Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 7
da abin ya faru Dakta Sadi bai moru ba kuma duk abin da ya taba a ranar sai tsautsayi ya afkawa abin misali da safe zai shiga wanka ya dauko bokitin roba cike da ruwa sai tunanin zainab ya fado masa a take anan ya jefar da robar ya dafe kirji cikin bege da bakin cikin ganin shi da ita sunyi hannun riga kenan. Bokitin robar fashewa ya yi sai da ya sayi wani. A ranar dai kuma kadan ya rage mota ta kade shi yazo tsallaka titi a daidai lokacin da ya hango wata mata za ta shiga asibitin awon ciki matar kamar su daya da Hajiya Zainab. Haka dai abubuwan tsautsayi suka yi ta faru a kansa har zuwa safiyar yau wadda rana ce da zai yiwa wani bawan Allah mai hannu da shuni tiyata. Kadan ya rage Dakta Sadi yace ba zai yi aikin ba to amma kasancewar duk likitocin dake asibitin babu wanda ya yi kwarewarsa kuma mutumin da za a yiwa mai fada aji ne ya ce shi baya son kowa ya tabashi sai likitan da ya fi kowa kwarancewa a asibitin wannan shi ya tursasa Dakta Sadi yin tiyatar. To ganin irin yadda tsautsayi da jarabobi suka yi ta samunsa duk sakamakon begen matar da a yanzu ya tabbata ya kamu da ciwon sonta su suka sa shi fargaba lokacin da ya fito daga dakin tiyatar A da can lokutan baya idan Dakta Sadi ya fito daga dakin tiyata za ka sameshi ne cikin fara'a da annashuwa domin ya san bai taba yin aiki an sami kuskure ba to amma a karo na farko cikin shekara kusan tara kenan sai Dakta Sadi ya sami kansa yana mai shakkar aikin da ya yi dan haka koda talfon din ya sake daukar ruri sai Dakta Sadi ya ji gumi ya rufeshi nan da nan ya nufi kan talfon ya dauka. "Hello, wa ke magana?" "Amburus ne" Aka ce dashi. "Sadi ka yi sauri ka dawo asibiti yanzun nan domin ana son ganinka da gaggawa." Dakta Sadi ya ji numfashinsa ya dauke tuni har tafin hannunsa ya fara jikewa da gumi da kyar ya ke rike talfon din.***** "Am....Amburus in ce dai ko lafiya?" Dakta Sadi ya tambaya "Uhm....to lafiyar kenan amma can daya bangaren iyalan wanda ka gamawa tiyata yanzun nan ba lafiya ba domin ka manta ka dinke tumbinsa dauke da kyawawan almakasanka guda biyu. Sadi ya rike numfashi cikin kaduwa ba zai yiyuwa ba sam- sam ba zai yiyu ba ace ya manta almakashi a cikin mutum haba dai kamar wanda ya fara aikin yau wannan dai kawai wasa ne Amburus ke son yi domin daman ya dade yana yi masa hassada akan aikinsa saboda ganin ya fishi kwarewa. "Amburus saurara da kyau ni ba wasa na tambayeka ba". Amburus dake bangaren ya gimtse dariya da kyar sannan yace. "Da gaske nake wallahi almakashi biyu ka manta a cikinsa." Dakta Sadi ya yi shiru gumi na kwarara akan fuskarsa kamar ruwa can ya nisa ya ce. "To ku bar shi yadda yake kada ku taba shi gani nan zuwa." Amburus ya yi ajiyar zuciya ya ce. "Ai tabashi ko rashin tabashi ba zasu amfaneshi da komai ba domin yanzu ya kusan mintuna biyar kenan a kiyama, ya tafi tare da almakasan ka guda biyu a tumbinsa Dakta Sadi ya yi jifa da kan talfon din cikin fushi da fargaba Karfe biyar da yan mintuna Hilal ya fito dauke da farar takardar tambayoyin jarrabawar a hannunsa. Hilal ya dubi sauran dalibai dake ta faman ife-ife da hayaniya gami da kade-kade wasu kuwa har da yaga kayan makarantar dake jikinsu domin wai duk murna ce ganin daga yau sun yi sallama kenan da makarantar sakandare. Hilal bai kula dasu ba domin shi rayuwarsa cikin tashin hankali take kuma shi kansa ya san jarrabawar da ya zana a yau sai wani gyaran Allah amma zai yi wuya in zai ci. Hilal ya bi ta gefen yan uwansa dalibai wadanda tun suna janyoshi akan ya shigo su dauki hoto har sun gaji sun kyaleshi wasu har da zaginsa wai daman mugun hali ne dashi baya son mutane wasu masu hankali kuma daga cikinsu suka ce a'a duk yadda aka yi dai Hilal yau ba lafiya ba domin ai ada ba haka ya ke ba. . To koma dai mene ne Hilal ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa. Ya bi ta gefen samarin a hankali ya nufi gindin wata katuwar bishiya ta dorawar turawa ya zauna, yana tunani ko kusa ko alama bai son tafiya gida ba don komai ba kuwa sai don ya san idan ya je din ma ba shi da sauran kwanciyar hankali Tuni ya fara nadamar abin da ya fadawa Zainab Duk da yake dai yace da ita ba za su sake haduwa ba hakan bai hanawa zuciyarsa tunaninta ba a wannan karon ma har abin ya fi na da Allah ka cire min kaunarta na huta Hilal yayi addau'a cikin zuciyarsa domin ya san abin da ya yi shi ne daidai ba'a dade ba sai ya ji hawaye ya fara cika masa idanu ya yi sauri ya kifa kansa akan cinyarsa don gudun kada wani dalibi ya hangoshi ya zo ya dami rayuwarsa Kusan mintuna biyar yana zaune a haka fuskarsa cikin hannunsa yana ta begen da ba zai amfane shi da komai ba sai tashin hankali. A daidai lokacin ne to yaji kamar motsi a daf dashi "Hilal." Wata sassanyar murya rarrauna ta kira sunansa. Numfashinsa ya tsaya cak a tsakanin kirjinsa. Duk duniya babu mai irin muryar sai Hajiya Zainab Hilal ya dago kai a hankali idanunsa jajur dasu kamar garwashim wuta "Ha Hajiya zainab me ya dawo dake kuma gurina." Hilal ya ce bakinsa na rawa. Hajiya Zainab ta dubeshi a tausashe ta ce. "Kaunarka ce Hilal ta dawo dani gareka Wallahi na kasa komai saboda kai na je gida nemanka shi ne Umminka ta ce dani kana makaranta ba ka dawo ba" Hilal ya katseta. "Amma...kin san na fada miki bai kyautatu ba abin da muke yi." "Hilal kada ka zalunci kanka na san kaima kana sona tashi muje gida in fada maka maganin matsalar mu ai komai yana da magani" Kafin Hilal ya sami damar musu Hajiya Zainab ta juya ta nufi inda ta ajiye motarta. Bazai iya rabuwa da ita ba ba kuma zai iya jure kunan rai na begenta ba don haka sai ya mike ya bi ta a baya da yan littattafansa a hannu iskar yammacin na karkada su kamar tutar Najeriya**** Dakta Sadi ya yi tagumi fuskarsa na ta faman naso kamar waina Kusan sa'o'i biyu kenan suna ta tattaunawa tsakaninsu da likitocin daga karshe dai suka yanke cewa a rufe maganar kada a sake ta fito fili domin yin hakan zai ceto sunan asibitin daga sharrin yan jaridu. Don kuwa ba karamin abin kunya ba ne ace a fitaccen asibiti kamar wannan ace wai likita ya manta almakashi a cikin majinyaci kuma wai har hakan ta yi sanadiyyar mutuwar majinyacin Wasu daga cikin daktocin dake gurin asirtaccen taron sun so a fito da maganar fili musamman ma Amburus an yi kiyasin cewa Dakta Sadi yayiwa majinyata sama da dari tiyata a cikinsu kuma ba a taba samun wanda ya mutu ba yayin gudanar da aikin. Hakan ce ta sa da yawa daga cikin daktocin ke jin haushinsa saboda ganin nasibin da Allah yayi masa. Sai wajen karfe shida da rabi na yamma Dakta Sadi ya dawo gida wujiga-wujiga kai kana ganinsa ka san ya ji jiki. Dakta Sadi ya shiga bandaki ya watsa ruwa sannan ya fito ya bude firjinsa ya dauko ragowar rabin gasasshiyar kazar da ya ajiye tun jiya ya zauna akan kujera sannan ya yagi tsoka daya ya kai bakinsa ga mamakinsa sai ya ji naman babu dadi. Ya yi sauri ya ajiye kazar akan farantin tangaran sannan ya nufi firjin a karo na biyu ya dauko tataccen lemo a cikin kwalba ya tsiyaya ya kai bakinsa ya hadiye da kyar ji yake yi kamar yana hadiyar ruwan allura. Dakta Sadi ya yi ajiyar zuciya sannan ya jingina bayansa a makarin kujera ya kurawa bango ido kamar yadda malamin kimiyya kan kalli sabuwar kwayar halittar da bai san da ita ba a da. "Zainab" Ya ce a sanyaye kai kace daman a dakin take zaune kusa dashi. Ba zan iya rabuwa da ita ba ya ce da kansa. "Kada ka sake na kara ganin mummunar fuskarka a gidan nan" Ya tuna bakaken magagannun da ta ta jifansa dasu. Dakta Sadi ya sake tashi tsaye ya nufi tagar dakin ya leka waje sannan ya dawo dakin ya kunna talabijin. Wata mata inyamira ce ke tikar rawa kusan tsirara daga ita sai dan kamfai wagagen bakinta a washe tana ta ihu ita a tunaninta wai waka take yi. Dakta Sadi ya yi tsaki ya kashe talabijin din sannan ya maida kayan jikinsa yasa takalminsa cikin sauri ya nufi kofar gida. "Babu abin da zai rabani da ita, wallahi idan na yi wasa kaunarta kashe ni za ta yi ko dai ban mutu ba to tunaninta zai bata min kyakkyawan aikina na kwararren likita gara in je in baiwa zuciyata magani" Dakta Sadi ne ke fadin hakan cikin zuciyarsa. Ya shiga motarsa kirar honda cikin gaggawa ya nufi gidan Hajiya Zainab a lokacin karfe bakwai da rabi na yamma. Ya kudurce a ransa cewa dole ne ma ya shawo kanta ko ta halin kaka domin idan har ya kasa shawo kanta to shi rayuwarsa bata da wani amfani tuni fa har ya kashe rai guda sakamakon tunaninta. To wa ya san kuma me gobe zata haifar ? BINDIGAR KWALI--> 8 . Tuni fa har ya kashe rai guda sakamakon tunaninta. To waya san kuma me gobe zata haifar ??? A daidai lokacin da duk wannan ke faruwa a can filin saukar jirgin sama na Malam Aminu Kano jirgin misara ne (Egypt) ke kokarin sauka. Tun kafin ya gama samun gurin tsayawa motocin agaji na hukumar kashe gobara da kuma motar nan mai dakon tsani suka nufi inda jirgin yake. Ba'a dade ba sai fashinjojin dake saukowa Larabawa ne da kuma bakake yan kasuwa, miliniyoyi. Daga cikinsu kuwa har da ALHAJI HAMISU JUMARE. Alhaji Hamisu Jumare dogo ne kakkaura garsakeken kato baki, amma fuskarsa tana da kyawun gani kuma da yawa daga cikin mutane basa ganin bakinsa saboda irin nairorinsa. Alhaji Hamisu ya biyo jerin gwanon mutanen yana tunane-tunane. Sau hudu kenan yana bugo waya gida domin ya sanar da Hajiya Zainab cewa karfe bakwai da rabi na dare zasu sauka amma ga mamakinsa babu amsa. Me yiyuwa yawace-yawacen nata na banza ta fita. Ya ce cikin Zuciyarsa me yiyuwa kuma matsalolin da iska ta saba kawowa ne akan injinonin sadarwa na Najeriya ya kawo haka me yiyuwa ma talfon din gidan ne ya lalace. Mintuna biyar da saukowarsa wata katuwar marsandi baka taja birki agabansa kamar an jefota. Alhaji Hamisu Jumare ya dubi motar cikin mamaki sannan ne to kofar motar ta bude, wani kurtun dansanda ya fito ya sara masa sannan kuma sai daya kofar ta bude. Nan da nan fuskar Alhaji Hamisu Jumare ta washe Cikin fara'a. "A'a kwamishina Mahmud yau da kai kuma Allah ya fara hadani daga shigowa kasar ?" Kwamishinan yansanda Mahmudu Sidiri ya mikawa Alhaji Hamisu hannu suka gaisa sannan ya ce. "Alhajin Allah kwana biyu rabonka da kasarmu" "Wallahi kuwa ka ga sai yanzu Allah ya dawo dani gashi ma kuma ko tarbata ba a zo ba, na buga waya har sau biyar gidan amma babu amsa" "Af, to shigo mana ai sai mu kai ka gida" Tun suna firamare har zuwa sakandare suke tare, kaddara ce irin ta rayuwa ta rabasu, daya ya zama kwamishinan yan sanda daya kuma fitaccen dan kasuwa. Kwamishinan yansanda mahmud ya dubi Alhaji Hamisu ya ce. "A gaskiya lokaci yayi da yakamata ka rinka tafiye-tafiyen ka da kyakkyawar matar nan taka, kada fa ka bari mu yi ma fashi idan baka nan" Mutanen biyu suka bushe da dariya. Alhaji Hamisu yakai masa zunguri ya ce. "Har yanzu dai kana nan da tsokanar nan taka kamar zamanin makaranta, in ban da abinka wane ne zai yi min fashin Zainab dita, bayan na san duk duniya ba ta da abin so da ya wuce ni..." suka sake fashewa da dariya. A can gaban motar da suke ciki, baburan yan sanda ne wajan guda shida suna ta faman gudu gamida jiniya domin a samarwa da kwamishina hanya. Kwamishinan yansandan ya dubi Alhaji Hamisu ya ce "kana da labarin wata mata da yan fashi suka kashe jiya, na ga an buga a mujallu da jaridu". Alhaji Hamisu ya girgiza kai cikin jimami ya ce. "Kisa! Tab, wato Najeriya ma ta fara baci da munanan dabi'un kashe-kashen al'ummar nan kamar a Amurka."**** Duk cutar da Allah ya halitta sai da ya halicci maganinta, in kuwa haka ne to ni na samo maganin tamu cutar." Hajiya Zainab ta ce tana duban Hilal. Hilal ya dubi tangamemen dakin shakatawar wanda wannan ita ce shigarsa ta biyu sannan ya dawo da idanunsa kan fuskar zainab yana yi mata kallon rashin fahimta. "Wanne magani kike dashi ke da kike matar aure kuma kike kokarin yin soyayya da wani ?" Hajiya Zainab ta girgiza kanta cikin damuwa "Wani lokacin idan kana magana wallahi kamar baka sona Hilal." Kamanninsa suka sauya. "Ba haka bane Zainab ai ke kanki ki dubi idanuna, can cikin kwayar idanuna za ki hango sunanki a rubuce a ciki." Hajiya Zainab ta saki wani tattausan murmushi na farin ciki sannan ta tashi daga inda take ta zo kusa da shi ta zauna, ta dubi inda Zuhuriyya ke kwance ta ga tuni ta yi nisa a cikin barcin da take. "Hilal kasan da ana sayen mutum da kudi, to da ko nawa ne in dai har ina dashi kuma in za ka sayu din zan bayar na sayeka, koda kuwa hakan na nufin na bada raina ne. Duk da yake dai Hausawa sun ce wai ina amfanin badi babu rai, to amman gara dai na mutu saboda kai." Ta dan yi shiru tana mayar da numfashi sannan ta ci gaba da cewa. "Ka ga dai gidan nan ban rasa ci ba, ban rasa sha ba, a cikin arziki muke ni da yata Zuhuriyya domin babanta miloniya ne, haka nan kuma duk abinda nake so na rayuwar duniya Allah ya hore mana, amma za ka yi mamaki idan na ce da kai duk wannan banzane a gurina." "Dan me za ki fadi haka Zainab, kada fa so ya saki fita daga hankalinki, shin yanzu a rayuwar mu ta yau har akwai wani mutum da zai iya bude baki ya ce da kudi banza." "Kwarai kuwa gani nan." Hajiya Zainab ta amsa masa. Kudi da daular gidan nan basu bane a gabana, ni so da kauna ne a gabana." Ta dan yi shiru sannan sai ta dubi Hilal ido da ido ta ce. "Hilal, na rasa kaunar mijina domin bai damu da ni ba, yanzu ka duba dai yau rabonsa da gida ya fi wata biyar kuma koda yana gida ma bashi da wani cikakken lokacina harkokinsa kawai ya sa a gaba yana zama ne dai kawai a matsayinsa na fitaccen mai kudi wanda ke mallakar kyakkyawar mace..." Ta share hawaye. "Ban san darajar so ba Hilal sai da na hadu da kai na gane cewa ashe so da kulawa sun fi komai rayuwar ya mace. Hilal ni dabara ta ko kuma in ce maganin matsalar mu da nake tunani bai wuce kawai idan maigidana yazo ba in yi masa bayanin na gaji dashi ya fadi duk abin da ya kashe na biya shi tun da dai nima iyayena ba talakawa bane ?" "Me ki ke nufi ?" Hilal ya tambaya cikin kaduwa. "Abin da nake nufi shi ne zan nemi ya sakeni da sharadin zan biya shi duk abin da ya kashe lokacin aurena ko kuma in auro masa wata matar domin ni Hilal kai nake so kai nake bege da kauna bana jin kuma zan iya zama da wani da namiji a doron kasa idan ba kai ba." "Kan ki daya kuwa Zainab ?" Hilal ya tambaya a rude. "Tabbas kaina daya Hilal in kuwa baka yarda ba to bari in tambayeka. Shin ka taba ganin mutum da kai biyu ?"**** Masoyan biyu masu makauniyar soyayya suka yi shiru na tsawon lokaci suna duban juna, sannan sai Hilal ya nisa gami da ajiyar zuciya ya ce. "Kina ganin yanzu za ki iya rabuwa da duk daular dake gidan nan domin kawai ki zauna dani?" Hajiya Zainab ta tabe baki ta dubeshi da fararen idanuwanta. "Hilal ka fi komai a gareni, ka tuna fa ni na ce ma zan iya bada raina ma saboda kai, to ina kuma ga dukiya kazantar duniya kai bari ma ka gani mu kulla alkawari." Kafin Hilal ya farga tuni Hajiya Zainab tayi caraf ta rike hannunsa ta zare wani kyakkyawan zobe na lu'u-lu'u dake dauke idanu ta sanya masa a hannu. Ta dubeshi ta yi murmushi. "A wajen mahaifiyata na yi gadonsu, ka ga dayan can a hannun Zuhuriyya." Ta nuna Zuhuriyya da dan yatsa. "Ka rike shi da kyau, domin zabon alkawari ne, dan mahaifiyata da za ta bani shi sai da ta ce dani mahaifina ne ya bata shi a zamanin soyayyarsu, ta ce dani kuma kada na bada shi ga kowa sai wanda na ji ina kauna fiye da komai a duniya." Hajiya Zainab ta yi murmushi sannan ta dada da cewa. "Hilal kaine ka cancanci abin da mahaifiyata ta ce shi yasa na baka shi." A daidai lokacin ne to ta kyalla ido ta hango zoben da shima yake sanye dashi, to sai dai kuma nasa na azurfa ne.**** "Kaima bani naka zoben." Zainab ta tambaya. Hilal ya gama rudewa da irin wannan so da wannan matar aure ke yi masa, ya yi kokarin ya cire zoben nasa amma abin yaci tura, zoben ya rike dan yatsansa gam-gam. "A'a bari kada ka ji rauni, tashi na nuna maka (toilet) ka shiga ciki akwai SABULU idan ka shafa nan da nan zoben zai fita." "Kwarai...kuwa" Hilal ya ce muryarsa na rawa, ya bita a baya ta kai shi har can kuryar ginin gidan inda bandakin yake ta ce dashi cikin murmushi. "Idan ka cire sai ka sameni a falo, nima so nake ka sa min kamar yadda na sa maka nawa zoben." A daidai lokacin da ta dawo dakin shakatwar ne to ta ga abin da ya sa hantar cikinta kadawa. A zaune a cikin daya daga cikin kujerun alfarmar da ke falon, yana kifkifta idanu kamar dillalin rakuma DAKTA SADI NE. "Zai...nab" ya ce bakinsa na rawa kamar wanda ke shirin hawa bori.**** Bakin cikin sake ganinsa ya shake Hajiya Zainab kamar ta fashe. "Shin ban ce da kai ka rabu dani bane!" Hajiya Zainab ta ce cikin karaji. "Ba zan iya rabuwa da ke bane Zainab, ban san abin da kika yi min ba Zainab, domin ji nake yi idan na rasa ki rayuwata ta zo karshe kenan." Idan kuwa hakane, to ina tabbatar maka da cewa kai kam an busa kahon tashin alkiyamarka, domin bani kaunarka, ban son ganinka, kai bana fatan ma na sake ganin wanda ma ya ganka tashi kuma ka fice min daga gida tun da ba gidan ubanka bane." Wani abu ya zo ya tokare masa makogoro..... BINDIGAR KWALI--> 9 . Ka fice min daga gida tun da ba gidan ubanka bane." Wani abu ya zo ya tokare masa makogoro. "Dan Allah Zainab ki yafe ni, Wallahi ba zan taba iya daina kaunarki ba...kin ji Zainab don Allah ki yi hakuri, duk zancen kudin nan ma da na ce ki bani ni na fasa bana son ko kwabo ke kawai nake bukata". Hajiya Zainab ta dubi hanyar bandakin a tsorace, bata son Hilal ya tarar da Dakta Sadi a cikin dakin nan. "Na ce da kai ka tashi ka fita wai shin kai wanne irin tsohon maye ne? Ka ga fa wallahi in ba ka fita ba zan sake ruguza maka kwalba aka irin ta ran nan, nan da nan sai Zainab ta dauki kwalbar lemon (Tree Top) ta nufi inda yake zaune yana zubar da hawaye. Ga mamakinta sai ta ga ko gezau bai yi ba. "Zainab, wallahi sai dai ki kasheni, amma ni ban daina sonki, in baki sani ba bari in fada miki tuni na yi babban kuskuren da ban taba yin sa ba saboda ke, tiyatar da na yi jiya a asibitin mijinki na manta da almkusa guda biyu a cikin mutamin ya mutu duk dan saboda wannan ko..." Zainab ta katse shi ta ce. "Wannan matsalarka ce ni babu abin da ya shafeni tashi ka fice na ce da kai." Ta yi shiru tana waigen hanyar da Hilal zai bullo can sai ta ga kamar motsi, nan da nan sai ta daga kwalbar lemon (Tree Top) din dake hannunta ta ce da Dakta Sadi cikin karaji. "Fice maye!" Dakta Sadi ya gane abin da take gudu, ya kuma gane cewa ba ita kadai ba ce a cikin gidan. Kishi da bakin ciki mai tsananin gaske suka tokare kirjin Dakta Sadi, hankalinsa ya fugunzuma ransa ya baci, idanunsa suka yi jajur da su kamar danjar mota. Da kyar yake numfashi kamar kumurcin maciji. Bai yi aune ba sai ya ji Zainab ta ruguza masa kwalbar a tsakiyar ka, kwalbar ta tarwatse, jini ya yi tsartuwa daga kan Dakta Sadi.********** ************** "Fice na ce, ko na kara maka." Zainab ta ce cikin karaji sauran tsinin kwalbar rike ahannunta. Dakta Sadi ya mike cikin fushi tuni jini ya gama wanke fuskarsa. "Daga yau...ba zaki sake dukan wani ba, shegiya karuwar gida." Dakta Sadi ya ce cikin fushi, nan da nan ya nufi Hajiya Zainab da gudu. Tun kafin ya karaso Zainab ta kwalla ihu cikin firgita, domin ganin kwayar idanunsa ma kawai sun isa su nuna mata cewa kwanakinta sun zo karshe a duniya. Dakta Sadi ya kama hannunta mai dauke da tsinin kwalbar ba tausayi ba imani sai kawai ya burma tsinin kwalbar a ruwan cikinta, Zainab ta fadi, gami da kara mai tsanani, daga nan kuma bata sake ko da shurawa ba, abu na karshe da ya darsu a zuciyarta shi ne tunanin masoyinta Hilal. Hilal ya rugo da gudu daga bandakin cikin firgici, yana zuwa sai suka yi ido biyu da Dakta Sadi cikin jini, sannan ya dubi Zainab kwance itama cikin jini. "Zainab...ah wayo Zainab!" Hilal ya fashe da kuka cikin razana sannan ya durkusa yana jujjuyata. A haka Dakta Sadi ya zurare abin sa ya bar gidan. Hilal ya mike tsaye yana kuka hannuwansa akan kirjin Zainab. Tabbas ta mutu ko shakka babu, yanzu kam ta tabbata zamansa a kano ya zo karshe, shi da kano kam sai abinda hali ya yi, ya mike tsaye yana kuka ya nufo kan kujera inda Zuhuriyya ke kwance tana barci abinta. Hilal ya shafi fuskarta, sannan yacire zoben da a da ya yi niyyar ya sawa uwarta sai ya kama hannun ZUHURIYYA ya sa mata zoben. Tun hawaye na zuba a idanunsa har hawayen ya kafe. A daidai lokacin ne to ya ji kamar sautin jiniyar yansanda ta nufo gidan. Nan da nan ya dawo cikin hayyacinsa, domin ya san idan aka sameshi agidan ko shakka ba ya yi ya gama yawo, domin babu wanda zai yarda ba shi ya kashe Zainab ba. Hilal ya durkusa a gaban Zainab ya yi mata duban karshe sannan ya ce. "Allah ya gafarta miki Zainab ba zan manta dake ba har iya rayuwata" ya mike tsaye ya sake komawa in da Zuhuriyya take barci ya dauki bindigar robarta ya jefa a aljihu, sannan sai ya shafi fuskarta. "Sai wata rana Zuhuriyya Zainab...Zainb sai wata rana" ya fice daga dakin cikin sauri, ko da ya kai kofar gidan sai ya ji sautin jiniyar ya fara matsowa kusa da kofar gidan . Nan da nan ya kara sauri ya fice daga gidan yana mai godiya ga Allah da ya sa Hajiya Zainab ta kori duk masu gadi da hadiman gidan ko da ya hau kan titi ya fara tafiya sai ya ga bakaken motoci fijo-fijo guda uku da marsandi daya sun tsaya a kofar gidan. Hilal ya kara sauri har yanzu hawaye bai daina zuba akan fuskarsa ba. Ko da ya fara nisa da gidan sai ya taba bindigar robar dake aljihunsa da danyatsa. KARSHEN LITTAFI NA DAYA 1 LITTAFI NA BIYU 2 A zaune yake yana ta mafarki da wata kyakkyawar budurwa wai tana tsaye a gabansa tana yi masa murmushi wani kyakkyawan kofin azurfa a hannunta tana kokarin sa masa kofin a baki. "Ba zan sha ba" ya ce da ita a cikin mafarkin "Saboda me?" Budurwar ta tambayeshi cikin tsananin mamaki "Saboda ban sanki ba ban kuma taba ganin ki ba." Budurwar ta zabura a firgice har kofin dake hannunta ya girgiza wani abu kamar nono ya fantsala daga cikin kofin. "Lallai ka bani mamaki wallahi ban taba tsammanin za ka manta da ni ba ashe yanzu har akwai wani zamani da zai zo masoyi ya manta da masoyiya?" Tana gama fadin haka sai budurwar ta taba shi a kafada ta ce "Shi kenan tunda ka ce baka sanni ba." Budurwar ta juya a hankali ranta a bace ta bar shi anan tsaye A daidai lokacin da ya bude baki zai yi kiranta ne ya ji an girgiza kafadarsa a tausashe Hilal ya farka daga nannauyan barcin a rude sannan ya dubi fasinjojin dake cikin jirgin yana kokarin hangen kyakkyawar budurwar a cikin fasinjojin "Ya kamata ka sassauta bel din ka dan mun riga mun zo." Kakkauran mutumin mai sanye da shudiyar kwat ya ce dashi tuni har ya cire nasa bel din. Hilal ya yi doguwar mika akan kujerar jirgin gami da hamma sannan ya dubu mutumin da tattausan murmushi ya ce. "Wallahi wani nannauyan barci ne ya daukeni har da mafarki." "Ina fatan dai mafarkin naka na alheri ne?" Mutumin ya tambayeshi. Hilal ya yi shiru yana gajeran tunani domin shi kansa bai san ma'anar mafarkin da yayi ba. "Eh, to na alkairi ne mana tun da dai na yi ido biyu da wata kyakkyawar fuska tana yi min murmushi." Mutumin ya fashe da dariya, sannan ya kama hannun Hilal ya ce. "Zo mu tafi an fara fita." Hilal ya ji gabansa ya fadi sa'ar da ya fara gangarowa daga matattakalar jirgin, idanunsa na ta shawagi a farfajiyar filin saukar jirgin saman. Abu biyu ne suka cafki zuciyarsa a lokacin bakin ciki da kuma doki. Hilal yana doki ne domin rabonsa da kano yau shekaru ashirin da daya kenan. Tun daga ganin tsarin filin saukar jirgin saman jikinsa ya bashi cewa ko kusa ko alama wannan bata yi kama da kanon da ya sani a da can ba. Ya yi mamakin yadda zai ga garin kano a halin yanzu. Sannu a hankali har suka kawo izuwa farfajiyar filin saukar jirgin saman sannan suka bi ta cikin dakin tarbar baki suka fice izuwa farfajiyar bayan gine-ginen filin. Har yanzu Hilal tafiya yake yana ta kalle-kalle kamar sauna to sai dai shi kallonsa ba na kauyanci bane kallo ne na ya dade rabonsa da KANON DABO.********** ************* Hilal ya ci gaba da tafiya janye da wasu tika-tikan akwatuna guda biyu yayin da wani jibgegen saurayi ke biye dashi janye da wasu akwatuna shudaye guda biyu. A daidai lokacin da suka kawo dab da inda jerin gwanon motocin hayar dake filin saukar jirgin saman ne Hilal ya hangi wasu matasan ma'aurata guda biyu, suna tafe da yar karamar yarinyarsu a rike a hannun mijin cikin fara'a da farin ciki. "Lah! Baba dubi jirgi kamar zai fado." yarinyar ta ce cikin karaji. Uwar ta fashe da dariya sannan ta ce da yarinyar "Da Allah rufe bakinki shashasha yar kauye". "A'a rabu da ita ta kalli abinta, kema ba yar kauyan bace, wa ya san ma abin da za ki yi da ke ce ita." uban ne ya ce da uwar cikin murmushi sannan sai ya dada janyo yarinyar kusa da shi ya ce. "Zo mu bi ta can na saya miki jirgin roba." Hilal ya lura da duk abin da ke faruwa, hakan shi ya sa zuciyarsa kuna sannan wani irin kadaici da bai taba jin irinsa a duniya ba ya lullubeshi. A yanzu kam ya san duk fadin kano in ka dauke mahaifansa bashi da kowa sai mutum daya, mutum daya din da shi kansa a yanzu bai san halin da take ciki ba. Ganin wannan yarinya shi ya tuna masa da ita, domin a lokacin da ya bar ta ba tafi wannan yarinyar ba. Hilal ya share gumi, a daidai lokacin da aka fara sa akwatinansa a bayan motar. "Na gode fa." Hilal ya ce da jibgegen saurayin da ya rako shi da jakankunansa guda biyu, kana ya lalubi aljihunsa ya tsamo wasu adadi na takardun masu gidan rana ya mika masa. Saurayin ya karbi kudin cikin sauri har da dan rankwafawa. "Kudi masu sa kato ladabi." Hilal ya ce cikin zuciyarsa, sannan sai ya bude bayan motar ya shiga, direban ya tuka motar suka nufi cikin birnin kano. Koda suka fara tafiya sai Hilal ya sauke gilashin motar domin ya sami damar ganin irin sauyin da aka samu a birnin kano BAYAN TAFIYARSA BABU SHIRI BINDIGAR KWALI--> 10 . Koda suka fara tafiya sai

Chapter 3 of 7