Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 7
ya karyatashi yanzu ma ganin abin yake kamar ruda ido. Farida ya kira sunan yarsa a sanyaye akwai alamun nadama karara a fuskarsa Farida ta dago kai daga inda take ta share hawaye sannan ta fuskanci mahaifinta. Kin tabbata duk labarin nan da kika fadawa mahaifiyarki gaskiyane? Farida ta gyada kai batareda tayi magana ba. Gashi nan anyi ma agabanka Mahaifiyar farida ta fada bakinta na rawa. Na fadama tun farko baka saurareni ba dolene sai mun tashi tsaye akan yarinyar nan in bahaka ba wallahi da kyar zata auru. Alhaji ilyasu ya sunkuyar da kai kasa na tsahon lokaci yana tunani can saiya dago kai ya dubi farida yace da ita a tausashe. Ki shirya gobe zamu tafi kauye. Mahaifiyar farida ta kalleshi a rude. Akwai wani tsohon malamin mahaifinmu wai shi MALAM NA KOGO Waliyi ne nasan in Allah ya yarda ko ifiritu ne akan yarinyar nan sai ya barta Insha Allahu ai ita addu'a tafi karfin komai. Yadanyi shiru sannan saiya ci gaba da cewa. To daman in banda lalacewar zamani ma yanzu ace wai zanen kunshi ya wuce tafin hannu da sawu yatafi har zuwa kan tsaraici wannan wacce irin masifa ce yaushe za'a ace wai mace ta bude tsaraicinta agaban wani kato yayi tayi mata zane zanen banza . Alhajin yasake yin shiru akaro na biyu sannan ya juya inda farida take a takure yace. Saurara da kyau kijini daga yau sai yau kada nakara ganin kinsa wannan shegun kayan matsatstsu duk kifito min dasu zansa a kone su idan kuma kika sake na kara shigowa gidan nan natarar da gashinki awaje saina sa wanzami ya aske kan ki Ja'ira. Yana gama fadin haka sai ya dauki wayarsa ya daddanna sannan yace. Hello Alhaji Shu'aibu.... Nine dan Allah in anyi sallar isha'i saimu hadu anan gidanka zamu tattauna maganar auren yaran nan domin an sami wata yar mishkila ina ganin dole sai mun kara watanni ya danyi shiru yana sauraro. Toh shikenan duk daya ne idan kai din ma kazo. Yana ajiye wayar ne aka sake sallama akaro na biyu Wannan Karon wani saurayi ne kyakkyawan gaske yashigo dakin saidai shi anyi sa'a bashida kofato yana shigowa sai yayi turus zai koma cikin jin kunya. Ah...shigo...shigo mana Alhaji ilyasu yace lokaci guda kuma ya dubi farida. Farida ta dago kai ta dubi saurayin taji gabanta ya fadi sa'ar dataga sunyi kama da kabir dinta. Ga mamakinta saitaji tana addu'ar Allah ya rabata da wannan masifa ta wannan Aljan indai har wannan shine mijin da za'a bata to tayi dace ta fada acikin zuciyarta sannan saita sunkuyar dakai kasa a kunyace azuciyarta tana mai fatan Allah sa shima wannan saurayin bazai koma gida karkataccen Baki ba. . MAMA Motar kirar fijo tsohon yayi ta fito daga tashar ta nufi arewa dauke da fasinjoji shida. Abayan motar a zaune kusa da wani kyakkyawan saurayi mamace idanunta sunyi jajur saboda kukan da taci da kuma tashin hankali. Ga alama mutum uku ne yakamata su zauna abayan motar amma dayake kyakkyawan saurayin mai dogon hanci ya biya kudin mutum biyu sai ya kasance daga shi sai mama ne zaune aciki. Mama ta dubi agogon dake jikin wayarta karfe shida da yan mintina tuni hasken rana ya fara sallama duhun dare yafara maye gurbinsa ahankali kamar yadda suka saba akullum kwanan duniya. Daga inda mama take zaune tana iya hangen yan mata birjik abakin titin kurna asabe zuwa bachirawa wasu na tafiya abinsu me yiwuwa unguwa zasu wasu ko dauke da farantin talla wasu ko sanye da dogayen riguna da hijabi sun taso daga islamiyyar yamma. Mama taji wani bakin ciki marar misaltuwa ya mamayi zuciyarta ga mamakinta saitaji tana mai fatan inama ace tana daga daga cikin irin wadannan yara inama ace itama agaban magabatanta take da yanzu fa meyiwuwa tayi aure ko? Me yiwuwa har da ya'yama da yanzu haka tana zaune ita da mijinta lafiya cikin kwanciyar hankali babu taraddadin wani aljani ko wasu jami'an tsaro akaro na farko sai mama tafara Nadamar dukkan wani iya shege data aikata adoron kasa yanzu ina ribar irin wannan rayuwa mara manufa? Mama ta tambayi kanta nan da nan sai hawayen bakin ciki ya fara sartu akan fuskarta lokaci guda kuma tana tunanin shin ko su bebi sun karaso gidan tare da jami'an tsaron. Ita kam ta riga tasan ta tafi zuwa duniyar da bata san abinda zata tarar ba shin yaushe ne mai zai karewa tsohuwar motar? Mama ta tambayi kanta a tsorace. . Kukan me kikeyi? Wata tattausar murya ta tambayeta mama ta juyo ahankali yayinda sukayi ido biyu da kyakkyawan saurayin dake kusa da ita. Ki daina kuka komai na duniya mai wucewa ne tunda dai kina tare dani. Saurayin yace sannan sai ya lalubi aljihunsa ya dauko wani farin kyalle ya mika mata. Goge fuskarki kada hawaye yabata miki kyawunki Saurayin ya hasketa da murmushi. Mama ta dubi kyakykyawan saurayin cikin mamaki lokaci guda kuma taji zuciyarta na harbawa tsakanin hakarkarinta hakika kyakkyawa ne na gaske mama ta fara hasko hotunan mazan data taba mu'amala dasu abaya ta kasa tuna daya daga cikinsu daya kai koda rabin kyawu na wannan dake kusa da ita. Karbi mana ki goge.... Kada nima ki sani kuka. Jikinta ta rawa mama ta karbi farin kyallen ta goge fuskarta sannan ta mika masa. Nagode. Tace da saurayin. Nine da godiya ai da kika saurareni kika kuma karbi kyallen dana baki. Suka danyi shiru na yan mintina suna duban juna direban motar ya dada kara gudu domin yagama fita daga cikin gari. Ina kika nufa? Mai mujiya. Mama tace tana duban kyakkyawar fuskarsa cikin shauki. Kaifa ina zaka. Guri daya muka nufa saurayin yace cikin murmushi. Duk inda zaki muna tare don bana gajiya da ganinki. Mama ta dube shi cikin mamaki. Yanzu fa ka fara ganina. Ke kike ganin haka ni na dade da saninki...... Ina kuma kaunarki. Mama taji kamar an watsa mata ruwan sanyi. Adaidai wannan lokaci sai wani tattausan murmushi ya subuce daga bakinta tayi murna da bata jefar da layar dake makale akanta ba. Tabbas tasirin layar bokance tafara aiki. Mama uwar gaggawar tare mubarak tayiwu me yiwuwa alokacin layar ce bata fara aiki ba babu mamaki ma da tabi ahankali har gida mubarak zai sameta. Mama ta haskake kyakkyawan saurayin dake zaune kusa da ita lokaci guda kuma tana wasa da wayar tafi da gidanka dake hannunta. Tayaya daga ganina zaka fara.. . Tayaya daga ganina zaka fara kaunata? Mama ta bukata. . Haka daman abin yake kowa kinsan da irin abinda yake so baki san ana kaunar mutum ba tun ma ba'a ganin shi ba. Mama ta lumshe idanu kana ta shafi layar dake kanta awayance Kaidai fadi gaskiya yanzu danace ka aureni guduwa zakayi. Saurayin ya matso dab da ita yace Auren ki shine abu mafi soyuwa agareni gwada ni ki gani in ban aureki ba. Mama taji wani farin ciki ya lullubeta. Tabbas maganin bokan yaci ta dada jaddadawa kanta gashi ma nayi sa'a wannan yafi mubarak kyawun sura nesa ba kusa ba. Zaki Aureni? Saurayin ya tambayi mama a tausashe kamar wanda yake tsoron kada na kujerar gabansu suji. Gwada ni ka gani mama tace lokaci guda suka fashe da dariya me yiwa dariyar da takeyi ne yasa wayarta subucewa daga hannunta ta fada kasa inda kafarta take babu mamaki kuma wata gargada da motar ta fada ne. Oh wayarki ta fadi ko bari na dauko miki. Cikin dariya mama ta girgiza kai sannan tayi masa far far da idanu irin na kwararriyar yar duniya lokaci guda kuma ta dafe hannayensa tace. Bari na dauko kayata kada na baka wahala darling. Tana gama fadin haka saita sunkuya domin ta dauko wayar sannan ne to taga abinda ya tsayar da bugun zuciyarta ya kafar da yawun dake bakinta sannan yasa yasa tunaninta a rudani. Da farko da mama taga abin ta dauka wanine daga cikin fasinjoji ya ajje musu akuya akasa amma data duba da kyau sai taga ba kafar akuya bace kafar kyakkyawan saurayin da zata aura ne har da kofato kamar kafar doki. Mama ta dago kai a gigice ta kwalla ihu nan da nan motar ta hade da farin hayaki. . FADILA Da yamma misalin karfe saura yanayin garin ya sauya nan da nan gashi dai lokacin sanyi ne amma sai garin ya daure aka fara zafi. A zaune cikin dakin shakatawa na alfarma masoyan biyu ne zaune yau kwana uku kenan kacal da mayar da aurensu. Tun da suke arayuwarsu basu taba shiga farin ciki irin na wannan kwanaki ukun ba. Kullum suna tare faisal yace ba zaifita nan da can ba sai nan da sati biyu. Don haka koda yaushe suna tare da amaryarsa fadila ko dai suna tare da amaryarsa fadila kodai suna kallo ko kuma wasan ludo ko kuma wasanninsu irin na masoya masu sabon aure. . Kai ni fa nagaji da ludon nan. Faisal yace lokaci guda kuma ya aje dan kofin ludon akan faifan gilashin Fadila ta dubeshi tayi far far da fararen idanunta tace cikin shagwaba. Me to zamuyi? Faisal ya matso kusa da ita yace zauna kawai nayita kallon ki my love cikin farin ciki sai fadila ta karkace ta kwanta akan cinyarsa tana fuskantarsa. Sai kayi ta kallona har barci ya daukeni. Faisal yasa hannu yaja dogon hancinta Kada fa ka tsine min hanci don kaga yafi naka kyau ko? Ba wani nan ai wallahi nawa yafi naki kyau. Faisal yace yana jan hancin. Fadila ta tashi zaune firgigit cikin tsiwa ta wasa. Allah ya sawwake ace kafini kyau kana kallon madubi kuwa? Faisal ya mike tsaye ya dubeta da murmushi yace In ba tsoro ba ajje daki aduba madubin mana. Fadila ta zunkuda kafada tace Naki aduba dai anan ga madubi can. Faisal ya girgiza kai ban yarda ba bayan wancan madubin zo muje daki agani yana gama fadin haka sai ya ruga da gudu ya shiga daki daga cikin dakunan kwanansu na alfarma. Faisal na shiga dakin sai yayi turus cikin tsananin kaduwa. A kwance akan gadon kwanansu wata santaleliyar budurwa ce sanye da wata irin doguwar riga ta bakin gashi. Faisal bai taba ganin irin rigar ba. Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un. Faisal yace a fili sannan saiya dubi budurwar cikin hali yace. Ta Ina kika shigo mana daki kuma me ya kawo ki? Budurwar ta mike zaune akan gadon ta kashewa faisal idanu tace. Yar zaman daki ce aka kawo muku amma tun da naga baka farin ciki da zuwana bari inyi tafiyata kada ku isheni da surutu. Tana gama fadin haka saita zama farin hayaki. Adaidai lokacin ne fadila ta shigo dakin a guje tana zuwa saita rungume mijinta faisal tana dariya tace. Ilove You Faisal. Nima ina kaunar ki fadila tsahon dakiku suna tsaye ahaka can sai fadila ta dada kankame shi tace. Faisal ina son kayi min alkawari. Faisal ya dubi fuskar amaryarsa a rude yace alkawarin me? Fadila ta lumshe idanu tace Alkawarin bazamu sake rabuwa ba har abada kaga wancan karon saki biyu kayimin yanzu saura daya. Faisal ya dada janyoya jikinsa idanunsa na kan farin hayakin dake bayansu yace a tausashe. Nayi miki alkawarin ba zamu sake rabuwa ba. Fadila tayi ajiyar zuciya cikin farin ciki sannan ta kalli fuskarsa tace. Kishiya fa ita ma ka dauki alkawarin bazakayi min ba? Faisal ya kuma kallon amaryarsa ido da ido sannan ya kalli dan sauran farin hayakin da har yanzu yake makale a sararin samaniyar dakin yace da murmushin Yake. BANSANI BA ME YIWUWA NAN GABA IN AURO MIKI ALJANA. Masoyan biyu suka fashe da dariya. . KARSHE. . NAZIR ADAM SALIH Abinda Nayi kuskure a gafarceni masu karatu Mutum Ne Ni Ajizi A Aiko Min Da Gyaran Kura Kurai Na. . NAGODE SAI MUN SAKE HADUWA IN ALLAH YA NUFA. ZAYYANA 1 and 2 Littafin Nazir Adam salih (c) Nazir Adam Salih Created and design by :- Shuraih Usman . Publish:- http://shuraih.xtgem.com . This Ebook is available in our website just click here and download it , http://shuraih.waphall.com An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 7 of 7