Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 7
guntun tikiti bai kare ba da ma ba za ka same mu ba." Ikko. Hilal ya maimaita sunan a zuciyarsa. Sannan cikin sauri sai ya nufi inda ake sayar da tikitin motar. Karfe bakwai da rabi suka bar tashar. Kusan sa'arsu guda suna tafiya babu wanda ya ce da wani kala tsakanin dan duniyar da Hilal. "Hala wannan shi ne zuwanka Ikko na farko?" Dan duniyar ya ce da Hilal a karo na farko tun sa'ar da motar ta fara tafiya. A zuciyarsa yana mai mamakin abin da zai kai wannan kyakkyawan saurayi Ikko babu ko jaka a hannunsa. "Uhm...shi ne zuwana na farko." Hilal ya ce da shi muryarsa na rawa. Dan duniyar ya gyada kai xikin fahimta. Tuntuni, tun sa'ar da saurayin ya zo gare shi da tambaya ya san yaron na cikin bala'i. To amma kwarewa da gogewar yawon duniya su suka sa shi yin gum da bakinsa a zuciyarsa yana cewa. Me yiyuwa sata ya yi. ko kuma wani babban abin kunyar. Hilal ya jingina kansa a majiginin motar bai yi mamaki ba sa'ar da ya ji duk lakar jikinsa ta mutu gajiya ta lullube shi ba a dade ba sai ya ji idanunsa sun fara rufewa sannan sai sarkin barayi ya lallabo ya sace shi (Barci) Bai san iya adadin sa'ar da ya kwashe yana barci ba sai kawai yaji kamar ana girgiza shi. Cikin sauri ya bude idanunsa a firgice a tunaninsa abokin tafiyarsa ne me dogon sanko yake girgiza shi. Bude idanunsa ke da wuya sai ya ji mutane sun fara kururuwa motar sai tangal-tangal take yi ba a dade ba sai yaji karar fashewar wani abu tus!! Iya abin da yaji kenan sakamakon jifan da aka yi da shi kansa ya daki wani abu me kamar dutse sannan wasu bakaken taurari marasa adadi suka lullube Idanunsa.****** **** "Lah! Alhaji ka ga ya fara bude Idanunsa...yana motsi!" Da farko Hilal bai fahimci abin da muryar take cewa ba sai daga baya sannan ya fara fahimtar kalaman. To sai dai kuma sama- sama ya ke jiyo murya kamar me maganar a can nesa yake da shi. Sannu a hankali Hilal ya bude idanu, sannan ya fara kokarin fahimtar dashi-dashin surorin dake tsaye akansa. Ba a dade ba idanunsa suka samu saiti sannan ne ya dara idanu biyu da su. Wani dattijo ne da wata Hajiya tsaye a kansa. Dattikon fari ne dogo mai dogon gemu fari me yiyuwa zai kai kimanin shekara sittin babu kadan. Matar dake kusa dashi ita ma doguwa ce amma ba ta kai mutumin fari ba to sai dai kuma mutumin ya dan girme mata zai yi wahala ko iya fadin shekarunta me yiyuwa arba'in da biyar in har za a yi la'akari da busassun idanunta me yiyuwa kuma talatin da wajen takwas idan aka yi la'akari da cikakkiyar fuskar da ke dauke da tsohon alkawarin annurin kuruciya. A lokacin Hilal ya tsammaci yar mutumin ce ko kuma kanwarsa. Sai bayan mako guda da sallamarsa daga asibitin ne ya fahimci ashe wai matar mutumin ne. Kwanansa ashirin da uku a asibitin yana jinyar yankan dake kirjinsa da kuma dan raunin dake tsakiyar kansa. Hilal ya lura da cewa a kullum kwanan duniya sai sun zo duba shi su ke biyan kudin jinyarsa su kuma ke kawo masa kayan lashe-lashe. A ranar da aka sallame shi su suka zo da mota marsandi shudiya mai dauke da karfen lambar APAPA tare da direba yana tukasu suka dauke shi zuwa wata unguwa wacce daga baya Hilal ya fahimci cewa ashe a cikin garin Ikko take. Duk abin da ake yi Hilal bai taba tambayar wani labari a game da dawainiyarsu ba to saidai ya kan gaishe su kuma ya kance da su. "Na gode Allah saka da alheri." Dan haka a ranar da aka sallameshi bayan sun isa gidan sai suka shiga da shi cikin wani falo to amma tun daga farfajiyar gidan Hilal ya lura da tarin samari kusan ashirin duk majiya karfi wadansu na wankin sutura wasu mota wasu na baiwa shuke-shuke ruwa wasu kuwa na gefe suna kada karta abin su. "Ina fatan ka san a inda kake a yanzu?" Dattijon ya tamabayi Hilal bayan sun zauna a dakin shakatawar. Hilal ya girgiza kai. Ban sani ba, a ina na ke?" Mutumin ya dubeshi da tattausan murmushi ya ce. "Ederaba ne...ina datan ka san abin da ya sameka a hanya? Hilal ya dubeshi cikin shakka. "Ina tsammanin hadari na yi." Mutumin ya sake dubansa da murmushi ya ce. "Gaskiya ne me yiyuwa za ka so ka ji yadda aka yi muka same ka? Hilal ya gyada kai. Sannan ne to mutumin ya dubi matarsa da ke gefe ya ce. "Mun je ziyarar wani dan uwa ne a asibitin, muka iske an kawo ka tare da gawawwaki." "Gawawwaki!" Hilal ya maimaita kalmar cikin kaduwa Mutumin ya gyada kai "Kwarai kuwa gawawwaki, domin kai kadai ne a motar ka tsira da rai, mun sameka a kwance duk an zubar da ku a farfakiyar asibitin tare da gawawwaki, shi ne matata da ta ga kana da rai ta tausaya ma ta nemi na taimaka maka." "Kai ne wa?" Hilal ya ce a zuciyarsa, amma bai fadi hakan a fili ba. "Na gode Alhaji..." "Kada ka gode min." Mutumin ya ce yana duban matarsa da murmushi. "Ka gode mata, domin ita ta sa na dauki nauyin komai naka, duk abin da take so shi zan yi." Aka yi shiru a dakin na dan lokaci sannan sai mutumin ya dubi Hilal ya ce. "Daga wacce jiha kake, kuma ina za ka?" Hilal ya ji gabansa ya fadi, ya bude baki zai yi magana, bayanin ya ki fitowa. Nan da nan sai mutumin ya daga hannu ya ce. "Shi kenan...shi kenan ya isa ba sai ka ce komai ba, barka da zuwa Ikko, muna da irinka da yawa anan, wadanda ba sa son a san daga inda suke....duk wadannan samarin da ka gani a farfajiyar gidan nan irinka ne." Mutumin ya dan yi shiru. A karo na farko sai matar ta dubi Hilal ta ce. "Yanzu me kake son yi a garin nan?" Hilal ya dubi matar cikin girmamawa ya ce. "Duk sana'ar da...na samu... In kuma na sami dama nan gaba zan so ci gaba da karatu." Matar ta dubeshi cikin mamaki ta ce "Ka taba yin makaranta daman?" Hilal ya tuna da jarrabawarsa ta karshe da ya bari a gida ko sakamako bai zo ba. "Na taba yi amma ina shekarata ta karshe a sakandare na bari." Matar ta girgiza kai cikin tausayawa, sannan sai ta dubi mijinta ta ce "Alhaji...ina ganin wannan dan bangarena ne a sashi a makaranta." "An gama...gimbiyat a." mutumin ya ce. To sai dai kuma Hilal ya lura da alamun fuskar mutumin bai ji dadin abin da matar ta ce ba. "Oh..wacce irin rayuwa kuma na jefa kaina? Hilal ya tambayi kansa *** Tun daga wannan lokacin Hilal ya fara karatu. Da farko ya karasa sakandare, ya wuce jami'a inda ya yi shekaru bakwai yana karatun koyon aikin likita, a shekarasa ta karshe ne ya yi gamo da tsautsayi aka kore shi a dalilin wata yarinyar bayarbiya da aka kama shi yana bata satar amsa. Yan ajinsu da duk wani mai kaunar Hilal ya yi bakin ciki da wannan kora da aka yi masa a jami'a, amma duk wani mai jin haushi a bayan Hajiya Uwar dakin Hilal yake. "Ka yi hakuri Hilal, Haka nan rayuwa ta ke kada ka damu ai faduwar da namiji ba ita ba ce karshen rayuwarsa. Bayan wannan kalami nata sai da Hilal ya shafe sama da shekara hudu yana zaman banza. Ba shi da aikin komai sai dai ya yi wanka ya ci abinci. Idan bokon ya motsa sai ya dauki tuma-tuman littattafansa na karatun likita ya yi ta karantawa cikin bakin ciki. Wata sa'ar kuwa idan ya tuno da mahaifansa musamman ma mahaifiyarsa sai ya shige wani lungu a cikin katon gidan ya yi ta kuka duk kuwa da cewa a lokacin shekarunsa kusan sha daya kenan da barin gida. A cikin wannan shekaru Hilal ya fuskanci abubuwan girgiza zuciya da yawa a gidan da ya sauka. Hilal ya gane cewa a she dai dattijon mutumin nan mai tarin farin gemu turun barayi ne. Al'adarsa ita ce duk saurayin da ya ga ya isa Ikko ba shi da gata, ba kuma ya son a san daga inda yake, sai mutumin ya dauki nauyin mutum na ci da sha da sutura da zarar ya fahimci ka sakankance ya kuma lura da cewa kai ma lalatacce ne, sai ya rude ka ya sa ka a hanya. Dan haka sama da karti majiya karfi talatin ne a gidan, kuma duk karnukan farautar mutumin ne na harkar fataucin dare Akwai sa'ar da Hilal yana kwance cikin dare zai tashi ya ji ana ta shigowa da buhuna dauke da wasu abubuwa da bai san ko mene ba Tun Hilal na kawar dakai har dai ran nan ya gaji ya tambayi uwar dakinsa abin da ke faruwa a gidan "ka rufawa kanka asiri ka yi zamanka a yadda kake. Ka iya bakinka ka fita daga harkar abin da ake yi a gidan nan tun da ba a kasa dakai ba" Matar ta ce dashi tana kallonsa akwai alamar gargadi karara a cikin kwayar idanunta "Ina son ka sani Hilal duk fadin gidan nan NI KADAI NAKE SONKA BINDIGAR KWALI--> 14 . ......"Ina son ka sani Hilal duk fadin gidan nan NI KADAI NAKE QAUNAR KA gani daya na yi ma a cikin jini na ji ya kamata in taimaka ma domin ka yi matukar kama da dana daya kwallin kwal da shima ya mutu a hadarin mota Kamar ku daya da shi ganinka shi ya tuna min da shi idan ina kallonka sai in ga kamar shi nake gani saboda haka ina son ka iya takunka a gidan nan domin samin dorewar farin cikinka da kuma farin cikina ina fatan ka fahimce ni? Hilal ya gyada mata kai kamar kadangare a tsorace Tun daga ranar bai kara yi mata zancen abin da ke faruwa a gidan ba Wata sa'ar ko barci yake yi idan ya ji ana shigowa da buhuna gidan sai ya dada runtse idanunsa ko kwakkwaran motsi ba ya yi dan kada ma a ga kamar yana sauraren abin da ake yi A shekararsa ta sha bakwai ne a Ikko Hajiyarsa ta bashi jari tun da dai karatun ya gagara. Hilal ya bude shagon sayar da kayan wutar lantarki a unguwar koyi Sannu a hankali rumfar ta fara habaka har dai tsawon kimanin shekaru uku. Ran nan da daddare sai suka sami labarin cewa wata mummunar gobara ta tashi a rukunonin da shagunan su Hilal suke ta kone shagunan kurmus A ranar Hilal kwana ya yi yana kuka. A karo na farko cikin shekaru ashirin da doriya tun barinsa gida sai Hilal ya yi mafarki da mahaifiyarsa. A washegarin ranar da aka yi gobarar ne to Hajiyarsa ta kira Hilal dakin shakatawarta ta dubeshi ta ce. "Hilal ina son yau dai na san tarihinka shin me ya fito da kai daga garinku?" Hilal ya dubeta a rude domin tambayar ta zo masa a bazata don ya yi tsammanin maganar shagonsa da ya kone za ta yi masa. Hilal ya so ya boye mata to amma mafarkin da ya yi da mahaifiyarsa a daren jiya shi ya raunana niyyar karyarsa. Hilal ya ba ta labarin tun daga farko har karshen dalilin barinsa gida. Tsahon lokaci Hajiya na kallonsa cikin kaduwa da abin da ta ji. Hawaye ya fara sartu akan kamatunta. "Ni daman. da ganinka na san ba mutumin banza bane..amma ka dauki hakkin mahaifiyarka... na san yadda rashin da yake kona zuciyar uwa." Ta fashe da kuka. Bayan wasu yan dakiku ta share hawaye sannan ta dubeshi ta ce. "Ka shirya gobe ka tafi gurin iyayenka ka nemi gafararsu Allah sa suna da rai in kuwa ba gafararsu ka nema ba duk abin da ka taba da wahala ya yi albarka...ka yi kuskure Hilal dan me ya sa za ka bar iyayenka bayan ka tabbata ba kai ka kasheta ba?" Washe gari tun da asuba ta tashi Hilal a asirce sannan ta mika masa wata katuwar jaka kodaddiya ta ce. "Tashi ka tafi neman gafarar iyayenka ko ka yi albarka." Ta dan yi shiru tana duban jakar "Ga kudi nan naira dubu dari biyar ne kawai... Ita ce gudunmawata ta karshe a gareka zan kuma yi maka gargadi daga yau kada ka sake yin abin da zai batawa iyayenka rai in ba so kake ka lalace ba." Hilal ya dubeta cikin hawaye ya ce "Na gode...Hajiya.. .na gode kuma in Allah ya yarda zan koma gida yau din nan...Allah sa dai suna da rai." Sa'ar da suka zo rabuwa sai ta dubeshi ta ce. "Hilal ina son bayan mun rabu ka yi min abu guda biyu..." ya dubeta cikin mamaki, "Me kike so Hajiya?" "Ina son idan ka koma gida ka bincika in dai har yanzu wannan mutumin da ya kashe zainab din da ka bani labari yana da rai ka yi duk abin da za ka yi ka tabbatar wa jami'an tsaro laifinsa domin a hakunta shi." Hilal ya gyada kai ya ce "Na yi miki alkawarin haka daman kuma abin dake raina kenan duk tsawon shekarun nan da shi nake kwana da shi nake tashi." "Sai kuma abu na karshe da nake son ka yi min." Hajiya ta ci gaba da cewa. "Ina son Hilal a duk lokacin da ka sami dama ka yi min addu'ar Allah ya rabani da auren tshohon barawo!"******* *** Mahaifiyar Hilal ta fashe da kuka sa'ar da Hilal ya kawo karshen labarin. "Haba Hilal...haba dan me za ka tafi ka bar ni bayan ka san ba kai ka aikata laifin nan ba." "Ki yi hakuri mama yarinta ce da rudin shaidan...ki yafeni." "Ban taba fushi da kai ba Hilal haka ma mahaifinka har ya mutu yana cewa. Hilal yaron kirki an rabani da shi...idan mutuwa ya yi Allah ya ji kansa idan kuwa yana da rai to Allah ya dawo mana da shi." Ta sake fashewa da kuka. Bayan an sami yan dakiku suka nutsu. A daidai lokacin ne suka lura ashe har rana ta fito sosai. Hilal ya dubi agogon dake hannunsa "Har karfe tara ta yi." A wannan lokacin ne mahaifiyar tasa ta dubeshi da jajayen idanu ta ce. "Zan so ka je har gida ka yiwa yarinyar nan godiya, domin tun da ka bace, mahaifinka ya rasu duk yan uwa suka guje ni, babu me taimaka min sai ita, ka ga ita ta sa aka sake ginin gidan nan da har na fara waina ta sayarwa saboda talauci ita ta hanani duk karshen wata sai ta kawo min kudi da sutura." Hilal ya bude baki yana kallon mahaifiyarsa a rude domin bai san wacce yarinya take nufi ba. "Wai mama...wacce yarinya kike nufi?" kamar amsar tambayarsa, sai suka ji wata siririyar murya ta ce daga kofar daki. "Assalamu Alaikum....mama ke kadai ce a dakin ko kuwa baki kika yi...?" Mahaifiyar Hilal ta dubeshi da murmushi sannan ta dubi kofar dakin ta daga murya cikin farin ciki muryarta kamar za ta yi kuka tace. "Yar halak kin ki ambato...yanzun nan muke zancenki sai ga ki...zo ki taya ni farin ciki yau Allah ya dawo min da dana Hilal....shigo RUKAYYA.******* **** Sa'ar da ta shigo dakin sai ta kasa zama ta zura masa idanu cikin tsananin kaduwa tana kallon fuskar da ba zata bata mantawa ba fuskar da ke yaye mata bakin ciki. Hilal ya kura mata idanu cikin tsananin mamaki, domin kwata- kwata ko a mafarki bai taba ganinta ba ya mance da ita to amma da yake ta dade tana naci akan sai ta sami soyayyarsa bai mance da fuskar ba rabonsa da ita yau shekara ashirin da daya kenan tun a farfajiyar makaranta. "Hilal..." "Na'am....Rukay ya." jin ya kira sunanta, sai dadi ya sa ta fashewa da kuka. "Hilal ashe ba ka manta da ni ba." Ganin haka sai mahaifiyarsa ta mike tsam ta fice daga dakin domin ta riga ta san abin da ke tsakanin tsohuwar soyayyar. A zuciyarta tana cewa Allah ka daidaita tsakaninsu. Ta riga ta san cewa ko kusa ko alama Hilal bai taba damuwa da Rukayya ba. "Zauna Rukayya.." Hilal ya ce da ita. Jikinta na rawa ta zauna a gabansa. Hilal ya kurawa yar karamar budurwar da ya sani a da yanzu ta zama cikakkiyar mace amma idanunta da bakinta mai yawan son murmushi da kuma dogon hancinta su suka tabbatar da tsohuwar kamarta duk kuwa da kibar da ta dan yi. "Rukayya kin girma." "Shekara ashirin ba wasa ba Hilal kaima ai ka girma sosai Hilal dubi fa yadda ka zama...sai ka ce malamin turancinmu malam Kabiru." suka dan fashe da dariya. A karo na farko cikin shekara ashirin da daya sai Hilal ya ji tausayin Rukayya ya kama shi tabbas ya san duk mutumin da zai iya son ka har na tawon shekaru ashirin ba tare da yana ganinka ba wannan ba karamin masoyi bane. "Umma ta fada min duk abinda kike yi mata...Allah saka da alkhairi. "Haba Hilal mahaifiyarka ai mahaifiyata ce." suka sake yin shiru na yan dakiku. "wane ne mijinki yanzu?" Rukayya ta dago kai ta kalleshi ta ce. "Ba ni da miji yanzu...bayan tafiyarka dai aurena biyar amma babu wanda ya dore." "Aure biyar? Hilal ya maimaita cikin kaduwa. "Haba Rukayya dan me za ki yi haka?" Rukayya ta dubeshi ido da ido ta ce. "Saboda na rasa soyayya Hilal...daman kai kadai nake gani na ji dadi duk kuwa da cewa ba wani damuwa kayi da ni ba." Hilal ya sunkuyar da kai domin ba shi da abin cewa. Dan lokaci ya dago kai. "Wannan duk wani abu ne da ya wuce Rukayya." Cewar Hilal. Rukayya ta ji wani irin dadi ya lullube doron zuciyarta, shin kalamin da ya yi yanzu nan na nufin cewa Hilal ya fara kaunarta ne ko kuwa mene ne? "Wai....Hilal ina ka tafi ne duk tsawon shekarun nan? Hilal ya dubeta "Labarin na da tsayin gaske Rukayya amma nan gaba idan lokacin da ya dace ki sani yazo zan fada miki'. Rukayya ta dubeshi zuciyarta na harbawa shin ko har yanzu baya kaunata ne? Ta tambayi kanta sannan sai ta ce da sauri. "Wane lokaci ne ya dace ka fada min?" Hilal ya dan saurara kadan. Ya lura tun shigowarta dakin ya hade da wani daddadan kamshi. Haka nan Hilal ya lura da cewa hankalin Rukayya a kwance yake ko da can ma zamanin da suke makaranta Hilal ya riga ya san cewa Iyayen Rukayya masu hannu da shuni ne to amma bai dauka bayan duk tsayin shekarun nan zai sami Rukayya da sauran kuruciya ba. Hilal ya yi mamaki domin a fuska Rukayya ba tafi yar shekara ashirin da tara ba duk kuwa da cewa a yanzu haka ta doshi talatin da hudu. "Lokacin da zamu zama daya Rukayya." Hilal ya ce, a zuciyarsa yana cewa. Ita ce daidai dani sannan sai ya fara tunanin yawan shekarunsa a duniya. A yanzu kam yana da kusan shekaru talatin da tara a duniya. Rukayya ta dubeshi cikin farin ciki da faffadan murmushi sannan ta ce "Yaushe ne zamu zama dayan?" "Nan da dan lokaci kankane....akwa i wani abu da nake shirin karasawa!" Hilal yace da ita yana kallon kilishin tsakar dakin lokaci guda kuma ya fara tambayar kansa. "SHIN....... ??? . ****kash masu karatu wayata babu chaji ku jira nepa su kawo wuta**** BINDIGAR KWALI--> 15 . "Yaushe ne zamu zama dayan?" "Nan da dan lokaci kankani....akwai wani abu da nake shirin karasawa!" Hilal yace da ita yana kallon kilishin tsakar dakin lokaci guda kuma ya fara tambayar kansa. "SHIN.... a ina zan sami mutumin nan da ya kashe Zainab?" Sai da suka kwashe sa'o'i uku suna hira daga karshe Rukayya ta yiwa mahaifiyarsa sallama. Hilal ya rako ta kofar gida. Suna fitowa sai Hilal ya rike numfashi cikin kaduwa. Dankareriyar motar baka wuluk tana sheki a cikin rana ita ta fara gaishe da idanunsa. Abin da ya sa Hilal rike numfashi shi ne motar da Rukayya ta zo da ita irinsu daya da motar maigidansa dan tsohon nan turun barayi na Ikko. "Tana da kyau?" Rukayya ta tambayeshi da murmushi sa'ar da ta ga ya kurawa motar idanu. Hilal ya yi sauri ya dauke idanunsa daga kan motar gami da ajiyar zuciya, ya ce "kai kyawun ma ai ya isa." kadan ya rage ya ce mata irinta ubangidana yake hawa a ikko. Sai kuma ya tuna da cewa lokaci bai yi ba da ya kamata ta san komai a game da tafiyarsa Ikko Domin labarin da saura bai kare ba tun da dai har yanzu bai san matsayin da mutumin nan da ya kashe Zainab ya ke ciki ba. "Irin wannan motocin guda uku na ke da su." Rukayya ta ci gaba da cewa. "Kana son irinta ne?" Hilal ya tabbata da wasa take don haka sai ya girgiza kai cikin sauri ya ce. "Haba Rukayya ina ni ina hawa motar manya. Wannan ai ta yayan sarakuna ce da masu abin duniya irinku." Rukayya ta fashe da wata zazzakar dariya. "Ka ga Hilal daina tsokanata...kai ma ya dace ace ai kana hawan wannan." Ta dan yi shiru "Bari na koma gida zan turo direban mu ya kawo maka ita har ma da takardunta na baka ita." Hilal ya fashe da dariya ya ce "Ke kuwa Rukayya wallahi ba kya rabuwa da tsokana kyautar irin wannan mota sai ka ce wata riga." Sannan ne to ya ga Rukayya ta hade fuska kana ta matso daf da shi ta dubi kwayar idanunsa ta ce a tausashe. "Na fi karfin dari na irin wannan karamar motar Allah ya hore min duk abin da nake bukata na duniya abu daya na rasa a duniya shi ne soyayya...kai ne abin so na Hilal Allah ya dawo min da kai bayan tsayin shekaru masu yawa, a yanzu haka ni na rasa ma abin da zan yi maka." Ta sunkuyar da kai na yan dakiku. "Idan kana ganin kyautar da nayi maka da wasa nake ka tsaya anan, nan da minti ashirin za a dawo maka da motar nan domin ka fita a gurina." Tana gama kalaminta sai ta juya da murmushi ta shige motar alfarmar ta rufe sannan ta leko kai ta cikin tagar motar ta ce. "To sai na dawo...in an jima da yamma." Da haka ta tuka motarta ta fice daga layin. Yara dake wasa a gefen kwatocin dake layin suka bi motar da kallo. Daya daga cikin kananan yaran ya dauki bawon gyada ya jefi motar a daidai lokacin da ta wuce su. Sauran yaran suka dauki sowa "Lah...Habu ya sameta wallahi." Hilal bai lura da su ba sai ya juya zuwa cikin gidan a zuciyarsa yana cewa. "Oh, wannan mata da kuri ta ke wanene ya isa ya yi kyautar irin wannan mota a wannan zamani da talauci ya yawaita?" ko mintuna talatin Hilal bai yi da shiga gida ba sai wani yaro ya yi sallama. "Wai ana sallama da Hilal a waje." Mahaifiyar Hilal na tsakar gida tana wanke-wanke sa'ar da yaron ya shigo. "Je ka ce yana zuwa." Ta ce da yaron. Sannan sai ta daga murya "Hilal!" Cikin sauri Hilal ya fito daga dakin ya nufo inda take wanke-wanke. "Wai ana sallama da kai a waje." Hilal ya dubeta cikin mamaki. "Ni kuwa wazai yi kirana...bayan kusan duk an manta ni ma." "Je ka gano mana...yanzu haka ma tsofaffin abokanka ne na makaranta suka sami labari kasan fa duk labarin dawowarka ya hada unguwar nan kamar wutar daji." Hilal ya dan yi jim, sannan sai ya nufi kofar gidan. Tun kafin ya karasa fita ya hangi hancin dankareriyar Honda wani dan tsoho motsattse ya fito daga cikin motar cikin sauri sannan ya durkusa a gaban Hilal ya mika masa dan mukulli da wata jakar wasika fara ta roba ya ce. "Yallabai ga wannan Hajiyace tace nakawo ma...wai takardun motar yana ciki." Hannunsa na rawa kamar ana yi masa gangi Hilal ya karbi dan mukullin da jakar da kuma wata yar guntuwar takarda da rubutu a jiki. Hilal ya kara karanta gajeran jawabin kamar haka..... . Na san dazu ka dauka kyautar da na ce zan yi ma ka duk BINDIGAR KWALI ce HARSASHIN RUWA ko? To ba haka bane dan ka raina ne idan kana so kuma ina da iko zan iya ba ka Hilal. Ga motar nan na baka kyauta nasan za ka so ka dan zaga gari domin gaisawa da tsofaffin abokanka...kada ka yi kokarin zuba mata mai domin tankinta a cike yake... Na gode, sai na zo. MATAR KA RUKY.*** . Tun misalin karfe hudu da rabi Rukayya ta dawo gare shi, cikin wata motar kirar marsandi. Sun yi hirar bayan rabuwa. Hilal ya yi kokarin yin godiya sai Rukayya ta bata rai ta ce. "Don Allah Hilal kai ka cika mita Wallahi nawa kyautar take da har za ka yi ta damun kanka?" Bata bar gidan ba sai karfe shida da rabi, tare da alkawarin za ta dawo gobe da safe, domin ta kai shi ya gaishe da mahaifiyarta. Tafiyarta ke da wuya sai Hilal ya shiga wanka bayan ya fito sai ya yi alwala ya nufi masallacin dake can karshen layinsu. Bayan an idar da sallar magriba ne ya dawo dakinsa ya sauya kayan da ke jikinsa, sannan ya zauna ya zubawa bangon dakin idanu yana mai tambayar kansa. Tambayar da ya fara yiwa kan nasa ita ce "Shin...ta ina zan fara neman wannan azzalumin mutum da ya kashe Zainab?" "Ta inda al'amarin ya fara mana." Wata zuciyar ta ce dashi. Wani zazzafan gumi ya karyo masa. Shin ko a wane hali gidansu Hajiya Zainab yake a yanzu, shin ko mijinta Alhaji Hamisu Jumare na nan da rai? Shin ina yar karamar yarinyarta da ya sawa zobe?....me yiyuwa tayi aure, ya baiwa kansa amsa. A daidai wannan lokacin ne to zuciyarsa ta fara kwadaita masa cewa ya koma gidan Hajiya Zainab ya ga irin halin da yake ciki, me yiyuwa idan ya yi dace yana iya samun hanyar da zai bi ya gano inda azzalumin nan yake. Jikinsa na rawa Hilal ya dauki dan makullin motar sannan ya nufi dakin mahaifiyarsa. "Mama za ni unguwa?" "Ina za ka?" ta tambayeshi tana kallonsa a tsorace, domin gani take yi kamar idan ya tafi ba zai dawo ba. "Gidansu abokina Aminu...zan je mu gaisa...Allah sa ma ya ganeni." Hilal ya yi mata karya. Mahaifiyarsa ta yi ajiyar zuciya ta ce cikin murmushi "Me zai hana ya gane ka, ai aboki baya manta aboki duk tsahon zamanin da aka yi ba a hadu ba. A dawo lafiya, kada kuma ka dade." "Ba zan dade ba." Karfe takwas saura kwata daidai Hilal ya bar gida. A hankali yake tuka dankareriyar motar da bai taba mafarkin za a rage masa koda hanya ne a cikinta ba. A zamansa na Ikko ya sha addu'ar ina ma wata rana Hajiyarsa ta aike shi cikin motar Alhaji ko ya taba hawa. Amma maimakon haka kullum in za ta aike shi wata tsohuwar Toyota take bashi. Hilal ya yi mamaki sa'ar da ya ga yana fahimtar hanyoyin da ya dade bai bi su ba. Sannu a hankali yana tafiya, yana lura gami da mamakin irin yadda babura suka cika garin kano, har dai ya kawo kan kwanar gidan marigayiya tsohuwar masoyiyarsa matar wani, Zainab. Hilal ya shiga cikin layin a hankali, kusan cikin sanda ma yake tuka motar. In ba dan doguwar hasumiyar masallacin dake kan kwana ba da har abada Hilal ba zai taba gane titin ba. Kome ya sauya a titin, gidajen duk an sake gininsu, da tsarin rufinsu an maida su kamar tsarin GIDAJEN KASAR SIN.... BINDIGAR KWALI--> 16 . Hanjin cikinsa ya kulle sannan yaji kamar zazzabi zai rufe shi don har yanzu tunani yake yi kamar idan ya koma gidan zai samu su dan Ba'u me tireda a kofar gidan, sannan kuma idan ya shiga cikin gidan zai sami gawar Hajiya Zainab kwance cikin jini yarta a gefe a kwance. Wannan tunanin shi ya sashi jin kamar bashi da lafiya. Kwantar da hankalinka Hilal. Wata Zuciya ta ce dashi. Wannan duk wani abu ne da ya riga ya faru a wani shudadden zamani. Hilal ya ci gaba da tuka motar zuwa cikin layin, idanunsa wuri- wuri kamar na barawon akuya. Yana tafe yana kallon kyawawan gidajen zamanin da suka yi sahu-sahu a gefen layin fitilun lantarki na ci tarwai a kan katangunsu kamar rana. Kusan ko wace kofar gida a rufe take sai dai jifa-jifa ya kan hangi kan masu gadi suna dan lekowa. Hilal ya gama dube-dubensa bai hangi tiredar su Dan Ba'u ba ballantana ma ya gane gidan marigayiya Zainab. Zuciyarsa ta fara shakkar anya kuwa nan ne layin. Tabbas masallacin dake can kan kwana ya nuna hakan domin shi kadai ne bai canza ba hatta gurbin famfon dake daf da masallacin nan alwala yana nan. Sa'ar da Hilal ya tabbata ya isa tsakiyar layin sai ya tsayar da katuwar motar. Sannan ya jingina bayansa sosai a tattausar kujerar mota yana tunanin abin da ya kamata ya yi. Na bata lokaci anan a banza. Ya ce da kansa domin ya tabbata ba zai taba iya gane gidan marigayiya Zainab ba. A daidai wannan lokacin ne kofar wani gida ta bude wani dan siririn yaro, dogo fari dan kimanin shekaru goma ya fito sanye da bakar shat da gajeran wando kore hannunsa na dama dauke da dutsen guga wani dan dukurkushin kare mai yawan gashi na bin sa a baya. Hilal ya sauke gilashin motarsa yana kallon yaron da ya nufo inda yake, a wannan dan takin lokacin

Chapter 5 of 7