Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 7
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BINDIGAR KWALI (c) Nazir Adam Salih . Daga - http://fb.com/hausaebooks Ga wayanda suke son su samu littafan hausa a cikin ebook sai kui sauri ku ziyarci shafin http://hausaebooks.cf BINDIGAR KWALI--> 1 . (c) Nazir Adam Salih . Typing: Yarima Gangariya(Jikan Sidi Mai Jaka) . In ban da dai lamari irin na makaranta musamman ma kuma lokacin jarrabawa to da babu abin da zai sa ni zuwa makaranta yau." Dan kyakkyawan saurayin ne ke fadin haka cikin zuciyarsa, adaidai lokacin da ya kawo bakin titin, bugu da kari kuma yana ta faman kokawa da sassanyar iskar ruwan daminar dake kokarin wafce ledar dake hannunsa, sau biyu kenan akan hanyarsa ta zuwa bakin titin iska tana bankare lemar, shi kuma yana maida ita yadda take. Haka nan kuma lema bata hana shi jikewa ba musamman ma gaban rigar makarantarsa saboda sassanyar iskar dake kadawa. Saurayin dogo ne wankan tarwada kyakkyawa. Da yawa daga cikin yan matan zamani sun sha kamuwa da ciwon son sa kawai daga ganin hotonsa.**** Shi kansa yakan yi mamakin abin da yan matan ke gani a jikinsa da har suke rububinsa haka, tamkar shi ne halittar karshe ta yan samarin duniya. To amma duk sa'ar da ya dubi madubi ya ga dogon hancinsa, da kyakkyawan lebban bakinsa, gami da fararen idanu ma'abota girar baki sidik gazar-gazar, gagara tunku, to sai ka ga ya yiwa kansa murmushi domin tabbas ya san shi kyakkyawa ne to amma kuma wannan ce kawai take sa yan mata kaunarsa ?? Abin da bai sani ba shi ne tattausan murmushinsa ma kawai narkar da zuciyar su yake, ballantana dariyarsa. Tun kusan karfe goma sha biyu na daren litinin din ake ta tafka ruwan, shi ne kuma ya kawo har ya zuwa wannan safiya ta litinin wacce ke da matukar muhimmanci ga dan saurayin.**** Yau ita ce ranar da zai fara jarrabawar sa ta karshe a sakandire, daga nan kuma sai shirin shiga jami'a. Hakan ita tasa ruwan saman da kakkarfar iskar ba su hanashi fitowa ba, domin ya san ko da ya zauna a gida, to wasu daliban zasu je su yi, idan kuwa jarrabawar ta wuce shi, to ta wuce shi kenan har abada, sai dai ko ya sake zama shekara mai zuwa. Ya share ruwan daya fara shigar masa idanu, sannan ya dada kankame lemar da ke hannunsa don gudun kada iska ta sake bankareta. Abin da ya fi tayar masa da hankali shi ne titin babu motoci kamar an share, kuma yan tsirarun motocin ma dake ta murginawa a cikin ruwan saman da ya cika kan kwaltar, a ciccike suke zuwa da jama'a, mafi yawancinsu ma'aikata ne da yan makaranta sai yan tsirarun yan kasuwa ma'abota zafin nema.**** Saurayin ya dubi agogonsa sai ya ga tuni ya kusan makara, domin karfe tara za a jarrabawar gashi yanzu tara saura minti ashirin. Nan da nan sai ya yanke shawara kawai ya bi turba a kasa ya tafi makaranta a kalla dai koda zai makara bai fi ya makara ta minti biyu ba zuwa uku ba. Ya sunkuya ya nade kafafun wandonsa, dan gudun jikewa, domin duk kusan in da zai bi yan kananan fadamu ne na ruwan saman. Ya fara tafiya kenan sai ya hango wata dankareriyar marsandi daga can nesa ta nufo inda yake da gudun gaske. Tayoyin marsandin sai tsaga ruwan suke yana ta faffaflatsa gefe guda, hakan ita ta sa saurayin sauka daga gefen titin tun kafin ta karaso don gudun kada ta bata shi da ruwa. Koda ya koma gefe guda sai ya yi mamakin ganin motar ta rage wuta kuma ta fara gangarowa bangaren daya ke, sannan kuma sai ya ga tana kokarin tsayawa daf dashi. Tun kafin motar ta gama tsayawa ya hangi abin da ya sa zuciyarsa Das ! Das !! Das !!! Kamar zata tsaga kirjinsa ta fito waje. Abin ya dame shi domin tun da yake bai taba ganin wata kyakkyawar halitta da tasa zuciyarsa bugawaba sai a wannan karon. A daidai lokacin ne to iska ta sami nasarar wafce lemar dake hannunsa, ta yi jifa da ita gefe guda kamar fulfulwa.***** Hajiya Zainab Jumare bata ji dadin irin yanayin da aka tashi dashi ba a ranar litinin din saboda dalilai guda biyu. Na farko shi ne babu abin da ta tsana a rayuwarata irin tuki a cikin ruwa musamman ma idan aka ce ruwan saman bai tsagaita ba. Na biyu kuma shi ne hargitsin daya shiga tsakaninta da masoyinta na boye, Dakta Sadi. Hakika ba karamin tashi hankalinta ya yi ba lokacin da sabanin ya faru. Dakta Sadi likita ne a asibitin JUMARE MEMORAL HOSPITAL. . Ku Biyoni Don Jin Cigaban Labarin Wannan Somin Tabi Ne . Salon Rubutun Yayi Kokuwa Yayi Yawa A rage Yawan shi ???? BINDIGAR KWALI--> 2 ...Dakta Sadi likita ne a asibitin JUMARE MEMORAL HOSPITAL. Tun sa'ar da ya gama makaranta ya yi dace aka daukeshi aiki a matsayin likita a asibitin. Yau shekararsa hudu kenan yana aiki a asibitin. Tun da yake bai taba ganin mace da kyawun halitta kamar Zainab ba. Ba kuma kyawunta ne kawai ya rudeshi ba, akwai wani abu daban dake jikinta wanda a kullum yake hana Sadi barci. Da zarar ya rufe idanunsa sai ya ga fuskartatana yi masa murmushi. Dan haka tun sa'ar da ya kyalla idanu ya dora a kanta. To amma a lokacin da aka ce dashi Zainab matar mai asibitin ce, sai duk maitarsa ta narke a cikinsa. Ya fitar da rai, sai dai kuma duk sa'ar da ta kawo ziyara to shi ke kan gaba yana nunnuna mata gurare da ci gaban da aka samu a asibitin. Sannan kuma idanunsa akan ta kamar maye.***** Alhaji Hamisu Jumare shi ne mijin kyakkyawar matar kuma shi ne mai asibitin na jumare Memorila Hospital, ko kusa Alhaji Hamisu bai damu da zama gida Najeriya ba, manya yawan harkokinsa ya fi yinsu a kasashen ketare. Sai ya yi wata shida yana zazzaga kasashen ketare. Sai ya yi wata shida yana zazzaga kasashen duniya kamar wani tauraron dan Adam. Mutum ne da kullum yake cikin aiki babu hutu kamar zuciya. Ya fi damuwa da kudi fiye da komai a rayuwarsa, mutane na kusa dashi kan yi mamakin abin da ke sashi barin wannan zukekiyar mata Zainab ya yi tafiyarsa ba zai koda waiwayeta ba sai bayan wata shida koma fiye da haka. Zainab ta dade da gajiya da irin wannan halayya ta mijinta.**** "Bai kyautu ba abin da kake yi, ka tafi ka bar ni a gida ba ka ko tunanin hakkina a kanka, ka tuna fa so da kauna ce ta sa ka aure ni, amma dubi shekara biyu kawai da auren ka yi fatali da ni kamar ma ni ba matarka ba ce." Ta ce dashi wata rana suna zaune. "kada ki damu zainab, ni mata basu fiye damu na ba, kuma in ban da abin ki ma me ye na damuwa da rashin zamana ?? Ga kudi nan ki yi abinda kika ga dama, ki shakata abin ki, ga kuma asibiti na nan kina kula dashi." ya dafa kafadarta ya ce. "Haba Zainab meye na damun kan ki ma ??" Tun daga ranar Zainab ta daina yi masa zancen. To sai dai kuma shedan ya yi halinsa. Ba ta dade da fara zuwa asibitin ba, sai ta hango Dakta Sadi, nan da nan sha'awa da kaunarsa ta lillibe zuciyarta ta ga babu wanda take sha'awa ya zo kusa da ita in ba Sadi ba. Dan haka sai ta fara gayyatar sa gida ta hanyar sashi ya kawo mata wasu bayanan asibitin marasa dalili zuwa gidanta. Da farko Sadi bai saki jikinsa da ita ba, to amma da ya fahimci abin da take nufi sai ya ga abin da ya kamata kawai shi ne shima ya saki jikinsa ya sha gara.***** Yau kusan wata uku kenan da kulla huldar masha'a tsakaninsa da Hajiya Zainab Jumare, sau da yawa ma a gidan yake kwana yau wata biyar kenan da tafiyar Alhaji Hamisu Jumare, ba shi kuma da ranar dawowa. A daren litinin din ne to suka sami rashin fahimta tsakanin Dakta Sadi da Hajiya Zainab Jumare, saboda wasu kudi da ya nuna mata yana son ya handame. Ba zai yiyu ba, Hajiya Zainab ta ce da shi. Ya ya ma zata yiyu haba Sadi miliyan uku fa!! Kai baka gode Allah ne ka tuna fa duk yan kananan kudin da kake cinyewa a asibitin bana cewa da kai komai, amma duk da haka kuma kake son daukar miliyan uku, kanka ya tabu ne ?? Ta tambayeshi.***** "kaina bai tabu ba, kuma da kike zancen ina cinye kananan kudin asibitin ai wannan kamar biyana kike yi tun da dai ni nake taya ki jin dadin rayuwa a asirce, ba tare da mijinki uban gantali ya sani ba". Hakan shi ya bata mata rai ta fatattake shi, ta ce kuma kada ya sake shigo mata gida, fitarsa ke da wuya sai ta kifa kai ta fara kuka, domin ita ba zata taba iya rayuwa ba sai da da namiji, to gashi kuma mijinta bai damu da ita ba, idan ta nemi ya saketa kuma ta tonawa kanta asiri, domin babu sauran jin dadi in ta rabu dashi, ba kudin kashewa, ba kuma za a sake girmamata ba tun da daman duk girman da mutane suke bata na kudin ne. Dole ne na sami wani sabon masoyin da zai ke biya min bukatuna a asirce ta ce da kanta.***** Wannan ita tasa safiyar litinin din ta zo mata cikin mawuyacin halin tunani. Kamar dai kuma dan kyakkyawan saurayin, itama in ba dan tana son kai yar karamar yarta Zuhuriyya makaranta ba, to da babu abin da zai sa ta fito cikin wannan ruwan. A daidai lokacin da take tukin motar ne, to tana tunanin abin da ya faru a daren jiya tsakaninta da Sadi, ta hango dan kyakkyawan saurayin a gefen titi yana tafiya cikin ruwan. Ga dukkan alamu kuma makaranta zai tafi, wani abu ya yi yar! Kamar tafiyar kyankyaso a cikin jijiyoyin jikinta. Kai wannan yaro da kyau yake ta ce a zuciyarta. A daidai lokacin ne ta Hango.......... ME HAJIYA ZAINAB TA HANGO KUMA ??? BINDIGAR KWALI--> 3 . Kai wannan yaro da kyau yake ta ce a zuciyarta. A daidai lokacin ne ta ga iska ta wafce lemar sa ta yi jifa da ita. Nan da nan ta taka birki a gabansa ta sauke gilashi ta ce. "Makaranta za ka ne ??" Dan kyakkyawan saurayin ya dubi kyakkyawar matar kirjinsa na harbawa kamar dakikar agogo, sannan kuma ya dubi yar karamar yarinya dake bayan motar bata fi shekara uku ba, tana wasa da dan karamin mutum-mutumin karen roba gashi kamar na gaske. Sannan kuma a gefenta bindigar roba ce akan kujerar motar. "Makaranta za ni". Hajiya Zainab ta yi murmushi sannan ta kashe idonta na hagu ta ce. "Wace makaranta kake zuwa saurayin ya dubeta cikin mamaki, sannan ya ce. "JUMARE PRIVATE SCHOOL"**** Zainab ta dubeshi cikin mamaki tana murmushi. "JUMARE ?? Amma kuma ban taba ganinka ba, ai kusan kullum sai na kai yarinya ta makarantar" Ta dubi zuhuriyya dake zaune a bayan motar. "Shigo to mu tafi na rage ma hanya" Saurayin ya bude motar ya shiga sannan ya ce. "Ai ba dole bane ki ganni, tun da ke bangaren (Nursery School) din kike zuwa" Hajiya zainab ta dubi saurayin ta kyalkyale da wata irin daddadar dariya mai kamar busar sarewa a kunnen saurayin ta ce. "Ai makarantar miji na ce, ni ce Hajiya Zainab Jumare ba ka taba jin sunana bane ?? Ta sake murmushi. Saurayin ya dubeta cikin mamaki da kaduwa ya ce bakinsa na rawa. "Daman ke ce ?? Na sha jin sunan ki amma ban taba ganinki ido da ido ba, mijinki dai na taba gani" Hajiya zainab ta dubeshi cikin sha'awa. Ba ta taba ganin kyakkyawa kamarsa ba, shin ko wannan yaro zai iya zamowa canjin SADI ? Ta tambayi kanta.***** "Wannan yar ki ce ?" Zainab ta yi murmushi har hakoranta suka fito, sannan ta karawa motar gudu ta ce. "Oh! Zuhuriyya, ya ta ce". A daidai lokacin ne to Zuhuriyya ta turo mutum- mutumin karen robar ta tsakanin kujerar motar ta ce da saurayin. Kana son wannan?" saurayin ya yi mata dariya, sannan kuma ya yi mamakin irin kamar da suka yi da mahaifiyarta, kamar an tsaga kara. "Ashe tana magana". Ya ce da Zainab. "Lah!! Wace, ai surutu ne da ita". Zainab ta ce tana murmushi. Zuhuriyya ta zuro bindigar robar ta zunguri kunnen saurayin ta ce. "Wa na kama?" Zainab da saurayin suka fashe da dariya gaba daya. "Na tuba zuhuriyya kada ki harbeni". Saurayin ya ce yana satar kallon fuskar zainab, Zuhuriyya ta fashe da dariya ta ce. "Kai ba ta gaske ba ce, BINDIGAR KWALI ce!" Zainab ta fashe da dariya kamar zata saki sitiyarin motar. "Shashashar banza, bindigar roba za ki ce ba ta Kwali ba."**** Dan saurayin ya fito daga cikin motar ya dubi agogon dake hannunsa, tara saura minti goma, tuni har dalibai sun fara shigewa tangamemen ajin da aka tanada don zaman jarrabawar. Ya dawo da hankalinsa gurin Hajiya Zainab wacce ke ta faman kallonsa kamar zata hadiye shi. "Sha daya da rabi". Ya amsa yana dubanta. "Ban san kuma sunanka ba". Ya dubeta da lallausan murmushi ya dauke kansa kadan ya ce. "Sunana Hilal... Hilal Aliyu". Ta yi murmushi ta ce. "Hilal sunan larabawa ne". Suka yi dariya gaba daya, sannan sai zainab ta miko masa Naira ashirin-ashirin sababbi fil. Hilal ya dubeta cikin mamaki yace. "Hajiya wannan na mene ne?" Ta yi murmushi. "karbi mana, ai ba ka na yi, kyauta ce, kada ka maida hannunta baya." Halil ya karba. "Na gode. Ni zan tafi na ga an fara shiga aji".**** Zainab ta dubeshi ido da ido ta ce. "To Hilal Allah ba da sa'a." Ta dan yi shiru tana dubansa, sannan sai ta ce. "In ba ka damu ba, ina gayyatarka" Birthday Party" bikin haihuwar Zuhuriyya ranar Asabar din nan mai zuwa." Hilal ya yi murmushi. "Ba damuwa Hajiya." ya dubi zuhuriyya. "Shekara nawa za ta cika" "Shekaru Hudu kenan a duniya, Ina fatan dai zaka zo bari in baka adireshin gidana......"***** Ta laluba ta dauko biro daga jakarta ta dubeshi ta ce. "Ba ni littafin ka daya in rubuta maka, dan bana jin ina da takarda a motar nan, wannan rigimammiyar kuma ba ta barin a yagi littafinta". Ta dubi Zuhuriyya. Hilal ya mika mata littafin. Zainab ta saci kallonsa, ta dan kara littafin a kirjinta, sannan ta ajiye shi akan cinyarta ta rubuta masa adireshin. "To Hajiya ni zan tafi lokaci ya yi sai na zo din". "To... Hilal sai na ganka". Mutanen biyu masu kusan shekaru daya suka dubi juna, idanun kowa ya aika da sakon dake zuciyar kowa izuwa gurin kowa sannan sai suka yiwa juna murmushi. Hajiya Zainab ta ja motar tana daga masa hannu, ta nufi bangaren da (Nursery) makaranta kananan yara take. A fuskarta akwai wani tattausan murmushi na gamsuwa. Ko shakka ba ta yi akan lamarin ta san Hilal ya yi masifar kamuwa kamar yadda itama ta kamu Koda ta karawa motar wuta, sai tunanin mijinta Hamisu Jumare ya fado mata shin ko yana ina? Ta tambayi kanta.**** Lokacin da ya zo rubuta sunansa akan littafin amsa jarabawar sai ya yi mamakin ganin kalmar farko da alkalaminsa ya yi kuskuren rubutawa ita ce (Z) Hilal ya rikice saboda dalilai da dama. Wasu daga cikin dalilan rikicewarsa sune abin da ya gani a idanun Zainab. Kauna ce a gareshi ba ya ko shakkar hakan. To yaya za ta yi wannan abu kuwa ya yiwu ai bashi yiyuwa kwabar kasa da Cokali, yaushe!! Ya ya ma za a yi ace matar babban mutum kamar Alhaji Hamisu Jumare ta kaunace shi, bayan kuma har yanzu da aure a tsakaninsu. Sai kuma gayyatarsa da ta yi da sunan wai za a yi (birthday) shima ya jefa shi cikin tunani, domin ko shakka ba ya yi ya san ba bikin haihuwar yarinyar ba ce kawai ya sa ta gayyaceshi ya san akwai wani abu daban, musamman da ya dubi cikin kwayar idanunta murmushinta, dariyarta, kallonta, kai hatta motsinta duk suna nuni ne da abu daya wato So, to amma zuciyarsa ta kasa imani da hakan. Lokacin da aka tashi daga makarantar sai ya ji bashi da ra'ayin magana da kowace budurwa da ke ajinsu, ballantana ma namiji, zuciyarsa babu komai a ciki sai fatalwan murmushin kyakkyawar fuskar Zainab ne ke kai kai kawo cikin zuciyarsa, wata zuciya ta ce dashi kada ka je (birthday) din nan. To amma ya san babu abin da zai hana shi sake ganin kyakkyawar fuskar shi ya san ba daidai bane hulda da matar wani musamman ma idan ka ga kamar wani abu na shirin shiga tsakani***** To amma duk da haka zuciyarsa bata iya jurewa sai ya sake ganinta. A daidai lokacin ne to ya ji an taba kafadarsa. Hilal ya juya firgigit! A farfajiyar makarantar. "Tunanin me kake yi ne?" Rukayya ta ce dashi tana dubansa fuskarta a hade. Ta dade tana bata lokacinta akan kaunarsa, amma shi bai ma san tana yi ba. Duk da yake dai da yawa daga cikin yan matan ajinsu suna mutuwar sonsa, to amma babu wadda maitarta ta fito fili kamar ta, Hilal ya dubeta. "Ni ba tunanin da nake" "Ya ya jarrabawar ta yi sauki?" Rukayya ta tambaya. Hilal ya yi dum dashi yana kallon gabansa bai bata amsa ba. "Na ce da kai tunani kake ka ce a'a." Rukayya ta ce tana dubansa. "Me ya sa ne kika cika damun mutum?" Rukayya ta dubeshi a yatsine ta ce. "Wace ce wannan dazu ta kawo ka a mota?" Hilal ya dubeta a fusace ya ce. "Kin cika shiga harkar da ba ta ki ba, wata rana za ki yi dana-sani." ya juya a fusace ya nufi kofar makarantar. Har ya kai daf da rumfar masu gadi bai juyo ba, to amma jikinsa ya fada masa cewa idanun Rukayya a kansa suke suna kallon bayansa. Koda ya kawo ga kofar makarantar sai ya yi ido biyu da sunan makarantar "JUMARE PRIVATE SEC. SCH." Gabansa ya fadi ras!! Daga nan ya san cewa duk inda ya ga sunan sai gabansa ya fadi domin ganin sunan kamar ganin ZAINAB ne.***** Kusan duk wadanda ta gayyata gurin bikin haihuwar ya karaso in ka dauke mutum daya. Wannan mutum shi ya fi muhimmanci fiye da duk wanda ya halarci bikin a gurin Zainab. Tun kusan karfe hudu ta caba kwalliya, duk jikinta sheki yake, bugu da kari kuma ga kayan adon da ta caba reras a jikinta suna ta kyalkyali kamar amaryar indiya. Da yawa daga cikin mutanen da basu san me ake ba a gurin idan suka kalli kwalliyar da ta caba sai su dauka bikin zagayowar ranar haihuwarta ne ake, ko kuma ma bikin aurenta baki daya. Yawa- yawa bakin da ta gayyato gurin duk yan uwanta ne mafi yawa samari ne, yan kasa da shekaru ashirin, wasu kuma ashirin da biyu, sai kuma yan mata wadanda su kuma mafi yawan su malaman asibitin mijinta ne. Tuni an jera tebura da guraren zama, a gaban kowa dake farfajiyar gidan ga kayan shaye-shaye da romo nan wasu ma mutum bai ko taba ganin irin su ba ballantana ma ya dandana. A tsakiya kuma wani dan madaidaicin teburi ne lillibe da farin kyalle na leshi wanda aka kawata jikinsa da kayan ado masu kyalkyali kamar ruwan lu'u-lu'u. Akan kyallen a tsaye kamar mutum- mutumi, wani zungureren (cake) ne da aka yi shi da madara, da sauran dangogi ma'abota zaki da sa kunnen duk wanda ya shasu mikewa tsaye.***** Zuhuriyya na zaune akan wata yar karamar kujera wace aka kawata da ado. Ita ma zuhuriyya ta sha ado kamar dai mahaifiyarta Zainab. Zuhuriyya na zaune sai ta dubi wannan ta yi murmushi ta dubi wancan ta yi fari da fararen idanunta, yan samari da yan matan dake gurin suka dubeta cikin sha'awa kowa so yake ta matsa kusa dashi ya dauketa, ko kuma ya rike hannunta kawai. Abin kuma da yafi burge kowa da ba da mamaki shi ne irin yadda ta yi tsananin kama da mahaifiyarta, hancinta, idonta, bakinta, girarta, kunnenta, shan fuskarta, kallonta, murmushinta kai hatta tafiyar Zuhuriyya irin ta Zainab ce. Duk abin nan da ake Zainab bata zauna ba, sai zagaye-zagaye take tana dube-dube, amma har yanzu bata ga koda alamar Hilal ba. Misalin karfe hudu da rabi ta gaji da jira, tuni mutane har sun fara shaye- shaye da ciye-ciye. Tun karfe hudu Zuhuriyya ta yanka (cake) dinta da wata yar karamar wuka ta azurfa mutane suka dauki sowa da tafi.**** Hajiya Zainab ta gana yanke kauna da zuwan Hilal dan haka sai ta koma cikin mutanen ta fuskance su zuciyarta cikin kuna sannan ta dafa kan yar ta Zuhuriyya ta fara yi wa jama'a bayani da godiya. Nan da nan gurin ya yi tsit. Zuhuriyya na tsaye gaban mahaifiyarta tana rike da bindigarta ta roba, hannunta daya kuma rike da katuwar balam-balam, kwatsam sai ta bata shirun, ta dauki sowa ta kwace daga hannun mahaifiyarta, ta nufi bayan inda mutane ke tsattsaye da gudu tana sowa tana cewa. "Sai na harbe ka da bindigar kwali na durum!!" Tace tana kumbura baki. Hilal ya yi sauri ya dauke ta yana dariya. Duk mutane suka juya suna dubansa cikin mamaki. Zainab ta yi sororo tana duban Hilal dauke da yarta Zuhuriyya cikin mamaki. Zuhuriyya ta dubi mahaifiyarta tana murna ta ce. "Mama ga SHILAL ya zo!".***** kusan rabin wadanda suka zo liyafar sun tafi sai yan tsiraru da ke can da can su da yan matansu suna neman gindin zama. Zainab da Hilal zaune a kusa da jerin wasu yan dukus-dukus din fulawowi masu kamar lema. Har yanzu Zuhuriyya na kan cinyar Hilal tana wasa da bindigarta. "Haba Hilal ya ka yi min haka?" Hajiya Zainab ta ce tana dubansa kamar ta hadiye shi. "Ki yi hakuri Hajiya, wallahi mahaifiyata ce ta tashi jikin ba dadi". Zainab ta dubeshi cikin tausayi. "Ayya Allah ya sawwake me ke damunta ne? Hilal ya dan yi shiru yana wasa da gashin kan zuhuriyya. "Hauhawar jini ce ke damunta, ta dade da cutar dan tun ina dan karami nake jin labarin cutar"**** Zainab ta dube shi cikin tausayawa. "Allah sarki. Allah ya ba ta lafiya, idan dai ka ga cutar ta dawo sai ku wuce da ita asibiti ni kuma ka zo ka fada min". Ta ce tana dubansa "To na gode Hajiya" Hilal ya ce ba tare da ya dubeta ba. "Me ya sa kake son kirana da Hajiya? Kamata ya yi kana kirana kawai da sunana Zainab kamar yadda nake kiranka da sunanka Hilal." Ta yi masa murmushi ta kashe idanu sannan ta ce da Zuhuriyya "ke sauka daga cinyarsa, ki tafi gurin su Anti Zaliha ki gaida su" BINDIGAR KWALI--> 4 Zuhuriyya ta sauko daga kan cinyar Hilal sannan ta dubeshi ta ce. "Ina zuwa Shilal yanzu zan dawo". Ta tafi gurin wasu mata dake can gefe guda na farfajiyar gidan wanda Hilal yake tsammanin a nan Anti Zalihar da Zainab take fada take. Zainab ta dubi Hilal cikin sha'awa. Hilal ya yi sauri ya dauke kansa bai iya yarda sun hada ido ba, domin duk da kasancewarsa da namiji sai ya sami kansa yana mai kunyar hada idanu da zainab, kansa a sunkuye gabansa yana dukan uku-uku. Hakika ya san ya kamu da masifar kaunar matar da ba tasa ba. Bai kuma zargi kowa ba sai kansa, domin kuskure ne da ya yarda har matar da ba muharramarsa ba ta rage masa hanya, domin shedan na iya yin galaba akan duk macen da namijin da suka kadaice, kuma babu aure a tsakaninsu. Shirun da ya yi a yanzu zuciyarsa na bugawa, sai ya gane cewa tuni shedan ya yi galaba a kansa, domin kuwa ya san ya kamu da matsananciyar kaunar matar da ba muharramarsa ba. "Hilal..." Ta kira sunansa muryarta na rawa "Tunanin me kake yi". Ta tambayeshi Hilal ya dago kansa, sai ya ji gabansa ya sake faduwa a karo na biyu, domin koda ya kalli idanunta, ya san itama ta mace a kansa kamar koma fiye da yadda shi yake kaunarta. Irin kallon da take yi masa shi ya tona sirrin dake Zuciyarsa. Domin Hilal ya sha ganin irin kallon a cikin idanun Rukayya, kallo ne dake isar da sakon macewar Zuciya akan abin begenta. "Zainab..." Hilal shima ya kira ta a sanyaye. Zainab ta tashi tsaye sannan ta rankwafa a kan Hilal wanda ke zaune akan kujera ta dubeshi cikin kwayar idanu. Hilal ya ji hucinta na bugun fuskarsa, hakan shi ya sashi dimaucewa jikinsa ya fara rawa kamar mazari, domin tun da yake wata ya mace bata taba kusantarsa ba kusa-kusa haka. "Zainab... Mene ne?" Ya ce bakinsa na rawa. "Ka fi ni sanin ko me Hilal, dubi idanuna ka karanta sakon dake cikin zuciyata Hilal..." Ta yi shiru tana dubansa, idanunta suka yi rau-rau kamar za su zubar da kwalla. "Ban fahimce ki ba zainab, na kasa...." Ta katse shi. "Ka da ka zolayi kanka Hilal. Haba! Kada ka zama dan karamin yaro mana, kai ko makaho ne Hilal in ka shafi fuskata ai dole ne ka fahimci sirrin dake zuciyata". Hilal ya dubeta cikin kunya ya buda baki zai yi magana sai ya kasa. Zainab ta dada rankwafawa kamar za ta hada fuskarta da tasa ta ce. "Fadi mana Hilal, ai na san kaima kana kaunata, in ma kuma ba ka sona to bari ni yau na warware ma sirrin dake zuciyata ni kaunarka nake yi Hilal!!". *** Kaunarka nake yi!! Amsa kuwwar kalamanta na karshe ya sake dukan dodon kunnen Hilal, tamkar mari da kususun roba akan gadon baya. Duk da yake dai ya dade da sanin cewa Zainab son sa take, to amma abin da ta ce ya girgiza shi, domin bai taba tsammanin ma za ta bayyana sirrin dake zuciyarta ba a gareshi. "So na?" Ya tambayeta a shashance baki bude. Hajiya Zainab ta zauna tana dubansa. "Abin da na ce kenan Hilal, kuma ina nufin hakan har can cikin autar zuciyata." Hilal ya yi shiru yana tunani. Tabbas ya san ya jefa kansa cikin hadari. Ya san cewa wannan matar dake zaune gabansa, tana daya daga cikin matan manya masu fada a ji. Yanzu idan Alhaji Hamisu Jumare ya dawo ya ya zai yi da rayuwarsa? Na farko dai ya san idan mijinta ya dawo babu shi ba sake koda ganinta in ba a hanya ba. Na biyu

Chapter 1 of 7