure sai Rukayya. "Hajiya Zainab ita nake so ta riga ta mutu..." Hilal ya fadawa kansa "Zuhuriyya daban rayuwata daban, tana da wanda take so...babu ruwana da ita." Hilal ya sake fadawa kansa. To amma sa'ar da ya karkata kan motar ya shiga layin shi kansa ya san abin da ya fadawa kan nasa babbar karya ce domin ya san muddin zai ci gaba da ganin Zuhuriyya tsahon son mahaifiyarta dake cikin ransa na iya yin tasiri a kansa. Ko a lokacin ya fi dokin ganin Zuhuriyya akan Rukayya. Karfe biyar da yan mintuna agogon dake cikin motar ya nunawa Hilal. Kamar jiya a wannan karon ma a hankali yake tafiya a cikin layin to sai dai kuma akwai saukin faduwar gaba sabanin jiya a kalla dai yanzu ya san ta san shi. Hilal na wuce wasu tagwayen gidaje masu kama daya, sai ya hango Zuhuriyya tsaye a jikin wata katuwar mota shudiya kirar Toyota, mai duhun gilasai, domin daga inda yake ba ya iya hango wanda ke cikin motar. Wannan shi ya sa Hilal yin fakin a gefe guda bai karasa kofar gidan ba. Ga mamakinsa sai ya ji zuciyarsa ta harzuka, ransa ya baci. "Me ke damuna ne? Hilal ya tambayi kansa, sannan ya dan dada kwantarwa da kansa hankali sai ya saki wani busasshen murmushin yake wanda ya fi kuka ciwo. "Mijinta ne...tabbas mijin da zata aura ne...to in ma wanene ina ruwana...Zuhuri yya kamar ya' ce a gurina." Hilal ya sake fadawa kansa yana kuma kokarin lallashin zuciyarsa domin ji yake yi kamar za ta tsaga kirjinsa ta fito saboda tsananin kishi, Ba'a dade ba sai ya ji gumi ya fara wanke masa fuska, cikin sauri ya lalubi aljihun tazarcensa ya zaro wani farin kyalle ya goge fuskarsa, sannan ya lumshe idanu gami da ajiyar zuciya ya fara addu'a. "Allah...ka rabani da ciwon son abin da zan sha wuya ban same shi ba. A daidai lokacin da ya fara addu'ar ne ya ji sautin injin mota ta nufo inda yake. Hilal ya bude idanunsa sai ya ga ashe shudiyar motar ce da ya ga Zuhuriyya tsaye kusa da ita. Hilal ya yi kokarin hangen mutumin da ke cikin motar, amma da yake motar ta riga ta dan gifta kafin ya bude idanunsa kuma duk gilasan gefe na motar masu duhu ne, bai iya ganin direban motar ba, amma ya ji tattausan kidan wata wakar fim na Hausa na tashi daga cikin motar. Zuciyarsa Na.BINDIGAR KWALI--> 18 . Zuciyarsa na kuna kamar ta kama da wuta Hilal ya kunna motar da niyyar ya karasa kofar gidan dubawar da zai yi haka, sai ya hangi Zuhuriyya ta cikin madubin motar ta nufi inda yake dauke da wata farar ambulan a hannu. Dan haka sai ya kashe motar, sannan ya fara niyyar kiranta idan ta zo wucewa domin ga tsammaninsa gidan makwabta za ta shiga. Amma ga mamakinsa sai ya ga kai tsaye gurinsa ta taho. "Sannu da zuwa...kai na gani na taho." Zuhuriyya ta ce lokacin da ta karaso ta bangaren da yake rungume da farar ambulan din gami da faffadan murmushinta. "Har ka dawo mu sake gaisawar haka da wurwuri, ai na dauka sai nan da wata zan sake ganinka?" Hilal, zuciya na bugu, ya dubeta da murmushin yake. "Ji na yi ba zan iya daurewa ba sai na sake zuwa na yi kwalli da...kyakkyawar fuskarki." Zuhuriyya ta fashe da wata zazzakar dariya gami da rufe idanu "Kai dai wallahi ba ka rabuwa da tsokana, ina wata kyakkyawar fuskar take anan, kuma ina kai ina kallon fuskar matar wani." Hilal ya ji kamar ta soka masa wuka a kahon zuci. "Wan...nan da na hange ku tare shi ne mijin naki?" Zuhuriyya ta gyada kai "Shi ne mana, ai da ka karaso ma kun gaisa" Hilal ya yi murmushin yake "Zan so ace kuwa mun gaisa" Ya yi karya "Amma ba komai wata rana ma gaisa" "Haka ne" Zuhuriyya ta ce tana wasa da farar ambulan din dake hannunta Hilal ya lura kamar hotunane a ciki. Suka yi shiru na dan lokaci. Hilal ya yi zaton za ta ce dashi "Ni zan tafi" Amma maimakon haka sai ya ga ta ci gaba da tsayuwa. "In ba damuwa...ina ganin ai gara ki zagayo nan ki zauna ko...maimakon ki yi ta tsayuwa" Hilal ya ce da ita a tausashe. Zuhuriyya ta dan yi jim, sannan ba tare da ta dube shi ba sai ta ce "To" Tana rangwada kamar dawisu ta zagaya daya bangaren motar. Tun kafin ta karasa Hilal ya bude mata kofar motar gidan gaba, Zuhuriyya ta zauna a hankali, kusan duk a tsorace, kafafunta a waje, amma ta yi kokarin juyowa kadan yadda za ta ke ganinsa, ta ajiye farar ambulan din a kan cinyarta. Hilal ya dubeta da murmushi sannan ya dubi farar ambulan din dake kan cinyarta ya ce "Wannan ko hoton mutumin ne a ciki?" Zuhuriyya ta gyada kai "Mijina za ka ce" Hilal ya ji kamar ta kara soka masa kibiya a kahon zuci, sannan ya dubi fuskarsa yana cewa "Na san dai ko wane ne mijin nan nata sai dai ya fi ni kuruciya, amma ba dai kyawun fuska ba." "Mijin naki a ina yake?" Hilal ya tambayeta zuciyarsa na kuna. Zuhuriyya ta sunkuyar da kai gami da tsuke baki. "Likita ne...a asibitin kudi na baba na...me yiyuwa ma ka sanshi kwararran likita ne anan gidajen ma'aikata na asibitin ma yake gida mai lamba (24)" Zuhiriyya ta dan yi shiru tana duban Hilal. "Ah, ki ce layin mu daya, nima likita na karanta." Hilal ya ce, zuciyarsa na tuna bakin cikin ranar da aka koreshi a shekararsa ta karshe a Ikko. "Ashe kai ma likita ne?" Hilal ya gyada kai yana kallon farar ambulan din dake hannunta. Haka kawai sai ya ji yana son ya ga hoton wannan miji da take son aura. "Zan iya ganin hoton mijin na ki?" Hilal ya bukata yana kallonta ido da ido. Zuhuriyya ta dubeshi cikin mamaki. "Me za ka gani a hotonsa...ba fa wani saurayi bane...kai ma ka fi shi yarinta." Akwai alamun daci a muryarta sa'ar da ta furta bayanin. "Babu ruwana da tsufansa, ni dai so nake kawai na ganshi, kika sani ko wata rana ma hadu da shi bayan ya aureki...ina laifi idan mun yi mutunci da shi." Zuhuriyya ta zunkuda kafada. "Tun da dai ka dage gashi nan ka gani, amma fa na fada ma ba yaro bane..." Ta mika masa farar ambulan din ta dauke kai gefe guda. Hilal ya karbi farar ambulan din ya zaro hotunan sannan ya sami kansa yana kallon wasu fararen idanu kamar idanun maciji. HILAL YAJI KAMAR AN TAFKA MASA GUDUMA A KIRJI. . Da Allah ya sa Zuhuriyya na lura da ta ga zaburar da Hilal ya yi sa'ar da ya ga hoton. Doguwar fuskar dake kallonsa da fararen idanu a tsaitsaye gami da dogon hanci mai dan doro kamar hancin aku su suka hautsuna hanjin cikin Hilal, suka dagula duk wani lissafi dake kwakwalwarsa, sannan sake yi jifa da tunaninsa zuwa can baya...shekaru ashirin da daya da suka wuce, har abada koda zai yi tsahon ran shekara dubu a duniya Hilal ba zai taba manta fuskar mutumin ba. Jikinsa na rawa Hilal ya ajiye hoton a hankali sannan ya dubi Zuhuriyya muryarsa na rawa ya ce a sassarke. "Wannan shi ne mijin da za ki aura?" Zuhuriyya ta gyada kai. "Ya ya sunan shi?" Zuhuriyya ta dubeshi cikin zargi. "Me ya sa kake son ka san sunansa?" "Saboda ya yi min kama da wani mutum da na sani tun ina karami." Zuhuriyya ta lumshe idanu ta ce "Ai daman na fada ma da wahala ma idan ba ka san shi ba sananne ne in dai kana zuwa Jumare Special Hospital dole ka san shi...sunansa DAKTA SADI." Hilal ya lumshe idanu, ji yake yi kamar zai sume, domin a karo na farko cikin shekaru ashirin da daya ya gano adireshi da sunan azzalumin da ya kashe uwa yanzu kuma yake kokarin auren diyarta MARAINIYA Zuhuriyya.******** . Lokacin da Hilal ya kawo kofar asibitin tuni har goma na dare ta wuce. "Lokacin ziyara ya wuce." Maigadin asibitin ya ce dashi, wani motsattsen tsohone mai fuska da tsayi kamar silifan tsofaffi kansa babu gashi sai wasu adadi dake makale akan doron kan shan kwai adadin yawan gashin bai fi ashirin da uku ba. "Ka gafarce ni baba, ba ziyarar marar lafiya na zo ba gidan dakta Sadi na ke son zuwa." Dattijon me gadin ya karkatar da kai gefe guda. "Ba ta nan ake shiga gidajen ma'aikata ba, zagaya ta can baya bangaren katangar kudu za ka ga shudiyar kofa ta nan ake shiga." "Na gode." Hilal ya ce da faffadan murmushi kai ka ce gafara dattijon ya yi masa. Mintuna uku da faruwar hakan Hilal ya ja birki a kofar gida mai lamba ashirin da hudu (24) Tun karfe biyar din da suke tare da Zuhuriyya basu sami damar rabuwa da juna ba sai karfe tara. Lokacin da magariba ta yi sai Hilal ya kada baki ya ce. "Ya kamata na tafi kin ga lokacin sallah ya yi." "Ba ga masallaci can ba, akan kwana je ka yi sallar ka dawo mana ko wani gurin za ka?" Zuhuriyya ta ce. Abin ya bashi mamaki shi kansa yana son ya tsaya ya yi ta sauraron daddadar muryarta, to amma ba zai iya jin wani dadi ba a duniya bayan babban makiyinsa na nan raye a duniya ya kashe wacce ya fi kauna fiye da komai a duniya. "Akwai wani tsohon abokina da na dade ban kai masa ziyara ba gidansu nake son zuwa." Hilal ya yi mata karya. "Ka bari to ka tafi karfe tara ku maza dare baya hana ku yawo..." Zuhuriyya ta ce "In ban da abinka yanzu idan na yi aure kuma ba shi kenan ba." Akwai alamun sosuwar zuciya a muryarta sa'ar da ta ce hakan. Lokacin da karfe tara ta yi, sai Hilal ya dubi agogo. Zuhuriyya ta dubeshi cikin damuwa. "Har karfe taran ta yi?" Hilal ya gyada kai "Ai kin san yanzu dare baya wuyar yi." Zuhuriyya ta sunkuyar da kai kasa "Za ka dawo gobe ne?" Hilal ya ji zuciyarsa ta harba. "Me...me zai hana indai kin ce na dawo din." Zuhuriyya ta fita daga motar ta rufe masa kofar sannan ta leka ta tagar motar, ta ce dashi a tausashe. "Bawan Allah, gashi ko sunanka ban sani ba, amma wallahi ji nake yi kamar na fi shekara goma da saninka shi ya sa bana son rabuwa da kai." Hilal ya ce a ransa., Kin fi shekara ashirin da daya da sanina yar budurwa, tunawa ne kawai kika kasa. Sannan sai ya dubeta ya ce a fili. "Gobe war haka muna tare...nima ji nake yi kamar na fi shekara ashirin da saninki........BINDIGAR KWALI--> 19 . Zuhuriyya ta saki wata faffadar dariya hannunta kankame da tagar motar. "Allah ya kiyaye to ka gaida gida...ina jiranka goben." Ta juya a hankali ta nufi kofar gidansu. Har ta shige gida bata juyo ta kalleshi ba. A yanzu da Hilal ke zaune cikin motar yana kallon dan madaidaicin gidan Likitan wanda ke zagaye da dogayen bishiyoyi da shuke-shuken furanni sai ya yi mamakin in har Zuhuriyya ta taba cewa da daktan "Ina jiranka gobe. Me yiyu ta taba fada masa hakan. Hilal ya ce da kansa. Tun da dai ita bata san shi ya kashe mata mahaifiya ba." Tsawon mintuna goma Hilal na zaune yana kallon gidan. Babu wani mahaluki da ya shiga ko ya fita daga gidan. Don haka jikinsa na rawa sai Hilal ya rufe motarsa sannan ya taka a kasa ya ratsa ta tsakanin shuke-shuken da bisoshin da ke gidan ya nufi kofar gidan yana sauraro babu komai sai tattausan kidan zamanin dake tasowa daga cikin gidan. Hilal ya dauke numfashinsa sannan ya danna kararrawar dake manne a jikin bango. Dannawarsa ke da wuya sai kofar ta bude kai ka ce daman jira ake yi ya danna a bude kofar. "Malam da Allah ka bar ni na huta bana iya ganin majinyata a gida gobe ka sameni a asibiti." Dakta sadi ya ce da Hilal a fadace daga shi sai gajeren wando babu komai a jikinsa. Hilal ya ji kamar ya daga hannu ya naushe shi sai ya hana zuciyarsa. "Ba rashin lafiya ta kawo ni ba magana nake son yi da kai." Hilal ya ce yana dubansa ido da ido. Dakta sadi ya dubi kyakkyawan mutumin sama da kasa bai gane shi ba amma jikinsa na bashi cewa kamar ya taba ganinsa a wani wuri. "Ba na iya ganawa da kowane mutum a wannan lokacin..ka zo gobe ka sameni a ofis yanzu lokacin hutuna ne." "Ni yanzu nake son magana dakai idan aka kai gobe ai ta yi tsami maganar." "To ka bar ta ta yi tsamin ta har ta rube dan bani da ra'ayin jinta a yanzu." Dakta sadi ya ce a harzuke. "ka da ka yi fushi Dakta." Hilal ya ce dashi a tausashe "Na san dan ba ka san wacce magana ce ke tafe da ni ba shi yasa kake kokarin korata." Dakta sadi ya dubi Kyakkyawan mutumin a rude. A zuciyarsa yana cewa yau Allah ya hadani da mahaukacin mutum lallai ciwon hauka ne ke damunsa. amma dan me za a turo min mahaukaci da wannan daren bayan kowa ya san ni ba likitan mahaukata bane? "Dan Allah malam ka da ka takurawa rayuwata.. wacce magana kake son fada min ne?" Hilal ya dafa kofar gidan da hannunsa sannan ya dubi Dakta Sadi da faffadan murmushi. "Daman magana na zo ma da ita akan tsohuwar masoyiyarka Hajiya Zainab wacce ka kashe...amma tun da ka ce baka son ji yanzu to mu bari sai gobe din idan na sami lokaci na dawo in kuma ban samu ba na fadawa amaryarka Zuhuriyya sai ta yi maka bayani." Hilal na gama fadin haka sai ya juya zai tafi. Dakta Sadi ya zabura a tsorace "A'a....malam.. .shigo-shigo daga ciki dan Allah." Hilal ya juyo kadan kana ya girgiza kai ya ce. "Ka je ka huta kada na bata ma lokacin barcinka ka huta lafiya Sai goben ma hadu kamar wannan lokacin." Cikin sauri Hilal ya juya zuwa gurin da ya ajiye motarsa. Koda ya kai ga motar sai ya juyo ya dubi kofar gidan. Dakta Sadi na

Chapter 6 of 7